damuwar ki na magance maki ita yanzu, domin yau ranar mu ce, bai kamata duk wani ɓacin rai ko ƙunci da kuma hawaye su raɓe mu ba, faɗamun my luv, meye damuwar ki?" Cikin kuka ta ɗago kai tana kallonsa idanuwanta cikin nasa, ta ce
"Kai ne damuwata"
#Comment
#Vote
#Share
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 26_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1240398682?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=XUf6U0thucbnMvAx5O3LULkyGkS9C6P%2FVbtkcwUSZ9AIv7qPeMLJaS6zFzWaOqqGn4tZ4PqIhL7Qt%2BXGPCVqEIBULj3t%2BmspEw5zvGuhe0jYJ%2F5E%2ByXStQLSvK6f6GNc_
______________________________
Kallonta yayi irin kallon nan na da gaske kike yi kafin yace "Janan, da gaske kike yi ni ne damuwar ki?" Ta jinjina mashi kai tana share hawayen da suka miƙa mata fuska da bayan hannu haɗe da cewa.
"Yes upcouse kai ne"
"Ok come, let talk between me and you now, idan wani matsala ne sai muyi solving ɗin ta tun yanzu" ya ƙare maganar tare da miƙo mata hannu, hannun ta kalla haɗe da banka masa harara sannan ta kauda kai gefe tana folding hannayenta akan ƙirji, ganin haka yasa ya fahimci me take nufi don haka kawai sai ya nuna mata hanya tare da wucewa gaba suka nufi can gefen da babu mutane sosai,
Saida ya sauke ajiyar zuciya bayan ya naɗa hannayensa shima ya ɗora akan ƙirjin sannan ya ce,
"Now tell me, meye na miki da har ya sakaki kuka ko nace ya haifar maki da damuwa?" Cikin natsuwa da tauna duk wata magana da zata furta ta ce,
"Am sorry yaya asgar for what am going to tell you, sincerely ni ina da wanda ke sona kuma nima nake son sa, shiyasa yanzu da mahaifina ke sanar mun cewa kai ne wanda ya zaɓamun na aura na shiga damuwa da tashin hankali, saboda bansan yanda zan iya rayuwa da wani namijin da bashi ba, amma kayi haƙuri bawai don bana so ka ba, ko ba komai ni dakai duka 'yan uwane kaga kuwa bazan ƙika ba, matsalar kawai shine nariga dana bawa wancan gaba ɗaya ragamar rayuwata" ba tare da ya damu da girman kalaman da suka fito abakin ta ba ya ce,
"And so what Janan, Ina dai bakya ƙi na tunda har kika ce mun zama 'yan uwa, and i know ɗan uwa bazai ƙi ɗan uwansa ba ko?, Don haka ni ban damu da kina son wani a zuciyar ki ba, haka nake son ki kuma zan iya auren ki a haka, with time nasan nima zuciyar ki zata koyi sona a hankali, zancen kuma wai wani na son ki, left to him, ya rage nasa ya haƙura dake ya hutawa kansa, idan kuma yaƙi shima ya rage nasa don shine da rashi bani ba, ina fatar kin fahimta kuma zaki janye wannan damuwar a ranki don kada tahana mana farinciki da walwala"
Kusan mutuwar tsaye Janan tayi jin kalaman dake fitowa daga bakin asgar, cikin ɓacin rai take ƙare masa kallo haɗe da cewa,
"Kada ka yaudari kanka yaya asgar domin zuciyata yare ɗaya take ji kuma take fahimta, a shawarce zaifi kyau ka tattara inaka inaka ka koma inda ka fito kuma ka shedawa iyayen mu cewa ni bana son ka, don haka su nema maka wacce ta dace dakai kuma daidai kai" Tana gama faɗar haka ta juya tabar wajen ranta a ɓace, saurin shan gaban ta yayi tare da haɗe hannayen sa waje ɗaya idanuwan sa a kanta ya ce,
"Pls Janan, ki tsaya mu fahimci juna, wlh komai zai faru bazan iya haƙura dake ba don haka ƙara ma ki tsaya mu walwale wannan damuwar da kanmu" wani irin kallon banza ta watsa masa haɗe dayin tsaki ta raɓa ta gefensa zata wuce kawai ta ji ya kamo hannunta ya maido da ita a gabansa, buɗar bakinsa keda wuya da zimmar yi mata magana yaji ta ɗauke sa mari,
"How dare you zaka riƙamun hannu? Ka ɗauka ni irin 'yan matan ƙasar ka ne da
suka saba zubarwa da kansu mutunci a wajenki, wannan shine banbancin dake tsakanin ka da zaɓin dana yiwa kaina da kuma kai da ake ƙoƙarin zaɓamun, a zahiri ma sam bamu dace ba" tana rufe baki itama taji saukar mari a fuskarta, kafin tace wani abun ta sake ji an ɗauketa da wani marin, mahaifin tane ta gani a tsaye cikin ɓacin rai ya sauke mata waɗan nan maroran da suka kusa gigita mata ƙwaƙwalwa, wani irin kuma ta fashe dashi tare da juyawa tabar wajen aguje, cikin ɗaga murya ya ce,
"Kisa aranki wannan shine mijinki nan da wata uku kokina so ko bakya so, shashar yarinya kawai" sannan ya juyo yana kallon asgar haɗe da cewa,
"Am sorry my son, Zan hukuntata daidai da laifinta pls ambassador ayi haƙuri.."
