Share this page
maka albarka, to ina ƴar uwar taka take ne?" "Bari nayi har sai na fara zuwa na gano ƴan uwanmu tukuna daga baya sai na kawota ita" Ɗago kai Baffa Ali yayi yana kallon ƴan uwan nasa mata dake tsaitsaye fuskokin su ɗauke da farinciki, ya ce "Indo kinga abunda nake faɗa maki ko?, jikina na bani cewa duk inda jinin ɗan uwana Muhammadu suke suna raye da yardar ALLAH, to gashi ALLAH ya bayyana mani akan da kansa" wacce ya kira da indo na matsar ƙwalla, ta ce "Na gani malam, ALLAH gagara misali ne huwar Rahmanu a lamurransa" mm ya ɗan rissinar da kai ƙasa ya shiga gaishesu ɗaya bayan ɗaya, murmushi indo tayi bayan sun amsa tare da matsowa ta shafa kansa tana cewa, "ALLAH mai iko sannu Muhammadu yanzu kai ne ka girma ka koma haka?" Daga shi har baffan murmushi sukayi kafin Baffa Alin ya sake juyawa gefen da sauran matan ke tsaye sun zubowa mm idanuwa suna kallon ikon ALLAH daya sake maido masu da ɗan-ɗan ɗan uwansu , ya ce "Mariya kin tuna jiyan nan nake faɗa maki cewa nayi mafarkin ina tafiya nayi tuntuɓe, har zan faɗuwa sai ga wani saurayi yayi saurin taro ni na faɗa a jikinsa, ina ɗagowa naga fuskarsa sak irin ta yana marigayi Muhammadu?, To kinga fassarar mafalkina, ashe da shi har ƙanwar tasa suna raye ALLAH ya kuɓutar dasu kamar yanda itama mahaifiyar su ta kuɓuta" Wata irin razana mm yayi haɗe da fisgo kai yana kallon Baffan nasa jin abunda ya faɗa, cikin rawar baki da karyewar murya ya shiga faɗin, "Um..m..mah...ummah nada rai bata mutu ba?" Ya ƙare zancen cike da mamaki jikinsa na wani tsima tare da matsuwar jin amsar da Baffa zai sake basa, "Sosai Muhammadu, mahaifiyar ka bata mutu ba a wancan lokacin, yanzu dai ne ba muda tabbacin tana raye ko kuma ALLAH yayi nasa iko akanta don sam ba muda labarin ta" "Kamar ya Baffa" ya faɗa tare da matsowa kusa dashi ya riƙe hannunsa, wani yanayi yaji ya tsinci kansa a ciki yanzu, shi ba farinciki ba kuma shi ba baƙin ciki ba, ganin yanda gan ɗaya ya tashi hankalinsa yasa Baffa cewa, "Yi haƙuri Muhammadu zan faɗa maka komai, yanzu dai ka daure ka fara tashi ka watso ruwa kaci abinci sai muyi magana a tsanake kaji ko?" "Baffa dona ALLAH..." "Subhanallahi, kaddai kacemun har yanzu halin nan naka dana sani na kafiya da naci na nan" babu yanda mm ya iya dole ya haƙura Baffa ya ce su wuce dashi cikin gida ya watsa ruwa ya huta kafin yazo, don zai je gidan mai gari ya aiko kiransa ɗazu kafin ayi Sallah, haka mm na ji na gani Baffa ya fice daga gidan ba tare daya basa labarin komai ba akan mahaifiyarsa, ƴan uwa kuwa sai murna sukeyi da aka shiga dashi cikin gida ga ɗan ɗan kawo Muhammadu daya ɓace ya dawo, babban gida ne sosai dake ɗauke da ɓangaren shiyoyi har guda biyar aciki, shiyar farko itace ta Baffa Ali da matan sa su biyu, indo da kuma Atika, sai shiya ta biyu da umma Mariya ke ciki ita da ƴaƴanta su bakwai, ita ɗin yaya ce a wajen mahaifin mm da kuma Baffa Ali, ta dawo gidan da zamane sanadiyar mijinta da ALLAH yayiwa rasuwa, sai shiya ta ukku, talatu ce a ciki wato matar Baffa Bala, shima an kashesa lokacin da ɓarayi suka shigo ƙauyen, kasancewar ƴan mata uku ne da