Share this page
hadari dake haɗuwa yana kaɗawa a hankali, zuciyar ta cike fal da farinciki, Kasancewar an fara kiraye kirayen sallar magrib ya sa ko da ta shiga bata tsaya bi takan kayan nata da Hajiya ta sa aka ɗauke aka mayar a wancan ɗaya falon dake gefe ba, kai tsaye upstairs ɗin ta nufa da sauri da sauri ta shige ɗakin ta tare da jefa jikkarta da ledar kayan maƙulashen data shigo dasu akan gado ta faɗa toilet tayo arwala ta fara gabatar da sallar magrib, bayan ta gama ta ɗauko littafin ta na HISNUL-MUSLIM tayi azkar ɗin ta na mare ce, ganin har lokacin ba a kira sallar isha ba ya sa ta sake ɗauko alƙur'anin ta ta shiga karantawa cikin ƙira'arta mai daɗin saurare, bata dai na ba sai da ta jiyo kiran Sallah daga masallatan dake anguwar sannan ta ajiye ta gabatar da sallar ta ta ishah, tana gamawa ta faɗa toilet ta watso ruwa, fitowar ta keda wuya tana tsane jikin ta da towel ta ji wayar ta na ruri, murmushi ta yi bayan ta ɗauko wayar ganin wanda ke kira haɗe da karawa a kunne, ta ce "Hubby barka da dare, ka isa lafiya?" "Lafiya klw ƴan mata na, ya kike?" "Alhamdulillah, yasu momy, Razina da kuma ba ƙi?" "Duk lafiya ƙlw suke duk da dai har yanzu ban ƙara sa gidan ba" "Ina ka tsaya to, nifa bana son kana wahalar mani da kan ka haka" ta ƙare maganar cikin shagwaɓe murya tamkar za tayi kuka, murmushi ya saki da har sai da ta jiyo sautin fitar sa a kunnen ta haɗe da cewa, "Sorry noorul albi na, na koma inda muka je ne na karɓo mana hotunan da muka yo soft copy, yanzu haka ina kan hanyar zuwa gida sai dai an jealous duk kin canye hoton" "Laaa..kodai na ɓata hoton, ni da ko make up babu a fuska ta taya zan canye hoto ga ɗan balarabe na a gefe, kawai kace kana so ka zolaye ni ne, kuma nagode" "Ok, Zaki gani ne da kan ki, ai na turo maki a watsApp, hop kin ci abinci?" "Noo...na bari ne har nayi sallah na watso ruwa, yanzun nan ina gama shirya wa zan sauka naci" "Ok, to bari na barki sai munyi waya" "Okay byebye, ka kula mani da kan ka" "I will in Sha ALLAH" ya faɗa tare da katse kiran yana ƙarawa motar gudu don ya isa gida don har Momy ta kirasa tana faɗa ina yaje yabar mutane su kaɗai, daya tambaye ta ina Jabir yaje sai dai tayi tsaki haɗe da cewa ya dena zancen sa gashi can a kitchen ya yiwa Razina zaune yana zuba mata surutu, shiyasa yake son ya ƙarasawa da sauri kafin ta sake kira, Janan kuwa tana ƙoƙarin buɗe watsApp ɗin ta taji Muryar Abba na ƙwalo mata kira daga downstairs, gaban tane ta ji ya yi wani irin mugun faɗuwa haɗe da zabura lokaci ɗaya har wayar dake hannun ta na rigegeniyar faɗuwa ƙasa ita da towel ɗin dake ɗaure a jikin ta, bata tsaya bi takan su ba ta nufi wadrobe ɗin kayanta ta jawo wata doguwar riga da mayafin ta ta zuba tare da ficewa da sauri, a daidai bakin hawa upstairs ɗin ta tadda shi lokacin data sauka fuskar nan tasa ba ɗigon annuri ko ɗaya akai, tana ƙoƙarin duƙawa ta gaishe sa ya wuce wancan ɗayan falon, hakan ya sa tabi bayan sa itama cike da fargabar abun da ke shirin faruwa, cike da