"No dad, ka ƙyaleta yarinya ce, nasan zata dena nan gaba" asgar ya faɗa yana murmushi don shi sam baiji zafin marin ba saima ƙara son ta da ya ji ya yi a cikin zuciyar sa, shi kuwa ambassador Hussain cikin sakin fuska haɗe da nuna halin ko in kula akan abinda Janan ta yiwa ɗan sa ya kamo hannun Abba yana faɗin,
"Kaima dai meye naka, banda abunka mita kaika shiga sha'anin yaran, musamman da kasan Janan ba son abun nan takeyi ba sai an lallaɓata, and i know my son is willing to do so, a shirye yake da facing ɗin duk wasu challenges da zata zo masa dasu saboda he's madly loving her, kasan yaran zamanin" suka kwashe da dariya tare da tafewa kafin Abba yace,
"I know who's Janan ambassador shiyasa kaga nayi mata hakan, yanzu badon ALLAH ya taimaka baƙin mu sun wuce ba shikenan ta kunyata mu agaban su?"
"Ƙurciya ce Alhaji, kuma nasan zata dena, duk wannan abun da takeyi saboda yaron ya riga ya hure mata kunne ne, amma da sannu yarona zai janyo hankalin ta garesa"
"I hop so! Kuma ina idan har hakane ya kamata mu jawo bukin nan in the next 2month instead of 3month, to avoid many problems dake iya ɓullowa daga gareta, nasan zuwa lokacin everything will be right kuma ta gama final exam ɗin ta"
"Ok hakan yayi, thank you so much, amma fa ga dukkan alamu dole sai kasa mata tsaro yanzu saboda kada taje ta riƙa haɗuwa da wancan yaron, kasan ko guduwa yana iya sawa tayi"
"Haka ne ambassador, amma fa badai 'yatah ba, dole tabi abinda nake so kuma tayi yanda nake so, amma duk da hakan zanyi yanda kace"
"Yawwa, yanzu naji zance don zamani ya riga ya canja" haka suka ci gaba da tattaunawa akan yanda bukin zai kasance don dama tuni baƙin amma daya tara duk sun wuce kasancewar marece yayi gashi dama sun daɗe suna jira kafin isowar Janan, shiyasa yana gama gabatar masu da ita tare da maƙasudin haɗa taron duk suka wuce suna masu taya aminan biyu dake ƙoƙarin ƙarfafa zumuncin su ta hanyar haɗa 'ya'yan su aure murna.
Janan kuwa tana shiga ta kulle kanta cikin ɗakin tana kuka, ji takeyi ko zata rasa ranta bazata taɓa amincewa da zaɓin mahaifinta ba haka kuma bazata taɓa yarda tana ji tana gani a aura mata wancan mai ƙirar samudawan ba dako rantsuwa tayi baza tayi kaffara ba bayada banbanci da bunsuru,
Tana kukan mm ya kira wayar ta har kusan sau biyu ba'a ɗaga ba sai ana ukun ta ɗaga,
"Nurul alb, ya kk?"