ita alokacin yasa ita kaɗai take zaune a ciki sai jikokin ta dake zuwo don gaba ɗaya ta aurar da ƴaƴan nata da take dasu, sai shiya ta huɗu ita kuma rufe take ba kowa aciki, wacce ta kasance shiyar Baffa sule ce, kasancewar shi mazaunin Katsina ne acan yake aiki, don shi kaɗai yayi karatun boko acikin su shi yasa yayi aurensa acan tare da matar sa ɗaya da yaran su biyu, macce da namiji, yasa baya zama ciki, saidai idan wata hidima ta tashi yazo da iyalinsa kuma ana gamawa zasu koma, shima ALLAH yayi masa rasu a ranar da ɓarayin suka shigo ƙauyen, ba tare da saninsa ba yazo ganin gida, yana shigowa sukayi arba da shi suka kashe sa, sai bayan anzo ana har haɗa gawarwakin mutanen ƙauye da aka kashe suka tsinci gawar sa aciki, sosai Baffa Ali ya so anso yaran alokacin amma karamci da mutuncin dangin mahaifiyar su yasa suka bar su acan, yanzu haka duk sun girma har ta farkon mai suna Ruƙayya tayi aure shekaru biyu da suka wuce, shi kuma namijin mai suna Ahfan yana India wajen karatu, a shekarar nan ma zai ƙarewa, don dangin mahifiyar tasu sukan kawo su lokaci lokaci tun suna ƙanana shiyasa duk halin da suke ciki suka sani, ita kuma shiryar ƙarshe wacce itace ta biyar autar su Baffa ce aciki umma luba, har wayau itama mijinta kashesa akayi a shekarun baya ya je gona, saidai aka dawo mata da gawarsa anyi masa yankan rago, shine dalilin da yasa itama ta dawo anan gidan da ƴaƴanta su biyar, kuma cikin taimakon ALLAH gaba ɗaya familyn duka Baffa Ali ne ke ɗauke da nuyin su yana kulawa dasu dai dai gwargwado iyawarsa saboda duk ankashe mazajen su, daga matan nasa har matar ƙanensa da yayarsa da ƙaunarsa shine da baƙin kula dasu don shi kaɗai ya rage masu na miji, sai kuma yanzu da ALLAH ya dawo masu da mm agaresu, wanda ko shakka babu dawowar tasa itace fassarar mafarkin Baffa, don shi zai kama masa wajen cigaba da kulawa da wanna ahalin nasu. (Wannan matsalar itace al'ummar ƙauye harma dan birnin ke fuskanta a yanzu, sai kasamu macce sama da goma, amma namiji ne ɗaya jigon dake kula dasu sanadiyar mazajen su da aka kashe, ya ALLAH ka kawo mana sassaucin wannan rayuwa, kasa mu canye wuɗan nan jarabawoyin) Kasancewar akwai gajiya sosai a tattare da mm yasa ko daya watso ruwa a shiyar umma Mariya yaci abinci bacci yayi awon gaba dashi, don ba kaɗan tafiya mai nisa ta mota ke jigata sa ba saboda sabon daya yi da tafiye tafiye cikin jiragen sama, bai farka ba sai da lokacin sallar la'asar yayi, umma Mariya ta tadasa bayan ta zuba masa ruwa a buta, wani irin bacci ne mai daɗi daya jima baiyi ba cike da daɗaɗan mafarkai yayi, hakan yasa ko daya farka baccin ya ji kaso saba'in bisa ɗari na cikin damuwar daya kwanta da ita ta gushe, tare da fatar ALLAH ya tabbatar masa da abun daya gani cikin mafarkin nasa, Bayan ya dawo wajen Sallah indo ta bakka Maryam fura mai sanyi da nono ta kawo masa, lokcin yana zaune ƙofar gida yana jiran fitowar Baffan nasa, Baffa kuwa ana ƙare Sallah ya juyo ya sanar da mutanen ƙauye cewa ALLAH ya bayyana masa ɗan wajen Malam Muhammadu yayan sa daya ɓata, yanzu haka yana nan yazo, wannan dalilin yasa ya jima bai fito