muryar takai ci da kuma ɓacin rai taji Abban na faɗin, "Look at this Janan, dubi abun kunyar da kika jawo mun, in whole me ace ƴatah aka kawowa waɗan nan ƙazaman kayan? A very shameless to you and me, Ni na rasa me kika gani ga wannan yaron da kika na ce wa rayuwar ki sai shi, look..look at this Janan" ya ƙare zancen yana shusshura kayan da ƙafa, kasa cewa komai tayi sai bin kayan da idanuwa da tayi, dariya ke son kucce mata amma ba halin yi saboda yanda Abba ke bayyanar da ɓaci ransa ƙarara akan su, tsaki Abba ya sake yi a karo na ba adadi tare da duƙowa inda take zuƙun ne ya riƙo kafaɗun ta yana bin cikin ƙwayar idanuwan ta da kallo, "Janan, ki dawo hayyacin ki ki fahimci fatar da nake son yi maki, wannan yaron da kike gani sam ba sa'ar shi bace ke, bazai iya kula mani dake kamar yanda na kula dake ba har kika girma haka, amma Asgar zaki samu duk wata gata da tarairaya a wajen sa fiye da yanda kike tunani" "Banda farinciki Abba domin zuciyata ba shi take so ba, ALLAH ma ya sani bazan ji daɗin da kake so naji ba matuƙar aka aura mani shi, Muhriz kuwa zai bani dukkanin gatar da kake mafarkin na samu Abba, zai kula maka dani fiye da tunanin ka" Sake hamɓara akwatin kayan dake gefen sa ya sake yi cikin ɓacin rai haɗe da miƙewa sannan ya ce, "Ƙaniyar gatan da zai baki Janan, wace irin gata kike tunanin samu ga wanda ya kasa fidda ke da kuma mahaifinki kunya?, Da ace manyan abokanan kasuwanci na ne suka yi arba da wuɗan nan kayan ɗazu da bansan inda zan saka kaina ba, a hakan ma ba ƙaramin kunyata nayi agaban idanuwan su ba" sake da wowa yayi agaban ta yana nuna ta da yatsa sannan ya ci gaba da cewa "Look Janan, Bazan iya wannan abun kunyar, wether you like or not dole yaron nan ya bar ki..." Kafin ya rufe baki Janan ta shiga girgiza kai ganin yanda yake maganar da gaske da gaske hawaye na zubo mata a fuska haɗe da cewa "A'a Abba kada kayi haka, wlh shine zaɓina" "Zaɓi yaci ƙabilar sa Janan, will you keep quiet?" Ya fada cikintsawa haɗe da ɗaga hannu kamar zai daketa, wani irin kuka ta fashe dashi tare da faɗuwa ƙasa dir shan tana faɗin, "Wlh Abba ni shi nake so, kuma ko kashe ni za a yi bazan taɓa yadda na auri Asgar ba.." bata rufe baki ba ta ji ya ɗauke ta da wasu zafafan marora har guda biyu tare da nuna ta da yatsa, ya ce "Idan ba kya cikin hayyacin ki wannan zai maido dake cikin sa, idan kuma kina cikin hayya cin naki to ina so ki sani ko mutuwa zakiyi bazan taɓa bari ki aure sa ba" Shura ƙafafuwa ta shiga yi tana sake ɓare baki tamkar wata ƙaramar yarinya, tsaki Nihal dake zaune gefe kan kujera tana latsar wayar ta tayi haɗe da cewa, "Pls Abba let her be, ai rayuwar tace kuma tun yanzu ta fara ganin bugun lamba, ya riga daya gama da ita ta yanda baza ta taɓa sauraren kowa ba, ka ƙyaleta, nasan dole nan gaba tayi nadamar auren sa idan ya wulaƙan ta ta haɗe da saka ta a kunyar da sai ta fimu dana sani, a wannan lokacin hankalin ta zai dawo kanta ta fahimci ko me ake nufi kuma ake gudar mata, mutum sai kace mayen