Share this page
ya haɗu da ita bai ce yana son ganin ta ba, idan kuwa hakan ta faru ba ƙaramin farinciki zata yi ba, don yanda Janan tayi kyau ɗin nan bata fatar su haɗu da mm ɗin ta, Ai kuwa hakan ta faru don ba kunya suna rufe baki Ingaski ya ce Janan ta biyo shi office ɗin sa, ji tayi kamar ta ɗora hannu saman kai ta ƙwalla ihu haɗe da juyowa ta naɗawa Amira duka a kafaɗa kamar za tayi kuka ta ce, "Wlh duk sherin ki ne Amira, sarai kin san malamin nan baya biya ta da alkhairi amma ki tsiri gaishe sa, gashi yanzu kin jamun ko banai wa ALLAH dole naje tun da banda hanyar guduwa" "Ikon ALLAH! Yau ni naga ƙarfin hali, to sai na fasa gaida malami na saboda ke bakya shiri dashi?, Ina kika ji an taɓa haka? Ban da abunki ma ina laifin wanda ya ce yana son ka?" Ta ƙare maganar tana dariya, don kuwa gaba suke da office ɗin nasa, duk yanda Janan taso guduwa hakan bazai yuyu ba, harara ta maka mata haɗe da yarfar da hannu kafin tace, "Baza ki gane ba Janan, wlh ni zuciyata tana da wanda take so, bance ya yi laifi ba, amma tunda ya ga bana sonsa ai sai ya haƙura dani tunda bani kaɗai ce macce ba a school ɗin nan" har lokacin Amira na dariya ta ce, "Ehm, yanzu dai jeka kada yaga kin daɗe, ni naje nayi maki order ɗin abinda zaki ci daga nan na biya na karɓo maki saƙon ki a wajen mm" Tsabar takaici Janan bata tsaya bi takan taba ta nufi office ɗin nasa tana mai ƙudurta abubuwan da zata faɗa masa a zuciya, ita kuma ta buga tsalle haɗe da kimtsa kanta sosai sannan ta nufi wajen su mm zuciyarta cike fal da farin ciki, Fuska a tirniƙe ta shiga office ɗin nasa babu alamun fara'a ko kaɗan a tare da ita tayi tsaye a bakin ƙofa ba tare da ta ce komai ba hannayenta na akan ƙirjinta rungume da wani practical text book data karɓa hannun class rep ɗin su da zasu fito, Murmushi Ingaski yayi haɗe da cire glasses ɗin idanuwan sa yana ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, yayi mintuna biyar a haka kafin can ya ce, "Gimbiya Janan ƙaraso daga ciki mana" ya ƙare magana yana wani kasar baki haɗe da kwantawa baya akan kujerar da yake zaune, sai da ta furzar da iska abakin ta haɗe da juyar da kanta gefe sannan ta ce, "Malam gani, ka faɗi mun dalilin da yasa ka kira ko.." bata ƙarasa ba taji yake, "Tsaya Janan, ai kinsan labarin gizo dai bai wuce ƙoƙi, har yau dai na kasa haɗiye yawuna akanki, gashi kwana biyu kinyi mani wuyar gani, ina kika shige ne haka?" "Shikenan malam?" "A'a gimbiya Janan, idan akwai wani abun ma ai sai kin shigo daga ciki za muyi magana a kan sa, ko kin fi so ne ni da kaina na taso muyi maganar anan?" Ya ƙare maganar haɗe da miƙewa ya nufo wajen da take tsaye, ba tare data ankara ba sai dai ta ji hannunsa sama kafaɗarta yana murzawa, ƙoƙarin ƙwacewa ta shiga yi kawai taga ya nufo da fuskarsa zuwa saiti wuyanta yana ƙoƙarin sumbatar ta, cike da ɓacin rai ta ɗago hannu ta wankesa mari tare da turesa gefe tana hawaye, cikin kuka ta fara magana haɗe da cewa, "Tir!, wa'iya zubillah da wannan rayuwar, meye ribarka malam idan kayi ƙoƙarin lalata wa yarinyar daka kusa haihuwa rayuwa? Wannan itace amanar da iyayen yara ke damƙawa a hannun ku bacin duka sun tattara yardar su da kuma yaƙini akanku cewa zaku kula masu