agidan su shiyasa baisan darajar mutane ba" ya ƙare maganar tare da tattara babbar rigarsa sannan ya zauna yana hucci,
Tsaki Hajiya tayi da duk inda ranta yake ya gama ɓaci tare da cewa, "sannu kai wanda kasan darajar manya, ai naga kai daka shigo ka fara gaishe ni kafin kafara wannan baƙar fitinar taka da bata ci bata canyewa, haba! Kai ko gajiya baka yi? Na rasa sai yaushe zakayi hankalin gane cewa Annabi ya faku, idan shi wancan bai gaisheka ba kake masifa, to shi wannan da ina kallo ya gaisheka ka ƙi amsawa me zaka ce?, Wlh Usman ka kiyaye ni da wannan halin naka domin ya fara kaini bango, har kake cewa babu manya a gidansu baisan darajar su ba, to taya za ayi yasan darajar tasu tunda sun yakice sa ajikin sun wofantar dashi sannan kuma sun zubar da tasu darajar da suke da ita agaban sa, ai barewa baza ta taɓa yin gudu ɗan ta yayi rarrafe ba" ta ƙare zancen cikin ɓacin rai haɗe da miƙewa ta shige bedroom ɗinta ta barshi falon zaune.....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 46_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
TUKUICIN SO FAN'S GROUP, JOIN 👉https://chat.whatsapp.com/J6t2zj6zhcv5ZeQ8IJLHNo FOR COMMENT😍
_____________________________
Kwana ɗaya mm ya so yi a ƙauye nasu amma ganin yanda abubuwan suka kasance ya sa ya ƙara kwana ɗaya, acikin kwanaki biyun kuwa yaga soyayya da gata awajen dangin iyayensa, lungu da saƙo wajen ƴan uwa duka sai da Baffa Ali ya kaisa aka gaggaisa, ya kuma yi masa bayanin matsayin kowanensu a wajensa, tsabar farinciki mm har kuka yayi, sai yanzu ya tabbatar da babu abunda yakai dangi daɗi aduniya, duk da irin rayuwar da sukayi da babu abunda ya nema ya rasa sai yake ganin sait yanzu ne jin daɗin sa da kuma farincikin sa suka kammala, bai baro ƙauyen ba sai daya samu wani waje da ake cirar kuɗi p.o.s ya ciri kuɗi masu yawa ya bawa Baffa don ya rage lalurorin nauyin mutanen dake kansa, ya kuma bi sauran dangi ya rarraba masu dubu biyar biyar wai kuma goma goma ya ce suƙara suyi hidimar gida kafin ya sake dawowa, Sosai Baffa ya so bin sa don yagano inda suke, saboda tsoron kar su sake kucce masu amma sai mm ya ce yayi haƙuri in sha ALLAH bada jimawa ba zai sake dawowa shi da ƙanwar sa, saboda a ganin sa bai kamata yatafi yabar garin ba tunda kusan shi kaɗai ne namiji jigo da ahalin ke kallo dake taimakon su,
Haka Baffa ya haƙura yana ji yana gani mm ya kama hanya ya tafi bayan sun cikashi da abun arziƙi sun ce ya kaiwa Momy,
Ba ƙaramin daɗi Momy da Razina suka ji ba dawowar mm musamman labarin daya je masu dashi na cewa ashe mahaifiyarsu na raye bata mutu ba, duk data wata fuskar gaba ɗaya jikinsu saida yayi sanyi jin labarin halin da take ciki lokacin data ɓata da rashin takamammen wurin da za a sameta, kuka Razina ta fashe dashi tare da faɗawa jikin Momy tana faɗin, "Momy i want see even once in my life" Momy ta shiga bubbuga bayanta alamun rarrashi haɗe da cewa,
"Sorry my dota, very soo we will all see her since she was alive"
"Momy not sure"
"But we prayed so" ta bawa mm amsa tana ƙoƙarin calming nasu, ajiyar zuciya Jabir dake zaune gefe ya ƙurawa ɗan uwan nasa idanuwa ganin halin da yake ciki yayi kafin yace,
