za a yi, kuma kadena wannan ƙuncin haka bana so kaji ko?"
"In Sha ALLAH Hajiya"
"Yawwa, sai kun iso yanzu can na nufa kafin ku ƙara so, ko ƙarfe nawa zaku kai da yardar ALLAH dole ya saurare ku, saboda haka kuyi komai a hankali saboda gaggawa aikin sheɗan ne kuma shike haifar da tarin nadama"
"To Hajiya, ALLAH yaƙara yawan rai"
"Amin ya rabbi ALLAH yayi maku albarka"
Wata irin ajiyar zuciya mm ya sauke haɗe da ciro wayar a kunnen sa ya miƙa wa Jabir, "ka tsaya a wancan store ɗin zanyi sayayyar" ya faɗa tare da kauda kansa gefe,
"Lafiya Muhammadu" Baffa ya faɗa shima yana kallonsa, murmushi ya ƙaƙaro a fuskarsa haɗe da cewa,
"Lafiya klw Baffa"
"ALLAH yasa"
"Amin" ya amsa ba tare daya sake cewa komai ba,
Suna kawowa bakin store ɗin da mm ya nunawa Jabir sukayi parking, mm ya juyo yana kallon su Baffa haɗe da cewa,
"Baffa kuyi haƙuri, zan ɗan yi sayayyar abunda zamu wuce dasu don daga nan gidan su yarinyar zamu sauka saboda a wannan lokacin suka bamu damar zuwa"
"Too!, Shikenan babu damuwa" Baffa ya faɗa yana jinjina kalmar mm ta ƙarshe, sheɗan ne ya fara yimasa saƙe saƙen anya Muhammadu ya nemi aure gidan mutunci kuwa?, Ya yi saurin u'uziya tare da kauda zargint nasa a zuciya, basuyi mintuna biyar da fita ba don tare suka je da Jabir, sai gashi sun dawo yara na biye dasu, lemu na ne katam uku da ruwan gora katam biyu, sai biskit kwali uku shima da cingwam kwali biyu da minti kwali biyu shima Jabir ya buɗe boot aka saka aciki, har wayau tsohuwar kasuwa mm ya ce su tafi saboda yana son ya sayi goro da dabino tare da sake bawa su Baffa haƙuri suka ce ba komai,
Mintuna goma suka sake ɗaukar su zuwa tsohuwar kasuwar ya sayi goro sunƙi ɗaya, sai dabino daya sa aka auna masa tiya biyu shima, shi dai Jabir tun yana ƙumshe dariyar sa har ya bayyana ta a fili, murmushi mm dake kallonsa ya yi shima haɗe da cewa,
"Meya rage mu siya"
"Babu, lefe kawai ya rage muje mu ɗauko"
"Nop...nasu Baffa ya isa" ya faɗa tare da gimtse fuska yanar wajen, dariya Jabir ya dinga kwasa har yana rike ciki kafin ya karɓo dabinon da aka auna masu tare da sunƙin goron ya biyo bayansa,
Kasancewar but ɗin ya cika yasa Jabir buɗe bayan motar inda su Baffa suke zaune ya ajiye goron da dabinon sannan ya zagaya ta can gaba gefen driver ya zauna har lokacin yana ƙunshi dariyar dake cin sa, kallon sa mm yayi haɗe da girgiza kai sannan ya tayar da motar don yanzu shi ya karɓi tuƙin suka nufi gidan su Janan,
Bushewa da wata dariyar Jabir ya sake yi haɗe da kallon mm cikin kwantar da murya yanda su Baffa baza su iya jiyo sa ba har yana matsowa kusa dashi, ya ce
"Gaskiya ba kada kirki ɗan uwa, kace hauka kake son manna wa tsohon na ku"
"Na mu wato kai banda kai?"
"Wa?, ALLAH satari buƙui... ai ni na bar maku ku da ALLAH ya jarab ta, kuje can kuyita fama dashi ku da zaku iya" ya ƙare zancen tare da maida kansa gefen glasses ɗin tagar motar yana kallon yanda suke wuce abubuwa,
Ƴar dariya mm ya yi tare da cewa,
"ALLAH ka shirye ka, ko kana so ko baka so baffan kane don ba ataɓa canja wa tuwo suna"....