ƙarfe?, Wlh Abba ɗazu ji nayi tamkar na nitse ƙasa da naga kayan nan, saboda ko mai aikin Hajiya aka yiwa kyautar su ina da tabbacin sai dai ta kaiwa ƴan uwan ta na ƙauye su, amma ace kamar kai billonaira za a kawowa ƴarka su, wlht is a biggest shameless thing to you Abba, kuma duk ita ta jawo maka, laifin tane" ta ƙare zancen tana nuna Janan da yatsa, "Very good sweetheart, that's exactly what i wanted her to understand" "She won't Abba, just let her be" ta faɗa cikin haushi tare da maida earpiece ɗin ta a kunne tana ci gaba da sauraren waƙar taf, Rafke hannaye baya Abba ya yi haɗe dayin ajiyar zuciya yana zagayar ɗakin kafin can ya nemi waje ya zauna yana kallon Janan, Sinne kai tayi ƙasa hawaye na saukar mata a idanuwa haɗe da cewa, "Pls Abba...." Kafin ta ƙara sa ya ɗaga mata hannu haɗe da cewa, "Shikenan kije na amince zan aura maki shi, amma ina so kafin nan duk abunda kika san ni na saya maki shi ka ma daga kan sutura har zuwa sauran kayayyakin dake sake alfaharin jin cewa ke ƴatah ce ki ajiye su, ki je duk inda ki ke so a faɗin duniyar nan zan ɗaura maki aure da wanda ki ke so, amma kibar mani gida na kuma kada ki sake tako ƙafar ki aciki, ki manta cewa kina da wani uban a duniya don daga yau ba ni ba ke har abada, kuma kada ka ki kuskura ki taka ƙafar ki gidan mahaifiya ta, idan kuma kika yi hakan ban yefe maki ba" yana gama faɗar hakan ya miƙe zai bar falon tayi saurin riƙe ƙafafuwan sa haɗe da fashewa da wani irin kuka tana faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, don ALLAH Abba kayi haƙuri, bazan iya jurewa rayuwa babu ku ba Abba, na rasa mahaifiyata tun ina cikin tsumma, kada kace zaka rabani daku bayan na rayu tare daku, bazan iya ba Abba don ALLAH kayi haƙuri, i know Muhriz will be the right man that you wanted me to marry" Banza ya yi da ita haɗe da ci gaba da tafiyar sa tana riƙe da ƙafafuwan nasa tana kuka har suka isa bakin ƙofar sashen sa, cike da rashin tausayi ya sa ƙafa ya hamɓare ta ya shige tare da banko ƙofar da ƙarfi, ba don tayi saurin janye hannun ta ba da ƙofar ta datse ta, Ta sowa Nihal tayi daga inda take ta isko Janan haɗe da duƙawa kusa da ita tasa tafin hannayen ta akan fuskar ta ta goge mata hawayen dake kwance akai sannan ta ce, "It's over Janany sister, meye na kuka kuma?, Ina kin samu wanda kike so kuma kike mafarkin aure, to meye na kuka? Meye na damuwa?, Ba kece sarkin so ba?, Da anyi magana sai kice so..so.so kina son sa?, Idan har da gaske kina son nasa kuma kin tabbata zai iya share maki wuɗan nan hawayen fine, sai ki je abunki, Abba dai bazai yarda ya sayar da akuyar sa ba ta dawo tana ci masa danga" ta ƙare zancen tare da miƙewa tana yimata wani banzar kallo sannan ta bar wajen, cak Janan ta ji hawayen idanuwan ta sun tsaya tana ƙara mamakin ƴar uwar tata, ko da yake izuwa yanzu ya kamata ace ta dena mamakin duk abun da za tayi don time ya riga da ya yi revealing kansa tsakanin ta da ita, wani irin ƙwarin guiwa ta ji ta samu na nesan ta kanta dasu fiye