yi har ya kai kan Janan, tsaye ya yi yana kallon yanda take amsa tambayoyin a natse kafin ya miƙa hannu yana jujjuya kwalaben chemicals ɗin dake gaban ta sannan yabar wajen, yana ɗagawa Amira ta sake miƙa hannu zata ɗauki cikin chemical ɗin kawai Janan tasa hannu ta ɗauke ba tare data kalli inda take ba tana duba reaction ɗin da sauran chemical ɗin data haɗa suke bayar wa tana observing amsar ta aciki, wanda ta ɗauko shine na ƙarshe da zata zubawa ta samu amsar da take buƙata, don haka tana zubawa wani irin hayaƙi ya taso sai ga idanuwan ta, saɓanin na sauran ɗaliban da suna zubawa zai basu reaction mai kyau da kuma amsar da suke buƙata, kalmar innalillahi wa inna ilaihirrajiun ta fara furtawa da ƙarfi kafin can ta saki wata irin ƙarar da sai da tasa sauran ɗalibban firgita sannan ta faɗi ƙasa tana wayyo Amira idanuwana, wani irin cira Amira tayi jikinta na rawa haɗe da rugawa zata bar lab ɗin, in tayi nan tayi nan su kuma sauran ɗaliban musamman mata suka yo kan Janan suna ƙoƙarin taimaka mata, jin sunanta da Janan ta kira da ganin yanda Amira ke ƙoƙarin guduwa ya sa supervisor ɗin ya ce a kamata, kafin ya rufe baki har ta fice daga lab ɗin aguje, nan take cikin mazan ajin nasu wani ya bi bayan ta haɗe da ci gabanta ya ɗauke ta mari kafin ta dawo hayyacin ta har wani ya sa ƙafar sa ya sharɓeta ta faɗi ƙasa kanta ya bugi dutsi, suna ƙoƙarin rufeta da duka malaman dake kusa suka dakatar dasu ganin yanda jini ke zuba daga kanta sai faɗi suke a bari su illatata itama don Janan nada good contact da dukkanin ƴan ajin nasu, ba tada abokin faɗa haka kuma abunta bai taɓa haɗa ta da wani ba, shiyasa ran kowa ya ɓaci saboda yanda ƙarara ta bayyana ko ma meye yafaru da Janan ɗin ita ce, musamman yanda supervisor ɗin ke masifa yana a kama Amira kada a bari ta gudu,
Janan kuwa tsananin zafi da masifar da take ji cikin idanuwan ta yasa ta kasa buɗe su sai faɗi take a taimake ta daga ƙarshe ma sai somewa kawai tayi, nan take aka ɗauke ta da ita har Amirar akayi asibiti dasu bayan hukumar makaranta ta kira police ta sanar dasu halin da ake ciki, wanda nan take suka bi bayan motar da aka ɗauki su Janan ɗin zuwa asibiti, ganin tare ake da police ya sa nan take likitoci suka karɓe su aka shiga basu taimakon gaggawa.
Abba kuwa tuni ya ƙara so makarantar sanadiyar kiran sa da akayi aka sanar dashi halin da ake ciki, cike da tashin hankali yake masifa duk da ƙoƙarin tausar sa da shugaban makarantar keyi yana faɗin bazai yarda ba lallai lallai sai an kama kowace yarinya ce kuma ko ƴar gidan uban wace an bima ƴar sa haƙƙin ta idan kuma ba haka ba kama daga kan makarantar har zuwa kan malaman dake cikin ta sai yasa ankulle masa su, daƙyar da suɗin goshi aka samu aka shawo kansa bayan an tabbatar masa da cewa yanzu haka yarinyar da ake zargi ta aikata abin tana hannun hukuma kana ya fice ya yi asibin da akace tana can, mm kuwa yana zaune ya ga kiran Janan wacce basuyi awa ɗaya da rabuwa da ita ba ya shigo, hakan ya sa yana ɗagawa ya ce,
"Ƴan mata na kar dai ace har kin gama exam ɗin?"
