Share this page
Ni nace maku Amira ce silar faruwar haka agareni?, Wannan wane irin ɗaukar mataki ne haka kukayi ba bincike?, Faɗa mun kai ne kasa a kamata ko" ta faɗa tana kuka haɗe da kwace hannun ta daga riƙon daya yi mata, "Pls Janan, ki natsu muyi magana, kin fa san ko wace Amira, zata iya aikata maki komai" "No..Amira baza ta so na malam ce ba, kawai kusa a saketa ni babu wanda ya aikata mani hakan, kaje kasa a sake mata yarinya ni ba ruwana, wannan ai ɗaukar alhaki ne, kasan ko wacece Amira kuwa?, Kasan wace irin rayuwa sukeyi a ɗan ƙaramin muhallin da suka wadata zuciyar su dashi suna rayuwar su cike da farinciki? Kasan halin da mahaifiyar ta ke ciki na rashin lafiya kuwa?, kasan irin taimakon da suke buƙata arayuwa? Shine zaka sake cillasu a cikin wani yanayin haba hubby, wannan ba dai-dai bane kuma sam ba halin ka bane, kawai kasa asaki yarinyar mutane domin ni bata yimani komai ba" tana gama faɗar haka ta miƙe tana lalaben hanyar komawa cikin gida, so yakeyi ya taimaka mata amma ta shiga buge masa hannuwa tana faɗin, "Bana so, kaje kasa asaki ƴar muta ne kawai, ni ba abunda tayi manit" "Ok naji, Amma bari na taimaka maki tukuna kada ki bugu" ya ƙare maganar tare da lallaɓata har ya samu ya maida ita cikin gida tare da yiwa Hajiya sallama kansa a kulle, to me Janan ke nufi? Kenan tana so tace ba hannun Amira acikin abunda ya faru da ita? Ko kuwa dai so take ta kareta kamar yanda ta saba yi akoda yaushe. _Kuyi hakuri dashi, in sha ALLAH gobe zaku samu mai yawa_ *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/28, 12:06 AM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 62_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ********** ______________________________ Tafe yake a zuciyar sa yana yiwa kansa wuɗan nan tambayoyin daya kasa samawa kansa amsoshin su kafin ya fiddo wayar tasa ya sake kiran Sajan Maryam, bugu ɗaya ta ɗaya haɗe da cewa, "Yes sir" "Where's is the woman?" Kafin ta bashi amsa ya ci gaba da cewa, "just allow her to see her" "Sir she's already gone" "Ok, next time zaku iya barinta ta ganeta, zan yi magana da shi inspector Sadeeq ɗin" "Ok sir, thank you" Kashe wayar ya yi tare da shafa kansa yana jin maganganun Umma na sake dawo masa a ƙwaƙwalwa, so yake yi ya tuna a ina ya taba jin shegen muryar baiwar ALLAH nan amma ya kasa, jin da ya yi kansa na ƙoƙarin fara ciwo sakamakon matsawa ƙwaƙwalwarsa da tunani da ya yi yasa ya kunna ƙira'ar sudaisa yana bin karatun a hankali har ya ƙara sa gida, yanda Momy taga fuskarsa kamar ɗauke da damuwa yasa ta zaunar dashi tana tambayar sa meke faruwa, bai ɓiye mata komai ba ya sanar da ita yanda sukayi da Janan akan case ɗin Amira dake kulle, shiru tayi haɗe da cewa, "A gaskiya ya kamata ka duba zancen ta, takan yuyu kayan aikin ne aka samu matsala ƙilan sunyi expired" "A'a Momy, hakan bazai taba yuyuwa ba saboda ba ita kaɗai ce a kan ɗin ba, taya za a yi ace na kowa lafiya suke amma nata ya yi expired, dole fa akwai wani abu a ƙasa" "To idan haka ne kaga bincike ya kamata a fara yi daga can makarantar tasu don samo bakin