Share this page
idan ka samu" Ganin ya riƙe kuɗin baice komai ba yasa ta karɓar tare da buɗe aljihunsa na gaban riga ta saka masa haɗe da cewa, "Thanks Janan, i love You" tana kashe masa ido ɗaya, murmushi ya saki tare da cewa, "Haka kike so na faɗa?" "Eh, amma kacire thanks ɗin tunda na riga da nayi maka" "To shikenan, i love You so much my nurul alb, I feel like the most luckiest guy in the whole world to have a beautiful, lovely and sweet girl like you. I hope my luck never runs out and i can make you mine forever, I love you very much" "Wow.!" Ta faɗa tare da aza hannayenta akan kumatunta tana zaro idanuwa haɗe da buɗe baki cike da mamaki, don har ga ALLAH bata taɓa tsammanin mm yayi nisa da boko haka da har zai iya irin wannan turancin ba, shi kansa bai san lokacin da ya yi ba don haka sai yayi saurin cewa, "Kinyi mamaki ko" "Sosai kuwa, dama kayi karatu da yawa haka?, Pls say it again don ALLAH" ta ƙare zancen cike da farinciki tana yarfi da hannuwa, dariya yayi yana sake maimai ta mata kalaman ta langaɓe kai tana kallonsa, "Wayyo ALLAH, hubbin ruh ka shamma ce ni, wai dama kayi karatu?" "Eh, ko don kinga bana turanci kike ɗauka ko banyi ba?" "Am no lie to you, haka nake expecting tun tuni, to gaskiya aiki ya kamata mu fara nema indai haka ne" "A'a, barni a ɓangaren sana'ar nafi gane mata" "Noo.. bazai yuyu ba dole ma mu nemi aiki" Ganin ta nace yasa yayi ƙoƙarin shashantar da maganar ta hanyar cewa, "Kinga bari naje gida Jabir na jirana akwai inda zamu je" ɓata rai tayi haɗe da cewa "Haba dai! Tun yanzu?" "Eh, duba agogon hannunki ki gani, past 3 fa" "Ok to muje sai na sauke ka ko?" "A'a saidai in rakaki kike so nayi gida?" "Eh to muje ina buƙatar hakan" ta ƙare zancen tare da miƙewa, "kawo na riƙa maki jikkar" "Laaa..rufan asiri kar a fara kiran ka mijin hajia, bara dai nake na ɗauko motar" Amira dake can gefe zaune na ganin Janan ta ɗauko mota mm zai shiga da sauri ta taso ta nufo wajen tana ji tamkar ta shaƙo wuyan Janan, fuskarta a sake ta ƙara so wajen tare da kallon mm tana murmushi ta ce, "Sannun ku, Janan" ta juya tana kallonta tare da kiran sunanta, "Ah Amira, Ashe kin shigo, ya ko, ɗazu ban ganki a class ba?" "Ai kuwa dai baki duba da kyau ba, ya gida?" "Lafiya klw" "An don ALLAH ko zaki sauke ni a round" "Ehmm.amma" "Ma zai hana" mm ya faɗa ganin Janan na ƙoƙarin cewa a'a, Badon Janan ta so ba ta ce, "Ok, to shikenan shiga muje" Ba kunya Amira ta je ta buɗe gefen gidan gaba tana murmushi ta shige, Janan ta kalleta haɗe da cewa, "Ko zaki koma baya, tare da mm zamu je" fuskarta a ɗaure, lokacin shi kuma yana ƙoƙarin buɗe ƙofar baya ya shiga ya ce, "No..ki bar ta ni Zan zauna a baya ɗin" Wani irin haushi da takaici ya kama Janan ta tada motar tana ji tamkar ta kaiwa Amira naushi, A can gida kuwa tuni ya cika da manya manyan mutane da Abba ya gayyata jiya sai maƙulashe da ciyeciye akeyi kafin isowar Janan da Abba yasa guard ɗin sa su je su ɗauko masa ita a school ganin har marece na neman yi bata dawo ba, gashi tuni wanda aka haɗa taron don shi da ita wato Captain ASGAR HUSSAIN SALIM, da mahaifinsa ambassador Hussain Salim da sukayo tattaki tun daga