Share this page
nuna mm da yatsa fuskar nan ɗaure babu annuri ko ɗigo acikin ta. #Comment #Vote #Share *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 21_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattapad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1237958831?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=CG4hW%2FtlXTjqt970Cz9WflupMrwfyDYLR64I0PaW9XkUj6vCwBuOBK8AReDYztGDr8QO3tT4bukGqZEn50877vCoXsQOFacn0fRzFZ69hCrJfW2gFnozVrD2sje4lYls_ *KIN SAYI SHIRINMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SAYA BA MAZA KI HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN DOMIN SAMUN ƘARIN BAYANI +447894142004, 07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU MASU MATUƘAR ƘAYATARWA AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, ƳAR UWA GWADA KI GANI IDAN KINA CIKIN WUƊAN DA SUKAYI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADAMA BA😍* ______________________________ Cike da girmamawa da kuma mutuntawa mm ya sinne kai yana ƙoƙarin gaishe sa, ɓuɗar bakin sa keda wuya ya daka masa wata uwar tsawa tare da dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu, "Look bana buƙatar gaisuwar ka, baka ji mena faɗa bane?" "Yi haƙuri Abba, ni masoyin 'yar ka Janan ne.." tun kafin ya ƙarasa Abba ya yayi saurin runtse idanuwa alamun kalmar cin zafin kalmar, haka ya ci gaba da sauraren mm zuciyarsa na tafarfasa akan Janan data kawo masa mutum maƙasƙanci irin wannan da har yake iya tsayawa gabansa don tsarin idanuwa yana faɗa masa cewa shi masoyin 'yar sa ne, "Sunana Muhammad Muhriz, ni ɗane awajen mahaifina dake da ƙaramin ƙarfi a ƙauyen caranci, amma yanzu ALLAH yayi masa rasuwa, nazo gidan nan ne bisa dalilin soyayyar da nake yiwa 'yar ka Janan.." cike da ɓacin rai Abba yayi saurin ɗaga masa hannu yana faɗin, "Kai wane irin bagida je ne haka, tambaya ɗaya zuwa uku nayi maka amma don rashin hankali ka zauna kana bani labarin rasuwar mahaifin ka, wannan ba shine damuwata ba, yana da rai ko ba ya da rai buƙata ta kawai inji in kana da arziƙin iya zamowa surukin cikin gidan nan, saboda haka tunda baka da shi kada ka kuskura na sake ganin ka da 'yatah, haka ma gidan nan kar in ƙara ganin ƙafar ka aciki, wannan gargaɗi ne, idan kuma ka ƙi zan sa a fahimtar da kai ta ƙarfi da yaji, don haka maza ka ficemun daga gida yanzun nan" ya ƙare maganar yana nuna masa hanyar fita, "A'a Abba kada kayi haka don ALLAH, wlh ina son sa ko sau ɗaya ne ka tsaya ka saurare shi.." "Will you keep quite my dear ko sai nazo na tattaka ki a wajen?" Abba ya faɗa da ƙarfi haɗe da yowa kanta, wata irin zabura tayi haɗe da fashewa da kuka tana bubbuga ƙafa, "pls dad wlh shine rayuwata, ina son sa bazan taɓa iya rabuwa da shi ba" "Haka ne Abba, don ALLAH kayi haƙuri ka amince da soyayyar mu, son gaskiya nake yimata kuma zan tashi tsaye wajen nema iya ƙarfina don na kula maka da ita" mm ya ƙare zancen haɗe da duƙawa a gaban sa, wani irin mugun kallo ya bishi dashi yana ganin gaba ɗaya ma mm ya rena masa da wayo, banda laifin da yayi na shigowa rayuwar 'yar sa da matsayinsu bai zo ɗaya ba, ya ƙara da laifin saka 'yar sa na ƙoƙarin ja in ja dashi abunda ko a mafarki bata taɓa