Share this page
na gaji da rayuwa hakan ba tare da kowa dangi na kona mijina ba, aduk lokacin dana tuna hakan abun yana damuna sosai" ta ƙare zancen kamar za tayi kuka, a hankali mm ya shiga shafa bayan hannuwan ta dake riƙe da nasa alamun rarrashi haɗe da cewa, "Calm down Momy, by God grace komai zai zo ƙarshe, You see, atimes abubuwa na cakuɗewa mutum waje ɗaya adaidai lokacin daya kusa cimma nasara arayuwar sa, to a wannan lokacin shi kuma sai yayi ƙoƙarin tsanan ta haƙurin sa sosai saboda cimma nasara, yanzu haka jikina na bani cewa lokacin yin farin cikin ku ya kusa bayyana da yardar ALLAH" cike da tausayin halin da suke ciki gaba ɗaya ta ɗora hannunta a gefen fuskar sa tana faɗin, "How my son? bayan yanzu ne damuwa ke sake ƙoƙarin fuskan to ni saboda halin da yarona zai iya faɗa wa akan soyayyar sa?" "Kar ki damu da hakan Momy, ai dama farin cikin wasu na wanzuwa ne a yayin da wasu ke cikin baƙin ciki, na tabbata wannan damuwar tawa da sannu zata zomo mana farin ciki da yardar ALLAH, domin alamu sun nuna cewa cike take da abubuwan da zasu zamo silar walwalewar matsalolin mu baki ɗaya" ya ƙare zance yana murmushi tare da ɗora hannunsa akan nata dake kan fuskarsa, jiki a mace ta ce, "Ina fatar haka my son, amma su ɗin ne suna da matuƙar matsala sosai" "Momy karki dami, in Sha ALLAH, ALLAH zai shige mana gaba" yana gama zancen ya miƙe ya bar falon shima jikin sa ba ƙwari, A taƙaice dai dashi har Momy daren basu runtsa ba saboda tunanin me zai iya faruwa aduk lokacin da Abba ya san cewa shima mm ɗin matsayin ɗa yake a wajen ta, ganin ba suda wata mafita banda addu'a yasa kowanen su ɗauro arwala suka shiga faɗawa ALLAH dukkanin damuwowin su da buƙatocin su saboda shi kaɗai ne zai iya yi masu maganin su, washe gari misalin ƙarfe goma da rabi mm na bacci Janan ta kirawo wayar sa, miƙa hannunsa yayi ya lalubo wayar haɗe da ɗaga kiran ya aza akunnen sa yana cewa, "Hello janany tawan" cikin muryar bacci yake maganar duk da bai kalli wanda ya kira wayar ba amma ya gane cewa ita ce saboda ringing ɗin daya saka mata daban yake dana kowa, murmushi tayi da har sai da ya jiyo fitar sautin sa a kunnuwan sa sannan ta ce, "Barka da hutawa yallaɓai, kar dai ace har yanzu baka tashi bacci ba?" "Kamar kin sani, amma dai gashi kin tadani yanzu, ya kike?" "Lafiya klw, ai mun abufuwa in tuba, ko da yake alamu sun nuna cewa ka daɗe baka kwanta ba jiya shiya saka kaiwa wannan lokaci baka tashi ba, saboda haka na ƙalubalance ka akan haka, me yasa?" "Tunanin ki mana ranki shi daɗe, ke san ke ce duniya ta, shiyasa matuƙar tunanin ki bai barni runtsawa ba to fa ban isa nayi hakan ba" Duk wannan wayar da suke yi tana kan shirin ta na zuwa makaranta ne wanda daga nan take so su haɗu a can gidan grand ma dashi, kallon kanta tayi ta madubi don shigar yau da tayi ta musamman ce wa masoyinta shi kaɗai, man baki dake ajiye akan madubin ta ɗauka ta muttsiƙawa bakin ta tare da rolling idanuwanta ganin yanda tayi kyau gwanin burgewa, murmushi ta saki jin abunda ya faɗa, cikin shagwaɓe murya ta ce, "Kai hubbin ruh, kada ka fasa mun