Share this page
ki fashe" ya ƙare zancen yana kallon gefen da Abba yake zaune ya cika yayi fam, Hajiya kaka da batasan inda maganar tasa ta nufa ba ta ce, "Ai kai ɗin ne wani zubin ka fiye taurin rai, ya Momyn taka?" "Lafiya klw take, kiyita haƙuri da taurin ran nan nawa, kin san wuce gado wuya ne dashi" "Ah to, kuma kayi gaskiya, ALLAH to yayi maka magani" "Amin Hajiya, yanzu dai ga saƙon ki nan, ta ce na gaisheki, kuma Razina ta ce na faɗa maki, ki ɗauke idon ki daga ɗan saurayin nan nata, don sama ta riga data yiwa yaro nisa saidai yasa ido yayi kallo" "Ita dai ta sani da kishin nan nata, indai tani ka faɗa mata cewa na haƙura na bar mata kai gaba ɗaya" "Kai Hajiya, da wuri haka?, Ko da yake matar tawa ta musamman ce, dole kowa yakkara da ita yaja baya don ita ɗin kainuwa ce dashen ALLAH.." "Oh kai kam ALLAH yayi maka magani, ba kada aiki sai karin magana abaki kamar wata tsohuwa, ko dai ni ban fiye yin wannan ɗabi'a ba balle kai" "To ya zakiyi, kinga ke bakiyi ba amma jininki nayi, don haka kawai kiyi haƙuri tunda anriga angama" "Ya zanyi fa, ai na haƙura kaji dashi can" "Nadai ji, ina mutuniyar?" "Wa kenan?" "Uwar ɗakin ki mana" "Au, waccan ja'irar?, Kai rabani da zancen ta kwana biyu bata shigo ba" Gaba ɗaya Hajiya ta manta da zancen Abba a wajen har sai da taji yayi gyaran murya haɗe da miƙewa yana faɗin, "Hajiya zan wuce" "A'ah, shin dama baka tafi ba?, To ALLAH ya kiyaye" "Amin ya faɗa tare da gyara babbar rigar sa yasa takalman sa zai fice" Ba tare da Jabir ya kalli gefen da yake ba ya ce, "Grandma kenan, yanzu dai da kanki kin banbance tsakanin ke da Razina, duk dake ɗin jinin jiki ce dake yawo ajikina to ita kuma wani mahaɗi ce ta wanzuwar farinciki agareni, indai kina son ki riƙa ganin walwalata haka to tabbas sai kin dena nisanta ni da ita domin hakan ne kaɗai zai tabbatar maki da samuwar farinciki na" Tsaye Abba yayi kamar zai juyo sai kuma ya fasa yaci gaba da tafiyar sa, kallon Hajiya Jabir yayi ya saki murmushi ganin saƙonnin sa na isa inda yake so yanda ya kamata sannan yaci gaba da cewa, "Ya naji kinyi shiru, ALLAH dai yasa ba ɓaci ranki yayi ba, domin yin hakan na illa ga lafiya, don haka ki kula" Da sauri Abba ya ƙarasa ficewa cikin ɓacin rai tare da gajiya da tarin habaice habaicen da Jabir ke aiko masa, tabbas sai ya yi maganin wannan yaron domin yana nema ya tsallake gona da iri, kuma shi sam baya ɗaukar hakan ga kowaye, Shiru Hajiya tayi tana kallon Jabir daya cije gefen leɓensa na ƙasa yana kallon ƙofar da Abba ya fita haɗe dayin gyaran murya ta ce, "Anya Jabir rayuwa zata tafi haka? Shi ɗin fa ƙanen mahaifin ka ne, jefar da haƙƙin ka da ALLAH ya ɗora akansa da ya yi bashi zaisa kaima ka jefar da nasa haƙin dake kanka ba, duk lalacewar sa shi ɗin tamkar mahaifin ka ne kuma bazaka taɓa sauya hakan ba, nasan bai kyautawa ga abubuwan da yakeyi amma ina nan ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na sauyasa kafin ta ALLAH ta kasance agareni, saboda haka ko kaɗan ne ka samu gurbin da zaka iya basa a zuciyar ka kamar yanda kayimun ka yafesa kuma ka bashi girmansa na ƙanen mahaifin