haɗe da jan abincinsa ya fara ci don tun ɗazu ƙamshi ya cika masa hanci,
"Oyoyo my son's, how are you?" Momy da tafito daga kitchen tana tsane hannuwanta da towel ta faɗa tana nufato wajen, miƙewa duk sukayi har da Razina suna kallonta fuskokinsu ɗauke da murmushi,
"Sit down my dearest" ta faɗa tare da jawo ɗayar kujerar dake kusa da mm ta zauna, ko me tagani kuma ta tashi haɗe dasa Razina ta dawo kanta ita kuma ta zauna wacce Razina ta tashi akai tana aza mata plate ɗin abincinta acan ita kuma ta jawo wanda zata ci nata, kamar ta sani dama duk a takure Razina ke jin ta ta kasa cin abincin saboda yadda Jabir ya tsareta da idanuwa,
"Am sorry yau anyi lattin gama abinci ko,ya kasuwar taki?"
"Alhamdulillah" mm dake kallon Jabir daya murtuƙe fuska don Momy ta canzawa Razina wajen zama yana dariya haɗe da sarƙewa, da sauri Momy da Razina suka miƙo masa ruwa har suna rige-rige Jabir ya balla masa harara tare da cigaba da cin abincinsa. Na hannun Momy ya karɓar haɗe da cewa,
"Thank you Momy" ita Kuma Razina ta juya tana kallon Jabir da taga yayan nata ya a zama dariya, 'yar gyaran murya tayi ganin fuskarsa a murtuƙe ya ɗago ta ƙasan ido yana kallonta, ɗaga masa idanuwa tayi alamar mi tana tambayarsa yayi mata murmushin yaƙe kawai, murmushi tayi itama fuskarta na duƙe ƙasa ta ware babban ya tsanta na hannu da mai bi masa kusa da bakinta har haƙora ta na bayyana alamar yayi murmushi, ba shiri kuwa ya saki fuskarta tare da ɗago kansa yana murmushi, ɗago nata itama tayi tare da sake haɗa yatsun biyu tana kaɗa masa kai alamar hakan yayi masa kyau tana kashe masa ido ɗaya, gaba ɗaya ta manta da yayanta da Momy dake wajen sai zuba soyayyar su sukeyi da yaren da ba lallai bane kowa ya ankara ba, karaf taji Muryar Momy a kunnuwan ta tana faɗin,
"What happend my dota?, Har yanzu baki ci abincinki ba gashi har yayi sanyi, ko bakya son shi ne na dafa maki Noodle?"
Cike da jin kunya Razina ta ce, "No Momy is ok"
"Gud, ko yayan ki na takura ki ne?" Da sauri Jabir ya miƙe yana dariya,
"Momy am going ooo.., since kin fara cewa zan takura maki yarinya"
"Yes, i saw you my son, pls don't go but allow her to eat ehm"
Dariya mm yayi haɗe da cewa "leave him Momy, borin kunya yake yi tunda yaga asirinsa ya tonu agunki"
"What?" Ta tambaya tana kallon mm cike da son jin ƙarin bayani daga bakinsa.
"Momy, he and Razina are in luv with each other."
"Heeee.... Muhriz!, Are you serious?"
"Yes Momy, they luv each other, so you have to know so that you will bless them" miƙewa tayi tana rawa tana wani irin yare da bai san me take faɗa ba, da sauri Razina tamike da gudu ta shige ɗakinta zuciyarta cike da farin ciki, kenan hakan na nufin both yayanta da momynta sun amince da alaƙar dake tsakaninta da yaya Jabir?, What a nice day and happy moment, ta faɗa tare da faɗawa kan gado fuskarta na kallon aikin ɗakin ta rufe idanuwa,
Turo ƙofa taji anyi da sauri ta tashi zaune, Momy ce har lokacin tana rawa ta shigo cikin ɗakin tare da buɗe wa Razina hannuwanta ta taso a kunya ce ta shige Momy ta maida ta rufe tana ci gaba da rawarta haɗe da rera waƙa cikin yarensu da ba komai take ganewa ba aciki sai "alhamdulillah" da take ta yawan faɗa.