kai da yawa fa!, ni Janan ni nafi cancanta dana kira ka duniya ta domin babu wanda nake gani sai kai, haka kuma kullum wayewar safiya tunanin ka shike zamowa annurin dake haska duniya ta" "Hmmm! Naki kika sani yarinya, bari rai da lafiya suyi mana faɗa sannan mu jira yi zuwan lokaci, a sannan ne zaki tabbata kuma ki faɗa da bakin ki cewa tabbas ke ɗin nan ke ce duniya ta saboda yanda zan mallaka maki duka ragamar rayuwata, Janan yanda nake jin soyayyarki araina zan yarda na rasa komai a duniyata in dai zan same ki, Ni Muhammad Muhriz ina matuƙar sonki sosai" lumshe idanu tayi cike dajin daɗin kalaman sa ta ɗauki jikkarta ta rataya tare da saka takalman ta masu ɗan tudu sannan tace, "Ya Muhriz, nima ina son ka irin son da nake da tabbacin babu wata macce aduniya da zata taɓa iya yima wani namiji shi, haƙiƙa ni ɗin mai sa a ce aduniya dana sameka matsayin masoyin raina, haka kuma ina godeya ga ALLAH daya zaɓa mun kai acikin jerin maza je, wanda na tabbata hakan ba iyawa ta bace ba kuma cancanta ta bace, bisa haka nake roƙon ALLAH daya ci gaba da bani tsaro da kariya acikin burnin zuciyar ka ni kaɗai domin na samu damar yi masa cikakkiyar godiya da ni'imar daya yi mani ta samun ka" "Janan kenan, ai kisa aranki Ubangiji ya riga daya amsa addu'ar ki da daɗewa, domin gaba ɗaya gangar jiki, ruhi da kuma zuciya sun gama shaida cewa ke ce ta farko kuma ke ce ta ƙarshe azuciya ta, ni ɗin naki ne ke kaɗai bada kowa ba, sannan zaki ci gaba da kasancewa aburnin zuciya ta ba tare da kin samu karɓar baƙuncin kowace irin halitta ba har abadan abada" "Madallah da wannan kyakkyawar safiya mai cike da kyakkyawan albishir daga bakin masoyin daya zamo mamallakin wacce ke sauraron sa, kunnuwa sun gaskata zancenka haka kuma zuciya ta yarda da kalaman ka, shi yasa baki yanke shawarar yin godiya agare ka bisa wannan karamci da halacci da kayi mun , ina roƙon aminci da yardar ubangiji su lulluɓe dukkanin rayuwar ka da kuma tawan ya kai sadaukin zuciyata, amma kafin muci gaba da magana zan so ka taimaka mun ka tashi baccin nan haka yallaɓai, ko ka manta ne da inda zamu je?" "Ko ɗaya ban manta ba, domin na fiki buƙatar ganin mun isa wajen, sanin da nayi cewa sai kin taso daga makaranta za muje shiyasa baki ji nayi zancen ba, amma bara na tashi yan zun nan na watsa ruwa sannan sai na gyara, zuwa ƙarfe nawa kike sa ran zaki gama lectures ɗin yau?" "Ƙarfe biyu daidai, badon nasan mun fara haɗa C.A ba ma da babu inda zan je sai dai nazo na ɗauko mijina" "To ayi haƙuri dai aje tunda an riga an san da hakan, ina son matata tafito da first class ta yanda itama zata karantar da wasu kamar yanda aka karantar da ita" Dariya tayi tare da rufo ƙofar ɗakin ta sannan ta nufo upstairs ɗin. A hankali take saukowa daga kan upstairs ɗin tana sauraren muryar sa har ta ƙaraso ƙasa, ɗagawa Madam florence kai tayi tana mai faɗaɗa murmushin dake kwance akan fuskarta tare da nufar ƙofar fita tana ɗaga mata hannu, Nihal kuwa dama tuni sun yi breakfast ɗin su da ita tun safe, shiyasa bata tsaya bi takan ta ba ta wuce abunta, wayar ta na a kunnen ta