masa jin abunda mm ya faɗa, wai ya ɗage motoci, sai kace wata guguwar iska?, Kamar ya shiga zuciyarsa ya ji abunda yake faɗa kawai yaji ya ce,
"ALLAH ina faɗa maka iskan nan daka fitar ko guguwa albarka, don ALLAH jb karage fushin nan haka, nasan grandma bata kyauta ba, atleast ko barayi komai ba alokacin ya ci ace ko sau ɗaya ne ta dakatar daku daga tafiya, sai ALLAH yasa batayi hakan ba, wannan kuskure ne kuma laifine ta aikata" sai alokacin Jabir ya juyo yana kallonsa haɗe da cewa,
"Ka yarda da hakan da tayi kuskure ne kuma tayi laifi?"
"Na yarda, amma ai itama ta fahimci hakan kuma tayi nadama shiyasa kaga tana neman yafiya, in son samu ne kayi haƙuri ka kuma yafe mata kamar yanda Momy tayi, na tabbata zaka samu wani farinciki a zuciyar ka"
"Babu wani farinciki da baku bani ba aduniya kai da Momy, farinciki ɗaya ya rage mani shine ku aura mani Razina, dana samu wannan shikenan na samu dukkanin farincikin duniya daga gareki ba sai na je neman sa a waje ba" ganin har yanzu da saura Jabir bai sauka ba ya sashi haƙura da cigaba da maganar har sai zuwa nan da kwana biyu tare da cewa,
"Shikenan, yanzu dai ɗan hanzarta lokaci na ƙurewa kuma amanar Momy, Janan da kuma kaka na hannunka kafin na dawo, ka kula mani dasu sosai" wani kallo Jabir ya jefa masa sannan ya ci gaba da tuƙinsa, kamar bazaiyi magana ba sai kuma can ya ji ya ce,
"Ka manta baka haɗa da tsohon naku ba" dariya mm yasa har yana dukan dashboard ɗin motar kafin yace, "to shikenan ka haɗa duka dashi ka kular mani dasu sosai" daidai lokacin Jabir yakawo ƙofar shiga airport ɗin ya turo kan motar ya shiga ya samu wuri ya yi parking haɗe dayin tsaki, ya ce
"Dallah malam fita nidai, ALLAH ya kiyaye ya saukeku lafiya, matar tawa da baka bani amanar tata ba kace kar nakula da abata" dariya mm ya sakeyi tare da juyawa ta sit ɗin bayan motar da jikkarsa ke ajiye ya miƙa hannu ya ɗauko jikkar sannan ya fice daga motar, duƙo da kansa yayi ta jikin tagar motar yana kallon Jabir da shima kallon nasa yakeyi ya ce,
"ALLAH ya baka haƙuri yaron baffansa angon kaka.." kafin ya rufe baki ya ɗauki biron dake ajiye a tsakankanin kujerun ya jefa masa, da sauri mm ya caɓe yana dariya sannan ya bar wajen, murmushi Jabir ya yi haɗe daji tamkar yabi sa saboda kewar sa da tun yanzu ya fara ji, ya jima a zaune cikin motar har saida ya ji an fara sanar wa jirgin nasu zai tashi sannan ya kunna motarsa shima ya bar wajen.
Ko daya dawo gida baibi takan kowa ba ya shige ɗakin su ya nemi gado ya haye, kafin kace me tuni bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi,
A ɓangaren Janan kuwa bata koma gidan ba sai bayan sallar isha, tafe take cikin mota tana waya da masoyin nata har ta ƙaraso gida tayi parking ta fito ciki tare da miƙa hannu ta ɗauki jikkarta sannan tasa makulli ta rufe ta nufi cikin gidan, tana kaiwa tsakiyar falo taji muryar mahaifin nata ya ce,
"A ina kika fito?" Cikin kaishi murayar dake nuna mai ita babu walwala a tattare dashi, mm ba tare data kashe wayar ba ta jefata a jikka haɗe da kallon mahaifin nata ta ce,
"Abba barka da dawowa, yaushe ka dawo ne" a tsawace ya ce,
"Answer my question from where are you?"