Ɗago kan Razina ta yi tare da sa hannayenta ta tallabo fuskarta dasu ta ce,
"My dota, am so much luv you, bansan me zan faɗa ba da kika so yarona alokacin da wata taki sa, all i want from you shine ki tabbatar zuciyar ki na sonsa ɗari bisa ɗari, hakan shine zai bani ƙwarin guiwar aura masa ke, saboda dake da shi duka matsayin ku ɗaya a wajena, bana son abunda zai cutar da kowa nen ku, kada kiyi dubin matsayi, alaƙa da kuma kusancin da kike da Jabir ki kasa faɗa mun abunda ke ranki ko kuma ki kasa faɗa mun wani abu idan yayi maki ba daidai ba, idan kika yi hakan i will never forgive you, a duniya babu abunda yafi auren so daɗi, don shi na baro 'yan uwana da iyayena nake zaune anan ni kaɗai ba tare da nadamu ba, so kada wani tunani yasa ki amince da proposing naki da my son yayi badon kina son sa ba, You and him are all the same, don haka bana son kowanenku ya cutu, good blesses you my dear, i will be for ever happy with you"
"Mee too Mom" ta faɗa tare da shigewa jikinta, don ita kam ko kaɗan bata jin zata iya sauya matsayin da Momy take dashi na uwa a gunta balle har ace zata wani yi sarakuna da ita.
#pls Comment
#vote
#Share
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭*
[8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 17_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1235096912?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=n8S4%2BmEJ0uvww2QfSSdZ7OtyqQMlo0mA2fUE4GAg5PeqrZ3h2ODEldkfFDzfhXa6scyO0pOYf5DC%2BD3yEtcHmA5aTrtmS5wyBywDWGVcx0i5ilKsxeU3e8uDelHB1G4n_
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
______________________________
Bakin gado suka koma suka zauna suka ci gaba da firar su gwanin ban sha'awa tana bata labarin irin gwagwarmayar da tasha da iyayenta akan mahaifin Jabir da irin tarin soyayyar da take yi masa, a wannan daren kam komai ya dawowa Momy sabo don har kuka sai da tayi, hatta irin 'yar firar da suka saba yi bayan sallar isham ranar basu samu yi ba, sai dai Momy tasa mai aikinta ta ɗauki cincin ɗin data soya masu ta kai masu acan part ɗin su.
A ɓangaren Jabir kuwa cikin daren ya kira wani abokin aikinsa daya taɓa faɗa masa yana da ƙane dake lecturing a cikin school ɗin tasu Janan ya ce don ALLAH ya sashi ya binci ko masa ko wace ce Janan da duk wani motsi nata a makarantar da kuma su waye da waye suke tare da ita, cikin sa'a kuwa nan take abokin nasa ya lakabi ƙanen sa ya faɗa masa alfarmar da suke nema gun sa, bai yi ƙasa a guiwa ba ya fara sanar dashi ai yasan Janan don a department ɗin su yake karantarwa, sosai ya faɗa masa kyawawan halayen ta da irin haza ƙar daya san ta da ita da sauran abubuwan daya sani dangan ce da ita akan malaman da basu taka kara suka kawo ba, don ashe akwai malaman dake sonta a school ɗin sosai, sanin halin mahaifinta da fuskar da bata bayar ba yasa suka kasa tunkarar ta sai kuma Ingaski daya ɗauki alwashin lasa zumar ta ko tana so ko bata so wanda a gaban shi ɗazu ya kira ta officer ɗinsa ta shiga kuma a gaban shi ta fito da gudu tana kuka, wanda yasan ko shakka babu ɗaya daga cikin munanan halayensa ne ya fara nuna mata, godiya sosai yayi masa sannan shima ya kira mm ya sanar dashi komai, dukkansu sun ji daɗin kyakkyawan shedun da suka samu akan Janan sai dai abu ɗaya ne ya ɓata masu rai, lamarin Ingaski, musamman mm dake jin zuciyarsa na wani tafarfasa, kenan wannan dalilin ne ya jefa Janan cikin ƙunci da damuwa ɗa zun?, Tabbas ko waye shi sai ya nuna masa kuskurensa, kalaman Janan ne suka shiga daɗi masa a ƙwaƙwalwa, lallai ko ba don ita da yake so ba ko don sauran ɗalibbai irin ta zai koyawa wannan malamin darasi, musamman idan matakin da zai ɗauka baiyi tasiri a kansa ba.
