Share this page
da ita, ajiyar zuciya umman tata ta sauke tare da juyar da kanta tana kallon wayar ta data jefar ƙasa, "innalillahi wa inna ilaihirrajiun, ashe Amira ban isa in faɗa maki ki ɗauka ba? Bana faɗa maki cewa ki fita sabgar Yaron nan ba tunda da bakinki kika faɗamun cewa akwai wacce yake so take son da ba?" "Umma na kasa jurewa ne wlh, kullum safiya sai ƙara son sa nakeyi" "To tunda shi bai ma san kina yi ba don me da bazaki haƙura ba" "Umma ya sani wlh, ya sani yanzu na faɗa masa" "Da kanki?" Umman ta tambayeta tana zaro idanuwa cike da mamaki, "Eh Umma, shine wai yace na haƙura akwai wacce yake so shi, kuma nasan ba kowa bace face Janan" "Ikon ALLAH, to tunda har kinsan da hakan to ki haƙura mana" "Wlh bazan iya haƙura dashi ba umma, ta fasan ni nafara son sa, amma ta je ta munafucceni suka ƙulla soyayya dashi, wlh ko zan mutu bazan bar mata shi ba, sai dai dani da ita kowa ya rasa" Sallallami ummanta ta saka tare da ture kanta dake saman cinyar ta tana faɗin, "Anya Amira lafiyar ki ƙalau kuwa? Kar fa kije ki jawowa kanki fitinar da tafi ƙarfin ki, Janan ba sa'ar yinki ba ce, daga ni har ke kin san dadyn ta zai iya sakawa a ɓatar damu idan kikayi yunƙurin aikata wani abu ba daidai ba, shin ana so dole ne? Kuma ita meye laifinta da zaki ɗauki karan tsana akan ɗa namiji ki ɗora mata" "Ba a yi umma, amma badon ta shiga rayuwar sa ba wlh bazai taɓa rejecting soyayya ta ba, kin kuwa ga ita ce mai laifin" "To tunda an riga da an gama ai sai ki haƙura, ubangiji kema ALLAH ya fiddo maki da wanda ya fishi" "Umma ki dena yimun irin wannan addu'ar, wlh nasan babu namijin da yafi mm a wannan zamanin, kawai dai ki roƙamun ALLAH ya bani shi kuma yasa ya soni ko baya so" "Kinga, ni bazan iya da wannan shirmen naki ba, in zaki tashi muje gidagida ki tashi muje tunda an riga da an bamu sallama, in kuma bazaki tashi ba sai kiyita zama anan, wannan sakarci har ina? Ni da nasan wannan shirmen naki shiya janyo maki baƙar wahalar da kike ciki to da ban kashe kuɗi na a banza a wofi ba wajen kawo ki asibiti da siya maki magani ba na je na biyawa ƙannen ki kuɗin makarantar su, shashashar yarinya" ta ƙare zancen tare da ɗaukikke mata wayar data jefar sannan ta ci gaba da harhaɗa masu kayan su, Tana gama haɗawa sai ga ƙannen Amirar sun shigo saye da kayan su na islamiya, Sai da duk suka je suka gaishe da masu jiki sannan suka iso wajen gadon da yayar tasu ke kwance tana faman kumbura fuska, "Umma ina wuni?, Aunty Amira ya jiki?" Zarah da Al-amin suka faɗa suna kallon ta, wata uwar harara ta dakawa zarah da takai hannu zata ɗauki wayar tata da umma ta ajiye mata a gefenta haɗe da cewa, "Don U..rki in kika taɓa mun waya saina ɓallaki" "Tofah, ALLAH baki haƙuri" "Amin zarah, zo ɗauki kayan nan mu tafi" Umman tasu ta faɗa fuskarta a ɗaure, 'yar hararar Amira itama Zarah tayi sannan ta ɗauki kayan tana cuno baki haɗe dayin gunguni, "Me kika ce?" Ta taso da ƙarfi tana kallon Zarar, "Meta nace?" "Na rantse saina fasa maki baki yanzun nan" Girgiza kai umma tayi kawai haɗe da tasa yaranta gaba tana faɗin, "ALLAH ya baki lafiya, ku tafi muje, idan taga dama ta biyo mu mutafi gida" "Umma an sallame mu