ƙasar chadi suka amsa kiran mahaifin nata, sun iso ita kaɗai ake jira, Wani irin tsaki Abba ya ja tare da kirawo Madam florence dake faman kai da kawo da jimamin abinda ke shirin faruwa agidan ya ce, "Florence" "Yes sir" ta faɗa tare da rissinawa a gabansa, "Ko kin faɗawa Janan wani abune dangane da wannan taron shiyasa taƙi dawowa" "No sir, I only told her to came back early be cause we're having strangers in the house" "Damn it, who ask you to do so?, Idan guduwa yarinya ta tayi ki tabbata sai kin kuka da kanki, wayasa ki faɗa mata hakan?" ya faɗa cikin ɓaci rai yana dukan table ɗin dake gabansa..... #Comment #Vote #Share *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 25_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1240050252?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=gutw10QauAYUto7pKMSLF5z%2FYYSeOdoeW4kyGSZKSI3vrUOKdepJGCrJSE0dgEWXdBVy%2F9wRCifEWPGXSxgAwlIgc3jzzI4f%2BewYnWVncyI1yBVaY0EU5zVnUbtaj8M%2F_ ______________________________ Ta gefen idanuwa Janan ta kalli Amira cike da jin haushi kafin ta saita mirror ɗin motar saiti da fuskar mm dake sun kuye da kai yana latsar wayarsa tace, "Yallaɓai, kabari in saukeka gida, daga can kaga sai na gaida momy da Razina" A ɗan Razane ya ɗago kai jin abunda ta faɗa idanuwan su suka yi karaf da juna ta cikin madubin ta kashe masa ido ɗaya haɗe dayin murmushi, "Yes, ko akwai wani abune?" "Ko ɗaya ranki shi daɗe, gidanmu ai gidanku ne, saboda haka babu buƙatar sai kin tambaya, yanda duk kike so haka za a yi" "Awwnn..that's my golden man, in sha ALLAH zan je amma ba yau ba saina shirya, saboda yau muna da baƙi agidan kuma nasan za a jira dawowata" "Dama nasan ai bada gaske kike yi ba" ya faɗa tare da sauke ajiyar zuciya don har ga ALLAH bai shiryawa zuwanta gidan ba, "Haka dai kake tunani, amma zan baka mamaki wata rana" "Ina jiran haka, amma kafin nan ya kamata ki aji yeni a bakin gate da mun fita saboda na tuna akwai inda nake son zuwa, ke kuma kinga kince kunada baƙi a gida kar ya zamana na ɓata maki lokaci" "Babu ɓata lokaci acikin kasantuwa tare da masoyi, uzurinka kaɗai zaisa na ajiye ka ɗin kamar yanda ka buƙata, saboda ban sani ba ko wani babban aiki ne zaka je nemo mana ko kuma wani alkhairin ne ke kiranka, badon haka ba bazan sauke ka a ko ina ba sai inda ya kamata" "Nagode nurul alb, shiyasa kike daɗa shiga zuciya ta, Amira ki tayani godiya ga ƙawarki, kirkinta ba kaɗan bane, haka ma karamci da mutuntakar ta sun shallake tunanin mai rai, ina matuƙar jinjina wa halaccin ta da yanda take gudanar da rayuwarta a tare dani ba tare da ganin fifikon kuɗi ko wani abu a tsakanin mu ba, a gaskiya ita ɗin ta daban ce, a mata kaf banda kamar ta kuma na tabbata bazan taɓa samun kamarta ba, kai ko kusa da irinta bazan taɓa samu ba arayuwa" ya ƙare zancen yana kashe mata idanuwa ta madubi, murmushi tayi mai cike da jin daɗi haɗe da kallon gefen da Amira take zaune tana ji tamkar ta haɗiye zuciya ko ta kurma ihu tsabar baƙin ciki, sai da tayi 'yar gyaran murya ganin gaba ɗaya Amiran ta shiga wata duniyar sannan ta ce, "Hubbin ruh kenan, ai indai Amira ce ko ƙinka bata yi, da alama yau 'yan surutun nata basa