Share this page
sannan ya juyo yana kallonta ya ce, "A'a Janan, ba fa lallai ne ki iya karɓar tukuicin da zan baki ba, kawai ki faɗi duk abun da kike so kar nazo ina dana sanin faɗar abunda zan baki" "Faɗi kawai, na tabbatar ko meye ma zan amsa ba tare da na sakaka yin dana sani ba.." kafin ta ƙarasa taji ya ce, "Har da idan na ce ina sonki Janan" wani irin burki ta taka da ƙarfi haɗe da juyowa tana kallonsa, jin takeyi tamkar a mafarki ne kalamansa, juyi ta ji kanta ya fara yi zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, cikin i'inar muryar da ita kanta bata san tana yi ba ta ce, "M.me.me kace mm?" "Ina son ki Janan" ya sake maimaitawa idanuwansa cikin nata "Ban ji ba, ɗan ƙara faɗa da kyau mana" dariya yayi yana ji tamkar ya jawo ta ya sakar mata kiss yanda za tafi fahimtar inda zancen sa ya maida gaba, a ɗaya ɓangaren zuciyarsa kuwa tsoro ne cike fal acikin ta na kar ta kasa amsar sa a matsayin masoyi, tattaro dukkanin jarumtar sa yayi haɗe da ɗan rintse idanuwan sa ya buɗe tare da jimƙe hannunsa sosai ya ce, "Da gaske nakeyi ba wasa ba Janan, ina sonki, ina kuma ƙaunarki fiye da tunanin ki, na rasa yanda zan yi na fuskance ki da wannan maganar saboda tazarar dake tsakanin Ni dake shi yasa na kasa faɗa maki, yanzu ma shahada kawai ne nayi na faɗa maki saboda da zuciyata ta kasa jurewa, rauni na a kanki sai daɗa hauhawa yake yi hakama tunaninki sai faman addabar ƙwaƙwalwata yake, ke ɗin ta musamman ce Janan, haka ma halinki daban yake, kyan sura da kuma kyawon da ALLAH yayi maki duka suma ɗin abun burgewa ne, natsuwarki da girmama ɗan adam sune suka fi komai jan hankali na a kanki har na manta da banbancin dake tsakanin ni da ke naje na fa ɗa a kogin son ki, Janan da zuciya ɗaya nake ƙaunarki duk da nasan ke ɗin ba Sa'a ta bace, ta kuma kinfi ƙarfina, kawai ba yanda zanyi ne tunda Zuciya ta riga da ta gani kuma taji tana so, idan har zaki amince Janan to wannan shine TUKUICIN dana tana agareki, kuma zanji matuƙar daɗi sosai idan kika karɓesa da hannu biyu ba tare da kin watsa mani ƙasa a idanuwa ba" Tun daya fara maganar take kallon sa tana langaɓe kai tare da saurarar zazzaƙar muryarsa har ya kammala, ganin yaƙi ko motsawa balle yasa ran zata amsa shi yasa ya ce "Janan, ya naji kinyi shiru baki ce komai ba, ko dai banyi maki ba bakya so na?" Ya ƙare zancen cikin marairaice murya kamar zaiyi kuka, sai alokacin ta dawo hayyacin ta tare da sauke ajiyar zuciya, saurin sinne kanta ƙasa tayi jin yanda wata irin kunyar da bazata iya kallonsa ba ta rufesa, hakan yasa yayi murmushi tare da buɗe marfin motar ya fice, dama sun iso inda zata ajiye sa don haka sai ya leƙo ta jikin glass ɗin motar data sauke lokacin data kashe a.c, ya ce "Kar ki wani damu da bani amsa yanzu Madam, kije kiyi tunani mai kyau da kuma bawa ALLAH zaɓi, zaki iya ƙarawa da neman shawara ga amintattun ki da zasu iya faɗa maki gaskiya, nayi maki alƙawarin zamani duk hukuncin da zuciyar ki ta yanke a kaina, ina kuma saurarenki a kowane lokaci, ki isa lafiya ranki shi daɗe na gode" ya ƙare zancen yana kallon kyakkyawar fuskarta tare da sakar mata murmushi sannan ya juya ya bar wajen, a hankali ta ɗago kai tana