ba saboda tsayawa tayasa murna da sukeyi, kallonsa Maryama data ajiye masa fura tayi haɗe da cewa, "Ɗan bunni wai gashi inji indo ta ce akawo maka" kaɗai mata kai yayi sannan ta wuce ciki haɗe da regowa tana kallonsa, sai ta kwashe da dariya ta koma ciki aguje, dariya abun ya bashi don haka tana sake regowa ya ce, "Zo nan mana" cikin jin kunya ta rufe fuskar ta da tafi haɗe da zuwa gabansa tayi tsaye, sai daya girgiza kai sannan ya ce, "Ya akayi ne halan kike leƙena" saida ta washe haƙora haɗe dayin dariya sannan ta ce, "ALLAH irin ka muke gani a talabijin ɗin umma luba" "Dagaske kike yi?" "ALLAH kuwa" "Ya sunan ki?" "Maryama.." tayi saurin rufe baki da komawa cikin gida aguje hango Baffa tafe shida mutane, dariya mm yayi haɗe da miƙewa tsaye lokacin da suka ƙaraso wajen suka shiga miƙa masa hannu ana gaisawa tare da sanya masa albarka, bayan duk sun wuce Baffa yayi masu godiya haɗe da rakkiya sannan ya juyo yana kallon mm, "Ho malam Muhammadu, tun ɗazu ka matsu na fito ko?" ya sosa gefen kunnensa haɗe da sinne kai ƙasa yana murmushi, cikin gida Baffa ya shiga ya ɗauki tabarma ya sake shimfida masu anan soro sannan ya ce, "Bisimillah yayan Baffa" don yakan kirasa da hakan tun yana ƙarami, ɗaukar kwanon furar da Maryama ta kawo masa ya yi sannan ya wuce ciki shima haɗe da cire takalmansa ya zauna akan tabarmar suna fuskantar juna shi da Baffa, kusan rige-rige sukayi wajen fara magana Baffa ya ce, "Fara ɗaukar furar ka kasha tukuna sai na baka labarin ko" kasancewar shi mutumne da bai fiye son gardama ba da ɓata lokacinsa ya sa duk irin yanda ya matsu daya san labarin mahaifiyar tasa ya haƙura ya fara ɗaukar furar ya sha, sai daya sha fin rabi sannan ya ajiye kwanon furar, "Ta isheka?" Baffa ya faɗa yana murmushi tare dasa hannu ya goge masa gefen baki da ƴar furar ta taɓa masa, "Na gode Baffa, amma nayi mamaki da ka ce mahaifiyar mu bata mutu ba Baffa, a gabana ta ƙara sa rasuwa kuma nasa hannu na shafeta" "To Muhammad, wannan al'amari ai na ALLAH ne, bana tunanin zaka iya sanin yanda mutuwa take daidai bayan a lokacin baka wuce shekaru goma sha biyar ba a duniya" "Kenan hakan na nufin doguwar suma ce ummatah tayi a lokacin?" "Sosai kuwa, don ko da hukumar ƴan sanda ta kawo agaji bayan tafiyar ɓarayin ana har haɗa gawarwakin da suka kashe, tare da wuɗan da suka ji rauni an samu mahaifiyar ku kwance cikin jini itama kamar matarta, amma ana ɗauko gawarta sai aka ga numfashin ta ya dawo, hakan yasa da sauri aka sanyata cikin motar asibiti wato ambulance aka wuce da ita general hospital dake can cikin gari, ganin taji rauni dole tana buƙatar aikin gaggawa yasa aka wuce da ita babbar asibiti dake can cikin Katsina, babu wanda ya sa mata ran fita hatta likitoci saboda yanda dafin wuƙar da aka daɓa mata ya shiga jikin ta sosai ya kuma yi nasarar yankewar gefen ƴan hanjin ta, amma cikin ikon ALLAH da aka gwada yimata aiki tare da dasa mata gefen ƴaƴan hanjin daya yanke sai gashi anyi nasarar ceto rayuwar ta, ta sha jinya sosai don wata biyar tayi a asibiti kwance, kuma alhamdulillah ba laifi mun samu tallafi gwamnati a wancan