har ta kai bakin motar suna ta ɗanɗasa soyayyar su hankali kwance, tana saka makullin ajikin motar taji muryar mahaifin ta daga can jikin window ɗin ɗakin sa dake sama na faɗin, "Dakata anan ban amince kifita ba!" cike da mamaki ta ɗago kai tana kallonsa kafin ta ɗan ja baya daga jikin motar tana cewa mm dake kan waya, #COMMENT PLS. *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/24, 9:14 AM] Beey Sai dake: _Page 29_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ "Bye hubbin ruh, muyi waya anjima kaji" ta faɗa cikin sigar yanga da shagwaɓa, dariya ya saki don ba kaɗan yake samun nishaɗi ba idan tana yi masa iren-iren wannan shagwaɓar sannan ya ce "Ok babynah bye, I luv you..." "Luv you too hubby" itama ta faɗa tare da kashe wayar, daidai lokacin mahaifinta ya ƙara so wajen don yana gama yi mata magana ya sauko, sadda kai tayi cikin girmamawa haɗe da cewa "Good morning Abba" ba tare daya amsa taba ya miƙa mata hannu yana faɗin, "Miƙo mun makullin motar nan" "Abba saboda me?, Meyasa zaka ce kada nafita ko ka mantane akwai school yau" ta ƙare zancen tana miƙa masa makullin motar ba tare da tayi masa musu ba tamkar zatayi kuka, fuskarsa ɗaure ya amsa haɗe da cewa, "Ban manta ba, ki jira Asgar zai zo ya kai ki, daga yau ban yarda ki sake fita ke kaɗai ba shiyasa na yanke hukuncin Asgar zai zauna anan domin yaci gaba da kai ki makaranta har zuwa lokacin da zaki ƙare" "What?" ta faɗa da ƙarfi idanuwanta na kawo hawaye, Muryar Nihal ta jiyo da bata san lokacin data ƙaraso wajen ba na faɗin, "No Abba, kada kayi hakan domin kuwa kuskure ne, samarin yanzu ba abun yadda bane musamman waɗanda sukayo cuɗanya da 'ya'yan turawa, inaga kuskure ne kace zaka haɗa janan dashi ya riƙa kaita makaranta saboda komai zai iya faruwa, don haka Abba kabata makullin motar ta ta tafi don ALLAH" ta ƙare zance tare da warware hannayenta dake naɗe akan ƙirji ta haɗe waje ɗaya alamar roƙonsa, sinne kansa ƙasa yayi na tsawon saƙwanni kafin ya ɗago yana kallon Nihal ɗin sannan ya juyo ga Janan ya miƙa mata makullin yana faɗin, "Shikenan kiije, amma ki sani idanuwana na akan ki akoda yaushe, idan kika kuskura kika yi wani abun ya dawo kunnuwana zaki sha mamaki" yana gama faɗar hakan ya ƙwalawa Jazz dake tsaye a bakin gate kira, da gudu ya ƙara so wajen cike da girmamawa ya ɗan rissina kai yana gaishesa, ko ta kan gaisuwar sa baibi ba ya ce, "Jazz kubi bayan Janan, kuma ku tabbata daga makaranta babu inda taje har ta dawo, sannan idan wannan yaron yayi kuskuren tunkaro inda take, to ina so kuyi masa abunda ya dace dashi kafin ku dawo" "Ok sir" Jazz ya faɗa tare da tafa hannuwan sa sai ga sauran guard ɗin duk sun fito, Ita kuwa Janan abun ma ɗaure mata kai ya soma yi, duk da tasan haka zata iya faruwa, amma bata taɓa tsammanin Abban nata zai ɗauki matakin da ya yi girman hakan ba, tsaye tayi ta zuba idanuwa tana kallon ikon ALLAH sai faman jawo motoci guard ɗin suke yi kuma wai duk wa ita, murmushi mai cike da takaici ta saki tana kallon mahaifin nata dake tsaye yana jiran su gama cika umurnin daya basu, cikin muryar kuka