ƙare masa kallo, don gaba ɗaya ɗauke mata kai yakeyi wasu lokutan, musamman idan yayi wasu abubuwan sai taga kamar bashi ba ne, gaba ɗaya sai ya sauya kamar ba mm mai dabino ba, yanzu ma yanda yake tafiya cike da natsuwa, izza da kuma burgewa sai ka ɗauka wani ɗan gaye ne daya mallaki wasu 'yan daloli, ta ƙare maganar a zuciyar ta haɗe dayin dariya sannan ta tayar da motar ta bar wajen zuciyarta cike fal da farin ciki marar misaltuwa, a hankali ta furta "alhamdulillah" ko ba komai shikenan daga yau haƙarta ta gama cimma ruwa, faɗuwa kuma tazo daidai da zama, lumshe ida nuwa tayi sannan ta buɗe tana faɗin, "Ina ƙaunar ka mm nima fiye da tunanin ka, na jima a kogin ƙaunar ka kuma koda baka furta kana so na ba, na tabbata zuciyata ba zata iya ci gaba da jurawa ba har sai na bayyana maka hakan ni da kaina, Ubangiji ALLAH ya zaɓa mana mafi ƙololuwar alkhairi my man" Haka tayita sabbatunta ita kaɗai cikin mota tana tariyo kalamansa dake faman yimata amsa kuwa acikin kunnuwa har ta isa gida. #pls Comment #vote #Share *ALLAH KA JIƘAN IYAYEN MU👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 15_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1234404906?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=fEqRI7OzKpcATYDeeKuHbztv83KSSFu%2BlVAh2pFHeI%2B05GRFznszicop%2FR%2FLaO1mgrCdgQHgk7B9iTSNtiB%2Fqdf0Bf%2Flcngj3XHr4wf9V9GhmopSknC83ERBVGuSion5_ *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B* INA KUKE MAKARANTA?? INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️ TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI. DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA (1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_ 👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 +447894142004 07065283730 ______________________________ Amira kuwa tana fita rasa inda zata je tayi, gaba ɗaya ma ta rasa ina zata saka kanta, fashewa da kuka tayi haɗe da ɗora hannu bisa kai ta ce, "Wayyo ALLAH na na shiga uku, me nayi maki ne haka Janan da kike nema ki ruguza mani rayuwa?, Me yasa zuciyarki ba zata yi maki adalci samun wanda kike so can daban ba sai wanda ƙawarki take so?, Why Janan? Wlh kin cuceni kin gama dani, kuma bazan taɓa yafe maki ba har sai na jefa ki acikin ƙunci da damuwar da kika sakani a cikinsu, sai kinyi nadamar cin amanata Janan" Duk wannan sabbatun da take yi bata ma san tana yi ba har ta haye tsakiyar titi saboda tsananin tashin hankali da take ji, Ingaski ne da yau shima ya wuni cikin ƙunci da damuwar abunda Janan tayi masa ya zo aguje cikin mota zai fita, tun daga nesa daya hango mutum tsakiyar titi yake ta horn har ya ƙaraso kusa da ita bata ji ba, da sauri ya juyar da sitarin motarsa don kaɗan ya rage ya kaɗeta, wani irin wawan burki ya taka da sai da shi kansa yaji tsoro, a fusace ya leƙo kansa da nufin gani wace fitsararriyar student ɗin ce yaga ashe Amira ce ƙawar Janan, kwafa yayi tare da tada motarsa zai tafi kamar ance ya kalli madubin gefen sa ya hango tana kuka, ribas ya dinga yi har ya kawo kusa da ita, "Amira lafiya?" Ya faɗa har kusan sau biyu bata ji saba har sai a karo na uku, shima ɗin sanadiyar danne horn ɗin motar da yayi ne sosai, cikin