ka" "Kiyi haƙuri Hajiya kaka, bazan iya haka ba" ya faɗa tare da miƙewa ya fice abunsa, kuka ta fashe dashi tana mai sake nadamar barin aikata kuskuren daya faru acikin zuri'ar ta tare da roƙon ALLAH ya yafe mata ya haɗe mata kansu aduk inda suke, A ɓangaren Janan kuwa yau kimanin kwanan su uku kenan da fara jarabawa, karatu takeyi sosai ta yanda gaba ɗaya ta tattara hankalinta ta maida akanta, ta jingine komai a gefe ta ajiye ta fuskanci abunda ke gaban ta, ba tada wani buri a yanzu daya wuce taga ta ƙare exam ɗin ta lafiya kuma tafito da A fly, hatta fita ma ta dena yi kullum tana guiden tana karatu idan kuma bata can tana ɗakin ta, abu biyu zuwa uku ne ke tsaida ta, sallah da wanka ko kuma kiran mm kawai ke tadata, amma hatta abinci wani lokacin tana ci tana karatu ne, gaba ɗaya har faɗawa tayi saboda yanda take stressing kanta, ganin haka yasa shima mm ya rage damun ta da kira koda kuwa yana buƙatar hakan don ɗai ya tayata ganin ta cika burinta, Ata ɗaya ɓangaren kuwa tuni ya gama yiwa Momy da Razina visa, kwana biyu masu zuwa ya rage su wuce ƙasar china tare dashi don haɗo lefensu, haka ma ta ɓangaren Captain Asgar, tuni suma sun gama haɗo lefensu da sauran kayan aure, wanda Abba ya gama tsarawa cewa ana saura sati ɗaya Janan ta kammala jarabawa zasu zo a kawo tare da fara shagalin bikin bayan ta kammala.... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 48_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* *********** _https://www.wattpad.com/1257064678?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=n01QYbdmE1VmpOZhkfOBdxk5IfMfXscET1zmvuK7qBgi5RICEHiad6fGUtKxqZrlaUCfZR0B3%2Fq0FwITj04KFLztmRf3eI4Oa8%2BJNyGCBSoM%2FOADG342bVhojxlhOpVy_ ****** *Page ɗin yau naku ne AUNTY MAIJIDDA MUSA, AUNTY FARIDA MUHAMMAD ABBAS, SISTER NAJIDA BICCHI da kuma NANA RUƘAYYA, Ina matuƙar godiya yanda kuke ƙoƙarin bibiyar wannan littafi, alkhairan ALLAH sukai maku aduk inda kuke haɗi da nagartaccen farinciki a zukatan ku marar yankewa, ALLAH kuma ya raya maku zuriarku ya sanya mata albarka ya ƙare maku ita ga dukkanin abun ƙi, fillah ina yimaku ƙauna ta musamman har cikin zuciyata, ngd, ngd sosai ALLAH yabar taren mu har a aljannah👏* ______________________________ Kasancewar a chana mm zasu fara sauka idan sun ɗauki passengers kafin su wuce dubai bayan kwana biyu, suyo kwana uku acan suna jigilar kai da komowa a tsakanin ƙasashen sannan su sake dawowa china su ɗebi passenger ɗin da zasu dawo Nigeria dasu ya sa ya yanke shawarar kiran wani abokin sa dake zaune can wanda mafiya lokutta wajensa yake sauka idan yaje ƙasar mai suna Mu'azzam, haifaffen ɗan Nigeria ne a jahar Zamfara, aikine ya kaisa ƙasar a wani kamfanin ƙera motoci, sai kuma ALLAH ya nufi acan zaman nasa yake, bayan sun gaisa ya sanar mashi da cewa yau suna kan hanyar isowa ƙasar yana so ya sama masa ɗaki ɗaya a hotel da zai sauki su Momy acan kafin ranar da zasu koma, sosai abun ya bawa Mu'azzam mamaki daya ji mm ya ce wai ya kama masa ɗauki ɗaya a hotel don zaizo da mutane, murmushi kawai yayi ya amsa masa da to don yasan indai shine kaɗan daga