ne?" "Eh Al-amin" "To aunty Amira ta warke ne?" "Ba kaga tana fitina bane? Ai ko bata warke ba dole a bamu sallama tunda alamu sun nuna ciwon nata so yake ya koma mata taɓin hankali" "Shiyasa take harara ko umma" "To ai kaima dai ka gani ko?" "Eh, to.." ba ƙarasa ba yaji an ɗauke masa ƙeya, juyowar da zaiyi Amira ce dake biye dasu ya gani bayan sa ta daka masa wata uwar harara, "Parrot, rabamu kona shuraka a wajen" Da yake ƙaramine sosai bazai wuce shekara biyar zuwa shidda haka ba sai ya koma gefen umma haɗe da cewa, "ALLAH ya baki lafiya" "Amin Al-amin". Ummansu dake dariya ta faɗa tare da tare masu keke napep suka shiga suka nufi gida, Amira talakawa ne sosai, amma mahaifinsu mutum ne mai son karatu, gaba ɗaya ya ƙare rayuwarsa wajen kula da karatun yaransa duk da bayada wani ƙarfi sosai, tun daga primary har zuwa Amira dake jami'ah yanzu, noma shine sana'arsa, kuma yakan yisa ne domin rufawa kai asiri ga abunda za a ci da kuma karatun yaran sa bawai don sayarwa ba, Amira itace babba sai zarah dake bi mata da kusan shekaru huɗu tsakani, sannan Al-amin auta wanda Zarah zata bashi shekara kusan takwas, mahaifinsu bai jima da rasuwa ba don shekarar data wuce ya rasu, kasancewar akwai ɗan sauran abun rufin asirin daya bar masu ne yasa suka jima basu shiga cikin ƙunci da halin rashin babu ba sai yanzu da komai ya ƙare, don ma ALLAH ya taimaka umma na sana'ar sai da kayayyakin miya da kuma icce, sannan dukkansu a shekarar ƙarshe suke ta ƙarewa, Amira a jami'a, itama kuma Zarah secondary, Al-amin ne kawai ke primary 2 yanzu shiyasa abubuwan suka zo da sauƙi, duk da haka zaka iya fahimtar irin halin rashin da suka fara shiga ciki saɓanin da da mahaifinsu ke raye. ***. ***. ***. A ɓangaren Janan kuwa ranar yini tayi sukutum a cikin ɗaki ba ruwanta da kowa, hatta mahaifin nata bata koma bi ta kansa ba balle tasan halin da yake ciki, banda saƙawa da warware wa na samowa masoyin ta mafita akan sana'ar daya dace yafara yi yanzu tunda ta dabinon ta tsaya babu abunda takeyi, wayar ta ta ɗauko da miyar buga balance ɗin account ɗin ta na banki don tasan akwai kuɗi sosai a ciki sai ga madam Florence ta shigo, "Good afternoon my dota" ta faɗa tare da tsayawa daga bakin ƙofa, murmushi Janan tayi tana ajiye wayar haɗe da cewa, "Afternoon madam, came in mana" A gefen gado Janan ta nuna mata ta zauna tana kallon ta, ɗan sinne kai Janan tayi ƙasa tana murmushi ganin irin kallon da Madam keyi mata, "Did i do something very wrong madam?" "Yes, upcouse my doughter, that's why i always loving you so much" shiru tayi tana nazartar fuskar Janan kafin taci gaba da cewa, "My doughter, a duk lokacin da zan sameki a ɗakinki haka, kina saurin fahimtar cewa akwai kuskuren da kikayi, but before that! Meya hanaki sauka ƙasa kuci abinci ke da sistern ki? Don't even thinking lie to me?" Ta ƙare zancen tana nunata da hannu, murmushi Janan tayi haɗe da cewa, "Madam!..."sai kuma tayi shiru don tabbas bazata iya yimata ƙarya ba, "Pls tell me, kina fushi dasu ne?" "Kusan haka Madam" "To meyasa? Kin manta duk duniya bakya da wuɗan da suka fisu" "No Madam, but i think each and every person have the right over him self, so