firgi cewa ta juyo tana kallonsa ya ce, "Ya akayi ne Amira?" Ai kamar jira yakeyi ta sake fashewa da wani kukan, ɗan tsaki yayi ba tare daya damu da student ɗin dake kai da komowar fita ba, ya ce "Shigo mota muje, lemme hear what happened to you" tare da miƙa hannu ya ɓuɗe mata can ɗaya side ɗin dake gefensa ta shiga, Ruwan gora ya ɗauki ya miƙa mata ba tare daya ce komai ba tare da hankacif yana ci gaba da tuƙinsa haɗe da kallon gabansa, "What is happening to you?" Shiru tayi ta kasa cewa komai sai faman shesshekar kuma take yi haɗe da ajiyar zuciya, ganin haka ya sa ya ce, "Where's Janan?" "Ban sani ba" ta bashi amsa tana goge majina a hancinta da hankacif ɗin daya bata, "Kunyi faɗa da ita ne?" "A'a" "What else? Ko ta faɗa maki wani abu ne?" "Eh" da sauri ya juyo yana kallon ta, don a tsammanin sa wanda ya shafi abunda ya faru tsakanin sa da ita ne ɗazun. "What did she said to you? "She cheated on me sir?" "How Amira?" Ya faɗa cike da mamaki don babu wanda bai san tarenta ita da Janan ba, ko yau she suna tare da wuya kaga ɗaya su baka ɗaya ba, cikin muryar kuka ta fara magana kamar hakan, "Sir, Janan is cheated on me, saurayin da nake so kuma nake ƙauna shi taje tana so, kuma tsabar cin fuska har tazo tana faɗa mun baki da baki, kenan tana so ta nunamun ƙarfin arziƙin mahaifinta akai nai, tana so ta aure shi saboda su suna da dukiyar da zasu iya samun duk abun da suke so aduniya, meyasa ?" Tunowa Ingaski yayi da abunda ta yimashi ɗazu shima, kenan tayi haka ne duk akan wannan saurayin da take so? Ya tambayi kansa tare da dukan sitarin motar da ƙarfi, cikin ɓacin rai ya juyo yana kallon Amira haɗe da cewa, "Waye shi?, Kina nufin duk abubuwan da take yimun a kansa ne?, Tabbas zan koya masa hankali daga shi har ita" Gaban ta ne yayi muguwar faɗuwa jin abinda ya faɗa daga ƙarshe da yanda taga idanuwansa sun bala'in sauyawa cikin lokaci ɗaya, "Malam shi fa baida laifi tunda ita ke son sa, ina ga ita ya kamata a hukunta tare da nuna mata kuskurenta" "Haka ne kuma" ya bata amsa yana ƙiyasto irin wulaƙancin daya tanadar mata, a daidai lokacin aka kawo inda Amira zata sauka ta ce, "Malam anan zan sauka" A bakin titi yayi parking haɗe da juyowa yana kallonta, ya ce "Karki damu Amira, indai Janan ce sai tabar maki saurayin ki haka kuma sai na nuna mata ita ba kowa bace acikin makarantar, yanda ta wulaƙan tani sai na wulaƙan tata, nasa tayi nadamar abinda tayi mana daga ni har ke, kedai kawai kisa ido" yakai zancen yana raɗa mata wata magana a kunnuwa, Dariya ta qyalqyale da ita tamkar ba ita bace ta gama kuka ba yanzu, "ALLAH malam?" "Sosai kuwa, kedai kawai ki bani haɗin kai ta yanda babu wanda zai san me muka shirya" "To malam na gode" ta faɗa cike da farin ciki sannan ta buɗe marfin motar ta fita, shi kuma ya ja motarsa yayi gaba, wani tsalle ta buga haɗe da cewa, "She..ya, yanda kika sakani kuka da baƙin ciki in sha ALLAH sai kema kinyi naki, mm kuwa ko kina so ko bakya so nawa ne sai kin bar mun abina don da ni kaɗai ya dace ba dake ba," (hmmm! To kunji fa!