zaren" "Haka ne Momy, shiyasa binciken mu ya fara akan Amira, domin tafi kowa kusanci da ita acikin makarantar kafin su fara samun matsala daga baya ta sanadiyar ita Amirar data nuna cewa tana sona, duk da Janan bata nuna damuwar ta akan hakan ba, kawai ita kaɗai ke shirmen ta kuma na tabbatar da tana jin haushi sosai ganin Janan ɗin nake so ba ita ba, kinga kuwa dole bincike ya fara ta kanta" "Eh gaskiya dole a tuhume ta, koma dai meye abu abun a hankali, koda ba zakayi kamar yanda Janan ɗin ta ce ba, Ya kamata kabari ko mahaifiyar ta ce ta riƙa ganin ta, kasan mu mata muna da rauni, dole zata shiga damuwa sosai akan halin da ƴar tata take ciki" "Shikenan Momy, Bara naje na kama masu Mu'azzam hotel ɗin da zasu sauka, don munyi waya dashi ya ce sun sauka suna kano har ma sun kamo hanya" "Masha ALLAH, ALLAH ya kawo su lafiya tare da iyalin nasa suke tafe?" "A'a gaskiya, kin san yanda abun yazo kwatsam a ƙurarren wuri shiyasa bai zo dasu ba tunda bai shirya komai ba, tare dai suke da wasu abokanan namu" "ALLAH sarki, to ALLAH ya kawo su lafiya" "Amin Momy, ina Jabir ne da Razina" "Na aiki Razina, shi kuma yana can gidan na turasa yakai kayan kitchens ɗin da aka siyo, kayi waya da baffan ka kuwa?" "Eh munyi waya ɗazu, ya ce ma su Umma Mariya na nan tafe suma" "Eh haka ya faɗa mun, har ma an gyara masu ɗaya ɓangaren can da zasu sauka, ALLAH ya kawo su lafiya" "Amin Momy, thank you so much" ya faɗa tare da rungume ta, murmushi tayi haɗe da cewa, "Yau kuma ni yaro na ke yiwa godiya, for what?" "For everything Momy, I love you so much" "Luv you too my boy" ta faɗa tana ƙara jin ƙaunar sa aranta, bata dai san yanda mahaifiyar sa tayi ta haifesa ba amma gaba ɗaya abubuwan daya kamata ace ita yake yiwa ya kasance ita yake mawa, a hankali bayan ya fice daga falon ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa " ya Ubangiji ALLAH ka bayyanar masa da mahaifiyar sa aduk inda take matuƙar tana raye domin ta mori ɗan ta da nake cin ga jiyar sa" adduar ta kenan akoda yaushe tunda ta samu labarin mahaifiyar tasa tare da fatan tana raye bata mutu ba, haka kuma ko yaushe cikin aikawa da sadaka take a masallatai da kuma makarantun islamiya tana cewa a taya su addu'a, shi kanshi mm duk dare baya bacci dashi har Jabir, Razina ma haka suna masu tsananta addu'ar da Momy ta koya masu haɗe da istigfari ALLAH ya bayyana mahaifiyar su duk inda take, wanda ko shakka babu hakan yayi matuƙar tasiri akan lamarin shiyasa sauyuwar abubuwa keta wakana ba tare da sun fahimci hakan ba. A ɓangaren mahaifin Asgar kuwa tuni ya yi nasarar sa a tura Asgar wajen wani aiki da har bayan ɗaurin auren bazai dawo ba sai ya yi sati ɗaya, kusan hauka Asgar ya yi lokacin daya samu takardar turasa aiki a daidai lokacin auren sa inda ya ce shi babu inda zai je sai dai ya rubuta takardar ajiye aiki ya basu, ba ƙaramin ɗauki ba daɗi akayi dashi ba kafin ya amince da tafiyar don saida mahaifin nasa ya nuna masa ɓaci ransa sosai haɗe da cewa matuƙar yace ya fasa tafiyar to tabbas zai cire hannunsa ga dukkanin lamarin sa, ciki kuwa har da zancen auren