Share this page
ita da Razina suje su haɗo don sune ƙasashen da zai je wannan karon, yana so ko da Janan zata gama jarabawa a ƙarshen wata mai zuwa ya kammala komai sai dai kawai ayi batun auren su don wannan satin shima zai je ƙauyen su in ALLAH ya yarda saboda Hajiya sai daɗa matsa masa takeyi akan zancen, a cewar ta hakan zai taimaka masa sosai wajen samun cikakkiyar natsuwa a tattare dashi, ta faɗi hakan ne saboda bata taɓa jin kanta cikin natsuwa da kwanciyar hankali ba tun lokacin dasu Momy suka tafi sai yanzu da suka dawo gareta, kuma shi kansa ya tabbatar da zuwan nasa kaɗai ne zai sama masa natsuwar da yake yima kansa fata shida ƴar uwarsa.... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 44_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Kasancewar yau saura kwana ɗaya mm yaje ƙauyensu ya sa da marece ya ce Momy da Razina su shirya ya suje gidan grandma gaisheta daga nan suga juna ita da Hajiya, ya so su haɗu da Janan amma a yanayin yanda zasuyi tafiyar bai kamata ace ya haɗu da ita ba, hakan yasa da sukayi waya da ita ya ce tabari zai zo nan gida da daddare suyi bankwana saboda gobe sakko yake so yayi, bata so hakan ba don taso su haɗu gidan grandma susha firarsu, cikin shagwaɓe murya ta ce, "Amma dai kasan idan kazo nan gida ba wani jimawa zamuyi ba kasan Abba na gari" "Na sani mana, me kike tsoron ya faru don Abba na a gari" "Abubuwa da dama gaskiya saboda bana son duk wani abu da zai cutar mani dakai, musamman lafiyarka domin itace tawa" "Shikenan, kisa aranki in sha ALLAH babu abunda zai faru" "I wish so" ta faɗa muryarta na nuna alamun ba hakan taso ba, murmushi yayi haɗe da cewa, "Come on, trust me kinji ko" "To shikenan sai kazo" "Good beb, smile make i hear" ta saki wani irin ƙayataccen murmushi da sai da sautin sa ya dakar masa kunne tare dasa hannu ta kulle fuskarta tamkar tana a gabansa, dariya yayi sannan ya ce, "Ko kefa, sai nazo" "Bye, ALLAH yakawo ka lafiya" "Amin" ya faɗa haɗe da kashe wayar, daidai lokacin Momy tafito saye da hijab ɗin ta har ƙasa Razina na biye da ita a baya riƙe da leda a hannun ta, "Momy kun fito?" "Eh my son, Ina mutumen naka?, Ko bada shi za a je ba?" "Ya ma isa, yana waje yana karɓa waya" "To muje naga ankusa magrib" Saida ta wuce gaba sannan ya miƙe tabi bayanta haɗe da kallon ledar dake hannun Razina ya ce, "Meye wannan?" "Sauƙin Momy ne aciki wai zata kaiwa Hajiya" "Au! Wai me?, Ko kishi kikeyi da ita kema" ya ɗaya makullin motar dake hannunsa karamar zai doka mata akai tayi saurin janyewa tana dariya, "Ya mm to meye laifina ma idan nayi, ai Auntynah ta koya mun" murmushi kawai yayi don yasan Jabir ya faɗa mata abunda ya faru ranar, ba tare daya sake cewa komai ba ya wuce gaba abunsa tana biye dashi tana dariya ƙasa ƙasa har suka ƙaraso bakin motar ya buɗe ya shiga ya tayar, Jabir da har lokacin bai gama wayar da yakeyi ba ya yiwa horn alamun shi suke jira, yana juyowa suka haɗa idanuwa da Razina dake ƙoƙarin shiga motar ta dalla masa harara sannan ta shige abunta, ƴar dariya ya yi ganin kishin namu na mata ya motsa mata ganin yana waya haɗe da shafo sideburn ɗinsa sannan ya yi