gwada yi masa ba, juyawa yayi ga guard ɗin sa da ke tsaitsaye fuskar nan ba imani ya yiwa babban su signal da idanuwa, kan kace me ya dira gaban mm tare da finciko wuyan rigar sa, Janan na gani haka tayo wajen mahaifinta, "A'a Abba don ALLAH kada kasa ayi masa komai, kace su ƙyalesa don ALLAH Abba" ta ƙare zancen tare da zubewa gaban sa tana kuka ganin sun fara kai masa duka, "Leave this place Janan before I slap you" "Pls Abba.." "I said leave" ya faɗa da ƙarfi, ganin irin dukan da suke yiwa mm da shi gaba ɗaya ma hankalin sa baya kansu ya shagala da kallon Janan dake kuka tana roƙon mahaifin nata yasa cikin rashin tsoro ta miƙe haɗe da yowa kan guard ɗin dake dukan sa tana tutturesu haɗe da cewa, "Ku dena dukan sa nace" in ta ture wannan ta ture wancan haka tayi ta biyar su tana turesu haɗe da yi masa garkuwa ta tsaya agabansa tare da haɗe hannayen ta waje ɗaya tana riƙon su, "Ku ƙyalesa haka na roƙeku don ALLAH, ku ƙyalesa zai tafi" Tsananin takaici yasa Abba yi masu tafi dake nuni da su ƙyalesa haka tare da wucewa cikin gida, kai tsaye sashen sa ya wuce ya dinga aafa da marwa a cikin falon nasa yana tunanin wane mataki ya kamata ya ɗaukarwa Janan kafin ta jawo masa abun kunya akan waccan talakan da bai ma san cikakken asalin sa ba, Wata shawara ce ta faɗo masa a rai da sauri ya ciro wayarsa ya kira wani aminin sa ambassador Hussaini Salam dake zaune a ƙasar chardi, sun jima suna waya da shi kafin daga ƙarshe suyi sallama da shi yana faɗin, "Ok ba damuwa sai ya iso" Wannan wayar ita ta ɗan kwantar masa da hankali saboda yasan kaso tamanin cikin ɗari na damuwar sa ya gama magance ta, Ita kuwa Janan mayafinta ta cire ta shige gogewa mm jini a gefen baki da suka fasa masa tana kuka, "Kayi haƙuri hubbin ruh, wannan kaɗan kenan daga cikin abinda mahaifina ke iya yi maka akan soyayyar mu, shiyasa kaga na shiga damuwa ɗazu, kar ka sake zuwa nan mm ka bari kawai muci gaba da haɗuwar mu makaran ta don ALLAH" Riƙe mayafin yayi yana kallon cikin idanuwan ta haɗe da sakar mata dariya har yana riƙe ciki ganin yanda duk tabi ta ruɗe, kafin yace, "Meye haka Janan!?, Kar dai ace har kin karaya akan wannan ɗan dukan da aka yi mani?" Mayafin ya sa ya share mata hawayen dake kwance a fuskarta tana ƙare masa kallon cike da mamaki tamkar ba shi ne aka daka ba ya ci gaba da cewa, "share hawayen ki ranki shi daɗe tawan!, Ai in dai akan wannan ɗan dukan da aka yi mani ne bazan dena zuwa ganin ki ba aduk lokacin dana buƙaci hakan matuƙar za a barni na gane kin, ban da abunki ma ai nan ya kamata naci gaba da zuwa muna ganin juna bawai a makaranta ba matuƙar na amshi sunan cikakken masoyi, buri na kawai kada ki bari faruwar hakan ya raunata soyayyar mu, kuma kada ki bari ya ɓata maki rai ko kaɗan don shi zai sa ƙwarin guiwar da nake dashi akan ki ya ragu kin ji ko Janany tawan" ya ƙare zancen yana kashe mata ido ɗaya, ɗan turo leɓen ta na ƙasa tayi tana son sake fashewa da kuka ya girgiza mata kai, "Kar kiyi hakan bana so, fitar wuɗan nan tsadaddin hawayen naki yafi azabtar da zuciyata fiye da dukan da aka yimun, saboda haka ki dena kin ji ko?" Murmushin dole ta ƙaƙaro haɗe da cewa, "Kai maƙura ne mm, ina matuƙar