da ƴaƴan su tamkar naku? Ina girman malan takar da kake iƙirarin kana da ita a kaina?, a ina so da ƙauna suka samu gurbi a zuciyar dake da irin wannan mugun nufi acikin ta?, Ina..." Da sauri ya ɗaga mata hannu cikin ɓaci rai yana zaro mata idanuwan sa da suka kaɗa suka yi jajir haɗe da nuna mata ƙofar fita da hannu yana faɗin, "Fice mun daga office Janan, zan gwada maki cewa lallai kinyi kuskuren yin shuka a gonar mai hauya, kuma daga yau ki fara ƙidayar kwanakkin baƙin cikin ki acikin makarantar nan, don sai na sa kinyi nadamar zuwan ki cikin ta, kin kuma yi nadamar wannan kyawon da kike dashi da har yake saka ki iya ɗaga hannu ki mari malamin ki, idiot gerrout in my office" ya ƙare maganar cikin ɗaga murya da ƙarfi har sai da ta ra zana, da gudu ta fice daga office ɗin aguje tana kuka... #comment #vote #share. *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 13_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1233714499?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=%2FZCXoGlLdbifSbATAz2UeuNRbhPFrpZVPNq3kNLZza%2FgPkeFJV9VLz7dzW3EBnlU9nks2qvKGiGfL2Iho68XT3LgMsgq%2BngDoogWVxyZOE9%2BipwLz1FYqd1pacbjPKT0_ *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B* INA KUKE MAKARANTA?? INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️ TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI. DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA (1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_ 👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 +447894142004 07065283730 ______________________________ *B* ata tsaya ko ina ba sai a can bayan science theater in da suke ɗaukar lectures wani lokacin ta ci kukanta mai isarta sannan tayi shiru ta goge fuskarta da nan take ta yi jajir haɗe da bayyana halin da take ciki, haka ma idanuwanta da suke farare ƙal sai da sukayi ja har wata 'yar siririyar jijiya na ratsawa ta tsakiyarsu, cikin natsuwa da damuwar dake faman nuƙurƙusar zuciyarta ta nufi wajen su mm, don gaba ɗaya ma ta manta da zancen Amira ta ce zata karɓar mata, murmushi ta fara ƙoƙarin ƙaƙarowa lokacin data ƙara so wajen haɗe da kallon sa ta ce, "Sannun ku mm, kayi haƙuri kaga ban ƙara so karɓar saƙona ba sai yanzu ko?" "Eh, akwai wata yarinya da nake ganinsu tare tazo ta karɓar, amma me yake faruwa dake ne haka Janan?" Ya faɗa yana kallon cikin idanuwan ta haɗe da ƙare mata kallo, sun kuyar da kanta tayi tana jan majina a hancinta haɗe da cewa, "Bari inje muna da practical yanzu" ta juya har lokacin kanta na sun kuye a ƙasa, cike da damuwa mm da gaba ɗaya duk hankalinsa ya bi ya tashi ganinta cikin wannan yanayin tare da miƙa hannu alamun tsai da ta kamar zai yi kuka, ya ce "A'a Janan, kada ki tafi cikin wannan yanayin hakan, don ALLAH idan zaki iya ki faɗamun me yake faruwa ne?" Cak ta tsaya wasu zafafan hawaye na zo mata, haka kurum taji ta kasa yimasa musu ta tafi, a hankali ya juyo yana kallon Jabir fuskar sa ɗauke da damuwa ya ce, "Jabir bani mintuna biyu ina zuwa?" Ya kaɗa masa kai don shima bai ji daɗin yanayin da yaga Janan aciki ba, sai daya fara zuwa wajen wata mata dake kusa dasu dake sayar da kunun aya da ruwan sanyi ya karɓi ƙwayar ɗaya sannan ya nufi wajen da take