Hajiya kuwa suna gama magana da mm ta ƙwalawa mai aikin ta kira ta ce taje ta cewa Ado driver ya fiddo da mota za su tafi gidan Abba, kafin ta dawo har ta miƙe ta je ta ɗauko mayafin ta, tana fita Ado na fiddo motar ta faɗa suka fice gidan tana faɗin,
"Ubangiji ALLAH ka shiryi al'ummar Annabi, da tsufanka amma ƴaƴa baza su bari ka zauna ka huta ba, wannan wace irin rayuwa ce haka muke ciki da bata banbanta banbancin dake tsakanin ƴaƴan goye da kuma manyan ƴaƴa?"
Ado driver dake saurarar maganganun da Hajiya keyi a zuciya suka fito fili ba tare data sani ba ya ce,
"Ai Hajiya kuskuren bana rayuwa bace, na iyaye ne da basa tunanin tanƙwasa yara tun suna ƙanana, a wautar su ai yara ne sunyi ƙanƙanta da hukunta wa ko ladabtar wa ko kuma nuna masu tausayi a wajajen da bai kamata ba, sai a wayi gari yaran sun girma suna son nuna masu daidai haɗe da hukun tasu bisa kura-kuran da aka kasa gyarawa tun farko, su kuma yaran na nuna masu basu isa ba, wasu ma su saka su kuka tare da tarin nadama mai yawa"
Duk da kalaman Ado sun daki zuciyar Hajiya, kasa cewa komai tayi don tasan gaskiya ce ya faɗa, ita kuma gaskiya dama ɗaci ne da ita, sai dai kawai ta sauke ajiyar zuciya a hankali haɗe da cewa,
"ALLAH ya kyauta kuma ya sawaƙe mana duk abunda ya fi ƙarfin mu" Ado ya amsa da amin tare da tura kan motar cikin gidan na Baffa da tun kafin su ƙara so ya wangale kansa, suna yin parking Abba na fitowa tare da wasu abokanan sa su biyu, ɗaya daga cikin ma cousin brother ɗin Abba ne don dashi da Abba ɗan ya da ɗan ƙane ne, cikin girmama wa suka ƙara so wajen suna gaida Hajiya lokacin data fito, shi kuma Abba na can baya yana waya,
"A'ah, Alhaji Sadeeq yaushe a gari?"
Hajiya ta faɗa tana takawa zuwa cikin gidan, sai da ya yi dariya yana sinne kai ƙasa alamun girmamawa sannan ya ce,
"Jiya na dawo Hajiya, yanzu nake cewa idan muka dawo meeting zan je na gaida ki"
"ALLAH sarki, kai dai ko don ka ganni shi yasa kace hakan, sharabon ka da wajena tun shekarar data wuce, sai dai naji labarin cewa ka je Austaraliya agun mahaifin ka"
"Ayi haƙuri Hajiya, yanayin kasuwancin ne a haka"
"Kai dai kassa ni, yaran yanzu kun ɗauki zumunci ba abakin komai ba, bayan ALLAH da kansa ya ce a sada zumun ta domin laƙe take a igiyar al-arshi"
"In Sha ALLAH Hajiya za gyara"
"ALLAH yasa, ya mahaifin naku da iyalan naka duk suna lafiya?"
"Lafiya klw Hajiya"
"Madalla ALLAH yayi albarka" ya amsa da "Amin" dai dai lokacin Abba ya gama waya shima, cikin girmamawa ya ce,
"Hajiya sannu da zuwa"
"Yawwa Usman, ina zuwa haka kuma?"
"Meeting zamu je Hajiya tare dasu Alhaji Sadiq" ya faɗa yana nuna su,
"Ikon ALLAH, to baƙin naka da ka ce kana jira?"
"To Hajiya, na ce su zo kafin sallar azzahar amma har yanzu ban gansu ba, gashi har ƙarfe biyu ta wuce basu zo ba wanda hakan ya nuna mani ba da gaske suke yi ba"
"Assha, kasani ko wani abun ya hana su ƙarasowa da wuri, halama ƙarfe nawa zaku shiga meeting ɗin?"
