aka rufe ƙofar don dama su kaɗai ake jira, da sauri ya ƙara sa can wajen tuƙin ya samu har abokan tuƙin nasa Erik da James sun fara daidaita komai shi kaɗai suke jira a tashi, cikin mintuna ya gama saita na ɓangaren sa shima sannan jirgin ya fara tafiya a hankali kafin daga bisani kuma ya tashi sama, Mu'azzam na ganin sun tashi ya ƙara janyo Shahida ajikin ya yiwa Ƙaisa kiss a kunci sannan ya juya suka nufi wajen motar su suka wuce gida.
***. ***. ***.
A ɓangaren Janan kuwa kwanaki shidda suka rage masu su kammala jarabawa, kallo ɗaya zaka yimata ka fahimci ba kaɗan ta bawa karatun muhimmanci ba saboda cikakken lokacin kanta ma bata da shi yanzu, sallah da kuma wanka kadai ke tada ita idan tana karatu amma hatta abincin wani lokaci tana ci tana karatu ne, duk da tarin soyayyar da take yiwa mm ta danne ta maida hankali wajen karatun ta sosai saboda shima ya faɗa mata cewa zai rage damunta a waya saboda ta samu isasshen lokacin da zata maida hankali ga karatun ta, shiyasa duk kwanakin nan da yayi tafiya ba tare daya samu kiranta akai akai ba sai dai message bata wani damu ba tunda dama yariga daya faɗa mata,
Yau ma kusan zaune ta kwana tana karatu don exam biyu suke da ita gobe, ɗaya practical ce da rana zasu yi misalin ƙarfe sha biyu, ɗayar kuma sai zuwa ƙarfe huɗu zasu rubuta ta, kasancewar bata son tayi latti yasa ƙarfe sha ɗaya na bugawa ta ɗauki motar ta ta wuce school gabanta na faɗuwa, gashi duk jikin nata baya yimata daɗi amma sai ta ta'allaƙa abun da rashin samun isasshen baccin da bata yi bane daren jiya,
Tana fita ko awa ba'a yi ba motocin ambassador Hussain Salim kusan ƙwaya bakwai suka iso gidan nasu, dama tuni Abban yasan da zancen zuwan nasu na kawo kayon auren Janan kamar yanda ya tsara ya kuma yi order duka abunda zasu ci su sha a hotel don kar ma kowa yasan da zancen har sai sun iso, suna isowa ya kira hotel ɗin ya ce akawo masa order ɗin da yayi sannan ya fita wajen tarbon su, manyan mata ne hamshaƙan masu ji da nera ko wace taci ta ƙoshi, kana yi masu kallo ɗaya zaka san hutu da jin daɗi ya zauna ajikinsu su bakwai, sai ambassador Hussain Salim da kansa da kuma Asgar.
Da kansa yayi masu iso har cikin gida dama koda yaushe gidan a gyare kuma a tsaftace yake kamar yanda Madam florence ta saba yi akoda yaushe, bayan sun Zazzauna a inda aka tanadar masu acan ɗayan falon ɗan madaidaici dake gefen ƙarin falon dake nan ƙasa su kuma su Abba da ambassador Hussain salim da Asgar suka zauna a kujerun dake nan tsakiyar falon suna kallon yanda ake shigowa da kayayyakin ɗaya bayan ɗaya Abba na faman kiran masha ALLAH yana wasar baki tare da cewa Madam florence taje sama ta kirawo masa Nihal, ko kaɗan Nihal bata so tasowa ba don baccin bai isheta ba amma jin kamar sautin hayaniyar mutane ya sata ɗago kai tana kallon Madam florence haɗe da cewa,
"Madam so we have visitors me?"