"Lafiya klw hubbin ruh" ta faɗa cikin muryar kuka, miƙewa yayi daga kwancen da yake haɗe da cewa,
"Matata lafiya?, Waya taɓa mun ke?, Me yasa ki kuka?, Ko wani abune ya faru?"
"Wlh mutuwa zanyi mm, bazan iya rayuwa a bayan wani ba idan ba kai ba, ni dai pls koma ya za'ayi don ALLAH kafito a ɗauka mana aure"
"Ban fahimta ba Janan, ki tsaida wannan kukan naki kiyimun bayanin meka faruwa?"
"Abbana ya kawomun wani na aura, sune baƙin da akayi agidanmu, yanzu haka zancen da nake yimaka ya bada aurena ga ɗan amininsa, ina nufin yayi mana baiko bada sani na ba balle amincewata ba, kuma ni kai kaɗai nake so, kai kaɗai nake mafarkin goya ɗanka aduniya ta, idan ba haka ba wlh zan iya rasa rayuwata" duk da hankalin mm ya matuƙar tashi dajin abunda ke faruwa haka ya danne yanayin da nan take ya shiga ciki haɗe da cewa,
"Yanzu kina ina?"
"Ina gida"
"Ina Adda Nihal?"
"Tana ƙasa"
"Zaki iya sauka?"
"Eh"
"To share hawayen ki, sauka ƙasa kike ki bata wayar kinji?"
"To" ta faɗa tare da miƙewa ta goge hawayen dake kwance akan fuskarta sannan taje ta wanko fuskarta ta sauka ƙasa, acan gefen dining ta hango Abba zaune shida asgar da kuma mahaifinsa suna taking lunch da hidima da baƙi ta hanasu yi tun ɗazu, juyawa tayi gefe ta hango Nihal ta ɗauko wani tray ɗin abincin daga kitchen zata kaiwa su Abba, da ɗan gudunta ta ƙara sa fuskarta ɗauke da fara'a tamkar ba ita ba tana faɗin,
"Hello hubbin raina"
"Hello matata" ya faɗa cikin sanyin murya don zancen ya taɓasa ba kaɗan ba,
"Ga Adda Nihal" ta karawa Nihal dake kallonta cike da mamaki wayar a kunne,
"Hello.." Nihal ta faɗa haɗe dayiwa Janan signal da idanuwa tana tambayar ta waye, Muryar mahaifin nasu ce ta daki kunnen Nihal adaidai lokacin da mm ke ƙoƙarin yin magana, ba tare data tsaya saurarensa ba tayi saurin wucewa wajen da Abban nasu ke kira,
"Hello..hello.. hello Adda Nihal" da yake ta faman faɗa yasa Janan turo baki haɗe da cewa,
"Sorry hubbin raina, Abba ya kirata"
"Kin san me?"
"No hubbi sai ka faɗa"
"Ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru, in sha ALLAH zan san me zanyi, amma kafin nan kibi komai a hankali, idan mukayi garaje a lamarin shi zaisa Abba yayi komai lokaci ɗaya don tabbatar da cewa mun rabu, amma in kika kwantar da hankalin ki zasu ɗabi lokaci mai tsawo kafin asaka ranar ɗaurin auren, wacce inada tabbacin cewa dani za'a ɗaura"
"Wane irin tabbaci kake dashi a lokacin da zaisa na kwantar da hankali na?"
"Tabbacin so da kuma ƙauna, indai soyayyar da mukewa juna gaskiya ce, to ALLAH zaiyi mana mafita alokacin, amma a yanzu babu abunda zamu iya, ko turo iyayena nayi mahaifinki bazai yarda ya aura mani ke ba"
"To shikenan, gobe zanje gidan grandma ko zamu haɗu acan?"
"Kina buƙatar hakan?"
