Share this page
ɓangaren sun ɗauko Razina daga wajen saloon da Momy ta kira su ta ce idan zasu dawo su biya su ɗauko mata ita, da sauri Janan ta sauke glass ganin wani kamar mm ɗin ta cikin mota ya turo hannu zai jefar da gongon lemun power shot daya gama sha, tunani ta shiga yi shin mm ɗin ta ne ko kuwa? Gashi sun riga sun wuce kuma bata hannu ɗaya suke ba balle tace Nihal tabi bayan su, dubara ce ta daɗi mata da sauri ta ɗauki wayar ta ta kirasa har kusan kira biyu ba'a ɗaga ba, shi kuma ƙa'idar sa ce matuƙar yana tuƙi baya ɗaga kiran ko waye har sai ya samu waje yayi parking, gashi yazo daidai round a lokacin shiyasa ko da yaga kiranta bai ɗaga ba har sai da ya fita ciki, daidai gefen titi yayi parking kusa da masallaci yana faɗin, "minti biyu don ALLAH" "Mun baka ashirin" Jabir dake gefe zaune ya faɗa don dama yana son zantawa da masoyiyar sa Razina amma kunyar yayanta da take ji ya hanata sakin jiki, sai faman aika saƙwanni yake ta idanuwa ajikin madu bi ta kasa bashi amsa, Ita kuwa tsaki tayi da taji bai ɗaga ba har Nihal na tambayar ta ko lafiya? Ta ce da ita ba komai, sai dai wata zuciyar a gefe na tambayar ta ya za a yi waccan ya zamo mm ɗin ta bacin tasan irin raunin da yake tattare dashi, asali ma ina yaga motar da zai hau irin waccan, tana dai yimasa fatan haka, wataƙil gizo ne yakeyi mata shiyasa taga kamar shi, murmushi ta saki lokacin da zuciyarta ta gama faɗa mata haka tare da ɗaga kiran nasa daya shigo a daidai lokacin, "Hello mm" "Na'am Janany" "Wani na gani yanzu kamar kai" ta faɗa cikin sanyin murya haɗe da kwantar da kanta saman kujera, juyowa Nihal tayi ta kalle ta sannan taci gaba da driven ɗinta yayin da shi kuma gabansa yayi wata irin muguwar faɗuwa tare da juyawa da ƙarfi yana kallon gefe da gefen titi, kaddai ace Janan ta gan sa? Ya faɗa cikin ransa haɗe da cewa, "Ni kuma? A ina?" Ya tambaye ta "Anan babban round na cikin gari, cikin wata mota mai matuƙar kyan gaske.." da sauri ya katse ta yana faɗin, "A'a bani bane gaskiya, ni ga ni nan a anguwar mu na ajiye baro na zan shiga masallaci sallar isham, kin ji kiran salla ma ko?" Ya faɗa tare da kara wayar a dai dai saiti inda kiran ke fitowa daga masallacin dake kusa dashi cike da son gamsar da ita, "Ina ga dai a mafarki ne kika ganni Madam, ke kina ina yanzu?" "Gamu akan hanya zamu je bebeji plaza ni da Adda ta" Wani irin zaro idanuwa yayi jin inda zata je, kenan itama wajen zuwan ta kenan, bebeji plaza? ya tambayi kansa yana ƙoƙarin goge zufan daya soma tsattsafo masa a goshi, don har ga ALLAH baya buƙatar tasan ko shi waye yanzu har sai zuwa nan gaba, in kuwa haka ne shi da bebeji plaza sun yi bankwana har sai komai ya daidaita, zazzaƙar muryarta da yaji ta daki kunnuwan sa ce ta sashi dawowa daga dogon tunanin daya je, "ka gani ko hubbin ruh, son ka yayi mun kamu sosai gashi har ya fara sawa kana yi mun gizo, gaskiya ina son ka da yawa" ta faɗa a shagwaɓe, wata irin ajiyar zuciya ya sauke haɗe da lumshe idanuwa kafin yace, "Naki kika sani ranki shi daɗe, ai ni nawa