Muryar ɗaya daga cikin matan ajin data ɗauki jikkar ta ce ya jiyo cikin kuka tana faɗin,
"Ba ita bace, kazo ka karɓi kayan ta anyi assibiti da ita"
"What?" Ya faɗa da ƙarfi haɗe da miƙewa daga zaunen da yake,
"Me ya samesa?, Tana ina?, Wace asibiti kenan?" Ya jero mata tambayoyin lokaci ɗaya tare da ɗaukar makullin motar sa ya fice daga gidan,
"Amira ce ta watsa mata chemical cikin idanuwa" ita kaɗai ce amsar data iya basa ya tsinke kiran tare da fizgar motar ya nufi makarantar tasu Janan,
Dama tunda abun ya faru gaba ɗaya ɗaliban sukayi submitting ɗin jarabawar haka nan ba tare da sun ƙara iya rubu ko a aciki ba du suka watse, hatta ɗan celebration na ƙare wa da suka haɗa kasa yi suka yi duk suka nufi asibitin suma cike da jimami,
A'isha kaɗai ce ta iya tsayawa saboda ta miƙa jikkar Janan a hannun mm wanda sarautar Allah kawai ce ta kawosa makarantar saboda gudun da yake shararawa, bai wani tsaya ɓata lokaci ba jikkar kawai ya karɓa sai asibitin da aka kai ta daya tambayi malaman dake tsaye a bakin acadamic staff suna sake maimaita maganar aka faɗa masa,
Yana isa ya tadda su Abba suna ƙoƙarin fita da Janan zuwa wata assibiti mai tsada da za a bata kulawa, Amira kuwa da aka goge mata inda ta bugu aka ɗaure wajen bayan anyi mata alluran tetonus, kai tsaye ƴan sandan sukayi arresting ɗin ta suka kamata akan laifin ta watsawa Janan chemical a idanuwa don likitoci sun tabbatar mata da babu wata matsala dake damun ta, kuka takeyi tana faɗin "wlh ban yi mata komai ba, mm don ALLAH ka taimake ni kada su tafi dani, wayyo ALLAH na mm wlh ban yi mata komai ba" wani irin mugun kallo ya bita dashi yana nuna ta da yatsa haɗe da cewa,
"Kiyi fatan kar wani abu ya sami matata, hakan kaɗai ne zai sa na iya sauraren ki" yanda yake kallonta da idanuwansa da suka kaɗa suka yi jajir ya sa hawayen idanuwan ta ƙafewa saboda wani irin abu da ta ji ya taso mata a zuciya, cikin ɗacin rai ta ce,
"Mm kenan ka yarda cewa na aikata abunda ake zargi na dashi, Ka yar da cewa zan iya cutar da ita bayan nasan kaima ba kada tabbaci akan haka?, shikenan, amma idan ma nayi haka ɗin laifin waye?, Waye sila idan ba kai ba?" ta ƙare zancen ƴan sandan na janta tana zillo kamar zata dake sa, da haka suka samu suka tura ta cikin mota sannan suka ja motar suka nufi Police station da ita, ganin ta acikin motar ƴan sanda ba ƙaramin tayar mata da hankali ya yi ba, wanda hakan yasa jikinta yin sanyi tare da fashewa da kuka,
Mm kuwa bayan motar su Abba ya bi yaga asibitin da aka kai Janan, ya so ya tunkari wajen amma ganin Abba ya sa ya kasa saidai ya kira Jabir ya sanar dashi, ba a fi mintuna biyar ba Jabir ya iso wajen hankalin sa tashe shima ya samesa cikin mota, yanda yaga mm ya fita hayyacin sa ya sashi fara ƙoƙarin kwantar masa da hankali sannan ya fice ya nufi wajen daya hango su Abba ɗin da Hajiya dake faman rusar kuka, ko kallon inda Abba yake baiyi ba ya nufi wajen Hajiya yana tambayar ta me yafaru, cikin kuka ta ce,
