wicked hubbin ruh, sincirely i'm so tired enough" ta faɗa haɗe da duƙewa ta riƙe guiwowin ta kamar mai yin ruku'i, da yake suna gb da in da ake zaunawa a huta haɗe da shan ice cream ko drinks idan mutum na buƙata sai kawai ya shige ya anso masu gorar ruwa guda biyu ya dawo ya miƙa mata haɗe da buɗe mata bakin gorar yana faɗin,
"Sorry ranki shi daɗe, ke ɗin ce idan kika tashi sai ki koma tamkar baby 15, kinga kuwa ai dole nayi dariya" ba tare data tanka saba ta karɓi gorar ruwan ta sha fiye da rabi, ba tare daya sarar ba tana ɗagowa ta tuttule masa sauran ajiki tana dariya don shima gorar ruwan ce a bakin sa yana sha, tsuke fuska ya yi irin ransa ɗin nan ya ɓaci ya ɗaga hannu kamar zai masgeta tayi saurin runtse idanuwan haɗe dasa hannuwa ta kare fuskarta, dariyar shima ya fashe da ita yana ɗaure bakin gorar ruwan dake hannun sa haɗe da cewa,
"2-1 ƴan mata na, ashe ma ke kura ce,ga tsoro ga ban tsoro, ai idan ramuwa ki ke son yi baza ki iya ba saboda mm ɗin naki jarumi ne, kafin ki iya rama abunda zan yi maki in sha ALLAH sai mun yi 6 -1"
"Haka kace" Ta faɗa tare da gyara mayafin ta tana kallon sa, sai daya kashe mata ido ɗaya sannan ya ce,
"Haka nace yallaɓiya ta, musamman ma idan kika shigo hannu na"
Cike da jin kunya ta sinne kai ƙasa kafin yace da ita su tafi don har ƙarfe biyar na marece ya soma yi, inda ya ajiye motar suka nufa bayan ya biya kuɗin sannan suka wuce zukatan su cike da jin daɗin lokutta da suka kashe yau tare da juna, sai daya hau titi dai-dai sanna ya juyo yana kallon yanda ta sinne kai ƙasa don tunda ya yi zancen idan ta shiga hannun sa taji wata irin kunya ta rufeta, shi yasa bata sake cewa komai ba har suka shigo cikin motar, murmushi ya yi haɗe da maida hankalin sa ga tuƙin da yake ya ɗan yi gyaran murya haɗe da ambaton sunan ta cikin wata iriyar muryar da bata san shi da ita ba, wadda sai da hakan yasa gaban ta faɗuwa tare da jin bakin ta yayi mata nauyin da zata iya amsa kiran nata da ya yi, jin bata amsa ba shi kuma ya sa ya sake juyowa a karo na biyu yana kallon ta cike da so da ƙauna don har lokacin kanta na sun kuye a ƙasa,
"Wai me nene Janany? Daga yin magana shikenan kin bi duk kin wani takura kanki, tom am sorry baza ki zo hannuna ba, ina dai wannan shine yasa duk kika bi ka wani takura kanki ko?" Yanda ya yi maganar kamar da ɗan haushi haushi a ciki ya sa murmushi ya suɓuce mata ta sa tafin hannayen ta ta rufe fuskar ta tana faɗin,
"Ka ji haushi ne?"