kanta" Sai alokacin Amira ta juyo tana kallon ta tare da sakin murmushin da ya zame mata tamkar an sakata dole ne haɗe da cewa, "Janan kenan, ai yin shirin shiyafi zama alkhairi a wurina saboda bansan me zancewa ba, tsakanin ki ne dashi ko ba haka ba mm" "Eh..amma kuma ai ya kamata ki tofa bakin ki tunda na sakoki aciki" "Acan dai, wacce kafaɗa don ta ai na tabbata taji kuma ta yaba, don haka ba sai nace komai ba" "To shikenan, godiyar fa? Itama bazaki tayani yi ba?" Karaf Janan da haushin firar da yakeyi da amiran ya fara kamata ta ce, "Yallaɓai kadena tunanin akwai godiyar da zatayi tasiri azuciyar masoya sama data junan su, tuni zuciya ta amshi saƙon ɗaya fito daga ƙasa zuciyar ka, haka kuma kunnuwa suka saurari mafi soyuwar kalamai masu matuƙar daɗi daga bakin ka, ni Janan matar Muhriz ina godiya da tarin yabonka agareni, ALLAH ya nuna mana ranar da mafarkin zai zamo gaskiya, a ranar zan baka TUKUICIN SO na wannan kyakkyawan yabon da kayi agareni" "Ajiye ni anan Janan" Amira ta faɗa daidai lokacin da suka kawo bakin gate ɗin makarantar tana ƙoƙarin danne ɓacin ran daya gama cika mata zuciya, "Kiyi haƙuri har miƙa rasa fita daga wajen tunda shima hubbin ruh anan zai sauka, koda yake ke bazan ajiye ki nan ba tunda round kika ce zaki sauka" ta ƙare zancen tare da jan wani irin wawan burki a daidai lokacin da suka fito ɗin sanadiyar motocin da taga sun tari gabanta har guda uku sun sakata a tsakiya, kafin tayi yunƙurin yin wani abu har guard ɗin na mahaifinta sun fito su wajen tara sun zagaye motar ta suna mazurai, cike da takaici ta sauke glass ɗin tagar gaban ta na faɗuwa saboda gudun abunda zai iya faruwa ga masoyin ta, cikin dakewar murya ta kalli ɗaya daga cikinsu ta ce, "Jazz, meye haka?" "Oga ne ya bamu umurnin muzo muje dake gida, saboda haka ki fito muje" "What! Akan me? Ni ƙaramar yarinya ce da zaku tasani agaba?" Ta faɗa cikin ɓaci rai tana kallonsa, bai tsaya wata wata ba ya buɗe marfin motar kafin ta sake cewa wani abun yana faɗin, "Bisimillah Madam muje ko" ganin taƙi fitowa yasa yayiwa sauran 'yan uwan nasa signal da idanuwa, nan take suka buɗe gefen da Amira take suka jawota haɗe dayin wurgi da ita gefe goshin ta ya bugi symbol ɗin makarantar dake kafe a kan ɗan express ɗin da za'a bi daga bakin gate ɗin a shiga makarantar su kuma suka shige, dai dai lokacin mm ya fito shima ganin guard ɗin na ƙoƙarin sa hannu ya janyo Janan da taƙi fitowa da ƙarfi, "Pls kabita a hankali mana zata fita" "Babu inda zanje fa mm, suke muje nabisu a baya, be side duk wannan abun ma na meye?" "Kinga Janan, koma meye ki bisu ɗin kinji?" "Ni bazan bisu ba tunda ba laifi nayi ba mm, kawai su tafi muje zan bisu a motata" Ganin da gaske takeyi har tana ƙoƙarin fidda masa da ƙwalla yasa mm dawowa gaban guard ɗin ya shiga tsakanin su, "Mai gida, don ALLAH kuyi haƙuri kuje zata biyo bayan ku yanzu..." Bai rufe baki ba guard ɗin yasa hannu ya turesa tare da finciko Janan da ƙarfi don mahaifinta ya basu umurnin kota ƙarfi ne su zo masa da ita, cikin zafin kishi da hasala mm yayo kan guard ɗin ya ɗauke sa mari tare da fincike Janan daya riƙo da hannunsa yana shirin turata cikin motar