"Ban sani Jabir, amma duk wanda keda hannu a cutuwar yarinyar nan kada ALLAH yasa yaga daidai a rayuwar sa, Janan ta jarabtu a rayu ina addu'a ALLAH ya bata ikon canye jarabawar"
"Amin Hajiya, ai haka rayuwa take cike da ƙalu bale, haka kuma idan ALLAH nason ɗaukaka bawan sa sai ya yita jarabtar sa, rayuwa kuma da kike gani Hajiya ai makashin ka yana tare dakai, kawai ki kwantar da hankalin ki kidena kuka, duk matakin da ALLAH ya nufa Janan da takai na farin ciki ko ana so ko ba'a so dole zata kai"
"Ni wannan yarinyar da aka ce ta yi mata aikin nan nake so na gani naji me Janan tayi mata ta aikata mata hakan?, Kai ubangiji ALLAH ya ɗebe..." Bata ƙara sa ba Abba ya ce,
"Haba Hajiya, wai meye amfanin wuɗan nan suruttai, kawai kiyi addu'a ALLAH yasa ba abunda ya sameta" ɗan sosa kai Jabir ya yi haɗe da cewa,
"Gaskiya ne Hajiya, muyi addu'a saboda ɗebewa yarinyar albarka bayada amfani, kin san wani lokacin muna tunanin wuta a maƙera ne amma sai a sameta a masaƙa" cikin ɓacin rai Abba ya yo kan Jabir haɗe da cakumo kwalar rigar sa ya ce,
"Me kake nufi da haka? Ko ka manta ita ɗin ƴatah ce" fizge jikinsa yayi tare da cire hannayen Abba daga jikinsa cikin ɓaci rai ya ce,
"To meye na damuwa daga magana?, Ko da yake baka cika sharuɗa da nagartar zamowa mahaifi ba dole kayi shakku akan haka"
"Maganar sa ta fara yawa fa." Abba ya faɗa yana kallon Hajiya,
Kafin tayi magana sai ga likitan ya fito fuskar sa ba walwala, hankalinta ta mayar a wajen sa haɗe da cewa,
"Likita ya jikin nata" girgiza kai ya yi kafin yace,
"Hajiya waye mahaifin ta?"
"Gani" Abba ya faɗa,
"biyo ni office" ya bashi amsa tare da ƙoƙarin wucewa, dakatar dashi Hajiya tayi haɗe da cewa,
"Dukkanin mu da kake gani wajen nan ba bare, shine mahaifin ta ni kuma mahaifiyar ta, wannan kuma da kake gani yayan ta ne, don haka ka faɗa mana ko meke faruwa"
"To shikenan, dukkan ku ku biyo ni office"
Ya faɗa tare da wucewa, kallon su ya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa,
"Ammm...yarinyar ku babu abunda ke damunta yanzu alhamdulillah, sai dai an sorry to say, munyi iya yin mu wajen ganin munyi mata aikin daya kamata amma mun gaza, ba lallai ne ta sake gani da idanuwan ta ba saboda chemical ɗin daya shigar mata a idanuwa yanada ƙarfi sosai, shiyasa kafin a ƙara so asibitin har ya taɓa mata gilashin dake taimakawa idanuwan ta wajen gani da kuma tsinkayar abubuwa"
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" Hajiya ta faɗa tare da fashewa da wani irin kuka, daƙyar da suɗin goshi Jabir ya lallasheta haɗe da janta suka fita, nan likita ya bawa Abba shawarar cewa zasu iya gwada kaita waje ko ALLAH zai sa adace, amma nan ƙasar dai baya tunanin akwai asibitin da za a iya yimata aiki ganin ta ya dawo, godiya Abba ya yi masa sannan ya fito jikinsa a mace jin abunda likita ya faɗa,