"Daga gidan Hajiya kaka" ta bashi amsa tana tare da sunkuyar da kanta ƙasa,
"Me kika je yi acan" cike da mamaki ta ɗago kai ta kallesa jin tambayar data sake fitowa daga bakinsa kafin tace,
"Na je gaida ta ne"
"Kint je gaida ta ko kunje haɗuwa da wannan ɗan iskan yaron?"
Jin tayi shiru bata bashi amsa ba ya sashi kaɗa kai yabar wajen ranshi na suya da sululi, kenan abunda su Jazz suka faɗa masa gaskiya ne, dole ya ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki cikin gaggawa kafin komai ya lalace masa,
Ita kuwa ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗago kai tana kallon gun daya bari sannan ta juya ta nufi upstairs ɗin, Nihal ta hango tsaye ta naɗe hannayenta akan ƙirji tana kallon meke faruwa, da ɗan sauri sauri ta shiga hawa upstairs ɗin har takai inda take,
"Sannu Adda Nihal" ta faɗa kaɗai tare da ɗaga mata hannu ta shige ɗakinta, bayanta Nihal tabi tare da tsayawa bakin ƙofa tana ƙare mata kallo, Janan data soma kwaɓe kayan jikinta ta juyo ta kalleta ta ɗauke kai,
"Adda lafiya?"
"Lafiya lau Janan, ina kika je ne yau?"
"Gidan grandma"
"Shine baki faɗa mun ba muka je tare"
"Naga kina bacci ne, be side ba lallene kije ba kona faɗa maki, shiyasa banyi hakan ba"
"To ya akayi kika ƙi ɗaga wayata dana kira"
"Sorry ban lura ba ina can ina fira nida mm" takai zancen tare da excusing kanta ta nufi toilet don tawatsa ruwa,
"Wait Janan..."
"Please....am so tired Adda, bara na watso ruwa zan sauko ƙasa sai muyi magana"
"Ok" ta faɗa haɗe da juyawa tabar ɗakin cike da takaicin mm a ranta, gaba ɗaya yasa ƴar uwarta sauya mata daga Janan ɗin data sani zuwa wata daban, badon shine farincikin taɓa da tasa anyi masa tsakani da ita, yayansa ko kan hanya ya ganta bazai kalleta ba,
Janan kuwa na fitowa wajen wanka ta ciro wayar ta daga cikin jikka takira mm, bugu ɗaya ya ɗaga don dama cike yake da tunanin meya faru ta dena magana ɗazu bacin kiran bai tsinke ba,
"Yallaɓai afuwan, na iso gida ne ɗazu Abba ke tambayata daga ina nake shine fa na tsaya bashi amsa ba tare dana kashe ba"
"Ok, ya dawo kenan?"
"Eh, na taddashi agida"
"Masha ALLAH, to yanzu meye labari?"
"Yana hannunka hubbin ruh"
Haka suka ci gaba da firarsu ta soyayya hankali kwance, dama tayi taking dinner ɗin ta a gidan grandma hakan yasa bata damu da sauka ƙasan ba, haka Nihal tayita zuba idanuwan ganinta har ta gaji bata sauko ba kamar yanda ta ce ɗin, sosai abun ya ƙonawa Nihal rai amma duk da haka saita danne saboda tana son Janan tadena yimata shariyar data tsiri yimata yanzu,
Saida ta watso ruwa ta saka kayanta na bacci sannan ta kashe wutar ɗakinta ta jawo ƙofar ta nufi ɗakin Janan, har lokacin suna laƙe da juna ita da mm suna waya, tana kallonta ta shigo ta haye kan gadon nata ta kwanta taaare da jan duvet ta rufa dashi fuskarta na kallon p.o.p ɗin saman ɗakin, kasancewar Nihal ta saba'in hakan wani lokacin ya sa bata bi ta kanta ba taci gaba da wayarta, saida taga anyi wasu mintuna talatin basu ƙarƙara wayar ba sannan ta ce,
"Janany sister magana nake son yi dake"
"Ok bani Adda bani mintuna biyar" karaf taji mm ya karɓe da,
"A'a, jeki kuyi maganar ku saida safe, nima na gaji bacci nake ji" ya faɗi hakan saboda yaji sautin muryar Nihal lokacin da take magana, ko bacin haka shima yanada buƙatar kwantawa ya huta don gobe sakko zasuyi zuwa ƙasar dubai, yasan ko idan bai kwanta dawuri ba tofa bazai tashi dawuri ba, badon Janan taso ba ta ce,
"Shikenan saida safe"
"Ok bye, ki kula mani da kanki"
"Zanyi hakan, kaima kayi mafarkina"
"Love you, nightttt.."