ta ce, "Abba wai duk wannan abun na meye?, Janan ce fa 'yar ka, ko ka manta ne?" A hasale ya juyo yana nuna ta da yatsa haɗe da cewa, "Wannan sunan tana amsa shine a lokacin data tabbatar wa da kanta cewa ita ɗin 'yata ce, amma a yanzu da take ƙoƙarin bijirewa umurnina bana tunanin cewa ta yarda har yanzu ni ɗin mahaifin tane" "Abba.." da hannu yayi saurin dakatar da ita haɗe da cewa "ya isa haka Janan, bana son jin komai daga bakin ki, kuma daga yau in har kina son fita dole ayi cikin ɗayan cikin biyu, ko Asgar ya riƙa kai ki duk inda zaki je ko kuma su Jazz su kasance atare dake a duk inda zaki, wannan shine" yana ƙare faɗar hakan ya wuce cikin gida abinsa saboda yasan dole guard ɗin zasu aikata abunda ya sa su, da sauri tabi bayansa kamar zatayi kuka Nihal tayi saurin dakatar da ita, "Kada kiyi haka Janan, gaggawa bata biyan buƙata, kin san ko waye Abba, ba zaki taɓa iya dakatar da wannan hukuncin daya yanke ba yanzu, jeki kawai abunki zanyi magana dashi ya janye maki wuɗan nan sharuɗɗan tunda bakya buƙata" "Amma Adda don me..." "Haba Janany sister kije abunki nace, komai zai daidaita" jiki ba ƙwari ta juya ta nufi wajen motar ta ta shiga ta tayar sannan ta fice daga gidan, tana fita su Jazz suka bi bayan ta, ajiyar zuciya Nihal ta sauke haɗe da girgiza kai sannan ta koma cikin gida, kai tsaye falon Abba ta nufa yana zaune saman kujera yana latsar system, bakin ta ɗauke da sallama ta shige ba tare data tsaya ya bata izinin shiga ba, "Abba good morning" ta faɗa haɗe da zaunawa kusa dashi, "Morning Nihal, kin tashi lafiya?" "Lafiya klw Abba, aiki kake yi?" "Eh Nihal, ko zaki taya Abban naki?" "Me zai hana Abba idan har zan iya" ta ƙare maganar haɗe da miƙa masa hannu zata karɓi system ɗin, sai alokacin ya ɗago kai yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce, "I trust you my dota, nasan zama ki iya saboda wasu kayane nake turawa ƙasar Paris da za a kawo mun next month da mutane ke so, sai dai ban sani ba ko za a same su akan lokaci tunda mutane jiraye suke dasu" "In Sha ALLAH ma za a samu Abba, bari na gani" ta amshi system ɗin tana duba kayayyakin shima yana sake nunnuna mata wasu da yanda zata tura su acan kamfanin da yake hulɗa dashi a ƙasar Paris, a hankali take yimasa aikin cikin natsuwa suna yi suna ɗan taɓa hira har ta kammala ya sake nuna mata wani ta shigar masa sannan ya karɓi system ɗin yana faɗin, "Thank you my sweet dota, God bless you" "Ameen Abba, what about my sister?" "ALLAH yayi maku albarka gaba ɗaya, amma Janan has totally change Nihal, kuma nasan ba kowa ya hure mata kunnuwa ba sai wannan ɗan iskan yaron da take tare dashi" "A'a Abba, ka kasa fahimtar Janan ne da kuma soyayyar ta, amma ko ɗaya bata canja ba, Abba na san kai ma kasan ko meye zafin so tunda na san yanda kake matuƙar son Umman mu, kuma kasan yanda nima nake matuƙar shan wahala akan mutumen da bansan ta inda zan samesa ba yanzu!" Ta sinne kai ƙasa haɗe da kasa ci-gaba da maganar saboda wani irin ƙunci da taji ya dakar mata zuciya, ganin hakan yasa ya ajiye system ɗin agefe haɗe da dafa kafaɗar ta ya