tana mamakin yaron nata dako faɗa mata baiyi zai bisu ba haɗe da cewa,
"ALLAH ya tsare hanya ya kaiku lafiya" sai da taga ficewar su sannan ta koma cikin gida cike da kewar yaran nata,
Janan kuwa suna kammala jarabawa gidan Hajiya ta nufa don sam bata sha'awar komawa can gidan saboda tsoron abunda zata yadda acan, dama tuni Hajiya ta koma don haka tana isa ta fara shiga toilet ta watso ruwa haɗe da ɗauro arwala tayi sallah, bayan ta gama taci abinci sannan suka hau fira ita da Hajiya, inda take sanar da ita cewa mm ya tafi garin su don ya sanar da mahaifin sa zancen turowa, murmushi Hajiya tayi haɗe da cewa,
"ALLAH sarki, yaron nan da gaske yake sonki, ubangiji ALLAH yaji tausayin sa yayo masa mafita don ba ƙaramin aiki bane gabansa zancen auren nan" shiru Janan tayi kamar mai wani nazarin kafin tace,
"Hajiya kenan, wai ke har yanzu baki fahimci komai akan Muhammadu nki ba?"
"Kamar ya Janan"
"Ni fa na fara tunanin akwai abunda yake ɓoyewa da baya so a sani game dashi, domin wani lokatcin in kika gansa bazaki taɓa tsammanin yana da ƙaramin ƙarfi ba, jikinsa kaɗai in kika kalla zaki san baya son wahala kamar yanda shi yake nunawa, a gaskiya ina zargin basaja yakeyi, sai dai banida tabbas akan haka, hasashe ne nakeyi saboda sauye-sauyen da nake gani akansa wasu lokutan, rashin hujja da kuma sanin dalilinsa na aikata hakan yasa na kasa tunkarar sa da zancen saboda bansan me yake so ko yake nema ba daya sashi ɓoye gaskiyar ko waye shi, iya abunda na sani ko waye shi ina son sa kuma zan iya auren sa a haka" jinjina kai Hajiya tayi haɗe da cewa,
"Ni ma ina wannan tunanin araina, musamman data bayyana tare yake dasu Jabir, sai nake ganin a irin sana'ar da yakeyi da kuma shigar da suke dashi har Jabir to sunfi ƙarfin ta, don in kin lura daga ita mahaifiyar tasu har ƴar uwar tasu ba haka suke ba, to koma dai meye mu alkhairi muke fata agun su ba sharri ba, babu komai girman ta idan akwai wadatar zuci zaki iya ganin mutum a yanda suke, arziƙi kuwa duk yawan sa in ba wadatar zuci da kwanciyar hankali baza a samu natsuwa acikin sa ba, komai zai iya faruwa indai akan mahaifinki ne tunda ya nuna baya son talaka"
"ALLAH to ya kyauta, ai wannan dalilin ne yasa ma Abba baya son mm"
"To ALLAH ya shirye sa yayi masa maganin wannan baƙar a ƙidar"
"Amin ya rabbi" ta faɗa tare da kwantawa ta ɗora kanta akan cinainan Hajiya tana faɗin,
"Yau dai bari na ɗan ɗana ƙafafuwan nan dake nema sufi karfin mai su nima na more su" ga mamakinta sai taga Hajia ma ta gyara mata kanta tana faɗin,
"Ga ki ga su, moriyar ta nawa kike so kiyi masu bacin wacce kukayi kuna ƙanana, ALLAH dai yasa ɗiya na da zaki haifa mun leda Muhammadu nada rabon moriyar su suma" saɓanin da da tana kwantawa zata ture mata kai a gefe tan mita wai kar ta karya mata ƙafa...
