Ai mun kusa kammalawa a huta"
"Haka ne, nayi kewar ki sosai"
"Nima haka" ta faɗa tare da lumshe ido ta buɗe tana kallonsa.
Sai da suka ɗan taɓa fira ta mintoto ya miƙa mata wata leda daya siyo mata chocculate masu kyau aciki haɗe da cewa,
"Ga tsara bar ki amma ba yawa" ta sa hannu biyu ta karɓa cike da farinciki sannan ta ce, "Na gode sosai, ALLAH ya ƙara buɗi" tare da ajiye ledar a tsakankanin sit ɗin nasu, tana ƙoƙarin tada mota ta hango Amira tafe ita da wasu ƙawayenta ta madubi tana ɗaga mata hannu alamun ta tsaya, da sauri ta bar wajen haɗe da wucewa abunta tana sake regen Amirar ta madubi, kwashewa yayi da dariya don shima yana hango yanda Amirar ke faman ɗaga mata hannuwa amma tayi kamar bata ganta ba,
"Ya haka Madam?, Ba Amira ƙawarki ce na hangowa tana yimaki hannu ba?" Cikin rashin damuwa da abunda tayi, ta ce
"Ita ce mana" tare da juyowa tana kallonsa,
"To ki tsaya mana ki ɗauketa"
"Nop, ba a motata ba mijina na ciki"
"Au kin fara kishina kenan?"
"Dama can inayi, kawai Amira ɗin ce ban fiye damuwa ba don kana ciki idan na ɗauke ta, amma waccan zugar dake tare da ita bazan iya jurar su kalle mani kai ba"
"Me yasa to"
Saida ta tsallake titin sannan ta kallesa haɗe da cewa, "Ka fini sanin koma me yasa" tare dasa dariya, ta so ta fara ajiyesa gida amma ya ƙi wai bai gaji da ganin ta ba, hakan yasa kai tsaye ta nufi gida tare dashi, suna tunkaro ƙofar gidansu ta hango jerin motoci a bakin gate, gaban ta ne yayi wata irin muguwar faɗuwa ta juya ta kalli mm,
"Hubbin ruh kamar motoci nake gani a ƙofar gida ko"
"Nima haka na gani" ya faɗa tare da leƙo da kansa ta tagar motar yana ƙare masu kallo, sanin halin dady da tayi ko yaushe baya rabuwa da baƙi ya sa ta basar da zancen tare da kashe motar anan ƙofar gida sannan ta jingina kanta ajikin sit ɗin da take zaune tana kallon sa,
"What Madam?"
"Ina matuƙar ƙaunar ka ya mm, sai nake ji tamkar zan iya rasa rayuwata idan na rasaka"
"To waya faɗa maki cewa zan iya barinki balle har ki rasani Janany ta, ai ni dake mutu ka raba takalmin kaza, komai rintsi komai wuya ina nan tare dake, ke kaɗai ce keda mallakar fadar zuciyata tare da sarrafata yanda kike so"
"Da kuwa na fi kowace macce sa a aduniya"
"Bari in tafi, kije ki huta kin ji" ya faɗa tare da buɗe marfin motar ya fita, da yake itama a gajiye take sosai sai ta fito tare da ɗauko ledar daya bata da jikkar ta, zagayowa yayi ta ɓangaren da take tsaye haɗe da miƙa hannu ya karɓi ledar dake hannun ta yana faɗin
"Bari na rakaki ciki don naga daƙyar kike ɗaukar kayan" ya karɓa duka har da jikkar hannunta ya rataya a kafaɗa, dariya ta saka masa haɗe da cewa, "Ai kuwa zakayi kyau da zuwa anguwa hubby ka ganka kuwa?"