data zautna tare dasu suna ci tgaba da ƙuntata rayuwar ta da bata san lokacin da zata samu sauyi agunsu ba, ƙwanda taje ta rayu da masoyin ta in yaso komai zai biyo baya tasan a ƙarƙashin ibadar aure ne kuma zata samu lada, Miƙe wa tayi jiki ba ƙwari ta nufi upstairs ɗin, yayin da shi kuma Abba na shiga ya kira su Alhaji Sadeeq ya sanar dasu yanda suka yi da Janan har yake sanar masu da cewa gata can tana kuka, da alama zata haƙora da yaron, dariya Alhaji Sadeeq ya yi haɗe da cewa, "Yaro man kaza, ai na faɗa maka kana cewa hakan zata haƙura" ashe dama su suka ɗora Abba akan wannan shawarar, da yake shi kuma hankali ya yimasa yawa sai kuma ya yarda, Tana shiga ɗakin ta ta nufi wajen credentials ɗin ta da niyar ɗauke duk wani abu nata masu muhimmanci amma ga mamakin ta babu komai a wajen, cikin ruɗewa ta nufi inda system ɗin ta ke ajiye, nan ma aka ce ɗauki inda kika ajiye, ƙarar shigowa messages da ta ji na shigowa ajere a jere ya sa ta shiga lalabar wayar ta dake ƙasa towel ya rufeta, tana dubawa alart ne daga account ɗin bankunan da take amfani dasu gaba ɗaya a cire kuɗaɗen dake ciki, ba tare data damu ba ta miƙe ta shiga duba gefen madubi inda ta ajiye a.t.m ɗin ta da mm ya bata ranar, nan ma ba komai, hakan ya tabbatar mata da cewa already Abba ya riga ya kwashe komai, da ma kuwa haka ne don tun da rana kafin ya dawo ya sa Nihal ta shiga ɗakin ta ta kwaso mashi duk abunda tasan mai mahimmanci ne kuma zai iya amfanar Janan idan ya barta dashi, Runtse idanuwa tayi wasu hawaye na sake zubo mata a fuska ta juya tana kallon ɗakin hawaye na sake zubo mata a fuska, a hankali ta tako inda Hisnul muslim ɗin ta ke ajiye ta ɗauka tare da alƙur'anin ta sannan ta zira hijabin da take Sallah dashi ta ɗauko wayar ta ta baro ɗakin tana jin wani irin kuka na sake taso mata, a hankali take saukowa daga kan upstairs ɗin don ko gani bata yi da kyau saboda tsabar baƙin ciki, tana ƙarasa saukowa Abba dake tsaye ya yi folding hannayen sa yana kallon ta cike da mamaki don baiyi tsammanin zata iya tafiya ba ya ce, "Suma waɗan nan da kuɗina aka siya, matuƙar kin amince zaki tafi dole zaki bar su anan" tasan me yake nufi don haka ta je ta miƙa masa wayar tare da alƙur'anin da kuma Hisnul Muslim ɗin tana kallon sa, kauda kai ya yi gefe haɗe da cewa Nihal dake tsaye gefen sa tayi folding hannayen ta itama ta karɓi kayan, Sai alokacin ta ɗan ji tausayin ta kaɗan, amma duk da haka hakan bai hanata karɓar kayan ba, Janan na kuka ta fice da gudu tana share ƙwalla, me tayi wa Abban ta haka ya tsaneta da yawa, me yasa ƴar uwar ta zata juya mata baya ta guje ta, wai duk suna hakan ne saboda dukiya?, Dukiyar da idan antara baza a je lahira da ita ba dole a barta?, Wannan wace irin rayuwa ce a duniya mai cike da ruɗi da kuma son kai, ta tambayi kanta? Madam florence ce da tun ɗazu ke saurarar abunda ke faruwa tafito da sauri tana kuka itama cike da tausayin Janan ta zube gaban Abba tana faɗin, "H, Alhaji I beg you, I beg you in the name of God don't