Kwaɓa yayi haɗe da jawo wayar sa ya sake kiran abokin nasa ya ce ya tambayi ƙanen sa idan yana da lambar provost na makarantar ya turo masa, cikin mintuna biyar aka turo masa, jikinsa har wani tsima yakeyi saboda ɓaci rai ya dannawa lambar kira,
Jin Muryar provost ɗin dake cike da dattijan taka yasa shi kwantar da murya haɗe da gaishesa, bayan sun gai sa yayi masa bayanin sunan sa da kuma ko waye shi, nan take provost ɗin ya miƙe zaune yana ƙara gaishe sa saboda ba ƙaramin taimako manyan mutane da 'yan kasuwa ke samu gun sa ba ga duk wani abunda ya shafi fita ƙasar waje da sauran su, haka kuma ya taɓa aiko wa da makarantar tallafin naira milliyan biyar lokacin da wajen kwanan ɗalibbai ya ƙone amma dai basusan shi ba, suna dai jin sunansa da irin taimakon da yake bayarwa,
Ba tare da ɓata lokaci ba mm ya shiga yimasa bayani tiryan tiryan akan malaminsu Ingaski daya samu labarin abubuwan da yake yiwa ɗaliban makarantar na rashin ɗa'a wanda a yanzu har yazo kan 'yar uwarsa, don haka yana roƙon hukumar makaranta data ɗaukar masa mataki daidai da laifinsa ko kuwa ya jazawa makarantar gaba ɗaya abinda zai ɓata mata suna.
Haƙuri sosai provost ɗin ya bawa mm tare da tambayarsa sunan 'yar uwar tasa mm ya ce babu buƙatar hakan, kawai suke suyi abunda ya kamata, godiya provost ɗin yayi sannan sukayi sallama mm na kwatanta abunda zai yiwa Ingaski idan ya koma shiga gonar Janan ɗin sa.
Tsabar kishi da takaicin abubuwan da Ingaski keyi a makarantar ranar mm beyi bacci ba har aka kira sallar asuba, sai saƙawa da warwarewa kawai yakeyi, yana gama sallah ya kwanta saboda ya samu ko baccin awa ɗaya da rabi yayi kafin safiya ta waye,
Haka ma ta ɓangaren provost ɗin makarantar abun ya matuƙar ɓata masa rai, duk da yasan ana samun irin wuɗan nan matsalolin a makarantu amma bai taɓa tsammanin kamar Dr Ingaski zaiyi hakan ba, mutumen da gaba ɗaya hurhura ta cika masa kai tako ina, ya tabbata a makarantar ɗaiɗaiku ne kawai bazai haifa ba, saura kuma har jikoki zai iya yi dasu, wannan wane irin lalacewa rayuwa ne? Ya tambayi kansa yana goge zufan daya tsattsafo masa a goshi,
Musamman yasa aka haɗa meeting ɗin gaggawa lokacin da ya isa school ɗin ƙarfe 8 da rabi na safe bayan notice ɗin daya tura a groups na malamai da acadamic staff dake watsApp, koda goma tayi na safe zuwa goma da rabi gaba ɗaya malaman sun gama hallara ciki kuwa hadda Ingaski, dama akwai meeting ɗin da za ayi jibi ƙarshen satin, don haka sai aka maido shi yau,
Sai da aka gama tattauna abubuwa masu matuƙar muhimmanci da suka shafi makarantar sannan provost ɗin yayi gyaran murya bayan ya miƙa gaisuwa ga manya manyan malamai da shuwagabannin ko wane sashe da ɓangare na makarantar, cikin har shen turanci ya ce,
