zaiyi idanuwa biyu da Nihal, hakan na faruwa ne kuwa saboda mutuwar da mahaifiyarsu tayi lokacin da zata haifi Janan, sai Abban nasu ya d'auki hakan a sanadiyar haihuwar Janan badon haka ba da still yana tare da matarsa kuma mahaifiyarsu, sai wannan abun daya saka aransa ya haifar da rashin shaquwa da jituwa sosai tsakaninsa da ita ya kuma fifita soyayyar Nihal azuciyarsa musamman da take da sunan mahaifiyar tasu hajia Aisha, itace babba saboda ita suka fara haihuwa, tarin qaunars da yakewa mahaifiyar tasu tasa ya saka sunanta lokacin data haihuwa, inda sukayi alqawarin cewa idan ta sake haihuwar d'a namiji ita kuma sunansa take so yasaka mata, sai gashi ALLAH bai nufa ba ta haifi 'ya macce ta rasu, 'yarce aka sakawa sunan mahaifiyarsa wato hafsat sai suke kiranta da Janan,
Abu d'aya ne kesa Janan bata damuwa da fifikon da mahaifin nasu ke nunawa tsakaninta da yayarta Nihal, shine soyayyar da da take nuna mata, Nihal na matuqar sonta sosai, irin son da ita kanta bazata iya kwatantasa ba shiyasa kawai take kauda kai ga dukkanin tarin soyayyar da mahaifin nasu zai nuna mata fiye da ita,
"Ok, sai ki kula idan kunje, idan kuma kikaga zaki takura kawai ki dawo gida kinji ko?"
"Shikenan Abba, ALLAH ya kiyaye" Nihal d'in tafad'a tana murmushi ya amsa da
"Amin" shima fuskarsa d'auke da murmushin, sanyayyar ajiyar zuciya Janan ta sauke had'e da janye dukkan mugun tunanin dake zo mata ga mahaifinta itama tace
"Abba saika dawo"
"Saina dawo Janan, ku gaida Hajia"
"Zata ji" ta bashi amsa ataqaice sannan ya fad'a cikin motar ya rufe, bodyguard d'in suka zo da sauri duk suka shishshiga motocin da zaya fita tare dasu sannan driver yaja suka fice,
"Welcome back my sister" Nihal tafad'a tare da rungume Janan dake tsaye tana kallon motocin mahaifin nasu dake ficewa daga gidan, murmushi ta sakar mata tare da cewa,
"Thank you Addah Nihal, ya zaman gida?"
"Ba dad'i tunda kika tafi school, amma ya akayi yau kika dawo dawuri haka?" Ta d'ago kai daga rungumar data yimata tana kallon fuskarta,
Qoqarin tafiya Janan tafara agajiye, kafin ta bata amsa ta sake jefo mata wata tambayar,
"Janan sister, waya tab'aki ne?, naga damuwa kwance a fuskarki"
Dariya Janan tayi sabida tasan za'a rina, little change idan yayar tata ta gani a fuskarta saita gano akwai wani abun, don haka ta a dariya tace,
"Hohoho Adda Nihal, anya ba aljannu ne dake ba?, yanzu har kin gano something goes wrong dani?"
"Sosai kuwa, nifa second mom ce ko kin manta? Taya Zan kasa gano damuwar 'yata kuma one and only sister?" Taqare zancen had'e da zolayarta, dariya Janan tayi sosai lokacin suna tattaka matattakalar da zata sadasu da d'akunan kwanansu, tace
"Adda Nihal kenan!, badai son girma ba, ai second mom yayi maki yawa a yanda kiken nan, kedai kawai ki karb'i big aunty don shine daidai ke"
Cak ta tsaya had'e da murtuqe fuska, tace "So what do you mean now?"
"I mean you're my first and only aunty in the world, not second mom ooo..." taqare maganar tare da kauda kanta gefe tana qunshe dariyar dake qoqarin zo mata, zaro idanuwa Nihal tayi cikin wasa had'e da cewa,
"Ki kace me?"
