kike dani ko?" Girgiza kai tayi haɗe da kallon Abba sannan ta sun kuyar da kan ƙasa,
"Au! Ko har wayar duka ka anshe ne?, Ubangiji ALLAH ya shirye ka Usman ya nuna maka hanyar gaskiya, ina wayar tata ne?" Ganin bai ce komai ba yasa ta ce,
"Jeki ɗakin ki ɗauko ai nasan tana ciki" sumui-sumui Janan ta miƙe ta shige ɗakin Abba, badon bazata iya yiwa Hajiya musu ba da bazata karɓi wayar ba tunda shi ya ƙarɓi abussa, shiyasa ko zancen mota bata sanar da ita ba don kar tasa dole ya mayar mata da ita, tana shiga taci karo dasu falo saman centre table ta ɗauko, ɗakin ta Hajiya ta ce ta wuce haɗe da cewa ta cire komai aranta ta natsu taƙarasa karatun ta na jarabawar da zata yi gobe ta ƙarshe ta amsa da to haɗe da hayewa sama, da kallo Abba ya bita dashi cike da takaici Hajiya dake kalle dashi ta ce,
"Ko kana da magana?"
"A'a Hajiya, ALLAH ya baki haƙuri" bata tsaya amsa shi ba tayi gaba sai ga Nihal ta saukowa daga saman benen itama, wani kallo tayi wa Janan ba tare data ƙyelata ba ta wuce abinta yayin da Hajiya ta kalleta tun daga sama har ƙasa ta juya ta kalli Abba haɗe da cewa,
"Ko ba wannan ba? Na rantse ba baki nayi maka ba, matuƙar baka gyara tsakanin ta da ƴar uwar ka ba ko kaffara bazan yi ba sai ta saka ka a irin halin da kake jefa ni aciki yanzu, dama alƙawarin ALLAH baya tashi, kama tudini tudan, ina maka addu'a ALLAH ya kare ka kuma ya shiryar dakai" tana gama faɗa hakan tayi gida, Nihal data tsuke fuska jin abunda Hajiya ta faɗa ta kalli Abban nata haɗe da cewa,
"Meye Abba?"
"Ba komai Nihal" ya bata amsa tare da miƙewa ya koma cikin ɗakin sa, tabbas Hajiya na neman ɓallo masa gagarumar fitinar da bazai juri zuwan ta ba, adai gama wannan auren da daya sani tun farko bai ɗauko zancen yiwa Janan shi ba gaba ɗaya,
Nihal kuwa cikin ko in kula ta koma saman tana mamakin yanda Hajiya ma tasan da zancen har ta dawo da Janan ɗin gida, don ta so tun yanzu Janan ta fara banbancewa tsakanin hatsi da tsakuwa kafin taje hannun da zaisa dole ta gano cewa gata suke yi mata da suka ce baza ta arewa ba.
Mm kuwa yana cikin trying kiran lambar Janan daya ji ankashe sai ga Razina ta shigo ɗakin ta ce wai yazo Baffa na kiran sa, hakan ya dakatar dashi daga cigaba da gwada kiran nata ya jefa wayar a aljihu haɗe da miƙewa yabi bayan ta,
"A'ah. Baffa baka kwanta ba?" Ya faɗa lokacin daya shiga masauki da aka tanadar wa su Baffa, wayar dake hannunsa ya miƙa masa haɗe da cewa,
"Ungo nan ɗan uwan ka ne Ahfan dake ƙasar Indiya yana karatu zai faɗa maka inda ƴar uwar ka Ruƙayya da mahaifiyar ta suke aure sai ka samu lokaci kaje ku gaisa dasu, kasan na faɗa maka anan take zaune ita da mahaifiyar ta"
Karɓar wayar yayi tare da karawa a kunne haɗe dayin sallama, bayan ya amsa masa ya ce,
"Barka da warhaka, sunana Muhriz.." kafin ya ƙara sa ya ji Ahfan ya iyar masa da cewa
"Ɗan Baffa Muhammadu?, Yayan Razina kuma angon sati mai zuwa ko?" Faɗaɗa fara'ar sa ya yi cike da mamakin jin abunda ya faɗa kafin yace,
"Tabbas haka ne bakayi ƙarya ba, kenan dai Abba ya sanar dakai komai akaina?"