su, cike da ɓacin rai mm keyi mata magana dake tabbatar da tsantsar kishinta da yakeyi, cikin tsawa ya ce da ita, "Kije ki shiga motar mana, ko kin fiso wu ƴannan gardayen 'yan iskan su riƙa taɓa maki jiki ne?" "Mm ni bazan.." "Ki bisu nace" ya faɗa da ƙarfi idanuwanta sunyi jajir tamkar an watsa masa borkono saboda tsananin kishi, kansa ɗaya guard ɗin yayo zai dakesa ya riƙe hannun haɗe da cewa, "Ni ba karen farautar ku bane balle ku dakeni, a wancan ranar na bari kun dake ni ne saboda in tabbatar da soyayyar da bakeyiwa Janan agaban mahaifinta, a yau duk wanda yayi gigin taɓani na rantse saidai uwarshi ta haifi wani, don ba abinda zai hana na turasa kan titin can mota ta taka sa" ya ƙare maganar yana nuna masu babban titin dake gaban makarantar da manyan motoci ke zirga zirga akai, wani irin kwarjini duk suka ga yayi masu da yasa nan take suka koma gefe sukayi tsaitsaye suna kallon sa, juyowa yayi ga Janan data turo leɓenta na ƙasa tana shirin sa masa kuka shagwaɓa ya ce, "Pls Janan jeki ku tafi, kada ki bari zuciyata ta buga sanadiyar raɗaɗin da nake ji azuciya ta bisa riƙa maki hannu da wancan gardin yayi, pls kitaimaka mun kinji don zan iya mutuwa idan ya sake yunƙurin ko da taɓa maki ɗan yatsa ne, "Kana nufin kana kishi na kenan?" "Fiye da tunanin ki, don ALLAH ki taimakamun yallaɓiyata" Dariya tayi sannan ta juya zata shiga motar tana yi tana juyowa tana ɗaga kallonsa tamkar wacce aka cewa sun rabu kenan har tana yin tuntuɓe da wani dutsi, saurin nufo wajen yayi haɗe da miƙo hannu kamar zai riƙota tayi dariya sannan ta shige motar tana ɗago masa hannu, ai kuwa kamar jira sukeyi da sauri suka shisshiga cikin motocin wasu kuma suka shiga tata suka ja suka bar wajen, 'yar ajiyar zuciya mm ya sauke tare da juyowa jin ana kwasar dariya ta bayansa, kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai ya nufi bakin titi da zimmar samun abun hawa, da gudu Amira ta cimmasa haɗe da duƙewa tamkar mai ruku'i ta ce, "Sannu mm" har lokacin tana dariya, "Kece da sannu Amira, in jin dai lafiya" ya bata amsa ataƙaice ganin irin dariyar da takeyi, miƙewa tayi tana kallon fuskarsa cike da shauƙin so kafin tace, "Wlh mm Janan ba sa'ar ka bace, kawai kafita rayuwar ta in ba so kake yi mahaifinta yasa ayi maka shegen duka a makarantar nan ba" "Sai kuma me?" "Ehmm..shi dai ɗin ne, don a gaskiya sam mahaifin Janan ba mutumen kirki bane, bai damu da rayuwar kowa ba sai tasa data ƴaƴansa, sannan ba yada wasu maƙiya aduniya sama ga talaka, kaga kuwa ba ƙaramar yaudara bace tasa Janan shiga rayuwar ka, don na tabbata halin ƴar dole zai zamo irin na mahaifinta" "Shikenan?" Ya jefa mata tambayar yana kallon tsaurin idanuwa irin nata da har ta iya kallonsa ta faɗa masa haka, ɗan ɓata fuska tayi ganin kamar ma bai san da zancen da take yi masa ba haɗe da cewa, "Kamar ya shikenan mm?, magana fa nakeyi maka akan abunda zai taimaki rayuwarka amma sai nuna mun kakeyi kamar ba komai bane, wlh tlh ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba Janan ba son ƙwarai takeyi maka ba, kawai akwai abunda take so tattare da kai" "Kamar me Amira? kuɗi, kyau, tsari da kuma ilimi ko me? Duka