"Ƙarfe huɗu"
"To alhamdulillah, ka ga sai kayi masu uzuri tunda ko uku bata yi ba, na tabbata suna nan ƙarasowa yanzu" ta ƙare zancen haɗe da juyowa tana kallon su Alhaji Sadiq dake tsaye jingina a jikin mota suna latsar wayoyin hannunsu tare da yi masu bayanin cewa su ɗan jira suma su koma ciki baƙi ne za su zo dake neman auren ƴar su Janan kafin lokacin shigar su meeting yayi,
Ba yanda suka iya dole suka koma daga ciki Abba naji kamar ya fasa ihu, part ɗin Hajiya zee ta fara shiga suka gaisa ta sanar da ita cewa za a yi baƙi da zasu zo neman auren Janan kuma tasan babu abunda Abba ya tana da daza a tarbe su dashi, don haka in akwai abunda zata iya haɗawa da sauri don kar aji kunya ta ɗan haɗa masu,
Dama Hajiya zee ma'abociya son snacks ce ba ta rabuwa dasu akoda yaushe, don haka tana jin haka ta tashi tayi warming ɗin samosa da cake da take dasu ajiye cikin fridge data yi jiya, sannan ta zuba su a cikin try tayi rafin ɗin su da foilpaper, dama ko da Hajiya tazo tana suyar kaji, don haka suma ta zube su gaba ɗaya cikin try tayi rafin ɗin su kamar yanda ta yiwa snacks ta kawo gaban Hajiya ta ajiye tana faɗin,
"Hajiya wuɗannan kaɗai ne akwai, sai kuma in abinci za a ɗora kafin su ƙara so"
"Me nene anan" ta nuna try ɗin kaji, Hajiya Zainab tayi murmushi haɗe da cewa,
"Wannan kaji ne aciki soyayyi, shi kuma wannan snacks ne, samosa da kuma cake"
"To agaisheki ALLAH yayi albarka, ai nasan baza a rasa lemuna acan ba ko?"
"Eh Hajiya"
"To ki gyara, duk da naga a gyaren ki kike tubarkallah, in yaso in suka ƙara so sai akawo masu, ni bara na shiga can"
"To Hajiya" ta faɗa tare da rakkota har bakin part ɗin, suna fitowa Jabir da mm na fito da kayan da suka zo dashi, wani irin faɗuwa gaban Hajiya zee ya yi lokacin da idanuwan ta suka sauka akan fuskar mm daya zagayo ta baya ya fiddo da goro da dabino, sak fuskar tsohon mijin ta da kuma ɗan ta Ahfan dake India wajen karatu, wanda jiya-jiya suka gama maganar sa ita da Hajiya har take cema ta sai nan da wata uku zai dawo, dafa Hajiya tayi tana nuna mm da yatsa haɗe da cewa,
"Hajiya wancan bawan ALLAH dawa ya yi maki kama"
"Wa kenan" Hajiya ta faɗa daidai lokacin da mm ya buɗe motar ya shiga haɗe da tayarwa ya bar gidan don ba dashi za a shiga ba, asalima ya yi waya da Janan zai same ta acan makaran ta, Jabir kawai ne da Baffa da amininsa zasu je nema masa auren, murmushi Hajiya tayi lokacin da idon ta suka sauka ga wanda take nufin don shi bai ma lura da Hajiyar ba sannan ta ce,
"Wai Muhammadu kike nufi?, Ai shine wanda Janan ke so kuma shi zata aura" dama su Baffa tuni sun wuce ciki don haka sai Hajiya zee bata kawo komai aranta ba sai dai ta ce,
"Wlh kama yake yi da mahaifin su Ahfan, sai ma naga kamar su ɗaya da Ahfan ɗin"
Juyowa Hajiya tayi don ta ƙara tabbatar da zancen ta amma inaa.., tuni mm ya fice daga gidan, shiru tayi kamar mai wani tunani kafin can tace,
"Tabbas sunyi kama da Ahfan ɗin, mahaifinsa dai ne kin san ba wani wayuwar juna mukayi dashi ba"