Kasancewar babu inda ke yiwa Janan ciwo kuma ba wani rauni ko ƙwarzanewa da tayi a fuska ko cikin idanuwan ta yasa kwanan ta biyu kacal a asibiti aka sallame ta, tunda Janan taji abunda ya sameta ba tada wani aiki kullum sai kuka, Hajiya da Jabir sunyi rarrashi har sun gaji, mm ma ba a magana don duk ya kalleta tausayi take bashi, cikin kwanaki biyu duk yabi ya zabge ya rame saboda damuwar da yake ganin ta aciki, gashi hatta shi taƙi bari ya ganta tun da aka sallamota, kasancewar gidan Hajiya aka wuce da ita Nihal sai dai ta kirata a waya, baifi sau ɗaya zata je a yini dubata ba shima idan taga tana kuka ta dinga yimata faɗa kenan wai tayi haƙuri ƙaddarar tace a haka,
Sosai Hajiya ta shawarci mm da a ɗaya bukin har zuwa nan da wata ɗaya idan Janan ta samu na tsuwa ganin yanda kwanaki keta matsowa don kwana biyu ya rage ɗaurin auren kuma Abba bai fasa shirin sa ba, a cewar sa tunda ba kwance take ba kuma ba wani abu ke damunta ba tana iya tafiya magana da dai sauransu ai ba buƙatar a ɗaga bikin, da Hajiya ta matsa masa kan zancen ɗagawar sai ya ce,
"Ai dama duk wanda bai ji bari ba dole zai ji hoho, wannan kaɗan kenan daga cikin sakamakon bijire masa da tayi ta gani" ranar Hajiya tayi faɗa kamar ranta zai fita, ta ce idan har bijirewa iyaye nasa mutum ganin ba daidai ba shi sau nawa zai ganta?, Jarabawa ce ALLAH ya aiko mata kuma tana yimata addu'a ALLAH ya bata ikon canye ta, a ɓangaren mm ma kuwa ya dage akan baya buƙatar a ɗaga bikin shima ya fiso ayi kawai a bashi matar sa yaje yaci gaba da kulawa da ita,
Hakan yasa a bangaren Momy taci gaba da shirye-shiryen buki hankali kwance tare da addu'ar ALLAH ya nuna mata wayewar jibi lafiya ko hankalin ɗan nata zai dawo a jikin sa, don gaba ɗaya ya birkice masu ko gane ma kansa basa yi saboda tsananin damuwa, abinci ma baya ci sai ta zaunar dashi da kanta tayi masa dole tukana, shima tana basa a baki sannan zata samu yaci kaɗan.
Umma kuwa tun ranar da wani ɗan unguwar su dake class ɗaya da Amira ya je ya sanar da ita halin da ake ciki hawan jinin ta ya tashi saboda tashin hankali, kukan safe daban na rana daban na dare daban, kullum suna kan hanyar zuwa police station wajen ganin Amira kwanaki huɗu kenan amma an hanasu ganin ta, nau'ukan azaba kuwa kala kala anyi mata don ta amsa laifin ta amma ta kafe akan ita bata yi mata komai ba, tun tana saka tsaurin ido da taurin kai ga lamarin har tayi laushi tana yi masu magiya akan su rabu da ita wlh ba abunda tayi mata, musamman umma ta je har makarantar su Janan ta roƙi shugaban makarantar dasu taimaketa a fito mata da ƴar ta ya ce tayi haƙuri case baya hannunsu yanzu, taje wajen mahaifin yarinyar ta roƙe sa shi kaɗai zai sa a iya fiddo mata da ƴar ta ko kuma ya bada izinin abari ta ganta, ba ita kaɗai ba hatta su Zarah kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci irin tashin hankalin da suke ciki, tasan ba tada wata hanya da zata iya ganin Abba balle har ta roƙesa hakan yasa ta haƙura taci gaba da zuwa police station ɗin ko ALLAH zai sa suji tausayin ta su bari ta gane ta, so take yi tayi mata tambaya ɗaya akan ta faɗa mata gaskiya shin da gaske ne ta aikata abunda ake zargin ta dashi, idan har ta tabbatar mata da cewa eh ta aikata to zata haƙura da ita bazata sake waiwayar ta ba har sai bayan an hukuntata daidai da laifinta tunda rayuwar data zaɓawa kanta kenan...