"Sosai ma, ina so kugaisa da ita daga nan na shaida mata kaine zaɓina"
"Idan Abba ya riga ya faɗa mata zancen mijin daya zaɓa maki kuma fa"
"Nasan bazai faɗa ba don bazata yarda ba har sai da amincewa ta, shiyasa nake so nayi masa rigage"
"To ALLAH yasa nayiwa grandma kar itama ta koroni"
"Ai tunda kayi mani to kasa aranka itama kayi mata"
"Kituromun address ɗin ta, in Sha ALLAH zan zo, amma abunda nake so dake ki kwantar da hankalin ki pls, kin san bana son damuwar ki matata"
"Zanyi hakan wakai masoyina" ta faɗa daidai lokacin da take ƙoƙarin hawa saman tare da ballawa asgar harara dake can gefe tun ɗazu ya kafeta da idanuwa yana kallo ganin yanda take wayar cike da farin ciki da nishaɗi, ganin har lokacin ya kasa ɗauke idanuwansa akanta yasa ta ɗora wayar daidai bakinta haɗe da jan wani dogon kiss tana kallon asgar ɗin ta sakarwa mm a waya sannan ta haye sama abinta tana dariya, ji takeyi tamkar batada wata damuwa don tanada yaƙin akan mm ɗin, sannan tunowa da grandma da tayi ba ƙaramin sama mata kwanciyar hankali da natsuwa abun yayi ba,
Asgar kuwa ture plate ɗin gaban sa yayi rai aɓace ya fice daga gidan, ya so ace wancan zazzafan kiss ɗin data saki washi tayi wa, amma ko tantama bayayi waccan ɗan iskan ne da take iƙirarin tana so ta yiwa shi, kuma koma waye zaiyi maganin sa, su Abba kuwa sunyi busy da firarsu basu san abunda ke faruwa ba sai dai suka ga asgar yabar wajen a ɓace suka bishi da idanuwa, hango Janan na haye upstairs ɗin da ɗan gudu gudu da Abba yayi yasa ran shi ya bashi akwai abunda ta yiwa asgar ɗin, don haka yayi kwafa tare da rayawar kansa cewa zaiyi maganin ta in har bata shiga taitayinta ba.
Mm kuwa wani abu yaji ya tsara masa tun daga ƙasar ƙafafuwan sa har zuwa tsakiyar kansa lokacin da Janan ta sakar masa kiss, wanda hakan yasa yayi saurin katse kiran tare da kwantar da kansa saman kujerar da yake zaune ya lumshe idanuwa, tunani ya shiga yi ta ina zai fara neman auren Janan daga hannun mahaifin ta, matsalar dake nan da tasa ko yana son yin fito na fito a wannan gaɓar bazai iya ba, don samun nagartaccin mutane da zai tura ba tare da an samu matsala ba shine damuwar, a ɗaya ɓangaren zuciyarsa kuwa wata irin ƙaunar Janan ce ke ƙara ruruwa acikin zuciyar sa, da dukkanin ransa yake jinta ba azuciya kaɗai ba kuma ya tabbata idan ya rasata zai iya rasa ransa,
Ina mafita?
Shine tambayar da zuciyarsa ta jefo masa, muryar Razina data shigo falon tana ƙwala masa kira ce tasa shi buɗe idanuwa yana kallonta, ƙirjin sa ne ya sake bugawa tunowa da yayi itama fa auren zatayi, akwai buƙatar bayan shi ta samu wani babban jigo da zai tsaya mata acikin rayuwar aurenta, domin duniya yanzu batada tabbas, duk da yasan bata da wata damuwa da wanda zata aura da kuma mahaifiyarsa, amma dangin sa fa? Dole zasu dawo gareshi komai daren daɗewa kuma idan hakan ya faru to fa babban ƙalubalene arayuwar ta don tabbas zasu tuhumi waye ita da kuma nata dangin?,
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" ya faɗa haɗe da dafe kansa ya duƙar dashi ƙasa.