"Haka ne, tun ma ranar da ka je can ƙauye ta farko"
"Masha ALLAH ya karatun?"
"Alhamdulillah, mun kammala kuma in sha ALLAH nan da wata biyu cikin na uku zan dawo"
"To ALLAH ya dawo dakai lafiya"
"Amin ya rabbi, ai Baffa ya faɗamun cewa ashe kai matuƙin jirgi ne, nace to wataƙil ma mun taɓa haɗuwa ko anan ƙasar ko kuma a cikin jirgin bamu san ƴan uwa muke ba"
"Haka ne, amma yanzu tunda mun sani nasan in Sha ALLAH zamu haɗu, don next Flight ɗin mu in the next one month a India da kuma Germany zamuyi sa, so in Sha ALLAH idan nazo zan neme ka"
"Wow! Thank you so much brother, rilly nice to meet you"
"Me too broth" mm ya faɗa yana murmushi, nan ya faɗo masa address ɗin da sister ɗin sa Ruƙayya ke aure da kuma na mahaifiyar su, wani irin shocking mm yayi jin address ɗin daya basa na mahaifiyar su, amma sai bai nuna masa ba har suka yi sallama, kallon Baffa mm ya yi yana miƙa masa wayar haɗe da cewa,
"Baffa akwai matsala fa"
"Ta me kuma Muhammadu?"
"Ya sunan mahaifiyar su Ahfan ne?"
"Zainabu, lafiya?"
"Lafiya klw, sai dai ina ga duk da bamu taɓa zancen Abba mahaifin Janan nada wata mata ba, inaga itace mahaifiyar su Ahfan"
"Ita Zainabun?, To amma ai da muka je kakar yarinyar kaɗai muka gani da kuma yayar ta, ba muga wata mata ba agidan"
"Ta yuyu ba anan cikin gidan take ba, don gaskiya bamu taɓa zancen da Janan ba, amma address ɗin gidan da Ahfan ya bani da sunan mijin nata duka na Abban Janan ne"
"Ikon ALLAH, dama kuwa ance mijin da take aure mai kuɗi ne sai dai yana da tsanani sosai don ko ƴan uwan ta bai cika bari tana biyawa ba, haka itama baya bari aje mata" ni sawa mm ya yi haɗe da cewa,
"Tabbas ita ce, amma zan tambayi Janan don mu sake tabbatar wa"
"Kaiiii...wannan mutume bai da daɗin al'amari da ganin sa, kuma in shine ba ƙaramin haƙuri take dashi ba, don mukam ɗan uwan mu ba haka yake ba, kuma nasan dole zata riƙa tuna shi, mutuwa kenan mai yankin ƙauna"
"ALLAH ka jiƙan musulmi"
"Amin ya rabbi" shiru ne ya biyo na dan wani lokaci tsakanin sa da baffan kafin ya miƙe yana faɗin,
"Baffa bari in tafi, ko akwai wani abu da kuke buƙata?"
"Babu shi Muhammadu, munci mun ƙoshi ga kuma kazan nan har ta rage, Alhamdulillah ALLAH dai ya yi maka albarka"
"Amin Baffa to sai da safe"
"ALLAH ya tashe mu lafiya"
Aminin Baffa kuwa dama yana can part ɗin su suna kallo shi da Jabir, bai bar part ɗin ba sai kusan sha biyu sannan shima ya je ya kwanta yana mai jinjina yanda ƴan birni ke jin daɗi abun su hankali kwance..