cikin aikinsa kenan, a cewar sa baya son yana ɗora masa lalura shiyasa ko shi sai da yayi da gaske sannan ya amince ya riƙa sauka wajensa a maimakon hotel, don haka kawai ya ƙyalesa ya sa aka gyara ɗaki ɗaya daga cikin ɗakunan dake gidan, cike da farinciki da ya sanar da matar tasa mai suna shahida wacce ta kasan ce ƴar nan ƙasar China cewa mm ne ke tafi da baƙi ta shiga shisshirya masu abunda zasu ci kafin su ƙara so, don itama ba laifi tana da matuƙar son mutane sosai, anan ƙasar ya haɗu da ita wajen aikin sa, wasa wasa kuma suka fara soyayya kuma cikin ikon ALLAH har ta kaisu gayun aure, yanzu haka suna da yara biyu, Haisam da kuma Ƙaisah. Suna isowa mm ya kirasa suka je suka ɗauki su daga airport shi da Shahida, basu wani jima ba da sauka ba suka isa inda cikin girmamawa Mu'azzam da Shahida suka shiga gaishe da mom, haka ma Razina ta gaishesu itama sannan suka yi masu iso wajen motar da suka zo da ita suka shiga Mu'azzam ya ja suka tafi, kai tsaye hanyar gida mm yaga ya nufa dasu a maimakon hotel kamar yanda yayi tsammani, juyowa ya yi ya kallesa fuskarsa ɗauke da alamun tambaya mu'azzam ya yi kamar bai ganesa ba, ita kuwa Razina tuni fira ta ɓarke tsakanin ta da Shahida kai kace sun saba da juna sai faman zuba idanuwa takeyi kan titi tana kallon gari duk inda suka wuce sai ta tambayeta ina ne ita kuma tana bata amsa cikin harshen turanci kamar yanda tayi mata don ba laifi takan fahimta kaɗan kaɗan, Hausar ce dai har yanzu bata zauna mata abaki daidai ba, ita kuwa Momy tunda suka gaisa bata sake cewa uffan ba saboda yanda jikinta yayi mata tiɓis saboda gajiya, juyowa mm yayi tare da kallon Razina ya ce, "Ai fa, ba zama ɗan ƙauye ya zo birni, duk kin bi kin ishi mutane da surutu sai kace ke kaɗai acikin motar" dariya Shahida tayi don ta fahimci me yake cewa, sai da ta kalli yanda Razina ta ƙwaɓe fuska jin abunda ya faɗa sannan ta ce, "Yeah is good, is good, allow her to talk, i like the way she's" "Nooo..I don't want her to disturb you, she's very talkative" "Rilly! Wow I like her" dariya Mu'azzam yayi haɗe da kallon sa ya ce, "Kama fidda bakinka malan, in ba haka ba ka ji kunya don indai Shahida ce to an haɗu da an dace, itama ɗin gwana ce ta bugawa ga jarida wajen surutu" "ALLAH?" "Hmmm, ai yanzun nan ne zata baka kunya in kafiye zaƙewa tsakaninsu, shiyasa nake roƙon ALLAH yasa kar yaran nan idan sun girma su biyo ta da ɗan banzar surutu, musamman ma Haisam da babu ruwansa" dariya mm ya kwashe da ita ganin yanda Shahida ta kwaɓe fuska ta madubi tana ballawa Mu'azzam harara jin abunda ya faɗa haɗe da cewa, "Tab..aikuwa kasan barewa baza tayi gudu ɗan ta yayi rarrafe ba, ai kaima ɗin ba abarka a baya ba indai wajen surutu ne" "Inaaa...ai ko kaɗan ban kamo ƙafarta ba, parrot ma daya ganta sai da yayi saluting nata har kake wani haɗa ni da ita" ya ƙare zancen cikin zolaya yana ƙyarenta ta madubi haɗe da kashe mata ido, ɗauke kai tayi tayi kamar bata ganesa ba shi kuwa mm ya ce, "Yanzu dai tsakanin ku ne ba ruwana a fiddani ciki, Madam sorry pls" Da haka suka ƙarasa gida mai gadi ya buɗe masu gate ya shige da