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/18, 11:56 AM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 54_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
********
_https://www.wattpad.com/1259942819?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=cpas5pc4uX6syLtIzszICDlqga%2Fx%2FKxvAko8ToUqa0UYeRYGFpvlHDfXlrlBFukMph%2FlzK80p2KlVJOBx3CMr5Ji7EdWSTQ2LmibcPPVBNXmpIMFhodbTFj3%2B%2FFy1gQy_
______________________________
Ta jima gidan Hajiya kafin ta shirya ta tafi gida, ko data isa ta tadda Abba zaune a compound ɗin gidan riƙe da jarida yana karatu, a zahiri zaka ɗauka idanuwansa na akan jaridar dake hannunsa ne, amma ba haka bane don tunda motar Janan ta kunno kai cikin idan ya maida kallonsa wajenta har ta ƙara so ciki tayi parking tare da fitowa tana gyara zaman mayafin ta dake neman cire wa, sai a lokacin ya ɗauke idanuwansa daga kanta ya maida ga jaridar yana jin wani tuƙuƙuƙi na taso masa azuciya, hannu ya miƙa ya ɗauki cup ɗin dake ajiye gefen sa da Jazz dake tsaye saman kansa ya gama tsiyaya masa ruwa ya kai a baki, bai dire sa ba har sai da ya shanye ruwan ciki tas sannan ya sake ajewa Jazz ya buɗe gorar ruwan ya sake tsiyaya masa wasu suma ya ɗauka ya shanye tare da sauke wata irin ajiyar zuciya, dai dai lokacin Janan ta ƙaraso wajen ta ɗan rissina ƙasa tana gaishesa cikin girmamawa, ba tare daya kalli gefen da take ba ya ɗaga mata hannu alamun amsawa sannan ta wuce cikin gidan jikinta a sanyaye,
Da Madam florence ta fara cin karo tsakar falon tana jere abincin data gama na dare akan dining table ta gaishe ta sannan ta nufi upstairs ɗin da ɗan gudu gudu tana faɗin,
"Madam what do you cook now"
"Is pounded yam with stew my dota, and then with cowtail pepper soup"
"Ok, thank you" ta faɗa lokacin data ƙara sa hawa, cikin ƴar ɗaga murya Madam florence ta ce, "hope you like it?"
"Yes but now am ok"
"Are you sure?"
"More than that madam" ta bata amsa tana murmushi tare da juyawa zata shiga ɗakin, muryar Nihal dake tsaye a bakin ƙofar ɗakin ta tayi folding hannayen ta ta jiyo tana fadin
"Hy Mrs mm, welcome back" har ta ɗora hannunta akan handle ɗin ƙofar ɗakin nata da niyar buɗe wa ta shiga sai kuma ta tsaya, sai da tayi sekonni uku a haka sannan ta juyo murmushi ɗauke akan fuskarta tana kallonta, folding hannayenta tayi kamar yanda itama tayi haɗe da cewa,
"Help me and repeat it again, it was sound so Sweet"
"Rilly?"
"Upcouse" Janan ta faɗa tana rolling idanuwanta akan Nihal, juyawa tayi tare da mere baki tan ƙoƙarin buɗe ɗakin nata ta shiga haɗe da cewa,
"Kiyi addu'a tare da fatan hakan ta tabbata, domin abune mai wahala samun maiƙo akai"
"Kyaji dashi don ke ya dama bani ba"
"Haba! A tunaninki kenan, ai abunda baki sani ba na gaba shi ya riga da ya yi gaba na baya kuma sai labari"
"ALLAH?, to ai shikenan, amma ina so ki sani matuƙar akwai rai sannan layi na ja, to na baya ma sai ya kai, don haka thanks for the wanderful name given to met (Mrs. Mm)" ta ƙarasa zancen tare da ƙarasowa inda take ta rungumeta, kallon tun daga sama har ƙasa tayi mata bayan ta saketa haɗe da cewa,
"Wish you a very good luck Mrs..." Kafin ta ƙara sa Nihal ta ce,
"Asgar, Mrs Asgar and also a dadys proud" ta faɗi maganar kai tsaye tana jujjuya kai tare da buɗar hanta, with so excited Janan ta waro idanuwa had'e da cewa,