son da nake yi maki baya kwatantuwa balle ya faɗu, fatana kawai na rayu aduniya don na bauta maki don kece abincin ruhina da zaisa yaci gaba da wanzuwa acikin gangar jikina, aduk lokacin daya rasaki kuma daidai yake dana rasa rayuwata gaba ɗaya, don haka ki kwantar da hankalin ki, kece rayuwar muhammad Muhriz, kuma shi ɗin naki ne ke kaɗai" "Ina fatan mala'ikun dake tare damu su karɓa wannan zance naka ta hanyar amsa mana da Amin, kai maƙura ne mm, zan iya bada komai nawa indai za'a bani kai, zan kuma jure wahala duk girmanta duk tsananin ta na rayu dakai har a badan aba da" "Godiya nake yi ranki shi daɗe, bari na shiga Masallaci an tayar da Sallah daga nan nayi mana addu'a ALLAH ya cika mana burin mu" "Shikenan, ka kula mani da kanka" "An gama ranki shi daɗe, i love you" dariya tayi cike dajin daɗi kafin tace, "I love You too hubbin ruh" sannan ta kashe wayar, "Waye shi?" Nihal ta tambayeta "Mm, your inlow to be" ta bata amsa a taƙaice, Dariya Nihal tayi haɗe da cewa, "Eyyeeee..kice autan Abba aure take so? Waye shi?, Kin faɗawa Abba kuwa tunda ni ɓoyo ake mun?" Dariya Janan tayi har tana rufe fuska a'a tilas taji kunya, Hannu Nihal ta ɗaga kamar zata kai mata ranƙwashi haɗe da cewa, "Wace kunyar tawa zaki ji ke da kika gama zaro kalamai sa la sa la a gabana" Sai da Janan ta ɗora kanta a saman kafaɗar Nihal sannan ta ce, "Adda soyayya ta cike take da ƙalubale shiyasa na kasa fuskantar ku daga ke har Abba da ita, sunansa Muhammad Muhriz mai dabino, talaka ne shi sosai domin sana'ar dabinon itace sana'ar sa, ba kowa bane, ba kuma ɗan kowa bane, amma a haka zuciyata ke son sa saboda shima yana so na sosai, kamar dai irin yanda kike jin girman soyayyar the charming ɗinki a zuciya haka nima nake jin soyayyar sa, nasan Abban mu na son ki sosai kuma zai iya yi maki komai, na roƙeki don girman ALLAH daki sa baki a lamarin soyayyata da mm hakan ne kaɗai zai cika mani mafarki na da kuma burin mu" Duk da ran Nihal ya ɓaci da jin kowaye mm, haka tayi parking a harabar bebeji plaza da isowarsu kenan jikinta a mace tana kallon 'yar uwar tata, kafin can tayi wata irin ajiyar zuciya haɗe da cewa, "Ke kuwa Janan meya kaiki aikata wannan kuskuren?, Kin fi kowa sanin yanda Abba ya raba hanya da irin wanda kike so, don me zaki bari hakan ta faru dake?, Look Janan! Kije kiyi tunani kuma ki sauya shawara domin wannan batayi ba kinji na faɗa maki" "But i love him Adda" "And i hate him ni kuma tun kafin na gansa, kina so ne kije ki jefa kanki a ƙangin wahala da bauta akan so? Nooo, hakan bazai yuyu ba, and i will never support that" Turo baki Janan tayi tare da haɗe rai ta kauda kanta gefe ba tare da ta koma cewa uffan ba, yayin da ita kuma ta saukar da glassis ɗin tagogin motar tana baza idanuwa inda zata hango the charming ɗin ta... #Comment #Vote #Share *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 20_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1237585076?