i dont see reason why da za'a ce zuciyata bata da ikon son abunda take so bayan ina kallo ake fighting yanda za'a samawa 'yar uwata abunda take so, Madan are we not equal with her?" "You're, but you have to understand them first Janan, you see, they luv you so much shiyasa basa son abunda zai wahal sheki a rayuwa" "I know madam, but this is my life, my heart, ni na zaɓesa and i don't even care with his poorness, a haka nake son na zauna dashi ban damu da duk wani yanayi da zan shiga ba" "You are right amma kisani, kada ki bari komai ƙanƙantar abu ya haɗaki da sistern ki, just let her deserve that respect and love from you, haka ma da ɗinku, ki basa haƙuri because ba kida wanda ya fishi aduniya, and a good child basa bari parent ko elders ɗin su na fushi dasu?" "Ok madam, now what do you want me to do?" "I have already told you naa..., Go down and have your dinner with your sister, say sorry to her and also apologize to your dad" "Shikenan?" Janan ta faɗa tana kallonta haɗe dayin murmushi, Madam florence ita ta ce "Yes, cikenan" sukasa dariya tare, sosai Madam florence ke son Janan koma nace dukan su saboda ba ta da wata matsala dasu musamman Janan saboda sauƙin kanta shiyasa da taji musayar baƙin da sukayi ɗazu ta kuma ga Janan bata sauko ba suka ci abinci ta biyo ta don tasan abun daya farun ya ɓata mata rai, kuma ita kaɗai ce zata saukar ta sauka ba tare da an samu matsala ba, Koda Janan ta sauko ƙasa bata isko kowa a falon ba ta kuma buɗa abincin taga babu alamun ko taɓasa Nihal tayi balle tasa ran taci, hakan yasa ta koma saman ta tura ƙofar ɗakin nata ta shiga, nan ma wayam ta isko ba ta ciki, ƙarasa shiga ciki tayi haɗe da zuwa ta janye labulen tagar dake saiti da garden ɗin gidan dake ƙasa bayan ɗakunan su, hangota tayi kan kujera zaune ta ɗora ƙafafuwan ta akan wani icce da aka yimasa alamar mazauni idanuwanta arufe, da alama ta faɗa kogin tunanin da ya zamemata tamkar ibada yanzu, ba safe balle rana da kuma dare, ajiyar zuciya ta sauke cike da tausayin ta don tasan babu abunda ke addabar ta fiye da daɗin so, wanda da tana da yanda za tayi tafidda ta aciki da tayi, tana matuƙar son yayar tata ɗazu ma kawai tayi abunda tayi mata ne saboda ta fahimci yanda take ji haka itama take ji akan masoyin ta, kuma da zata iya haƙura da farincikinta data haƙura da shi tayi yanda suke so ko don raɗaɗin tunani da damuwa su rage mata don tasan duk abunda takeyi akan soyayyar ta tana yine don guje mata wahala kuma hakan shima so ne, amma matsalar bazata iya haƙura da masoyinta ba ko ɗaya, a hankali ta saki labulen tagar ta sauko ta nufi garden ɗin haɗe da lallaɓawa yanda baza taji motsin ta ba haɗe dasa hannu ta rufe mata idanuwa, Seda ta sauke ajiyar zuciya haɗe dayin murmushi sannan tasa hannu ta riƙo hannun Janan dake rufe da fuskarta tana faɗin, "Janany sister" ta ƙare zancen tare da mai dota a gabanta tana kallo cike da mamakin ta, dariya Janan tayi sannan ta turo baki tana faɗin, "Kai Adda, wannan irin kallo fa?" "Mamaki nakeyi yanda Janany sister ta iya fushi da Adda ɗin ta har take yiwa abinci yaji" "To ke meya hana kici abinci?" "Taya zanci bayan ke baki ci ba, dukkanin abunda