ƙaunar ka" "Kema haka ranki shi daɗe, bari naje kafin ƙattin can su wai wayo ni, don kuwa ba kaɗan suka iya mazga da sambaɗa ba" ya ƙare zancen yana zazzaro idanuwa haɗe da kallon gefe da gefe kamar mai tsoron dawowar tasu da gaske, dariya Janan ta kwashe da ita ganin yanda yayi tana faɗin, "Ashe dai zaka ji tsoron su shine ka ƙi guduwa ɗazu" "Ai indai kina akusa dani, ba wani tsoron su da zan ji don ko sanin suna wajen bazan yi ba, amma kinga idan kika tafi na bawa ƙafafuwan nan nawa iska ai sai dai su kamoni a bakin titi, shima ɗin idan na tsaya sun riskeni a wajen" sosai ta riƙa yin dariya har dimple ɗin ta na loɓawa, ganin ta ɗan saki akan ɗazu da ta shiga damuwa ya sa mm cewa, "To Madam bari ni naje gida na samu na gasa jiki na, wannan soyayyar taki mai tsananin tsada ce na ciyo Janany" dariyar ta koma yi haɗe da cewa, "Sannu, zan biya duka wannan da kyakkyawan TUKUICIN SO agare ka" "Kin tabbata hakan?" "Sosai ma kuwa, ka ƙara haƙuri pls kuma don ALLAH ka yafewa mahaifina" "Ki manta da wannan, ai nima mahaifina ne ko kuwa?" Wata irin kima da ƙaunarsa ta ji sun ƙara shiga ranta kafin ta kashe idanuwa tana kallon sa haɗe da shagwaɓe murya, tace "Ok to shikenan nagode, bye bye, ALLAH ya kai ka lafiya mintin zuciyata, hasken idaniyata, muradin raina" "Iyyeeeee, duka wuɗan nan suna yen wani kaɗai? Ko dai na sake dawowa gobe na ƙara shan duka ko zan samu wasu irin su?" "Laaa...ba sai kayi hakan ba ai, in dai irin sune, to kasa a zuciyarka yanzu ka fara saurarar su daga bakin Jananyn ka" "ALLAH kuwa?, To godiya nake yi nima nurul albi na, ko zaki raka ni ki taya ni gasa jiki na?" Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, da sauri tasa hannayen ta ta rufe fuskar ta cike da jin kunya ta bar wajen aguje, shi kuwa dariya yayi sannan ya juya ya fice daga gidan yana jin shi yanzu ma ya fara son Janan a zuciyar sa, Forward ever, backward never.... Daidai lokacin Nihal ita kuma ta fito ganin yanda mahaifin nasu ya shigo rai a ɓace, tana yimasa sannu amma ko jinta baiyi ba wanda hakan ya sa tabi bayan sa zuwa sashen nasa, maganar da taji yana yi da ambassador Hussaini Salam ita tasa ta fitowa don ganin halin da saurayin na Nihal da Abba ya cewa aminin nasa yasa anyi masa duka yake ciki, don kuwa ji tayi ya bata matuƙar tausayi, kusan karo suka yi da ita kasan cewar ta zo aguje, da sauri Nihal ta riƙe mata ka faɗu tana regen mm dake ƙoƙarin fita da bayan sa kawai take iya hangowa. #Comment #Vote #Share *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 22_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1238247824?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=1QlowtszfqDjsDRL%2F7CCnYoU8qm3gITXJnQCNFsWYntOICNW03KGPC8Q51hEr61iLGznpVX7RXdyiv8K8YB6tfNpCI7f1LKuNDApDA4pCi4TsXNPK10Bxy%2BoLjKDp7go_ *KIN SAYI SHIRINMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SAYA BA MAZA KI HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN DOMIN SAMUN ƘARIN BAYANI +447894142004, 07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU MASU MATUƘAR ƘAYATARWA AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, ƳAR UWA GWADA KI GANI IDAN KINA CIKIN WUƊAN DA