"Yeah! Upcouse you..." Ai kuwa kafin taqarasa Nihal ta d'aga hannu kamar zata daketa, ta ruga da gudu tabar wajen tana dariya had'e da juyowa tana yimata gwalo, nan itama tabi bayanta aguje tana fad'in "tsaya man in kin cika", kusan tare suka kai tsakiyar d'akin Janan suka fad'a kan makeken gadon nata atare suna dariya,
"ALLAH zanyi maganinki ne Janan tunda kin renani" tafad'a tana juyo fuskarta suna kallon juna,
"Ok am sorry, na yarda, bara na samu na watso ruwa, Wlh i have been tired enouph"
"Ayya sorry darling, bari na taimaka maki na had'a maki ruwan wanka, idan kin gama saiki sameni aqasa muci abinci"
"Ok big aunt nagode" Janan tafad'a tana kallonta cike da soyayyarta itama azuciyarta.
Kafin Janan ta iya miqewa tacire kayan jikinta har Nihal ta gama had'a mata ruwan tafito,
"Yawwa Addah Nihal sannu, kinsan wani abu?"
"Sai kin fad'a sis" taqare maganar tana folding hannayenta had'e da jingina bayanta ajikin madubin dake cikin d'akin,
"I have alot of gist to tell you"
"Wow! About..?
"Adda sarkin son labari to bari nafito" tafad'a ta shige taoilet tana dariya.
Dariya itama tayi sannan ta sauka qasa tare da qwalawa ai aikinsu madam Florence tace ta had'a masu abinci ita da Janan yanzunnan ta amsa mata da to, cikin mintuna qalilan madam Florence d'in wacce itace ke kula dasu tun suna yara bayan rasuwar mahaifiyarsu har girma ta jera dining table d'in da kalolin abincin da sukafi so,
Cikin qananan kaya riga da wando triquater itama Janan ke saukowa daga matattakalar fuskarta d'auke da wani irin nishad'i da ita kanta batasan dalilinsa ba ta sako irin hular nan da ake yayi mai butterfly agaba red colour akanta ta saki gashin acan baya,
"Wow! Janan sister you look so beautiful, Wanda duk ya aureki yayi sa'ar samun kyakkyawar mata 'yar fara tubarkallah"
"Kinji Adda Nihal na kaiki?"
"Hmm zolaya ta zakiyi kenan!, Kedai kika sani" Nihal taqare zancen tana miqo mata plate d'in agabanta, ita tayi masu serving abunda suke so suna ci suna d'an tab'a fira har suka gama madam Florence tazo ta kwashe kayan ta gyara wajen su kuma suka koma mai falon dake nan qasa suka kunna tv suna kallo, at the same time kuma Janan na bawa Nihal labarin duk abunda yafaru da ita a makaranta tun daga kan accident d'in da sukayi da mm, har zuwa fad'anta da qawarta Amira da zuwanta clinic da mm da kuma yanda tayi da Ingaski, don babu abunda take b'oyewa yayar tata itama haka babu abunda take b'oyewa Janan, sun shaqu sosai irin shaquwar da misiltata zaiyi wahala, suna son junansu sosai ganin yanda suka taso cikin maraicin uwa kuma basa qaunar abunda zai had'asu balle har suyi fad'a.
Banbancin halayyane kawai suke dashi, duk da mutum d'aya ya basu tarbiya amma sam halayen Nihal basuyi kama dana Janan ba, Nihal nada matuqar izza awaje da kuma d'agawa da tsiwa saidai sam bata bari hakan ya shafi qanwarta ba saboda soyayyar da takeyi mata, tsaf Nihal ke iya kallon wanda duk yayi mata kan kara ta tata masa rashin mutunci komai tsufansa kuma komai qanqantarsa, shiyasa ma yanzu da Janan ke bata labarin abubuwan da suka faru take ji tamkar ta kameta tayita duka tsabar takaici,
"Adda Nihal naji kinyi shiru bakice komai ba tun d'azu inata zuba ni kad'ai"
"Zaifi kyau ki kama bakinki kiyi shiru don takaicin wannan Jabir d'in abokin nn yake ko waye shi da d'an iskan malaminku zai iya sa na taso nayita dukanki da baki tata masu rashin mutunci ba, wai Janan sister sai yaushe zakisan right d'inki kidena bari ana takaki"
"How Adda? Kusanfa duka inada laifi ga abubuwan da suka faru"
"Mtss...bara nadena sauraronki kar takaici ya illatani awurin, shi Jabir d'in ina ruwansa dake da zai fad'a maki magana tunda bashi kika kad'e ba, itama Amiran meya dameta aciki, shegiya inaga ma sonsa takeyi, sai kuma the big idiot d'in malamin nan nakun, uwar me zayayi maki idan kika samesa a office? Meyasa baki dalla masa mari ba da kikaga yana kallan maki jiki?"