"Yes my dota"
"Ok, tell him am coming" ta ƙare zancen tare da sauko da ƙafarta daga kan gadon sannan ta mike tsaye, bata wani tsaya sauya kayan baccin dake jikinta ba irin masu dogon wando da riga mai dogon hannu ta shiga toilet ta wanko bakinta sannan ta fito daga ɗakin nata kanta ko ɗan kwali babu tana saukowa a hankali, kamar wacce aka tsaida ta tsaya cak a bakin hawa matattakalar tana ƙare wa kayan dake wajen kallo sake da baki har tana faɗin "wow..fantasti" ba tare da tasani ba, Muryar Abba dake faman murmushi da taji yana faɗin,
"Morning sweetheart, ƙara so mana" ta sata yin wata ajiyar zuciya tare da tattab'a saitunan kalolin akwatayye dake wajen ƙwaya biyar tana ratsawa ta tsakiyar su tare da juyawa tana kallon kayayyakin da aka shigo dasu, kama daga kan katam katam ɗin drinks da na swan water, kwalayen biskit, cingwam, chaculate da sauran kayan tarkace na na gani ina so, hatta dabino buhu guda suka zo dashi da ƙwallayen goro ƙwaya biyar, a gefe kuma ga buhuhuwan shinkafa, semovita, taliya, makaroni da harkokin manja da na mangiɗa da maguna da za ayi amfani dasu wajen hidimar bikin suma an tule su waje ɗaya, ga wani kwali a gefe shima da kalolin invitation na ɗaurin aure dana programs ɗin da aka tsara,
"Abba wannan kayan fa" Nihal ta faɗa tana kallonsa haɗe da ƙara sawa wajen, ambassador Hussain da Asgar data hango yasa bata bari ya bata amsa ba ta ci gaba da cewa,
"Wai all dis is for my Janany sister, wooo...how lucky she's"
Dariya ambassador yayi shida Abba suna kallon juna kafin Abba yace,
"Your lucky most past her own by God grace sweetheart, where she's"
"Ta je school exam, Kuma Inaga biyu zasu yi yau"
"Eh na sani, amma nazata ɗaya zasu yi dt's 4:00 -6:00 na marece kenan"
"No za suyi practical by 12:00, think yanzu haka ma sun shiga" ta bashi amsa tana kallon kayan saboda gaba ɗaya sun gama ruɗata tare da tafiya da imanin ta, don kusan hilux huɗu ta kwaso kayan shiyasa duk girman falon sai da aka cika ko ina da kaya, Asgar kuwa sai ƙamshi yake sha yana wani basarwa shi aka tilas ya sai girma,
Miƙewa Nihal tayi ta gaida ambassador Hussain sannan ta matsa kusa da Asgar tare da ɗaya masa hannu ta ce, "hy Asgar" ya kauda kansa gefe ba tare daya amsata ba don shi haushi ma take basa, shi yanzu ba wadda ya matsu ya gani sai princess ɗin sa Janan, yaga yanda zai burgeta idan taga irin fatar da yayi mata shi da iyayen sa, yasan tunda har kayan suka burge wannan mai rawar kan tsiya to tabbas zasu burge Janan ɗin sa,
Kai tsaye falon da iyayen Asgar mata suke ta nufa ba tare data damu da kayan dake jikin ta ba, kallo ɗaya Madam florence tayi mata ta ɗauke kai yayin da ita kuma ta ƙaraso wajen su tana faɗin,
"Hi, sannun ku da isowa" sannan ta wuce abunta,
Ɗago kai ɗaya daga cikinsu dake saye da wani danƙareren lace mai matuƙar kyau da tsada, ga gwala gwalai ajikinta data saka tun daga sama har ƙasa sai faman taltalniya sukeyi, a hankali ta cire glasses ɗin idanuwanta tana ƙare wa Nihal kallo ta bayan ta data juya tana tafiya sannan ta maido kallon ta ga ƴan uwan nata haɗe da cewa,
"Kar dai ace wannan yarinyar Asgar ya kwaso mana?"
"To waya sani yaya Jalila" ɗaya daga cikin matan wacce ƙanwa ce ga ambassador Hussain ta bata amsa, wacce aka kira da yaya Jalila ɗin kuma itace yayar ambassador Hussain Salim,
Hura hanta tayi haɗe da maida glasses ɗin ta ga idanuwa sannan ta ce,
"Lallai da sake idan har ita ce yarinyar, sam bata yi mani ba saboda na tsani reni haka kuma bana son fitsara ko kaɗan"...