"Wow! congrats my darling sister, now i hv seen the real love you hv for me tunda har kika amince zaki sharewa Abban mu hawaye ki auri zaɓi sa, congratulation once again" Janan ta faɗa cike da farinciki tare da miƙa mata hannu, tsaki tayi sannan ta shige ɗakin ta yayin da Janan ta saki wata ƴar ƙara haɗe dayin tsalle cinikin ɗaya murya ta ce,
"Thank you dady's proud and also Mrs Asgar to be, much luv, hug and kisses Adda na" sannan ta wuce ɗakin ta cike da farinciki, a ɗaya ɓangaren zuciyar ta kuwa cike da mamakin yanda ta amince da auren Asgar cikin sauƙi duk da tarin ƙaunar da take iƙirarin tana yiwa the charming man ɗinta,
Su mm kuwa suna gab da shiga ƙauyen nasu Jabir ya juyo yana kallon sa haɗe da cewa, "can't believe Wai mahaifin Janan ya amince katuro iyayenka, anya ba wani abun yake shiryawa ba" saida mm ya tashi daga kishingiɗen da yayi akan sit ɗin sannan ya ce,
"Koma dai da me ya yi ni hakan yayi mun, na rantse maka da ALLAH Jabir tun ranar da Janan ta kirani tana faɗa mun cewa Abba yayi pixing ɗin ranar aurenta immediately idan ta ƙare jarabawa hankali na ya tashi, gaba ɗaya ko bacci mai kyau bana samun nayi uwa uba cin abinci daidai, na kai tunani na iya maƙura don samun mafita da kuma hanyar da zan ɓullo wa lamarin amma na kasa, addu'a ita na saka agaba a ƴan kwanakin nan inata faɗa wa ALLAH sai gashi da kansa ya kawo mana mafita, shiyasa naga bazan iya ƙara minti ɗaya ba har sai nazo na faɗawa Baffa, kuma ina fatar samun goyon bayansa ɗari bisa ɗari,
"In Sha ALLAH a yanda ka bani labarin sa babu wata matsala da zaka samu, zai amince da zancen, but amma wannan wace irin addu'a ce haka kayi dake saka biyan buƙata a ɗan ƙanƙanen lokaci, gist me pls nima nayiwa Razy baby tayi dying akaina" ya ƙare zancen tare da juyawa yana kallon Razina dake sit ɗin baya, ɗan murmushi tayi haɗe da lumshe idanuwanta ta buɗe sannan ta kashe masa ido ɗaya tana dariya,
Sakin starring motar Jabir ya yi haɗe da dafe saiti zuciyarsa ya ce,
"Washh.." da sauri mm da baisan wainar da ake toyawa ba ya juyo ya kallesa haɗe da dafe staring motar yana faɗin,
"Lafiya?"
"Zan mutu ne akan soyayyar ƙanwata"
"Mtsss..taka burki ɗan iska kar kazo kayi.un baƙin cikin zama ango" mm ya faɗa cike da takaici yana kallonsa, dariya ce ta kuccewa Razina tayi saurin rufe baki tana kallon yanda Jabir ɗin ke ƙoƙarin parking a gefe,
"Wai me zakayi ne?"
"Me kace nayi?" Ya tambayesa shima bayan yayi parking a gefe yana ƙoƙarin fita, cike da mamaki yake kallonsa har ya fice ya za gaya ta baya inda Razina ke zaune ya buɗe ya shiga haɗe da rufe marfin motar ba tare daya damu da kallon da mm keyi masa ba,
Rasa me zai ce masa da yayi ya sa shi fitowa ya shiga gefen drivern ya tayar da motar suka ƙarasa shiga ƙauyen, dama tuni ya sanar da Baffa zancen zuwan su a waya, don haka koda suka isa an haɗa masu liyafa daidai gwargwado, don kwanon abinci yafi ƙarfin goma sha biyar da ƴan uwa suka riƙa kawo masu jin cewa yana tafe,