lokacin, bayan ansallamota ne ta fara bijiro mana da zancen inda kuke, mu kuma bamu san amsar bata ba, kullum ƙoƙarin mu shine mukwantar mata da hankali, amma hakan ya cutara saboda kullum cikin ƙunci kuka da kuma damuwa take tana ambaton sunan ku, wasa wasa abun ya fara zame mata sabbatu ta koma tamkar mai taɓin hankali, ta sha wahala sosai saboda munyi tsammanin ko aljanu ne ke damunta kullum cikin ruquya da shan magunguna take yayin da wani likita ɗaya taɓa dubata ya ce mana babu abunda ke damunta sai tarin damuwa da kuma tunani kuma idan ba'a kula sosai ba zai iya taɓa lafiyar ta, da muka ga abun sai ƙara ƙarfi yakeyi yana nema yafi ƙarfin mu sai muka yanke shawarar miƙata asibitin mahaukata domin sama mata lafiya, kwatsam daren da za'a zo a ɗauke ta muka nemeta muka rasa, mun ji ɗa ci sosai mun kuma yi baƙin ciki da faruwar haka, kama daga jahar Katsina birni da ƙauye har zuwa zagayen ta babu inda bamu je neman ta ba amma bamu ganta ba, dole muka haƙura muka barwa ALLAH lamarin tare dasa ran bayyanar ta agaremu indai tana raye ko don ƴaƴanta, amma har yanzu ba muda wani labari akanta, tana raye ko kuma akasin hakan ALLAH kaɗai ya sani, " "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" kaɗai mm ya iya furtawa haɗe da fashewa da wani irin kuka mai tsima zukatan wanda ke saurara, babu abunda ya tayar masa da hankali irin jin halin da take ciki kafin ta ɓata, cikin kuka ya ce, "Ya ALLAH kada ka sanya gushewar ni'imar hankali da kake bayarwa ga bayinka ga wannan baiwa taka, ALLAH ka haramta tabbatuwar baƙin ciki da ɗacin rai azuciyar ta bayan wanda ta ɗanɗana na rashin mahaifin mu damu kanmu da ba tada tabbacin muna raye ko mun mutu, ALLAH kai kayi alƙawarin amsa duka addu'o'in ƴaƴaye ga iyayensu na roƙeka kasanya ganawa tsaknin mu da mahaifiyar mu kafin ka ɗauki rayukkan mu" Abba ya amsa masa da Amin yana mai rarrashin sa tare da bashi magana, sun jima a wajen har lokacin sallar magrib ya yi Baffa ya sa aka kawo masu ruwa sukayi arwala sannan suka wuce masallaci jikin mm ba ƙwari, bayan ya dawo ya kira Jabir sanadiyar missed call ɗinsa daya gani shi dasu Momy, Razina Janan har da Hajiya kaka, dama kuma yana da niyar kiransu kafin ya kwanta, cikin ƙarfin hali ya daidaita muryar sa haɗe da labarta masu cewa ya samu dangin mahaifinsa kowa cikin ƙoshin lafiya don dama kusan family ɗaya ne har na mahaifiyar tasu, sun ji daɗi sosai inda Razina ta matsa masa lallai yaba Baffa Ali su gaisa tana son jin Muryar sa, labarin mahaifiyar su kaɗai ne bai sanar da kowa ba, yabar wannan sai ya koma gashi ga su don susan ta inda zasu fara neman ta duk da ba abu bane mai sauƙi, Janan kawai ce bai samu damar kira ba har saida ya dawo sallahr isha, bayan sun gama fita da duka mutanen gidan ma gaba ɗaya da suka zagayesa irin al'adar mutanen ƙauye da sukeyi duk bayan sallar isha da daddare kafin a kwanta ya basu labarin yanda suka tsinci rayuwarsu a katsina shi da ƴar uwarsa Razina da irin gudummawa da taimakon da Momy da Jabir suka basu acikin rayuwar su, inda kowa yayita sawa Momy albarka, haka Baffa ya tabbatar masa da cewa duk randa zai