sallama da wanda suke wayar ya kashe, Har ya shigo motar ko kallonsa bata koma yi ba duk da juyowar da ya yi yana kallon ta haɗe da cewa, "Sorry Madam na tsaidaku ko? Na ga sai harara ake aikamun da ita, afuwan" "Oh, kodai ma meye kaika sani kar ka shawa yarinyata kai da surutu" Momy ta faɗa tana kallon Razina da fuskarta kecan gefe tana kallon waje ta cikin glass ɗin tagar motar, murmushi tayi haɗe da sinne kai ƙasa wanda hakan ya sa shima ya yi murmushin tare da maido fuskarsa a gaba yana faɗin, "Ka kira Janan kuwa" "Eh, amma bana so muhaɗu shiyasa na faɗa mata cewa zan zo anjima da daddare acan gidan baffan muyi sallama da ita" "What? Kace munemi robb yau, Momy kinji yaron ki ko?, To nidai wannan gidan ko rakkiya bazan je ba balle nakai kaina" "Ai kai kace, shi ba matsoraci bane shiyasa zai je, kuma in sha ALLAH ba abunda zai samesa, jeka yarona ka gayarmun da ƴar rawa in ka je" "Yawwa Momy, faɗa masa dai, in sha ALLAH zata ji, ina dawowa zan kawo maki ita har gida tagaisheki" "ALLAH ya nufa, amma naso mu haɗu yau da ita, inga ƴata na kuma bata amanar yarona" "To ko nakirata Momy nace tazo ku haɗu?" "A a karka damu, yau da jibi ɗin duka ɗaya ne awajen ALLAH, idan ka dawo ɗin sai ka kawo mun ita" "Shikenan Momy, da yardar ALLAH haka za a yi" "ALLAH ya yarda" "Amin" Haka suka ci gaba da fira har suka iso gidan grandma, kasancewar basu sanar da ita ba yasa mm ya tura mai gadi ya ce yaje ya faɗa mata cewa tayi baƙi, bada jimawa ba mai gadin ya dawo ya buɗe masu gate suka shigo da motar har ciki don ya riga daya sanar da ita ko su waye data tambayesa, A daidai bakin ƙofar falon sukayi sallama Jabir ya fara shiga cike da tsokana yana faɗin, "Ina wannan tsohuwar yayin ta shige?, Fito ga alƙawarin dana yi nan ALLAH ya taimakeni na cika" yana rufe baki ta fito daga bedroom ɗin nata tare da dafat kan kutjerar dake tsakiyar falon haɗe da cewa, "Ka kuwa yi arziƙi daka sauke wannan nauyin, ina ƴar tawa take?" Ta ƙare zancen tana kallon bayansa da masu ƙoƙarin shigowa, kamo hannunta ya je ya yi tana takowa a hankali ya zaunar da ita akan kujera idanuwanta ƙyam akan Momy da ganin Hajiyar yasa ta nufo wajen cike da fara'a dajin daɗi ta durƙusa agabanta tana faɗin, "Sannu, sannu Hajiya Barka da fitowa" kunsan halin yare da girmama nagaba, wanda har yau wannan ɗabi'ar bata saki Momy ba, cikin karyewar murya Hajiya da kunya ta gama rufeta tasa hannuwa ta ɗagota tana faɗin, "Kaico da ranar tarin nadama da dana sani, kiyi haƙuri ƴatah kiyafemun abunda na aikata maku a shekarun baya, haƙiƙa na cutar da jinina Jamal da kaina duk da baya raye" ta ƙare maganar tare da rungume Momy ba tare data ji kunya irin wacce akeyi tsakanin sarakkai ba, itama Momy rungumeta tayi tana jin wasu hawaye masu sanyi na sauko mata a fuska wanda ya tabbata bana komai bane sai na farinciki, musamman data kira masoyin nata da bazata taɓa mantawa dashi ba wato Jamal, sai taji tamkar shi ɗin ne a tare da ita a dai dai wannan lokacin, kasa cewa komai tayi tana ajikin grandma daketa faman kuka har tayi mai isar ta ta gama sannan ta cirota a jikinta haɗe dasa hannu ta kamo fuskarta, ta ce "Ƴatah kina