Sai da suka ci abinci suka huta sannan mm ya yiwa Baffa bayanin abunda ke tafe dasu, ya kuma gabatar da Razina kamar yanda ya alƙawarta masu a waccan lokacin daya zo a matsin ƙanwar sa, Jabir kuma ɗa kuma amini da zai auri Razina, sosai Baffa ya ji daɗi har yake zolayar mm da cewa kace har ka riga ka bashi ƙanwar taka namu kawai muzo mu shafa fatiha, kunya ce ta kama sa ya sinne kai ƙasa haɗe da cewa, "tuba nakeyi baffa ai nawa bai isa ya wadatar ba har sai in kai ka basa, na faɗi hakane saboda na bayyana masoyin nata agareku" baffa na dariya ya dafa kafaɗar sa haɗe da cewa, "ai wasa nake yi malam Muhammadu, in ka cire ni duk duniyar nan Razina batada wani wanda ya isa bada auren ta sama dakai, ko baka ji yanda hausawa ke faɗaba?, babban wa mahaifi, saboda haka kowa ka bawa ƴar uwar taka kayi dai-dai bakayi laifi ba don kana da damar aikata hakan ko a musulun ce, Jabir ya cancanci ka aura masa Razina ko don halaccin mahaifiyarsa agareku, hakan shine TUKUICIN SO da zaka iya mayar a garesu da suka yi maku" yana ƙare zancen ya tara ƴan uwa da abokanan arziƙi ya sanar masu da zancen auren mm ɗin da za a yi sati mai zuwa bayan ya gabatar masu da Razina da Jabir kamar yanda ya yi masa shima,
Razina kam tuni ta zama ƴar gida kuma ƴar gata, dangi sai nan nan akeyi da ita, ita kuwa tsabar farinciki sai faman kukan daɗi take yi, a ɗaya ɓangaren kuma abokanan wasanta tun da suka ji cewa tare take suke da wanda zata aura suka taso ta gaba da tsokana wai tun yanzu ta maida shi bita zai-zai duk inda zata je sai ya bita, ita dai banda dariya babu abunda take don ita kam zuciyar ta cike take da farincikin kasancewa tare da ƴan uwan ta, umma Mariya ce tazo ta kore mata su tana faɗin "kubar mun ƴah tahuta mana, kun zo kun isheta da surutu sai kace tsuntsaye" duk suka sa dariya tare da barin wajen, ta kalli Razina haɗe da cewa,
"Ɗan kwanta ki huta ƴatah kafin akira sallar la'asar, in kika biye wuɗan can zasu saka maki ciwon kai ne, gashi kin kwaso gajiya" dama kuwa tana jin baccin don haka kawai ta gyara kwanciyar ta akan ɗan ƙaramin gadon na umma Mariya daya sha gyara.
Daren ranar kusan zaune suka kwana ana fira bayan baffa yasa su zainaba yarinyar umma luba da Maryama sun rakata gidajen wasu ƴan uwan acikin daren saboda gobe zasu koma.
Washe gari da yake Baffa ya faɗa wa ƴan uwa cewa kwana ɗaya kacal zasu yi suka shiga aikowa da mm kayayyakin haɗa lefe dai dai ƙarfin su, daga masu aiko da zannuwan atamfuna, sai masu aiko masa da yadukka da shaddodi, wasu kuma mayukkan shafawa dana kwalliya da gyaran kai da kuma fata, abunka da ƴan uwa masu yawa da zuciyar yi sai gashi nan take da ɗai ɗaya sun tarawa mm kaya masu yawa, Baffa kuwa dama cikin daren ya je ya siya masa a kwatuna irin na jikkuna ƙwaya biyu masu kyau babba da ƙarami aka zuba kayan aciki, dama su haka sukeyi a ƙauyen idan yaro zaiyi aure ƴan uwa zasu har haɗo masa abunda suke dashi dai-dai ƙarfin su sai a bashi ya ƙara da abunda yake dashi shi yasa shi ma suka yimasa haka duk da sun san cewa yana da hali sosai,
Mm kam rasa bakin yi masu godiya ya yi don bai taɓa tsammanin hakan daga gare su ba lura da yanayin ƙarfin su, shi yasa malam bahaushe ke cewa talaka mai zuciyar yi yafi tarin masu arziƙin da baza su taɓa iya fidda suhe a wuta ba, ɗaya bayan ɗaya Abba ya rakashi ya je ya yi masu godiya sannan suka kama hanyar koma wa tare da Baffa da kuma wani aminin sa malam Saleh, wanda kusan tare suka tashi tun suna yara, a wannan karon mm ke riƙa motar Razina kuma na gefensa, sai Jabir dasu Baffa a sit ɗin baya,
Razina kuwa har da kukan ta wai mm ya barta anan har sai ya dawo maido dasu Baffa sai su koma tare, kai tsaye Jabir ya faɗa mata cewar hakan bazai yuyu ba tayi haƙuri ai zasu sake dawo tare, ba yanda ta iya don ta riga da tasan halin kafiya da kuma naci irin nasa dole ta haƙura da zancen tayi yanda ya buƙata amma kana kallon fuskarta zaka fahimci ƙuncin da take faman yi, dariya Jabir yayi a ransa ya ce,