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 49_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
*Page ɗin yau naku ne mu dear sister's, AYSHA-FAREEDA, AUNTY JAMILA, XEEEEEEEEEE, BODEINGHR, Ina matuƙar jin dadin comment ɗinku da yanda kuke bibiyar littafin nan, Nagode sosai da saka ƙwarin guiwa a muhallin daya kamata, ALLAH yayi maku sakayya da mafi ƙololuwar alkhairi a rayuwarmu, much luv💋*
______________________________
Da sauri Abba ya taso hango Jazz daya tura a ɗauko Hajiya suna shigowa biye da ita a baya, ya ƙaraso wajen cike da biyayya yana yimata sannu da isowa tare da riƙo hannun ta suka ƙara so cikin falon tare, a inda ya tashi ya yiwa grandma data bi falon da kallo tare da mutanen dake ciki wurin zama sannan ya zauna ƙasan ƙafafuwan ta yana gaisheta,
Fuskarta a sake ta amsa haɗe da kallonsa ta ce,
"Usman lafiya tun daga waje naga motoci ga gida cike da mutane da kuma kayan arziƙi?"
Murmushi ya yi tare da juyawa yana kallon kayan dake shaƙe acikin falon sannan ya maido da kallonsa ga Hajiya yana sosa ƙeyar kansa ya ce,
"Ammmm.. Hajiya kin dai gani, arziƙi daga sama kin san in kafi wani wani ya fika, shiyasa ma na aika a ɗauko ki saboda ki ganewa idanuwan ki tare da sanya albarka, faɗin malam ba haushi ya ce daka tara arziƙi ka barwa yaro ƙara ka haifesa dashi, duk da dai ban sanar dake zancen da wuri ba saboda ina son naga tabbatuwar lamarin"
"Ban fahimceka ba Usman, ƴar lelen taka ta samu mijin aure ne?, Ko zaɓin nata ne ka nemo mata" saida ya yi dariya sannan ya ce,
"A'a ba ita bace, takwarar ki dai ce, ai ita muna addu'a ne har yanzu tunda lamarin yaron ya zamo gaibu.."
"Kuma akace dole sai shi zata aura ba" Hajiya tayi saurin katsesa tare da bashi wannan amsar cike da takaici, jin haka yasa Abba saurin cewa
"ALLAH ya baki haƙuri Hajiya, ba haka nake nufi ba, amma kinsan ai komai lokaci ne dashi, kina addu'a kema sai kiga ALLAH ya kawo mata shi har gida, yanzu dai bari na gabatar maki da aminina ambassador Hussain gaya can zaune nasan kin sanshi, to ɗan wajen sa ne yaga Janan tun a shekarun baya ya ce yana so, kwanaki ya bijiro da maganar saina bashi damar zuwa ya nemeta don na tabbatar da zancen sa inda gaske yakeyi, kin san halin abokin nawa? Yana jin haka shi kuma sai ya kwaso kaya suka zo gaba ɗaya don su nuna mani cewa eh da gaske ɗin suke" ya ƙare zancen tare da ɗagawa Asgar hannu alamun yazo, tunda ya fara magana Hajiya ke kallonsa cike da mamaki har ya gama, bata ce dashi komai ba sanadiyar ambassador Hussain daya ƙara so wajen yana gaisheta cike da girmamawa, cikin sakin futska shima ta amsa haɗe da tambayarsa ya iyalin nasa da sauran ayyukan duk lafiya, ya amsa mata da komai lafiya yana murmushi,
Dafa Asgar Abba yayi daya zauna kusa dashi yana gaida Hajiya shima, ya ce
"Hajiya wannan shine Asgar ɗin dake son Janan, babban soja ne da ƙasar sa ta Ethiopia ke alfahari dashi" murmushi Hajiya ta yi tana danne wani takaici dake taso mata daga ƙasan zuciya haɗe da cewa,
"Au kace shine maigidan nawa?, Kun zo lafiya?"