tsaye ta sinne kai har lokacin tana kuka ya miƙa mata ruwan, "Ungo wannan kisha don ALLAH ba don ni ba Janan" ba musu ta karɓa ba tare data ɗago kanta ba ta fasa ladar ruwan ta sha sosai haɗe da cewa, "Na gode" cikin muryar kuka, sake rikicewa mm yayi yaji kamar ya buɗe zuciyarta ya yaye mata ɓaci rai da ƙuncin daya saka ta cikin wannan yanayin, amma da yake baya da hurumin yin hakan sai kawai ya kalli can tsallake titi inda guiding luv ɗin makarantar yake, ya ce "Ko zamu iya zuwa can?" Ya ƙare zancen yana nuna mata wajen da hannu, ganin bata ce komai ba ya sa kawai ya wuce gaba ta bisa baya suka nufi wajen, Ɗaya daga cikin kujeru dake wajen ya nuna mata ta zauna shi kuma ya jingina ajikin iccen dake fuskantar kujerar yana kallon yanda take wasa da hannun ta, don agaba ɗaya jin ta tayi wani iri kasancewar su a waje ɗaya tare kuma alokacin da batayi tsammanin hakan zai faru a tsakanin su ba, ji tayi yayi gyaran murya haɗe da cewa, "Kiyi haƙuri Janan ina neman shiga rayuwar ki duk da irin tarin banbancin matsayi dake tsakanin mu, ban san me yasa nake son Jin damuwar ki ba, wataƙil saboda iri tarin damuwowi ne dana fuskanta a rayuwata, shiyasa bana son ganin wani cikin damuwa ko kaɗan, musamman macce, maccen ma irin ki mai matuƙar hankali da natsuwa da sanin kimar ɗan adam, Ni maraya ne dana taso cikin halin talauci tun ina ɗan shekara sha huɗu ni da ƙanwa ta, shi yasa na fuskanci ƙalubalen rayuwa kala kala da a halin yanzu nake tunanin zan iya magance duk wata damuwa da zata fuskan to rayuwar mu, ina roƙon ki da don ALLAH ki bani damar sanin damuwarki kema, wataƙil zan iya taimaka maki kema ko da da shawara ne mu magance ta" Sai da tasa hannu ta share hawayen da har yanzu ta kasa tsaida su sannan ta ɗago fuskar ta tana kallonsa, "Damuwa ta damuwa ce irin wacce baza ka iya magance ta ba mm, idan ma ka magance mani ita akwai 'yan mata da yawa ire-irena dake cikin irinta kuma suke buƙatar maganin ta, musamman waɗan da suke da raunin zuciya da kuma arziƙi, su kuma waye zai iya magance masu ita?" "ALLAH!, ALLAH zai magance masu ita mana koda taimakon wani iri na ko babu" shiru ta sakeyi har lokacin tana wasa da hannunta haɗe da jan majina kafin tace, "Idan haka ne kuwa zaifi kyau ka tayani da addu'a fiye da kasan damuwata, don bazaka iya magance mani ita ba" "Na ji, amma ai zan iya baki shawara ko? Ko baki yarda dani bane?" "Ko ɗaya mm, a nawa tunanin dai ba a yi ciki kawai don cin abinci ba, anyi sa ne har da don ɓoye wasu sirrukan rayuwa a cikinsa, iya wannan kulawar daka nuna mani ta rage mun sama da kaso arba'in cikin damuwa ta kuma na gode sosai da hakan" Ji mm yayi ta ƙara burgesa, don kuwa yana son mace mai iya riƙe sirrin ta, ko da wannan halin kaɗai aka tsaya Janan ta cancanci zamowa matar sa, saboda yasan matuƙar yayi sa ar mallakarta a matsayin mata, ba ya da wani sauran haufi a rayuwa, don kuwa zata riƙe masa sirrin gidan sa ɗari bisa ɗari (abun da yayi ƙaranci kenan ga mafiya aksarin matan aure yanzu, sai kaga macce har jira takeyi ace meke faruwa da ita ko meke faruwa a gidan ta?, Jiki na rawa zata buɗe baki tamkar ruwa a kwando tayi ta zuba tana romawa kanta, mijinta, iyayenta da kuma 'ya'yanta asiri saboda