kika ga nayi maki ina yine saboda bazan iya jurar ganinki cikin wahala ba, a yanzu na fahimci damuwarki da kuma yanda kike ji aranki and i support your choice tunda shine farincikinki, yanda bazan canja ra'ayinka da kuma zaɓen rayuwar ki ba to haka kada kiyi tunanin zan canja rayuwata ko tunani na akan masoyinki domin kece kaɗai tawa kuma damuwata ba shi ba" Ga mamakin ta kawai taga Janan ta rungumeta haɗe da cewa, "Hakan ma ya wadatar Adda, nasan da sannu komai na iya daidaita in sha ALLAH, thank you so much" girgiza kai tayi don gani takeyi har yanzu ƙuruciya na samun ƙanwar tata shiyasa ta kasa banbancewa tsakanin duhu da haske, walwala da ƙunci, samu da kuma rashi har take ƙoƙarin tura kanta a inda rayuwarta bata dace a can ba, Sun jima awajen zaune suna firar su tamkar wani abun bai faru tsakanin su ba kafin su miƙe su koma ciki suyi having lunch ɗin su tare, suna tsakar ci sai ga Abba ya fito zai je part ɗin hajia zee da sauri Janan ta taso ta biyo bayan sa, "Abba" ta faɗa da ɗan ƙarfi yanda zai ji don har ya kusa fita, Tsayawa yayi yana gyara hannun rigar sa haɗe da ɗagowa yana kallon ta fuskar sa ba walwala, "Abba an sorry" "Sorry for what Janan?" Sinne kanta tayi haɗe da cewa, "For what happened ɗazu Abba, wlh ina son sa ne sosai, kuma nasan kaima zaka so shi idan ka bashi dama.." "Enough Janan" ya faɗa tare da ɗaga mata hannu sannan ya ƙara ficewarsa, juyowa tayi tana kallon Nihal data zubo masu idanuwa tamkar zatayi kuka, ta girgiza mata kai haɗe da cewa, "Don't cry, I will talk to him.." Ranta ba daɗi ta dawo suka ci gaba da cin abincin da sai faman tutturasa kawai takeyi ba don tana jin daɗin sa ba.... #Comment #Vote #share. *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 24_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1239373978?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=34NHId77Xja9Ca7srt62byRqk0YnNbIejq%2FffJgmlqMcpOcugE%2FHwyaA91zLKPDvOGIM%2B8b8kdGVHila2%2FiB5cEexENnRgZLE0XhWxOMcqhEdzB5VzhJlrw0cNoX3QRG_ *GA MASU BUƘATAR A TALLATA MASU HAJOJINSU, KO KUMA SABABBIN LITTAFANSU DA SUKE SON FIDDAWA ZASU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR KAI TSAYE TA HANYAR WATSAPP 07040402435* ______________________________ Sun jima a falon suna fira bayan sun kammala cin abincin har da Madam florence tana ƙara basu shawarwari akan halin rayuwa, yayin da Nihal ko jin abunda take faɗa ba tayi balle ta amfani da Alkhairan dake cikin sa, tunani kawai takeyi ina zata samu mafita arayuwarta akan ciwon son dake addabar zuciyar ta, ta wani ɓangaren kuma tunani takeyi na yanda zata shawo kan Abban nasu akan zancen 'yar uwar tata, har suka kammala firar su bata ce ƙanzil ba Janan ta juyo haɗe da cewa, "Wai Adda bazaki dena wannan tunanin hakan ba?, Tun ɗazu sai magana Madam keyi maki amma kinyi shiru" "Srry Madam, what are you saying?" Nihal ta faɗa haɗe da sakin wani gauron nishi tana kallon Madam, itama kallon nata takeyi tare da mere baki irin abun nan ya sha maka kai har tana ɗora hannayenta akan ƙirji, ta jima a haka tana kallon Nihal kafin tace, "Look my doter, don't go and kill your self saboda tunanin wanda baki ma san shi ba, am sorry ba