#Comment
#Vote
#Share
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 27_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1241594347?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=LbkNSq93a4%2FqKT7WcAgw5buJKslmsQs%2BObyPK9nk7oD1l4ae0Ap8C57ICn7cM%2Bcb%2FiG%2BweTpcB3pnFsfC%2F6cAusT73w9cfjc%2Fm7Zya%2FTY71iAdNas6BsOrbLsU0SF0bv_
______________________________
Da sauri Razina dake tsaye tana kallonsa ta ƙaraso wajen tana faɗin,
"Ya mm lafiya?" Ta tambayesa Fuskarta ɗauke da damuwa ganin halin da yake ciki, ɗago kai yayi a hankali shima yana kallonta kafin yayi wani irin ajiyar zuciya haɗe da cewa, "lafiya klw Razina, ya akayi ne?" Sanin da tayi ba lalle ne ko ta matsa masa ya faɗa mata abunda ke samun sa ba yasa itama ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa,
"Kazo inji Momy tana neman ka"
"Ok, he kice gani nan zuwa" ya ƙare zancen haɗe da miƙewa ya shige bedroom ɗin nasu ita kuma ta fita, tana kawowa bakin ƙofa ta hango Jabir na shigowa daga wajen gate, murmushi tayi tana ƙare masa kallo kafin ta nufi wajensa tana wasa da hannayenta tamkar yanda yara keyi, ledar hannunsa daya shigo da ita tamiƙa hannu ta karɓa tana faɗin,
"Oyoyo yaya na sannu da zuwa"
Ƙara faɗaɗa murmushin dake kwance kan fuskarsa yayi haɗe da cewa,
"Yawwa matar, ya kike?"
"Cike da tarin kewarka na wuni, amma ganinka a yanzu yasani tsintar kaina cikin tarin farinciki da kuma kwanciyar hankali" ta ƙare maganar tana tsaresa da wani sihirtaccen kallo haɗe da langaɓar dakai gefe, wani lumshe idanuwa yayi cike da tsokana ya dafe saiti zuciyar sa yana faɗin,
"Wash.." haɗe da ƙoƙarin duƙewa ƙasa, da sauri ta miƙa hannayen ta tana ƙoƙarin riƙosa tare da cewa, "Subhanallahi, hubby lafiya?"
"A a wifey, Ina fa lafiya, don ALLAH yaushe ne auren mu masoyiyata?" Murmushi ta saki tare da miƙewa tsaye cike dajin kunya ta ce,
"Nima kai nake saurare hubby, duk sadda ka tashi a shirye nike nima"
"Yanzu pls" ya faɗa yana marairaice mata murya, zaro idanuwa tayi tana kallon sa kafin tace,
"Hubby yanzu kuma?"
"Eh wifey, Baki ga irin kallon da kikeyi mun bane? Matuƙar zaki ci gaba da yimani irinsa to tabbas bugun numfashi na zai iya tsayawa, musamman idan bakya kusa dani kamar haka" ya ƙare zancen cike da zolaya yana ƙoƙarin aza kansa a saman kafaɗar ta, da sauri ta goce tana turo baki kafin tace "kai ko?" Yanda tayi shima ɗin yayi hadda su maka mata harara, ai kuwa ta dagargaje zata maka masa ledar dake hannunta data karɓa a hannunsa da yake ɗunkunan ta na hijabs ne daya karɓo mata aciki da gudu yabar wajen yana dariya itama ta bisa baya tana dariyar haɗe da cewa, "ALLAH daka tsaya saina maka maka ita a saman ƙaton kannan naka mai kama da nawa"
"Ni ɗin?"
"Eh mana, to meyasa zaka kwaikwaye ni?" ta ƙare maganar tare da maka masa harara, daidai lokacin mm yazo wuce zuwa part ɗin na Momy, ya girgiza kai ganin Jabir ya riƙe kunnuwan sa yana faɗin, "An sorry wifey, never repeat that" har yana ƙoƙarin yin up and down, tsaki ya ja tare da sake girgiza kai akaro na biyu yana kallon Jabir haɗe da cewa,
"Girma ya faɗi, wai yaya ke yiwa ƙanwar sa up and down sekace wasu yara"
"Na dai ji, in hitsari banza ne kaza tayi mugani, malam wannan shi ake kira da salon so in baka sani ba ko wifey?"
Ita dai Razina sinne kanta tayi tana dariya ƙasa ƙasa, indai ya mm ne babu randa zai dena tsokanar Jabir da ire-iren wannan zancen, shi kuma bakinsa bazai mutu ba wajen mayar masa da raddi sai kace wasu abokanan wasa, mm kuwa dariya ce taso kucce masa da sauri ya ƙarasa daga ciki, har ga ALLAH yana matuƙar jin daɗin yanda Jabir ke tafiyar da rayuwar sa ga 'yar uwarsa, gaba ɗaya ya maida shekarunsa daidai nata sai faman biyewa shirmen ta yakeyi wanda ya tabbatar da hakan ba ƙaramin taimakawa rayuwar su zaiyi ba idan sunyi aure.