throw her out, she's your blood, your daughter Alhaji, why are you doing this to her, pls Alhaji for the sake of God forgive her" juyawa kawai ya yi ba tare daya ce mata komai ba yabar wajen, cikin ruɗewa da tashin hankali irin na inyamurai ta aza hannuwa saman kai tana faɗin, "Oh my God, I won't allow this to happen over my died body, forgive me Alhaji, me i will follow her, I will not allow her to go on her own, I won't do that Alhaji I beg forgive me ooo." Ta ƙare zancen tare da ficewa tana kuka......... _Mtsss...😏😏😏Janan kina da matsala kema, kin cika kafiya na miji ba uba bafa, ba kuma ɗan goyo ba, i can't leave my family, my properties b'cos of him_🚶🚶 *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/23, 7:19 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 58_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ********** _https://www.wattpad.com/1261231293?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=gCATJPA%2F5dL3ZYAeLOA7cBYWm6EjeVBcTz5pTKK2ISf4ww%2BpzixiJtrqLwcIEGFgTM7Y%2BYkM7XOE0m7QohJV6%2B%2BFGiDWVQFCMtp7WZ4Vz0%2BtG97OJhnXEFxvx4YH%2Bdcw_ ________________________________ Wayar Janan ce dake hannun Nihal ta fara ruri, ba tare data damu da ƙarar da take yi ba ta nufi ɗakin Abba riƙe dasu, zaune ta isko sa ƙafarsa ɗaya akan ɗaya yana amsa waya hankali kwance tamkar wani abu bai faru ba, saman Centre table ɗin dake tsakiyar falon ta ajiye alƙur'anin da wayar tana faɗin, "Abba meyasa baza ka bar mata wayar ba?" Sai daya janye wayar sa daga kunne da yake amsawa sannan ya ce, "Saboda da kuɗina itama aka siya" "So i can't keep it with me Abba saboda bana son damuwa, gashi har an fara kiranta, so just keep it with you" ta ƙare zancen tare da juyawa tabar ɗakin, tana barin wajen wayar ta sake ɗaukar ƙara, wannan karon mm ne ya kira yana so ya ce ta hau za suyi magana a watsApp, har ta aza ƙafar ta bakin ƙofa zata fita taji Abba ya kirata cikin ɗaya murya don har lokacin bai gama wayar da yake yi ba, dawowa tayi ya nuna wayar Janan ɗin dake ƙara da hannu, tana miƙa hannu da niyar ɗauka kiran ya katse, sake jaye wayar sa ya yi daga kunnen sa akaro na biyu haɗe da cewa, "Switche off the phone" sannan ya ci gaba da wayar sa, Tana ƙoƙarin kashe wayar saƙon message ya shigo ta watsApp da lambar mm da Janan tayi saving da *Hubbin ruh*, har ta kai hannu zata buɗe saƙon ganin kamar hotuna ne ke shigowa da sauri da sauri, wani bayan wani sai kawai taji wayar ta ta hau ruri, ɗan tsaki ta ja tare da danne power ɗin wayar ta kashe gaba ɗaya ta ajiye haɗe da ɗaga kiran nata da akayi sannan ta bar ɗakin. Wani irin tsaki Hajiya dake faman sake trying number Janan ta ja, don kiranta ne ya fara shigowa a wayar ta Janan ɗazun tana so tace mata kada taje ko ina ta jira har ta ƙara so, jin an kashe wayar gaba ɗaya ya sa ta juya gata Madam florence ta kirata itama don ita ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki, ganin bata ɗaga ba ya sa cikin tashin hankali ta kalli Ado dake driven ɗin ta cikin