nasa da zai ajiye aikin nasa akan sa, babu yanda ya iya dole ya haƙura ya tafi badon ransa ya so ba yana mai jin wani tuƙuƙi da baƙin ciki aran sa, inda tun ana saura kwana biyu ɗaurin auren mahaifin Asgar da kuma ƴan uwa da abokanan arziƙi da zasu halarci ɗaurin auren daga can ƙasar yugurnda suka fito ƙasa Nigeria, wanda gaba ɗayan su Abba ne ya nema masu masauki a babban hotel ɗin dake cikin garin mafi kyau da kuma tsada, ya kuma buɗe bakin aljihun sa yana kashe masu kuɗaɗe wajen kula daci da kuma shan su, haka ma gidan sa gaba ɗaya ya sa an canza funitures ɗin dake ciki da coutins, an kuma sake fenti, haka ma Hajiya ya sa an je anyi mata sabon fenti, ko ina sai ƙamshi yakeyi da taltalniya, Nihal kuwa dama ba wasu abokanai ne da ita ba haka kuma acewar ta tunda ba auren da take so bane babu wanda zata gayyata, in son samu ne ma bata so kowa yasan da cewa tayi auren, shiyasa bata damar da kanta da wani shiri ba da sunan amarci, da Hajiya zee ma tayi ƙoƙarin gwada bata wasu abun don ta gyara ta magana ta sakar mata, hakan yasa ta ƙyaleta tare da fita shirgin su ta zuba masu idanuwa, Janan kawai ce idan taje dubawa take ɗan ƙoƙarin bata tana sha tare da fahimtar da ita cikin hikima akan amfanin da zasu yi mata don data gama aikin gida acan gidan Hajiya take tare wa suna shirye shiryen bukin, anan ma ranar ta sake haɗawa da mm, inda da kansa ya yimata zancen Ahfan da ruƙayya, ta matuƙar jin daɗi sosai da hasashen nata ya zamo gaskiya, nan take ta kira Ruƙayya ta sanar da ita zancen haɗuwar ta da Muhriz ɗin wanda dama tuni Ahfan ya faɗa mata komai, ta kuma ce idan mijinta ya amince ya kamata itama tazo wajen bukin ko badon ɗan uwan nata, Jabir da Razina kuwa iyayen biki ƙirjin biki, gaba dayan su sun rame saboda yanda basu zaune basu tsaye akan hidimar auren, Muhammad Muhriz kuwa tuni ya tare hotel ɗin daya kamawa abokanan nasa da sai faman hidimar haɗa reception ɗin da suka shirya bayan auren sukeyi, da yunƙuro da zancen bada kuɗi a kara dasu cewa sukayi basa buƙata kawai yaje yaji da amaryar sa idan akwai abunda take buƙata su kuma ya barsu suyi shirye shiryen su, haka ma a ɓangare ɗaya gaba ɗaya mutanen wajen aikinsu dake can Abuja duk sun hallara, wayewar safiya kawai suke jira a ɗaura auren da dukkanin su ke matuƙar taya sa farinciki, gudun mawa kuwa har mamaki suke basa don shugaban wajen aikinsu sukutum ya bashi kyautar mota saboda yanda yake jin daɗin aiki dashi, kuɗaɗe kuwa saidai kawai yaji alart, daga masu dubu ɗari sai masu ɗaruruwa, wasu kuma kyautukka ne suka kawowa Janan, hatta abokanan sa turawa dake ƙasar waje duka sun samu isowa suma tare da tarin kyautukka da suka haɗo masa, tsabar farin ciki harda ƙwalla ya yi don bai taɓa tsammanin cewa yana da mutane kamar haka ba, a daren daga shi har Janan babu wanda ya runtsa suna maƙale da juna a waya har aka kira sallar asuba saboda farinciki da kuma muhimmancin dake cikin zuwan wannan ranar. Su Umma Mariya kuwa tuni sun hallara Bus guda hadda wasu matan garin da suka yowa su Baffa kara, kuma sun samu kyakkyawar tarba wajen Momy tamkar sun saba