"Ko ɗaya, kunyar ce dai naga kamar za tayi yawa, amma ina son haka kuma don ado ce ga ƴa mace"
Bata dai ce dashi komai ba wanda hakan ya bashi damar ci gaba da cewa, "Amm..dama akwai maganar da nake so muyi dake amma kafin nan ina so na fara baki haƙuri bisa ɓoye maki asalin ko ni waye da nayi, a gaskiya banyi hakan don wani abuba sai don na samawa kaina macce ta gari da nake burin samu a rayuwa nake son ta zamo uwar ƴaƴana wacce za suyi alfahari tare da bugun gaba da ita aduk inda suka shiga, kuma alhamdulillah gaki na samu, sana'ar dabino da kike gani ba itace asalin sana'ar da nake yi ba, sana'a ce da kusan zan iya cewa gado ce dana gada daga wajen mahaifina, ita yake yi acan ƙauye kafin ALLAH yayi masa rasuwa, shiyasa nima nayi sha'awar yin ta a wancan lokacin dana fito samawa ƴaƴana uwa tagari, Janan duka labaran dana faɗa maki akaina tun farko gaskiya ne, wannan kaɗai ne na ɓoye maki kuma shima kin ji dalilina na aikata hakan, saboda haka ina fatar zaki fahimceni kuma ki yafe mun idan har kina ganin hakan dana yi ban kyauta ba"
Ko kaɗan bata wani yi mamakin jin kalaman dake fitowa daga bakin sa ba don dama ta jima tana zargin haka a zuciyar ta, musamman da Hajiya ta hakaito haka itama, sai dai ta ji zancen wani irin ban bara kwai tamkar yana zo mata a mafarki, ajiyar zuciya ta sauke haɗe da ɗago kai tana kallon sa kafin tace,
"To amma me yasa sai ni zaka zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa bayan kana sane da tarin ƴan matan dake ƙaunar ka fiye dani, kuma kasan ko waye mahaifina ba lalle ne ya iya baka aurena ba"
"Janan kenan!, ke ɗin kika fi cancanta da rayuwata shi yasa na za ɓeki, maganar gaskiya a waccan ranar da kika kaɗe ni na hango duka qualities ɗin da nake son matar da zan aura ta kasance dasu daga cikin idanuwan ki, shi yasa zuciya ta rasa zaɓin daya wuce tayi rom dake kuma ta baki kyakkyawan matsugun ni acikin ta"
"Wuɗan ne qualities kenan kake nufi?"
"Suna da yawa Janan, amma kaɗan daga ciki sun haɗa da tausayi, sanin darajar ɗan adam, kwantar da kai da yarda da kuskure, haƙuri da dai sauran su da baki bazai iya faɗar adadin su ba, wannan dalilin ya sa na manta ko waye mahaifin ki na kuma shirya wa fuskantar duk wata matsala daga gare sa ma damar za ki zamo mallaki na, zancen kuma ƴan mata da kika yi ai su suke so na ba ni nake son su ba, ke kuma ni nake son ki kuma kike so na, kinga kuwa zaɓin ranmu ya fi cancanta da mu bi ba wai nasu ba, sannan a tunanin ki duk cikin su akwai wacce zata kai ki sona balle kuma tafiki?, indai a wajen Muhammad Muhriz ne babu ta kuma baza ma taɓa yin ta ba, Janan! Ki yar da dani idan nace ke kaɗai ce maccen da tayi tasiri a zuciya ta kuma zata ci gaba dayin tasiri a ciki har abadan a ba da, ina matuƙar son ki irin son da ko mutuwa bata isa ta fiddasa acikin zuciya ta ba" ya ƙare zancen tare da juyowa yana kallon ta, tun daya fara magana take kallon sa itama ba tare data ɗauke idanuwan ta a gare sa ba har ya dasa aya, ko wace kalma da yake faɗa jin ta take yi tana sauka a zuciyar ta tamkar yanda narkakkiyar roba ke sauka akan leda tana huda ciki da wajen ta, wani irin azababben son sa ta ji na ƙara shiga dukkanin sassan jiki, ruhi da kuma ƙwaƙwalwar ta, a zahirin gaskiya jin take yi a yanzu shi ɗin mahaɗi ne na rayuwar ta da idan babu shi baza ta taɓa iya rayuwa ba,
