za'a sama maka shi" yana rufe baki ya tafa hannu sau biyu sai ga masu aikin hotel ɗin duka sun iso wajen, cikin bada umurni ya ce,
"Iska ya yi kaɗan ga mahaifin ango mu da amarya, don haka za a iya ƙara gudun na'urorin ɗakin" kamar jira suke ya gama bada umurni nan take duk suka rarraba zuwa wajen maku nan na'urorin a.c dana fanka, kan kace me tuni yanayin sanyin wajen da ƙamshin sa ya ƙara sauya wa, ɗari kai Abba ya yi ya kalli Jabir da kyau kafin ya maida kan nasa ga plate ɗin dake gabansa dake shaƙe da abubuwan morewa da tun ɗazu ya kasa taɓa ko guda, kusan gasasshen rago biyu ne akan dogon bencin nasu amma komai ya kasa ci, gorar ruwa kaɗai ya iya miƙa hannu ya ɗaukahaɗe da buɗe bakinta ya aza ga baki, sai daya kusan shanye ta tas sannan ya iya ajiyewa tare da kallon ambassador Hussain da shima ya kasa cin komai ya matsa kusa dashi zai yi magana, Jabir ne ya sake ƙarasowa wajen da sauri yana faɗin,
"Akwai wani abu da kake buƙata ne Abba?" Tare dayin tsaye akansu, runtse idanuwa Abba ya yi haɗe da girgiza kai yana furzar da iska ta baki sannan ya gyara zaman sa daidai don maganar daya so suyi da ambassador bazai iya yin ta agaban Jabir ba, gaba ɗaya yabi ya takura sa da sunan kulawa ko motsi mai ƙarfi baya da ikon yi sai ya zo ya ishesa da tambayoyi, ganin haka yasa Jabir yin murmushi haɗe da duƙowa kusa ga Abba ya ce,
"Sorry sir" sannan yabar wajen, ko second biyar bai yi da jaye wa wajen ba sautin microphone ya mamaye wajen ana faɗin,
"Hello, hello" don janyo atteniɗin mutane a wajen, ba tare da mai maganar ya bayyana ba yafara bayanin cewa suna yiwa kowa sannu da zuwa tare da fatar komawa gida lafiya, sannan ya gabatar da cewa ango zai iso wajen don yin godiya bisa amsa gayyatar su da kuma taya su murna da suka zo yi, wani lallausan sautin aka sake sawa haɗe da canja launin hasken fitillun wajen zuwa masu ɗan duhu, amma duk da haka za a iya hango abokanan ango dake biye dashi sun sanyo sa a gaba zuwa gaban hall ɗin, suna isowa wajen duk suka koma bayansa suka tsaitsaya, cikin sanyin murya ya fara maganar kamar haka,
"Alhamdulillah, Alhamdulillah, sunana Muhammad Muhriz Muhammad, wanda akafi sani da mm mai dabino, tsohon jami'in ma'aikatar kula da tashi da kuma saukar jiragen sama na kamfanin Airline dake reshin Abuja, ina farinciki da zuwan wannan rana mai ɗinbin tarihi a wajena tare da addu'ar ALLAH ya sanya alkhairi da albarka a cikinta, haka kuma ni da matata Janan Usman mai fata muna miƙo saƙon gaisuwa ga iyayen mu, yannen mu, ƙannen mu, ƴan uwan mu da kuma abokanan arziƙi da suka taru don shedar auren mu, mun gode mun gode sosai ALLAH ya sakawa kowa da alkhairi ya kuma maida kowa gida lafiya, ƙarin jinjina ga iyayen mu da suka jajirce kuma suka yimana gata wajen ganin sun bamu farincikin da mu bamu isa mu bawa kanmu ba balle kuma muce zamu biya su, mun sani cewa Ubangiji kaɗai ne zai biya su don haka muna roƙon sa daya biya su da aljannah fiddausi, mungode mungode ALLAH ya sauki kowa gida lafiya" ya ƙare maganar tare da ɗaya hannu gaba ɗaya shi da abokanan sa, daga haka reception ɗin ya zo ƙarshe inda duk wuɗan da suka samu halar ta wajen suka fita da ɗinkin farinciki da kuma fatan alkhairi ga ango da amarya, don ba ƙarya an ci an sha anƙoshi ga kuma jikkunan da aka rarraba kowa ya ɗauki tashi ya nufi gida,