*_Ina matuƙar miƙo sauƙin godiya ta gare ku bisa tarin addu'o'in ku, Nagode sosai ALLAH ya sakawa kowa da alkhairi ya kuma sake tsanan ta mani rabo ta hanyar karba addu'o'in ku, one luv💞_*
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/26, 11:35 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 61_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
____________________________________
Kamar kullum yau ma Umma ta shirya don ta je police station duba Amira duk da ba barin ta ganin ta akeyi ba, kallon ta Zarah tayi haɗe da cewa "Umma ya kamata kiyi haƙuri haka ki zauna gida ki huta, kinga ba ko wata isashshiyar lafiya ne dake ba, tunda har ba barin ki sukeyi ki ganeta ba kibari nake na kai mata abincin"
"A'a Zarah, bazan iya barin ki kije wannan wajen ba, nima don ta kama dole nake zuwa, Al-amin bai kai girman da zan iya tura sa ba ai dashi zai riƙa zuwa, sai yanzu nake ƙara jin ɗacin rashin ya yanku a tare dani domin wajen maza ne suka fi cancanta da zuwan sa ba mata ba"
"Umma dama muna da yaya bamu sani ba?"
Share hawayen da suka zubo mata tayi haɗe da cewa,
"Ƙwarai Zarah, kuna da yaya da kuma ya macce, sai dai ba mahaifin ku ɗaya dasu ba?"
"Amma Umma ya akayi baki taɓa sanar damu ba?"
"Meye amfanin sanar daku tunda ban sani ba suna raye ko sun mutu, wannan cikin da nake fama dashi shine silar daya sani ɗaukar wa mahaifin ku alƙawarin bazan koma ɗauko zancen su ba, saboda aduk lokacin da nafara tunawa dasu ko kuma zancen su komawa nakeyi tamkar wata zararra saboda damuwa, mutum ne shi mai son farinciki na da kuma damuwa da dukkanin lamurra na shiyasa aduk lokacin da na shiga cikin irin yanayin sai ya zamana damuwar sa ta kere tawa damuwar saboda shima yana fama da matsalar hawan jini da diabetes, dalilin daya sa kenan na ɓoye wannan damuwar a raina don wanzuwar nasa farincikin"
"Tirƙashi! Amma umma tunda ba kida tabbaci akan mutuwa sukayi ko kuma ɓata me yasa baki kai cigiyar neman su ba agidanjen redio ko television da kuma gidajen jaridu ko ALLAH zai sa a dace a gane su"
"Ba muda wannan ƙarfin ni da bayin ALLAHn da suka taimake ni, bayan haka tun lokacin dana gudu daga ƙauyen daya kasance asalin mahaifa ta ni da mahaifin su ban koma waiwayar sa ba saboda bana son tunowa da abubuwan da suka faru balle na samo hotunan su, ALLAH na barwa cigiyar su ta hanyar addu'a, nasan matuƙar suna raye wata ran zasu dawo gare ni"
"Duk da haka Umma...." Tari ta fara yi haɗe da dafe saiti zuciyar ta tana jin wani irin zafi, hakan ya sa Zarah dakatar da maganar da take son faɗa tare da miƙewa ta riƙota daga tsayen da take ta zaunar da ita tana faɗin,
"Sannu Umma"
"Yawwa bani ruwa nasha"
Haɗowa tayi har da maganin ta ta ɓaɓɓalla mata ta bata ta sha, a hankali take sauke lumfashi har ta samu ciwon ya lafa mata, miƙewa ta sake yi Zarah ta ce, "Umma don ALLAH ki haƙora da tafiyar nan"
"A'a Zarah, bari naje ai na samu sauƙi"
"Shikenan, amma kuke tare da Al-amin sai ya riƙa maki kwandon"
"To ba laifi" ta faɗa Zarah ta ɗan daki Al-amin a ƙafa dake bacci ta ce ya tashi ya ɗauki kwandon ya raka Umma,
Har sun kai bakin ƙofa Umma ta juyo haɗe da cewa, "Zo kije gidan baba mai ƙuli kafin mu dawo kar ki zauna ke kaɗai"
"To Umma" Zarah ta faɗa tare da ɗaukar mayafinta ta rufo ɗakin suka fita tare, sai da ta raka su har bakin titi sannan ta nufi gidan baba mai ƙuli,
Kasancewar yau Lahadi mafiya yawan police ɗin dake aiki wajen Christian ne duk suna coci ya sa police station ɗin yin tsit sai ɗai-ɗaikun hausawan ƴan sanda dake kai da kawo wajen kula da masu laifi da kuma masu kawo ƙorafi, Sajan Maryam ita ta karɓi abincin Amira ta kaimata sannan ta dawo ta zauna tana kallon Umma da kallo ɗaya zaka yimata kasan ba tada cikakkiyar lafiya cike da tausayi, cikin harshen Hausa da bai zauna a bakin ta sosai ba don yare ce ita ba bahausa ba ta ce,
"Mama meke damun ka ne?"