"I think wannan ba wata doguwar damuwa bace, kawai abunda ya kamata muyi shine mu samu hotunan umma mukai gidan talabijin da jaridu, sannan mubada sanarwa gidajen rediyo, ina hakan shine hanya mafi sauƙi da zamu fara nemanta"
"Haka ne JB, nima abunda nake tunani kenan, but na tambayesu ko akwai mai hoton ta ya bani suka ce a'a, amma Baffa Ali ya yimun alƙawarin cewa kafin nasake komawa zai bincika mun cikin family ko za a samu wanda ke dashi" cikin sanyin murya Momy ta ɗago kai don gaba ɗaya jikinta ya gama sanyi jin halin da ake ciki ta ce,
"Before that my soon, yana da kyau mufara gayawa ALLAH, mu bashi cigiyar baiwar sa shi da kansa kafin mukai a gidajen rediyo, Inaga wannan shi zai taimaka mana ta hanya mai sauƙi wajen cin nasarar ganinta"
"Upcouse Momy kin kawo shawara, gobe zan kai sadaka a masallatai da kuma makarantun islamiya ayi mana saukar alƙur'ani"
"Hakan ma nada kyau, kafin nan kuma kaima damu duka mu dage wajen addu'a, mu lizimci istigfari da kuma faɗar laa ilaa ha illa antas subhanaka inni kuntu minazzwalimieyn, na ji malaman sunnah da yawa na faɗar cewa babu abunda yafi istigfari saurin warware matsaloli, haka ma duk girman matsala da damuwa idan bawa ya taso istigfari agaba yana yi ba safe, rana, dare to ALLAH zai warware matsalar kuma ya buɗe masa ƙofofin alkhairi da suka toshe masa, don haka sai mu maida su abokanan firar mu daga yau, sai kuma azumi, idan son samu ne ko sau biyu ne zuwa uku muriƙayi gaba ɗaya mu a sati, sai muyi tawassuli da wannan azumin muroƙi ALLAH ya bayyanar mana da ita, Ni nayi imani da ALLAH cewa matuƙar muka koma ga ALLAH gaba ɗayan mu muna masu sanar dashi damuwar mu da buƙatocin mu tabbas zai amsa mana domin shine waraka kuma maganin kowace matsala da damuwa saboda shi nariƙa alokacin da duniya tai mani ƙullin goro, yayin da dangi na suka guje ni, dangin mijina suka kore ni suka juya mani baya, sai gashi ALLAH da baya gudun bayin sa ya riƙe ni irin riƙon da su dangin nawa bazasu iya yimani ba, yayi mani gata irin gatar da dangin miji bazasu iyayi mani ba ya kuma zame mani kariya jigo na rayuwa daga ƙarshe ya fiddani aƙuncin da nake ciki ya dawo da ahalin mijina agareni, kuma ina da tabbaci da yaƙini akansa cewa suma dangin nawa zai dawo mani dasu in Sha ALLAH" ta ƙare maganar tare dasa gefen hannu ta goge hawayen da suka zubo mata tunawa da iyayenta, don idan tace basa cikin ranta to tabbas tayi ƙarya,
"Alhamdulillah da samun uwa tagari kamar ki, haƙiƙa ni da ɗan uwana Jabir da kuma ƙaunar mu Razina mun fi kowa sa a arayuwa da muka sameki a matsayin mahaifiya, mun ji shawarar ki sannan mun aminta da ita, zamu riƙe ta a matsayin wasicci koda bayan rayuwar ki ne don warwarewar matsalolin mu aduk lokacin da damuwa tayi mana ƙullin goro" mm ya faɗa yana mai jinjina imani irin na Momy a zuciyar sa, Jabir kuwa murmushi kawai yayi don hausawa kan ce labarin zuciya a tambayi fuska, ko bai faɗa ba ansan dole yayi alfahari da samun nagartacciyar uwa da yayi a wannan duniyar.