tsabar rashin sanin ciwon kai, wannan ɗabi'a ba mai amfani bace saboda haka mata mu kula mu kiyaye don ALLAH👏), ɗari kai yayi haɗe da sake son jaraba ta a karo na biyu ya ce, "Shikenan Janan, ina ga dai ban cancanta bane kawai naji saboda banbancin matsayi dake tsakanin mu" "Ya Salam! Ba haka bane mm, ai babu wani banbanci dake tsakanin ni dakai, kai mutum ne nima haka, kana da ido da baki, ƙafa da hannuwa, zuciya da kuma rayuwa, nima kuma haka, to meye banbancin mu?" "Arziƙi mana, kin san shi da daban ne, dole wanda ke dashi yaga yafi kowa" "Hmm! Ai wannan shirmene mm, ai ALLAH daya halicce mu gaba ɗaya cewa yayi _inna akramakum indallahi atƙakum_ saboda haka don mutum nada arziƙi bazai ce yafi wanda baya da shi ba, shi kuma wanda baya dashi bazai bari ya zama koma baya ba har a nuna masa an fishi saboda an ɗaya shi tarin arziƙi" "Haka ne kuma" "To ka cire wannan tunanin ranka, idan ma har haka ne to Ni ba haka nake ba, kuma kada ka ƙara yin wannan tunanin a kaina sai in so kakeyi mu samu matsala" "ALLAH ya baki haƙuri Hajiya Janan na daina, amma don ALLAH ko meye damuwarki ki cireta aranki, ki ɗauka babu abunda yafi ƙarfin ALLAH, kuma ina sha ALLAH zai magance maki ita" "To shikenan, ina fatan hakan mm, Na gode sosai da kulawar ka" ta faɗa tana murmushi, Ɗan sosa kai yayi tare da kauda kai gefe yana tunanin kuma me ya kamata ya sake cewa kafin ta tafi, ganin yayi shiru ya sata miƙewa tana faɗin, "To Bara naje ko? Yau dai nayi missing practical ɗin nan, sai dai kuma wani lokacin" ta ƙare zancen tare da gyara jikkarta tana ƙoƙarin barin wajen, da sauri yayi saurin dawowa hankalinsa tare da furta kalmar "Janan!" Ta juyo a hankali tana kallon sa haɗe da son jin ƙarin bayanin kiran sunan ta da yayi, "Ammm..dama cewa nayi ko zaki rage mun hanya anjima kafin ki tafi" sai da tayi murmushi sannan ta ce, "Me zai hana?, Sai dai ai ba a lokacin kuke tashi ba ko?" "Eh, ina son na siyo wani dabinon ne acan hanyar Umaru musa ƴar aduwa saboda nawa ya kusa ƙarewa, kuma naga kamar tacan hanyar ne kike bi ko?" "Eh, amma gaskiya ɗauke wa nakeyi ta gefen sabuwar kotu sai dai in abakin junction zan ajiyeka ka ƙara sa da ƙafa" ta ƙare zancen cike dazolaya don tasan irin ƴar tazarar dake tsakani, murmushi yayi yana sosa kai haɗe da cewa, "Hakan ma yayi Na gode" "To shikenan, ka ajiye mun TUKUICI na kafin lokacin?" "An gama" ya faɗa yana dariya suka fice suka bar wajen, a ransa yana tunanin a yanzu kam ya samu damar da zai iya bayyana mata sirrin zuciyarsa, Kai tsaye class ta wuce yayin da shi kuma ya wuce wajen sana'arsa haɗe da labartawa jabir yanda sukayi da ita, ya ƙara da cewa, "Sai dai ni jikina na bani kamar akwai wani abu daya faru saboda acadamic staff na hango ta zata shiga lokacin da suka taho da wannan yarinyar data karɓar mata saƙo, koma meye ni zan bincika da kaina saboda idanuwanta kaɗai sun nuna tsantsar tashin hankali da damuwar da take ciki" "Gaskiya kam, saboda ban taɓa ganin ta cikin irin wannan yanayin ba, ALLAH dai ya kyauta" "Amin" mm ya faɗa jiki a sanyaye, duk da wani fanni na zuciyarsa cike yake fal da farin cikin haɗuwar da zasuyi anjima da ita a motarta... #Comment #Vote #Share. *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU,👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 14_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1233959240?