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=0eOE%2F2y9oLisTGjT71L4rWlnWxdNWPfDaNN89Oo6lj8oD0QnQi4%2FebE9Hbn7wlq1f1e%2BOTsokQO7rFBk7TkE5QPfyCC8h9TXKd%2FPuto36%2BGONu41%2Fu12BnXk9M%2FeGUZL_ *KIN SAYI SHIRINMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SAYA BA MAZA KI HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN DOMIN SAMUN ƘARIN BAYANI +447894142004, 07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU MASU MATUƘAR ƘAYATARWA AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, ƳAR UWA GWADA KI GANI IDAN KINA CIKIN WUƊAN DA SUKAYI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADAMA BA😍* ______________________________ Mm kuwa leƙawa yayi ta jikin tagar mota yace da Jabir daya tasa Razina a gaba yana yi mata labaran ban dariya tana kwasar abutta hankali kwance, "Malam fito muyi Sallah" "In bar matar tawa cikin mota ita kaɗai?" "Ohon maka, in zaka fito malam ka fito tayarwa za a yi yanzu" "Gaskiya jeka, ai addinun nasiha malam, ai isham ce, zan iya yi idan zan kwantawa" Zaro idanuwa mm yayi ganin da gaske Jabir keyi har yana gyara zama, tsaki ya ja haɗe dasa hannu ya buɗe ƙofar da Razina take zaune ya ce, "Ke fito ki jiramu anan tunda shi ɗin bazai fito ba, wannan ai kai ne mayen soyayya bani ba" Habawa kafin mm ya rufe baki har Jabir ya fito ransa a ɗan ɓace ya zagayo ta inda suke yana faɗin, "Wai meye haka mm zaka wani fiddo mun da mata kan titi kowa ya gama kallemun ita, ba fa na son haka, pls my wife taimaka mun ki shiga daga ciki kar zuciyata ta buga, don ga wani munafiki can na hango yana arwala yana kallon ki" ya ƙare maganar fuska a ɗauke tare da sa Razina ta koma cikin motar tana faman yi masa dariya, shima mm dariyar ya basa don haka sai kawai ya mere baki yabar wajen, dama da arwalar su ta magrib, sai ya faɗa masallaci kawai, Jabir kuwa sai da yaleƙa ya cewa Razina, "Wato dariya ma kikeyi ko?, Zaki dena ne idan kika ji ance gani can ana dambe dani da shi a masallaci saboda kalmar mun mata da ya yi" "Kayi haƙuri na dena, ni da bana kallon kowa a matsayin namiji sai kai, haka kuna nima bana da banbanci da namiji a idanuwan kowane namiji in ba kai ba, ƙyale yaya mm jeka kayi sallah kayi mana addu'a kaji zauji na" Murmushi ya saki haɗe da shafa kai saboda jin kunyar yanda ƙaramar yarinya ke driving ɗin sa like crazy haɗe da barin wajen da sauri jin har anyi ruku'i, kusan mintuna goma sha huɗu suka shafe kafin su dawo daga wajen sallar, suna dawowa suka nufi hanyar gida suna tafe mm na bashi labarin yanda sukayi da Janan ɗazu, wai ta gane sa lokacin da suka shigo round, sosai Jabir ya s dariya haɗe da cewa, "Kace kawai asirin ka ya tonu" "Asirin mu dai malam, ai guguwar da bata barni ba bazata taɓa barin ka ba" "Wannan kam dole sai ta barni, kai ne dai aruwa" "To shikenan, ina ga dai zan rage fita da mota, hak kuma zan dena zuwa bebeji dama ɓarayin cikin garin nan" "Kai ta jiyo malam, ni dai na faɗa maka tallan ma na kusa dena raka ka, zan koma shafi abunda kai kuma sai kaci gaba da gashi ko ba haka ba wifey?" Ita dai Razina dariya kawai tayi bata ce komai ba, amma in son samunta ne