da ita, hakan yasa gaba ɗayan su aka taru ana ta hidimar dafe dafen abincin da za a tarbi baƙi dashi, wanda hakan ba ƙaramin farinciki ya saka Momy ba. Alhamdulillah, rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, tun da safe Hajiy ta kira Hajiya zee ta ce tazo ta ɗauki Janan su je da ita can gidan Abba domin a har haɗa mata kayanta da take buƙata bayan tayi mata nasiha mai kashe jiki akan aure da kuma muhimmancin dake cikin sa, ta kuma yimata addu'a ALLAH ya bata zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba ya kauda sheɗan acikin auren ta, kasancewar Abba ya faɗawa Hajiya cewa ta sanar da mm ana gama ɗaurin aure ya turo a ɗaukar masa amaryar sa shiyasa grandma ta yanke hukuncin cewa ƙara azo a tafi da Janan idan za suje ɗaukar amaryar su je can gidan mahaifin nata su ɗauke ta, Janan na kuka suka rabu da Hajiya kaka, inda driver na fita dasu Ruƙayya ɗiyar Aunty zee data iso tun da safe ta ce ya wuce dasu HURRIYA'S TOUCH ganin amaryar tasu tamkar ba amarya ba dom ko ƙunshi ba tada, dama tare suka zo da Hajiya zee anan gidan grandma ɗin, gyaran kai da ƙunshi tasa akayi mata, wanda nan take cikin awannin da basu wuce uku zuwa huɗu ba aka gama gyare Janan ta fito sai amaryar ta, ita kanta jin takeyi ta fita daban tamkar ba ita ba duk da ba ganin gyaran da akayi mata takeyi ba, ganin akwai sauran lokaci don sha biyu da rabi yasa Ruƙayya tace a haɗa mata da gyaran jiki tasan zuwa ƙarfe biyu dai anyi komai an gama, daga farko kin amincewa Janan tayi amma da Ruƙayya ta kira mm ta sanar masa amaryar sa taƙi tsayawa a gyare masa ita sai ya kirata ya lallashe ta haɗe da nuna mata cewa tasa aranta indai tana tare da ita baza a taɓa cutar da ita ba, kuma zai turo mata Razina yanzu don ta ƙara kula masa da ita, hakan yasa ta ƙara samun natsuwa ta kuma amince aka yi mata gyaran, ko mintuna goma ba a yi da fatawa ba Razina ta iso tare da kayan da mm ya tanada kala uku da amaryar sa zata saka a wunin, lokacin Janan na can cikin ɗakin da ake yimata gyaran jiki, Ruƙayya kaɗai ta isko anan wajen da aka tanada don masu zuwa dama Hajiya zee da driver ya ajiye su ita wucewa ya yi da ita saboda kiran da Abba ya yi mata akan tayi sauri ta dawo saboda ga baƙi nan nata zuwa ba ta nan, "Sannu aunty Ruƙayya ina wuni?" "Lafiya klw Razina, ya kike ya hidima?" "Alhamdulillah Aunty Ruƙayya, hidima ai tauku ce, dangin ango dangin amarya" "Ai kuwa, amma dai bar ni a dangin angon don sai nafi kima da marta ba, nima zuwa anjima kaɗan ina nan zuwa gidan Momy mu tar bi amaryar mu" duk suka sa dariya tare sannan Razina ta nemi waje ta zauna tana faɗin, "Yawwa Aunty Ruƙayya, ga kayan amaryar ku in ji yaya mm" "Au na zata fa suna can gida ko gidan Hajiya" "A'a wlh, dama da safe yake cewa naje naje na kaimata su gidan Hajiya sai gashi na tafi wajen ƙunshi da niyar idan na dawo zuwa ƙarfe goma zan kai mata, to har naje can ɗin sai Hajiya ta ce naje tana gidan Abba, ina kan hanya sai gashi ya kira ya ce nazo nan nasa me ku, ga ma kuɗi ya ce na baki da za'a biya na gyaran da akayi mata" ta ƙare zancen tana miƙa mata dubu