motar ya yi parking, suna fitowa mm yayi saurin zagayowa ya miƙa wa Momy dake ƙoƙarin fitowa hannu ta riƙosa haɗe da cewa, "Sannu Momy, kin gaji ko?" "Bari bari Muhriz, jin jiki na nake yi tamkar an bani kashi, kai gaskiya kuna ƙoƙari ni irin wannan doguwar tafiya ba sonta nake yi ba" "Kai Momy, ni dake son ƙarshen shekarar nan na kaiki hajji, idan kin dawo kuma mutafi umura tare" ya ƙare zancen yana dariya ganin yanda take takawa a hankali riƙe da hannunsa saboda yanda ƙafafuwan keyi mata tsami, "Indai hajji ce zan daure naje, amma umura na yafe bazan iya ba", ta ƙare zancen da dukkanin gaskiya dake fitowa daga ƙasan zuciyar ta, Sai da suka fara watso ruwa suka ranka sallolin dake kansu sannan suka zauna cin abinci, duk da ba irin abincin Hausawa bane sun ci sosai don ba laifi yayi masu daɗi, hakan kuwa ba ƙaramin farantawa Shahida rai yayi ba saboda tana son mutum mai sakin jiki da kuma rashin nuna mata ƙyama, wanda mafiya lokutta hausawan mu haka suke ga ire iren yare da basu sani ba, Bayan sun kammala mm ya kalli Mu'azzam dake latsar waya ya ce, "Wai ina yaran nawa suke ne?" "Oh!, wai Haisam da Ƙaisa?, shi yana wajen lesson ita kuma Inaga bacci takeyi" "No wander, shiyasa banji ƙilbasar su ba tun da muka iso" "Ai kuwa, haddai Ƙaisa uwar rigima, da yanzu ka ji kukan ta ya fi a ƙirga" Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mm ya yi haɗe da cewa, "Think lokacin Sallah ya yi fa" "Oh, haka ne fa, tashi muje daga nan sai mu biya mu ɗauko Haisam" "Wai dama ba anan cikin gida ake lesson ɗin ba?" "Eh acan gidan uncle ɗin Madam ne ake yimasu shida ƙannen ta" Daga haka mm bai sake cewa komai ba ya yi gaba shi kuma ya bisa a baya bayan ya ƙwalawa Shahida kira dake can zaune tana kwasar fira ita da Razina Momy na aka baki itama jefi jefi ya ce ta ɗan haɗa masu abu marar nauyi kafin su dawo sannan ya fice, sai da ta koma ta sanarwa dasu Momy lokacin sallar magrib yayi sannan ta wuce ɗakin ta itama, kasancewar su Momy nada arwalla sai kawai suka tashi suka yi sallar su sannan suka fito falo suka zauna, daidai lokacin Ƙaisa da bata wuce shekaru uku ba ta taso bacci tana murzar idanuwa, tana kawowa falon ta saki idanuwa tana kallon baƙin fuskar dake ci, hannu Janan ta miƙa mata haɗe da cewa, "Come.." kafin ta rufe baki ta ja baya haɗe da ƙwalawa Shahida dake zaune tana addu'a kira, "Mahmah" Shahida ta fito da sauri don ta zata wani abun ne sai kawai taga Ƙaisa ta ɓuya a bayan ta tana nuna mata inda su Janan ke zaune, ajiyar zuciya tayi tare da jawo ta ta nufo wajensu da ita tana faɗin, "Come Ƙaisa, ki gaishe ku kin ji ta" Dariya Razina tayi haɗe da cewa, "Ba haka zaki ce ba, ki gaishu su, kin ji ko" "Ok , to ki gaisheta kin ji ko" "Gaishe su zaki ce" ta sake gyara mata tana dariya, cike da ƙosawa koyon yanda zata faɗa ɗin ta ce, "Oh my God, Ƙaisa greet them, they are your momys" ta ƙare zancen tare da ɗorata akan jikin Momy, da sauri ta zille tana maƙe kafaɗa haɗe da cewa "No momm.. she's an old woman, i don't want her to be my mom" Dariya duk suka saka cike da jin kunya shahida taji tamkar ta nitse a ƙasa, hannu