ce, "Kada ki damu sweetheart, in Sha ALLAH soonest zamu same sa kinji ko?, Kidena saka damuwa a ranki, ko kaɗan bana jin daɗin hakan, sosai ganin ki cikin irin wannan damuwar ke jefani cikin ƙunci" ya ƙare zancen tare da goge mata ƙwallan da suka samu mazauni a fuskar ta, cikin kuka ta ce, "Amma Abba me yasa baza ka dubi lamarin Janan ba itama ka tausaya mata?, Duk da nasan bisa ƙurciya Janan ke al'amuran ta kuma idanuwan ta arufe suke yanzu, amma hakan ai ba zai sa a hanata abunda zuciyar ta ke so ba, Abba tunda shine zaɓin ta kuma shi take mafarkin rayuwa dashi ba wani daban ba, don ALLAH Abba na roƙeka kabar ta ta auresa matuƙar zata samu farinciki tare dashi" "Nihal, babu abunda zaki roƙa aduniya in kasa yimaki shi, sai dai wannan karon kin roƙe sa a ƙurarren wuri, da ace ban riga na zaɓawa Janan wanda zata aura ba kuma na yiwa aminina alƙawarin aura ma ɗan sa ita to dana duba maganar ki, amma yanzu kinfi kowa sanin halina, kaifi ɗaya nake idan nayi magana bana canja wa, beside Janan bata kawo mun irin mijin daya dace dana aura mata ba, gaba ɗaya yaron nan bai dace da ita ba saboda baida arziƙin iya riƙe mun ita, to don me zan biyewa ra'ayin ta na aura mata mutumen da bai gama sanin kansa ba balle duniya da abunda ke zagayen ta" "Haka ne Abba, ba mutumen zaka kalla ba, soyayyar da take yi masa itace abun dubawa, cancanta kuma kai zaka iya mai da sa yanda kake buƙatar ya zamo albarkacin 'yar ka" Shiru ya yi tare da ɗago kai yana kallon ta, sam baya so yaci gaba da kallon ta cikin ɓacin ran dake shimfiɗe a fuskarta yanzu, sannan baya jin shima zai iya janye ƙudurin sa, amma don ya kwantar mata da hankali ya ce, "Shikenan, zanyi tunani akan haka, ina shikenan ko?" "Abba da gaske kake yi?" "Sosai, amma wake nayi hakan" "Na gode Abbana, sai abu na biyu, Abba kasan ko wacece Janan, batun yau ba, tana da matuƙar gudun zuciya akan duk abunda tasan zai ɓata maka rai, saboda haka don ALLAH ka janye mata guard ɗin nan daka saka mata plss" "Nihal kenan, ai ada ne Janan keda gudun zuciya, yanzu ko mutuwar zuciya ta bata gudu saboda yaron nan, amma shikenan zan sa su dena binta, sai dai shi yaron zan ɗaukar masa ƙwaƙƙwaran matakin dako ganin ta ya yi akace yaje inda take bazai je ba" "What ever dai Abba ita kabarta ta sakata ta wala abinta, don guard ɗin can naka suna da matuƙar takura, shiyasa lokacin da nake karatun degree ɗina a alƙalam daka haɗa ni dasu nace ka janye mun su bana buƙata, sun fiye takurawa sosai haddai Jazz ɗin nan mai kama da oduduwa" Dariya Abba ya saki haɗe da cewa, "That's very good, wannan shine tabbacin sun san aikin su kuma shiyasa nake ƙara son Jazz sosai" "Ni dai bana sonsa Abba" "No my dota, kifara son sa don kada kisa abbanki shima yadena son sa, kin kuwa ga korarsa zai yi idan hakan ta faru" Murmushi kawai tayi saboda wani irin yanayi da take jin kanta aciki, ba tare da ta ce komai ba ta miƙe ta nufi hanyar fita tana jin jikin na ta duk ba daɗi, "Nihal.." Abba ya faɗa yana son ganin yanayin da take ciki, kafin ya rufe baki yaga ta riƙe kanta a dai dai lokacin data kai bakin ƙofar