gaskiya masoyin ta ya dena fita tallar nan haka rana na koɗa mata shi haka, ga shi 'yan mata kullum cikin kalle mata shi suke, Bayan wata ɗaya da faruwar abubuwan da suka wuce tsakanin Jabir da masoyiyar Razina, Janan da masoyinta Muhriz, Amira da ƙawar ta Janan, Nihal da the charming ɗin ta, ingaski da kuma ɗalibar sa Janan, cikin wannan lokacin soyayya da shaƙuwa mai tsananin ƙarfi ce ta sake shiga tsakanin mm da Janan, inda suke jin baza su taɓa iya rayuwa ba idan babu junan, matuƙar bata da ecture ko kuma sun ƙare to fa suna tare maƙale da juna, haka zata zo su sha firar su cikin so da a guarding luv ko a motar ta ko kuma anan inda suke sana'ar su, a bayyane suke nuna juna soyayyar ba tare da wani shayi ko shakku ko kuma tsoro ba, inda nan take kowa yasan irin ƙauna da alaƙar dake tsakanin su, da irin tarin soyayyar da suke yiwa juna, da yawa sun taya su murna saboda ganin sun dace da juna, yayin da da yawan su ire iren Amira dake ƙaunar mm sun ji baƙin cikin taren ta su kuma sun nuna jin zafin su a fili tare da nunawa Janan ƙiyayya marar ɓoyuwa, don kuwa da wuya tawuce bata ji ana zaginta da tsincen ta ba akan ta maƙalewa wanda bai dace da rayuwar ta ba don taga yana da kyau, komai dai meye ita ko a jikinta don ba ta damu ba balle ma ta nuna masu tasn suna yi, Amira ma tayi hushin da ita har ta gaji ta dena don taga ba abun da ya rageta dashi sai ma ƙaruwar farinciki da taga tana samu ita da masoyin ta, a zahiri sun koma kamar yanda suke a da amma a ƙasan zuciyarta tana nan ƙullace da ita tare da neman duk wani abu da zai kawo kusanci tsakanin ta da mm yanda zata ƙulla mata makirci da ko yana so ko baya so sai ya rabu da ita, a ɓangaren Ingaski kuwa ko hanya baya fatan ta haɗasa da Janan, a class ma idan ya shiga yi masu lecture baya barin idanuwan sa su haɗu da nata, ita abun har mamaki yake bata, mutumen daya ɗauki alwashi akan yi mata wulaƙanci da tozar ta ta, sai gashi shine ko ido baya son haɗawa da ita, ko me yasa ta tambayi kanta a karo na ba adadi, ɗaya ɓangaren zuciyar ta ne ya bata amsa da cewa ƙarfin addu'ar da takeyi ne, don tun lokacin da abun ya faru tsakanin ta dashi take addu'a ALLAH ka shiga tsakaninsu ya kuma kare ta da dukkanin sharri da mugun nufinsa. Haka ma soyayyar Jabir da Razina abun sai wanda ya gani, kullum sai daɗa shaƙuwa suke yi tare da ƙara son juna, ta yanda basa barin duk wani abu da zai ɓata ransu ya shigo rayuwar su, idan ka ga yanda suke rayuwa sai ka rantse dama sun daɗe a ƙaunar juna, Nihal kuwa tayi yawo har ta gaji amma ta rasa samun farin cikin ta, sannu a hankali ta fara shiga damuwa da ƙunci, ganin haka yasa Abbansu ya je har bebeji plaza da ita ya biya maƙuddan kuɗi akan a nuna masa cctv cameras ɗin dake cikin wajen gaba ɗaya, cikin rashin sa a aka ce ai gaba ɗaya system da memories ɗin sun ƙone sanadiyar gobarar da aka samu a ɓangaren wajen kwanakki, gaba ɗaya ma cctv cameras ɗin satin nan aka gama abun tasu da wasu sababbi, gashi mm ya dena zuwa plaza lokacin balle a samu wasu bayanin sa acikin