fa Janan tafini waɗannan abubuwa to me zata so agareni da nake dashi wanda bata dashi?" "Kacire zancen kyau aciki mm, ai kai ƙarshene, kyawon da kake dashi yafi ƙarfin haɗawa da kowace irin halitta aduniya, wanda ko tantama bana yi shi Janan ke bibiya akanka wanda ni daka fahimceni tun farko zaka gano sam ba shi bane agaba na, son ka da ƙaunarka kawai nake yi a cikin dukkanin ruhi da kuma gangar jikina, kuma wlh zan iya sadaukar da rayuwata duka a gareka amma kai ka kasa gane haka, sai hange-hange kakeyi a inda nake da tabbacin bazaka taɓa daraja awajen ba, tunda gashi a gabanta yanzu aka nemi wulaƙan ta ka, badon kai ɗin ka kai namiji ba da tuni za kasha duka a wajen su tana ji tana gani" "ALLAH ko? Ina ga idan ma hakan ta faru dani to ba komai bane, giyar so da haukan ƙaunar ta ne suka ja mun har suka sa na kasa gane cewa bata dace dani ba, kin kuwa ga babu yanda zanyi dole na haƙura tunda bazan iya kankare su a zuciya ta ba, kuma a gaskiya yanda kike mun bayanin ko wacece Janan da mahaifinta to ba haka suke ba, tare kawai kike da ita amma har yanzu baki san ta daidai ba, Sannan wannan taren taku a gaskiya ita ake kira da mugun tare tunda har bazaki iya faɗar alkhairi akan ta ba, yanzu ke baki ji kunyar buɗar baki ba kice kina sona?" "Kunya?, Kunya fa kace mm, dama akwai zancen kunya a harkar so?, To idan ma akwai ni na tattara ta duka na watsa a kwandon shara, ka buɗe idanuwan ka da kyau ka gani, nice nan sa'ar ka kuma wacce ta dace da rayuwarka ba Janan ba, kwanciyar hankali da duk wata soyayya da kake mafarkin samu a rayuwa zaka samesu a wajena, banda ma abunka meye na tsalle-tsalle da hangen nesa bacin ga Alkhairin ka a kusa dakai, bari kaji mm wlh Janan shigar sauri kawai tayi mani a wajen ka amma na tabbata na fita son ka kuma na fita ƙaunar ka" ta ƙare zancen tana zagayar sa tare da kashe masa idanuwa, wani irin dogon iska ya ja a hanci ya furzar dashi ta baki yana girgiza kai kafin yace, "ALLAH ya baki lafiya Amira domin na fahimci buguwar da kika yi a jikin symbol ɗin can ya haifar maki da taɓuwar hankali, banda abunki shi so ai ba cancanta yake dubi ba, ba kuma duba dacewa yakeyi ba balle kice Janan bata dace da rayuwata ba, kwata-kwata ma idan na fahimceki duka wannan zancen da kike yi a mafarki ne don haka kiyi gaggawar farkawa kafin yakai ki ga jin munanan kalaman da zasu zo maki a matsayin sakamakon amsar maganganun ki" yana gama faɗar hakan ya tare mai acaɓa ya haye abinsa, "Karka damu mm, ai yanzu ne wasan tafara tsakanin ni dakai, zanga waye ke mafarki a tsakanin mu kuma kasa a ranka Amira ita tafi dacewa dakai, sosai nake masifar son ka ko ka yarda koma karka yarda" ta ƙare zancen cikin ɗaga murya tana dariya, wanda kusan duk ɗalibban dake tsaye wajen suna jiran abun hawa saida suka juyo suna kallon ta cike da mamaki, shima dai kusan mamakin ne ya rufesa duk da ya jima da sanin take taken ta basarwa kawai yakeyi, amma ko kaɗan bai taɓa tsammanin zata iya furta masa kalmar so ba bayan tasan abinda ke tsakaninsa da ƙwarta, "hmmm ALLAH dai ya kyauta, wasu matan ba amana" Ya faɗa a zahiri yana jinjina lamarin, shi dai mai acaɓar bai ce dashi komai