"Love you too hubbin ruh" ta faɗa cike da nishaɗi sannan ta katse kiran,
"Sorry Adda, gani meke faruwa ne?" Ta juyo tare da ɗora kanta a saman kafaɗar ta, "hmm Janan kenan!, Meyasa kika sauya mun kwana biyun nan?"
"Kece kika fara sauyamun Adda, shiyasa na biki ayanda kike so"
"To danayi maki me?"
"Abubuwa da dama mana"
"Kar kiyi ƙarya domin baki saba yimun ba, asali ma batayi maki kyau"
"Haka ne Adda, fisabilillahi yanda kike reacting akan mm bayayi mun daɗi gaskiya, haka ma Aunty zee, kiyi rayuwarki a yanda kike so bazani hanaki ba, amma maganar gaskiya son kai da wulaƙanci duka basa da daɗi, Aunty zee mahaifiya take agaremu ko muso ko kar mu so, wajibi ne agaremu mubata girmanta da ALLAH ya bata koda ace mun girmeta, balle gaba ɗaya tayi ƴaƴa damu, yanda kike kalamai marasa daɗi da rashin girmamawa agunta shiyasa nakeyi maki haka saboda kiji idan akwai daɗi kuma..."
"Pls ya isa haka, naji wannan sai me kuma?"
"Bana son kina faɗa e maganganu akan wanda nake fata kuma nake mafarkin ya zamo mijina, gaskiya hakan baya yimun daɗi shiyasa nafita shirginki"
"Ina akan wannan na baki haƙuri ko?, Kuma wai me kika ɗokesa ne da zaki nemi baƙanta mun akansa, kenan haka zai rabamu idan kika auresa?, haka zaisa ki gujeni bayan kinsan duk duniya banida wata wacce ta fiki?, Wlh ALLAH hakan ya fara sakani tsoron ki auresa don na tabbata rabamu zaiyi" ta ƙare zancen tare da saka kuka bil haƙƙi har cikin zuciyar ta, ɗan matsowa Janan tayi kusa da ita tare da cewa, "am so sorry, kiyi haƙuri in Sha ALLAH na dena, sannan kidena tunanin mm zai rabani dake, wlh bazai taɓa yin hakan ba na tabbata, ki gyara kurakuranki ni kuma nayi maki alƙawarin canzawa daga sauyin da nayi"
"Kin tabbata?"
"Sosai kuwa, kefa second mom ɗina ce, taya zanyi maki alƙawarin ƙarya" murmushi tayi tare da rungumota ta ce,
"Ina matuƙar sonki Janany sister don ALLAH kidena biyewa masu son rabani dake kin ji ƴar uwata?, Ƴar dariya Janan tayi kafin tace, "babu fa mai iya rabani dake na faɗa maki, don haka kidena wannan tunanin, nima ina son ki sosai"
Nan fa suka shiga wata sabuwar fira cike da son junan su kafin bacci mai matuƙar daɗi yayi awon gaba dasu, mm kuwa yana kwantawa wayarsa ta shiga ruri, da har bazai ɗauka ba sai kuma ya miƙa hannu ya ɗauki wayar daya saka a caji yana tunanin ko Janan ce, ganin lamba ya sashi sakin tsaki tare da kashe wayar gaba ɗaya bayan ta katse sannan ya koma ya kwanta,
Turo baki Amira dake kwance tayi bayan ta sake kiran wayar a karo na biyu ance kashe take, gidan tura saƙo ta shiga tare da rubuta masa message kamar haka, _Mm wlh Inaga baka san meye cutar so ba, amma ina riƙon ALLAH ya saka maka ita, musamman tawa, tayanda bazaka taɓa samun sukunin da kwanciyar hankali ba har sai kaji muryata sau takwas a rana, kaga fuskata sau bakwai a sati, sannan ka ƙuduri mallakata lokaci ɗaya, ina son ka, ina son ka ya Muhriz na_ ta tura alamar kiss💋 da kuma heart❤️ sannan ta tura masa tare da rungume wayar, a haka itama bacci mai nauyi ya zo ya yi awon gaba da ita.