"Ai Hajiya Ahfan gaba ɗaya fuskar mahaifin sa ce dashi, ALLAH dai ya jiƙansa da rahama yasa aljannah ta zamo wajen hutu agaresa"
"Amin ya rabbi, kinga bari na koma ciki tunda sun ƙarfi" Hajiya ta faɗa tare da juyawa ta koma cikin part ɗin Hajiya zee, ita kuma tayi tsaye tana kallon gate ɗin da mm ya fice cike da tunani kala-kala a zuciyar ta jima a tsaye kafin ta juya ta koma ciki itama tare da shiga kitchen ta fara ƙoƙarin haɗa abincin da bazai ɗauki lokaci ba kafin su tafi, hakan ya sa ta kunna gida uku na gas kowane ta aza masa abinda zata haɗawa a jellop ɗin ta ta priderice with vegetables da tayi tunanin ɗorawa
Jabir kuwa ya shiga kwashe kayan yana shiga dasu daga ciki ba tare daya damu da sai gate man ɗin dake tsaron wajen dake kallonsa ya riƙa masa ba, a mayar ƙarshe da zai ɗauko akwatunan kayan da suka zo dashi ya ci karo da Nihal na fitowa daga cikin guiden kunnen ta laƙe da earpiece, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai tare da ƙoƙarin shiga daga ciki, ganin ɗayar jikkar daya riƙon na ƙoƙarin faɗuwa ya sa ya duƙa yana ƙoƙarin gyarata yanda zai iya riƙe ta har ya ƙara sa daga ciki, Nihal na zuwa ta bingije sa har sai daya faɗi ƙasa tunda ya riga ya duƙa ne bai sarar ba bingije sa ɗin, kuma ta wuce abunta ba tare dako kallon sa tayi ba, cikin zafin rai ya ɗago kai haɗe da miƙewa, yana taku ɗaya ya ya damƙo gashin kanta da tayi parking haɗe da janyo ta baya, tana juyowa ya ɗauke ta da wani zazzafan mari da sai da duk wanda ke falon ya ɗago kai yana kallon su, ba tare daya damu ba ya ce,
"Ke wace irin jaka ce, daƙiƙiya, dabba da bata san darajar mutane ba, ko an faɗa maki cewa mu bayin gidan ku ne da zaki bin gujeni kuma ki wuce abunki ki kasa bani haƙuri?"
Cike da zafin rai abokin Abba ya miƙe zai yi magana Abba dake zaune ya shige can cikin kujera tare da aza ƙafarsa ɗaya akan ɗaya ya riƙe baki da hannu yana kallon su ya dakatar dashi, komawa ya yi ya zauna yana kallon Jabir daya nuna ta da yatsa yana faɗin,
"Idan kika ci gaba da rayuwa haka saboda ganin wannan dauɗar duniya to tabbas rayuwar ki zata zama abun tausayi nan gaba, wawiyar yarinya kawai, fice daga gabana kafin nayi ball dake" ya ƙare zancen cike da yimata gargaɗi sannan ya koma ya ɗauko jikku nan ya shigo daga ciki ya ajiye sannan ya fice ransa a ɓace,
Nihal kuwa kallon Abba tayi taga ya kauda kai gefe, upstairs ɗin ta nufa tare da fashewa da kuka ta haye da sauri da sauri tana ji kamar ta nutse ƙasa,
Runtse idanuwa ya yi saboda jin zafin kukan da take yi tare da buɗe wa a hankali ya saukar da idanuwa akan Baffa dake faman zuba bayani, cikin isa da gadara ya dakatar dashi haɗe da cewa
"Ba waɗan nan maganganun nake son ji daga bakin ku ba, so kawai na keyi naji shin kun shirya aurar da ɗan ku ne?"
"Eh Alhaji, ai shine dalilin ɗaya kawo nan"
"Ya sanar daku cewa sati mai zuwa ne ɗaurin aure?"
"Eh ya sanar damu"
"Kuma kun aminta da hakan?"