"Kamar yanda kuka sani muna da masu kawo mana rahotanni akan matsaloli dake faruwa acikin makarantar nan da bara gurbin malamai da suke neman lalata mana yaran da muka karɓar amana ga iyayensu, to har wayau ba dena saka idanuwa mukayi ba, muna kalle da duk wasu abubuwa dake faruwa kuma muna gani da ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakai akan masu aikata wannan ɓar nan, in bamu manta ba yaran nan dai ƴaƴan mu ne, ƙannen mu ne kuma jikokin mu, a ta wata fuskar ma iyayen mu ne, domin mata sune tushen al'umma, idan sun gya ru to fa al'umma ta gya ru, idan kuma suka ɓaci to al'umma ta ɓaci, don haka don ALLAH da girmansa mu kiyaye, mu masu isar da saƙonni ne ga wannan al'ummar bai kamata ba ace mu ne ke lalata masu rayuwa da kanmu, mu riƙe girma da matsayin da ALLAH ya bamu akansu, idan ba haka ba to walaƙanci da tozarci na biye damu kowane lokaci, muji tsoron ALLAH mu kama mutun cin mu kafin ya tuɗe a idanuwan su, don ko shakka babu duk malamin da aka koma kawo mana ƙarar sa ko kamashi da wannan laifi hukumar makaranta zata dakatar dashi daga karantarwa kuma ta koresa bayan an tabbatar da anlalata takardun sa gaba ɗaya ta yanda duk makarantar da zai je baza'a ɗauke sa ba, wannan shine tunasarwar da kaɗai nake so nayi a wannan zaman sai kuma wani zaman na gaba idan muna da rai"
Yana gama faɗa ya miƙe ya wuce office ɗin sa sakataren sa na biye dashi ɗauke da takardun da aka gama har haɗa matsaya akan taron da akayi,
Ingaski kuwa kusan hitsare wandon sa yayi, ganin yakeyi kamar Janan ta tona asirinsa akan abunda ya faru jiya, gumi kuwa ya goge ba adadin sa a goshi don har tsiyaya yakeyi cikin jikinsa saboda tsananin tashin hankali, a hankali ya miƙe jikinsa duk yayi sanyi sai ga sakataren provost yazo kiransa, ji yayi cikin sa yayi wata iriyar murɗawar da sai daya samu ya fidda iska sannan yaji sauƙin sa tare da bin bayan sakataren.
Sosai provost ɗin ya rufesa da faɗa tare da nuna masa illar abunda yakeyi da matsalar da zai jawowa makarantar idan be dena ba, ya kuma ce yafita sabgar yaran mutane ya ɗauke idanuwa akansu, musamman yarinyar da aka kamashi jiya ya kira a office ɗin sa yana neman lalata mata rayuwa, idan ba hakan ba kuwa yana gab da rasa aikin sa don ɗan uwanta babban mutum ne kuma zai iyayin komai akanta, mamaki ne ya kama Ingaski jin wanda ma ya kawo ƙora fin ba mahaifinta ba kamar yadda ya yi tsammani, ba tare daya ce komai ba ya miƙe ya fice daga office ɗin jin ya sallame sa hankalinsa a matuƙar ta she, ji yayi gaba ɗaya ya rasa inda zai sa tare da janye duk wani alwashin daya ɗauka akanta don samawa kansa salama,
Gab da zai shiga office ɗin sa kuwa ya hango motar ta tana shigowa kasancewar yau basu da lecture ɗin safe sai ta goma da rabi, da sauri ya juya ya canja hanya tare da fasa shiga office ɗin har sai da ta wuce, da Amira kuma ta samesa akan zancen fatattakarta yayi ya ce ta fita wannan zancen ba ruwan sa shima ya fita, kar ma ta koma zuwa office ɗin sa, idan ba haka ba kuma shiyasan me zai yi mata, cike da mamaki ta fita tana tunanin to meye ya faru haka tare da jin ta ƙara tsanar Janan a ranta, shi kenan yanzu burin ta bazai cika ba akan ta saidai ta haƙura? Wannan wace irin baƙar sa'a ce take da ita, ta ganin samu da rashi a lokaci ɗaya?, haka ta shiga class jiki ba ƙwari ba tare data kalli koda inda take ba.