😁)🏃🏾‍♀️ Janan kuwa tana isa gida kai tsaye part ɗin aunty zee ta wuce bayan ta ajiye motarta a parking space, zaune ta taddata tsakar gida tana gyaran kayan miya ita da ɗaya daga cikin 'yan aikin Hajiya data turo mata don kada aikin ya yiwa madam florence yawa, fuskarta a sake ta gaisheta haɗe da zaunawa kusa da ita ta ce, "Masha ALLAH aunty Zee jiki yayi sauƙi?" "Eh sosai Janan, sai yanzu?" "Wlh kuwa, naji daɗin ganin ki wajen nan, hakan ya tabbatar mun da kin samu sauƙi" "Sosai kuwa, alhamdulillah" "To aunty ALLAH ya ƙara sauƙi" "Amin ya rabbi, Mariya tashi ki zubo mata abinci" "Aunty bara dai na shiga ciki na na fara watso ruwa" "To shikenan" Auntyn ta faɗa fuskarta kamar bata ji daɗi ba, dama inda sabo ya kamata ace ta saba izuwa wannan lokacin don haka Janan take aduk sadda ta shigo tayi mata tayin abinci, kuma tasan hakan ya samo asali ne daga mahaifinsu shi zai hana su saboda tunanin kada ta cutar masa dasu, ita kanta Janan bata jin daɗin hakan da takeyi, kawai tana time don kar asamu wata matsala wata rana bayan taci abinci wajenta ya zamana ta janyo mata matsala ko kuma damuwa tunda Abban ya riga daya hana su, shigar ma badon ransa na so takeyi ba sai dai kawai don babu yanda zai yi, amma in sha ALLAH itama wannan matsalar zata kawo ƙarshen ta, Tana shiga part ɗin su ta tadda Nihal ta fito gayu tana ƙoƙarin fita, "Ahhh.. Adda irin wannan gayu sai ina haka?" "Bari Janany darling zan je nemo the charming ɗina ne" "Wow! Are you kidding me?" Janan ta faɗa haɗe da ɗan zaro idanuwa. "Serious zan je bebeji supermarket na sake dubo abuna, don na tabbata wurin wajen zuwan sa ne" "Good luck Addah, bari na watsa ruwa, ki kula da titi" "Never mind sweet heart" ta wuce tana wani kar kad'a makullan mota dake hannunta tana taunar cingam, fuskarta saye da ƙaton rado daya mahe kusan rabin fuskarta. ***. ***. ***. A ɓangaren Razina kuwa tunda yayan ta ya furta mata kalmar so suka fara wasar ɓuya dashi, hatta makaranta da suke fita tare wani lokacin su ajiye ta dena tsayawa tayi, tun da safe zata shirya kafin su fito har ta wuce, amma zata iya tsayawa su sha firar su ta waya hankali kwance, yau ma tana falo zaune suna waya dashi mm da dawowar sa kenan daga inda aka neme sa wajen aiki ya shigo, da sauri ta katse wayar haɗe da miƙewa tana kallon yayan nata, "Sannu da dawowa ya Muhriz" basarwa yayi kamar bai gane me takeyi ba haɗe da cewa, "Yawwa Razina, ya karatu?" "Alhamdulillah" "Gud, Ina Momy?" "Tana ciki bacci takeyi,ko na kira ta ne?" "No ƙyaleta" ya faɗa tare da juyawa ya bar falon, a can gefen parking space ya samu ɗaya daga cikin kujeru dake gefe ya haye yana latsar wayar sa kafin lokacin sallahr magrib ya ƙara sa, Razina ya hango tafe ɗauke da tray da cup da kuma gorar ruwa da juice a kai, jawo wata kujerar tayi ta zauna itama tare da ɗaukar gorar ruwan ta tsiyaya a cup ta miƙa masa, ba tare daya kalli inda take ba ya karɓa ya shanye su taso don dama ƙishirwa yake ji, "Ammm..na kawo abinci yaya ko zaka jira ya Jabir ne?" Sai lokacin ya ɗago kai yana kallon ta haɗe da cewa, "Kina buƙatar na kirasa ne?" Sadda kai tayi tana murmushi ta ɗauko juice ɗin shima ta tsiyaya ta miƙa masa, wannan karon karɓa kaɗai yayi bai sha ba sai daya gama tura wani saƙo a wayarsa sannan ya ɗan kurɓa kaɗan tare da maida hankalinsa gareta