ina ganin laifinki bane, nasan zuciya bata da ƙashi kuma so gaskiya ne, amma ya kamata ki sassauta wa kanki hakan" "Madam, what are you trying to tell me? Na dena son sa?, What the biggest mistake you are trying to do" ta ƙare zancen tare da janye throw pillow ɗin dake saman cinyarta tana yiwa Madam florence wani irin kallo mai cike da tsantsar reni da tarin tambayoyi, "Noo...ba haka nake nufi ba, ina nufin kirage wannan tunanin da kikeyi akansa, saboda bana son kisake shan wahalar da kika sha kwanakin baya na ciwon zuciya" "And so what idan nasha wahala akan sa?, can't you know that tunanin shi ne kaɗai ke sa ma mun natsuwa tare da ragemun raɗaɗi da zafin da nake ji azuciya ta? So lemme tell you one thing madam, wlh even if am gonna die bazan dena tunanin sa ba, and don't ever try to tell me dis again, just leave me, haka nake buƙata kuma haka zanyi" ta ƙare zancen cikin fushi tare da jifa da pillown sannan tamiƙe ta bar wajen, Kasa cewa uffan Madam tayi sai ma binta tayi da kallo tana taka upstairs ɗin har ta shige, girgiza kai Janan tayi tare da dafa kafaɗar Madam florence ta ce, "Am so sorry Madam, halin Adda Janan kenan, sam bata saurarar kowa akan duk abinda take so, shiyasa kika ga nima na ari wannan halin this time, let her be tunda ita ta saka kanta, kawai muyi mata addu'a" "But i pity her Janan, tana shan wahala fa idan ciwon ya tasar mata" "I know, but ya zamuyi da ita tunda haka take so?" "Oh ALLAH, have mercy on her, be cause zai iya taɓa mata lafiya" ta ƙare zancen tare da ɗaga hannayenta sama tana addu'a, nan ma sun ɗan jima ita da Janan suna sake ɗan taɓa fitar kafin suyi saida safe ta haye sama ita kuma ta wuce kitchen tana rarrage 'yan aikace aikacen da zatayi gobe, tana tsakar yi Abba ya leƙo ya ce "Madam gobe za a yi baƙi a gidan nan, ko akwai abunda kike ganin za'a iya buƙata da babu?" "No sir, just that the remaining meat in the freezer is little" "Nevermind with that, all i want , make sure that the house is very clean and i will handle the remaining issues" "What about the food sir" "Don't mind that" "Ok sir" ta ƙare zancen haɗe da miƙewa ganin ya juya yabar wajen, Kasancewar sai 12 Janan take da lectures yasa tayi kwancenta bata tashi bacci ba sai ƙarfe goma da rabi, ko banza dama jiya ta daɗi bata yi bacci ba saboda firar da suka sha da Madam florence, sosai tayi mamaki lokacin da take saukowa daga upstairs ɗin taga sai faman kai da kawo ma'aikatan gidan keyi, kallo tabi ko ina dashi ganin ana sake decoration ɗin falon kama daga kan frames ɗin dake jikin bango har zuwa labulayye da sauran su, ko ina yayi tas sai ƙyalƙyali yakeyi kamar yanda Abba ya buƙata, ɗage kafaɗa tayi irin ko ohon nan don inda sabo sun saba saboda haka Abban nasu yake da saurin canje canjen abubuwa akoda yaushe, shiyasa bata kawo komai a ranta ba ta sauka ƙasa ta nufi kitchen kai tsaye, koda ta shiga nan ma tsaf angyare ko ina, ganin Madam florence bata ciki kuma yunwa take ji yasa ta kunna gas haɗe da haɗa ruwan Lipton ta buɗe wani glass da ake saka snacks aciki ta ciro doughnut guda uku ta ɗora a ɗan ƙaramin bowl sannan ta koma sama, Tana gama ci ta faɗa toilet tayo wanka ta