"Lafiya klw" Asgar ya amsa mata yana sinne kai cike da kunya, cikin ƴar tsokana Hajiya taci gaba da cewa,
"To kai ga ni me zakayi da Janan yaro, ko baka ga na fita kyau da kuma ƙarko ba?"
"Ah Hajiya ai ke ta musamman ce, ki bari idan na riƙa matata a hannu sai muyi wannan zancen, amma dai kiyi ƙasa ƙasa da muryar ki kada taji tace ta fasa yina" ya bata amsa yana dariya, kasancewar grandma nada son barkwanci yasa tayi dariyar itama haɗe da cewa,
"To ashe kai ragon namiji ne tunda kake tsoron ta, ai ba'a san soja da tsoro ba musamman na macce"
"Kai, ai Hajiya ita ko soja ke tsoro don babu abunda ke tsorata soja aduniya kamar macce, take ne zata narkar da busasshiyar zuciyar sa idan sukayi arangama"
"To masha ALLAH, ALLAH ya tabbatar da alkhairi, mudai amincewar junan ku shine muradin mu, matuƙar aka samu haka tsakanin ku to muna farinciki tare da sanya albarka" ba asgar ba hatta Abba da mahaifin sa sun yi farincikin yanda Hajiya ta karɓi zancen hannu biyu, a tsammanin su matsalar su ta kau don indai ta ɓangaren Janan ne ganin suke kamar ma ta gama amincewa idan ta zo, nan yake sanar da ita cewa ai tare suke da baƙi mata suna wancan ɗayan falon bari a kira su su gaisa ta ce a'a ya bari ta ƙarasa can su gaisa dasu, tare suka miƙe har ambassador da Asgar suka nufi falon da su yaya Jalila ke ciki har lokacin suna mita akan tabbas in Nihal ce wacce ɗan nasu zai aura baiyi mata ba,
Suna shiga duk sun kayi shiru suna raba idanuwa, kujerar dake farko ɗaya daga cikin su ta miƙe ta bawa Hajiya da tayi tsaye ɗauke da murmushi akan fuskarta suka shiga gaggaisawa dasu tare da zaunawa tana ƙare masu kallo ɗaya bayan ɗaya, ƴar gyaran murya Abba ya yi kafin yace,
"Hajiya Jalila wannan itace mahaifiya ta wato kakar Janan" sannan ya juyo yana kallon Hajiya tare da ci gaba da cewa, "Hajiya waɗan nan iyayen Asgar ne, wannan yayar ambassador ce Jalila, ga kuma ƙannensa can guda biyu Hajiya Jamila da Hajiya Najida, sai yayun sa ga su can Hajiya Hassan da Hajiya Hussaina, sai kuma ƙanwarsa Bilkisu gata nan" ya ƙare zancen yana nuna wata kyakkyawa a cikinsu da bata ida shekarun su ba, duk da itama za a iya kiranta da babbar mace saboda yanda hutu ya sata buɗe wa, tayi aure kusan shekaru biyar da suka wuce har da yaran ta uku, tunda suka shigo hankalinta na kan wayarta ba tare da ta ce uffan ba sai yanzu da taji an ambaci sunan ta, ɗago kai tayi ta kalli Abba da Hajiya sannan ta maida kanta ƙasa ta ci gaba da latsar wayar ta, jinjina kai Hajiya tayi haɗe da kiran Madam florence dake shigowa da kayayyakin abincin da Abba yayo order daga hotel tana jerewa tsakiyar falon da taimakon wasu daga cikin ƴan aikin gidan dake kula da ɓangaren share-share da goge-goge, ta ce
"Ina Hajiya Zainab ne, bata san da isowar su bane?"