ta ɗaga da niyar dukan ta Momy ta ce, "Noo...allow her mana, she's a small girl abi" kallonta Razina tayi har lokacin bata dena dariya ba kafin tace, "So, what up me, do you like me?" "Yeah i like you" ta faɗa haɗe da zuwa jikinta ta faɗa, dariya Momy tayi haɗe da kallon Shahida ta ce, "You see!, this are the kind of children we have now, they already know their parents since before they where born, thank God i hv my own by my side, ku riƙe naku in riƙe nawa" "A'ah Momy kar kice haka, kika sani ko Ƙaisa ce zata kaiki Saudiya" "Ta makaro ai yarona ya riga daya rigata, taje can na yafe ta biyawa iyayen ta" yanda Momy ke tsokanar Ƙaisa ɗin da wasa ana dariya har tana riƙon ƙafar ta tana janyewa ba ƙaramin burge Shahida yayi ba, sai taji ina ma ace anan take zaune tare dasu, da family ɗin nata sunfi kowa zama cikin farin ciki akoda yaushe. Miƙewa tayi ta shiga kitchen ta barsu nan falo zaune bayan ta kunna masu tv, ɗan farfeaun kayan ciki daya sha vegitables ta shiga haɗa masu kamar yanda maigidan nata ya ce tayi, bayan ta ƙarasa ta shiga ciki tayo wanka ta saka atamfarta mai kyau itama ta fito falon ta zauna riƙe da ɗan kwalin a hannu tana ƙoƙarin ɗaurawa amma ta kasa, ajiye Ƙaisa Razina tayi dake jikinta akan kujera haɗe da miƙa hannu tana cewa Shahida, "lemme help you aunty" ba musu ta miƙa mata ɗan kwalin ta yimata ɗauri mai kyau haɗe da fikkar da jelar gashin nata a gefe sannan ta ɗan ja ɗan kwalin kadan a baya yanda goshin zai ɗan fita tana faɗin, "Wow! aunty you look more beautiful" "I know my sister, shiyasa ina son kayanta nan naku" "Not kayanta nan naku, kayan nan naku" "Ok , kayan nan naku" Shahida tafaɗa tana dariya, suna zaune su mm suka dawo tare da Haisam da shekarunsa zasu kai biyar zuwa shidda haka, cike da natsuwa ya ƙaraso cikin falon ya fara gaida mom ɗin sa sannan ya gaida su Momy da Razina yana binsu da kallo, "Haisam, do you know them" Mu'azzam dake riƙe da makullin mota yana ƙoƙarin zaunawa kusa da Shahida ya faɗa yana kallonsa, "No dad" ya bashi amsa tare da ɗago kai ya kalli mm sannan ya sake maida kallonsa ga Razina dake zaune, ya ce "But dad she's looking a like with uncle Muhriz" "Yes, sibling ɗin sa ce, wannan kuma mom ɗin su" ya bashi amsa da Hausa don sosai yake son su iya yaren nasa, murmushi Haisam yayi yana kallon Momy tare da sake gaisheta ta miƙa masa hannu ta ce yaje kusa da ita ya zauna, ba musu kuwa ya je ya zauna ta shiga tambayarsa ya karatu, bayan ya amsa masa ta ɗago kai tana kallon mm haɗe da cewa, "To da alama shi wannan maigidan nawa yana auren, su o'oh dai ne ba yarda" mm na dariya ya ce, "To Momy banda abunki wake yarda da kishiya in ba dole ba, ai da gaskiyar Ƙaisa ƙara tayi ta kanta ko little ɗin uncle" ya ƙare zancen tare da lakutar chick ɗin ta yana yimata wasa, "To ai shikenan, sai taje can ta ƙarasa" Mu'azzam kuwa tuni ya shafa'a da kallon Razina dake ɗauke da Ƙaisa, sai yaga har wata kama takeyi da ita musamman da yaji wani yanayi akanta cikin zuciyar sa, kallon da yakeyi mata ya sata tsarguwa ta miƙe tare da ajiye Ƙaisa ta nufi kitchen inda taga Shahida