Tunda asuba daya gama Sallah ya kunna wayar sa saboda yasan abokin tafiyarsa da zasu riƙon jirgin da zai isa dubai da safen nan zai iya nemansa, kusan a tare message ɗin guda biyu suka shigo, na farko na Amira ne data turo daren jiya, na biyu kuma na Janan ne data turo yanzu, na Janan ya fara buɗe wa da ta ce, _Barka da safiya hubbin ruh, ina fatar ka tashi lafiya cike da aminci da kuma kyakkyawan annuri daya haskaka zuciyar ka, ALLAH ya amintar mun dakai daga dukkanin abunƙi na wannan safiyar, yankuna sadaka da alkhairan wannan wuni, have your break, I love you_ murmushi yayi tare da kissing message ɗin sannan ya furta "i luv you too wifey na" haɗe da rubuta mata amsa _lafiya klau natashi kamar yanda matata take, Nagode da addu'ar ki ALLAH yayi maki albarka, i luv you too sai na kiraki_ ya tura yana mai jin wani kuzari da ƙarfi acikin jikinsa, har zai mayar da wayar ya ajiye sai idanuwansa suka sake sauka ga message ɗin Amira, ba tare daya san ita bace har sai daya buɗe sauƙon ya karanta, girgiza kai yayi tare da cewa
"Mahaukaciyar yarinya" sannan ya rufe wayar ya ajiye.
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 43_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
******
*Ina masoya littattafan ASMY B ALIYU?, Kumar matso kusa yazo maku da wani shahararren littafin ta mai suna WAMINAL HOOB!, Hmm tirƙashi dajin sunan wannan littafin kinsan zaku gwangwaje da soyayya da kuma chakwakiyar ƙauna acikin sa, domin na tabbatar maku da hakan nazo maku da kaɗan daga cikin wannan ƙayataccen littafi nata mai matuƙar ɗaukar hankali, ta bakin malam bahaushe dai, ya ce gani ya kori ji👇*
*Waminal Hoob*
_Asmy b Aliyu_
PAID BOOK##
Love#
Friendship#
Family#
NooryAli#moments
Tana ganin yarda jikinsa ke wani irin kadawa ,jawota yyi ta fado kansa Yana shakar kamshinta Yana sakin ajiyar xuciya ,kallon cikin kwayar idanunsa take .Wanda ya canja kala har kwallah take hangowa acikin su ,a hargitse ya shiga subbatar ta ta koina Yana tura kansa cikin Wuyanta,hawaye taji suna cika Mata ido tuno farhaan kurum,hade fuskarsa yyi da Tata fuskar Yana goga hancinsa da nata da wani irin Murya Yake fadin"I try Am very try Noory u belong tot someone else,ya fada muryarsa na karyewa A hankali kafin ya hade bakinsa da nata.
T
Friendship#
Aliyu waxeer
Farhaan Shagari
"Da Alamar bakada hankali Farhaan ka Samu tabin kwakwalwa,ni kake tunanin naje na auri yarinyyar da kakeso har na tsawon shekara daya??''yyi maganar so pissed up ,farhaan ya kwantar da Kai Yana fadin nasan Nooriyyah Bata cikin kalar matan da kakeso ,nasan ba ajinka bace .Haka nasan baka sha'awar (BAKAR MACCE")bestyn ka xakayiwa wannanr Alfarma da xarar na kammala master's Dina xan dawo gareta muyi Aure!!"girgixa Kai Aliyu waxeer ya shigayi Yana fadin ka haukace Farhaan!!!"
Waminal Hoob#
Is out on the 31july..stay tuned and find out!!!!
Love is in the Air#
Team Noory-Ali#Forever❤️
FRIENSHIP##
Aliyu waxeer
Farhaan Shagari
Areefa Mansoor
Laylah waxeer
FAMILY#❤️
Wazeer Family
Shagari Family
Azeex Ali Family..