fushine dani har yanzu? Ki yafemun don ALLAH na gane kuskurena, abun da muka aikata ni da yaro na sam ba koyarwar musulunci bane kuma baya cikin kyawawan ɗabi'u, don haka nake roƙonki daki yafe Mani kema albarkacin jikana da kuma ɗan Jamal kin ji" Sake rungumeta Momy tayi tana jin wani irin sanyi a ranta haɗe da cewa, "Sam uwa bata laifi ga ƴaƴan ta saidai kuskure, wannan kuskuren kuma tana aikata shi ne bisa tsananin so da ƙaunarta ga ƴaƴanta, idan ma wancan abun daya faru laifine to na yafe maki a matsayinki na uwa kuma mahaifiya agareni, Jamal mutumen kirki ne mai amana da halacci da ko sau ɗaya bai cancanta agareni na yarda da cewa mahaifiyarsa zata cutar damu ba, asali ma ni yakamata na baki haƙuri dana nisanta ki da jininki, nayi hakan ne don dakatar da tsanar dake iya wanzuwa a zuciyarsa idan ya ci gaba da ganin abinda ke faruwa tsakanin ni da kuma dangin mahaifinsa, don ALLAH kiyafemun Hajiya" Da gaskiya ta yiwa Hajiya yawa jin gaba ɗaya laifin ma Momy ta tattarashi ta ɗora akanta kawai sai ta tsinci kanta da ɗaga hannu sama tana kwararowa Momy addu'ar da bata tsammanin ko ɗaya daga cikin ƴaƴanta ta taɓa yiwa irin ta ba, daga ƙarshe ta rufe da cewa, "Alhamdulillah, ALLAH ko yanzu ka amshi rayuwata kayi mani duk abunda yakamata tunda na samu yafiyar mutanen dana cutar mafi cutarwa a duniya, kuma yanda wannan baiwa taka ta yarda dani bayan duk girman laifin dana aikata mata kaima ka yarda da ita, ALLAH ka albarkaci duk wani tsatso nata dazai rayu a wannan duniyar kasanya farinciki a zuciyar ta har zuwa mutuwa, Na gode ƴatah ALLAH yayi maki albarka" Momy ta amsa da amin tana jin wani farinciki aranta, wai yau ita ce agaban mahaifiyar Jamal data nuna mata tsana da kyara take yimata irin wuɗan nan daɗaɗan addu'o'i da bata taɓa jinsu a bakin kowa ba, alhamdulillah tabbas babu abunda yafi komai daɗi a duniya sama da haƙuri, ta faɗa cikin zuciyarta tana mai godewa ALLAH daya nuna mata wannan rana da Jabir ya dawo cikin dangin mahaifinsa, mafarkin data dade tana fatar tabbatuwar sa kafin mutuwarta sai gashi ALLAH ya amsa mata, Kafin kace me tuni Hajiya taba mai aikinta umurni a shirya mata lafiyayyaen abinci mai kyau da surukarta kuma ƴarta zata ci sannan aka shiga gaggaisawa tare da firar yaushe rabo tsakanin ta da Momy, duk dai ba wata jituwa ce tun can tsakanin su ba amma kasancewar mafi aksarin firar ta Jamal ce mahaifin Jabir ya sa suka koma tamkar tun can da sun shaƙu, Kallon Razina da tun bayan gaisawar su da Hajiya bata sake cewa komai ba tana ta dannar wayarta Hajiya tayi haɗe da cewa, "Tunda kishi bai barinki fira Dani aromun wayar sai nakira ɗan saurayin naki ni sai nayi fira dashi" "Indai ɗan saurayi na ne, ba fira kaɗai ba, ki ɗauka duka na bar maki" "To ni ban barmata kaina ba Malama, taso muje inji waya taɓa mun ke har kike kyauta dani haka, kuma kirasa inda zakiyi sai wajen wannan tsohuwar" ya ja hannunta suka bar ɗakin suka nufi farfajiyar gidan, dariya Mm yayi haɗe da cewa, "Hajiya to ai ƴar gida za a yi tsakanin ki da ita, amma ga alama ta gama ƙwace maki shi don haka karki yarda" "To..to..to, ranar yayita tarensa ban fahimta