Bayan mm ya gama sauke gajiya da kuma hutawa da marece ya shirya ya faɗawa Momy zai je wajen Hajiya tayi masa ALLAH ya kiyaye tare da cewa ya gaisheta, har ya fita ta kirasa ta ɗibar masa kayayyakin daya zo dasu daga ƙauye ta ce yakai mata, dama tuni ya kira Janan ya faɗa mata su haɗu gidan grandma, don haka ko da ya je ya tadda ita acan,
Cike da farinciki ta tarbe sa tare da taya sa murnar ganin ajalinsa da ya yi, har tana tsokanar sa ALLAH yasa ba a samu ƴar bafillatanar data disashe mata tauraruwa ba, cikin zolaya shima ya amsa mata da cewa, ba a samu ba amma dai ankusa, don ya baro Maryam tauraruwar ta na neman kutso wa cikin duniyar sa, nan take Janan ta ɗaure fuska tare da juyar dakai gefe tayi fushi, murmushi ya yi haɗe da juyawa wajen grandma data fito tana yi masa lale mar haban ya shiga gaishe ta yana dariyar Janan,
Dariyar itama grandma tayi kafin tace,
"To ita waccen iyayen fushin da bata gajiya me akayi mata"
"Ƙyaleta Hajiya tambaya tayi na bata amsa shine take fushi"
"Toooo...kun fi kusa dai ni bazan ce komai ba"
Saida suka ɗan taɓa fira da Hajiya sannan ta koma ciki ta basu waje bayan ta cewa mai aikinta ta kawo mata abinci saboda bata samu taci da rana ba,
Mm kuwa da yake ya kwana biyu basu haɗu da noor alb ɗin tasa ba har aka kira sallar isha yana can, dama bayan sallar magrib Jabir ya iskosa acan shima ya je gaida grandma, don haka ya zauna jiransa har zuwa bayan sallar isha, ganin dare ya yi ya matsawa Janan tawuce gida su kuma suka zauna suka ci gaba da firarsu da grandma har ƙarfe tara da rabi na dare yayi sannan sukayi sallama da ita, suna fitowa daga falon Abba na ƙoƙarin shigowa shi kuma, wani irin mugun kallo ya bisu dashi ɗaya bayan ɗaya yana ƙoƙarin tunano inda yasan fuskokin su, mm ne yayi ƙarfin halin rissinawa ya gaishe shi, shi kuwa Jabir ko inda yake bai kalla ba ya wuce abunsa don kar ya gane fuskarsa, kallo Abba ya bisa dashi ba tare daya amsa gaisuwar da mm keyi masa ba ya wuce ciki ransa nayi masa suya,
Yana shiga cikin fushi da ɓaci rai ya fara magana,
"Hajiya su waye wuɗan nan yaran marasa tarbiya, musamman wancan ɗayan dake saye da wasu ƙazaman ƙananan kayi ajikinsa amma yake ɗaukar kai kamar wani isasshe, sai nasa atumurmusa mani shi yanzun nan, matsiyacin banza da wofi, Inaga babu manya agidan su shiyasa baisan darajar mutane ba" ya ƙare maganar tare da tattara babbar rigarsa sannan ya zauna yana hucci,