hamsin da mm ya ce ta bata cikin kuɗin dake hannun ta ita kuma yayi mata transfer ɗin su a account ɗin ta, Ƴar hararar ta tayi kafin tace, "Ina ga Razina ƙarawa kanki laifin da kike dashi a guna zakiyi" "A'a aunty nifa ƴar saƙo ce, kuma wlh ana gama bukin nan ya Jabir yace zai kaini wajen ki na goge laifina, kiyi haƙuri don ALLAH" "To shikenan, ki mayar masa da kuɗin sa zan biya duka a matsayin gudun mawata" "To Aunty ALLAH yaƙara buɗi yabar zumunci" "Amin" Haka suka ci gaba da firar su kafin can miss hurriya ta fito karɓar kayan da Janan zata saka, kamar ta sani kuwa anzo dasu don haka sai Razina ta miƙa mata, wata doguwar rigar atamfar mai golden ɗinkin Abuja gown ta ɗauka ta kaiwa Janan ta saka sannan ta fito da ita, tun kafin ta ƙaraso wani irin ƙamari ya daki hancin su, tsayawa faɗar irin kyan da Janan tayi ɓata lokaci ne da sauri Razina ta miƙa ta riƙota tana faɗin, "Wowwww! Aunty Janan ɗin mu ce haka, tubarkallah masha ALLAH, fatabarakallahu ahsanil halkiƙeen, ta ƙare zancen haɗe da fiddo wayar ta tana ɗaukar Janan dake tsaye sai faman murmushi takeyi, ita kanta wani irin daɗin jikinta da sanyayyen iska take ji na ratsata tako ina wanda ko ba'a tambayeta ba itama tasan ta sauya kuma tayi kyau, riƙo hannun ta Razina data gama ɗaukar hotunan tayi haɗe da cewa, "Aunty Ruky ya kika ga amaryar ya mm ɗin mu?" "Masha ALLAH, she was looking so wow!" Suka dariya tare, rokon hurriya Ruƙayya ta shiga yi don ALLAH tazo ko ta basu cikin yaranta suje da ita a yiwa Janan ɗin make up, don har lokacin da sauran lokaci saboda ko ƙarfe ɗaya bata ida bugewa ba, tabbatar mata tayi da su tafi zata zo zuwa ƙarfe biyu tayi mata in sha ALLAH tare da karɓar address, ba tare da sun damu da rashin motar da zata maida su ba suka tare napep suka wuce gida, Ƙarfe ɗaya da rabi nayi babban masallacin juma'ar dake anguwar su Abba ɗin ya cika da mutane maƙil ƴan wurin aure, wanda kana gani kasan bana ƙananan mutane bane saboda yanda manyan motoci ke magana awajen, wani abu daya ɗaurewa Abba kai shine yanda manyan gidajen rediyo da talabijin da ƴan jaridu suka cika wajen, wanda shi yasa bai gayya to su ba amma sai ya ta'allaƙa abun da sunan da yayi ajahar ne da kuma matsayin aminin nasa na wakilin ƙasa wato ambassador a ƙasar yugurnda, Har aka fara gudanar da ɗaurin auren mm da abokanan sa basu iso ba, Baffa kawai ne da kuma ayarinsa da sukayi mota biyu acan ƙauyen, suna ji suna gani aka yiwa iyayen Asgar masauki na musamman amma su aka barsu gefe zaune, ba tare da sun damu ba suna kallo aka ɗaura auren *Asgar Hussain Salim* da amaryar sa *Nihal Usman mai fata* bisa sadaki Naira dubu ɗari uka lak'adan ba ajalan ba, wanda mahaifinta ne da kansa ya bada auren nata ga mahaifin Asgar, ana gamawa kuma aka gabatar dasu Baffa da yasha sabuwar shaddar sa fara mai kyau da mm ya ɗun tka masa shi da aminin sa, wanda liman ɗin masallacin ne wakilin Janan da Abba ya wakilta, ana ƙoƙarin ɗauka auren comboi ɗin motocin su mm da abokanan sa suka iso wajen tare da ƴan sanda da suka tako masu baya suna buɗa masu hanyar da zasu wucewa har suka ƙara