ba yaci gaba da zura gudunsa don baisan inda zancen nasa ya nufa ba. Amira kuwa sosai taji daɗin tsayuwarta da mm yau duk da babu wasu kalaman farinciki data samu a wajensa, amma kaso ashirin bisa ɗari na nauyin da zuciyarta keyi mata akansa ya sauka, hakan yasa ta ji duniyar ta ta fara haska mata haɗe da jin cewa za tayi nasarar ƙwato mm daga hannun Janan tunda har ya iya saurarar ta. ***. ***. ***. Janan kuwa cike da ɓacin rai ta iso gida, inda ta bisu duka da mugun kallo lokacin da suka iso aka buɗe mata marfin motar, ba tare data damu da tarin manyan motocin data gani a harabar gidan ba kai tsaye ta wuce cikin gidan tana ƙwalawa Adda Nihal kira, tana jin muryarta ta fito daga cikin ɗaki jiki ba ƙwari tana saukowa daga upstair ɗin, don tun da taji me Abban nasu ke shirin aikatawa jikinta ya mutu, gashi duk hanyar da zata bi ta samu damar yin magana dashi yaƙi bata, hakan yasa duk sai jikinta yayi sanyi ta kuma rasa me zata iya aikatawa adaidai wannan lokacin, Baƙin fuskokin data tadda acikin katafaren falon nasu ne ya hana taci gaba da maganar da yazo da ita abaki akan don me Abba zai sa aje a ɗaukota sai kace wacce tayi wani laifin take ƙoƙarin guduwa, cike da girmamawa ta dinga ratsowa ta cikinsu tana gaishesu har ta iso bakin upstairs ɗin adaidai lokacin da Nihal ta sauko itama, 'yar dariya tayi tare da riƙo hannunta tayi ƙasa ƙasa da muryarta yanda baza aji ba ta ce, "Wow! Adda Nihal wannan taron fa?, Ko dai Abba ya samo maki the charming ɗin naki ne?" Kafin Nihal ta bata amsa Abba ya ƙara so wajen fuskar sa a sake tamkar bashi ba ya riƙon hannun Janan, "Abba...." "Shiiii..." Ya faɗa tare da ɗora hannunsa akan baki alamun tayi shiru, ba yanda ta iya dole kawai ta bisa da kallo har ya iso tsakiyar mutanen dake wajen tana biye dashi riƙe da hannun ta, "Wannan itace 'yata Janan, yarinyar dana haɗa wannan gagarumin taro domin ta da kuma gabatar maku da mijin da zata aura wato ɗana kuma aminina ambassador Hussain salim da kuka sani da Captain ASGAR, jajir taccen jarumi kuma zaƙaƙuri da aduk faɗin ƙasar chadi babu na biyun sa, wanda kusan shekara uku kenan ya shafe yana neman hannun amincewar mahaifinsa da kuma ni akan soyayyar 'yar uwar tasa kuma ƙanwarsa Janan, duba da nagartarsa da kuma cancantarsa yasa adaidai wannan gaɓar naga dacewar miƙa masa ita domin ta zamo mallaki kuma matar sa ina ALLAH ya yarda, ina fatar zaku zamo shedar hakan da kuma tayasu murna" yakai zancen tare da jawo Janan ajikin sa yana dariya, "What? Abba..." Ya katse ta tahanyar ɗagawa mutanen hannu da sai faman tafi sukeyi yana faɗin, "Nagode Nagode" "Abba..." Ta sake faɗa akaro na biyu cike da mamaki idanuwanta na kawo hawaye, amma yayi tamkar bai jita ba sai ma jawo hannun ta da yayi zuwa inda ambassador Hussain salim ke zaune shi da ɗansa da tunda ta shigo ya kafeta da idanuwa, kyakkyawa ne sosai don zan iya cewa abu ƙalilan ne ya banban tashi da zama balarabe, rashin gashin kai da kuma fuskarsa dake kwalkwal babu alamun gashi ko ɗaya gareta, sai kuma hancinsa da bai ida tsawo irin nasu ba, amma fari ne sol dashi, haka kuma yana da idanuwa masu girma da yawan gashin girar ido, yana da tsayi