Tsaki Hajiya tayi da duk inda ranta yake ya gama ɓaci tare da cewa, "sannu kai wanda kasan darajar manya, ai naga kai daka shigo ka fara gaishe ni kafin kafara wannan baƙar fitinar taka da bata ci bata canyewa, haba! Kai ko gajiya baka yi? Na rasa sai yaushe zakayi hankalin gane cewa Annabi ya faku, idan shi wancan bai gaisheka ba kake masifa, to shi wannan da ina kallo ya gaisheka ka ƙi amsawa me zaka ce?, Wlh Usman ka kiyaye ni da wannan halin naka domin ya fara kaini bango, har kake cewa babu manya a gidansu baisan darajar su ba, to taya za ayi yasan darajar tasu tunda sun yakice sa ajikin sun wofantar dashi sannan kuma sun zubar da tasu darajar da suke da ita agaban sa, ai barewa baza ta taɓa yin gudu ɗan ta yayi rarrafe ba" ta ƙare zancen cikin ɓacin rai haɗe da miƙewa ta shige bedroom ɗinta ta barshi falon zaune.....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 47_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
***********
_https://www.wattpad.com/1257064678?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=n01QYbdmE1VmpOZhkfOBdxk5IfMfXscET1zmvuK7qBgi5RICEHiad6fGUtKxqZrlaUCfZR0B3%2Fq0FwITj04KFLztmRf3eI4Oa8%2BJNyGCBSoM%2FOADG342bVhojxlhOpVy_
*WANNAN PAGE ƊIN NAKU NE, ƳAN TUKUICIN SO GROUP COMMENT, NA GODE DA YANDA KUKE BIBIYAR WANNAN LITTAFI DA KUMA ƘAUNAR DA KUKE NUNA MUN, ALLAH YA BAR SO DA ƘAUNA A MUHALLI, NIMA ƊIN INA YINKU OVER💋♥️*
______________________________
Sake da baki Abba yabi mahaifiyar tasa da kallo yana mamakin kalaman dake fitowa a bakinta, me take nufi da barewa bata gudu ɗan ta yayi rarrage?, Ina zancenta ya dosa daya ji tana faɗin an wofantar dashi tare da zubar da daraja da kima agabansa?, Shi fa kansa ya kulle duk me hakan ke nufi? Ya jerowa kansa duka wuɗannan tambayoyin cike da fargabar amsar da ƙwaƙwalwarsa ke shirin basa, saurin kauda tunanin dake shirin faɗo masa arai ya yi haɗe da miƙewa ya nufi cikin ɗakin,
Zaune ya isko Hajiya bakin gado tana ta rafkar kuka ya yi saurin ƙarasawa haɗe da duƙawa gaban ta ya ce,
"Haba Hajiya! Haba Hajiya! Yanzu fisabilillahi meye abun kuka akan wannan ƴar tambayar dana yimaka?, Wlh yaron can da gani bayada tarbiya shiyasa kika ga nakasa haƙura na yimaki magana, amma don ALLAH kiyi haƙuri"
"Usman tashi ka ficemun bana son ganin ka a halin yanzu, kuma ina tabbata maka matuƙar bazaka dena wannan bangare ɗabi'ar taka ta aibanta mutane da wulaƙanta su ba, to tabbas kana gab da nemana ka rasa saboda nagaji da tarin damuwoyi da matsaltsalun ka da kullum basa ƙarewa sai hauhawa"
"Wai meye ne Hajiya kike ta waɗan nan maganganu akaina?, Me nayi maki haka? Ko me kika nema awajena na hana maki?"