_______________________________
Daidai lokacin itama Amira ta jawo wayarta bayan ta kammala sallah cike dasa ran ganin amsar sa koda kuwa ta baƙar magana ce, amma ga mamakin ta sai taga bai turo komai ba, hakan ya sa taji haushi sosai ta shiga shirin zuwa makaranta cikin nuƙura, kallonta Zarah tayi haɗe da cewa,
"Aunty Amira lafiya kike ƙunci?, Meya faru ne" saida ta maka mata harara sannan ta ce,
"Ubanki ne ya faru" saurin rufe baki Al-amin dake zaune cikin shirinsa na makaranta yana karyawa yayi haɗe da kallon umma dake miƙawa Zarah kokonta a kofi ya ce,
"Umma aunty Amira tayi zagi" bai rufe baki ba shima ta mangaresa gefe tana faɗin,
"To uban ƴan gulma da shedi, ka faɗa ka ji daɗi" cikin ɓacin rai umma ta ce,
"ALLAH kika sake taɓamun yaro sai ranki ya ɓaci, ka barta ai sai tayi ta yi in anfaɗa mata cewa zagi da zafin rai abun ƙwarai ne, ke kenan kullum bakyada aiki sai baƙar magana ga ƙannen ki, babu ranar da zata zo ace gaki zaune waje ɗaya tare dasu baki hantare su ba, wannan wace irin rayuwa ce haka da ba'a gane ana ci gaba?"
"To umma meye yasha ruwansu dani?"
"Babu, amma ai ba laifi bane don an tambayi mutum meke damun sa, ko addu'a ce ai ayi masa"
"Ni bana so, su ƙyaleni kawai" ta faɗa tare da ɗaukar jikkar ta tayi gaba,
"ALLAH ya baki haƙuri Aunty ya kiyaye hanya" Zarah ta faɗa cikin ɗaya murya, ita kuwa umma dariya tayi haɗe da cewa,
"ALLAHu ya shiryeki Amira, da alama dai wannan kumburi ga doki ne sakkiya ga jaki, ai sai kizo ki karɓi na abun hawanki ko ƙasa zaki je muƙara a cefanen abincin namu na rana?"
Har ta kai tsakar gida ta juyo ta dawo ta karɓi kuɗin sannan ta cewa umman ta tafi, ta ce da ita "ALLAH ya kiyaye yasa adawo lafiya" ta amsa da amin sannan ta wuce, batafi mintuna uku da fita ba itama Zarah ta riƙo hannun Al-amin zata kaishi makaranta tana faɗin,
"Umma mun tafi"
"ALLAH ya kaiku lafiya, ungo ga ɗari biyu idan kin kaishi ki bashi Naira hamsin, saiki siyo mana ƴan kayan miya da albasa na ɗari da hamsin idan zaki dawo"
"To umma, busasshe?"
"Eh mana, waya riƙa mana cin ɗanyu yanda sukayi tsadar nan"
"ALLAH" Zarah ta faɗa ataƙaice tare da ficewa, ko da suka iso baki titi sun tadda Amira tsaye acan gefe har lokacin bata samu abun hawa, da yake sai sun tsallaka acan gaba makarantar su Al-amin take yasa sai da Zarah ta tsaya ta tarar wa Amira mashin da tun ɗazu ma sai latsar wayar ta takeyi tana gwada kiran mm ko ALLAH zaisa ya ɗaga a wannan karon don itakam ta kasa haƙura da rashin jin Muryar sa, mm na ɗagawa mai mashin ɗin ya tsaya da sauri tayi masa alama daya tafi ta koma gefe tana faɗaɗa fara'ar data bayyana a fuskarta yanzu, Zarah na ganin haka ta girgiza kai tare da tsallakewa abunta suka barta a wajen,
Sallamar daya ji tayi yasa bai taso mata da fitina ba kamar yanda ya ƙudurtawa ransa, Muryar sa ba yabo ba fallasa lokacin yana tattaka matattakalar jirgi ya amsa sallamar haɗe da cewa,
"Pls dawa nake magana?" Yayi kamar bai san ita ɗin ce ba, marairaice fuska tayi kamar tana agabansa tare da gyara jikkar dake rataye a kafaɗar ta, ta ce
"Haba ya Muhriz, yanzu sai kace baka gane muryata ba, Amira fa ce"
"Oh! Wace Amirar kenan?"