tayi, saida ta shige sannan ya kauda kansa yana murmushi haɗe da kallon mm ya ce, "Friend na gani fa ina so?" Harara mm ya balla masa haɗe da cewa, "Bakada aiki gaskiya, to an rigaka" "Are you serious?" "Yes upcouse" mm ya bashi amsa tare da ficewa falon don kar ya ɓallo tmasa ruwa, a can wajen wani ɗan corridor ya nufa dake ɗauke da kujeru ya zauna tare da ciro wayar sa ya rubuta daddaɗan message tare da fatar nasara a jarabawa ya turawa Janan da mtn line ɗin sa da bazai nuna inda yake ba tunda shi every where you go ne, yana gama turawa Mu'azzam ya iso wajen riƙe da bowl guda biyu da ferfesun kayan cikin da Shahida ta gama haɗa masu ya miƙa masa ɗaya sannan ya nemi kujerar dake kusa dashi ya zauna shima, suna ci suna ɗan taɓa hira inda nan ya tabbatarwa da mm shida da gaske yakeyi yana son Razina, ba tare da mm ya ɓoye masa komai ba ya sanar dashi alaƙar dake tsakaninta da Jabir wacce har ankai ga maganar aure, ya ƙara masa da cewa yanzu haka ma dalilin shigowarsa tare dasu lefenta da nasa zasu haɗawa, ya kuma bashi haƙuri sosai don ko ba don haka ba baya tunanin zai iya amincewa ya auri Razina duk da ya cancanci fiye da haka a wurinsa saboda karamci da mutuncin sa, ba don komai ba sai bazai jurewa yayi nesa da ita ba har hakan, haka kuma yana jin nauyin Shahida don ta ɗauke sa da mutunci kuma tana girmamawa da mutunta sa, saboda haka ba ƙanwarsa ba ko wata ya ji abokin nasa zai auro mata to sai inda ƙarfin sa ya ƙare wajen hanasa aikata hakan balle ace shi da kansa zai ɗauki ƙanwarsa ya aurar da ita ga mijin ta, Duk da Mu'azzam yaji ba daɗi ya fahimci abokin nasa sosai tare da yimata fatan alkhairi, ya kuma yi alƙawarin binne wannan zancen acikin zuciyar sa har abada, bayan kwana biyu mm ya bawa Momy kuɗaɗe masu matuƙar yawa tare da MasterCard ɗin sa da zasuyi sayayyar kayan lefen kafin ya dawo don yau zai wuce Dubai, ya kuma roƙi Mu'azzam da yaba Shahida dama ta rakasu a siyo duk abunda ya kamata kafin ya dawo nan da kwanaki uku, don washe garin ranar daya dawo zasu koma Nigeria, sai da suka fara zuwa tare suka siyo akwatunan da za'a saka kayan ya zaɓawa Janan best colours ɗin daya san tana so sannan ya wuce, da daddare Mu'azzam ya sake sa suka shirya suka fita tare ya kaisu campaning wani abokinsa na cosmetic suka fara siyo kayan shafe shafe da turarukka da sauran abubuwan da suka shafi ɓangaren, wanda Momy bata san yanda akayi ba saidai taga sun dawo gida ba tare da ta biya kudin ba, suna isa gida kuma motar campaning na isa da kayayyakin da suka siyo, data yi masa zancen kuɗin sai ya ce ta barsu ya riga daya biya komai tayi ta saka masa albarka, haka ya riƙa fita dasu kullum tare da Shahida ana sissiyo abubuwan har aka gama, wanda kusan kaso talatin bisa ɗari cikin kuɗin kayan duk shine ya biya, ko da mm ya dawo ya yi matuƙar mamakin ganin yawan kayayyakin da aka siya, don a tsammanin sa daƙyar idan kuɗin daya bayar zasu isa shiyasa ya haɗawa Momy da MasterCard ɗin sa, sai gashi yaga ko kuɗin daya bata a hannu basu ida ƙare wa ba balle ayi tunanin ciro wasu cikin account ɗin sa, wani irin nauyi ne ya kamasa