"Tambaya kake yi?, To kaje kayi tunani akai domin tarin laifukan ka yawa ne dasu ba ɗaya ba balle na tsaya sanar dakai su, a ɓangarena lokaci sai daɗa ƙurewa yakeyi haka shekaruna sai ƙara hauhawa sukeyi, ina so inyi amfani da ɗan sauran lokacin daya rage mani a duniya domin gyara kura kuraina, waɗan da son zuciya da biye maka da nayi suka sakani na aikata"
Miƙewa Abba yayi tare sakin ajiyar zuciya yana naɗe babbar rigar sa ya ce,
"Yanzu na gano bakin zaren, na fahimci abunda kike nufi Hajiya, amma ina so ki sani, in har abunda zuciyata da ƙwaƙwalwa ta ke faɗa mani gaskiya ne tofa har yanzu ina nan akan bakata kuma babu abunda zan sauya a ra'ayi na, a matsayin mu na musulmai babu mu ba jinin kafirai, waɗanda akoda yaushe ashirye suke da suga bayan mu, banda abunki ma me zamuyi da tubabba acikin zuri'ar mu?, To wlh indai ina raye hakan bazata taɓa faruwa ba, taje can ta ƙarasa ita da abunda ta haifa munbar mata, ina wannan shine kuskuren da kike tunanin mun aikata har kike ganin baƙina yanzu? Sannan wuɗancan yaran da suka fita suna da alaƙa da ita shiyasa kike nuna mun ɓacin ranki don na faɗi gaskiya?, kenan ita ta turosu don ta sake shigowa rayuwar mu su gurɓata mana zuri'a ita da kafirin ɗan nata data haifa, shi kenan, kafin tayi hakan zansa a binciko mani ita duk inda take don na ƙara jamata kunne da tayi nesa damu kamar yanda nayi a shekarun baya, idan kuma ba haka ba to zan sa a ɓatar mani dasu.." kafin ya rufe baki ya ji Hajiya ta ɗauke sa da wani irin zazzafan mari jikinta har tsima yakeyi saboda tsananin ɓacin rai da ɗacin kalamansa da suka dakar mata kunnuwa tamkar a mafarki, don sam batayi tsammanin taurin zuciyarsa yakai ya iya cewa zaisa a ɓatar masa da wani, cikin zafin rai ta ce,
"Tir da halinka Usman, ai kai ne kafirin ba ita ba ba kuma ɗan ta ba, kuma daga yau kada ka sake kafurta mani jika domin ina son abuna, sannan da kake zancen tubabbiya ai ƙwanda ita ta tubarwa ALLAH ta amshi Musulunci da tsaftatacciyar zuciya, kai fa? Kana musulmi ne kawai amma duka ɗabiun da kakeyi sun sha banban dana Musulmin ƙwarai, kuma ka kasa ganewa ka tubarwa ALLAH nka, na roƙi Sarkin halitta ɗaya gyara maka halaye da kuma ɗabiu kada su kaika ga dana sani tahar abada" ta goge hawayen da suka jiƙa mata fuska haɗe da nuna masa ƙofa tana ci gaba da cewa,
"Fita kabar mun gida bana son ganin ka, kuma in ka fasa sawa a ɓatar maka da ita baka haihu ba, ina nan ina jiranka ga fili ga mai doki, maza ka fita nace" ta ƙare zancen cikin ɗaga murya haɗe dasa hannu ta turasa, ganin yana ƙoƙarin yimata magana yasa ta juya masa baya don yasan halinsa, yanzu ne zai kalallameta da maganganun da zasu iya taunar mata da zuciya taji tausayin sa kuma sam bata buƙatar hakan a yanzu, burinta kawai ya chanja ya dawo mutumen kirki yanda komai zai gyaru a yanda take so kuma take buƙata a yanzu,