fita tana ƙoƙarin faɗuwa, cikin taku uku ya ƙarasa wajen da gudu tare da taro ta ta faɗo a jikin sa, a kasalance ta ɗago idanuwa tana kallonsa haɗe da cewa, "Abba zuciya ta" ta kai hannun nata adaidai saiti zuciyar ta, gaba ɗaya zancen da tayi da mahaifinta akan Janan ya dawo mata da soyayyar masoyinta sabuwa, ji takeyi tamkar zata rasa ranta, banda shi babu abunda idanuwanta ke gano mata a halin yanzu, sai sautin muryarsa dake faman yimata amsa kuwa a kunnuwa, runtse idanuwa tayi hawaye na zubo mata haɗe da cewa, "Abba wlh zan mutu, ina matuƙar son sa sosai, don ALLAH Abba ka taimake ni a nemo mun shi" "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, Nihal bazaki mutu ba, zan sa anemo shi aduk inda yake kin ji ko" "Abba..." Bata ƙara sa abinda take son faɗa ba kawai yaga ta langaɓe masa, hankalin sa a tashe ya shiga ƙwalawa madam Florence kira yana yi yana jijjiga Nihal dake hannunsa, da gudu ta ƙara so ɗakin haɗe da tsayawa bakin ƙofa tana jira ya bata umurnin shigowa...... #COMMENT PLS *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 30_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Wata irin tsawa ya daka mata haɗe da cewa "Madam! Kina so na rasa 'yata ne?, Abeg shigo ki miƙo mun wayata na kira Dr." jiki na rawa ta ƙara sa daga ciki ya nuna mata inda wayar take ajiye ta je ta ɗauko ta miƙa masa tana kallon yanda Nihal ke kokuwa da lumfashin ta wajen fita, hannunsa na rawa ya karɓa gaba ɗaya duk yabi ya ruɗe saboda yanda hankalin sa ya tashi, ganin haka yasa Madam ta miƙa hannu zata kama masa ita ya daka mata wata tsawar a karo na biyu haɗe da ture hannun ta ya ɗauke Nihal cak tamkar wata jaririya yakai saman kujera ya aza sannan ya miƙe ya shiga lalaben lambar Dr da tun ɗazu ya kasa gani, daƙyar ya samu da taimakon ALLAH yaga lambar haɗe da kiran Dr ya ce yayi maza yazo nan gida yana neman sa ciwon Nihal ya tashi, yana kashe wayar ya kalli gefen da madam take ya nuna mata hannu data fita shi kuma ya shiga kai da komo yana jiran isowar Dr, Jiki ba ƙwari Madam florence ta fito cike da tausayin Nihal, wanda aganin ta duk alhakin Hajiya zee ne Ubangiji ke fanshewa akan ta shiyasa ALLAH ya jarabce ta da ciwon zuciya kamar yanda Hajiya zee ke fama dashi saboda yaji irin yanda raɗaɗin keda zafi, duk da ba a jikin sa ciwon yake ba shakka ko babu zai ji raɗaɗin zaginsa saboda soyayyar da yake wa ƴarsa, a zahiri kuwa numfasawa Madam florence tayi cike da jin zafin korowar da ya yi mata, a cewar ta tunda ya san baya buƙatar taimakon ta, to wane kicihin ya sa shi kiranta, cike da takaici ta ƙara sa kitchin abunta taci gaba da aikin ta tare da addu'ar ALLAH ya yayewa Nihal abunda ke damunta, don ita sam ba ta da wata doguwar matsala dasu da zai sa tayi farincikin faruwar wani abu agaresu. Janan kuwa tana kallon su Jazz dake biye da ita ta madubin motar tayi kamar bata san dasu ba taci gaba da tuƙin ta hankali kwance har ta iso bakin gate ɗin makarantar, tana kaiwa ta ciro kuɗi masu yawa ta miƙa wa mai gadin haɗe dayi masa raɗa a kunne akan kada ya bari guard ɗin ta dake biye da ita su