Turo baki Janan tayi had'e da cewa
"Kin gani ko Adda Nihal, ALLAH shiyasa bana son baki labari kin fiye zafin rai da yawa"
"Oho, to kidena man" tab'ata amsa cike da fushi don bakin Rai taji haushin abun.
"Ai bazan iya ba Adda Inna daina wa kikeso nabawa? Srry if I hot you pls" taqare maganar tana had'e hannayenta waje d'aya alamar ban haquri, saida tad'an harareta tukuna tace,
"ALLAH better know who you're a rayuwar nan, if not kin riqa shan wahala kenan kowa yace zai takaki"
Da haka dai har tasamu ta sauko sukaci gaba da kallonsu tare da d'auko wata firar ta daban kafin su can zuwa marece su gyara su nufi gidan grandma.
***. ***. ***.
A b'angaren mm kuwa basu suka tashi daga wajen sana'arsu ba har saida aka kira sallar magrib lokacin masu lectures d'in 4:00-6:00 duk sunyi sun gama sun watse, kasancewar makarantar ta 'yan matace zallah wato federal collage of education and technology (fcet) yasa tayi tsit ba kowa sai kukan tsuntsaye dake tashi da kuma security, wata dalleliyar mota naga tayi parking a bakin d'ayan gate d'in da suke fita dake cikin staff-quaters d'in makarantar drivern dake ciki na jiran isowarsu, da sauri ya fito cikin motar lokacin daya hangosu tafe mm na turo baronsa na dabino da kwakwa shi da Jabir ya karb'i na hannun mm shi kuma wani dake gefen gate d'in tsaye da alamu tare suke ya karb'i na hannun Jabir, cike da girmamawa suka gaishesu mm ya kalli hannunsa da yayi ja tukuna ya d'aga masu hannu yana amsa gaisuwar da sukayi masu,
Jabir kuwa leda ya ciro ya zuba dabino mai yawa aciki sannan ya nufi wajen motar tasu, ganin yayi mm ya nufi wajen zaman dake gefen sit d'in driver yace,
"Ya haka kuma?"
"Kai zaka ja motar mana"
"Haba! wasa kakeyi, ai ni ina gefe kawai koma can kaja mu muje"
"Wa? Ai bazan iya ba Jabir kaga hannayensa kuwa?, Ja kawai muje muje man" yaqare zancen tare da bud'e marfin motar ya shige, babu yanda Jabir ya iya dole ya shiga gefen sit d'in driver ya jasu suka tafi, shiru ne ya biyo na tsawon kusan mintuna goma kafin can Jabir ya juyo yana kallon mm daya d'an ja kujerarsa tayi baya ya kwanta idanuwansa arufe,
"Yadai mutumen!"
"Janan!"
"Dama nasan za'a rina, ai indai soyayyace tafi wahalda irinku miskillai da ako yaushe kuke kallon masu yinta a matsayin marasa aiki, wace tsiyarce bakayimun ba lokacin da muna soyayya da Hanan (yarinyar data cucesa)"
"Waccan Hanan take, Ni kuwa tawa Janan take kaga kuwa dole saka rai yakoma akan Janan tunda Hanan ta tafka maka tsiya"
"Kar dai ka zurma da yawa broth shine kad'ai shawarata"
Murmushi mm yayi had'e da cewa,
"Ai anriga angama kuma, se za'a ake shawara basai andawo ba, indai akan Janan ce nariga dana zurma sedai kar aqara"
Dukan starring Jabir yayi yana dariya ba tare daya koma bi takan saba, shi kuwa yaci gaba da tunaninta da yakeyi har lokacin idanuwansa na arufe, tafiyar mintuna da basu wuce goma sha biyar ba sukayi kafin su iso gida, asalin gidan da suke ciki ne ada amma an sake gyarasa anfidda part d'in Momy da Razina da kuma part d'insu, sai d'akin salame dake riqawa Momy aiki acan baya da kuma na maigadi dake nan jikin gate, juyowa yayi daidai lokacin da suka iso gidan bayan yayiwa mai gadi horn ya bud'e masu sun shiga yayi parking had'e da d'an bubbuga gefen sit d'in mm yana cewa,
"Wakeup man mun iso gida"
A hankali mm ya juyo suka had'a ido don dama ba bacci yakeyi ba sannan yafito hade da nufar part d'insu, shi kuwa Jabir yana fitowa ya rufe marfin motar tare da sakin wata uwar miqa Yana fad'in,
"Wow! Am seriously tired"
"Me too" Muhriz daya fara tafiya ya fad'a shima tare da wucewarsa jiki ba qwari,
Shi kuwa Jabir part d'in Momy ya wuce shima cike da gajiya, yana shiga ya fad'a kan doguwar kujera 2sitter dake falon yana fad'in,
"Wash.." ya d'ora hannayensa asaman kujerar
Dariya Razina da fitowarta kenan daga kitchen riqe da gorar ruwan sanyi da cup data d'auko a ciki zata sha ta tayi tana fad'in.