Jiki ba ƙwari Abba ya miƙe yana kallon ambassador Hussain da fuskar nan tasa tayi baƙi ƙirin saboda ɓaci rai yana faɗin,
"Honnarable yanzu gida zamu wuce saboda abun da muka tanada don baƙin mu, na tabbata yanzu haka wasu na can na jiran mu" ya ƙare zancen cikin jin kunya ba tare daya bari sun haɗa idanuwa da shi ba, ba tare daya tanka saba ya gyara zaman gilashin dake idonsa tare da yimasa wani irin kallo sannan yasa kai ya wuce abunsa, ko daya isa bakin motar sa ya tadda abokanan mm tsaye riƙe da manyan jikkunan da aka tanadar masu nasu na musamman, ko kallon su baiyi ba ya buɗe motar ya faɗa tare dasa drivern ya ja su wuce, Mu'azzam ya duƙo kansa saiti gefen da ambassador yake haɗe da cewa,
"Sorry mr. Honnarable wannan naku ne" kafin yayi magana yasa driver ya buɗe masu boot aka loda jikkunan kusan ƙwaya bakwai aciki sannan ya sake dawowa ya duƙar dakai haɗe da yimasa godiya, ambassador bai iya cewa komai ba saboda tsananin mamaki daya kama sa sai dai kawai ya bugi sit ɗin drivern ya ja motar suka yi gaba.
Haka ma su Abba da Baffa suma duk saida aka saka masu nasu kayan a boot ɗin motar tare da tabbatar da kowanen su ya ɗauki hanyar zuwa gida sannan abokanan nasa suka koma masaukin su, rasa da wane irin baki mm ya yi zai yi masu godiya ganin hidimar da suka shirya masa bada ko sisin saba, Momy ya kira yana faɗa mata tare da bawa mm wayar bayan ya sakata a amsa kuwa, cike da farinciki da jin daɗi ta shiga yi masu godiya tare da saka masu albarka, in da suka shiga maka masa harara wasu kuma suka dinga kai masa ɗan suka a gefen kafaɗa suna ganin bai kamata yayi hakan ba don duk abunda za su yimasa basu biya sa hidima da taimakon da yake yi masu dasu har iyalain su ba,
"Wash Momy zasu ɓalle maki yaron ki daga faɗar gaskiya" ya faɗa lokacin daya karɓi wayar a hannun Mu'azzam yana dariya, dariyar duk suka sa suma hadda Momy dake can tana fama da jama'a,
"Hello, Momy sai anjima"
"A'a dakata, wane anjima kuma?, Ba ance da an gama ɗaurin aure za a je ɗauko amarya ba?, Gafa su Umman ka nan dasu Ruƙayya duk sun shishhirya kai kaɗai ake jira ku turo motoci aje ɗaukar ta"
Sai daya ɗan shafa kansa tukuna ya kalli su Mu'azzam cike da jin kunyar me zai faɗa mata don sun gama tsarawa cewa da kansu za suje ɗauko amarya ba sai iyaye mata sun je ba, kallon da yake yiwa Mu'azzam yasa shi karɓe wayar a hannun sa haɗe da cewa,
"Momy mun jurar dasu suyi zaman su zamu je mu ɗauko amaryar da kan mu"
"Sallallahu alaihi wasallam, Mu'azzam a ina kuka taɓa ganin anyi hakan?, Maza da zuwa ɗaukar amarya"
"To Momy ai dama mu ɗin ne ke zuwa ɗaukar amarya tare da ƴan matan da ake zuwa dasu, ayi haƙuri abar shi a haka"
"Bazai yuyu ba ko Umman sa ne dole su je, wannan abun kunya haka har ina?"
"Pls Momy..."
"Bafa za ayi haka ba na faɗa maku" ta katsesa tare da ƙare zancen tana masifa, jin zai sake cewa wani abun ya sa ta katse kiran, Jabir takira haɗe da cewa yazo ya ɗauki su umma Mariya yanzun nan, kallon mm yayi tare da ɗaga kafaɗa irin babu yanda zasuyi dole su haƙura tunda haka Momy ke so kafin yace,
"To Momy ina Razina?"