Kafin ta bata amsa Abba yayi saurin cewa,
"A'a inaga akwai abunda ya tsaidata, bari na kirawota" yayi saurin ficewa zuwa part ɗin Aunty zee ba tare daya bari sun haɗa idanuwa da Hajiya ba don yasan me zai iya biyowa baya in taji cewa bai sanar da ita ba,
Ba'a jima ba sai ga Abba ya shigo aunty zee na biye dashi cikin shiga ta alfarma kamar yanda ta saba yi a koda yau she, shiyasa ma ko sauya kaya bai bari tayi ba saboda tayi masa ayanda yake so, kawai faɗa mata yayi tazo anyi baƙi, karo na farko kenan tun da aka kawota kusan shekaru goma sha shidda data fara tako ƙafarta cikin part ɗin na Abba da yaran sa, duk da wajen ya burgeta matuƙa haka ta sinne kai tana biye dashi har suka isa falon, da yake wayayyar macece suna shiga ta fara basu haƙurin rashin fitowa dawuri tare da gaida Hajiya don ta wanke mijin nata daga zargin rashin sanar da ita kamar yanda ya buƙata tayi, ta bata haƙuri itama sannan suka ci gaba da gaggaisawa dasu, ba laifi aunty zee ta samu karɓuwa wajensu don sun sakar mata fuska sosai ana ta fira kafin tayi masu bisimillah tana ƙoƙarin miƙewa haɗe da bubbuɗa abincin da taga an cika wajen dashi, Madam florence dake gefe tsaye na ganin haka tayi saurin ƙarasowa ta fara servin masu, abinci ne mai rai da lafiya ga soyayyin kaji da tsire a gefe, sai kuma haɗaɗɗiyar kabsa rice da gasashhen rago da kuma lemuna,
Saida yaya Jalila ta ɗauki tsinken tsire zata kai a bakinta sannan ta kalli Aunty zee ta ce,
"Nikam Hajiya wai ina ƴar tamu take ne?, Ko rowar ta ake yi mana?" Duk da Aunty zee bata fahimci waacce take nufi ba murmushi tayi haɗe da cewa,
"Ko ɗaya Hajiya, ai bama fara ba ku keda ita ai, bari nayi har ku gama tukuna idan ta dawo school sai tazo ta kawo gaisuwa wajen manyan iyaye da manyan yanne"
"Da kuma manyan ƙanne ba" Bilkisu ta faɗa jin Hajiya zee bata ambato da position ɗin ta ba, dariya duk suka saka kafin ta juyo tana kallon ta har lokacin kanta na ƙasa tana latsar wayar ta tamkar ba ita tayi magana ba,
"Duk da a matsayin matar yaya zata je wajen ku, kisa aranki cewa ke babbar aunty ce a wajen ta, don haka sai ki shirya karɓar girma tun yanzu" dariya aka sake sawa akaro na biyu Bilkisu ta ɗago kai cike da jin daɗin zancen Hajiya zee tayi murmushi, don ita mutumce mai son abata girma da kuma nuna mata tana da muhimmanci aduk inda ta shiga don haka ta ajiye wayar tata itama ta soma cin abincin kamar yanda sauran ke ci,
Ita dai Hajiya banda kallon su ba abunda takeyi, sai kuma mamakin Abba daya cika mata zuciya fal akan yanda ya iya wanzar da abu lokaci ɗaya ba zato ba tsammani ba tare da sanin ta ba, a ɓangare ɗaya na zuciyar ta kuwa Muhammadu ne ya faɗo mata arai, kar dai ace Janan tasan da wannan zancen ta zauna tana ta sata itama taya ɓera ɓari.
Muryar Hajiya zee data jiyo ta haɗo mata abincin itama a ƙaton tire ta ɗoro akan Centre table ta matso mata dashi a gaban kujerar da take zaune tana faɗin, "Bisimillah Hajiya" ya sata dawowa daga duniyar tunanin data fara lulawa, murmushi tayi mata haɗe da cewa,
"Sannu Hajiya Zainab ALLAH yayi maki albarka, ehm.. wai in ƴar taki take ne ma?" Ƙasa da murya tayi don bata san wacce take nufi a cikinsu ba kafin ta ce,
"Wacce kenan daga cikin su Hajiya?"