Da sallama ya shiga falon Momy na zaune saye da glasses a fuskarta tana karanta jarida, sai da ta amsa sallamar sannan ta ajiye jaridar agefe tare da ɗago kai tana kallonsa, cike da zolaya irin wacce ke tsakanin uwa da ɗa ta ce,
"Mai dabino, akwai dabino, abani dabino?" Dariyar daya ƙunmshi da Jabir ya sakasa ce tayi saurin kucce masa abaki haɗe da kallon Momy ya ce,
"Kai Momy har dake?"
"Eh mana, Muhammad muhriz mai debino abani debino na nera dari" ta sake faɗa cikin gwarancin hausar ta da bata ida zaunawa a bakinta ba har yanzu, wata irin dariya ya sake saki data bayyanar masa da duka tsantsar kyan da ALLAH yayi masa haɗe da cewa,
"To shikenan, Inaga dai wannan sana'ar bazan barta ba tunda kema kina so.." tun kafin ya ƙara da ta ce,
"No..in dai sakaci gaba da irin wahalar da kukayi a kwanakin baya bana so kabar ta, i prepare ko bama da kuɗin ne naci gaba da sana'ar abinci na akan na riƙa ganin ku kuna yawo da baron dabino, i hate that totally, wannan ma da kukayi da tunfarko kayi shawara dani bazan barka ba gaskiya, nabar ku kunci gaba dayi ne kawai don naga kana so, so let forget about it now, how are you being?"
"Am little fine Momy?"
"What's wrong with you" ta faɗa tare da cire glasses ɗin idanuwanta, sai da ya ɗan sosa kai kafin nan ya shiga bata labarin abunda ke faruwa tsakanin sa da Janan da kuma zancen yaɗata aure da Abban ta keyi da wani ba tare daya ɓoye mata komai ba, ɗan ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama sauraren sa haɗe da kallon sa ta ce,
"Who's her father?"
"Alhaji Usman sahabi maifata"
"What?" Momy ta faɗa haɗe da miƙewa cike da mamaki tana jinjina kai, tafi mintuna uku a haka kafin tafara safa da marwa a tsakiyar ɗakin tana jinjina maganar,
"Momy what?"
"Nothing my soon, but ka tabbata wannan yarinyar 'yar gidan Alhaji Usman mai fata ce?"
"Upcouse Momy, any problem with her"
"No.." ta faɗa tare da zaunawa kusa dashi sannan taci gaba da cewa,
"Sincirely i don no the girl, but I know her father, and if it's possible karabu da yarinyar sa kawai saboda na tabbata bazai taɓa baka aurenta ba"
"Momy why are you saying that?, I already knows his problem and i willing to change him by marrying his doughter, nasan matsalarsa bai fi talaka da baya so ba ya kuma tsani su ra ɓesa, so tunda 'yar sa na sona nasan no matter how zamu auri juna da ita kuma a irin fuskar da naje masa da ita saboda na koya masa hankalin cewa shi talaka nada daraja kuma yana da rana, sannan na nuna masa cewa talaka ma mutum ne kuma zai iya samun duk wani abu da mai kuɗi ke tunanin samu aduniya idan ALLAH yaso da hakan"
"Muhriz, you know Alhaji Mai fata, but you don't rilly know who is he!"