"Tana can wajen amaryar tun da ta je kaimata kayanta bata dawo ba" ta bashi amsa tare da kashe wayar, zaro idanuwa ya yi haɗe da kallon mm ya ce,
"Dama kai mugu ne?, Wato ake a ɗauki maka amaryar ka ni kuma tawa a baro ta can ko kuma kasa waɗan nan masu jaijayen kunnuwan suyi mani wuff da ita idan sun ganta, ya yi maka kyau 1-0 kuma zan rama" yana ƙare maganar ya karɓe makullin mota a hannun Mu'azzam dake dariya tare da ficewa daga hotel ɗin, tun akan hanya ya kira Razina dake zaune bayan miss hurriya ta gamawa Janan kwalliya itama tana yimata, tun kafin tayi magana ya ce,
"Hello duk abunda kike yi ki fito yanzun nan gani nan zuwa na ɗauke ki kafin ƴan ɗaukar amarya su ƙara so" bai kuma jira jin ko me zata ce ba ya kashe wayar sa, agurguje ta ce hurriya ta ƙara sa mata makeupɗin kafin ya ƙara so, shi kuma ya wuce gida ya ɗauko su umma Mariya su uku don aunty Ruƙayya tuni tayi can gidan amarya ana ƙara gyaggyara mata,
Abba kuwa sai lokacin yasa masu funitures su je kai kayan Janan wanda saida Hajiya kaka ta kirasa jiya tayi masa tass yasa aka sauya yo mata su don irin kayan nan ne nada na katako masu ɗoruwar fenti yayi mata, acewarsa wai bazai wahalar da kansa siya mata kaya masu tsada ba akaisu inda basu da daraja yayi asarar kuɗin sa, to shine fa ba a tashi kai wasu ɗin ba sai gaba da ɗaurin aure, suma irin kayan nan ne masu babban kai ƴan katsina, ko da akaje sai gashi an samu gaba ɗaya ɗakunan dake gidan mm ya riga daya saka kayan ɗauki irin na waje masu muguwar tsada kama daga kan gadaje har zuwa zannuwan gado da cuttins da kuma kayan kitchen babu abunda babu, gaba ɗaya wuɗan da ya tura sun zagaye gidan babu inda za a saka kayan wanda hakan yasa suka kirasa don su sanar dashi, lokacin ana ɗaurin aure shiyasa bai ɗaga ba sai suka kira Hajiya suka sanar da ita, cewa tayi su dawo da kayan nan gidan ta cike da jin daɗi da kuma farinciki, dama tasan yanda Muhammadunta ke son Janan bazai taɓa bari ta kunyata ba, kawai ta matsawa abubane ya yimata kaya masu ma'ana saboda haƙƙin tane itama, godiya tayiwa ALLAH tare da addu'ar ALLAH ya tsarewa Janan gidan aurenta ya kuma tabbatar da farinciki marar misaltuwa aciki,
Nihal kuwa dama ambassador cewa ya yi ai ƴar sa ce shima don haka ba sai Abba yayi komai ba, duk abunda ake buƙata an saka amaryar su kawai suke buƙata,
Ba'a fi mintuna goma ba Jabir ya iso dasu Umma Mariya ƙofar gidan Abba, da kansa ya yi masu iso har zuwa part ɗin Hajiya zee tare da ƴan uwan ta da suka zo mata kara, sosai ta ji daɗi itama tayi masu iso zuwa can part ɗin nasu Janan, saida ta tabbatar sun samu wajen zama acikin falon sannan ta koma part ɗin ta takira Abba ga waya, tayi masa kira ya kai sau ukku bai daga ba sai faman kai da kawo yakeyi can cikin kin sa, yayin da nihal ke zaune cike da mamakin labarin da Abba ya gama bata, ɗan yatsina fuska tayi kafin tace,
"To Abba wai taya hakan ta faru?"
"Shine abun tambaya Nihal" ya faɗa yana ware mata hannuwa.