"Takwarata"
"Oh Janan?, Inaga tana makaranta, ɗazu ta shiga kafin tawuce ta ce nayi mata addu'a, kin san jarabawa sukeyi"
"Eh haka ne, to ina ita ɗayar.." kafin ta rufe baki sai ga Nihal ta sauko cikin riga da sket na lace ta ya fo ɗan ƙaramin mayafi dako ƙirjinta bai gama rufewa ba bluethooth na laƙame a kunnenta na hagu, dama tana barin wajen ɗazu sama ta haye don ta watso ruwa, kallo ɗaya Hajiya tayi mata ta ɗauke kai har ta ƙara so, kamar dai yanda tayi ɗazu haka ta sake kallon baƙin ta ɗaga masu hannu haɗe da cewa,
"Sassannun ku fa" tare da zaunawa akan hannun kujerar da grandma ke kai,
"Hajiya yaushe kika iso?" balla mata harara tayi haɗe da cewa,
"Oho, wai ke shikenan baki iya gaida mutane tsabar rashin mutunci, hala bakya ganin mutane a wajen?, Kin wani zo kinyi masu tsaye ƙiƙam tsabar rashin sanin ciwon kai" Hajiya zee dake tsaye wajen ta janye ta shiga wata sabgar tana mai addu'ar ALLAH yasa dai ba Nihal ɗin aka zo neman aure ba kar ta zubar da mutuncin ta tun yanzu a samu matsala, su kuwa babu wanda ya sake kallon inda take balle su damu da zamanta wajen Hajiya Bilkisu ce ƙaɗai tayi ƙarfin halin ɗagowa tana kallon ta haɗe da mere baki jin irin taɓarar da take yiwa Hajiya,
"Kai Hajiya, wai menene haka don ALLAH, shiyasa ni bana mason ma na haɗu dake, meye zancen sa'annina anan, ina dai gaisuwa ce kuma nayi masu, then.." Bata ƙara sa ba Hajiya ta ce ,
"Tashi kibar nan kafin na saɓa maki, wawiyar yarinya kawai" ta miƙe tabar wajen tana tutar baki,
A ɓangaren Janan kuwa tun ƙarfe uku da wani abu ta gama exam, don a maimakon su shiga wacce zasuyi ƙarfe huɗu sai suna gama practical ƙarfe biyu zuwa biyu da kwata aka sa suka shiga ɗayar, kasancewar duk abunda ta karanta ne ya fito ya sa bata wani jima ba ta gama, tana ƙoƙarin shiga mota kiran mm ya shigo tayi saurin ciro wayar ajikka, sai da tayi murmushi sannan ta ɗaga ganin lambarsa haɗe da karawa a kunne, ta ce
"ALLAH ya taimaki hubbin ruh, manyan gari" sai da yayi dariya tukuna ya amsa da "Amin tare dake noorul alb, ya kike ya jarabawar"
"Alhamdulillah mun ƙare gani ma zan je gida"
"Da kyau matata, nima gani nadawo gari"
"Da gaske kake? Na zata wannan karon ma sati biyu zakayi" da yake Abuja ya ce mata zai je, ta ƙare zancen haɗe da saka makullin motar ajiki ta buɗe ta shiga ta zauna, jikinta na ciki ƙafafuwan ta na awaje,
"A'a bazan iya sati biyu ban gane ki ba, tunda ke karatu ma ya hana ki tambayi ko yaushe zan dawo"
"Wayyo hubby kayi haƙuri, kaifa kace na maida hankali sosai kana so nazo first class"
"Sai kuma nace adena bani kulawar daya kamata?"
"A'a amma am Kati haƙuri, ka dawo lafiya?"
"Lafiya klw, ya za a yi,?"
"Dame fa?"
"Alamu sun nuna cewa a gajiye kike, gashi ni kuma ina so na ganki"
"Ehm, hakan ba laifi, to mu haɗu gidan grandma ko?"
"No, bazai yuyu na wahalshe ki haka ba, ko dai in zo nan zaki iya jirana?"