"A'a, nadai ganki keda ke gabana" ya faɗa shima yana dariyar suka jera tare suka shiga ciki,
Daidai lokacin Asgar ya fito sanadiyar kiransa da akayi ga waya, ya fito da sauri yana ƙoƙarin ɗagawa saboda muhimmancin kiran, karaf idanuwansa suka sauka akan Janan dake ƙoƙarin ciro jikkar ta a kafaɗar mm tana dariya haɗe da cewa,
"Thank you ya hubby, sai munyi waya"
"Thanks you too wifey nah" shima ya faɗa murmushi kwance akan fuskar sa haɗe da miƙa mata ledar sannan ya juya ya bar gidan, har ya kusa kaiwa bakin gate sai kuma ya juyo tare da tsaida ita, ATM ɗin data bashi ranar ya ciro agaban aljihu ya miƙa mata haɗe da cewa, "thank you very much, rilly appreciate your luv and care"
Ƙin karɓa tayi har saida ya buɗe jikkarta dake sagale a kafaɗar ta ya jefa mata aciki tare da matsowa saiti fuskar ta yayi kamar zai yi kissin ɗin ta a chick tayi saurin rintse idanuwa, yayin da Asgar dake can tsaye yana kallonsu yayi wata irin razana da tasa wayar hannun sa faɗuwa, murmushi mm ya yi tare da saka yatsunsa biyu ya ɓalla mata ga kumatu yana faɗin,
"Sai anjima my fear lover" sannan ya wuce, murmushi itama taji ya kucce mata ta shafa chick ɗin nata sannan ta juya ta bar wajen tana dariya tare da maimaita abunda ya ce, "fear lover" ta sake sakin wata irin dariya cike da nishaɗi,
Gabanta ne yayi wata irin matsananciyar faɗuwa ganin Asgar a gaban ta lokacin da take ƙoƙarin shiga daga ciki, fuskar nan tasa a turnuƙe babu ɗigon annuri ko ɗaya saboda wani irin kishi daya turniƙesa ba tare daya damu da screen ɗin wayarsa ƙirar Samsung ML9 daya farfashe ba, cikin dakewa ta raɓa ta gefensa tare da runtse idanuwa jin yana kiran sunanta,
"Janan" ya sake faɗa cikin kaushin murya irin ta jaruman sojojin dake cikin shirin ko ta kwana a kowane lokaci, cak ta ja ta tsaya tana saurarar ko me zai faɗa ba tare data juyo ba, sake ɓaci ransa ya yi akaro na biyu ya juyo yana kallonta kafin ya fara zagayar ta yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, wani iska ta ja ta hanci haɗe da hurzar dashi ta baki kafin ta ce,
"Meye haka Malam, ina lafiya dai ko?"
Murmushi yayi cike da takaici lokacin daya zo daidai ta gabanta ya tsaya tare da sakin wata irin dariya mai ciwo arai kafin ya fara magana a hankali ta yanda ita kaɗai zata iya jiyosa, "Janan, wai don kin san zamu zo shiyasa kika tafi kika yi zamanki a school keda wancan talakan saurayin naki?, Sannan kika sake ɗauki sa kika shigo dashi har cikin gida don ki gwada mani cewa shi kike so bayan kin gama ɓata mana lokaci?" Gyara tsayuwarsa ya yi sannan ya ci gaba da cewa, "Hmm, to idan har kinyi ne don naji haushi nace na fasa auren ki to bazan yi hakan ba, ke infact haushin ma bazan ji ba domin kwanaki bakwai zuwa takwas ne suka rage ki zamo mallakina, alokacin nima zan zamo mamallakin dukkanin wannan kyakkyawar surar taki ko kina so ko bakya so" yakai zancen yana nuna jikinta tun daga sama har ƙasa, ɗan zaro dara-daran idanuwanta da suka soma lumshewa saboda tsabar gajiyar da tayi haɗe da cewa
"Wow!..ALLAH?"