ba sai yanzu, ashe ita Ranizar taka yake magana, ahhh lallai mijin yarinya, dole na sallamaku na nemi wani mijin tunda yawo kukai mani da hankali" "A a Hajiya ba Raniza take ba, Razina, ko duk kishin ne?" ya faɗa har lokacin yana dariya, daƙƙuwa Momy tayi masa haɗe da cewa, "Ƙyalesu Hajiya, ai dai basu taɓa canza maki matsayinki, kinanan a uwar gidanki ko suna so ko basa so, auren zobe ne tsakanin ki dasu mutu ka raba.." Sun jima sosai a gidan har aka kira sallar isha, sannan sukayi sallama da ita suka tafi, bayan Momy ta bata ledar da suka zo da ita cike da turarukka da sabulayye masu kyau da ƙamshi da tsada tare da zanen a tamfa maikyau da matuƙar tsada shima, nan ma saida Hajiya ta sake yin wani kukan saboda jin kunyar abunda suka aikata amma sai gashi Momy ta dakanka masu da akasin abunda sukayi mata, ta tayi mata godiya tare da ALLAH sa albarka. (Dama arayuwa babu hukuncin da zaka yiwa wanda ya cutar dakai ya zalince ka irin kai ka saka masa da alkhairi, wlh duk lokacin daya tuna sai yayi tarin nadama tare da zubar da ƙwalla, wannan kukan da yake yi akoda yaushe, to shine hukunci mafi girma da kayi masa bisa laifin daya aikata, ALLAH ya bamu ikon rama kyakkyawa da mummuna) Jabir mm ya bawa motar ya wuce dasu Razina gida shi kuma ya wuce kai tsaye gidan su Janan, tun kafin ya ƙarasa ya kirata ya sanar da ita gashi nan akan hanya, cikin faɗuwar gaba ta sauko ƙasan stairs ɗin tare da leƙa gefen Abba taga wajen a rufe sannan ta fice, nan ma saida ta duba jerin motocin dake ajiye taga babu wacce yake hawa sannan hankalinta ya kwanta don ta tabbatar ya fita, da kanta ta je bakin gate ɗin ta tarbosa suka nufi cikin guiden ɗin dake gefe, don ko ina akwai ƙwayaƙwayin lantarki da suka haske ciki da wajensa da kuma farfajiyar gidan, kasancewar tasan mawuya cin abune Abba ya dawo lokacin kuma duka guards ɗinsa basa nan suna can tare dashi yasa ta kwantar da hankalinta sosai suka sha fitar su har kusan ƙarfe goma sannan ta rakosa bakin gate ya wuce, bai fi mintuna biyar da fita ba comboi ɗin motocin Abba suka shigo shima ya dawo, lokacin tana ƙasa ita da Nihal suna kallo, yana shigowa Nihal ta miƙe cike da fara'a ta je ta rungume sa tana yimasa sannu da zuwa kamar yanda ya saba mata, yayin da Janan ta taso ta karɓi jikkar hannun Jazz haɗe da ɗan russunawa, ta ce, "Abba sannu da zuwa" "Yawwa Janan ya faɗa tare da buɗe mata ɗaya hannun sa ta shiga itama ya rungumeta" fuskarsa cike da fara'a yake kallon ta tamkar ba shi ba kafin yace, "Janan anturo saƙo through account naki, hop kin gani ko?" "A a Abba ban lura ba" "Ok ki duba ki gani, zaki ga alart ɗin 300thousand Naira, idan kin gani saiki sanar dani ko zuwa gobe ne zanyi maki bayani" "To Abba Nagode ALLAH ya saka da alkhairi" ta faɗa ba tare data kawo komai aranta ba don ya saba yimasu irin wannan kyautar, shiyasa ko kasheta za'ayi yanzu bata san iya adadin kuɗin dake account ɗin ta ba, saidai wannan karon kuɗin sunyi yawa, ko me zatayi dasu, oho ta bawa kanta amsa tare da bin bayansu riƙe da jikkar, "Abba nawa fa?" Nihal ta faɗa don duk lokacin da zai tura masu kuɗi tare yake turawa sai dai na Nihal sukan