"Eh mun amince tunda har suna son junan su"
"Shikenan, mu ma mun amince, tare da fatan baza mu saida akuya ta dawo tana cin danga ba"
"In sha ALLAH Alhaji, mungode ALLAH ya saka da alkhairi yabar zumunci..." ko rufe baki bai yi ba Abba ya miƙe yana bin kayan da suka zo dashi da wani irin mugun kallo sannan ya wuce ba tare daya sake cewa dasu uffan ba, da abokin Baffa ma yayi masa zancen yanka sadaki cewa ya yi su je duk abunda suke da hali su kawo don basu da arziƙin da zasu iya biyan sadakin ƴarsa, kawai suje su haɗa abunda ALLAH ya hore masu kafin ranar ɗaurin auren su kawo, shi dai Baffa imani ne ya cikasa haɗe da tsoron ALLAH ya bisu da kallo har suka fita,
Suna kaiwa bakin ƙofa Jabir na kawowa zai shiga, gefe ya raɓe har sai da suka wuce Abba na biye dasu a baya, kallon kallo suka shiga yi da Jabir sannan ya wuce yana jin wani tuƙuƙi da baƙin ciki aran sa, wanda ya tabbatar ba kowa ya jawo masa hakan ba sai Janan,
"Alhaji Usman wai wane ne wancan yaron?" Alhaji Sadeeq ya faɗa yana nuna Jabir daya shige cikin gidan,
"Kaman ta da zancen za muyi magana idan mun dawo"
"A gaskiya bai kamata ace kamar ka irin wancan yaron na rena maka da wayo ba, shin ba yaron gidan ne ba?"
"Ku muje" kawai Abba ya faɗa don baya son maganar, a halin yanzu sam baya da lokacin Jabir har sai ya gama da matsalar dake gabansa, abun da ma ya basa mamaki shine, meye haɗin sa da iyayen yaron nan daya gansa tare dasu, zai iya yuyuwa yaron abokin sa ne ko kuma cikin dangin maman sa, wata zuciyar ta bashi amsa a taƙaice, no bazai yuyu ace dangin mahaifiyar sa bane shi, idan kuma har haka ne kenan shima tubabbe zai aurar wa da ƴarsa, impossible, ya faɗa da ƙarfi ba tare da yasan maganar da yake yi a zuciyar sa ta fito fili,
Suna ƙoƙarin shiga motocin su Hajiya ta fito haɗe da cewa,
"A'ah, ya haka Alhaji Sadeeq?, Ina baƙin naku ne har sun wuce?"
"A'a Hajiya suna ciki mun gama magana ne, kinsan jiran mu akeyi"
Girgiza kai kawai tayi haɗe da cewa
"To shikenan ALLAH ya kiyaye, shi dai girma sayen sa akeyi idan kuma aka gagara siya, tofa tabbas zai faɗi" tana gama faɗar haka ta wuce part ɗin tana jin ɓacin rai a ranta,
Ko data shiga ta samu har sun miƙe suna ƙoƙarin fitowa su da Jabir, cikin sakin fuska suka shiga gaggaisawa tare da yimasu sannu da zuwa sannan ta fara basu haƙuri haɗe da cewa,
"Kuyi haƙuri fa, suna da meeting ne shi yasa kuka ga suna gaggawa haka, ya ce na baku haƙuri kuma kusan tsaya kuci abinci kafin kuwuce"
Mere baki Jabir ya yi yana kallonta kafin yayi ƙasa ƙasa da murya ya ce,
"Ke dai ƴar tsohuwa faɗi gaskiya, kice kawai kina kare ɗan ki ne don kar aga rashin kyautawar sa" ɗan duka ta kai masa a gefen hannu haɗe da cewa,
"Ja'iri, jeki ka kaisu wancan falon suci abinci kafin su wuce"
"Wane falon?, Ni ina zan san yanda wannan gidan naku yake, kece dai ƴar gida jeki ki kaisu, wannan gida haka sai kace gidan family gaba ɗaya, atunanina duka family ɗin mu gidan nan zai ɗauke su, amma ɗan ki ya tara irin wannan dukiya kuma baya iya taimako ƴan uwa da ita, sai yanda yake so yake yi da ita da shi da ƴaƴan sa, ba komai ALLAH ya bamu namu muma"
Ya ƙare zancen tare da wucewa falon data nuna masa da hannu yana cewa su Baffa dake tsaye acan gaba su wucik ke"
Hajiya kuwa jikin ta ne yayi sanyi da kalaman da Jabir ya faɗa tare dajin tausayin sa aranta, ƴan ƙwallan da suka zubo mata ta goge sannan ta ƙwalawa Nihal kira, ba a fi mintuna uku ba ta sauko tana tuƙuburi idanuwan ta sun yi jajir saboda kukan da tayi, kallon ta Hajiya tayi haɗe da cewa,
"Ke lafiya?"