"Imagine sadaki fa kace miliyan ɗaya, ni fa ko a littafan novel da kuma fina finan Hausa ban taɓa jin hakan ta faru ba, wai kuma ga mota da kujerar hajji, wannan Abba ai shirmene saidai ko in a mafarki suke zancen, kuɗin da gaba ɗaya in za a haɗa sun kai kimanin miliyan kusan biyar da wani abu kenan fa, kuma ace sadakin mace ɗaya, noo..ka bincika Abba akwai Agar tambaya anan"
"Abun da ya ɗauke mani kai kenan, shin wane yaro ne shi? Me yasa ya yimani ƙarya tun farko bai faɗa mani asalin sa ba?, Da duk wannan ɓacin rai da lokutta da aka samu ba a yi saba"
Shi dai Jabir yana komawa cikin mota ya danna wa Razina ya ce tafito gashi yana jiran ta, bata ƙara minti ɗaya ba ta haɗa inata inata ta kalli Janan dake zaune tayi matuƙar kyau kamar ba ita ba ta ce,
"Aunty Janany sai kin iso ga ƴan ɗaukar amarya nan sun zo" sai data lalubo hannun ta ta riƙe sannan ta ce,
"Kada ki tafi ki bar ni Razina"
"Kiyi haƙuri ya Jabir na jirana a waje, bari na turo maki Adda Nihal ɗin ki don na ganta ɗazu dana sauka ƙasa ɗaukowa miss hurriya ruwa" hawaye ne suka zubo mata tare da sakin hannun Razina ta juya baya haɗe da cewa
"Ina jin kewar ta sosai, ina so na zauna kusa da ita naji ɗimin jikin ta kafin a rabamu kowace take gidan ta, amma nasan bazan samu hakan ba, ki tafi abunki, tunda har Adda Nihal ta iya nesan ta kanta dani kowa ma zai iya haka" cike da tausayin ta Razina ranar ɗakin tana yi tana juyowa tana kallon ta, badon Jabir ya matsa mata data fito ba da zata kasance tare da ita har lokacin da masu ɗaukar amarya zasu shigo su ɗauke ta,
Tana shiga motar comboi ɗin motocin abokanan ango na tsayawa ƙofar gidan, hararar ta Jabir ya yi haɗe da cewa,
"Da kin bari sun riske ki aciki ko suka taddaki awaje kafin ki ƙaraso da na yimaki hukuncin da bana tunanin ni kaina zan ji daɗin yi maki shi"
"Alhamdulillah tunda ALLAH yasa hakan bata faru ba" ta faɗa tana dariya tare da kwantar da kanta saman kujerar tana kallonsa,
Motoci ne da adadin su yakai kimanin mota goma zuwa sha biyar jere da suka dangane tun daga kan titi har zuwa ƙofar gida, gaba ɗayan su babu kowa aciki sai abokan ango da suka shigo bibbiyu acikin kowace mota, ana kawowa duk suka firfito suka tsaya bakin gidan suna jiran a fito da amarya, kimanin kusan mintuna arba'in kenan su umma Mariya na zaune amma babu amarya ba labarin ta, sun yi zuba idanuwa har sun gaji amma ba a fito masu da ita ba, ganin jiran ya yi yawa yasa Jabir ya kira mm a waya ya ce,
"Malam, kasan halin da amaryar ka ke ciki, kuma wlh babu alamar zasu bada ita kawai kaje ka ɗauko abukka tunda anriga an ɗaura, idan kuma ba haka ba na rantse dattijon nan naku sai ya kunyata ka, an waiting for you zan shiga ciki" yana gama faɗar haka ya kashe wayar sa tare da excusing kansa awajen Razina ya fice cikin mota, kusan gaba ɗaya abokanan mm tare dashi suka nufi cikin gidan yayin da Jabir ya yimasu jagora, yanayin tsayawar motocin da Abba ya ji ya sashi ɗage labulen tagar falon yana hango su, "come and see my dota, see this is what exactly am telling you about this man"
"Wow!.." ta faɗa haɗe da zaro idanuwa ganin yawan motocin da kyan da suke dashi,
"Abba lemme go to Janan" ta faɗa tana ƙoƙarin fita, wait Nihal bari na fara zuwa na hango abokanan nashi sun nufo gidan, and you know ke matar wani ce yanzu ko,