satin, haka Abba ya koma tamkar wani mahaukaci wajen nemowa 'yarsa da yake ji da ita farin cikin ta amma hakan ya faskara, kullum ita ce kuka, na yau daban na gobe daban gaba ɗaya duk tabi ta rame tamkar ba ita ba, sosai abun ke matuƙar damun Abba da ita kanta Janan amma sun rasa yanda zasuyi su nemo mata wanda take matuƙar ƙauna safe, ran da kuma marece tunda ko sunan sa bata sani ba balle asan ta ina za a ci gaba da neman sa, musamman Abba yasa aka kawo masa mai zane don ta faɗi yanda surar sa take a zana amma tana farawa ta kasa iyar wa, daga ƙarshe ma kawai tasa kuka haɗe da ture allon zanen da sauran kayan aikin gaba ɗaya, don hatta bayanin da tafara bayar wa da aka zana cewa tayi sam ba shi bane, Janan dai banda addu'a babu abunda take yi mata, sai kuma nasihohi da baka rasa ba wasu lokkutan, Sanadiyar hakan ciwon zuciya ya kama Nihal saboda yawan tunani da damuwa, duk wani aiki da Abba keyi ya dakatar dashi gefe ya koma fafutukar yanda zai nemowa Nihal masoyinta, ana haka itama Janan ta nemi mm ta rasa, ɓat yayi mata ɓatan dabo a school ta dena ganinsa gaba ɗaya har aka kwashe sati ɗaya bashi ba labari, haka ma wayarsa idan ta kira sam bata samu, ta rasa ina zata sa kanta taji daɗi tun tana haƙuri har ta soma gazawa, gashi bai taɓa kai ta gidan su ba balle taje ta neme sa ta gani ko lafiya yake, wasa wasa har akayi kwana goma ba shi ba tsammanin sa, halin da Nihal take ciki yasa ta ɓoye tata damuwar da tashin hankali, sai dai idan abun ya dameta ta shige part ɗin Hajiya zee taci kukan ta mai isarta ta fito, school ɗin ma duk sai taji ta fita ranta dama watanni suka rage ta zama jarabawar ƙarewa, da ita da Nihal ɗin n rasa mai bawa wani baki yanzu, ƙwara ma Nihal kowa yasan damuwar ta, amma ita da take da matuƙar zurfin ciki babu wanda yasan meke damun ta, Madam florence da hajia zee sunyi tambaya har sun gaji sun sa mata ido tare da ta 'allaƙa abun da ƙilan rashin lafiyar ƴar uwar tata shine sila, ana haka suna kwance falon ƙasa ita da Nihal sai ga mai gadi yazo yayi sallama wai Janan ta fito ana yimata sallama a waje, "Je kace bata nan" ta faɗa tare da juya kwancin ta, har ya tafi sai mm ya faɗa mata arai da sauri ta ƙwala masa kira haɗe da cewa "jeka kace waye" don bata son fitar, ba a jima ba ya dawo ya ce, "Wai ya ce ace mm ne.." ai bai ƙarasa ba da sauri ta zari mayafin ko mai babu a fuskar ta don lokacin bata jima da gama kukan data saba yi ba a ɗan kwanakin, a dai dai block ɗin round about ɗin dake tsakiyar farfajiyar gidan taje ta tsaya tare da folding ɗin hannayenta cike da farin ciki ta ce gate man yaje ya ce masa ya shigo, "Hajia..!" Mai gadin ya faɗa cike da mamaki, ganin sam wanda yazo neman ta ba kalar ta bace kuma idan Abba ma ya iskosa cikin gidan zai iya korar sa daga aikin sa gaba ɗaya, "Ka shigo dashi nace ado" ta faɗa a ɗan hasale, ba yanda ya iya dole ya je ya shigo dashi, duk da mm nada gwargwadon arziƙin sa sai daya saki baki ganin irin tarin dukiyar dake shimfiɗe gidan, motoci kaɗai daya tsaya ƙirgawa sun kai