"Sannu da dawowa Ya Jabir, ya kasuwa?" Taqare zancen tare da zaunawa kusa dashi ta tsiyayo masa ruwan sanyin a cup ta miqa masa tana cigaba da cewa
"Ya Jabir ina Yaya Muhriz ne?" Saida ya karb'a ya shanye tas ta qara masa wasu yasha sannan yace,
"Ina Momy ne?" Shima ya jefa mata tambayar ba tare daya bata amsar tambayar da tayi masa ba, turo baki tayi had'e da cewa,
"She's there in her room" dariya yayi had'e da cewa,
"'yar rigimar yayanta, yanzun nan zaki gansa ya shiga yawatso ruwa ne"
Cike dajin kunya ta rufe fuskarta don indai akan yayanta ne tofa batada kara balle kawaici,
Momy ce ta shigo saye da dogon hijabinta gama salarta kenan ta tsaya qarasa azkar taji shigowarsa, miqewa Jabir yayi da sauri tare da nufowa inda take ya riqota suka qaraso cikin falon tare yana fad'in,
"Sannu da gida Momy kin wuni lafiya?"
"Lafiya klw my son"
"How's your body mom"
"Ah! Alhamdulillah am fine"
"Glory be to God Momy, am hungry"
"But where is your brother first?"
Kafin tarufe baki saiga mm ya shigo har yayi wanka ya canza kaya, da sauri Razina tayi welcoming d'insa cike da farincikin ganinsa tana fad'in "welcome ya Muhriz" murmushi ya sakar mata yana zaunawa qasan qafafuwan Momy tare da gaisheta cikin girmamawa, Saida suka gama gaisawa sannan ya juya ya amsa gaisuwar Razina Yana tambayarta Yaya school da batafi wata d'aya da jonawa ba a b'angaren B.ed computer science,
Saida yagama tambayar tata sannan Momy tasa tazubo masu abincin had'e da juyowa tana kallonsu d'aya bayan d'aya ganin yanda suka sauya mata sosai, kimanin watanni biyu kenan duk suka fita basa dawowa gida sai irin wannan lokacin kuma zasu dawo agajiye, gaba d'aya sunyi baqi kamar ba yaranta ba, a tsammaninta duka yanayin business d'in nasu kesa haka amma saita fahimci akwai abunda suke b'oye mata, don haka saita qyalesu saida suka gama cin abincin tukuna tayi gyaran murya tana kallonsu fuskarta d'aure babu alamun wasa aciki tace,
"Muhriz, Jabir! Me kuke b'oyewa momynku haka dake nema ya sauya mun ku daga yarana dana sani izuwa wasu yaran daban?, pls may i know what's exactly going on?"