"Zan fi ganewa wannan ƙuncin naki yarinya akan na tafi na barki anan" ɗauke kanta tayi daga ta madubin da yake kallonta yana dariya haɗe da jinginar da kanta a glass ɗin tagar motar dake gefenta,
Cike da farinciki da jin daɗin ganin ƴan uwa suka baro ƙauyen suna ji tamkar karsu tafi, abu ɗaya ne kawai har yanzu baya yi masu daɗi cikin zuwan nasu idan sun tuna, shine rashin samun hoton mahaifiyar su da ba a yi ba, amma Baffa ya tabbatar masu cewa su kwantar da hankalin su in sha ALLAH zaici gaba da nema masu, kuma da yardar ALLAH za a samu,
***. *** ***.
A ɓangaren janan kuwa cike da farinciki ta tashi washe gari don da sukayi waya da mm ya faɗa mata tare zasu zo da Baffa, kuma suna isowa zasu zo suga Abban ta ayi magana saboda haka ta sanar dashi saboda yasan da zuwan nasu kafin su iso, hakan ya sa yau take jin duniyar tata tayi mata daɗi, a maimakon taje ta sanar da Abba sai kawai ta kira Hajia ta sanar da ita, sai da Hajiya ta tsokeneta sannan ta kashe wayar itama ta kira Abba ta sanar masa ta kuma tabbatar masa da cewa ya tabbatar ya yi masu tarbar mutunci da kuma karramawa, idan kuma ba haka ba zata haɗu dashi, a halin yanzu lallaɓa Hajiya yakeyi saboda baya so ta ɓallo masa ruwa, badon haka ba da ya shayar da iyayen mm mamakin da su da kansu zasu hana ɗan su auren ƴarsa don ba ajin sa bace.
Cike da farinciki Janan ta fito zata tafi makaranta ta ji muryar Abba dake tsaye a falo ya dakatar da ita don sam bata ma lura dashi ba, cak ta tsaya tare da komawa baya ta isko sa, cike da mutum taka a matsayinsa na mahaifinta ta duƙa ta gaishesa, ba tare daya amsata ba ya miƙo mata hannu yana faɗin,
"Bani makullin mota ta, kuma daga yau kar ki sake ɗaukar ta"
Miƙa masa tayi don dama tasan haka zata iya faruwa sannan ta miƙe tana faɗin,
"Na tafi Abba"
"Dakata, naji saƙonki daga wajen mahaifiyata, ina so ki faɗa masa cewa awa ɗaya yake da ita acikin lokutan da nake dasu daga nan zuwa sallar azahar domin akwai inda zan je mai muhimmanci, if not da anyi Sallah bzan tafi inda zani, next time idan na samu free time sai su don bazan iya ɓata lokacina a kan zaman jiran su ba"
"To Abba " ta faɗa cikin sanyin murya don jikinta ya mutu sosai,
Tana fita ta jawo wayarta ta kira mm, duk da driven yake yi hakan be hanasa ɗaga kiran ta ba ta hanyar bluethooth ɗin dake laƙe a kunnen sa, kamar zatayi kuka ta ce,
"Abba ya ce awa ɗaya kuke da ita da zaku iya samun sa kafin nan da azzahar, idan ba haka ba shi akwai inda zai je sai dai a bari zuwa wani lokacin da yake free"
Duk da hankalin sa ya tashi ganin yanzu suka fito ƙauye hakan bai hana shi kwantar da murya ba don ya kwantar mata da nata hankalin da yaga ya tashi haɗe da cewa
"Kar ki damu, in sha ALLAH kafin ɗaya mun ƙara so, yanzu haka muna kan hanya"
"Shikenan ALLAH ya kawoku lafiya"
"Amin, ki kula mani da kanki" ya ƙare zancen ƙasa ƙasa don kar su Baffa su jiyo sa, murmushi tayi da har saida ya jiyo sautin sa a kunnen sa sannan ta kashe wayar tare da kallon agogon dake jikin wayar taga sha biyu saura kwata, da sauri ta ƙarasa fita gidan ta taka ƙasa da ƙafarta har zuwa titi ta tari mashin ta haye don bazata iya tsayawa jiran napep ba don sun kusa shiga exam.