koma tare zasu je yayiwa Momy godiya don ɗa na halak akeyiwa yayi ƙoƙarin ramawa, ya kuma yimata addu'a itama ALLAH ya maido da hankalin ƴan uwanta duk da krista ne agareta, Sun sha fira sosai da Janan inda tayita tambayarsa meya faru ta ji muryarsa kamar ɗauke da damuwa amma ya ce mata ba komai, don yana ganin wannan damuwar da yake ciki tamkar sirrin sa ce shi kaɗai sai kuma ƴan uwansa da suka zama dole su ji, ya ma yi mamakin yanda ta gano sauyi atattare dashi don ko su Momy basu fahimci hakan ba, ganin ya dage akan ba komai yasa ta ce, "Shikenan hubbin ruh, koma meye ALLAH ya kawo sauƙin da ya kuma musanya damuwarsa da tarin alkhairi" ya amsa da "amin Janany ta, i love you" ta amsa da "i love you too" sannan sukayi sallama, a daren dai kusan zaune mm ya kwana yana saƙa da warwarewa tare da ɗauro arwala ya dinga faɗawa ALLAH damuwarsa da kuma roƙonsa ya kiyaye masa mahaifiyarsa aduk inda take matuƙar tana raye, yana zaune aka kira sallar asuba har Baffa ya tashi ya je ya ƙwanƙwaso masa ƙofa suka nufi masallaci..... ***. ***. ***. A ɓangaren Janan kuwa gaba ɗaya ta manta da zancen kuɗin dake account ɗin ta bata koma bi takan su ba ta shiga sabgar shirye-shiryen final exam ɗinta da zata fara zuwa next week tare da fatan ta fito da first class, Abba na ganin haka shima ya fita batun zancen ba tare daya nemeta ba ganin bata nemi jin ba'asi akansu ba, dama dai muradi kuɗin suzo hannun ta tunda mallakin ta ne, kuma alhamdulillah sun je kuma tasan da zaman su, iya abunda ya rage masa shine ci gaba da shirye-shiryen sa kamar yanda ya gama tsarawa, tana gama jarabawa sai kawai a gudanar da komai yanda ya kamata. _Where Are Janan fan's?, Ku fito ta kusan fashe maku fa, can't wait to see that day😜💃_ _Team Asgar, come close and double tap to our Abba, mun kusa kwaso shiƙi muma😉, *#ASNAN2022*_ *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 46_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* TUKUICIN SO FAN'S GROUP, JOIN 👉https://chat.whatsapp.com/J6t2zj6zhcv5ZeQ8IJLHNo FOR COMMENT😍 _____________________________ Kwana ɗaya mm ya so yi a ƙauye nasu amma ganin yanda abubuwan suka kasance ya sa ya ƙara kwana ɗaya, acikin kwanaki biyun kuwa yaga soyayya da gata awajen dangin iyayensa, lungu da saƙo wajen ƴan uwa duka sai da Baffa Ali ya kaisa aka gaggaisa, ya kuma yi masa bayanin matsayin kowanensu a wajensa, tsabar farinciki mm har kuka yayi, sai yanzu ya tabbatar da babu abunda yakai dangi daɗi aduniya, duk da irin rayuwar da sukayi da babu abunda ya nema ya rasa sai yake ganin sait yanzu ne jin daɗin sa da kuma farincikin sa suka kammala, bai baro ƙauyen ba sai daya samu wani waje da ake cirar kuɗi p.o.s ya ciri kuɗi masu yawa ya bawa Baffa don ya rage lalurorin nauyin mutanen dake kansa, ya kuma bi sauran dangi ya rarraba masu dubu biyar biyar wai kuma goma goma ya ce suƙara suyi hidimar gida kafin ya sake dawowa, Sosai Baffa ya so bin sa don yagano inda suke, saboda tsoron kar su sake kucce masu amma sai mm ya ce yayi haƙuri in sha ALLAH bada jimawa ba zai sake dawowa shi da ƙanwar sa, saboda a ganin sa bai kamata yatafi