"Mtsss..nifa Abba wannan auren kawai anyi ne don kare yawa amma ni bana jin sa akaina, ina ma takardar yarjejeniyar mu dakai na adana don wlh komai daren daɗewa dole ka raba wannan auren alokacin daya kamata" ta ƙare zancen tan dudduba locas ɗin dake cikin falon don dubo tamkardar,
Abba na fitowa su Jabir na ƙarasowa cikin falon, cike da girmamawa duk suka zube gaban sa suka gaishesa Jabir ya ce,
"Abba munzo ɗaukar amaryar mu kamar yanda ka buƙata, tun ɗazu iyayen ango na falo kai kaɗai suke jira" juyawa Abba ya yi yana kallon su umma Mariya da Jabir ta nuna da hannu, gaishe sa suka yi ya amsa da ɗan murmushi a fuskar sa kafin yace,
"Masha ALLAH, ɗayar ku zata iya hawa sama ta gefen dama amaryar na cikin aikin sai ta fito da ita, amma ku sauko da ita a hankali kun san ba gani takeyi ba" wani irin abu mm ya ji ya sakar masa zuciya jin kalamin da Abba ya yi na ƙarshe tare da kallon su Umma Mariya daba lallai ne su iya hawa wajen ba tunda ba sabawa sukayi ba sannan ya kalli Abba haɗe da cewa,
"Abba ko zan iya shiga na fiddo masu da ita?" Cikin fara'a ya ce
"Ahhh..why not, she's your wife just go" ya ƙare maganar tare da juyawa ya koma cikin ɗakin nasa yana faɗin,
"Bari na kirawo ƴar uwar tata suyi bankwana kafin kuwuce da ita"
Basu Umma Mariya kaɗai ba hatta abokanan mm sake da baki suka bi Abba da kallo suna mamakin wannan wane irin ubane haka?, Ina ƴan uwan ta da zai ce dangin mm su shiga su fito da ita, ko kuma me zai hana shi da kansa ya je ya fito masu da ita.(Note: duk mutum mai hali irin na Abba babu yanda za ayi hidimar sa ta tashi kaga ƴan uwansa a gidansa gudun walaƙanci, wannan dalilin yasa ba lallene kowa yazo ba domin ko sun zo wajen wa zasu zo?, idan har akwai masu iya daurewa su zo don zumunci to fa sai dai suje can gidan Hajiya wanda wannan dalilin ne ya zama hujjar data hana Hajiya zuwa gidan).
A hankali ya tura ƙofar ɗakin kamar yanda Abba ya kwatanta, wani irin ƙamari ne ya daki hancinsa ya yi saurin lumshe idanuwa tare da buɗewa sannan ya ƙarasa daga ciki, kasancewar ta ba ƙofar baya ne yasa tana jin ƙarar an buɗo ƙofa tayi saurin zabura haɗe da cewa,
"Waye?..waye?" Har lokacin hawaye na sauka a kan fuskar ta, yanda ta razana ya sashi saurin ƙarasowa wajen ta yana faɗin,
"Am sorry Janany hayateey, am the one" ya ƙaraso tare da riƙota, ƙamshin sa da sautin muryar ta ya tabbatar mata da cewa shi ɗin ne hakan yasa ta faɗa a jikinsa tare da fashewa da kukan da tun ɗazu hawaye kaɗai ne suka iya zubowa,
"Hubby Ina so naga Abbana da kuma Addata, don ALLAH kada ku tafi dani har sai na gasu, na tabbata duka fushi sukeyi dani shiyasa suka nisan ta kansu dani, suka kasa zuwa su riƙoni izuwa wajen dangin ka, pls..." Kafin ta ƙara sa ya haɗe bakin sa da nata waje ɗaya yana tsutsa, jikin ta ne ya sake ɗaukar rawa hawaye na ƙara gangarowa a kan fuskarta, cikin wani irin salo ya sake janyo ta a jikin sa haɗe da sa harshen sa yana lashe mata dukkanin hawayen dake sauka, bata hanasa ba don tasan halaliyar sa ce ita shi kuma be dena ba har sai daya ga hawayen sun dena saukowa sannan ya riko fuskar da hannayen sa duka biyu ya yimata kiss a goshi haɗe da cewa,
"Matuƙar ina raye bazan koma bari waɗannan hawayen naki su ƙara sauka ba Janan, Abban ki na ƙasa shi da Adda Nihal ɗinkin suna jiran saukowar ki, bazan juri ganin an riƙon.un amarya ba a yanayin da ƙaddara zata iya sa ta bugu da wani abuba idan ba a kula mani da ita ba wajen saukowa, shiyasa na roƙi Abba daya bani damar shigowa na fito da abata da kaina, ina fatar banyi laifi ba"