Murmushi Umma ta yi jin abunda ke fitowa daga bakin matashiyar ƴar sandar haɗe da cewa,
"Ba komai ƴatah"
"Mama kadena damuwa akan yaron ka, baya jin magana dambu...uba ne, ka ƙyalesa ka je gida abunka ka huta"
"Ai bazan iya ba ƴatah, kudai taimaka mani ko sau ɗaya ne na ganta, na tabbata ni da kaina zan sa ta faɗi gaskiya"
"Mama! Mama!...yaron ka yana da taurin kai bazai faɗa ba, shiyasa wanda tana tsaye akan ƙararta ta ce kada a bar kowa ya gani shi har sai ya fadi gaskiya"
"Ki taimaka mani kin ji ƴatah"
"Ha! Mama ka rufa mani asiri, bazeyi haka ba, zan dai taimaka maka na roƙa maka shi a waya, idan ya ce, tom ze barki" Sajan Maryam ta ƙare zancen tare da ciro wayar ta tana ƙoƙarin kiran mm saboda gaba ɗaya yanzu shine mai ruwa da tsaki akan case ɗin, Abba tuni ya Bara zancen sai hidimar auren dake gabansa kawai yake, Sajan Maryam kuwa dama tuntuni take jin tausayin kai da komowa ɗin da Umma keyi, kawai dai babu yanda za tayi ne tunda case ɗin a hannun manyan ta yake shiyasa bata taimake ta ba, yanzu kuma basu nan shiyasa take son yin amfani da damar kafin su dawo,
Zaune yake kan kujera ya ƙurawa Janan idanuwa dake faman murmushi, don yau da kanta ta buƙaci ganin sa saboda tayi kewar sa ba kaɗan ba, hannu ta miƙa masa daga kan kujerar da take zaune itama a corridor ɗin dake can gaban falon Hajiya da zai sadaka da bayan gida inda masu aiki ke aiki haɗe da cewa,
"Hubbin ruh ya naji kayi shiru?, Ko ka tafine?"
Riƙo hannun ya yi idanuwan sa na hawaye ya ce,
"Bazan taɓa tafiya na barki ba har sai in ke kika buƙaci haka ƴallaɓiya ta" wani murmushi ya saki mai ciwo a zuciya kafin yaci gaba da cewa,
"A kowane yanayi kyau kikeyi Janany ta, badon makabta abu ce marar kyau ba da nace ahaka ma sai naga ƙin ƙara kyau sosai" ya share hawayen da suka zubo masa da tafin hannu cike da tausayin ta, baya so ko kaɗan tasa aranta cewa ta samu tawaye saboda rashin ganin da batayi, shiyasa ya daɗi hakan cike da son ƙarfafa mata guiwa, murmushi ta sake har lokacin yana riƙe da hannunta haɗe da cewa,
"Kawai kace kan zolaya tane, amma idan haka ne meyasa kake kuka?"