yabar garin ba tunda kusan shi kaɗai ne namiji jigo da ahalin ke kallo dake taimakon su, Haka Baffa ya haƙura yana ji yana gani mm ya kama hanya ya tafi bayan sun cikashi da abun arziƙi sun ce ya kaiwa Momy, Ba ƙaramin daɗi Momy da Razina suka ji ba dawowar mm musamman labarin daya je masu dashi na cewa ashe mahaifiyarsu na raye bata mutu ba, duk data wata fuskar gaba ɗaya jikinsu saida yayi sanyi jin labarin halin da take ciki lokacin data ɓata da rashin takamammen wurin da za a sameta, kuka Razina ta fashe dashi tare da faɗawa jikin Momy tana faɗin, "Momy i want see even once in my life" Momy ta shiga bubbuga bayanta alamun rarrashi haɗe da cewa, "Sorry my dota, very soo we will all see her since she was alive" "Momy not sure" "But we prayed so" ta bawa mm amsa tana ƙoƙarin calming nasu, ajiyar zuciya Jabir dake zaune gefe ya ƙurawa ɗan uwan nasa idanuwa ganin halin da yake ciki yayi kafin yace, "I think wannan ba wata doguwar damuwa bace, kawai abunda ya kamata muyi shine mu samu hotunan umma mukai gidan talabijin da jaridu, sannan mubada sanarwa gidajen rediyo, ina hakan shine hanya mafi sauƙi da zamu fara nemanta" "Haka ne JB, nima abunda nake tunani kenan, but na tambayesu ko akwai mai hoton ta ya bani suka ce a'a, amma Baffa Ali ya yimun alƙawarin cewa kafin nasake komawa zai bincika mun cikin family ko za a samu wanda ke dashi" cikin sanyin murya Momy ta ɗago kai don gaba ɗaya jikinta ya gama sanyi jin halin da ake ciki ta ce, "Before that my soon, yana da kyau mufara gayawa ALLAH, mu bashi cigiyar baiwar sa shi da kansa kafin mukai a gidajen rediyo, Inaga wannan shi zai taimaka mana ta hanya mai sauƙi wajen cin nasarar ganinta" "Upcouse Momy kin kawo shawara, gobe zan kai sadaka a masallatai da kuma makarantun islamiya ayi mana saukar alƙur'ani" "Hakan ma nada kyau, kafin nan kuma kaima damu duka mu dage wajen addu'a, mu lizimci istigfari da kuma faɗar laa ilaa ha illa antas subhanaka inni kuntu minazzwalimieyn, na ji malaman sunnah da yawa na faɗar cewa babu abunda yafi istigfari saurin warware matsaloli, haka ma duk girman matsala da damuwa idan bawa ya taso istigfari agaba yana yi ba safe, rana, dare to ALLAH zai warware matsalar kuma ya buɗe masa ƙofofin alkhairi da suka toshe masa, don haka sai mu maida su abokanan firar mu daga yau, sai kuma azumi, idan son samu ne ko sau biyu ne zuwa uku muriƙayi gaba ɗaya mu a sati, sai muyi tawassuli da wannan azumin muroƙi ALLAH ya bayyanar mana da ita, Ni nayi imani da ALLAH cewa matuƙar muka koma ga ALLAH gaba ɗayan mu muna masu sanar dashi damuwar mu da buƙatocin mu tabbas zai amsa mana domin shine waraka kuma maganin kowace matsala da damuwa saboda shi nariƙa alokacin da duniya tai mani ƙullin goro, yayin da dangi na suka guje ni, dangin mijina suka kore ni suka juya mani baya, sai gashi ALLAH da baya gudun bayin sa ya riƙe ni irin riƙon da su dangin nawa bazasu iya yimani ba, yayi mani gata irin gatar da dangin miji bazasu iyayi mani ba ya kuma zame mani kariya jigo na rayuwa daga ƙarshe ya fiddani aƙuncin da nake ciki ya dawo da ahalin mijina agareni, kuma ina da