SUKAYI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADAMA BA😍* ______________________________ "Janany sister in jin dai basu jimasa ba?" "Sun yi hakan Adda" "Shine kuma naga farin ciki a fuskar ki kina dariya?" "Ya zanyi Adda tunda soyayyar da muke yiwa juna ta kasa bari mu fahimci hakan, gaba ɗaya girman soyayyar da yakeyi mun ya hana ya nuna mani damuwa ko ɓacin rai akan abunda akayi masa, damuwar sa kawai nazama cikin farinciki, kin kuwa ga ai dole nayi hakan washi don faranta zuciyar sa" "Tirƙashi, lallai son gaskiya yakeyi maki, amma ya kamata ace kin yiwa kanki adalci shima kinyi masa Janan, tunda kin san Abba bazai taɓa bari ki auresa ba kada ki bari a riƙa gana masa wahala haka, ki haƙura dashi mana ki samu daidai ke wanda zai zamo daidai da ra'ayin Abbanmu" "Point of correction Addah Nihal, ba mm kaɗai ke yimun son gaskiya ba, ni kaina ina yi masa son gaskiya fiye da yanda kike tsammanin nasa, zancen kuma haƙura na barsa magana ce da bata da wani tasiri a ƙwaƙwalwa ta balle kuma ta samu muhalli a zuciya, mm rayuwata ne, saboda haka no going back akan sa" ta ƙarar maganar tare da ɗora hannunta akan kafaɗar ta tana rolling idanuwanta, ganin yanda ta saki baki tana kallonta cike da mamaki yasa tayi murmushi haɗe da wucewa ba tare da ta sake cewa komai ba, Ta fi Nihal ta yi tare da jinginawa a jikin bangon ƙofar shiga part ɗin sannan ta ɗora hannayenta data naɗe akan ƙirji tana faɗin, "Wow fantastic! yau she kika koma haka Janan?, Kenan kina nufin zaki bijirewa maganar mahaifin ki ne kibi zaɓin ranki?" Cak Janan ta tsaya daga bakin ƙofar da take ƙoƙarin shiga tare da juyowa ta kalli Nihal, girgiza kai tayi tana murmushi haɗe da sinne kanta ƙasa, tafi sakonni biyar a haka kafin ta juyo gaba ɗaya hannayen ta na akan ƙirji tana kallon yayar tata, "Adda Janan wai ni kike kira zan bijirewa mahaifina nabi zaɓin raina?, To ai inaga wannan ba ɗabi'a ta bace, don haka idan ma nayi hakan sai ayimun uzuri, kefi kowa sanin so ba ƙarya bane?, Ko don na kasa bayyana nawa yasa ake kallonsa tamkar wasar yara har ake ƙoƙarin nisan ta ni dashi? Yayin da ke kuma kullum ake kokuwar ganin an inganta naki son ta hanyar matso maki da abunda kike so a kusa dake ba dare ba rana, koma dai meye Adda ni ina son mm ko Abba baya son sa, haka kuma zan iya rayuwa dashi koda kowa zai rabu dani" "Haka kike gani kuma zaki iya?" "Sosai kuwa, wai ma meye matsalar soyayya ta Adda?, A zatona kece ta farko da zaki fara bani goyon baya tare da sharemun duk hawayen da zasu kwaranya a idanuwa na saboda kin san meye so, kin san zafin sa da kuma raɗaɗin sa, amma wai sai gashi ke da kanki ke neman yi mani kashedi da abunda kika san ke bazaki iya haƙura kiyi sa ba, anan ma kin bani mamaki" "A'a Janany sister, baki fahimceki bane, ko ɗaya bana jayayya akan soyayyar ki, halin da zaki shiga aciki ne nake tausayin ki a kansa, i don't want you to be suffer any more, rayuwar ki zata shiga garari ne aduk lokacin da kika faɗa hannun wanda bazai iya kulawa dake ba kamar yanda ni Abba muka kula dake, i know zaki ce ai bashi ya laƙawa kansa takaicin ba, but remember kowane tsuntsu kukan gidansu ya kamata yayi, sannan ko hausawa sukan ce kamata yayi ace