shirya a gurguje sannan ta ɗauki makullin motarta da ATM ɗin ta dake ajiye akan madubi ta jefe cikin jikka tafito da sauri don har 11 ma ta wuce, ɗakin Nihal ta nufa ta tura ƙofa haɗe da leƙawa ta hangota kwance kan makeken gadon nata lulluɓe da lallausan duvet har lokacin bata tashi baccin ba itama, "Hi Adda, good morning" Hannu ta ɗago mata cikin bacci haɗe da cewa, "Morning sweetheart how are you?" "Fine Adda, ni Zan tafi school" "Ok bye bye, safe trip" "Thanks, but you have to wakeup and take your breakfast almost to 12 now" "Ok darling, thank you" ta faɗa haɗe da miƙewa zaune ta saki wata irin doguwar miƙa, Murmushi Janan tayi tana faɗin "cutie angel" sannan tawuce, da sauri da sauri take saukowa har ta kawo ƙasa, daidai lokacin Madam florence ta shigo tare da wasu chif cookus ɗauke da manyan tireruwa da Abba yayi ordar ɗin abintayye da snacks a wata restaurant, "Oh my dota, har kin tashi?" "Yes Madam, good morning" "Morning my dota, sorry, have you eaten something?" "Yes madam" "Ok good bye, but you have to come back early because we have strangers today" "Who?" Janan dake ƙoƙarin tafiya ta faɗa haɗe da juyowa tana kallonta, "I don't no oo... Dis is what your dady telling me yesterday night" "Ok, I will" ta faɗa tare da wucewa, ba tare da ɓata lokaci ba tafice daga gidan aguje don time ya kusa, duk da tana sauri sai da ta tsaya banki ta ciri kusan dubu saba'in a account ɗin ta sannan ta wuce school, kai tsaye class ta wuce suka gama ɗaukar lectures sannan tafito ta nufi wajen da su mm ke zama duk da bata sa ran ganin sa ba ta ciro wayar ta tana ƙoƙarin kiransa, kusan kira uku tayi mata but its highly switch off, ki tayi kamar ta fashe da kuka haɗe da cuno baki tana ɓata fuska, kamar ance ta juyo ta hango ingaski acan gefen acadamic staff tsaye shi da Amira suna magana, bata kawo komai a ranta ba ta juyar da kanta gefe haɗe da gyara jikkar ta dake sagale a kafaɗar ta, sai da tayi kusan mintuna goma a tsaye wajen sannan ta hango mm mai acaɓa na ajewa agefen titi, wani irin murmushi ta saki tare da ɗan ja da baya ta ɓuya a bayan iccen da suke zama suna fira a wajen, kasancewar bai ganeta ba yasa lokacin daya ƙaraso wajen ya nemi waje ya zauna tare da ciro wata 'yar nokia ƙarama daya tsaya ya siya kafin ya ƙara so ya ciro sim a aljihunsa ya saka, yana ƙoƙarin kunna wayar ta lallaɓo ta bayansa haɗe dasa littafin dake hannunta ta rufe masa fuska dashi, ƙamshin turaren jikinta daya ji ya sashi sakin murmushi haɗe da cewa, "Sassanyan ƙamshin ki ai shi zai tona maki asiri tare da tabbatar mani da cewa keɗin ce a kusa dani nurul albi na" Cike da shagwaɓa ta bayyana a gabansa tana faɗin, "Aikuwa zan dena saka turare ko don na shammace ka wata ran, tunda dashi kaɗai ne zaka iya gano cewa ina kusa dakai" "Ai kuwa da kinci duka, don mm baya ɗaukar hakan ga kowace mace, kinga kuwa idan ban gane ke ɗin ce ba dole kisha mazga a hannuna" Dariya tayi haɗe da zaunawa a kusa dashi tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta ce, "Barka da rana yallaɓai" "Barka ranki shi daɗe kin wuni lafiya?" "Lpy klw, ya jikin?" "Ban sani ba tunda kin ƙi ki zo ki gasamun" rufe fuskarta tayi da littafin