"Kina kokon to ne"
"Gaskiya kam, to wai ma ina shi masoyin nawa zai je lokacin da har zai bari haka ta faru, ina ga dai baka san ko waye shi ba, kuma nakasa irin girma da matsayin da nake dashi awajen sa ba shiyasa ka faɗi hakan" ta ƙare zancen tare da cewa
"Excuse me pls" sannan tabar wajen, a bakin ƙofa ta ja ta tsaya ganin tarin kaya a falon, ya tsine fuska ta shiga yi haɗe da raɓawa ta gefe gefen su har ta wuce tana ƙoƙarin haurawa sama,
"Janan" ta ji Muryar Abban ta dake fitowa daga sashen sa ya kira sunan ta, tsayawa tayi tare da juyowa, alokacin ta hango mutanen dake cike da falon don da farko bata lura da kowa ba banda kayan dake ajiye, a kasalance ta nufo wajensa haɗe da ƙaƙaro murmushi akan fuskarta tana gaishe da Abban nata, sannan ta juya inda ambassador Hussain ke zaune ta gaishesa shima, cike da fara'a ya amsa tare da tambayar ta ya exam ta amsa masa da alhamdulillah, janyota Abba yayi a jikinsa tare da riƙo kafaɗar ta suka nufi ɗayan falon da su Hajiya Jalila ke ciki ya gabatar masu da ita, cikin girmamawa duka ta gaishesu kanta na sun kuye a ƙasa, Hajiya Hassan yayar Asgar ta taso ta rungumota tana faɗin,
"Masha ALLAH amaryar mu, don ALLAH ki taimaka mana ki ajiye wannan kunyar taki a gefe don mun kusa zama abu ɗaya nan da kwanakki ƙalilan ko ba haka ba Aunty Najida"
"Sosai kuwa Hassana, tubarkallah kam gambo ya iya zaɓi, ni kam na yaba ALLAH ya sanya alkhairi" Hajiya Jamila ta amsa da "Amin yaya, nima na yaba sosai saura aunty babba Aunty Jalila
Dariya Hajiya Jalila tayi da tunda Janan ta shigo take yaba kyawon ta da kuma hankalin ta tace,
"Ai Ni kam fin yabawa ma nayi Hajiya Jamila, dama nasan gambo bazai fara ɗauko mana fitsararriya a gida ba wlh, yanzu kam hankalina ya kwanta bari na kira Hajiya Ruƙayya na sanar da ita ɗana ya fita kunya ya samo mana first class" ta ƙare maganar tare da ciro wayar ta, ita dai Janan sauraren su kawai takeyi amma gaba ɗaya hankalinta ya fara barin gangar jikinta, kalaman da Asgar ya faɗa mata yanzu ta ɗauke su a matsayin ta tsuniya sun fara zama gaskiya kenan, juyawa tayi ta kalli Abban nata da tun ɗazu ya koma wajen ambassador Hussain yana faman dariya abunsa hankali kwance sai kuma tayi saurin sadda kanta ƙasa sakamakon wasu zafafan hawaye da ta ji suna zubo mata, cikin zuciyar ta tafara karanto kalmar _Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, Allahummah anta adudi wa anta nasri bika akhul, wa bika asuul wa bika uƙatil_ ya ALLAH ka kawomun ɗauki a lamarin nan ka zamo mani gata, dai dai lokacin Hajiya Zainab da taje yin Sallah itama ta dawo, ganin Janan a tsaye ta kasa motsawa ko nan da can ya sa taje ta riƙota tana faɗin,
"To Hajiya Jalila, ga dai surukar ku nan kun gani hankali ya kwanta ko?"