sosai da kuma kabarin jiki, don idan ka kalle shi zaka iya cewa yakai shekaru arba'in da wani abu, ganin sun miƙe da sauri haɗe da nufo wajensu yasa Janan furta kalmar, "innalillahi wa inna ilaihirrajiun" tana kauda kai gefe saboda irin kallon data hango asgar ɗin yana yimata, "Janan, wannan shine mahaifin asgar wato aminina, nasan kin sanshi, saboda haka ki gaishe shi" batayi musu ba taɗan rissina cikin girmamawa tana gaishesa yayi saurin riƙo kafaɗunta tare da jawota ajiki, "No my dota taso abunki kinji, ya karatu?" Sinne kai kawai tayi ba tare data iya amsawa ba sai wani irin jiri da take ji yana ƙoƙarin ɗibarta, "Janan, this is your feature husband dana zaɓar maki wanda shine da kansa ya zaɓeki, sunan sa asgar ya jima yana zancenki ban bashi dama ba sai yanzu, na tabbata zakiji daɗi kuma zaki samu farinciki sosai idan kika auresa.." "But Abba.." ta katsesa tana kallonsa idanuwansa cike taf da hawaye, yasan abunda take son faɗa hakan yasa shima yayi saurin dakatar da ita haɗe da cewa, "Asgar here is Janan, your always dream ko?" Ya ƙarasa zancen tare da rungumosa, "Yes dady, thank you so much for giving me the hand of the most beautiful lady in the world, i can't say thank you enough Abba" "Hhhh...karka damu, kai ma ɗana ne, Alhaji Hussain muje ko, muɗan basu waje" Kallonta Captain asgar ya shigayi tun daga ƙasanta har zuwa fuskarta dake duƙe ƙasa tana hawaye jin abunda abbanta ke ƙoƙarin yimata, gaba ɗaya ma yaƙi tsayawa ya saurareta balle tasan inda aka dosa, indai kunnuwanta ba ƙarya sukayi mata ba taji ya ce a sheda cewa yaba ɗansa asgar ita kuma a tayasu murna shin me hakan ke nufi, Sosai yake ƙare mata kallo irin kallon da ba don ALLAH yasa doguwar riga da mayafi ba ce pitch colour ajikinta ta rufe mata tun daga sama har ƙasanta da tuni ya gama da ita, saboda kallo ne irin na ƙurulla dake saka mutum tsarguwa da kuma takura, ganin bata ce komai ba kuma bata da niyar cewa ya sashi yin gyaran murya yana murmushi haɗe da cewa, "Hi Janan, my name is asgar Hussain salim, kamar yanda kika ji mahaifin ki ya gabatar maki dani, nasan baki sanni ba amma ni zuciyata ta daɗe da sanin ki tun a shekarun baya, na zaɓeki ki zamo matata ne saboda irin kyau da surar da ALLAH yayi maki, bazan yi maki ƙarya ba tun daga ranar dana gane ki bani da aiki sai tunanin ki da kuma mafarkan ki, ke kaɗai ce macen da zan iya kira mai matuƙar sa'a da tayi nasarar sace zuciya ta, bisa hakan nake yimaki albishir da tanadin TUKUICIN SO aduk lokacin da kika shigo gidana, zan so ki fiye da kowa a duniyar nan, zan kuma ririta ki tamkar ƙwai, kuma na baki kulawar da babu wani ɗan namiji da zai iya bawa wata macce ita aduniya" A daidai lokacin ta ɗago idanuwanta da sukayi jajir, jijiyoyi suka kwanta aciki ga kuma tarin cikar hawaye da sukayi kwance tab a ciki fuskarta ɗaure babu alamun walwala ko kuma annuri aciki, ta buɗe baki da niyar yimasa magana kawai hawaye suka zubo mata yayi saurin sa hannu ya taresu kafin su ƙarasa ƙasa yana murmushi, "Daga ranar yau da Abba ya yimun alƙawarin cewa kin zamo mallakina bazan koma bari hawayen ki su zuba haka ba, masoyiyata faɗa mun meye

Chapter 15 of 40