ɗara na Janan yawa, shiyasa da bata ji yayi mata magana itaba ta tambayesa cike da shagwaɓa, ita dai Janan ajiye masa jikkar sa tayi ta fito ta koma inda take ta zauna, sai da Abba yayi murmushi yana kallon Nihal sannan ya ce, "Sorry my dota, zan turo maki naki anjima, zan kuma haɗa maki da wuɗanda za kiyo maku sayayyar kayan da zaku saka" "Noo..Abba muna da isassun kayan sawa fa, indai sune kawai kabar kuɗin ka, nasan Janan ma idan kayi mata bayani zata maido maka dasu" har zai faɗa mata cewa ai Janan sadakin tane ya ba Asgar account no ɗin ta ya turo mata, sai ya tuna irin shaƙuwar dake tsakaninsu zata iya zuwa ta faɗa mata duka plans ɗin ta su rushe, don haka sai kawai ya basar da zancen ya ce taje ta faɗawa Madam florence ta haɗa masa dinner kafin ya fito wanka don yunwa yake ji, bayan ta fito ya furzar da wani iska a baki tare da nufar gefen show glass ɗin da aka jire kayan haɗin coffee da tea ya fara haɗa ruwan Lipton masu ɗan zafi ya sha saboda hanjin sa su saki don tun safe baici komai ba sannan ya wuce ya watso ruwa, ko daya fito har Madam florence ta gama haɗa komai tana gefe tsaye tana jiran fitowarsa don tayi serving ɗin sa, yana ƙarasowa saye da bathrobe ta ja masa kujera ya zauna sannan ta shiga zuzzuba masa abubuwan dake akwai wajen tare da tsiyaya masa ruwa a cup ta ajiye, har zata tsiyaya masa lemon juice ya ɗaga mata hannu haɗe da cewa, "You can go" ta ɗan rissina cike da girmamawa sannan tabar ɗakin. A ɓangaren Janan kuwa koda ta dawo sha'anin gabanta ta shiga yi ba tare data duba alart ɗin da mahaifinta yayi mata zance ba don gaba ɗaya itama ta manta da maganar sai yau da safe data gama waya da mm dake kan hanya, Cas taga kuɗin 300thousand kamar yanda mahaifin nata ya faɗa mata, saidai ga mamakinta kamar sauƙin ba daga mahaifinta bane don ba same bank ne da nashi da yake turo masu ba, ɗage kafaɗu tayi ta cilla wayar a gefe sannan ta koma baccin ta. ***. ***. ***. Ko da mm ya isa ƙauyen charanci ƙarfe sha biyu na rana, mashin ya hau aka ƙarasa shiga dashi can cikin ƙauye don bada motarsa ya zo ba ta kasuwa ya shigo, tun daga wajen garin ya fara ganin sauye sauyen da ƙauyen ya samu har zuwa bakin shigowa ciki, tsaida mai mashin ɗin ya yi tare da sauka ya nufi wajen da har ya mutu bazai taɓa manta shi ba, gaba kaɗan da wata bishiya daya riski mahaifiyarsa a wajen kafin ta rasu, wasu zafafan hawaye suka fara sauka a idanuwansa tuno yanda abubuwa suka faru a waccan ranar a kuma shekarun baya, kuka ya riƙa yi sosai haɗe da nemarwa mahaifiyarsa gafara da agaban idanuwansa ta mutu kafin ya miƙe ya koma ya haye mashin ɗin su nufi cikin ƙauyen, tun da suka shiga ya fara hango yanda waccan ranar mutane ke gudu, manya da yara, mata da maza da kuma tsofaffi, ganin jiri na shirin ɗibarsa yasa yayi saurin dafe kai tare da runtse idanuwansa, anan ma gungun ɓarayin ya hango yanda suka riƙa tunkaro su a waccan ranar da sauri ya buɗe idanuwa yana mai karanto duka addu'o'in daya sani a bakinsa sannan ya samu natsuwarsa ta dawo masa, kai tsaye gidansu yace mai mashin ɗin ya nufa inda yayi ta yimasa kwatance, basu wani sha wahala ba don kusa yake