"Ahhh..Sosai ma kuwa Hajiya Zainab, kuma wlh mun yaba ALLAH yasa ayi munada rayuwa"
Bilkisu ce ta ɗago kai tana kallon Janan dake sunkuye da kai ƙasa har suna haɗa baki ita da Auntynta Hajiya Hussaina wajen faɗin
"Amaryar mu ya kamata kirage kunya don wlh gambo ba kunya ne dashi ba, ba abunda bazai iya tuna duka agabanmu ƙara ma ki saba damu tun yanzu" da yake kusan duk da haka ake kiransa saboda shi ke biwa Hajiya Hassana da Hussaina, sannan wasu ƴan biyun maza dake bi masa da wani namiji ɗaya sannan Bilkisu, dariya duk suka sa kafin aunty zee tayi excusing kansu suka bar wajen ta kaita har bakin upstairs ɗin da zata hawa zuwa ɗakin ta,
"Da alama kin gaji da yawa Janan, kije ki kwanta ki huta, suma yanzu zasu wuce don dama ke kaɗai suka tsaya jira"
"Na gode Aunty" kaɗai ta iya faɗa muryar ta na rawa tare da hayewa sama tana jin wani irin jiri na ɗibar ta, daƙyar ta samu ta ƙarasa hayewa, tana ƙoƙarin shiga ɗakin ta taji an rungumeta wadda tasan ba kowa bace face Janan, cike da farinciki ta ce,
"Wow! Janany sister congrat, ke ɗin mai sa a ce gaskiya, wai kinga kayan auren ki kuwa?, Kinga yanda zinari da azurfa ke magana aciki, gaskiya na tayaki murna sosai" jin bata amsa ba yasa Nihal leƙa fuskarta dake sun kuye ƙasa hawaye na wasar tsere-tsere akai, sakin ta tayi jikinta a mace ganin tana hawaye tayi tsaye tana kallonta tamkar wacce ruwa suka ci, gaba ɗaya ita tama manta da cewa tana da zaɓin da ba wannan daya zo mata ba, ɗago kai Janan tayi tana kallonta cike da mamaki sannan ta wuce ɗakin ta, tana zuwa ta zubar da kayan hannunta haɗe da faɗawa kan gado ta fashe da wani irin kuka mai tsima rai,
Grandma ce data gamo Sallah daga part ɗin Hajiya zee ta faɗa mata cewa Janan ta dawo amma alamu sun nuna kamar batayi farinciki da abunda ta isko ba don hawaye ma taga tana yi ta turo ƙofar ɗakin cike da takaicin Janan, don hakan bazai sa ta dena zargin cewa tasan komai ba,
"Kukan me kikeyi kuma?, Ina shine zaɓin da kika yiwa kanki ke da mahaifinki? Don haka kamata yayi ace kinyi farinciki ba kuka ba" duk da maganganun Hajiya sun dakar mata zuciya hakan bai hanata tasowa da gudu ta rungumeta ba cikin shesshekar kuka take faɗin,
"A'a Hajiya kada kice haka, wlh Muhriz shine zaɓina kuma farin cikina, ni sam bana son wannan kuma ban taɓa son shi a zuciyata ba"
"To taya akayi har aka kai wannan matakin ba tare da kin sanar dani komai ba daga ke har mahaifinki idan har bakya son sa"
"Gani nayi Abba ya dena zancen a wancan lokacin saboda na nuna masa bana son sa akwai wanda nake so shi yasa ban faɗa maki ba" shiru Hajiya tayi tana nazarin maganganun ta tare da saurarar yanda kukan ke fitowa daga ƙasan zuciyar ta kafin tace
"Ya isa haka, amma kin tabbata bakya son sa?"
"Wallahi Hajiya dai-dai da rana ɗaya ban taɓa jin ina sonsa arai na ba, Muhammad ɗinki shine zaɓina kuma mafarkina" sauke ajiyar zuciya Hajiya tayi don ba kaɗan taji sanyi a ranta ba jin cewa Muhammad shine zaɓin Janan har yanzu, ɗan mangare mata kai tayi dake saman kafaɗar ta haɗe da cewa,
"To ya isa haka nace, ja'ira ai nazata halin yaudarar ne naku na mata zaki yiwa Muhammadu na, da kin biya sakamakon hakan daga ke har mahaifin naki, maza share hawayen ki kije ki watsa ruwa kici abinci, shi kuma bari na same sa, duk gama kwashe shirgin su zasuyi suyi gaba, ni dama daga yaron har iyayen nasa basuyi mani ba"
Wani murmushi ta saki duk da har lokacin hawayen nata sun kasa tsayawa tare da komawa kan gadon ta kwanta, ita kuwa Hajiya ta juya ta sauko ƙasa tana ƙara mamakin halin ɗan nata da kullum sai gaba yakeyi ba ya baya, cike da rashin sa a ta samu har sun wuce Nihal kaɗai ce ke faman bubbuɗa akwatunan kayan tana yaba kyawon su
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 51_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
*Haƙiƙa kun faranta mun nima dole na faranta maku, gaisuwa da kyakkyawar fata agareku a kowane lokaci, UMMUL HUSNA, ADAMURASHIDA007, MUM KHAIRY, MMN YASEER, nagode da comment ɗinku ku da ƴan group ɗina na BILLY S FARI NOVEL, nayi farinciki sosai haɗe da samun nishaɗi, ubangiji ALLAH ya faranta zukatan ku fiye da yanda kuka faranta mun yasa aljannah ta zamo tabbataccen wurin zama agareku👏*
_____________________________
"Ke ina Abban naki ne?" Hajiya ta tambayi Nihal tun kafin ta ƙaraso ƙasa, ba tare data ɗago ta kalleta ba ta ce
"Ya je rakasu"
"Tashi kije ki ce masa nace idan basu tafi ba ya tsaida su, saboda na shirin komawa tubƙa da warwara"
"Kamar ya Hajiya" Nihal ta faɗa tana kallonta tare da kulle akwatin dake gaban ta,
"Wannan ba hurumin ki bane, maza jeki dai ki kirawo mani shi.."