ƙwarya tabi ƙwarya ba wai akushi ba" "Adda kenan, wannan zance ai ba karatu bane balle ƙwaƙwalwa ta iya fahimtar sa, sannan bai zo a rubuce ba, bai kuma zo a aya ko hadisi ba, taya kike tunanin zan riƙesa a matsayin makami da zai bani kariya ko kuma tudun dafawa a rayuwata?, shi so babu ruwan sa da wannan ƙwarya ce wannan kuma akushi ne, ba akushi bama Adda, hatta kwando shi so zai iya haɗawa da ƙwarya babu abunda ya damesa, saboda haka in dai wannan tunanin shine ya hanaki supporting soyayyata to ki ajiyesa gefe, domin tuni zuciya da gangar jiki sun riga sun shirya tsaf da amsar ko wane irin kalar sauyi da zai zo a cikin rayuwata" tana gama faɗar hakan ta juya ta shige abinta, don ita kam shirye take da fighting da kowa akan soyayyar ta tunda har ya iya jure komai akan ta, Ajiyar zuciya Nihal ta sauke tana taliyo duka maganganun ƙanwar tata a ƙwaƙwalwarta, ƙwaya ɗaya bata iya fahimta ba aciki in banda kalmar so, ita kaɗai ce zata iya fahimtar ma'anar ta da kyau amma sauran duka ba sa damuhalli cikin rayuwar ta balle ma tasan inda suka nufa ba, a cewarta bata ga dalilin da zai sa ta jefa kanta cikin ƙuncin rayuwa ba bacin ta taso cikin arziƙi da wadata a gidan su, mere baki tayi haɗe da cewa, "Zan baki goyon baya Janan kibi zaɓinki amma bazan taɓa ɗaukar akwai wata alaƙa tsakani na dashi ba, rayuwar ki ce kuma ke kika zaɓarwa kan ki hakan, iya nawa shine idanuwa, da yardar ALLAH ina zaune zaki dawo kibi abinda shine zai zamo daidai da rayuwarki" ta ƙarashe zancen haɗe da sake kallon ƙofar gare ɗin gidan sannan ta fita, ***. ***. ***. A ɓangaren mm kuwa koda ya koma gida ya tadda Jabir kwance yana latsar waya, gama wayarsa kenan da Razina dake makaranta ya matsa mata ta turo masa hotunan ta yayi missing ɗin ta kafin ta dawo ta turo masa ƙwaya uku yana kallo, ɗaya ta turo baki alamar kiss, ɗaya kuma ta kashe masa ido tana murmushi, ɗaya kuma da alama bayarwa tayi aka yimata, shape ɗin heart ne ta haɗa da hannunta a saiti zuciyar ta tana dariya, shima ɗin kallo yakeyi yana dariya sai ga mm ya shigo masa a wani hargitse, kallo ɗaya yayi masa ya maida kansa ga hotunan yana sake jawosu ɗaya bayan ɗaya yana kallo, kamar wanda ya tuna wani abu da sauri ya sake ɗago kai yana kallon mm ganin kamar gefen bakin sa a fashe, "Hey broth, what happened to you?" Ya faɗa haɗe da miƙewa zaune daga kwancen da yake yana kallon sa, "Luv!" Ya amsa masa dashi kawai tare da nufar hanyar toilet, "Wait, wait kar dai kacemun daga gidan su Janan ne aka yi maka hakan?" "And so what?" Ya sake bashi amsar ataƙaice haɗe da shigewar sa, dariya Jabir ya kwashe da ita har mm na jiyo sa, shima yayi murmushi don dama yasan za a rina indai Jabir ne, "Kutumar...wai yanzu kai akan so ka bari aka yimaka haka da arziƙin ka? And you are telling me so what?, Hmm gaskiya ka faɗo warwas broth don nikam bazan iya ɗauka ba ko ɗaya, wannan ai rashin sanin darajar ɗan adam ne, shikenan idan kai talakan ne da gaske ka zama abun wulaƙan tawa don kace kana son 'yar sa?, Shiyasa na ce karka tafi kai kaɗai ka bari na rakaka ka ƙi, gashi nan ka hawa kanka abunda da ina kusa babu wanda ya isa yayi maka hakan" Daidai lokacin mm ya fito ɗaure da