yana ƙare mata kallo ta gefen idanuwa, magana take son yi dashi amma ta kasa sai faman wasa takeyi da yatsun hannuwanta da ƙafafuwa da suka kasa zama waje ɗaya, juyowa yayi yana kallon ta haɗe da cewa, "Lafiya dai ko Razina?" Sinne kai tayi ƙasa tana tattaro kalaman bakinta da take son faɗa masa, a zahiri saƙone take son isar masa akan alaƙar dake tsakanin ta da Jabir yanzu, amma kai tsaye a yanda take ƙoƙarin nunawa shawara ce ta zo da ita a wajen yayan nata kuma gudan jinin ta daya zamo uba kuma uwa agareta. #pls Comment #Vote #Share. *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 16_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari https://www.wattpad.com/1235096907?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=UrKwkb4z1Jz4wEArENoe6iGkRoKRHSo4NX5W1Zr9YVsLArG9Q97bJVIEFxK%2BJ0C%2B4D87fm3k5Tv7QxEm3g9jxqL9RYtwOD1%2FUeC%2FMNiof3sGTV0Jbwj4mKHQjz%2F4jf0J_ *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B* INA KUKE MAKARANTA?? INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️ TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI. DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA (1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_ 👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 +447894142004 07065283730 ______________________________ Kusan mintuna biyar suka shuɗe a haka Razina bata ce komai ba shima yaya mm baibi takan taba yana ta latsar wayar sa, ganin tabbas baza tace komai ba gashi yana so ya tashi yasa ya ƙarasa shanye juice ɗin dake hannunsa haɗe da miƙa mata cup ɗin yana ƙoƙarin miƙewa da sauri ta ce, "Amm...yaya magana nake son yi da kai fa" har tana miƙa hannu alamun tsaida sa, yana juyowa tayi saurin sadda kanta ƙasa cike da jin kunyar abun da take son faɗa masa, "Emhim..ke nake sauraro Razina, akwai wata matsala ce a school?" Ta girgiza masa kai alamun babu, "To meye? Faɗa mun mana ko kina da wani wanda ya fini banda Momy da zaki faɗa wa matsalar ki?" Nan ma sake girgiza masa kai tayi tana ɗan jan yatsun hannayen ta tamkar zata fizgesu, dariya ya yi tare dasa hannun sa ya janye hannunta da take faman jan yatsun ɗayan hannun dashi ya ce, "Kinga, barsu haka kada ki tsinkasu Razina, ai dai iya wahl kin basu ko so kike ki ragewa kanki sadaki garin jin kunyar abunda kike son faɗa?, Idan baza ki iya ba shikenan tashi ki shiga gida, idan na dawo Sallah ko zuwa anjima ne nayi waya" "A'a yaya, zan iya" "To ina ji" "Dama ni da yaya Jabir ne.." sai kuma ta kasa ƙarasawa, "Ke da yaya Jabir ne kuka yi me?" "Ya ce yana so..." Kafin ta ƙarasa sai ga Jibir ya shigo, idanuwansa kar a kanta har ya ƙaraso wajen, kamar da gaske ya ɗan rissina cikin girmamawa yana kallon mm daya juyo yana kallonsa ya ce, "Yaya ina wuni? barka da mare ce" wata irin kunya ce ta sake rufe Razina da sauri ta miƙe ranta tana faɗin shikenan ya gama tona mata asiri tun kafin ta faɗa da kanta, har wani hahharɗewa ƙafafuwan ta keyi tsabar yanda Jabir ya ƙura mata idanuwa har ta shige, shi kuwa mm mazewa ya yi duk da irin daɗin da ya jiya a ransa haɗe da cewa, "Mtssss, an dai yi abun kunya aboki ya koma yaya" tintsirewa da dariya Jabir ya yi haɗe da haye kujerar da Razina