Tana ƙoƙarin miƙewa saiga Abba ya dawo fuskar nan cike da farinciki tamkar an yimasa bushara da gidan aljannah, "Bama sai ta je ba, gani injin dai lafiya Hajiya?"
"Ina fa lafiya ga takwarata can sai faman kuka takeyi, ni na kasa gane yanda wannan al'amari yake shiyasa nace aje a kirawo ka idan basu tafi ba su dawo a sake zaunawa gani ga yaron da ita Janan ɗin don mu tabbatar suna son junan su bawai dole za a yi masu ba saboda yanda naga ita Janan ɗin na kuka kamar da akwai wani abu a ƙasa? Idan kuwa haka ne da sake a wannan zancen don bazan goyi bayan abunda babu tabbas akansa ga kowa balle kuma Janan"
Wani irin ras ras ya ji gabansa ya faɗi lokaci guda zufa ya keto masa a goshi cike da tashin hankalin daya bayyanar da hakan ƙarara a fuskar sa, sai daya sa babbar riga ya goge zufan sannan ya kalli Hajiya cikin rawar murya ya ce,
"Na..na..na'am" tare da zuba mata ƙula-ƙulan idanuwan sa yana kallonta, tsuke fuska tayi tana yimasa wani irin kallo mai cike da tuhuma kafin tace,
"Ban gane na'am ba, kai kurma ne ko bada Hausa nayi maka magana ba? Ga dukkan alama akwai abunda kake ɓoye mun, kuma duk ka kuskura ka yimun ƙarya wallahi sai kaji ɗaci na" marairaice fuska ya yi haɗe da cewa
"Haba Hajia, meya kawo zancen yimaki ƙarya anan, wallahi auren nan ba haɗi ne ba, shi ya ganta da kansa yace yana so, kin san halinta abu kaɗan ke sata kuka, wataƙil kukan farinciki ne takeyi ganin wannan gata da akayi mata" ya ƙare zancen yana nunnuna kayan da hannu, cike da takaici Hajiya tace,
"Kai dalla rufe mun baki can, sakaran mahaifi da bazai iya fahimtar damuwar ƴar sa ta hanyar kukan ta ba, to idan har shi yana son ta, ita ka tambaye ta ne tace tana son sa?"
"Amma Hajiya idan bata son sa ai bazan bari a kawo kayan auren ba ko?" Nuna sa tayi da hannu haɗe da cewa,
"Ka ganka babu gaskiya a al'amarin ka, ina ɗazu cemun kayi tun shekarun baya yaron ya ce yana son ta ka tsaya ka gani inda gaske yake yi shine mahaifinsa daya ji suka fito gaba ɗaya haka don su tabbatar maka da gaske sukeyi, kaga kenan ita baka ma tuntuɓeta kaji idan tana sonsa ko bata sonsa ba saboda ka haifeta ko?"