***. ***. . ***
Wata irin ƙara Amira sake kwance ta saki tare da sakin wayarta ta fashe da kuka, ba Umma kaɗai ba hatta Zarah da Al-amin da suka fara bacci sai da suka farka haɗe da miƙewa zaune cike da firgita da kuma tsoro,
"Lafiya Amira?" Umma dake zaune tana lazimi ta faɗa don kusan ƙarfe ɗaya saura lokacin, kasa amsawa tayi sai dai Zarah ta miƙa hannu ta jawo wayar Amira ɗin dake haske, hoton Janan ta gani tare da mm da suka ɗauka da rana acikin group watsApp ɗin Amira da farkowar ta fitsari kenan kamar an tsunkuleta ta kunna data ta hau watsApp ashe da rabon idanuwanta zasu gane mata abunda zai hanata bacci ne,
Rubutun dake ƙasan hoton Zarah ta shiga karantawa kamar haka _Good evening my colleagues, need your highly prayers and wishes, in Sha ALLAH soon to be Mr and Mrs Muhriz Muhammad Dabino (mm dabino), and the wedding day will announce definitely tommorow after our last practical paper_ yanda ƴar uwar tata ke kuka ya hanata nuna farincikin ta ga zancen auren nasu da Janan ta turo hoton su, cikin sanyin murya ta kalli umma dake faɗin, "wai lafiya kuka yi mani shiru daga ke har ita"
Wayar Janan ta miƙawa umma ba tare da tayi magana ba tana kallon yanda Amira ke faman tashar kuka kamar ranta zai fita, Umma na ƙoƙarin karɓa Al-amin da yafi kusa ga wayar shima ya miƙa hannu da zimmar amsa yaga hoton dake jiki da Zarah ke miƙawa umma ta gani kawai hannun sa ya buge wayar ta faɗi a kife ko da umma ta maza ta ɗauko gaba ɗaya screen ɗin ya shafe,
"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, oh ALLAH! Allahummah ajirni fi musibati wa ahlifni khairan minha" umma ta faɗa ba tare da ta sake cewa komai ba takai wayar gefe ta ajiye, don yanzu ba mutuwar wayar ce damuwar ta ba, kukan da Amira keyi shine yafi ɗaga mata hankali, ta sowa Zarah tayi haɗe da rungume ta ta ce,
"Kiyi haƙuri Aunty, dukkanin mai rai da irin tasa ƙaddara da kuma jarabawa, nasan yanda kike son Yaya mm ɗinki, shiyasa ban taɓa mantawa na roƙa maki ALLAH ya mallaka maki shi kuma yasa ya soki kamar yanda kike son sa ba, sannan nasan Umma ma tana yimaki addu'a ALLAH yasa ya zamo mijin ki saboda soyayyar da taga kina yi masa daga zuciya har jini, amma ya zamuyi da zanen alƙalamin ƙundin ƙaddara mu, dukkan mu bamu isa musa abunda ALLAH ya rubuto ba rabon ki ba ki samesa haka kuma bamu isa hana abunda ALLAH ya rubuto rabon ki ne ki samesa, kiyi haƙuri in sha ALLAH, ALLAH zai dubi zuciyar ki ya musanya makida wanda ya fishi, pls kiyi haƙuri kada ki saka mu kukan muma"
Waɗan nan maganganun da Zarah keyi su suka ankarar da Umma abunda ke faruwa, murmushi tayi haɗe da cewa,
"Kiyi haƙuri Amira, da bakin mahaifi nasa ka samu abunda ba naka ba na tabbata da babu abunda zai hana ki auri wannan bawan ALLAH, amma tunda kika ga baki aure sa ba to ke ba matar sa ce ba, Janan ita ce wacce ALLAH yasa zata zamo matar sa, haka rayuwa takan kasance ga bawa akoda yaushe, mutum zai kasance yana son wani abu amma ba alkhairi bane agaresa haka kuma zai kasance ya tsani abu baya son sa sai ALLAH yasa shine alkhairi agaresa, abunda ake so ga bawa kuma mumini na ƙwarai shine yarda da ƙaddara mai kyau da marar kyau sai ALLAH yayi mashi kyakkyawar sakayya, a matsayina na mahaifiyar ki ina yimaki addu'a ALLAH ya baki wanda yafi shi kuma ya sassauta maki soyayyar sa acikin zuciya, ita kuma Janan ALLAH ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya, ya kuma kauda sheɗan a tsakanin su"