tare da cewa, "Ai lokacin hakan beyi ba, idan yayi ba gasa maka kaɗai zanyi ba hadda tausa" "Iyyeee, kice dai matar tawa ƙwararriya ce bazan sha wata wahala ba? Ya Abban mu da big aunty?" "Suna lafiya" "Injin dai bai yi fushi dake ba?" "Karka damu, nasan in sha ALLAH zai sauka, muci gaba da addu'a" "To shikenan, ALLAH ya huci zuciyar sa ya amince mana mu mallaki junan mu" "Amin ɗan saurayi na, ya Razina, da yaya Jabir? Shine bazai rakoka ba tunda kun bar sana'ar?" "Qyalesa can, dama takura ni yakeyi idan ina hira da matata" "Lalala...shi yaya Jabir ɗin ne ke takura ka?" "Sosai kuwa, kin san suruki na ne wani lokacin" "Haba? Taya kuma" "Eh...shi zai auri Razina in sha ALLAH" "Wow! Nayi farinciki, ya Jabir nada kirki sosai kamar ita" "Taya akayi kika san tana da kirki itama" "Jininka fa ce, taya za a yi tasa kirki, nasan komai halayyar ka itace tata" "To naji, mu sai yaushe zamuyi auren?" "Sai ka shirya" "Idan nace yanzu zaki yarda?" "Mezai hana?, Nama yarda" "Au! To bazaki tambayi ina zan ajiyeki ba kuma dame zan aureki?" "Ba su bane a gabana, burina kawai na mallakeka, a ina zaka aje ni?, me zaka aureni dashi? Duka na barshi a hannunka" "Ko da ɗaki ɗaya ne?" "Ko agidan haya ne yallaɓai" "To adai bari har na samu sana'ar da zabi fara tukuna, kin san ita kaɗai zata bani damar iya kula da cinki, sha, lafiya da kuma suturarki" "To shikenan, yawwa har ma na tuna" ta faɗa tana jawo jikkar ta haɗe da zuge zif ɗin ta, kuɗin da ta ciro a banki ɗazu ta ɗauko haɗe da miƙa masa, ɗan harar ta yayi kafin yace, "Na meye wannan?" "Ka karɓa mana sai nayi maka bayani" Karɓa yayi yana juya kuɗin tare da ɗan laso leɓensa na ƙasa yana kallon ta cike da son ƙarin baya ni, "Ka dena yimun irin wannan kallon kar kasa nafara jin tsoron ka" "Na dena" ya faɗa yana gyara zamansa, "Dama cewa nayi tunda kaga yanda abun ya kasance game da sana'ar da kukeyi, me zai hana kaje da wuɗan nan kuɗin idan zasu isa a buga maku irin ɗan shafin nan kai da Jabir a ƙofar gida, in yaso sai muje a siyo ɗan provision a saka ku fara dashi kafin muga yanda ALLAH zaiyi, dama can ni na fara kishin sana'ar nan taka acikin makarantar nan ana kallemun kai, amma yanzu nasan babu wacce zata je har ƙofar gida ta ƙura maka idanuwa inba marar kunya ba" "Tofah, yanzu dai ungo kuɗin ki tukuna sai muyi magana" ya ƙare zancen yana ƙoƙarin maida mata ƙuɗin acikin jikkar, ɓata fuska tayi tare da turo baki kamar zatayi kuka, "Kada kayi mun haka don ALLAH, abuna abinka ne, bana son mijina ya koma zaman benci a anguwa ba sana'a, don ALLAH idan har soyayyar da kake yimun da gaske ne ka karɓi kuɗin nan" Kasa ƙarasa saka kuɗin yayi haɗe da tsayawa yana kallon ta kafin yace, "Soyayyar da nakeyi maki Janan ba ta buƙatar kwatantawa da komai balle kice hakan, soyayyata nada girman da ni kaina bansan dame zan kwatanta ta ba, ni ne namiji Janan, ni ya kamata na nemo kuɗi na baki don ƙara ƙawata soyayyata da kyautatawa bawai ke ba, idan kika yi hakan sai kisa naji nayi rauni ban cika namiji ba" "Don ALLAH kada kaji hakan, kai cikakken namiji ne ko acikin mazaje mm, kuma na tabbata lokaci zai nuna hakan don bazaka hanani naka kuɗin ba

Chapter 14 of 40