towel Jabir ya kalli yanda fatar jikinsa fara ƙal tayi wani ja saboda duka, ga kuma bakin sa a fashe, ai kuwa ya sake kecewa da wata dariyar duk da a ƙasar zuciyarsa abun yayi masa ciwo, "Sannu majanunin Janan, wai duk dukan ne hakan?" "Kaji dashi dai" mm ya faɗa tare da hayewa kan gadon yana ƙara gudun ƙarfin a.c da remote ɗin ta daya ɗauka a gefen bedside, ɗan matsowa kusa dashi Jabir yayi tare dasa yatsa ya danna gefen daya fashe a bakinsa, 'yar ƙara ya saki haɗe da cewa, "Awshhh.." yana kai masa duka a shoulder, cikin shaƙiyanci Jabir ya ce, "Au! Da zafi ko, sannu mr. Luv, bani labari nasha, kace yau kaga father kunyi Ido biyu?" "Sosai ma" "Se me ya faru?" "Emmm, kuma ya ce wai na dena kula 'yarsa sannan kada na sake dawo masa gida ko yasa a koya mani hankali" "An then?" "Sai yasa yaran nasa suka yimun duka a matsayin gargaɗi, shikenan?" Ya ƙare bayanin haɗe da ture laptop ɗin daya ɗauki zai fara amfani da ita yana nuna Jabir da hannuwansa alamun ka cika tambaya. "Easy broth, to yanzu to yanzu ka amshi gargaɗinsa ko kuwa?" Juyowa gaba ɗaya mm ya yi yana fuskantar Jabir haɗe da cewa, "Ko ɗaya gargaɗin bai shiga kunnuwa na ba, a sali ma sakawa ya yi na sake jin ƙaunar 'yar ta sa a raina" "To ka bayyana masa kanka mana" "Ba yanzu ba, kai bama zan bari yasan da hakan ba har sai bayan na auri 'yar ta sa" "What? Saboda me?" "Saboda na koya masa darasin rayuwa tare da sauya tunanin sa" "Baza ka iya ba domin shi ne zai fa baka auren ta, sannan in dai kana a haka bazaya taɓa baka ita ba ko da me kake taƙama a duniya inba arziƙi ba" "Bazan aureta tahanyar bayyana arziƙina ga mahaifin ta ba, zan aureta ne don taƙama da soyayyar da take yimani kaɗai" "Tirƙashi, kace mu nemi kwalin robb kuwa, don father sa zaiyi a sauya maka kamanni" "What ever, indai bai sa zuciyar masoyiyata sauyawa ba ai ta kwana gidan sauƙi" "Eh....lallai kace namu wasa ne" "Zauna nan, anfaɗa maki mu zallar soyayya mukeyi ne?, Luv with sacrifice mukewa junan mu yaro" "Naji, ai tunda ni mijin yarinya ne ba komai ka kirani hakan na gode" Haka dai suka ci gaba da zantawa akan matsalolinsu kafin ya sake ɗauki system ɗin su fara tsara yanda za suci gaba da expanding business ɗin nasu tunda ya koma bakin aiki, Kira ne ya shigo a wayarsa dake ajiye a ƙarƙashin pillow ya miƙa hannunsa ta baya ya ɗauki tare da ɗaga kiran ya kara a kunnuwa ba tare daya ga ko waye ke kiran nasa ba, Cikin kashe murya yaji anyi gyaran murya haɗe da cewa, "Aminci ya tabbata agareka hasken rayuwata, mallakin duka gangar jiki na da kuma ruhina" jin ba Muryar Janan bace yasa ya ciro wayar a kunnen sa yana kallon screen ɗin wayar, ganin baƙuwar lambar da bai sani ba yasa yayi tsaki haɗe da yanke kiran ya jefar da wayar akan gado, sake kira akayi har kusan sau uku ya yi banza da wayar, sai a karo na huɗu ya sake ɗaukowa ya saka a kunne cikin sigar faɗa ya ce, "Ina ga wrong lamba ce, don ALLAH kada a sake kira" ya tsinke ba tare daya tsaya saurarar taba, Sake kira akayi a karo na uku ba tare da andamu da yanda yake amsawa ba, tsaki yayi tare da jawo wayar da miyar kasheta gaba ɗaya sai hannun sa yayi kuskuren ɗaga kiran ba tare daya lura ba, can ƙasa ƙasa ya ji