"Sam banji haushin marin da kika yimani ba Hajiya domin ke mahaifiya ta ce, amma ki sani zuciyata cike take da tuƙuƙi, ɓacin rai da takaici jin cewa wancan yaron da hasashe na ya zamo gaskiya akan cewa bayada tarbiya ɗa ne ga waccan tubabbiyar matar da nayiwa tsakani damu na kuma haramta mata shigowa gidan nan, da tun shigowata nasan shine da wlh nasa su Jazz sunyi masa mugun dukan da sai kamannin sa sun sauya, ta yanda idan ta gansa ba gidan nan kaɗai ba hatta garin nan saita nisanta sa dashi.." sake juyowa Hajiya tayi ta ɗauke sa da wani kyakkyawan marin cikin dakewar zuciya tare da nuna masa ita ta haifesa ta ce,
"Fita kafin na faɗi kalaman da zasu rusa maka dukkanin farinciki da kuma rayuwa, idan kuma ka fasa aikata dukkanin abunda ka faɗa to na faɗa maka baka haihu ba" yanda yaga ta rikiɗe masa tare da fikkar da dukkanin ɓacin ranta dake cikin zuciyar ta a fili ya sashi saurin juyawa yabar ɗakin dama gidan baki ɗaya kamar zai tashi sama, a halin yanzu babu abunda yake buƙata illa ya keɓance shi kaɗai don ba ƙaramar guguwa ce ke shirin tunkaro sa ba matuƙar Hajiya ta sauya a yanda yake buƙatarta,
Tsabar tashin hankali da tsoron fitinar dake shirin kunno masa kai ganin yanda Hajiya ta sauya masa yau yasa da kanshi ya shiga mota ya tayar ba tare daya jira direban nasa ya ƙara so ba ya bar gidan aguje, da sauri shima ya faɗa cikin ɗayar motar guard ɗin na Abba dake ƙoƙarin tada motocin su kafin su bi bayan sa aguje cike da mamaki suma, yanda yake gudu badon tsarewar ALLAH ba da babu abunda zai hanasa yin accident, ko daya isa gida bai wani tsaya parka motar ba daidai haka kuma bai kasheta ba ya fice ya nufi cikin gidan zuciyar sa na halbawa da sauri da sauri, kai tsaye sashensa ya nufa yana jin tsanar Momy na sake taso masa arai, yana shiga ya fiddo gorar ruwa a fridge ya ya buɗe ya kafa a baki, bai ajiyeta ba sai daya shanyesu tas yayi wurgi da gorar gefe ya sake ɗauki wata ya kafa abaki, itama bai ajiye ba saida ya sha fiye da rabi sannan ya tuttule sauran akansa, hannu ya sa ya shafo fuskarsa tare da yarfar da ruwan daya shafo a gefe ya faɗa kan kujera yana fidda numfashi ɗaya bayan ɗaya kafin ya jingina akan kujerar haɗe da kulle idanuwansa,
A hankali yaji an turo ƙofa tare dayin sallama wanda ba kowa bace face Janan data karɓo masa jikkarsa daga hannunsu Jazz kamar yanda ta saba akoda yaushe,
"Abba.."
"Get out" ya faɗa da ɗan ƙarfi jin takira sunan sa tana ƙoƙarin gaishesa, a hankali ta ajiye jikkar kan kujerar dake nan farkon shigowa sannan tabar falon gaban ta na faɗuwa, kanta ta shiga tambaya ko meke damun Abban nasu ta ganesa cikin tashin hankali haka?. (Oho Janan, waya sani kuma, daga maganar gaskiya sai ya wani ruɗe ya tayar da hankalin sa? Kodai akwai wani abun aƙasa da bamu sani ba wanda ya sa yake tsoron sauyawar Hajiya?, Koma dai meye ja ƙafafuwan kiyi gaba kar ya saukar da ɓacin ran akanki)
Ya jima a haka kafin Nihal ta turo ƙofa ta shigo,
"Hi Dad, Ashe ka dawo" ta faɗa tare da isa wurin ta zauna kusa dashi, a hankali ya buɗe idanuwansa tare da ƙaƙaro murmushin ƙarfin hali yana kallon ta, cikin sanyin murya dake nuna akwai abunda ke damunsa ya ce,
"Na dawo Nihal, ya ake ciki?"
"Fine dad, what's wrong with you?" Ta tambaya tana kallon fuskar sa,
"Nothing Nihal, just want to be sleep"
"Are you sure dad?"