ta tashi yana faɗin, "Na dai ji, so ne ya jamun, alƙur'an ma in baba kake so na kiraka zan kiraka, roƙona dai kasa mani hannu kuma ka buga stamp, da kayi hakan shikenan ka biya ni yayan mu" "Wai da gaske kakeyi Jabir?, Razina fa ƙanwar kace kuma a nawa tunani tayi maka ƙaramar" "Eh, ƙara dai da kace a naka tunani, ALLAH yasa yau aka haifi Razina a haka nake son abuta, in kuma buƙulu zaka yimun sai na canja wajen neman auren na koma wurin Momy" "Ahh...kawai nasan dai kafi son irin riɗa-riɗan matan nan ne, Razina kuma sai naga kamar tayi ma ƙanƙanta" "To ɗan baƙin ciki Renon ta zanyi, ina shikenan ko?" Jabir ya faɗa cikin 'yar ƙwagewa tare da ɗaukar gorar ruwan dake wajen ajiye ya tsiyaya a cup ɗin da ya gani yana sha, dariya mm ya yi da sai da duka haƙoran sa suka bayyana haɗe da cewa, "Au! Yayan ne ma ɗan baƙin ciki?" "Tuba nakeyi man.." ya faɗa tare da riƙe hannuwanta yana ci gaba da cewa, "Wlh ina son Razina mm, ina yi mata wani irin so da ni kaina bansan adadin sa ba, bansan lokacin daya shigeni ba har yayi mani mugun kamu haka, kawai tsintar kaina nayi a cikinsa, kuma na tabbata bazan taɓa iya ci gaba da rayuwa ba sai da ita" "Jabir kenan, har kana ganin akwai abun da yake mallaki na aduniya da ba naka ba? Wlh ba Razina ba rayuwata duka zan iya sadaukarwa wakai da kuma Momy, yanda nake da iko da duk wata power akan Razina kaina kana da ita, don haka ka dena neman alfarmar auren Razina a waje na domin kai mai iya yin ta ce a wajen wani balle ma kai da kan ka, iya nawa shine nayi maku addu'a ALLAH ya tabbatar da alkhairi kuma ya kauda duk wata fitina dake iya ɓullowa tsakanin ku, ina murna da farin ciki akan wannan lamari ɗari bisa ɗari" Rungumesa Jabir da har sai da ya yi hawayen jin daɗi ya yi tare da cewa, "Thank God for the gift of brother also a friend like you, always proud of having you yayan mu" Ɗan naushi mm ya sakar masa aciki da sauri ya sake sa daga rungumar da yayi masa yana faɗin, "Awwshh..." "Bana son sunan nan, just keep it a side kada ya saka wani abu tsakanin ni da kai da zaka iya ɓoye mun, i dont like it" ya ƙara sa maganar yana kaɗa masa ya tsansa haɗe da yin dariya, "Shi kenan tunda baka so, ai Over my died body hakan bazata faru ba, ka manta banda wani ɗan uwa a duniya sama da kai kai kaɗai, kuma kai ne kaɗai aminin da nake dashi kuma babban yayan mu" "Are You sure?" "Sosai kuwa" Jabir ya bashi amsa tare da tsiyaya lemun yana sha, Kiran sallar da akayi na magrib ya sa su miƙewa tare suka yi arwala part ɗin su suka nufi masallaci, zuciyar kowanen su cike da farin ciki akan faruwar wannan lamarin. A ɓangaren Razina ma haka ta kasance duk da gabanta sai faman faɗuwa yakeyi saboda rashin sanin me yayan nata zai ce, zai amshi soyayyar su ne ko kuwa?, da wannan tunanin da takeyi aka kira sallah taje tayi arwala tayi Sallah, addu'a tayi sosai akan ALLAH ya daidaita raayinta dana yayan ta don kuwa ita kanta son yaya Jabir ba kaɗan yayi mata kamu ba, tana idarwa ta shafa haɗe da miƙewa ta nufi ɗakin Momy, addu'ar ta isko itama tana yi don haka sai itama ta zauna a kusa da ita tare da ɗaya hannayenta kamar yanda Momyn tayi har ta kammala ta shafe a fuskar ta, itama shafewa