#like
#share
#vote
#comment
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 6_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Follow me on wattpad@Billysfari9 httpson a userhttps://www.wattpad.com/1231665142?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=EwW9KlBM7lslQDR9ocKvcHE2Kh6HObz4smPNFZjvFoyf%2BzVLltD0tBsHM2bvRyWMIhmS%2FlPhBh9EqHHKEAerqqhmLTO6zBBU0VHXVkUXcNWnJxk274crMybs6d0iQKcE_
______________________________
*S* hiru duk sukayi har sai da ta sake maimaita tambayar data yimasu a karo na biyu sannan Jabir ya ɗago kai yana kallonta, har zai yi magana tayi saurin ɗaga masa hannu ganin Muhriz na susar gefen kunnensa da ɗan yatsa, ɗabi'arsa kenan aduk lokacin da zai faɗi wata magana mai muhimmanci, hakan yasa ta dakatar da Jabir don tasan maganar da zai faɗa sai tafi tasa,
"Muhriz kada ka Ɓoyemun komai, faɗamun ko meye kaji ko?"
Sai daya ɗan muskuta tare da sakin sanyayyiyar ajiyar zuciya yana kallonta sannan ya ce,
"Ammm...Momy kiyi haƙuri mun yanke shawarar aikata wani abu ko ince na yanke shawarar aikata wani abu bada sanin kiba don nine nakawo wannan shawarar kuma na hana Jabir ya sanar dake saboda sanin bazaki taɓa yarda ba"
"Muhriz, har akwai abunda kake tunanin zaka faɗamun akan wani lamarin daya shafi kasuwanci ki ko rayuwarmu nakasa yarda? Nifa na reneka kuma nabaka tarbiya! Ai matuƙar na yarda da tarbiyar dana baku to bazan taɓa hana kuba sai idan har nasan zaku cutu aciki, je kai tsaye ka faɗamun ko meye ma, in sha ALLAH zan fahimceku, wannan yanayin ne dai da nake ganinku aciki bazan lamunci jurar ganinsa ba"
"Eh to! Dama ganin halin da ɗan uwana ya faɗa ciki wajen neman matar da zai aura ne yasa nayi tunanin yin basaja don samawa kanmu mafita, ma'ana na sauya kaina daga Muhriz pilot da aka sani yanzu zuwa Muhriz maraya ɗan asalin ƙauyen caranci ta hanyar ajiye business ɗin da mukeyi da aiki na wani ɗan lokaci muka koma sana'ar saida dabino da kwakwa a makarantar kwalejin ƴan mata ta wannan garin..."
Tun kafin yaƙarasa maganar Momy ta aza hannu a ƙirji haɗe da cewa,
"Oh my god, why? Why naa!"
Ta ƙare maganar kamar zatayi kuka, ta sowa yayi ya dawo kusa da ita haɗe da riƙo hannuwanta ya ce, "pls Momy calm down!, Ba wani abu bane, damu dake da kuɗin da wuɗanda ke irin sana'ar duka ɗaya ne, all we want from you shine addu'a"
"I know mu son, amma kaga yanda kuka koma ne?, Akwai hanyoyi da dama da zaku bi kusamu matayen aure, amma wannan sam bata dace daku ba, look at your hands yanda suka koma" ta ƙare zancen tare da juya hannunsa tana kallon cikin tafinsa da yayi jaa sosai har da kanta"
"Momy this one is nothing as much as za'a samu abunda ake so, just pray for us"
Juyawa tayi tana kallon Jabir daya maida hankalinsa gaba ɗaya ga waya yana latsa shima ta riƙo nasa hannun tana kallo, bai wani nuna alamar gajiya da wahala ba atattare dashi kasancewar shi irin blacks beauty d'in nan ne, jikinsa bai cika nuna wani chanjin yanayi ba kamar na Muhriz dake da hasken fata, shiyasa ko jan da hannun Muhriz yayi nashi bai nuna hakan ba, skin ɗin ce kawai tayi ɗan tauri kaɗan ba kamar yanda take ba.