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=CIJYgmhi776%2BnnC4B%2B%2FCSfdTZpAd04jyXncfT8AJjOvZn6at4oFzZrrDfti9TiRh9kffXULjBpugj9SDRmWDA4883O%2FuXH72ENtBOM4g%2ByKpFAI%2FNyUCdzUj7O%2FCW60P_ *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B* INA KUKE MAKARANTA?? INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️ TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI. DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA (1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_ 👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 +447894142004 07065283730 ______________________________ Janan kuwa ko data koma class ta tadda har an kusa ƙare lectures ɗin da aka shiga bada ita ba, bata fi mintuna goma da shiga ba malamin ya fice, juyawa tayi wajen Amira tare da miƙa mata hannu ma'ana ta bata sauƙin ta data karɓo mata wajen mm, Wata baƙar leda Amira ta ɗauko dake gefenta ajiye tare da ɗari biyar ta miƙa mata tana faɗin, "Ina kika shige tun ɗazu?" Bata ce mata komai ba ta amshi ledar tana kallon tarin dabino da kwakwar dake ciki, shi kansa dabinon kaɗai yakai yawan gwango huɗu, kwakwa kuma ƙwallo biyu, ga kuma ɗari biyar ɗin data bashi ya dawo mata da ita, kallon Amira tayi cike da mamaki ta ce, "Ya naga haka Amira? Kema kin ƙara siya ne aka haɗe mana ne?" "Kamar ya? Ni dai haka ya bani yace in kawo maki, halama bana daidai kuɗin ki ba ne?" Har zata ce wani abu sai kuma tayi shiru tunda tasan anjima zasu haɗu, sai ta tambayesa dalilin da yasa zai kwashe kayansa haka ya bata kuma yaƙi karɓar kuɗi, 'yar ajiyar zuciya ta sauke haɗe da kallonta ta ce, "A'a ba haka bane, am just asking" "Yawwa, amma kin san wani abu?" "A'a sai kin faɗa" ta ƙare zancen tana jefa dabinon data kwanɗara a baki, "Hmmm..Wannan Jabir ɗin na tare dashi baya da mutunci wlh, wai kamar ni zai kalla ya ciwa mutunci a gaban mutane hadda faɗin na jaye na ba mutane waje na je na tsare su da idanuwa kamar na mujiya, wai idan ban tashi yin abunda ya kawo ni ba to naje naba customer ɗin su waje! Kin ga kuwa yanda ya yarfa ni wajen aka dinga yimun dariya?, wlh ALLAH ba don mm ba da sai na tata masa rashin mutunci daidai na kuɗinsa talakan banza talakan wofi" "To fah!, Iko sai ALLAH, shi talaka bai da ikon yin magana idan aka yimasa ba daidai ba?, Ashe duk ƙarya ce ranar kike yi da kika dinga masifa akan na kaɗe mm nazo nayi zamana a class don bansan darajar ɗan adam ba, yanzu ke wace daraja kika nunawa ɗan adam da kika kirasa da talakan banza talakan wofi?" "Hmmm Janan kenan, ai bazaki gane irin renin hankalin da gayen nan yayi mun ba ne" "Naji, bai kyauta ba amma ai wataƙil gaskiya ya faɗa, don in har bakiyi ba bazai ce kinyi ba" "Ok, kina goyon bayan sa kenan?" "A'a, ina dai goyon bayan gaskiya ne, akwai cutarwa ka ai bata mutum da yanayin da ALLAH ya jarabce sa da zama ciki, talauci ba shi ya zaɓawa kansa zama cikin sa ba, balle ki goranta masa" Dariya ta kwashe da ita kafin tace, "To Malama Janan naji!, irin wannan haƙiƙan cewa da kike yi hakan, kodai kodai?" Itama dariyar ta yi