mota ta ce, "Wai ya akayi ne Ado? Nifa gani nakeyi kamar ba tafiya muke yi ba, gaba ɗaya kaƙi sauri balle mu samu mu isa gidan can kafin yarinyar nan ta bar shi" "Wa kenan Hajiya?" "ALLAH ya raba ka da wahala Ado, shin kana ƙara gudun ko kuwa?" Ta ƙare zancen cike da zaƙuwa su isa gidan, kafin kace me tuni Ado ya iso ƙofar gidan su Janan, suna kawowa Janan na fitowa madam Florence na faman riƙe ta ta tsaya amma ta ƙi, ko dai-dai ta parking ɗin motar Ado bai gama yi ba Hajiya ta buɗe tafito jikin ta na wani irin tsima da kaɗan ma ta faɗi, duk da dare ne hasken wutar lantarkin dake zagaye da gidan na Abba gaba ɗaya ya haskaka ciki da zagayen sa, hakan ya bawa Hajiya damar hango yanda Madam florence ta zube guiwowin ta ƙasa data hangota haɗe da ɗaga hannuwa sama tana faɗin, "Thank you Lord, thank you kaka you are here, I love you God thank you so much" Ba tare da Hajiya tabi takan Madam florence ba ta nufi Janan da ta sa kai tana faman tafiya ba tare da tasan ma inda take aza ƙafafuwanta, sau kusan ukku kaka na kiran sunan ta amma bata ji ba don bata masan ta iso wajen ba, da sauri kaka ta sake ɗaga ƙafa tare da kamo hannun ta, a tsammanin ta Madam florence ce don haka sai ta tirje tana ƙoƙarin ci gaba da tafiyar ta, "Janan, kallo ni nan babu inda zaki je, kiyi haƙuri ki zo mu koma ciki idan ya haife ki shima haihuwar sa nayi" wata irin juyowa tayi jin Muryar Hajiya da ba tayi tsammanin gani a lokacin ba, wasu hawaye taji sun sake zo mata da sauri ta faɗa jikin Hajiya haɗe da rungumeta tana sake fashewa da wani kukan haɗe da cewa, "Hajiya Abba ya kore ni agidan sa, anya kuwa ni jinin sa ce?" "Tsaf ke jinin sace shiyasa dake har shi kuke wahala, saboda kinyi gadon sa da lafiya da kuma taurin kai irin nasa, ko anan kaɗai aka tsaya kin tabbata jinin sa, wannan wane irin tashin hankali ne haka cikin dare, to bai isa ba ya sha ƙarya wallahi" ta ƙare zancen tare da jan hannun ta ta nufi cikin gidan da ita, suna shiga Abba na fitowa sashen sa riƙe da makullin mota, yana buɗe baki zai yi magana ganin Hajiya ta ɗauke sa mari, kafin ya sake dawowa hayyacin sa ta sake ɗauke sa wani marin, haka tasa hannu bibbiyu tana marin fuskarsa tako ina haɗe da fashewa da kuka, ganin haka yasa Madam florence ta ja hannun Janan tayi can baya da ita inda wajen kwanan su yake, Hajiya kuwa bata dena marin Abba a fuska ba har saida ya durƙusa agaban ta, cikin kuka ta ce, "Kaico ni kaico rayuwata da wannan jarabawa da ALLAH ya yi mani, ina ma Jamalu na raye ya gyara kuskuren da ya yita ƙoƙarin nuna mani ina aikatawa akan ka na kasa ganewa, ina ma za a koma baya dana yakuce ka azuciya ta na tsaya na baka tarbiya kamar yanda na bawa ɗan uwan ka, istigfarullah ALLAH ka yafe mani na tuba, haƙiƙa yau tarihi keta maimaita kansa akaina bisa fifikon dana nuna tsakanin ƴaƴana, ashe ban sani ba ranar nadama na nan tafe gareni, yau ɗan dana haifa, na nunawa so fiye da ƴaƴan da na haifa shine nake bawa umurni yake ƙin yi, shine ke sakani zudda hawaye tare da