Zarah ta amsa da amin haɗe da sakin ajiyar zuciya tana mai tausayin ƴar uwar tata a ranta....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/24, 10:53 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 59_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
______________________________
Kuka take yi sosai kai ka ɗauka mutuwa akayi mata, Zarah da Umma sunyi rarrashi har sun gaji sun samata idanuwa, sosai umma ke jin takaicin kukan nata a ranta amma babu yanda ta iya dole tasa mata idanuwa, saboda tasan ba ita ta ɗorawa kanta soyayyar yaron ba don haka duk abunda za tayi bata isa ta dakatar da ita daga abunda take ji ba, sai da tayi mai isar ta ta gama sannan bacci ya yi awon gaba da ita, amma duk da haka ba abun da takeyi cikin baccin banda ajiyar zuciya tamkar wata ƙaramar yarinya, ita dai umma na zaune kan dardumar ta tana faɗawa ALLAH damuwowin ta har aka kira sallar asuba, sabbatu kuwa da buge-buge Amira ta shasu tsakar dare don har sai da taso karewa Umma sallah, hakan ya sa koda ta tashe su sallah da asuba gaba ɗaya jikin ta ciwo yakeyi, yanda take faman yatsinar fuska ya sa umma yin murmushi haɗe da cewa,
"Sannu Sarkin yaƙi in jin kin fanshe duk abunda ke zuciyar ki"
Kallon Umma ta yi da kumburarrun idanuwan ta da tasha kuka daren jiya haɗe da ɗan turo baki ta ce,
"Me yafaru Umma? Ni gaba ɗaya ma ji nake duk jikina nayi mun ciwo"
"Ai dole, wannan buge buge da kikayi jiya kamar mai faɗa da wani, ni dai in ya tsaya cikin bacci ɗai ai mun gode ALLAH" murmushi ta yi sannan ta miƙa haɗe da cewa,
"Umma kenen, ai kuma nariga dana haƙura, in sha ALLAH ba abun da zai faru, dama mun gama practical exam ɗin da za muyi zan roƙeta ta yafe mun duk abunda ke tsakanina da ita don nayi mata abubuwa da yawa akansa, kuma na tabbata ta sani kawai ta ƙyaleni ne, saboda daga yau umma ina mun rabu da ita ban san ta inda zan kuma sake haɗawa da ita ba"
"Kin yi tunani mai kyau Ubangiji ALLAH yayi maki albarka"
"Amin ya rabbi Umma" ta faɗa tare da ficewa daga ɗakin tana jin wani kuma na sake zo mata, yanzu shikenan mm ya yi mata nisa, data haƙura dashi dama kar ta haƙura babu yanda za tayi, ta faɗa cikin zuciyar ta tare da jin kukan ya kucce mata, da sauri ta rufe bakin ta cikin muryar kuka tana faɗin,
"Ya ALLAH kai ka jarabce ni da son bawan ka ba tare da nasan dalilin yin hakan ba, ALLAH na roƙeka ka bani dangana da haƙurin mantawa dashi" ta ƙare maganar tana share hawayen dake kwance kan fuskar ta da hannu biyu,
Bayan ta gama Sallah ta ce Zarah ta miƙo mata wayar, saboda tana so tayiwa Janan fatan alkhairi kamar yanda taga sauran abokanan karatun ta nata yi mata, nan umma ke faɗa mata cewa sai dai tayi haƙuri wayar ta riga data shahe jiya data faɗi a hannun Zarah,