da masallacin dake ƙauyen suka iso, gidan na nan yanda yake na ƙasa kamar yanda suka barshi, amma masallaci da sauran gidajen dake kusa dashi duk an canja gine-ginen su, ya ciro ɗari biyar ya miƙawa mai mashin ɗin yana ƙarewa wajen kallo, canji ya miƙo masa ɗari uku da hamsin ya ce ya ɗauka duka ya bar masa, mutumen nata godiya, Har zai tafi mm ya dakatar dashi haɗe da nuna gidan su da hannu ya ce, "Bawan ALLAH masu gidan nan nake tambaya" sai da mutumen ya ƙwalalo idanuwa kafin yace, "Wannan gidan, masu shi kake tambaya?" "Eh" "Tab, to nidai tun tashi na ban taɓa ganin wani mahaluƙi a cikin sa ba, abunda kawai bazan manta ba shine, ance asalin gidan na yayan limamin masallacin nan ne, wanda ɓarayi suka shigo a shekarun baya suka yiwa yankan rago" da sauri mm ya runtse idanuwa jin yanda kalmar ta daki zuciyarsa da yanda ya ga mahaifin nasa kwance cikin jini lokacin, yana jin mutumen ya ci gaba da cewa, "Banda wannan labarin bansan komai ba akan wannan gidan, kuma na tabbata babu masu shi yanzu inba aljanu ba" "To don ALLAH ina ne gidan limamin?" "Gashi can inda kaga bishiyar can, ba wani nisa ne da akwai ba balle na kaika" "To shikenan na gode" mm ya faɗa tare da miƙa masa hannu suka gaisa sannan ya nufi gidan, kasancewar ƙarfe ɗaya na rana ya kusan yi da kuma sauyawar lokaci saboda damana yasa ko daya isa ƙofar gidan ya tadda wani dattijo na arwala, sallama yayi masa haɗe da miƙa masa hannu suka gaisa bayan ya gama yana ƙare masa kallo, tabbas bazai manta wannan fuskar ba, ko waye shi ya tabbata yana da alaƙa da mahaifinsa don yana ƙarami yakan yawan ganesa a tare dashi, "Ɗan samari yi magana lokaci na ƙurewa masallaci nake son zuwa" tamkar wanda ya farka daga mafarki yayi firgigit haɗe dayin ƴar gyaran murya ya ce, "Ammm, dama limamin masallacin nan nake nema shine aka nuno mun gidan nan akace nan ne gidan sa" "To..to..to ALLAH sarki, ai nine, Amma kafin nan ɗauki ruwa ka gasu nan a buta kayi arwala sai mufara yin Sallah tukuna, daga ina halama ɗan saurayi?" "Katsina baba" ya bashi amsa yana ƙoƙarin gano kamanninsa daya sani, "Ahh..kasha hanya, sannu dazu" "Nagode Baba" "Idan ka gama arwalar ka shigo ayi sallah sai mu zauna idan na dawo ko" "Eh." Ya bashi amsa ataƙaice tare da ɗaukar bitar daya nuna masa ya fara arwala yana kallon yanda dattijon ke tokara sandar sa a hankali har ya isa masallacin, dama suna tsaye ladan yayi kiran Sallah, don haka dattijon na isa ya tada iƙama aka tada sallah, da sauri ya ƙarasa arwalar ya shiga masallacin aka daidaita sahu tare dashi.... _DON ALLAH DA GIRMANSA INA BARAN ADDU'O'IN KU GA MAHAIFINA DAKE CIKA SHEKARU UKU YAU DA RASUWA DAGA BAKUNAN KU MASU ALBARKA, UBANGIJI ALLAH YA RAHAMSHESA DA DUKKANIN MUSULMI DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA😭😭👏_ *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 45_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ********* *GODIYA MAI TARIN YAWA AGAREKU MASOYANA, NA GA ZALLAR KARAMCI DA TARIN ƘAUNA DAGA WAJEN KU BISA ADDU'O'IN KU GA MAHAIFINA, NA GODE NA GODE SOSAI ALLAH YA SAKA MAKU DA MAFI ƘOLOLUWAR ALKHAIRI YA KUMA JIƘAN NAKU IYAYEN WUƊAN DA SUKA