tabbaci da yaƙini akansa cewa suma dangin nawa zai dawo mani dasu in Sha ALLAH" ta ƙare maganar tare dasa gefen hannu ta goge hawayen da suka zubo mata tunawa da iyayenta, don idan tace basa cikin ranta to tabbas tayi ƙarya, "Alhamdulillah da samun uwa tagari kamar ki, haƙiƙa ni da ɗan uwana Jabir da kuma ƙaunar mu Razina mun fi kowa sa a arayuwa da muka sameki a matsayin mahaifiya, mun ji shawarar ki sannan mun aminta da ita, zamu riƙe ta a matsayin wasicci koda bayan rayuwar ki ne don warwarewar matsalolin mu aduk lokacin da damuwa tayi mana ƙullin goro" mm ya faɗa yana mai jinjina imani irin na Momy a zuciyar sa, Jabir kuwa murmushi kawai yayi don hausawa kan ce labarin zuciya a tambayi fuska, ko bai faɗa ba ansan dole yayi alfahari da samun nagartacciyar uwa da yayi a wannan duniyar. Bayan mm ya gama sauke gajiya da kuma hutawa da marece ya shirya ya faɗawa Momy zai je wajen Hajiya tayi masa ALLAH ya kiyaye tare da cewa ya gaisheta, har ya fita ta kirasa ta ɗibar masa kayayyakin daya zo dasu daga ƙauye ta ce yakai mata, dama tuni ya kira Janan ya faɗa mata su haɗu gidan grandma, don haka ko da ya je ya tadda ita acan, Cike da farinciki ta tarbe sa tare da taya sa murnar ganin ajalinsa da ya yi, har tana tsokanar sa ALLAH yasa ba a samu ƴar bafillatanar data disashe mata tauraruwa ba, cikin zolaya shima ya amsa mata da cewa, ba a samu ba amma dai ankusa, don ya baro Maryam tauraruwar ta na neman kutso wa cikin duniyar sa, nan take Janan ta ɗaure fuska tare da juyar dakai gefe tayi fushi, murmushi ya yi haɗe da juyawa wajen grandma data fito tana yi masa lale mar haban ya shiga gaishe ta yana dariyar Janan, Dariyar itama grandma tayi kafin tace, "To ita waccen iyayen fushin da bata gajiya me akayi mata" "Ƙyaleta Hajiya tambaya tayi na bata amsa shine take fushi" "Toooo...kun fi kusa dai ni bazan ce komai ba" Saida suka ɗan taɓa fira da Hajiya sannan ta koma ciki ta basu waje bayan ta cewa mai aikinta ta kawo mata abinci saboda bata samu taci da rana ba, Mm kuwa da yake ya kwana biyu basu haɗu da noor alb ɗin tasa ba har aka kira sallar isha yana can, dama bayan sallar magrib Jabir ya iskosa acan shima ya je gaida grandma, don haka ya zauna jiransa har zuwa bayan sallar isha, ganin dare ya yi ya matsawa Janan tawuce gida su kuma suka zauna suka ci gaba da firarsu da grandma har ƙarfe tara da rabi na dare yayi sannan sukayi sallama da ita, suna fitowa daga falon Abba na ƙoƙarin shigowa shi kuma, wani irin mugun kallo ya bisu dashi ɗaya bayan ɗaya yana ƙoƙarin tunano inda yasan fuskokin su, mm ne yayi ƙarfin halin rissinawa ya gaishe shi, shi kuwa Jabir ko inda yake bai kalla ba ya wuce abunsa don kar ya gane fuskarsa, kallo Abba ya bisa dashi ba tare daya amsa gaisuwar da mm keyi masa ba ya wuce ciki ransa nayi masa suya, Yana shiga cikin fushi da ɓaci rai ya fara magana, "Hajiya su waye wuɗan nan yaran marasa tarbiya, musamman wancan ɗayan dake saye da wasu ƙazaman ƙananan kayi ajikinsa amma yake ɗaukar kai kamar wani isasshe, sai nasa atumurmusa mani shi yanzun nan, matsiyacin banza da wofi, Inaga babu manya

Chapter 26 of 40