Bata ce komai ba ta tashi ta nufi tsakar gida tafara sabgogine data saba yi akoda yaushe, bayan ta gama ta watso ruwa tare da dawowa ta ɗauko littafan ta tana sake dubawa tunda jiya bata samu tayi karatun ba, dama sai umma ta tashi sallolin dare take ta data itama tayi karatu idan suna exam,
Kasancewar sai zuwa sha biyu zasu fara exam ɗin ya sa bata fita ba sai da taga ƙarfe sha ɗaya har da kusan rabi tayi sannan ta miƙe ta saka hijab ɗin ta tare da kallon Umma dake tsintar wake zata ɗora girkin abincin rana ta ce,
"Umma na tafi"
"To adawo lafiya, in sha ALLAH kafin ki dawo zan sa Zarah taje shagon can na _ya mu samu communication_ ta tambayo ko nawa za a gyara wayar, zuwa ƙarshen wata idan ALLAH ya hore sai na bayar a gyara maki"
"To Umma Nagode"
"ALLAH ya baku sa a ku duka yasa ku fito da kyakkyawan sakamako"
"Amin Umma na" ta faɗa tare da rungumeta sannan ta fice, a ƙofar gida ta haɗu da Zarah ta dawo daga wajen sayen omo za tayi wanke wanke,
"Zarah na tafi, kiyi mani addu'a"
"To aunty Amira ALLAH ya kiyaye ya baki sa a, bari na raka ki" suka jera tare har titi suna ta firar su abun gwanin ban sha'awa, ita dai Zarah sai mamakin yanda Amirar ta sauya sai kace ba ita bace kullum cikin hantarar su, tana dawowa gida ta ce,
"Umma yau Aunty Amira kamar ba ita ba, gaba ɗaya ta sauya baki ga yanda muke ta fira da ita ba dana je rakata bakin titi, ALLAH duk sai naji ta bani tausayi, tana son wannan yaya mm ɗin"
"To ya zatayi, ALLAH ya riga ya tsaro hakan, ubangiji ya bata wanda ya fishi kuma shima take son sa kamar mm ɗin"
"Amin Umma, nifa" ta faɗa tare da rufe fuskar ta,
"To kema ALLAH ya fiddo maki nagari mai albarka"
Da haka ta miƙe cike dajin kunya ta je ta wanke kwanon dake tsakar gidan tana mai yiwa kanta da kuma ƴar uwar tata fatan samun mazaje na gari.
Janan kuwa tun cikin daren da tayi posting take tasa ran ganin sauƙin taya murna daga ƙasar tata, amma har kowa ya gama yi masu fatan alkhairi bata ga Amira tayi mata ba kuma ta ganeta online, hakan ya sa ta ɗan ji ba daɗi duk da tasan ba lallene dama tayi mata ba, amma ta zata zata daure duk yanda take ji tunda har cikin mutane ne kuma ba wanda bai san su tare ba tayi mata, cike dajin haushi ta jefar da wayar tata gefe, kiran mm ne ya shigo tayi saurin jawo wayar ta ɗaga tana faɗin,
"Hello hubby" irin can ciki-ciki dake nuna tana cikin rashin daɗin rai, "lafiya na ji muryan ki haka Janany, ko kin fara bacci ne?"
"A'a hubby"
"To wani abun ne ke faruwa?" Tsintar kanta ta yi da kasa ɓoye masa komai, don haka ta sanar dashi abunda ke faruwa, dariya ya yi haɗe da cewa,
"To sai me idan Amira bata yimaki wishes ba?, Ina sauran colleagues ɗin ki sun yi ko?"
"Eh but kafa san babu wanda bai san yanda muke da ita ba, wlh it's shameless to me"
"So yanzu dai kiyi haƙuri, koma dai meye ita hassada ga mai rabo ai taki ce"
"Hubby kenan, amma kaima kasan dole Amira za taji ba daɗi, tana fa son ka sosai"
"To ko zaki haƙura ne ki bar mata" ƴar dariya tayi haɗe da cewa,
"Ai bazan iya bane, wallahi da tuni nayi hakan, kawai dai ina jin tausayin ta ne"
"To tunda kin san haka stop complaining about it"
"Shikenan na dena, ya akayi har yanzu baka kwanta ba?"