"Tunanin me kike yi Janan?" Ya tambaya tare da hura mata iskan bakin sa a fuska, sai alokacin ta dawo daga duniyar tunanin data antaya haɗe da relaxing akan kujerar tana jin gaba ɗaya jikin ta ya mutu, sake kallon ta ya yi a karo na ba adadi tare da cewa,
"Ki yar da dani Janan, wlh babu yaudara a kalamai na idan har haka zuciyar ki ke sanar maki, banyi hakan don nayi hurting ɗin ki ba ko kaɗan, kuma ina sake baki haƙuri akan haka, pls kiyi haƙuri, idan kuma kina kina ganin yaudara ce nayi maki to zan baki dama daga yanzu har zuwa ranar ɗauri auren mu kiyi mani duk hukuncin daya dace dani, nayi maki alƙawarin ko da zan mutu zan karɓe sa matuƙar ba zai cutar damu ba"
Murmushi tayi ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa da gefen mayafin ta haɗe da cewa,
"Ko ɗaya zuciyata ba tayi tmaka kallon mayaudari balle har nasa a raina cewa ka yaudare ni, abu ɗaya ne kawai bai yimun daɗi ba shine yanda ka jurewa kyara da cin fuskar da mahaifina ya dinga yi maka bayan kana da damar da zaka iya hana hakan ta faru, gashi sanadiyar hakan tsana mai tsanani ta shiga tsakanin ka dashi, kuma sam hakan baya yimun daɗi"
Sai daya ɗan sosa gefen kansa sannan ya ce, "wannan ma kiyi haƙuri domin a lokacin na haɗu da mahaifin ki ne ba tare dana shirya yin hakan ba, na so sai mun gama dai-dai ta kan mu sai na fito da dukkanin ƙarfina a bayyane, sai gashi ya fara gani na a wannan sigar da baya buƙata, kin ga kuwa ko da nazo da asalin siga ta daga baya ba lalle ne ya iya yar da dani ba, zai ɗauka kawai nazo ne na yaudare sa ko kuma na yaudari ƴar sa na tafi, shiyasa na zaɓi da naci gaba da neman auren ki a haka har zuwa lokacin da zaki zamo mallakina, gashi kuma ALLAH ya kawo mu, ƙiris kawai ya rage muga wannan lokacin"
"Haka ne, ubangiji ALLAH ya tabbatar mana da alkhairi"
"Amin ya rabbi amarya ta"
"Kin san me kuwa?"
"Sai ka faɗa" ta ɗago tana kallon sa ta gefen idanuwa, murmushi ya yi kafin yace,
"Su Baffa fa gaba ɗaya suka je da komai da komai na neman auren mu har da lefe ma da kuma kayan na gani ina so, yanzu kawai i.v ya rage na bugo mana, ban sani ba ko akwai wasu programs da kike son yi daidai ƙarfina sai ki faɗa a saka"
"Dai-dai Ƙarfin ka a matsayin wa to, wancan mm ɗin nawa dana sani tun farko ko kuma wanda ya bayyanar mani a yanzu?"
"A matsayin mm pilot dai ba mm mai dabino ba" zaro idanuwa tayi haɗe da cewa,
"Wai kana nufin kai pilot ne ban sani ba?, A gaskiya ka shammace ni da yawa"
"Amma ai na baki haƙuri ko?, Ko har yanzu baki haƙura ba?"