tayi haɗe da ɗora kanta a saman ka faɗar Momy tana gaisheta, sai da Momy tayi murmushi tukuna sannan ta amsa ta haɗe da cewa, "Kina lafiya autan Momy" "Lafiya klw Momy, me za'a aza yanzu?" "Ai tun ɗazu baki aza komai ba?" "Eh naga bacci kike yi shiyasa ban ɗora ba saboda bana so na tasheki" "Ayya, come here my baby, good bless you ko!" Momy ta faɗa tare da buɗe hannuwa ta rungume Razina, (kun san halin ƙabila, ko sun musulunta akwai ɗabiun da komai daren daɗewa komai shekaru basa sakin su, shiyasa har yanzu Momy take da wasu daga ciki ɗabi'un su). Ɗagota tayi ajikinta kafin taci gaba da cewa, "but my dota from today ko ina bacci karki sake jirana zancen ɗora abinci, yanzu past 7, akwai wahalarwa sosai kafin a ɗora abinci a gama, musamman yayyunki da basa wuni a gida, zasu iya buƙatar abinci da sun dawo sallah" "Momy they have not eating their lunch fa, sai a basu shi suci kafin agama wannan" "Yeah is true, but do you think zasu iya cin shi yanzu? Karki manta da tun 1 aka gama" "Momy a kula fa yake" "Even dough, yanzu muje dai naga me zamuyi mai sauƙi da zasu iya jira in the next 30minute" Ta ƙare zancen haɗe da miƙewa ta cire hijabin, karɓa Razina tayi ta linke ta ajiye a gefen gado sannan suka fita suka nufi kitchen, kasancewar su mm basu shigo ba sun tsaya watsa ruwa a can part ɗinsu yasa har su Momy suka ɗora tuwon alkama da miyar kuɓewa ɗanya ta sha bisashen kifi, da tamarin juice da aka sakawa jinja da kokuma ba basu dawo ba, gaba ɗaya falon ya ɗauki daddaɗan ƙamshin abincin, dama tuni Momy tasan suna son cincin sosai don haka tasa Razina ta ɗebo fulawa gwango uka ta haɗa haɗinsa, ita kuma take tayi sallar isham don har lokacin basu shigo ba, tana gamawa tazo ta karɓi Razina itama taje tayo sallahr ita kuma ta fara suyar cincin, tana tsakar suyar su mmm na shigowa daidai lokacin itama Razina ta gamo sallar zata shiga kitchen, gyaran muryar da Jabir yayi lokacin daya hangota ya sata ɗagowa ta ƙasan idanuwa tana kallonsa, murmushi ya sakar mata haka itama sannan ta ƙarasa daga cikin kitchen ɗin, "Momy they're back" "Ok, je kiyi serving ɗin su kafin na ƙarasa wannan, akwai man shanu a cikin wancan bowl ɗin ki haɗa dashi" Cike da natsuwa Razina ta ɗauki plate's ɗin da spoons da man shanu ta wuce, dama tun ɗazu ta jerikke kulolin akan dining table, gaishesu ta fara yi kafin ta fara ƙoƙarin buɗe kulolin zata zuba masu, riƙe cokalin Jabir yayi haɗe da cewa, "Koma ki zauna mana ƙanwata, kiyi abinci kuma ki koma zuzzuba mana?, yau dai na hutasshe ki ni zan zuba mana da kaina" ya ƙare zancen tare da jawo mata kujerar dake kusa da shi yayi mata nuni da idanuwa ta zauna, magana ta je yi ya haɗe fuska tamkar ba shi ba, ba yanda ta iya dole ta zauna ya sakar mata wani ƙayataccen murmushin da sai da ya sa zuciyarta kaɗawa yana fad'in, "Gud girl" tare da zuzzuba masu abincin, ita dai sadda kanta kawai tayi ƙasa tana wasa da yatsun hannunta yayin da shi kuma mm ke latsar wayar sa yana shigar da wasu baya nai aciki, turo masa plate ɗin da yaga anyi a gabansa ana faɗin babban yaya ga naka ya sashi ɗagowa suka yi ido biyu da Jabir ya ƙyalla masa idanuwa, girgiza kai kawai mm yayi

Chapter 9 of 40