"Ehmmm na tsaya yin magana da wani akan invitation ɗin auren mu, ɗazu na tambaye ki ko akwai program ɗin da kike son muyi baki cemun komai ba, so just tell me idan akwai don tuni ya gama design ɗin ta, ke muke jira in akwai sai a saka ya turo mani saboda mu fara turawa tun yanzu ko a media ne tunda wuri ya ƙure"
"Haka ne, but i don't think Zan yi komai, kawai ashafa fatiha is ok"
"Shikenan, nima haka na gani amma yanzu muka gama rigima da friends ɗina a watsApp group wai basu yarda ba dole ko reception ne sai an haɗa immediately bayan anyi ɗaurin auren, so sunfi ƙarfi na dole na bari suyi yanda suke so, dama gashi sai ƙorafi suke yi ban sanar dasu da wuri ba"
"Da gaskiyar su kam"
"To shiyasa nayi shiru don na goge laifina, amma ai kema kinsan ba laifina bane"
"Haka kuma kaima kasan no matter how indai za a ɗaura mun auren nan to fa tabbas da kai ne bada kowa ba"
"To naji tunda kema kin goyi bayan su, ya karatun in jin kinyi kar gobe kije kiyita raba idanuwa aka tilas ke amarya" dariya ta kwashe da ita kafin tace,
"Ai kwata kwata yau banda natsuwar karatu balle har nayi, thank God practical exam ce ba wani dogon karatu bane"
"ALLAH ya taimaka, gobe ƙarfe nawa zan zo"
"Kazo quater to 12"
"In Sha ALLAH"
Sun ɗan taɓa fira kafin suyi sallama, wanka ta sake yi sannan ta sauko ƙasa ta haɗa tea mai kauri tasha ta kwanta tana jin wata irin natsuwa na ratsa jikin ta.
Kasancewar bata kwanta da wuri ba yasa tun da tayi sallar azahar bata tashi bacci ba sai kusan ƙarfe goma sha ɗaya da rabi, lokacin har mm ya maida su Baffa gida don tun da safe suka shirya suka ce zasu wuce, bayan sun sa ya kaisu can gidan iyayen mahaifiyar su Ahfan sun gaisa, dama ba wani nisa ne tsakanin ƙauyen da kuma cikin garin Katsina ba don bazai wuce kilometer 50 zuwa 55 da biyar ba, shiyasa har ya kai su ya juyo a daidai wannan lokacin, ida ƙarasowa kawai ne beyi ba shiyasa da yaga 11:30 tayi ya kirata don ta ƙarasa shiryawa kafin ya ƙara so,
Agurguje ta faɗa toilet tayo wanka, tana gama shiryawa yana ƙarasowa ya kirata a waya ta fito, daga shi har ita yau wani fresh sukayi da kallo ɗaya zaka yi masu kaga dacewar su da juna, saye take da blue Black ɗin doguwar riga jalabiya tayi rolling kanta da mayafin ta, shi kuma jampas ne ajikin sa shima the same colour da kayan ta tamkar sun haɗa baki, juyowa ya yi ya kalleta haɗe da cewa,
"Yallaɓiyata ya da gasa haka?"
"Gasa tame?"
"Tasa kalar kayan da nasa mana"
"Hmm..zuciyar ce haɗe shiyasa mukayi zaɓe iri ɗaya" haka dai suka ƙara sa cikin makarantar duk inda suka ratsa sai an kallesu saboda yanda suka yi bala'in dacewa,
Yana yin parking da ita bakin department ɗin su ta hango Amira can bayan acadamic staff tana magana da Ingaski, kuka ma takeyi tana yimasa bayani cike da tashin hankali, shi kuma yana nuna mata ta kwantar da murya, ganin ta kasa fita cikin motar ya sa mm cewa,
"Lafiya?, Lokaci fa na tafiya" sauke ajiyar zuciya tayi haɗe da ficewa cikin motar ba tare da tace masa komai zuciyar ta cike da mamaki da kuma tashin hankalin ganin Amira da Ingaski,
Hakan yasa mm tada motar ya yi ribas haɗe da juyawa, kaɗan ya rage ya buge Amira data rugo aguje tana kuka zata shiga lab.. ɗin department ɗin nasu da za suyi exam, ba tare data lura da ko waye ba ta shige ciki, shi kuma ya bita da idanuwa tare da mere baki sannan ya bar wajen.