ana faɗa cikin sautin jiki ɗaya kariyar masa da zuciya nan take, "Don girman ALLAH ka saurareni kada ka kashemun waya, ni masoyiyar kace dana daɗe ina dakon soyayyar ka har na tsawon wasu watanni da nake kallo tamkar shekaru, yanzu haka ina kan gadon asibiti ina jinya akan cutar son ka da tayi mani mugun kamu, mm nasan kai mutum ne mai sanin ya kamata da darajar ɗan adam, na roƙeka daka ji tausayin jaririyar zuciyata da babu komai a cikinta face zallar son ka da kuma ƙaunar ka, ka tallafi rayuwata ko da da girman rabin cokali ne ka sama mun muhalli a cikin zuciyar ka, wlh ina sonka irin son da ban taɓa yiwa koda kaina bane balle wani, kwanaki goma sha na ɗauka ban gane kaba, amma ji nake tamkar na ɗau shekaru goma ban saka ka a idanuwa ba, sha yasa ciwon kewar ka yayi mun dukan karan mahaukaciya" Duk da yaji tausayinta a farko hakan bai hana sa cewa, "Lallai ke mahaukaciya ce, ko waye ke na tabbata kinyi mani farin sani tunda har kika kirani da mm, taya za ayi ki bari so yayi maki irin wannan kamun har ya haɗa maki da jinya bayan ina da tabbacin kin riga da kin san mm mallakin wata zuciyar ne, shi kansa baya da iko ko wani hurumin sarrafa zuciyar tasa sai yanda ta so tayi da ita, a shawara ce zaifi kyau kiyiwa kanki karatun ta natsu don rabuwa da cutar da bazaki iya samun maganin ta ba har abada, daga ƙarshe ina godiya tare da fatan ALLAH ya baki lafiya" yana gama faɗar haka ya tsinke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya, don karma ta sake kira balle ta damesa, ɗan tsaki ya yi ganin yanda Jabir ya tsare sa da idanuwa haɗe da cewa, "Mi kana kallona".... #Comment #Vote #Share *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 23_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* *GA MASU BUƘATAR A TALLATA MASU HAJOJINSU, KO KUMA SABABBIN LITTAFANSU DA SUKE SON FIDDAWA ZASU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR KAI TSAYE TA HANYAR WATSAPP 07040402435* ______________________________ Murmushi Jabir yayi haɗe da cewa "yo ai dole na kalleka malam, wannan tsattsauran gargaɗi da kake yiwa 'yar mutane sai kace wadda ta ce zatayi wuf dakai ai yayi yawa, ina laifin wanda yace yana sonka?" "Ai kuwa ka yi a kunnen Janan, don tun yanzu dole tasan irin zaman da za tayi dakai" "Ka ga mr.luv!, Rufani ka saya ni a hannun Janan kar mutuncin da nake dashi a hannunta ya tuɗe" "Ya dai fimaka malam, anan fadar babu mai faɗa naji inba ita ba" "Eh, ai na tabbata hakan" Jabir ya faɗa tare da miƙewa yabar ɗakin, shi kuwa yaci gaba da latsar system ɗin zuciyarsa cike taf da tunanin Janan, A ta ɗaya ɓangaren kuwa jifa Amira dake kwance akan gadon asibiti tayi da wayar ta haɗe da fashewa da kuka tana faɗin, "Na tsaneki Janan, wlh na tsaneki irin tsanar da ban taɓa yiwa wani mahaluƙi ba aduniya, shin me kika fini dashi ne da mm zai so ki kuma ya amshi soyayyarki fiye da yawa?" Mahaifiyarta ce dake shigowa riƙe da buta lokacin tayi saurin ƙarasowa wajenta ganin tana kuka tare da riƙo hannunta tana faɗin, "Amira lafiya?, Me kuma ya faru dake?" "Umma baya sona, ya tsaneni" ta faɗa cikin kuka haɗe da ɗora kanta sama cinyar mahaifiyar tata data zauna kan gadon kusa

Chapter 13 of 40