Shi kuwa Dr Ingaski jingina kansa yayi a jikin kujerar da yake zaune idanuwan sa a rufe yana kallon sama haɗe da jin gaba ɗaya zuciyar sa ta cunkushe masa waje ɗaya.
Janan kuwa duk da ta damu da son ganin mm haƙura tayi don tunda ta shigo makarantar take zuba idanuwa ganinsa amma ko wulgawarsa babu, kusan mayar ta uku inda suke zama amma bata ganesu ba sanadiyar wani irin bacci mai nauyi da yayi awon gaba dashi, shi kuwa Jabir ganin jiya mm ɗin bai samu isasshen bacci ba yasa ya kyale sa bai tashe sa ba, dama yau Razina basu da lectures suka Sha soyayyar su sosai awaya daga ƙarshe ma ya watsa ruwa ya fito abun sa nan wajen parking space itama ta fito suka dasa abur su a inda suka tsaya a waya.
Bai farka ba sai kusan sha biyu da rabi na rana, a gurguje yayi wanka ya fito ya saka kayan su na aiki, ko da ya fito zai je gaida Momy yaga Jabir ansha ƙanan kaya abinsa ana kwasar fira, harara ya balla masa tare da wucewa ba tare da ya ce dashi uffan ba,
"Damn it.." Jabir ya faɗa tare da bugun iska, dariya Razina ta ƙyalƙyale da ita haɗe da rufe rabin fuskar ta da tafin hannuwa, ɗauke fuska Jabir yayi yana hararar ta tare da ɗaya hannu kamar zai yi mata soko akai tayi saurin runtse idanuwa tare da aza hannuwa akai tana faɗin,
"Sorry yaya j, mai dabino"
Har ya sauke hannun Jin takirasa da mai dabino yasa shi gwalalo idanuwa yana kallon ta, cuno baki tayi kafin ta tashi da gudu ranar wajen haɗe da yi masa gwalo sannan ta shige cikin gida, murmushi yayi haɗe da shafa kansa sannan ya miƙe ya nufi part ɗin su yana sauya kayan sa shima haɗe da rera waƙar _Soyayyaaa lubiya, ƙyalƙyalin Zinariya_ 😅, dariya mm daya shigo part ɗin da niyar yi masa masifa akan rashin tayar dashi da baiyi ba ya kwashe da ita haɗe da cewa,
"ALLAH ya shirye ka Jabir, wai baza ka shirya mu wuce inda zamu ba?"
Yana rufe baki Jabir ya fito cikin shirin sa yana gunguni,
"Me kake cewa?"
"Eh ai gaskiya na faɗa, kawai mutum ya koma bainal faqri wal mali, yasin ni na gaji da wannan tallace tallacen dabinon" ya wuce yana wani ciccin magani kamar zai yi kuka, dariyar da mm ke ƙumshewa ce ta kucce masa, ai kuwa ya dinga yi hadda su ƙyaƙyatawa, sai daya yi mai isar sa ya gaji sannan ya fice shima, koda ya je ya samu Jabir bai wajen ya shiga wajen gaida momy.