so cikin masallacin, mamaki ne ya kama Abba ya shiga kallon su har suka ƙara so wajen suka zauna ba tare daya gane mm ɗin ba acikin su, anan liman ya fara gabatar da sigar aure a musulunce data tabbatar da ɗauruwar auren *Muhammad Muhriz Muhammad* da kuma amaryar sa *Janan Usman mai fata* bisa sadaki dubu ɗari biyar da kuma makullin mota laƙadan ba ajalanba, wata irin juyowa Abba ya yi haɗe da kallon liman ya ce, dubu ɗari biyar ko dubu biyar liman?, Kuɗin da kuma makullin motar ƙirar Honda mai bala'in tsada da kuɗin ta zai kai kimanin miliyan biyu da rabi liman ya aza agaban sa yana faɗin, "Abunda kunnuwan ka suka jiyo maka hakan ne, wato dubu ɗari biyar da kuma makullin mota, kana mamaki ne? Ai dama kowane ɗa da kalar arziƙin sa" Murmushi mm dake kallon sa ya saki haɗe dayin magana akunnen Baffa ya ce a faɗawa liman ya ƙara wasu dubu ɗari biyar akai tare da kujerar hajji, kabbar akayi wuɗan da ke wajen lokacin da liman ya sake yin sanarwar ango ya ƙara dubu ɗari biyar a dakin amaryar sa da kuma kujerar Hajji, inda nan take hankula mutane da ƴan jaridu suka dawo kan mm da iyayen sa ana mamakin wannan wane irin mai kuɗi a haka zai auri yarinyar, inda wasu ke surutun abun ya zama almubazzaranci wasu kuma suna faɗin yarinyar ta cancanci komai saboda halin ta ba irin na mahaifin ta bane, wanda azahiri ma wajen ɗaurin auren sun ga yanda abbtan ya banban ta tsakanin auren ƴaƴan nasa saboda suna tunanin talaka ne, sai gashi talakan ya bada mamaki fiye da masu kudin don sai da ambassador da jama'ar da suka rena kansu awajen, wanda hakan ba ƙaramin ƙona masa rai ya yi ba, ana gama ɗaurin auren wasu jami'ai na musamman daga waje suka riƙa shigowa ɗauke da dardumomin sallah dake ɗauke da sunan Janan da mm suna rarrabawa mita ne manya da ƙanana kafin nan kuma abada sanarwar cewa akwai reception na musamman da aka shirya ga duk wanda yazo daurin auren a falala hotel don aci a sha a ƙoshi, kuma akwai motoci a waje da aka tanada da zasu ɗauki nauyin kai wuɗan da basu da abun hawa a wajen tare da maido su, wani irin gumin Abba ya shiga sharewa cike da mamaki, ganin komai yakeyi tamkar a mafarki, bai gasgata hakan ba sai daya ga abokanan mm sun zo sun take masa baya shi da su ambassador Hussain domin yi masu rakiya zuwa reception ɗin da za a gudanar da taron, da kallo kawai yake bin su don har lokacin bai gane mm ba acikin su, Tun abakin hotel ɗin suka fara haɗuwa da ma'aikatan hotel ɗin saye da riguna masu ɗauke da sunan Janan ɗin da mm, ansa thanks for the coming suna welcoming ɗin mutane cikin girmamawa ga wata kafuwan bandana dake ɗauke da hoton mm da Janan da sukayi aranar da suka je Taula arena a saman gaban hall ɗin da aka shirya taron da gefe gefe, kan Abba ne ya shiga jujjuyawa yayin da Ambassador Hussain ya cika fam yana ganin dama cutar ɗan sa Alhaji Usman ya yi don ya samu wanda ya fishi arziƙi ya hana masa ƴar sa, in kuwa haka ne zai koyar dashi hankali ya kuma shayar dashi mamakin da bai taɓa zato ba...... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/28, 11:38 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 62_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ********* _GAISUWA TARE DA FATAR ALKHAIRI AGAREKA *IT'S ABBAS (BABBAN MUTUM)* NA HANNUN DAMAR MK, WANNAN PAGE ƊIN NAKA NE KAI DA ƘANENA *MUHAMMAD KAREEM* NA GODE DA GUDUMMAWAR KU ACIKIN KOWANE RUBUTU NAWA, UBANGIJI ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKAHIRI YA RABAKU DA DUNIYA LAFIYA, ALLAH YA FARANTA ZUKATANKU TARE DA ZABA MAKU ABOKANAN ZAMA NAGARI HAƊI DA DUKIYA MAI YAWA DA ALBARKA_ *GABA ƊAYAN WANNAN LITTAFIN NAWA SADAUKARWA NE GAREKI AUNTYNAH HADIZA D AUTA, INA SO KISANI INA SON KI AKODA YAUSHE DUK GIRAMAN TSANANI DA KUMA SAUYAWAR YANAYI, UBANGIJI ALLAH YA KULA MANI DA LAMARIN KI A KODA YAUSHE HAR ZUWA YAUMU LAA YUB ASUN* ______________________________ Duk da taron bana dinner bane ba kuma anyi sa ne don casu ko wani abuba hakan bai hana sound ɗin kiɗa mai taushi tashi daga cikin hall ɗin ba, sauti ne mai tsananin daɗin saurare da kuma ratsa jiki sai hasken fitillu dake haska wajen da wasu irin launona masu matuƙar ɗaukar hankali, waje ne na musamman da aka tanada domin iyayen ango da kuma amarya aka kai su Baffa da mutanensa da kuma Abba da Ambassador da sauran manyan baƙin su, dama tuni ma aikatan hotel ɗin sun cike kowane benci da zai ɗauki aƙalla mutane takwas da manya manyan tireruwan snacks naman rago gasashshe, naman kaji soyayye, tsire priderice da tasha haɗi da kayayyakin lambu, da sauran cimakar da idanuwana baza su iya cewa ga ko meye ba, ga kuma juice juice masu matuƙar tsada da ruwan gora a gefe, sai ƙwanƙwon sakace haure da tissue paper dake ajiye a tsakar bencin, haka kuma agaban kowane mutum ɗaya akwai plate da spoon da pork haɗi t da irin ƴan yuƙaken nan da turawa ke amfani dasu wajen cin abinci tare da cups ajiye, kowa sai abunda ya yi masa zai ci kuma zai sha, ba nan abun ya tsaya ba a gefen kowace kujera da mutum ya zauna zai tadda matsakaiciyar jikka dake ɗauke da, biro, handcachip, ceremonial books da kuma cups dake ɗauke da hoton amarya da ango aciki, iya naka kawai ka ɗauka idan zaka tafi, haka kuma ma'aikatan basu zauna ba sai round suke yi incase ko akwai wanda zai buƙaci wani abun, banan abun zai baka shawa ba, yanda abokanan ango gaba ɗayan su suka taru inda aka tanada domin iyayen amarya da ango suna yimasu sarving abinda duk da zasu ci da kansu, acewar su wannan wata hanya ce ta girmama iyayen nasu da kuma mika godiya agare su, dukkan su saye suke da fararen shaddodi da suka matuƙar yi masu kyau, hatta abokanan sa turawa da suka zo suma shaddodin ne ajikinsu suka sa abun tubarkallah sai ɗaukar idanuwa suke yi, wani iska ambassador Hussain ya furzar ta baki haɗe da sauke ajiyar zuciya ya juya yana kallon Abba da har lokacin sai faman goge gumin yakeyi da gefen babbar rigar sa yana faman raba idanuwa, Muryar Jabir ya jiyo ta kansa cikin girmamawa tamkar ba shi ba yana faɗin, "Haƙƙin mu ne kula da jin daɗin duk wani baƙo daya hallara a wannan bukin namu, don haka zaka iya yin magana Abba idan akwai wani abun ko kuma abunda kake buƙata, na tabbata yanzun nan

Chapter 38 of 40