hanani zama lafiya, ALLAH na tuba ka yafe mani" ta sake fashewa da wani kukan tunawa da yanda tayi ta nuna banbanci tsakanin mahaifin Jabir da kuma Abba, ta kuma nuna fifikon soyayyar Abba akan ta mahaifin Jabir ƙarara, wanda hakan ne ya sashi zuwa kudu nema har ya haɗu da Momy ya aurota, dukkanin kuskuren da Abba keyi yanzu tsakanin Nihal da Janan irin sa ta aikata tsakanin shi da mahaifin Jabir, banbancin kawai shine ita ba tada dalili ko hujjar aikata hakan in ba ɗabiar da hausawan mu da Fulani keyi ta nuna rashin kulawa ga ɗan farin, bayan haka kuma sai ALLAH yasa ya mata jarabawar son Abba fiye da dukkanin ƴaƴan data haifa a duniya, duk da dai duka rasuwa suke yi Abba da mahaifin na Jabir ne kaɗai suka tsaya, ji Abba ya yi gaba ɗaya jikin sa ya mutu kukan da yaga Hajiya nayi wanda hakan yasa ya kasa cewa uffan agaban ta, share hawaye tayi sannan taci gaba da cewa, "Usman haƙiƙa na soka so mai yawa acikin ƴaƴana wanda ayanzu nake dana sanin yi maka shi tunda har kake nuna cewa ban isa gare ka ba, amma bari in faɗa maka wani abu, daga yau na cire wannan son kuma na ire duk wani tausayi dake tsakanina dakai kamar yanda kayiwa ƴarka Janan, ina so ka sani babu inda Janan zata je, kai ne uban ta kuma tana da haƙƙi akan ka, kana so ko baka so ya zama tilas a ka aura mata wanda take so, sannan batun ta ajiye maka duk abunda tasan kai ka siya da kuɗin ka ne shima ya zama dole ka janye don ba ita ta haifi kanta ba haihuwar ta kayi dole ka kula da wannan, magana ta gaba ina so kasani ban yafe maka ba idan kaci gaba da fushi da ita ko kuma ƙuntata mata da wata ɓaƙar magana ko wani abu daban har zuwa lokacin da za'a ɗauka wannan auren agama, sannan tunda abun naka na gori ne dama tuntuni da naga jikana nake son sanar da kai cewa ka haɗa duk abunda kasan na Jamal ne acikin dukiyar nan abawa ɗan sa haƙin sa, kai kuma kariƙe taka" wani irin fizgo kai Abba ya yi cikin tashin hankali yana kallon Hajiya jin abunda ta faɗa, taya zata yanke wannan hukuncin bayan tasan hakan ba abubane mai yiyuwa, Ya faɗa cikin zuciyar sa haɗe dasa hannu ya goge zufan daya tsattsafo masa a goshi, "Kiyi haƙuri Hajiya..." Tayi saurin dakatar dashi kafin yaƙarasa faɗa, haɗe da miƙewa tana kallon kayan dasu Baffa suka kawo da Abba ya shusshure ɗazu, Madam florence ta ƙwalawa kira ta fito da sauri tana ƙoƙarin duƙawa a gaban ta ta dakatar da ita haɗe da cewa, "Ɗauke akwatunan nan ki kai man su part ɗin Hajiya Zainab, daga nan ki kira mani Ado ya kwashe sauran yakai can, ina Janan ɗin take?" Madam florence ta koma ta kirawo ta sannan ta ɗauki akwatunan ta nufi part ɗin Hajiya Zainab dasu, "Ke kuma abunda zan faɗa maki duk abunda mahaifin ki zai yi maki kiyi haƙuri, kiyi haƙuri kiyi masa biyayya dai-dai gwargwado tunda hannunka bazai ruɓe ba ka yanke, sannan ina kika bar wayar ne nayi ta kiran ki a kashe, daga farko ma ta shiga daga baya ne aka kashe, kuma na tabbata kinga kiran nawa amma kika ƙi ɗagawa ke mai zuciya wato har ni fushin

Chapter 35 of 40