Shiga yayi cikin motar ya tada ta haɗe da jiran sa har ya fito sannan suka tafi, suna kaiwa bakin gate drivern dake kula masa da motar tare da kawo masu barin dabinon na zaune na kiransu shi da ɗan uwansa, sai da suka gaisa sannan suka karɓa suka wuce suma suka ja motar suka tafi,
Koda suka iso wajen zaman su sun tadda Janan zaune wajen rungume da littafanta tana yi tana kallon agogon dake ɗauke a tsintsiyar hannun ta, wani farin ciki ne ya rufeta amma sai ta juyar da kanta gefe tayi kamar bata ga zuwansu ba,
Kallon sa Jabir yayi shima ya kallesa haɗe da cewa,
"Man..halama ka samu karɓuwa"
"Isar sauƙin jiya ne fa, taya za a yi in sani"
"To da alama fa ka samu shiga don tayi fushi"
"Ai kai ka ja mani koma meye da baka tada ni da wuri ba, da alama tayi kira har ta gaji"
"Koma dai meye jeka ka bata haƙuri, alƙur'an ni na faɗa maka nagaji da wannan tallace dabinon" duk wannan maganganun ƙasa ƙasa suke yin su yanda baza ta iya koyo su ba, gyaran murya mm yayi tare da zagayawa ta gefen da fuskar ta yake haɗe da yin tsaye ya ce,
"Nasan ni mai laifine tunda har na iya isar da saƙona amma na kasa yin sakkon zuwa na karɓesa, ayimun uzuri hakan ya faru ne a sanadiyar nannauyan baccin da yayi awon gaba dani, wanda ko shakka babu kina da sa hannu wajen yin haka saboda kusan kaso tamanin cikin ɗari duka mafarkan ki ne" duk da ɗan haushin da taji hakan bai hanata jin wani sanyi a ranta ba haɗe da cewa,
"Samuwar kyakkyawan sakamakon saƙon ka shine ya haifar da wannan zaman jiran da nake yi maka, tuni zuciya ta amince da mura dan ka ta kuma amince ka zamo abokin rayuwa agareta matuƙar ka shirya hakan, wahala ko rintsi, tsangwama ko tashin hankali, laifi ko fushi, duka baza su sa taja da baya ba, na karɓi uzurin ka amma ina tuhumar ka dalilin hana mani gangar jikin ka bacci? Me yasa hakan faruwa" mm da farin cikin sa ya kasa ɓoyuwa sai murmushi yake yi ya gyara tsayuwar sa haɗe da cewa,
"Tunanin masoyiya ta kuma bar ƙauna ta Janan da hukuncin da zata yanke a kaina shiya haifar da hakan, duk da hakan kuma bata barni ba har sai da ta kawo mun ziyara a cikin bacci na, haƙiƙa zan iya kiran jiya da daren alkhairi don kuwa shine silar wayur yau agare ni da daddaɗan albishir"
"ALLAH da gaske?"
"Sosai kuwa, ya kika tashi?"
"Lafiya klw cike da tunanin ka nima"
"To gani ga kuma ke, shikenan ta tunani ta ƙare ko kuwa"
"Da saura kuwa, don na tabbata yanzu nasa ƙafa akan tunanin ka"
"To shikenan Madam.."
"Zaka fara ko?" Ta katseta haɗe da nuna sa da ɗan yatsa tana cuno baki, kunnuwan sa ya riƙe yana dariya haɗe dayin up and down ya ce,
"Na tuba matata I will never repeat it again" sosai ya bata dariya ta riƙe yancin ta tana yi yayin da shi kuma ya zuba mata idanuwa yana kallo, Amira dake bayan wani icce itama tana dakon fitowar mm ta kwatsa wata irin ƙara tana ji kamar zuciyarta zata fashe saboda abun da idanuwan ta suka gane mata da kuma tsabar kishi dake nuƙurƙusar zuciyar ta...