shiga, su Jazz da basu san me take cewa mai gadin ba suna ganin ta wuce suma suka danno kai suna ƙoƙarin wucewa, saurin dakatar dasu mai gadin ya yi tare da hana su shiga, a cewar sa hukumar makaranta bata bayar da izinin barin motoci masu baƙin gilashi su shiga ba, sun yi iya yin su har suka gaji amma ya hana su shiga, hakan yasa suka faka motocin su a can gefen titi suka firfito suka taka da ƙafafuwan su har cikin makarantar, kasancewar basu san inda ta nufa ba yasa suka yita yawo har suka gaji basu ganta ba, sai can suka hango motar ta ajiye a ƙarƙashin bishiyar dake bakin department ɗinsu, da sauri suka je wajen suka tsai tsaya a bakin ƙofar department ɗin nasu da kuma inda motar take suna jiran fitowar ta, abun da basu sani ba, tuni Janan tabar makarantar, don tana shigowa bata tsaya ɓata lokaci ba ta ajiye motar ba tare da ta tsaya yin lectures ɗin ba ta nufi ta ɗayan wancan gate ɗin da ake fita ta fita abunta ta tare napep ta haye ta tafiyar ta gidan grandma, Ko da ta shiga ta riski grandma tana waya da madam Florence data kirata tana faɗa mata cewa Nihal ba lafiya amma ankira likita ya dubata ya yi mata allurai ya saka mata ƙarin ruwa, ga tacan har bacci ya soma ɗaukar ta, "ALLAH ya kyauta ya bata lafiya, in sha ALLAH anjima zan shigo na duba jikin nata, ni wannan wahalar ban taɓa ganin irinta ba sai a kan Nihal, taya mutum zai tsiri soyayya da abunda bai san inda yake ba, kuma bai san ta inda zai nemosa ba" ta ƙare zancen cike da takaici tana faman faɗa sannan ta kashe wayar gaba ɗaya, Kallon Janan ta yi ganin ta a ɗan hargitse kamar wacce aka koro haɗe da cewa, "Ke kuma me yake damunki kika shigomun a haka kamar an koro ki?" Ɗan sosa kai Janan tayi da yatsa kafin tace, "Hajia ina kwana?" "Lafiya klw, ya jikin 'yar uwar taki" "Wa kenan hajia?" "Au! kina da wata 'yar uwar ne bacin waccan shashashar da bata san inda kanta keyi mata ciwo ba?" Hajiya ta faɗa cikin ɓaci rai tare da riƙe haɓa, cikin jin haushin abunda ta cewa 'yar uwarta, ta ce "Kai hajia! Don ALLAH kidena ce mata haka, ni daga makaranta ma nake, bansan ba ta da lafiya ba wlh, meke damun ta kuma Hajiya bayan lafiya klw muka rabu da ita yanzu bada jimawa ba" "Oho, ciwon data ɗorawa kanta ne mana, ciwon zuciya dake shirin kaita ya baro, gaba ɗaya yarinya batada aiki sai baƙar kafuwa ita ala tilas abunda take so shi za a yimata saboda gata 'yar gwal 'yar gata, ana ji ana gani aka ƙyaleta ta tabi duk masu son nata ta ci masu mutunci ta koresu saboda shashanci, ai gashinan yanzu ta je tayi gamo da wanda bata san inda yake ba ta faɗa soyayyarsa, waya sani ma ko aljani ne" "Haba Hajiya, bai kamata ki faɗi hakan ba, kin san dai mutum ba zai zauna ya auri wanda baya so ba, In Sha ALLAH da sannu za taga zaɓin ta, kuma ina nan ina yi mata addu'a akoda yaushe" "To ALLAH yayi maku magani, ina ga dai kema ta sammaki taɓin hankalin nata, ALLAH ya baku lafiya kafin ku tsofe agidan naku" Dariya Janan tayi haɗe da miƙewa ta shige bedroom ɗin Hajiya tana faɗin, "Da baki ji daɗi ba hajjajun mu ta mutunci" "Ah to, ai ku kuka jiyo,

Chapter 17 of 40