"Pls Momy, kin san wani abune akan sa bayan wannan, ki faɗa mun saboda na ƙara shiga damuwa da tashin hankali"
"Ok relax my son!, Alhaji Usman sahabi Mai fata, ƙanan mahaifin Jabir ne, i mean uncle ɗin sa ne, idan baka manta ba na faɗa maka dangin mahaifin Jabir nada tarin arziƙi, wanda hakan ne yasa basu taɓa tada kai suka kalli ɗan abunda Jamal mahaifin Jabir ya bar mana ba, mutunene masu tsananin son kansu da yawa shiyasa suka sanya katanga tsakanina dasu saboda suna ganin akwai banbancin addinin da kuma yare tsakanin mu duk dako na musulunta, Alhaji Usman na daga cikin waɗanda suka koreni suka wulaƙanta ni tare da nuna ƙyama agareni, a lokacin mahaifiyar su tayi ƙoƙari wajen ganin sun barmu mun rayu tare dasu ko don Jabir da yake gudana jininsu amma suka kafe kai da fata akan hakan bazata yuyu ba, taso na bar mata Jabir alokacin sai ni kuma baƙi yarda da hakan, wannan dalilin ya hasala ta itama tafita rayuwar mu gaba ɗaya" cike da al'ajabi da kuma matsananciyar faɗuwar gaba mm ya ce,
"Momy kar dai kice shine wanda kika bani labarin yana wulaƙan taku alokacin idan kun je gidan sa"
"Yes upcouse shine, Finally ma ya ba security ɗin gidan sa dana mahaifiyar tasu umurnin aduk lokacin da suka ganni naje gidan to suyi mun duka kuma su kore ni, hakan yasa na nisanta kaina dasu kamar yanda suke buƙata don kar wani abu ya sami yarona, to be sincire shi mutum ne mai taurin kai da kuma kafuwa ga dukkanin abunda baya so kuma yasa agaba, shiyasa nace kawai ka ji nace haƙura da 'yar sa"
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" mm ya sake faɗa tare da dafe kai, a zuciyar sa kuwa tambayar kansa yake yi akan wannan wace irin jarabtar so ce haka ke shirin faruwa dashi, gaba ɗaya ji yakeyi abubuwa sun sake cakuɗe masa, sun yimasa ɗaurin goron da bai san ta ina zai fara warware su ba.
_Kuyi haƙuri da wanna, wlh sabgogine sun yimun yawa, dana warware zaku riƙa jina akai akai👏_
#Team Abba gida gida💃
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/24, 9:14 AM] Beey Sai dake: _Page 28_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
______________________________
Ganin yanda nan take hankalin sa ya tashi gaba ɗaya har tsantsar damuwar dake zuciyar sa ta bayyana a kan fuskarsa ya sa Momy ta dafa kafaɗarsa haɗe da juyo da fuskarsa suna kallon juna ta ce,
"My son, kana son yarinyar ne sosai?"
"Upcouse Momy, bazan iya jurar rashin ta ba"
"Shikenan, ka kwantar da hankalin ka kuma kayi ƙoƙarin yin addu'a akoda yaushe kana mai roƙon ALLAH ya za ɓa maka mafi ƙololuwar alkhairi akan ta, ni kuma zan sake wai wayar dangin mahaifin Jabir a karo na biyu a dalilin ka saboda bana son ganinka cikin irin wannan damuwar, wataƙil i zuwa yanzu sun jaye ƙiyayya da kuma tsanar da suke yi mana ni da ɗana"
Da sauri ya riƙo hannayen ta yana kallon cikin ƙwayar idanuwan ta haɗe da cewa,
"Pls don't do that Momy, a tunanina ba yanzu ne lokacin daya kamata kije masu ba, hakan zai iya sake lalata al'amarin gaba ɗaya, musamman idan hasashen da kike yi akansu bai tabbata ba, ma'ana, ina nufin idan har yanzu basu haƙura da abinda ke ransu ba game daku, kiyi haƙuri yau munyi magana da Janan akan za muje gidan grandma ɗin su gobe saboda ta gabatar dani a wajen ta, idan na je zan lura wane irin sauyi aka samu daga wajen ta yanzu, na tabbata a yanda Janan ke bani labarin ta ta daɗe dayin nadama akan abunda ya faru, idan kuma batayi ba zanyi ƙoƙarin shiga jikinta na sauya mata tunani na kuma nuna mata kuskuren abunda suka aikata maku a baya, fatana kawai shine na samu karɓuwa a wajen ta, kinga idan hakan ta faru shikenan zamu jefi tsuntsu biyu da dutsi ɗaya"
Shiru tayi kamar mai wani nazari kafin tace,
"I don't think zaka iya sauya su kamar yanda kake tunani matuƙar har yanzu basuyi nadamar abinda suka aikata ba, hakan kuma ba abu bane mai sauƙi, but zanyi addu'a sosai akan ALLAH ya baka nasara, nima
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 40