"Nooo..i was so surprise me wai mijin da zan aura pilot ne ban sani ba sai a satin auren mu, badon ma nayi magana ba da nasan baza ka faɗa mani ba ai, kai Sarkin basaja ko?" Ta ƙare zancen tare da shagwaɓe masa fuska, haɗe hannayensa ya yi waje ɗaya alamun ban haƙuri haɗe da cewa
"Tuba nake yi yallaɓiya ta, dama yau nayi niyar faɗa maki komai akaina, ba ma tuƙin jirgi kaɗai ne aiki na ba, ina taɓa kasuwanci na haɗin guiwa ni da ɗan uwana Jabir, kuma in sha ALLAH har kar dabinon ma zan ci gaba da taɓawa saboda ina matuƙar son ta sosai, amma bata waccan fuskar da kika sani zanci gaba da yin ta ba, ta wata fuska daban zan yi ta idan ALLAH ya bani iko"
"ALLAH ya taimaka ya kuma ƙara buɗi mai yawa da albarka, kenan dai botique ɗin daka ce an bawa Jabir tsaro na abokin sa naku ne in na cinka dai dai, shine kuka yimun zuƙi ta malle ko?, Kun kyauta"
Dariya ya kwashe da ita yana ƙoƙarin yin parking a ƙofar tagwayen gida jen nasu da fira ta ɗauke wa Janan hankali bata san ya iso da ita ba wajen ba, ji kawai tayi ya tsaida motar yana faɗin "fito muje" ɗago kai tayi tana ƙare wa anguwar kallo haɗe da cewa,
"Hubbin ruh ina ne kuma ka kawo ni nan" cike da tsokana ya ce,
"Wurin yan kan kanu" ya bata amsa tare da buɗe mata motar ta fito tana ƙare wa tankamemen gare ɗin gaban gidan da suka tsaya kallo,
"Hey jock aside, am not going any where fa" ta faɗa bayan ta fito tare da jinginawa ajikin motar tayi folding hannayen ta,
Tana kallo ya latsa wasu lambobi a gefen jikin gate ɗin tare da da aza shacin tafin hannunsa ajikin na'urar daya siyo zuwan su China aka haɗa masa ajikin gate ɗin ya buɗe, ya ce
"Common...ƴan matana, zo mana is your home"
"Are you kidding me?" Ta faɗa tana takowa tare da ƙarewa gidan kallo cike da mamaki, lallai mm ba ƙaramin don bane, kuma ba ƙaramin so yake yi mata ba tunda har yake da tarin dukiya haka amma ya iya jurewa yin rayuwa irin ta talauci just to be with her?, Ta faɗa cikin zuciyar ta lokacin da suka shiga cikin compound ɗin gidan, mamaki bai kamata ba sai da suka shiga cikin gidan taga irin kyau da tsaruwar da ya yi, blushing kawai take yi tare da yiwa ALLAH godiya a zuciyar ta don kuwa girma kaɗai gidan Abban ta zai fi gidan da masoyin nata ya tanada wa ita,gidan ya tsari sosai kuma ya yimata kyau domin ba bu abunda zaka nema ka rasa aciki,
Ganin ta kasa cewa komai sai bin ko ina da kallo take yi murmushin dake kan fuskarta na bayyanar da farincikin dake zuciyar ta ya sa shi sakin murmushi shima haɗe da cewa,
"Janan, ki duba ki gani ko akwai inda beyi maki ba da kike so a gyara kafin akawo min ke"
Da sauri ta rufe fuskar da tafin hannuwan ta haɗe da cewa,
"Idan tsarin yayi maka to nima yayi mun"
"Kin tabbata?"
Ta kaɗa kai har lokacin fuskarta na a rufe da tafin hannuwan ta, "ina zuwa?" Ya faɗa tare da shigewa wani ɗakin sannan ya fito, ba tare data ankara ba ta ganesa a gaban ta ya dur ƙusa hannun sa riƙe da ɗan akwatin zobe yana faɗin,
"Ki buɗe fuskar ki Janan mu yiwa junan mu alƙawari acikin wannan gidan da za muyi rayuwa a tare, mu haifi ƴaƴa kuma mu reni jikokin mu aciki cewa komai rintsi komai wuya muna tare da juna baza mu taɓa rabuwa ba, za muyi tarayya a cikin farin ciki da kuma baƙin cikin junan mu, damuwar ki zata zamo tawa haka kuma tawa zata zamo taki, zamu kula da junan mu kuma zamu kasan ce abokanan shawarar juna na har abada, Janan ni nayi wannan alƙawarin tsakani na da ALLAH saboda haka ina so kema kiyi wannan alƙawari tsakanin ki dashi saboda na samu natsuwa da kuma tabbacin cewa Janan ɗina zata zamo rumfa kuma bishiyar da zata riƙe dukkanin tsatso da zaya fito daga gareni da sayyun ta"
Toshe baki Janan tayi tana ƙoƙarin hana kukan dake ƙoƙarin fitowa fita, hawayen da baza ta iya tantance ko na meye ba ta ji suna wasan tsere akan fuskarta, gaba ɗaya ta rasa ta cewa akan wannan soyayya da mm ke nuna mata, ya girmama matuƙa a azuciyarsa tare da martaba ta, cikin shesshekar kuka ta ce,
"Nayi alƙawarin zan rayu dakai zan kuma mutu dakai komai rintsi komai wuya zamu rayu da juna na har abada, zan bautu acikin gidan ka ina mai baka kulawa haɗe da yi maka ladabi da biyayya har iya ƙarshen rayuwata"
"Na gode Janan ina ƙaunar ki sosai"
"Nima haka hubbin raina" ta faɗa tare da miƙa maƙa masa hannu ya ɗora mata zoben na gold mai shegen kyau daya siyo a dubai cikin tafin hannun ta kamar yanda yaga ta buƙata ta ɗauka ta saka a yatsan ta na tsakiya a hannun ta na dama tayi kissing ɗin sa tare da lumshe idanuwa ta buɗe akan sa,
Dariya ya yi yana kallon cikin idanuwan ta data ɗago tana kallon sa ya ce,
"Do dou luv it?"