"Hmmm wace Amira kake da ita bayan ni masoyiyar ka, ALLAH bana jin daɗin yanda kake yimun don kaga na bayyana sirrin dake zuciyata akanka, ni fa da gaskiya nake son ka bawai da wasa ba"
"Amira kenan, to ni kuma mena faɗa maki?, Zuciyata nada wacce take so kuma ..."
"Ya isa haka, kuma wacce kake ƙauna ko?, Ai na sani, kai fa namiji ne, mata huɗu ALLAH ya baka zaɓi ka aura, don me bazaka tausaya mun ba"
"Saboda nasan idan kece nake so tun farko bazaki yarda na haɗaki da wata ba duk da kinsan ALLAH ya bani zaɓi akan na auri mata huɗu, look Amira bada ni kaɗai ne namiji ba, akwai maza da dama a duniyar nan da suka fini komai kuma suke jiraye da samun kamar ki, kiyi haƙuri da ƙoƙarin bawa shukar dake kan dutsi ruwa domin bazata taɓa yin tsiro ba"
"Kar kace haka ya Muhriz, ai da shukar dake cikin ƙasa da wacce ke kan dutse duka ALLAH ke kula da tsirowar su, na tabbata idan yaso zai iya bata damar tsiro koda kuwa banyi mata ban ruwa ba"
"Shikenan, kibar ALLAH yayi masa ikon tunda kinyi imani da hakan"
"Imanina bazai hana nabawa shukata ruwa ba ya Muhriz saboda komai nada sila, zai iya yuyuwa jajircewa ban ruwan nawa ya zamo silar tsiron shuka ta, don ALLAH kabani dama naci gaba daban ruwana natabbata zan dace"
"A sanina hakan nada wahala kuma ɓata lokaci ne, ni kuma mutum ne da baya wasa da lokaci kuma yake martaba sa, don haka nake shawartar ki da kiyi amfani da lokacin ki kafin ya ƙure maki, sai anjima"
"Mm..." kawai taji ya tsinke wayar, wasu zafafan hawaye taji sun ziraro mata a fuska tayi saurin goge wa tare da folding hannunta ɗaya a ƙirji ta sa ɗayan dake riƙe da wayar a baki, wani irin silili take ji a ranta zuciyar ta nayi mata suya haɗe da ƙuna, ta rasa yanda zata ɓullowa soyayyar mm tasamu nasara, gashi ko yaushe sai ƙara nutso takeyi aciki, tana tsaye ta ga anyi parking da wata farar mota a gabanta, a hankali aka shiga sauke glass irin ƴan iskan gayun nan ke ciki, ɗaga mata gira yayi haɗe da cewa,
"Hy, watsup baby" ta dalla masa wata uwar harara haɗe da sakin tsaki tabar wajen tana tsine masa a zuciya, don gaba ɗaya kana ganinsa kaga ɗan iska mararan, wani tsakin ta sake saki akaro na biyu kafin tace,
"ALLAH ya isa, mai zubin sheɗanu kawai" tana rufe baki ta hango mai napep tayi saurin tare sa ta shige tana faɗin, "muje fcet zaka kaini" suna ɗagawa gayen daya tsaya daidaita tsayin motar sa ya iso wajen, aikuwa cike da takaici ya kaiwa bayan napep ɗin shuri ta leƙo da kanta haɗe dayi masa daƙƙuwa da hannu tana faɗin,
"Uwaka ɗan iska ahalin sheɗan"
"Kai...kai..kai. don ALLAH baiwar ALLAH kirufa mana asiri, irin gayun can ba mutunci ne dasu ba wlh" mai napep ɗin ya faɗa yana kallonta ta madubi, tsaki ta sake ja haɗe da cewa,
"Bar ni dashi, ai nima ba mutuncin ne dani ba, ya wani zo agabana ya tsaya har yana wani watsup, na bi watsup ɗin nasa da gudu ɗan rainin hankali kawai" dariya mai napep ɗin yayi kafin yace,
"E'ehm Hajiya, kedai yita kanki, zamanin nan kana biyewa shirgin mutane baka ji baka gani ba zasu wahalsheka"
Bata dai ce dashi komai ba suka ci gaba da tafiya har suka isa school ta ciro kuɗin sa ta bashi ya ƙara gaba ita kuma ta shige aji,