"Wallahi a a Hajiya saida na tuntuɓeta, taya zan yi hakan ba tare da sanin ta ba?"
"Wa ya sani tunda ba damuwa kayi da ita ba balle kuma lamarin ta, to bari na faɗa maka idan har baka sani ba to kasani yanzu, wannan yaro Janan bata ƙaunar sa don haka ka tattara inasu inasu ka mayar masu kaji na faɗa maka"
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Hajiya ina aka taɓa yin haka, har fa invitation duka an bugo jira kawai nakeyi ta kammala karatu ayi abun nan a huta"
"Tirƙashi! Lallai Usman ba kada hankali, ashe dai hasashen da nakeyi gaskiya ne auren dole kake so kayiwa wannan yarinyar? To bari kaji in faɗa maka wallahi baka isa ba, indai ina da rai ko waccen fitsararriyar baza kayiwa auren dole ba balle ita, Janan nada wanda take so wanda zai sama mata farincikin da kai bazaka iya bata ba a matsayin ka na mahaifinta, don haka ban yarda ba kuma ban lamun ta da wannan auren na tauyewa yarinya haƙƙi da farinciki ba, kuma na baka nan da kwanaki uku katabbatar sun kwashe wannan shirgin nasu, wato kai makwaɗaici da abun duniya baya isa kaga dukiya ka ruɗe tunda kai taka baza ta isheka ba ko?, to ni ba dani ba gaɗa a maƙabarta kaji na faɗa maka" tana gama faɗar haka ta miƙe tana watsa masa wani mugun kallo tare da barin gidan, dirshan Abba yayi tare da tallafe kansa yana jin tamkar ya kwatsa ihu, gaba ɗaya ya ma kasa cewa komai ba sai wani irin zufa dake tararar masa tun daga kai har cikin jiki ya sunkuye kai yana tunanin mafita,
Jin ana takowa daga saman upstairs ɗin zuwa ƙasa ya sashi ɗago kai, karafa suka haɗa idanuwa da Janan dake saukowa don ta ɗibi abinci saboda wata irin yunwa da taji tana damun ta, da kallo Abba ya bita har ta ƙara sa saukowa ƙasa kanta a duƙe tana jero addu'o'in neman tsari daga abunda mahaifin nata ke ƙiyasta yimata, don ƙarara fuskarsa ta nuna mata cewa cike yake da jin haushi da kuma takaicinta....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 52_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
_____________________________
Har ta ƙarasa shiga kitchen ta ɗebo abincin Abba na nan zaune a inda yake ya kasa ko motsawa balle kuma yace da ita wani abun, da alama adduar ta tayi tasiri don har ta haye sama bai samu cewa da ita komai ba, lumshe idanuwa tayi haɗe da dafe ƙirji lokaci ɗaya ta saki wata irin ajiyar zuciya tare da isa ƙara sawa cikin ɗakin ta tana mai godewa ALLAH,
Shi kuwa Abba jiki ba ƙwari ya miƙe tare da kiran Madam florence yace tasa a kwashe kayan dake wajen gaba ɗaya akai cikin store a kwatunan kuma a kai su nan sashensa cikin falo sannan ya fice daga falon ya nufi cikin guiden, kasa zaune ya yi balle tsaye sai faman kai da komowa yakeyi yana kwatanta yanda zai fuskanci ambassador Hussain da wannan maganar, mutumen da shi da kansa zai iya bada auren ƴar sa ace wai shi zai koma ya faɗa wa cewa ƴarsa bata amince da auren ɗan sa ba, kai ya shiga girgizawa tamkar wani zararre haɗe da cewa "impossible hajia bazan iya" da in samu matsala da ambassador Hussain ƙara ko mutuwa Janan zata yi idan an ɗaura auren tat mutu, ala bashshi koma meye nasan zai zo da sauƙi akan in hana masa ƴata da kaina don ɗari ta nuna bata son ɗan sa,