tana ci gaba da jefa dabinon a baki haɗe da cewa, "Rufamun asiri Amira, ni kuwa taya zan iya haɗa taura biyu a baki?" "Ban gane ba?" "Ta so dawo nan kisha labari, nasan da kanki zaki gano cewa kinyi kuskuren furta wannan zancen" Ta ƙare zancen tana nuna mata gefen kujerar da take zaune, da yake ALLAH yayi wa Amira son jin gulma ai kuwa ta taso har tana cin tuntuɓe ta dawo wajen tana faɗin, "Bani nasha ƙawata, kin san ma kuwa tun ɗazu nake son na tambaye ki ya kuka ƙare ke da mutumen ki, tun da kika shigo naga sauyi a fuskarki kamar kinyi kuka" "Ke manta dashi, mezan faɗa maki?" "Ina jinki" "Nifa mm na burgeni sosai, kuma wlh da yau zai furta kalmar yana so na to babu abunda zai hana na na amince masa kuma na auresa, seriously ƙawata bazan ɓoye maki ba ina matuƙar ƙaunar sa" Wani irin daram daram gaban Amira yayi tare da turo idanuwa waje jin kalmar dake fitowa daga bakin ƙawarta kuma aminiyarta akan namijin da take tunanin shine zaɓin ta kuma mafarki ta akoda yaushe, cikin tashin hankali ta ce, "Shi mm ɗin?" "Yes, upcouse! shi yasa kika ji nace bazan iya haɗa taura biyu a baki ba, a yanda zazzafar ƙaunar mm ke nuƙurƙusar zuciyata, bazai yuyu ba ace na faɗa soyayyar amininsa ba kuma" Cikin wani irin yanayi na tashin hankali, ƙunci, baƙin ciki, ƙunar rai da kuma hasada ta ce, "Janan bakya ganin yin hakan agareki babban kuskure ne? Mm fa bai aje komai ba kuma bai bawa wani ajiya ba, da ganinsa kin san shima takan sa yakeyi, to taya zai iya ajiye babbar yarinya mai aji irin ki?, Taya zai iya baki kula da gata irin wacce mahaifinki ya reneki kuma kika yi rayuwa ciki?, kar fa ki manta da ko waye abbanki?, Abune mai matuƙar wahala a garesa ya iya yar da da wannan zancen naki, zai ma iya sakawa a ɓatar masa da..." "Dakata haka Amira ya isa don ALLAH, waye mahaifi na da wace irin gata na taso cikinta duk basu da alaƙa da soyayya ta, matsayin mahaifina daban, rayuwata daban haka kuma soyayya ta daban, nice da hurumin zaɓawa kaina abokin rayuwa matuƙar yana da dukkanin sharuɗɗan da Musulunci ya gindaya ga irin namijin daya kamata a bawa aure, don haka ko kare nace zan aura babu mai hana hakan faruwa in ba matuwa ba, samu ko kuma rashin mm da kike zance ni duka basa gaba na, abu ɗaya ne kawai mai muhimmanci agare ni, shine mm ya furta yana so na kamar yanda nake son shi, idan hakan ta faru shikenan banda damuwar duk wani tarnaƙi ko matsala da zan fuskanta" A fusace Amira ta miƙa saboda ɗacin kalaman ta da take ji haɗe da cewa, "Tabbas kuwa kin ɗauko dala ba ganwo Janan, kuma zaki tafka kuskuren da baki taɓa tunanin zai haifa maki ɗa marar ido ba, sannan ni Amira bazan goyi bayan ki ba ki jefani a matsala, oh wannan shine dalilin da yasa kike walaƙanta Ingaski duk biyar da yakeyi maki, kina nema ki shafa mani baƙin fenti da kashin kaji a wajensa, to wlh bazai saɓuba wai bindiga a ruwa" tana kaiwa nan ta wuce fuuu..kamar zata tashi sama, Baki sake Janan ta bita da kallo tana mamakin irin wannan haƙiƙancewa da tayi, to wai meye nata aciki don ta ce tana son mm, ina ruwanta da rayuwar ta ko kuma matsalar gidan su, shi yasa bata fiye faɗar matsalolin ta ga mutane irin hakan ba, saboda kowane mutum da irin tasa fahimta, "ALLAH ya