"Yeah upcouse i only you, but indeed i like the ring"
"Rilly?"
"Yeah hubbin Raina"
Ɗan shafa kansa ya yi cike da farinciki sannan ya wuce gaba zuwa wani ɗakin daya ajiye akwatunan lefenta aciki yana faɗin,
"Shiga ki duba kayan lefen ki idan da akwai abunda ba a saka ba, gani nan ina jiran ki, ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerar dining table dake jere a wajen ya fiddo wayar sa yana latsa, kallon sa tayi kamar tana shakkun shiga ɗakin, sai kawai ya tashi ya koma can cikin falon da suka baro yana faɗin,
"Oya jeki mana tunda ba cin yeki nace zan yi ba" ya ƙare maganar tare da maida hankalinsa ga wayar sa yana ci gaba da latsar ta,
A ɗari ɗari ta shiga ɗakin duk da bata da wani haufi ko kokwanto akan sa, tsaye tayi tana ƙare wa a kwatunan da sai taltalniya suke yi kallo, a kwatuna ne kusan ƙwaya goma sha biyu da tunda take bata taɓa ganin irin design ɗin su ba, ji tayi kawai ta gamsu da nagarta da kyan duk abunda ke cikin su, don haka kawai ta juya ta nufo falon tana ci gaba da mamakin tarin dukiyar da mm ɗin nata keda ita, kusan karo suka ci da ita wajen fitowa jin ta shiru da ya yi haɗe da cewa,
"Har kin gama?"
"Eh hubby ba sai na buɗe ba, it's looking so gud, nagode sosai ALLAH ya ƙara buɗi"
"Nooo..ya kamata ki gani gaskiya" ya faɗa tare da shiga ciki ita kuma tayi tsayin ta abakin ƙofa, ɗaya bayan ɗaya take kallon yanda yake zuge zif ɗin akwatunan yana wangale mata su haɗe da cewa,
"Hop wannan sun yi?" Idan ya buɗe wani shima ya sake tambayar ta wannan yayi maki, haka yayi tayi har sai daya bar baje kayan cikin ɗakin, kayan sunyi matuƙar kyau sosai fiye da tsammanin ta don sai da suka kusa sa kanta bugawa saboda yawan su,
"Ok muje na sauke ki a gida kafin Abba ya turo su Jazz suke ko jakuzze su tumurmusa ni" ya faɗa tare da jawo ƙofar ya rufe ba tare daya gyara su kamar yanda suke farko ba sannan ya nufi ƙofar fita ta bi bayan sa tana dariyar abunda ya faɗa akan su Jazz.....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/22, 10:09 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 57_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
_https://www.wattpad.com/1261231289?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=Tr8OeQ725SaUdW91Ujht1wLCXmcLn%2Fe59ZlxvMtVsT27%2FPVNf4YPcZ6tRBwzuomtI39Y%2FMFws2w6p%2BLgFUYduVRT%2FKLgRk1XDaTEEC%2FqRgaUL8w2deJiYJKwGqcVf4wu_
______________________________
Saida ya tsaya kan hanya ya yi mata sayayyar kayan maƙulashe masu tarin yawa sannan ya ɗauki hanyar zuwa gida da ita yana faɗin,
"Madam wai ya akayi yau baki je da motar ki ba"
"Mota ta ko kuma ta Abba"
"To ai ni ke nasani da ita ba Abba ba"
"Duk da ni kasani da ita, ba yawa bace tasa ce kuma ya amshi abussa"
Da wani irin shock ya juyo yana kallonta cike da mamakin jin abunda ta faɗa kafin yace,
"Kina nufin mashin kika hawo ko napep?"