Mm kuwa suna cikin tafiya kawai ya ji tayar motar su tayi ƙara sakamakon gudun daya ƙara, da sauri yayi ƙoƙarin tsaida ita yana faɗin "innalillahi wa inna ilaihirrajiun" tare da buɗe marfin motar ya fito, wannan shi ake kira da sauri ya haifi nawa, ya faɗa a ransa, ba damuwar sa ne su isa adaidai lokacin da Abba ke buƙata ba don ko yaushe zai sake buƙatar ganin su kafin ɗaurin auren zasu iya zuwa, damuwar itace abunda zai iya biyo wa baya ga Janan idan har basu isa lokacin daya ɗi ba ba, ya tabbata cewa zai yi bada gaske yake yi ba shiyasa bai ɗauki abun da muhimmanci ba, daga nan kuma bai san wane hukuncin zai iya sake yanke wa ba tunda burin sa kawai ya samu hanyar da zai dakatar da auren, fitowa duk suka yi in banda Razina Jabir ya riƙa masa suka cire tayar don fashewa tayi....
*ALLAH YA JIƘAN IYAYENMU👏😭*
[8/19, 10:20 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 55_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
********
_https://www.wattpad.com/1260572299?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=ZKtE5D48OwPOJL76tLBMUYH6zXwV5ryHwU5GnwDLoIjup3EzpPMnSYOe%2BPLPBU6WZASL59hkwJjA3K7Hm2IYVxOJn7L8NDzXMI%2FuymlAaBRDEbZvKxeFfKDcf11p7RHR_
**********
*Gaisuwar yau taku ce haka ma page ɗin duka naku ne, UMMUL-ADNAN, JANNA, UMMU MUSPIQ, BEEY, HASY PRETTY, ASEEYA MAHRAZ RIDWAN,RROUWAIDA ABDOULRAHAMANE, MOMEEN AMATULLAH, MRS ALAMEEN, SADIYA AMINU BABA, AISHA ABDULLAHI & MAMAN WALID fatan amincin ALLAH da kuma alkhairinsa agareku, ubangiji ALLAH ya jiɓinci lamarinku akoda yaushe kuma yayi maku mafi ƙololuwar sakayya aduniya da kuma lahira, nagd da soyayyarku ga wannan littafi nawa ubangiji ALLAH yabar tare👏*
______________________________
Kimanin mintuna ashirin suka kwashe suna ƙoƙarin sauya tayar data fashe da wata, mm sai yi yakeyi yana duba agogon hannunsa cike da damuwa har ALLAH ya taimake su suka gama ɗaura wata tayar, suna gamawa ya kalli su Baffa dake yimasu sannu yana kakkaɓe hannun sa ya ce,
"Ku shiga muje Baffa"
"Sannu Muhammadu,wato badon ALLAH yasa akwai wata tayar ba da ALLAH ɗari yasan mezai faru, gashi hanya ba kyau tun ɗazu gabana sai faɗuwa yakeyi"
"In sha ALLAH babu abunda zai faru lafiya klw zamu isa, ku shiga muje" ya bashi amsa yana wanke hannunsa da gorar swan ɗaya miƙa hannu ta jikin tagar mota Razina ta miƙa masa, Jabir ya miƙama shima ya wanke nasa hannun tare da ɗago kai yana kallon sa,
"Meke faru mm naga tunda kayi waya ɗazu ka sauya gaba ɗaya" sai daya sauke ajiyar zuciya sannan ya dafa kafaɗar sa haɗe da cewa,
"Bari kawai Jabir, akwai matsala "
"Kamar ya? Wani abu ke faruwa ne?"