"My son, kuna ganin wannan plan ɗin da kuka shirya it work kuwa?, Kodai ku canza wani pls" ta faɗa cikin marairaice fuska don ba kaɗan take jin yaran nata arai ba, dariya yayi haɗe da kashe wayar ya jefa a aljihu sannan ya ɗora hannunsa akan nata ya ce,
"It work kuwa don har anyi wuf da zuciyar yaronki, and i'm sure soon brother zai kawo ta ta gaisheki"
Juyawa tayi fuskarta cike da farin ciki tana kallon mm daya sinne kai ƙasa ta ce,
"Izit true my son?" Sai ya ji ya kasa d'ago kai balle har ya iya bata amsa shikuwa Jabir sai faman yimasa dariyar ƙeta yake, 'yar harara yayi masa ta wasan idanuwa ashe momy na lalle dashi tayi murmushi haɗe da sakin hannayen su ta ɗaga nata sama tana addu'a ALLAH ya tabbatar da alkhairi kuma ya kauda sheɗan yasa wacce zata kula mata da shine kuma taso ƴan uwansa ba wacce zata raba masu kai ba, ta jima tana kwararo addu'o'in kafin ta tofa a hannayen ta ta shafe duka akawuna su, Razina dake zaune gefe ta ƙyalƙyale da dariya tana fad'in,
"Kai Momy, wai su wuƴan nan samarin naki basa girma ne?, Ko ni da nake ƙarama akansu ba kyamun irin abubuwan da kike yimasu, dubi fa har wani shafa masu addu'a kikeyi aka sai kace Yaran da ake tsoron mayu su kama.."
Bata rufe baki ba Muhriz ya d'auki throw pillow ɗin dake gefen kujera ajiye ya jefeta dashi,
"Su waye yaran? Bakya da kunya ko Razina?" Momy dake dariya ta ce,
"Noooo...kabar mun yarinyata tayi magana, ai gaskiya take faɗa, ban san me yasa akoda yaushe nake yimaku kallon ƙananan yara ba bacin you are too big now, itane ya kamata tasamu lunkin irin wannan kulawar fiye da wacce nake bata ko auta na?"
Ɗaga kai tayi tare da matsowa ta ɗora kanta saman kafad'an Momy tana dariya itama ta saka hannunta akan fuskar tata haɗe da cewa,
"Dole kema zan baki fiye da wannan kulawar saboda kin kusa tafiya kibar ni"
"Noo...Ni babu inda zan je ina tare dake now and for ever" Razina ta faɗa cike da shagwaɓa bayan tasa duka hannayen ta ta rungume Momy tana kallonta, dama Razina ba banza ba indai wajen shagwaɓa ne, sosai take samun waje tako wane ɓangare a wajen su, abun gwanin burgewa idan kaga yanda take yiwa Momy itama tana biye mata, duk da hakan kuwa bai hanata tsawatar mata ba aduk inda tayi kuskure.
Murmushi mm yayi yana kallonsu zuciyarsa cike da farin ciki marar adadi, baya da wani buri aduniya sama da yaga wuɗannan mutane guda uku na cikin farin ciki, sai yaji wata kwanciyar hankali da natsuwa sun mamaye masa ruhi da kuma gangar jiki, haka ma a ɓangaren Jabir yakan tsinci kansa cikin jin daɗi aduk lokacin da zai gansu gaba ɗaya cikin farin ciki da walwala, shiyasa yanzu ma ya shagala da kallonsu, duk da Razina ƙaunarsa ce sai yaji ina ma ace shima yanada ƙanwa kamarta, ɗaya matuƙar jin daɗi fiye da wannan, amma ko a hakan yana yiwa ALLAH godiya daya bashi ita a matsayin ƙanwa duk da ba momynsa ce ta haifa masa ita ba, murmushi ya saki shima lokacin da Razina ta gama magana haɗe da cewa,
"Kin makaro yarinya, keda zamu aurar nan bada jimawa ba kije can ɗakinki ki ƙarasa da wannan shagwaɓar taki da bata bar kowa ba"
Ɗan sosa kai mm yayi yana kallon Razina data b'ata fuska ta ƙasan idanuwa kafin can yace,
"A'a Jabir, kasani ko akwai d'an gayen data ƙyasa ma agidan nan, kama bakinka kar kazo ka kirawa kanka ruwa" ya qare maganar yana kallon Razina don yaga irin reaction d'in da zatayi akai, don shi har ga ALLAH bayada wanda yake yimata sha'awar ta aura sma ga ɗan uwa, aboki kuma aminin nasa wato Jabir, tun tana ƙarama yake da wannan burin, koda lokacin da yake soyayya da Hanan bai taɓa jin ra'ayin ya gushe masa arai ba saima ƙara alwashin da zuciyarsa keyi akan koda a matsayin matar Jabir ta biyu Razina zata zo zai cika wannan buri nasa, hakan ne kaɗai zai gamsar da kansa cewa yayiwa Momy TUKUICIN SO da abu mafi daraja da zataji dad'i, don haka sai ya natsar da hankalinsa ga Razina yana karantar canjin da tayi a sanadiyar maganarsa, don kuwa saida ta kalli Jabir da tun ɗazu idanuwansa ke akansu sannan ta turo baki haɗe da kallon Momy ta ce,
"Momy kin gasu ko?"