*Kuyi maleji da wannan wlh hankalina ba kwance ba an shigo gida an ɗauke mani system😭😭😭, don ALLAH kusaka ni a addu'o'in ku ALLAH ya bayyana mani ita ya toni asirin duk wanda ya ɗauka, project ɗina da document ɗin karatuna, presentations da sauran abubuwana masu muhimmanci duka na ciki, don ALLAH ku tayani addu'a 👏*
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/25, 10:42 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 60_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
______________________________
Kallo Janan ta bita dashi har ta ƙaraso kusa da ita tana ci gaba da kukan, ganin supervisor ya shigo lab ɗin har lokacin Amira bata dena kuka ba ya sa Janan tayi saurin tura invitation card ɗin auren su agroup watsApp nasu na department sannan ta kashe data ta jefa wayar cikin jikka ta kaita can gefe ta ajiye, ta dawo ta ɗora hannunta saman kafaɗar Amira da bata ma san kusa da ita take ba, cikin sanyin murya ta ce,
"Amira meke faruwa?" Da wani irin shock Amira ta ɗago ta kalleta jin muryar ta akusa da ita tayi wani irin janyewa da sauri tabar wajen ta kuma kusa da wata sai ya zamana akwai mutum ɗaya a tsakanin su, wani kallo Janan ta bita dashi cike da mamaki da kuma rashin jin daɗin abun da tayi mata, daidai lokacin supervisor ya kawo gare ta tare da aza mata question paper da kuma booklet yana faɗin, "Janan lafiya?, Is any thing wrong?" ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa,
"No sir" tana mai ɗaukar questions paper ɗin har lokacin idanuwan ta nakan Amira data kasa haɗa idanuwa da ita sai faman share ƙwalla da takeyi, daga ita har Amirar rubuta jarabawar kawai suke yi amma ba cikin daɗin rai ba, kasancewar wacce ke kusa da Janan sai faman regen booklet ɗin ta take yi tana satar amsa yasa supervisor ya ɗauketa daga wajen ya maida ta can baya, ya rage tsakanin Amira da Janan ba mutum ko ɗaya, daidai lokacin Ingaski ya shigo wajen don couse ɗin sa ne akeyi, line by line ya shiga bi yana tambayar su if there's any question tare da gyara masu apparatus ɗin da suke amfani dasu yana duba quantity ɗin kowane chemicals da suke haɗawa har yakai inda Janan da Amira suke, idanuwa ya ƙura wa Janan yayin da Amira ta riƙa ja gefe daga tsakiyar su ɗin da yake tsaye yana jefo ma Janan tambaya haɗe da mayen kallo, ganin tayi banza dashi ya sa ya yi murmushi ya bar wajen, ɗan tsaki Janan tayi haɗe da rolling idanuwan ta kafin ta miƙa hannu zata ɗauki wani chemical ta haɗa don fara amsa tambaya ta gaba, da sauri Amira ta miƙa hannu itama zata ɗauka, amma saboda hannun Janan ya riga kaiwa sai ta riga ta ɗauka, saurin wafce chemical ɗin Amira tayi a hannunta cike da ɓacin rai Janan ta ɗago kai, enough is enough ta faɗa cikin zuciyar ta saboda Amira ta fara kaita bango, ta fara ƙure haƙurin ta, don haka kawai itama ta wafce kwalbar tare da balle ma Amira wata irin harara, sake yunƙura wa Amira tayi da niyar karɓa supervisor ɗin ya daka mata tsawa haɗe da pointing ɗin ta yana mai yi mata gargaɗi akan idan ta sake yin wani misbehaving zai kece takardar ta ya kore ta,
Ingaski kuwa yana fita shugaban makarantar ya nufo lab ɗin shima yana amsa waya, wacce ba da kowa yake yi ba sai mahaifin Janan, zagayen ɗaliban ya shiga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 40