ƙwaya goma acan jere wajen parking space, a ta ɗaya ɓangaren kuwa guiding ne da aka kashewa maƙudan kuɗi dake ɗauke da kalolin nau'ukan tsuntsaye masu matuƙar burgewa da shikkoki na alfarma dake fidda wani irin daddaɗan iska da ƙamshi mai ratsa zuciya, lumshe idanuwan sa yayi haɗe da buɗe wa lokacin daya hangota a tsaye yana ƙara yaba irin kyawo da kyakkyawar surar da ALLAH yayi mata, ganin anyi tsaye an kasa ƙarasowa kuma taji shigowar sa yasa ta ɗago kai, karaf suka yi ido biyu da mm, ashe da gaske ɗin shine don sam zuciyarta bata gama amincewa da shi ɗin ne ba, cike da mamaki take kallonsa ta kasa koda motsawa a wajen yanda ta gansa a ɗan yamutse, don hatta kayan da ta gani a jikin sa basu ta saba ganin sa da su ba, hankalin ta ne ya tashi ta nufi wajen sa tana ƙare masa kallo cike da damuwa kafin ta tabbatar shi ɗin ne, kuma ta fashe dashi wanda za a iya kiransa da najin daɗi haɗe da cewa, "Ina ka shige ne haka mm ka barni cikin zullumi da damuwa? Ina kaje ne ka manta dani gaba ɗaya?, Wane laifi nayi maka da yasa kayi mani hukunci da mafi munin hukunci daya jefa Ni cikin damuwa tare da azabtar da gangar jiki da ruhina duka?, Mm..." Saurin dakatar da ita yayi ganin yanda hawaye ke kwaranya a fuskar ta haɗe da cewa, "Ya isa haka Janan ya isa, don ALLAH kiyi haƙuri bazan iya jurar ci gaba da ganin hawayen nan naki ba, Janan nima bada son raina nayi hakan ba, bada son raina hakan tafaru ba ko kaɗan, ni kaina na matuƙar cutuwa na kuma azabtu da rashin ki, dole ce kawai ta tilasta faruwar haka agareni" "Don me dole zata tilasta maka hakan bayan kasan zuciya ta bazata ɗauka ba?" "Sha'anin iyaye abune me matuƙar muhimmanci, Momy ce ba ta jin daɗi shiyasa hankali na ba a kwance ba, ni da Jabir munyi amfani da kuɗin hannun mu dana sana'ar mu don siya mata magani shiyasa muka dena shiga school ɗin ku, duk da haka kuma kuɗin basu isa mu biya mata kuɗin magani ba, hakan yasa muka sai da wayoyin hannun mu muka ƙara dasu, wannan shine dalilin da yasa kika ga ban kira ki ba, da kuma kika kira baki same ni ba, yanzu ma yau aka sallamomu nace bari nazo na ganeki" Hannayen ta tasa ta goge hawayen da suka jiƙa mata fuska haɗe da cewa, "Na gamsu kuma na yarda da bayanan ka, amma na roƙeka koda hakan zata sake faruwa bama fata don ALLAH ko saƙo ne kari ƙa bar mani, ko ka ari wayar wani ka sanar dani, idan ba haka ba, zaka iya tadda ka rasani a lokacin da zaka waiwayo ni" "Subhanallahi, ki dena faɗar hakan, ai a tare zamu rayu kuma atare zamu mutu in sha ALLAH" Ɗan hararar sa tayi cike da kewar sa tana turo baki haɗe da cewa, "Hubin ruh amma sai naga ka canza da yawa kamar ba kai ba, a zahiri za aga baka da kwanciyar hankali, amma ka ƙara kyau da haske sosai, ramewa kaɗai ce kayi itama bada yawa ba, da ƙyar ma idan kana tuno wa dani" takai zancen cikin shagwaɓe fuskar data saba yi masa, "Tunowa kai Madam!, Ai wannan ramewar itace zata tabbatar maki da nayi kewarki sosai ba kaɗan ba, hasken fata kuwa ai dole zan ɗan ƙara tunda kinga nadena shiga rana tallar da muke