"Janan kuka na na farinciki ne ganin gobe wara haka kin zamo mallaki na" ya ƙare zancen haɗe da sumbatar bayan hannunta daya riƙe sosai tamkar wanda za'a ƙwacewa ita, saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,
"Sam ƙarya bata yi maka kyau hubby, na tabbata halin da nake ciki na matuƙar ƙona maka rai, kayi haƙuri idan kana jin cewa baza ka samu kulawar da kake buƙata a wajena ba, zan ƙoƙarta sosai wajen ganin na baka ita ko da kaso hamsin ne bisa ɗari, amma don ALLAH kada kace zaka bar ni bazan iya jurewa ba"
"Ina neman tsarin ALLAH daga muguwar zuciyar da zata raya mani hakan koda sau ɗaya ne, a tunanin ki wai zan iya rabuwa dake kuma na rayu?, Hmm abunda bazai taɓa yiyuwa bane kuma kidena tunanin hakan ma zata faru, kin so ni so na gaskiya don haka dole ne nima nayi maki TUKUICI da SO mai girma, musamman wannan lokacin da zaki fi buƙatata fiye da ko yaushe.." kafin ya rufe baki wayar sa dake gaban aljihu ta ɗau ruri, da har bazai ɗauka ba tsoron kar ya jefa wa Janan shakku cikin zuciya na rashin ɗagawar ya sa ya ciro wayar haɗe da karawa a kunne bayan ya ɗaga tare da faɗin,
"Hello Sajan Maryam"
"Yes sir, good morning" don lokacin iyaka ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe,
"Morning, tayi magana?"
"No sir, mahaifiyar tace ke neman alfarma daga wajenki tana so tagan shi, pls sir if it's possible abeg help her to see her"
"No sajan Maryam, har sai ta amsa laifin ta tukuna"
"Abeg sir.." kawai taga Umma ta karɓe wayar a hannun ta jiki na rawar ta fashe da kuka, wani dum sun mm yaji gaban sa ya daɗi lokacin da sautin kukan Umma ya saukar masa a kunne, rumƙu hannun Janan dake riƙe acikin nasa yayi tare dajin kansa na juya masa ya yi saurin runtse idanuwa, kuka takeyi tana faɗin,
"Nasan ƴatah mai laifi ce da kuma taurin kai, amma ina roƙonka da kataimakeni kamar yanda ALLAH ya taimake ka ka basu izini su barni na gata ko sau ɗaya ne, ni da kaina zan sa ta amsa laifin koda ba ita ta aikata ba..." kasa ci gaba da sauraren muryar yayi tare da katse kiran, wani irin yana yi yake jin kansa aciki game da Muryar matar nan amma ya kasa gane ko na meye, so yake yayi tunani akan wani abu amma meye ya kasa, koma dai meye bazai taɓa bari Amira tasha bulus ba har sai an hukun tata, duk kuwa taurin kan da zata yi bazai taɓa bari a saketa haka kawai ba,
"Hubby meke faruwa ne?" Janan ta tambaya tana ƙoƙarin lalubo fuskar sa,
"Mtsss...akan case ɗinku ne da Amira, kin san tana Police station kulle kuma taƙi ta amsa laifin ta, to shine wai mahaifiyar ta ke so abari ta ganeta tayi magana da ita, so bazan iya bada wannan damar ba shiyasa na katse kiran da naji mahaifiyar tata ta fara roƙona, bana so ta raunana zuciya ta ko tasa mani tausayin da zan iya yafewa ƴar ta, bana buƙatar hakan ta faru" cikin tashin hankali daya bayyana ƙarara a fuskar Janan ta shiga girgiza kai haɗe da cewa,
"A'a hubby, me Amira tayi kuma? Wannan fa ƙaddara ce ta sameni sam Amira ba tada sa hannu aciki, waye ya kamata?, Wa yace ita ta aikata mani haka? Don me za'a rufeta bisa laifin da bata aikata ba.." ta riƙa jero masa tambayoyin tana kuka tare da girgiza kai, kansa ne ya kulle haɗe da riƙo hannuwan ta ya ce,
"Ban fahimceki ba Janan, wai kina nufin ba Amira ta watsa maki chemical a idanuwa ba?"
"Yau she na faɗi hakan?,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 40