kyauta" ta furta a zahiran ce tare da tura sauran dabino da kwakwar ta a jikka, kasancewar har anyi sallar azzahar kuma basu da wata lecture bayan ta yasa ta wuce masallaci ta fara yin Sallah sannan taje ta jawo motar ta don ta tafi gida, daidai wajen sana'ar su mm ta tsaya tare dayin horn, dama ita kaɗai mm ke jira don haka yana hango ta da sauri ya tsallaka bayan sunyi magana da Jabir akan zai iya wucewa gida idan yaga bai dawo ba saboda yana tunanin biyawa ta office ɗin su anyi masa waya ana neman sa, fuskarta ɗauke da murmushi ta miƙa hannu ta buɗe masa marfin ɗaya gefen dake gaba tana faɗin, "Shigo muje to malam mm" murmushin shima ya sakar mata daya kusan sa zuciyarta narkewa, da sauri ta ɗauke kai daga kallon da take yimasa ta juyar gefe gabanta na faɗuwa, kusan a tare suka ce, "Barka da rana" lokacin da take ƙoƙarin tayar da motar, Sai da tahau titi da kyau sannan ta ce, "Ina wuni mm ya kasuwa?" Ba tare data juyo ba. "Alhamdulillah Madam, ya karatun kema?" Ya bata amsa yana wani kakkama jiki ala tilas sanyin a.c yake ji, kasancewar tana kalle dashi ta gefen idanuwa yasa tayi dariya tare da miƙa hannu ta kashe makunnin gaba ɗaya tana faɗin, "Karatu alhamdulillah, yau kuma nice Madam" "Eh mana, ai girmanki ne hajia, ranki shi daɗi" "A'a fa, a'a fa mm kar mufara hakan dakai don ALLAH, wane Hajiya da Madam ana zaune ƙalau?, Don ALLAH dai kadena bana so" takai zancen daidai lokacin da suka fito gate tana ƙoƙarin hawan titin daidai don makarantar akan babban titi take. Saida suka hau titin daidai ta fara tafiya tana bin ƙira'ar sudais dake tashi cikin motar tukuna mm ya ce, "To ya kike nariƙa ce maki, sunan nan dai naki faɗuwar gaba yake sani aduk lokacin da na ji sa, idan kuma ni nakira sai naji bakina yayi wani irin kamar kowa ya fini iya faɗarsa" "Tab ni kuwa kaga sunan mm daɗi yake yimun ina matuƙar samun nishaɗi idan naji ana kiran hakan" da mamaki ya juyo fuskarsa yana kallon yanda tata ke fitar da wani annuri haske dake bayyana labarin dake cikin zuciyarsa, daidai lokacin kuma tana ƙoƙarin karya hannunta a kwantar da zasu shiga su miƙa, ƙara faɗaɗa murmushin ta tayi lokacin da ya shiga kwanar haɗe da cewa, "Wannan kallo haka mm lafiya?" Firgigit ya fito daga duniyar tunanin daya shige tamkar wanda ya tashi bacci tare da kauda kansa gefe daga kallon da yake yi mata ya ce, "Mamaki nakeyi yanda haruffa biyu (mm) ke daɗin faɗa da kuma saka nishaɗi, shiyasa nake kallonki inji taya hakan ta faru?" "Sirri ne wannan, tunda kai haruffa biyar na kalmar Janan na yimaka nauyi a baki" "Amm... Kin fa wuce wajen da zaki ajiye ni" ya faɗa yana basar da maganar da tayi, "Ina sane, ina so ne in ƙarasa ajiye ka acan inda zaka yi sayayyar taka, ni kuma sai na ɗauke ta ɗayan titin da zai sa dani da hanyar zuwa gida" "To shikenan, ina gode sosai" "Godiyar nan ta isa haka mana, a fara bada tukuicin da akayi alƙawari tukuna sai ayi wannan godiyar itama a bada tukuicin ta" ta faɗa tana miƙo masa hannu, "Faɗi duk abunda kike so, zaki samu" "Shike nan, kai ka fara faɗar abunda zaka bani ko kuma ka bani na gani, idan yayi mun kaga ka hutar dani da faɗar ko me nake so?" Sai da yayi 'yar dariya tare da ajiyar zuciya

Chapter 8 of 40