yi, ajiye wannan a gefe masoyiyata ya kike?" "Maganar gaskiya ba lau ba hubbin ruh, kai da kan ka idan ka kalleni zaka bawa kanka amsar wannan tambayar, ya jikin Momyn?" "Ta samu sauƙi" "ALLAH ya ƙara sauƙi, ya Jabir da sister Razina?" "Duk suna lafiya, sun ce na gaisheki sosai" "Ina amsawa" Shiru suka yi na ɗan wasu lokutta kafin mm, yace "Nurul alb ya soyayya ta?, injin wanda ya fini iya reno da kulawa bai zo ya ingije ni ba?" "Ka dena wannan zancen, zuciyar da ta kasa kula kowa taya za a yi ta gano wancan keda kulawa ko iya reno bayan wanda ke bata kulawar data saani shi kaɗai?, Ai zuciyar Janan babu wani mai kula da ita bacin kai balle har ya ingije ka a matsayin data ɗora ka akai" "Iyyeeeee kice na zama ɗan gata ni mm, ba nida abokin takara balle kuma 'yan adawa" "Sosai kuwa, amma fa karka saki jiki da yawa irin yanda kayi har na fara tunanin ko ka gudu ka barni ne, idan ba haka ba kuwa sai dai kaji wani yazo ya sace zuciyar nurul alb ɗin ka kuma yayi wuff da ita" "Tab! Ki dena faɗa kar kisa na some maki a wajen nan, waye zai yi wannan gangancin haka ya haɗu da mahaukaci Janan!?, Ai nafi so nayi masa dukan mutuwa akan matar nan tawa in yaso ni ayi wuff dani a prison.." Dariya ta saka har tana tafa hannayen ta don ba ƙaramar dariya ya bata ba, Da haka suka saki jiki suka yita firar su hankali kwance cike da farin cikin ganin juna da suka daɗe basu yi ba, wanda hakan ya faru ne sanadiyar komawar da mm yayi wajen aikin sa, inda nan take suka turasa ƙasar Lebanon da u.k da Austaraliya da kuma sauran ƙasashe uku da jiragen su za suyi zirga zirga acan, ya sani sanadiyar hutun daya ɗauka har na kusan wata uku ba zasu taɓa barin shi ya huta ba yanzu ɗaya koma, hakan yasa ya yanke shawarar yin amfani da damar ta hanyar kawo mata dalilin da zai nuna ya ajiye sana'ar dabino gaba ɗaya, ana haka ne kuma hawan jinin Momy ya tashi, lokacin yana ƙasar Austaraliya, shine fa ya bata hujjar cewa mom ce ba ta jin daɗi don tabbatar da hujjojin sa na rashin zuwa da kuma kiranta, amma shi kan shi ya san ba kaɗan ya ji jikin rashin ganin ta da kuma jin muryar ta ba. Gaban Janan ne yayi wata irin muguwar faɗuwa haɗe da razana lokaci ɗaya da ta ga gate ɗin gidan nasu ya wangame motoci na shigowa tare da guard ɗin mahaifin nata biye dasu aguje, wanda hakan ke nuni da dawowar mahaifinta daga tafiyar da yayi Abuja shekaran jiya, mota ɗaya ce a gaba sai wacce mahaifinta ke ciki a tsakiya da wasu guda biyu a bayan ta, kallo ɗaya mm yayiwa motocin ya kauda kai yana kallon yanda ta ɗan firgita da ganinsu, "Meke faruwa Janany?, Ko kina jin tsoron mahaifinki ya gane ni ne?" Cike da tsoro ta juyo tana kallon sa haɗe da cewa "ba tsoron ya gane ka nake yi ba mm, abunda zai iya yi maka ne nake tsoro" "Kar ki damu indai don ni ne, a shirye nake dana fuskanci ko wane irin ƙalubale ne indai a kanki ne" "Waye kai? Kuma kai ɗan gidan uban waye? wa kuma ya baka damar shigowa har cikin gidana haka da kai?" Suka jiyo muryar Abba tamkar faɗowar aradu a gaban su yana

Chapter 12 of 40