Haka rayuwar Amira taci gaba da kasancewa kullum wayewar safiya ƙaunar mm na ƙara nitso a zuciyar ta haka kuma tsanar Janan na lunkuwa a ranta, Janan kuwa ko ajikinta don tuni ta daɗe da sanin Janan na ƙaunar mm tun daga ranar daya yimata jan kunne akanta ta fahimci akwai wani abu daya faru tsakanin su da bata sani ba, wanda shine ya sashi faɗar haka, a fannin gidansu kuwa rayuwarsu sukeyi gwanin ban sha'awa da Nihal, duk abunda zatayi ya ɓatawa Janan rai ta denayi agaban ta, haka ma ta ɓangaren aunty zee an samu sauyi sosai don har part ɗin take shiga yanzu ta gaisheta musamman ma idan taje neman Janan, haka yasa shaƙuwar dake tsakaninsu ta dawo sabuwa fiye data da,
Jabir ma da sauƙi yanzu don kuwa Momy da mm sunyi nasarar saukar dashi, inda bayan dawowar mm da kwana biyu suka je gaida grandma, sosai taji daɗi har da kukan farinciki tana tayiwa mm godiya haɗe da cewa tabbas shi alkhairi ne acikin zuri'ar ta shiyasa ALLAH ya turosa cikin rayuwar Janan don ya zamo silar dawo mata da jikanta da surukar ta a gareta, nan Jabir ya dinga tsarguwar ta wai shi bazai zama mijin tsohuwa ba musamman mai yawan kuka irinta don kar ta hanasa bacci, sai dai in mm zai iya shi yayi maleji da ita amma shi kam mijin yarinya ne, Janan dake gefensa itama tace bazata yarda ba a haɗata kishi da tsohuwa mai kuka a aza cutar ta takeyi, ganin sun haɗe mata kai ya sa mm cewa tasha kurumin ta shi kam ɗari bisa ɗari auren shi da ita, itace uwar gida ran gida sai abunda tace za a yi, kuma auren su mutu ka raba takalmin kaza dashi da ita, nan fa Janan ta aza masa rigima wai lallai lallai sai yayiwa grandma shika uku agabanta in ba haka ba tace ita kuma ta fasa auren, nan dai akasa dariya ganin mm na ƙoƙarin jawo biron dake gabansa haɗe da cewa na bi ALLAH na biki Janany ta samo takarda, abun dai gwanin ban sha'awa, tun daga ranar komai ya daidaita tsakanin Jabir da Hajiya, ta so su kaita wajen Momy sosai amma Jabir ya ce a'a tabari zai kawo mata ita har gida tare da amaryar sa Razina, yayi haka ne gudun kar taje plan ɗin su ya watse kafin lokaci yayi,
Haka rayuwa taci gaba da garawa tsakanin wuɗan nan bayin ALLAH, inda tuni mm ya siya masu wasu tagwayen gidaje shi da Jabir da wasu magada suka saka a kasuwa bayan dawowar sa daga abuja, gidaje ne masu matuƙar kyau da tsaruwa don babu abunda zaka nema aciki ka rasa, kowanen su hawa biyu ne da kuma gate ɗin shiga sai parking space na motoci da ƴan shuke shuken fulawoyi dake gefe gefen gidajen, da kuma wajensu, lokacin da mm ya ɗauki Momy, Jabir da kuma Razina ya kaisu gidajen ya ce nashi ne dana Jabir ba ƙaramin farinciki da daɗi Momy taji ba don har da kukanta tana ta saka masa albarka da fatar gamawa lafiya, inda Jabir ya zama speachless saboda a tsammanin sa gidan da suke ciki zasu gyara idan lokacin aurensu yayi, sai gashi yaga akasin haka, Razina kuma rigama ta aza wai sai dai mm ya maida gate ɗin shiga gidajen ɗaya a kuma cire katangar data shiga tsakanin su, ai kuwa nan take ba tare da ɓata lokaci ba yasa akayi komai aka gama cikin ƙanƙanen lokaci, bayan kwana biyu kuma ya ɗaukowa momy batun haɗa lefesu da yake so ƙarshen watan nan in zai koma dubai da kuma chana yayi mata viza
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 40