lokacin da Momy ta faɗa masa cewa gaba ɗaya cosmetic ɗin da aka siyo da turarukka Mu'azzam ya biya kuɗin haka ma akwai wasu abubuwa da dama aciki da shine ya biya kuɗaɗen su, shiru yayi yana mamakin karamci irin nasa wanda ba tun yau ya saba yima shi ba, ƙoƙarin samunsa yayi masa godiya yayi amma aduk lokacin daya buɗe baki zai yi magana sai hanasa, bai samu damar yin hakan ba sai washe gari da suka rakkosu zuwa airport zasu wuce, ya miƙa masa hannu sukayi musabaha haɗe da riƙe hannun nasa sosai ya ce, "Thank you so much friend, indeed..." Mu'azzam yayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa, "Enough Muhriz, what a friends mean, kai dai sai mun iso buki in sha ALLAH" "Ba damuwa, kai ne mutum na farko kuwa da zan fara sanarwa" "Da dai yafi maka, don wannan karon duk ka gwadamin wariyar launin fata tofa zamu gartaya dakai" "Hakan bazai faru ba in sha ALLAH" "To yayi, ka gaida Madam Janan, kafaɗa mata cewa i solute her da tayi ƙoƙarin fitar mana dakai a jerin tazurai, don ni har nazata bakada lafiya sai mun garzaya dakai asibiti" ya ƙare maganar cike da shaƙiyanci yana dariya, dariyar shima mm yayi tare da bashi hannu suka tafe ya ce, "Ka shirya kuwa a cikin wata tara cif zan tabbatar maka da cewa ni ɗin lafiyayyen ne, kai badon jinjiri ɗan wata bakwai ba lafiyayyen bane to da nace acikin wata bakwai zan baku babynku a hannun ku don na tabbatar maku da cewa lafiya ta garau" ya faɗa yana wani jinjina jikinsa suka sake tafewa suna dariya, Shahida kuwa har da ƙwallanta don ba ƙaramar shaƙuwa sukayi da Razina ba, acikin ƴan kwanaki biyar ɗin nan da sukayi ta koya mata abubuwa da yawa da suka shafi makeup irin wacce akayi anan Nigeria da kalolin ɗaurin ɗan kwali da dai sauran su, haka itama Razina ta koyi kalolin yanda ake sarrafa abinci irin na kasar shina da kalolin abincin da muke dasu anan gida kuma suyi daɗi sosai, infact dukkanin su sun shaƙu da juna ga Ƙaisa itama sai faman kuka takeyi ganin Razina zata tafi, har ta ɗan yi nisa sai kuma ta juyo da gudu tana share hawaye ta karɓi ƙasa dake hannun Shahida tana faman zillo ta ɗauke ta, kiss tayi mata a kiss haɗe da cewa, "Zanyi kewarki my little, stop carrying kinji ko" ta sa hannu tana goge mata hawaye, daidai lokacin Mu'azzam ya ƙaraso wajen ya miƙa mata hannu ya karɓi Ƙaisa tare da cewa, "To amarya maza jeki ki tafi ke suke jira, ashe ba ni kaɗai zanyi kewar ƙanwar nan tawa ba har da family nawa, how i wish Zaki ci gaba da kasancewa a tare damu har abada" sinne kai tayi ƙasa tare da shafa kan Haisam daya rungume ƙafafuwanta, ba tare da ta ce komai ba ta juya tana goge hawaye tabar wajen, cikin ɗan ɗaga murya Mu'azzam ya ce, "Ki gaidai angonki Jabir da yayi mani rigage, kice nace shudin mai sa a ne kuma ina taya shi murna" ya ƙare zancen tare da rungumo Shahida a jikinsa ya sakar mata kiss a forhead, Mm dake can tsaye a bakin jirgi ya zuba hannayensa a cikin aljihu yana hangosu yayi murmushi tare da neman tsari akan duk abunda zaisa ya zamo silar rushewar farin cikin abokin nasa da kuma matarsa, Razina na shiga shima mm ya shiga

Chapter 28 of 40