RASU, WUƊAN DA BASU RASU BA KUMA ALLAH YA TSAWAITA MAKU RAYUWARSU CIKIN AMINCINSA YA TARAMU DUKA A ALJANNAH FIRDAUSI RANAR GOBE ƘIYAMA, ONE LUV* ♥️💋 ______________________________ Bayan sun kammala Sallah mutane duk sun gama fita dattijon ya juyo ya hango mm zaune ya ɗaya hannayensa yana addu'a hawaye na saukar masa a fuska, da alama sai a sahu na ukku ya samu yin sallahr, ɗan tsagaitawa ya yi har saida ya gama addu'ar sannan ya miƙe tsaye haɗe da jawo sandar sa ya nufo inda yake, miƙewa tsaye yayi shima yana ƙarasowa ya miƙa masa hannu sukayi musabiha sannan ya gaishesa cikin girmamawa, Hannunsa dattijon ya ja suka fita cikin masallacin zuwa gidan sa ya ƙwalawa ƴar autarsa Maryama kira ya ce ta kawo masu tabarma da ruwan sha anan soro anyi baƙo, Bayan sun zauna ya bari har sai daya sha ruwa ya sauke ƴar ajiyar zuciyar gajiya dake tattare dashi sannan ya dubesa haɗe cewa, "Bawan ALLAH ka ce daga katsina kake amma kuma baka yi mani bayanin ko kai waye ba da kuma abun daya kawo ka?" "Haka ne baffa" ya faɗa tare da lanƙwashe ƙafafuwan sa yana fuskantar dattijon fuska da fuska tamkar mai shirin ɗaukar karatu sannan ya ci gaba da cewa, "Da farko dai sunana Muhammad Muhriz, mahaifina kuma ana kiransa da malam Muhammad, manomine a wannan garin kuma yana sana'ar saida dabino da ashuwaki, na zo wannan garin ne neman dangin iyayena bayan kuɓutar da nayi a shekaru goma sha takwas da suka wuce sanadiyar shigowar da ɓarayi sukayi a wannan ƙauye suka kashemun mahaifi da mahaifiyata, guduwar da nayi ta ceton raina dana ƙanwata mai suna Razina har wani bawan ALLAH ya taimake mu shine silar zamana Katsina, kuma shine dalilin daya sa na ce maka daga katsina nake" tun kafin ya rufe baki dattijon da hawaye suka cikawa idanuwa ya shiga ƙwalawa mutanen dake cikin gidan kira, "indo, Atika, Talatu Mariya...kuzo kuga abunda nake faɗa maku koda yaushe, kuzo ga jinin ɗan uwana Muhammadu ya dawo gareni, kuzo ku gasgata mafarkin da ako yaushe nake faɗa maku inayi, ALLAH akbar ALLAH kai ne mai iko, kuma kai ne mai yin yanda ka so aduk lokacin da kake so" ya ƙare zancen yana kuka haɗe dayin sujudush shukar, mm kuwa a hankali ya runtse idanuwa wasu hawayen farinciki na saukar masa, tabbas yayi kuskuren rashin neman dangin iyayensa tuntuni, da wataƙil izuwa yanzu farincikinsa ya lunku fiye da yanda yake ji, Dattijon kuwa yana ɗagowa daga sujada mm yaji ya rungumo sa ajikin sa yana faɗin, "Taya akayi ka manta baffan ka haka Muhammad, taya ka kasa tunowa dani bacin kullum tare kake da mahaifin ka shi kuma tare yake dani" hannaye mm yasa shima ya rungume sa haɗe da cewa, "Kayi haƙuri baffa Ali, kallo ɗaya nayi maka na tuna zuwan da mukeyi a wajenka ni da mahaifina, wayon riƙe ko wane irin matsayi ne kake dashi awajensa kawai na kasa tunowa" "Za kace haka tunda kana can cikin birni hankali kwance, tashin hankalin daka barmu aciki kuwa ya kasa sa ka iya waiwayo mu" "Ba haka bane Abba, tunanina ne bai kawo hakan ba sai yanzu, amma daidai da rana ɗaya ƙauyen nan da duk mutanen dake cikinsa basu taɓa fita a raina ba saboda nasan duka ƴan uwana ne" "Haka ne, ALLAH yayi

Chapter 25 of 40