"Me zai hana yallaɓai?, Sai ka iso?" Kiss ya jeho mata sannan ya kashe wayar, dariya tayi tare da ƙarasa shigar da ƙafafuwanta cikin motar haɗe da kwantar da sit ɗin baya yanda zata iya ɗan kwantawa ta huta kafin ya ƙara so , ai kuwa ko mintuna uku ba a yi ba bacci ya ɗauke ta saboda rashin samun isasshen baccin da batayi ba jiya,
Shi kuwa Ingaski yana zuwa zai wucewa ɗauke da booklet ɗin ƴan wasu department daya yiwa invigilating kamar ance ya kalli gefen da motar tata ke ajiye ya hango kyakkyawar fuskarta daga cikin glass ɗin motar tana bacci, ji yayi tamkar yaje ya sumbace ta haɗe da lasar bakinsa ya haɗiye wasu yawun daƙyar saboda tsananin sha'awar ta daya ji lokaci ɗaya ta taso masa, ɗan sake matsawa yayi a jikin motar tare da miƙa hannu zai kai a jikin marfin motar kawai wayar ta tahau ruri, ba tare da tasan da wani a wajen ba ta saki gaba ɗaya jikinta haɗe dayin wata irin doguwar miƙa kafin ta miƙa hannu ta ciro wayar acikin jikka, kusan mutuwar tsaye yayi ganin yanda breast ɗinta suka turo lokacin da tayi miƙa har envelop ɗin dake hannunsa na booklet ya faɗi bai sani ba, ko data ɗauko wayar har ta tsinke, tana ƙoƙarin kira ganin lambar mm ce sai gashi ya sake kira, kamar ance ta juyo gefenta tare dakai wayar a kunnen ta taga Ingaski tsaye ya ƙurawa ƙirjinta idanuwadon ba ƙaramin tafiya da imanin sa sukayi ba, nan take ya fara hangosa kwance da ita yana tsotsar su, kanta ta kalla kafin tayi saurin janyo mayafi ta rufe ƙirjin nata da taga yana kallo sannan ta ɗago ta balla masa harara haɗe da cewa "ALLAH ya isa" ganin bai ma ji abunda take cewa ba yasa ta murtuƙe fuska tare da saka key ɗin motar ta tayar zata wuce don mm ya ce ya ƙaraso,
Da sauri Ingaski ya dawo hayyacinsa sakamakon ƙarar tashin motar da yaji tare da duƙawa ya ɗauko envelope ɗin, yana ɗagowa suka haɗa idanuwa da ita ta balla masa harara sannan ta ja motarta tayi gaba, wani irin abu ya ji tun daga tsakiyar kai har zuwa ƙasan ƙafafuwan sa ga wani irin mutuwa daya ji jikinsa yayi gaba ɗaya, wanda ko shakka babu ya tabbata dole sai yayi wanka, ya rasa wace irin sha'awa ce yake yiwa Janan dako tunanin ta yazo masa sai ya samu jin daɗi, gashi gaba ɗaya ya rasa ta hanyar da zai sama kansa ƙololuwar jin daɗi atare da ita, tabbacin babu fa yanda zai yi ya sa ya ja ƙafafuwan sa ya wuce inda zashi....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 50_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
*page ɗin da gaisuwar duka naku ne, AUNTY SHAFA ABU ƘAURA, ASY UMMU SAUDA, MAMA SA'A SHEHU, NAFISA ABUBAKAR ANKA, DOTA HANNATU AMINU, MAMAN WALID, NANA HAUWA'U, PHARTIMA LAWAL ABUBAKAR, FARIDA LAWALI, fatan alkhairi agareku haɗe da godiya mai tarin yawa bisa soyayyar ku agareni, ngd sosai ALLAH ya saka maku da alkhairi👏♥️*
______________________________
Janan kuwa tana gab da kaiwa bakin gate suka haɗu da mm don mai mashin a bakin gate ya ajeye sa saboda ba a bari ya shigo ciki dashi ba, a hankali tayi parking gefe tare da saukar da glass ɗin motar tana murmushi,
"Iyyee mutanen Abuja wannan irin fresh haka fa" ta faɗa daidai lokacin daya buɗe marfin motar ya shiga ciki, kallon ta yakeyi tun daga sama har ƙasa kafin yace,
"Anya baza muyi faɗa da wannan karatun naki ba, gaba ɗaya naga ya sa kin faɗa sosai"
"To ya za muyi?,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 40