Har zata buɗe baki tayi magana sai ga Jabir ya iso wajen, harar ta maka masa haɗe da turo baki ta koma ta bayan Hajiya,
"Kina yin magana zan sake zabga maki wani marin, daƙiƙiya kawai" ya faɗa shima yana maka mata harara,
"Haba Jabir, meye amfanin wannan maganar haka, ƴar uwar ka face amma kake kiran ta da daƙiƙiya, kalmar batayi daɗi ba"
"To Hajiya kiyi haƙuri na dena, amma wannan yarinyar da kike gani kan kifi ne da ita, kuma matuƙar za muci gaba da haɗuwa da ita sai na yi maganin ta" ya ƙare zancen yana nuna Nihal da yatsa,
"Ke jeki part ɗin auntyn ki ki karɓo masu abinci, dama nasan wannan rashin kunyar taki za a yi maganin ta duk ranar da kuka haɗu dashi, don haka gaki gashi" ta ƙare zancen tare da wucewa ta zauna akan kujera, ita kuma Nihal ta wuce part ɗin Aunty zee tana sake turo baki cike da haushin su duka.
Sai da suka ci suka ƙoshi sannan Jabir ya nunawa Hajiya kayan da suka shigo dasu, addu'a ta dinga yi tana sanyawa kayan albarka haɗe da yi masu godiya sannan suka wuce,
Suna fita Nihal ta sauko tana kallon Hajiya da Aunty zee dake bubbuɗa kayan suna kallo, ɗan zaro idanuwa tayi haɗe da ƙarasowa wajen tana girgiza kai da nuna kayan da hannu kafin tace,
"Hajiya wai meye wannan?"
"Kayan auren ƴar uwar kine mana, zo ki buɗe ki gani kema"
"What? Ni na buɗa waɗan nan ƙazaman kayan, dubi wasu atamfuna Hajiya, birkiɗa haka ake ce masu ko meye ma, i don know" ta faɗa tare da kwashewa da dariya, gimtse fuska Hajiya tayi haɗe da cewa "bar nan, ko yanzu in saɓa maki, Ina ruwan ki ko birkiɗa ubanki ne ba birkiɗa haka ba, marar kunya kawai ai har gida zan sa Jabir ya riƙa zuwa yana yimani maganin ki"
"Wai Hajiya kin damu mutane Jabir, Jabir..nifa bana son sa gaskiya, sam be mun ba"
"Ɗan yayan mahaifin ki ne Jamal, shi ɗin baya son reni in zaki shiga taitayin ki ki shiga, idan kuma ba haka ba zaki yabawa aya za ƙi don shima da alama halin ki baiyi mashi ba"
"Cab! Yayan Abba, ni ban san shi ba"
"In ke baki san shi ba ai shi uban naki ya san shi, sai ki tambayesa ko waye shi idan ya dawo"
Mere baki tayi tare da hayewa sama abunta tana ayyana irin shaƙiyancin da zata yiwa Janan idan ta dawo....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/21, 2:51 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 56_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
**********
______________________________
Sosai Janan tayi enjoying moment ɗin da suka yi spending yau tare da mm, don har wajen shaƙata wa na Taula areenah ya ɗauke ta suka tafi, hotuna masu kyau suka riƙa ɗauka a wajajen dake da matuƙar ƙayatar wa a wajen, so take yi ta jefa masa tarin tambayoyin dake cike fal a zuciyar ta amma ta kasa, gaba ɗaya yau ya sauya mata daga mm ɗin ta sani zuwa wani mm ɗin na daban, kama daga yanda yake ɗabiun sa har zuwa suturar dake jikinsa da motar daya hawo duka sun banbanta da na mm ɗin data sani, wani irin kwarjini ta ji yana sake yi mata yayin