Hawaye ne sosai suka riƙa yiwa Janan dake tsaye a jikin window ɗin ɗakin nata kwaranya a idanuwa saboda tausayin halin data hango mahaifinta aciki, da ace soyayyar mm bata riga tayi zurfi da kuma nitso acikin zuciyar ta ba wlh data haƙora dashi, amma kash! Mm ya riga ya zamo jinin jikinta da kuma ruhin ta, jinta ganinta da kuma tunanin ta duka nasane, to taya zata iya haƙura dashi in baso takeyi ta rasa rayuwarta gaba ɗaya ba, wani kukan ta sake fashewa dashi tare da faɗawa akan gadon tana ji tamkar ranta zai fita, tana ahaka Nihal ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, sai data mere baki tukuna ta ƙara sa gaban gadon tasa hannuwa ta ɗago Janan,
"Wai sister meye na wannan kukan haka?, Na rantse da ALLAH duk macen da aka yiwa kayan da aka zuba maki ba ƙaramar sa'a ne da ita ba, da kin kwantar da hankalinki kinci arziƙi kin juya kin mirgina acikin sa, na tabbata duk yanda kike ganin bakya son sa da sannu sai kin koma son sa fiye da tunanin ki, itama duniyar nan indai akace ga wuri mai kyau, ci da sha mai kyau, sutura mai kyau da sauran abubuwan more rayuwa tofa shikenan mutum baida wata sauran matsala a rayuwar sa, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki wlh zaki ji daɗin zama da kuma rayuwar aure dashi" cikin kuka Janan ke kallonta haɗe da jan majina har ta kai aya,
"Adda kenan! Wlh kin bani mamaki, ban taɓa tunanin a fasa ƙanƙara aga tsakuwa ba, ban taɓa tunanin son kan da kike dashi yakai haka ba!, Ina alƙawarin da kika yimani cewa zaki tsaya tsayin daka a matsayin ki na second mother wajen ganin Abba ya aura mun wanda nake so? Ina duka soyayya da ƙaunar da kike nuna mun?, Ashe duk na ƙarya ne bada gaske kike ba?"
"No Janany, Ni ina nuna maki inda zaki je ki huta ne bawai rashin so ko ƙauna da ba"
"Idan har haka ne wannan shine dataccen lokacin daya kamata ki tabbatar mun da haka, kamar yanda nasha gaya maki akoda yaushe bana son Asgar, kuma sam bana ƙaunar sa, da kike zancen kayan da suka kawo kuma ai bani na sasu ba balle har kyansu ko tarin yawansu ya jani nafaɗawa soyayyar sa"
"Duk da haka ya kamata ki fahimta, shi arziƙi sai wanda ALLAH ya so yake ba, wanda bai so ba duk yanda muke sonsa bazai taɓa yinsa ba, kiyi amfani da lokacin ki da kuma ƙurciyar ki ki rayu cikin arziƙi da wadata kamar yanda kika ta so, idan ba haka ba wlh tarin dana sani da nadama zasu iya biyowa baya ki domin ita dama takan zowa mutum ne lokaci ɗaya, kuma da kike zancen so so meye amfaninsa idan babu abunda za a iya rayasa da ingantasa?"
"Tabbas babu, to amma tunda kinsan haka mezai hana ke kiyi amfani da damar dana saki kije ki auri Asgar ɗin ta yanda zaku inganta rayuwarku" dariya Nihal tayi tare da tafa hannuwa kafin tace,
"Rufamun asiri, ai bani yace yana so ba balle haka ta faru, sannan kin manta cewa ni inada zaɓi?"
Tsaki Jannan ta ja haɗe da komawa ta kwanta tana faɗin,
"Sam ba kyada alƙibla Adda, zaɓi yafi zaɓi ne? Ko kuma kin manta yanzu kika gama faɗa mun cewa so baida wani amfani"
"Amma ai ni zaɓina nagartacce ne, wlh ko ke kika ganesa zaki san cewa bazan yi dana sanin kasancewa atare dashi ba har iya ƙarshen rayuwata"
"Mtsss wannan shine labarin ƙanzon kurege, ki bari har sai na ganshi tukuna na gane hakan, Adda wlh sai kinyi nadamar waɗan nan maganganun duk ranar da kika
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 40