"Yeah, mashin na hawo" wani irin wawan burki ya taka ALLAH ya tsare babu kowa a gabansa ya juyo yana kallon ta,
"Janan mashin fa kika ce?, Kin san yanda na tsani naga macce akan mashin kuwa?"
"Sorry hubby ai lalura ce, kuma ai kamawa tayi shiyasa"
"To meya hana ki hau napep?"
"Ban samu ba gaskiya, ga time ya yi shiyasa na hau"
"To gaskiya daga yau karki sake hawa mashin bana so, thank God kin gama school ɗin kuma kin kusa zama mallakina, ba don haka ba duk ƙaddara tasa kika sake hawa to wlh sai na kulle mai mashin ɗin" ya ƙare zancen in a serious talk tare da tada motar suka ci gaba da tafiya tana hango tsantsar kishi daga cikin idanuwan sa,
"Am sorry hubbyn ruh hakan bazata sake faruwa ba, na tabbatar maka da hakan"
Ba tare daya kalle taba ya ce,
"Better, if not zaki ja nayi ta kulle mazajen mutane ta yanda ko sun ganki a kan hanya baza suyi marmarin ɗaukar ki ba" ƴar dariya ta yi haɗe da cewa,
"In sha ALLAH hakan ma baza ta faru ba, an dena daga yau"
"Prayerd so" ya faɗa yana ɗan sakin fuska tare da juyowa ya kalleta ta lumshe idanuwa ta saukar akansa, murmushi ya saki haɗe da cigaba da riƙon ba tare daya sake cewa komai ba, sun jima a haka kafin ta ɗan muskuta ta gyara zaman mayafin ta tana jinginar da kanta a jikin glass ɗin motar dake gefenta, har lokacin shi take kallo yanda yake driven cike da gwanewa,
"Thank you so much fore everything hubbyn ruh, bansan dame zan biya ka tarin soyayyar da kake yi mani ba domin duk abunda zan baka ko zanyi bazai iya biyan ta ba"
"Kike gani?, Ai ni tun tuni kin biya ni tunda kika amsa tayin soyayya ta, tukuici kaɗai ne ya rage ki ƙara mani dashi, shi kuma na barshi har sai munyi aure"
"ALLAH ya nuna mana"
"Amin ya rabbi"
"Amm.. sorry to ask you, ɗazu kace har lefe su Baffa sun wuce dashi, yanzu kuma ga wani ka nuna mani, hakan na nufin lefe biyu kenan kayi..." Tun kafin ta rufe baki ya kwashe da dariya tunowa da yanda kayan suke da kuma irin dariyar da Jabir ya yi ɗazu, girgiza kai ya yi haɗe da cewa,
"Sorry Janan, ki ɗauka kayan da su Baffa suka kai tsaraba ce dana yo maki daga ƙauye bawai lefe ba, kaya ne da ƴan uwana suka haɗa mani daga ƙauye in ƙara a lefe na a matsayin tasu gudummawar, shiyasa nayi amfani dasu a matsayina na mm mai dabino kamar yanda suka sani na kai maki su a matsayin lefen ki, kuma ina fatar zaki karɓe su hannu biyu" ya ƙare zancen yana dariya,
Dariyar itama ta shiga yi duk da bata ga yanda kayan suke ba, sai da tayi mai isar ta kamar yanda yake yi shima don ita dariyar tasa ma ke ƙara sakata yin wata dariyar sannan ta ɗago kai haɗe da cewa,
"Hubby kenan! ALLAH baka da dama, any way Ina ƙara miƙa godiya ta to both of you Kai da kuma su Baffa, ko da ace su ne kaɗai abunda ALLAH ya hore maka da zaka iya yimun a matsayin lefe, i must like it and appreciate for it, so ka ɗauka ma har na karɓe su hannu biyu cike da mutuntawa da kuma farinciki"
"That's my wife, shiyasa nake ƙara son ki, you're not after any money or lexuries, thank you so much for being apart of my life"
Da haka suka ƙara so gida ya ajiye ta tare da miƙa mata ledar kayan maƙulashen daya siyo mata yana faɗin,
"Kar ki manta, gobe idan zaki je school ki kirani sai na ajiye ki, ban yarda ki hau mashin ba kin ji na faɗa maki ko?" ya ƙare zancen yana sake kokon ta mata maganar, cike da zolaya ta karɓi ledar tana faɗin,
"To napep fa?"