da gaban ta ke matuƙar yimata dukan uku uku, bin sa kawai takeyi da kallo sake da baki tana mamakin wannan sauyi daya zo mata dashi farat ɗaya ba tare da kuma ya yi mata bayanin komai ba, shi kuwa sai wasar sa kawai yake yi da wani yaro dake hawa can saman wani abu mai kamar baloon yana sulɓaɓo wa, shi kuma yana sake haurasa saman yana dariya, juyowar da zai yi ya ga Janan ta ƙura masa idanuwa tana kallo har dasu karkace kai gefe, murmushi ya yi haɗe da ɗaukar yaron ya sake azo sa a saman abun sannan ya dawo inda take zaune yasa hannunsa agefen fuskarta ya tallabo kan nata yana faɗin,
"Me kike kallo haka yallaɓiyata kike nema ki karya mani kan naki in shiga uku sau uku"
"Ba komai, mamaki kawai nake yi anya wannan mm ɗina ne ko kuwa hur hure akayi mani, I'm confused gaskiya"
"Common...zo muje zan yi maki bayanin komai anjima, kawai ki bari mu ɗan mori wannan lokacin kin san dama sau ɗaya take zo wa bawa a rayuwa, so dis is an opportunity that i got today, let enjoy it kin ji" ya ƙare zancen tare da riƙo hannunta ta miƙe daga zaune da take tana murmushi haɗe da kallon hannunsa dake riƙe da nata sannan ta ɗago kai tana kallon sa shima.
Saurin cika mata hannu ya yi haɗe da sosa kansa yana kallonta ta ƙasa idanuwa ya ce,
"Am so sorry Madam na manta har yanzu baki ida zama mallaki na ba" Janan na dariya ta wuce gaba tana faɗin "to me ya rage kuma? Kai dai ka ƙoƙar ta riƙe kanka kafin wannan lokacin, in ba haka ba zaka ɓata rawar ka da tsalle, don tsab zan buga kai nace na fasa yi dakai"
"Tab kin ma isa?, Ai da naje har cikin gidan naku na sace ki"
"Zaka iya?"
"Sosai kuwa, ko kina mamaki ne?"
"Sosai kuwa, don yanzu haka ma cike nake da mamakin abubuwa da yawa akanka"
"To ki dena, don aski ya riga da ya zo gaban goshi, ƙiris ya rage na mallake ki, wanda a wannan ranar zan kore duk wani shakku da kokwanto dake zuciyar ki akaina, kedai kawai kici gaba da haƙuri kin ji ko"
"Shikenan, amma faɗa mun a ina ka samo aron mota da kayan dake jikin ka?"
"Ga amsa nan acikin tambayar ki, aro nayi don na burge budurwa ta nima ta ƙara sona"
Tsuke fuska tayi haɗe da juyowa tana kallonsa jin abunda ya faɗa tare da shagwaɓe masa tamkar za tayi kuka ta ce,
"Au! Dama a tunanin ka zan iya ƙara son ka kaɗai ne idan kana da wani abun? Me yasa zaka fahimceni a haka?" Ta ƙare zancen tare da sauko da ƙwalla ɗaya daga cikin idanuwan ta lokaci ɗaya tana cuno leɓen ta na ƙasa tamkar zata fashewa da kuka, yanda tayi shima ya yi ɗin haɗe da cewa,
"Sorry my cry cry baby, ni fa ba haka nake nufi ba..." Bai ƙarsa rufe baki ba ta shiga buga ƙafafuwa irin na shagwaɓaɓin yaran nan, yana ganin haka ya fashe da dariya tare da rugawa itama ta bi bayan sa tana so ta ka masa ganin yanda yake yimata dariya, zagaye wajen suka shiga yi har sai da taga ta kasa ka mosa sannan ta tsaya waje ɗaya tana haki haɗe da cewa,
"You're too
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 40