Ɗan dukan sa tayi haɗe da cewa,
"Laifi ma mai yawa, domin kayi rashin kunya awajen mahaifina da gwaggwan min mu da suka zo ɗukata"
"Ki sa aranki a gaban kowa ma zan iya aikata irin wannan rashin kunyar domin baki kariya"
"Na gode da hakan hubbin ruh"
"Point of correction ƴan mata na, no more hubbin ruh again, just call me mijina uban ƴaƴana" ya faɗa cikin kunnen ta har numfashin su na sarƙewa dana juna" cike da jin kunya ta ɗan ja baya kaɗan kawai taji ya kamo hannunta ya azo a saman wuyan sa ya ƙara kamo ɗayan shima ya aza a saman wuyan nasa ya zamana sun zagaye wuyan nasa sannan ya ɗauke ta cak tamkar wata jaririya ya nufi ƙofar fita da ita, wuntsile wuntsile ta fara yi da ƙafafuwan ta wai ya saukar da ita yayi kamar bai jita ba sai ma kallon fuskar ta daya shiga yi numfashin sa na haɗewa da nata, farin yadine mai ɗan karen kyau ajikin ta doguwar riga pitet daya sha fararen stone ta ko ina, sai head shima fari da hurriya ta naɗa mata irin yanda ake yiwa amare, haka ma takalmin ƙafafuwan suma farare ne sai net ɗin da aka azo saman head ɗin yayi kamar mayafi, tsayawa faɗar yanda sukayi kyau ba ƙaramin ɓata lokaci bane don shima ɗin farar shaddar daya saka ɗaurin aure har lokacin ita ce ajikin sa, a hankali yake saukowa ɗauke da ita daga kan upstairs ɗin har suka kusa ƙarasowa, yanda sukayi masifar kyau ya sa abokanan nasa fiddo wayoyin su suna ɗaukar su hoto mm sai faman murmushi yakeyi, ita kuma tsabar kunya shigar da kanta tayi acikin ƙirjinta tana sauraren yanda zuciyar tasa ke bugawa haɗe da yiwa ALLAH godiya daya mallaka mata farincikin ta a yau,
Kusan mutuwar tsaye Nihal da fitowar ta kenan idanuwan ta suka kai gare su yayin da mm ke saukowar, jiri ta fara jin ya ɗebeta kafin ta muraza idanuwan ta da suka fara jujjuya mata falon a hankali, ganin bata dena hango abunda take gani ba sai ma sake matsowa da yakeyi kusa gareta yasa ta shiga nuna su da hannu tana faɗin,
"Abba shine wancan..wlh Abba shine, right man ɗin a ne kuma the charming ɗin da nake nema" ta ƙare zancen tana tunkarar wajen haɗe da jin wani sanyi da kiri na ɗibar ta lokaci ɗaya, Muryar Abban ta da ta ji yana faɗin,
"No Nihal, can't be possible wannan mijin ƙanwar ki ne Janan, ko bakya gani ne" da ƙarfi ta juyo haɗe da kallon Abba ta ce,
"What? Mijin ƙanwata jan..." Kafin ta ƙara sa kawai akaga ta faɗi wajen.......
_Wash!, hannuna ya yi ciwo, wow Alhamdulillah, anan na kawo maku ƙarshen littafina mai suna TUKUICIN SO part 1, sai ku kasance dani acikin part 2 ɗin sa ranar bakwai ga watan Satumba idan ALLAH ya kai mana rai, Nagode sosai bisa karamci da kuma soyayyar da kuka nunawa wannan littafi, da yardar ALLAH na biyun sa zai zo maku da ɗimbin darussa da kuma nisha ɗantuwa fiye da na farkon, ni daku ALLAH ya tara mu acikin ladar dake cikin wannan littafi zunubansu dake ciki kuma ALLAH ya yafe man, kar ku manta ranar 7bakwai ga watan Satumba wata mai zuwa kenan, zan sake maku cigaban tukuicin so part 2 kuma shima free ne in ALLAH ya yarda, yawan COMMENT ɗinku a ƙarshen wannan littfai shi zai ƙarfafa mani guiwa wajen cigaba da antayo maku yanda wasan zata ci gaba da kasancewa, SABON SALO mai cike da ZAZZAFAR WASA, Taku a kullum BILLY S FARI, domin gyara ko kuma wata faɗakarwa da tambayoyi akan wannan littafi kai tsaye zaku iya tuntuɓata akan wannan lambar 07040402435, NAGODE INA ALFAHARI DAUKU😍_
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 40