Pls #Comment
#Vote
#share
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 18_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1235678661?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=TLwR4un%2BsfBZPTtozWHX9UCaKszObmrcnbn8Uh%2BQCqKf6crJfvIK9mcVldRKlLMIjtveDnL0qoJgeE3H2E4jezsFzOHfAUOzDqT4HnEUw1SPpK0Olaum1QL0fNqSByVJ_
*KIN SIYI SHIRIN NAMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SIYA BA MAZA HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN 👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, GWADA KI GANI IDAN KIN YI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADA MA BA ƳAR UWA😍*
______________________________
Da sauri gaba ɗaya suka juya tun daga mm ɗin, Janan har zuwa Jabir dake sallamar wasu 'yan mata da suka zo siya dabino, cike da mamaki suke kallon gefen da bishiyar take tare da hango mutum a jikin ta duƙe, Jabir ne ya fara isa wajen kafin ƴan matan su rufa masa baya sannan Janan da mm suma suka bi bayan su, duƙe take ta saka kanta cikin cinyoyin ta tana darzar kuka, kan kace me tuni taron ɗalibai ya lulluɓe wajen, Jabir ne yayi ƙarfin halin matsawa kusa da ita don duk an zata aljanune ke damun ko wace a wurin jin yanda take gunki,
"Ke baiwar ALLAH lafiya?" Jabir ya faɗa yana ƙoƙarin matsawa kusa da ita, jin ba muryar wanda take tunani bace ya sa tayi banza dashi ba tare da ta ce ƙanzil ba balle har a sa ran zata ɗago tayi magana, Janan ce ta ƙara so wajen kasancewar sai yanzu ne ta tuna cewa Amira ce fa ta gani saye da irin wuɗan nan kayan yau, a hankali ta miƙa hannu cike tsoro tana ƙoƙoƙarin taɓa ta haɗe da cewa "Amira..." Ai kuwa kafin ta rufe baki tana jin muryar ta tayi wani irin kukan kura tayo kanta don dama cike take da ita tana faɗin,
"Baza mu ƙyaleki ba, sai mun kashe ki.." zaro idanuwa mm yayi a daidai lokacin da Amira ta kaiwa Janan wata irin shaƙura, yana faɗin,
"Subhanallahi, don ALLAH ku taimaka" tare da nuna su yana kallon ƴan matan dake wajen, ga mamakin sa kawai sai yaga duka sun dare suna ihu ko wace ta kama gaban ta, ɗaiɗai ku ne suka tsaya suna kallon ikon ALLAH suma ɗin sun ja baya saboda tsaron kai,
Janan kuwa abun ma dariya ya bata tayi tsaye tana kallon yanda Amira ke faman cukuikuya mata ɗan kwalin abayar data yi rollin dashi, cike da tsoron kada Amira ta cutar da ita mm ya ce,
"Pls Janan kiyi wani abu mana kada su cutar dake"
"Barsu na gani mm, me zasu iya yimun bacin gaka tare dani, ko sun manta cewa ni ƙawar tace"
"No bazan iya kallon wannan cin zarafin da take yi maki ba, zan fa iya karyata idan na ƙaraso wajen, kawai kiyi wani abun" ya ƙare maganar cikin ɓacin rai yana ji kamar yaje ya fizge Amira daga jikinta ya faffalla mata marora,
Tuni Janan ta fahimci babu wasu aljanu a jikin ƙasar tata don tunda tazo wajen take addu'o'i, kawai pretending ne takeyi, wanda bata san dalilin ta nayin hakan ba, murmushi kawai tayi haɗe da jawota ajikinta ta rungume ta raɗa mata a kunne, "Stop pretending haka Amira, zafa a iya gano ki, me yake faruwa ne haka har kike tunanin ɗaukar wannan ɗabi'ar a matsayin mataki?, Koma dai meye kiyi gaggawar sauya sa don gab yake da zubar maki da mutunci"
Wani irin kuka Amira ta fashe dashi tare da faɗuwa a ƙasa dirshan kamar wata ƙaramar yarinya tana faɗi
"Ke ce silar komai Janan, ko meye ya faru dani ke kika jawo, gaba ɗaya mutanen dake wajen suka maido hankalinsu ga Janan suna kallo cike da mamaki jin abunda ƙawarta ke faɗa, ɗan sinne kai Janan tayi ƙasa tare da takowa ta zo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 40