"Bana buƙata itama, kawai ki kirani" ya tada motar sa ya bar wajen ba tare daya tsaya saurarar amsar da zata bashi ba saboda ankusa kiran magrib,
Tana ƙoƙarin shiga ciki motar Hajiya na fitowa Ado ya ɗauko ta zai maida ita gida don tayi jiran dawowar Janan ɗin har ta gaji, a hankali ta saukar da glass ɗin motar lokacin da suka kawo kusa da Janan ɗin tana faɗin,
"A ina kika tsaya haka na zauna zaman jiran ki tun ɗazu baki dawo ba, ina ƙarfe huɗu da mukayi waya ɗazun kika ce mani zaku gama jarabawa?"
"Eh Hajiya, ina wuni?"
"Lafiya klw, meya tsaisheki har wannan lokacin nake tambaya"
"Mm ne ya ɗauke ni muka je wani waje, ki bari zan kira ki anjima in baki labari ko kuma idan mun ƙare jarabawa gobe sai nazo musha fira abun mu, don kuwa hasashen ki ya zamo gaskiya"
"To ALLAH yakai ranmu, amma kiriƙa lura Janan, kidena bari kuna kai irin wannan lokutta tare duk da dai bana da wani haifi akan Muhammadu, amma sheɗan da kike gani babu wanda yafi ƙarfin sa sai wanda ALLAH ya kare, musamman tsakanin macce da namiji akwai haɗari sosai kasantuwar su waje ɗaya koda kuwa muharraman juna ne"
"To Hajiya, in sha ALLAH zan kula daga yau kuma hakan baza ta sake faruwa ba"
"ALLAH ya nufa, maza jeki bana son ayi sallah ina kan hanya"
Har Ado ya ja motar tayi saurin dakatar dashi tare da leƙowa ta jikin tagar gefenta ta tsaida Janan,
"Yawwa idan kika shiga akwai kaya na nan da iyayen Muhammadu suka zo dasu, kayan rabawa da kuma na lefe, na so naje dasu amma bana son abun yazama tsegumi agun Abban ki shiyasa na bar su, ki faɗawa Madam frorence.."
"Kai Hajiya Florence take ba frorence ba" Janan ta katseta tana dariya,
"To koma dai wa take kice nace a ɗauke su akai part ɗin Auntyn ku idan Abban naku baiwa a kaushe su daga wajen ba, don nasan halinsa tsab zai iya barin kayan a walaƙance a wajen tunda ba kirki ne dashi ba"
"Kai Hajiya, ba kyau fa cin fuska"
"Mtsss...yo ni ina ruwana, ba cin fuska ba ko cin ƙafa sai nayi maku, jeka muje kaji ado" ta ƙare zancen tana bawa Ado umurni tare da ɗage glass ɗin motar data saukar ya ja sukayi gaba, dariya Janan tayi haɗe da ware hannayen ta sama tana shaƙar iskan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 40