"Eh kusan haka"
"Me nene"
"Wato Janan ce takira wai Abba ya ce awa ɗaya ya bamu kafin la'asar saboda akwai inda zai je, idan kuma bamu taho ba to sai kuma wani lokaci, gaba ɗaya jikina yayi sanyi wlh tunda yanzu ana zancen ƙarfe ɗaya da mintoto, bana son au Baffa su je yaƙi saurar su"
"Mtsss, akan wannan zaka tashi hankalin ka?, Ina saura kilomita ashirin da biyar mu ƙara sa ko?"
"Haka ne, but amfara sallolin azahar wani wajen"
"Wani wajen kuma ba'a fara ba sai zuwa ƙarfe biyu, don haka jeka shiga mota muje, kar ALLAH yasa ya saurare mu ɗin" yana gama faɗar haka ya shige gidan gaba inda mm ya tashi shi kuma mm ya koma baya wajen su Baffa, bisimillah Jabir ya yi tare dasa key ya tada motar sannan ya bata wuta cike da takaicin baffan nasa, kafin kace me tuni sun shigo cikin gari lokacin ƙarfe biyu saura mintuna goma, kallon mm ya yi tacikin madubi haɗe da cewa, "man, ina muka nufa?"
"Muje can Jabir"
"Da matar tawa?" Ya faɗa yana zaro idanuwa, don shi gaba ɗaya ma ya manta dasu Baffa acikin motar sai daya gama faɗar hakan sukayi idanuwa biyu da Baffa ta jikin madubi, da sauri ya sinne kai ƙasa tare da ɗauke hanyar zuwa gida kai tsaye, shi kuma Baffa ya yi murmushi haɗe da cewa,
"Jabir inaga dai auren nan naku a haɗe sa dana ɗan uwan ka in baso akeyi kayita tabka rashin kunya ba a bainar jama'a"
"Baffa ayi haƙuri,amma kasan ita macce ce batayi ƙarfin hali irin na maza ba balle ta iya juriyar mu, kana dubon ta za kasan a gajiye take sosai"
"Kai ƙyalesa zolayar ka ne yake yi, shima kansa nasan yana jin daɗin wannan kulawar da kake bawa shalelen sa" aminin Baffa ya faɗa yana dariya, daidai lokacin suka iso gida ya juya yana kallon Razina haɗe da cewa,
"Sannu ƴan mata na, jeki ki huta ki faɗawa Momy mun dawo amma mun wuce gidan su Janan, sai a gyarawa su Baffa inda zasu sauka kafin mu dawo"
"Ok" ta faɗa tare da ɗaukar jikkar hannunta tayi cikin gida shi kuma ya juya kan motar suka nufi gidan su Janan, akan hanyar su ta zuwa ya kira Hajiya ganin ƙarfe biyu ta buge ya sanar da ita abunda Abba ya faɗa, shiru tayi tana mamakin halin Baffa na kafiya idan baya son abu, to fa duk hanyar da zai bi ya ruguza sa sai ya bi,
"ALLAH ya kyauta" ta faɗa haɗe da cewa ya bawa mm wayar, juyawa ta baya ya yi tare da kallon sa sannan ya miƙa masa wayar yana faɗin,
"Ga Hajiya zakuyi magana"
"Muhammadu, kana jina?" Hajiya ta faɗa bayan mm ya karɓe wayar tare da karawa a kunnensa, cikin sanyin jiki ya ce,
"Eh Hajiya ina sauraron ki"
"Ka kwantar da hankalin ka yanzu gidan zan je, kuma abunda nake so dakai ka haɗa duk abunda kake dashi nayin wannan auren daidai ƙarfin ka kuzo dashi, bance ka ƙure kanka ba, abunda kake da hali shi nace ka haɗo kuzo dashi kaji ko?"
"Eh Hajiya"
"Ina ka dai tanadi wajen ajiye ta idan an ɗauka auren ko?"
"Eh Hajiya, baza a rasa ba in sha ALLAH"
"To shikenan, idan ma babu ka sanar dani zan san yanda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 40