"Qyalesu autana, bazamu rabu dake ba mutu ka raba takalmin kaza, mijin da zai aureki ma sai munyi takarda dashi kullum zai riƙa kawomun ke na ganki tukuna zan bashi aurenki"
"Tab..ashe kuwa akwai aiki Momy, don kuwa babu mai rabaki da ita tunda shi ba lusari bane ace kullum yana kan titi biye da mata zuwa gidansu, ko kuwa ma?" Jabir ya fad'a yana dariya haɗe da bawa mm dake dariya shima hannu suka tab'e tare da miƙewa jin anyi kiran sallahr isha'i suka nufi masallaci, Razina kuwa cuno baki tayi tana bubbuga ƙafafuwa har da d'an kukan shagwab'a, Momy dake dariyar itama ta ce,
"Oh! ALLAH, Razina ai kece yarinya, kuka kuma akan ƴar wannan magana, to yi haquri ƙyalesu ki tashi muje kiyi Sallah abunki, in sha ALLAH yanda kike so haka zai faru kinji ko" ta ƙare zancen tare da riƙo hannunta ta miƙar da ita suka wuce ɗaki, a zuciyarta tana mai addu'ar ALLAH yasa wannan plan da sukayi yazamo masu alkhairi kuma dasu da autanta ALLAH ya zaɓo masu abokanan zama nagari, da haka suka shige ɗaki tare har lokacin Razina na tuƙuburi bata dena ba.
Washe gari kamar yanda suka saba haka suka shiryo cikin shigar da suke yi idan zasu je sana'ar tasu ta saida dabino tunda yanzu babu sauran ɓoye-ɓoye Momy ta riga da tasan komai, sallama sukayi suka shiga cikin falon tana zaune tana linke kayan Razina da mai aikinsu tayi mata wanki ta kwaso mata, kallon yanayin shigarsu tayi kafin ta amsa sallamar cikin sakin fuska suka gaggaisa ta ce,
"Yanzu Muhriz kuna jin daɗin wannan shigar da kuke ciki?"
"To Momy ya za a yi? Dacewa kawai ake nema tunda abun naɗan taƙaitaccen lokaci ne"
"Shikenan, ALLAH ya taimaka kuma ya bada sa'a, don ALLAH ku kula da kanku"
"To Momy za muyi hakan, ina Razina?" Jabir ya faɗa yana bud'ar idanuwa kamar mai neman wani abu.
"Ta tafi school, ta ce yau tana da test bazata tsaya jiranku ba"
"Shine kuma sai tabar maki aiki? ALLAH Momy kidena shagwaɓa ta hakan, ki ajiye idan ta dawo ta ƙarasa abunta da kanta"
"Haba Muhriz, auta face!"
"Shikenan Momy, as you wish ai, jiya fa ina kallo kafin mu fita hadda ƙwallanta, kar fa ta sangarce ta koma komai tana yiwa mutane kuka"
"What ever!, ba ruwanku ai ku kuka sa ta, kuje ku karya ga breakfast ɗinku can kafin kuwuce"
"Thanks Momy" suka faɗa atare haɗe da miƙewa suka nufi wajen dining, saida suka ci suka qoshi sannan suka d'auki harmar zuwa makaranta bayan sunyi mata sallama itama tayi masu adawo lafiya har tana tsokanarsu da sabon sunan data saka masu wato MJ dabino's tana fad'in su bata dabino na ɗari biyu suna ta dariya.
***. ***. ***.
A ɓangaren Janan kuwa basu dawo wajen grandma ɗinsu ba sai kusan ƙarfe goma na dare, yauma baran-baran suka rabu ita da Nihal saboda abunda ta yiwa mai aikin ta ta buge plate ɗin abinci da ita da kanta tace ta dafo mata akan ta kawo mata shi a buɗe, gaba ɗaya abincin ya tuɗe ya qonawa mai aikin grandma ɗin qafa sosai har seda fatar wajen ta taso ta kuma bita da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 40