"Yeah upcouse my sweetheart" ya faɗa tare da kissing ɗin hannunta, murmushi tayi haɗe da miƙewa ta ce,
"Ok bye, gudnight" sannan ta fice daga ɗakin ta ja masa ƙofa ta rufe,
Komawa ya yi a yanda ta iskosa yana ci gaba da saƙawa da warware akan yanda zai ɓullowa Hajiya tabar zancen nan da take ƙoƙarin tadowa, ganin ya kasa samun mafita yasa ya fara ƙoƙarin natsar da hankalinsa da tunanin sa waje ɗaya, wanda shi kaɗai zaisa yasan yanda zai ɓullowa bakin zaren al'amarin, don a yanzu babu abunda yake buƙata sama da haɗin kan Hajiya da goyon bayanta akan shirin dake gaban sa, kuma ci gaba da tafiya a hakan ko yunƙurin ɗaukar wani mataki zai iya hanasa cimma gurin sa matuƙar bata sauko daga wannan fushin data hau ba, don haka zai haƙura da wannan damuwar har sai yagama kauda ta gabansa tukuna, in yaso duk yanda ya dace yayi zaiyi don ya shafe wannan zancen da baya ƙaunar bijirowar sa ko tasowar sa acikin rayuwar sa har abada, nesanta Momy da kuma wannan fitsararren ɗan nata dasu shine kawai rufin asirin sa, amma matuƙar ba haka ba to tabbas akwai gagarumar matsala da kuma damuwa tattare dashi, ɗan tsaki yayi haɗe da tambayar kansa meyasa tun ada bai yi tunanin shafe labarin su ba a maimakon ya nisan tasu dasu?, Wani tsakin ya sake saki a karo na biyu kafin ya miƙe ya wuce bedroom ɗin sa ya watso ruwa toilet, falo ya dawo ya haɗa coffee mai zafi ya koma kan kujera ya zauna haɗe da kunna tv yana kallon labarai yana kurɓan coffee ɗin hankali, don ba laifi ya ɗan samu natsuwa yanzu fiye akan ɗazu.
Washe gari tunda safe ya shirya ya je gidan Hajiya, zaune ya iskota tana karyawa ya turo ƙofar falon a hankali ya shigo, suna haɗa idanuwa ta kauda kanta gefe tare da ƙoƙarin miƙewa tabar wajen, da sauri ya ƙara sa tare da gurfanawa a gabanta,
"Don ALLAH Hajiya kiyi haƙuri karki tashi"
ALLAH daya haɗata dashi yasa ta koma ta zauna tare daci gaba da karinta, tanƙwashe ƙafafuwan sa yayi agabanta ya gyara zamansa yana karantar fuskarta, har yanzu akwai sauran ɓacin rai ɗauke da ita amma duk da haka bazai tafi ba zai tsaya ya bata haƙuri, sai da ya bari ta gama sannan yayi gyaran murya haɗe da cewa,
"Ina kwana Hajiya" batayi niyar ta kasa ba amma sai ta taushi zuciyarta kasancewar tanada matuƙar raunin zuciya da kuma tausayi wanda hakan yasa yake cin galaba akanta akoda yaushe, cikin kwantar dakai da sanyin murya ya ce,
"Hajiya kiyi haƙuri ki yafemun abunda ya faru, wlh Hajiya ko bacci ban samu nayi ba jiya don ALLAH kiyi haƙuri"
"ALLAH ya sawaƙe" ta faɗa tare da miƙewa fuskarta a ɗaure tabar falon, ganin haka ya tabbatar masa da har yanzu cikin fushi take bata sauka ba, don haka shima sai ya mike ya nufi uwar ɗakin tata, yana azo ƙafarsa ta ce,
"Me na faɗa maka jiya ne?"
"Kiyi haƙuri Hajiya"
"Tafi abunka in kuma shigowa zakayi ni sai in tashi inbar maka ɗakin" jin ta ce haka yasa ya koma baya haɗe da ficewa daga gidan gaba ɗaya, da yake yasan akwai wani nufi azuciyarsa haka ya dinga zuwa kullum.yana bawa Hajiya haƙuri amma tayi banza dashi ta nuna masa da yinsa da rashinsa duk ɗaya agareta matuƙar bai shirya sauyawa ba izuwa yanda take so, kimanin kwana uku ya kwashe yana faman lallashi da bata haƙuri kafin ya samu a kwana na huɗun ta haƙura, shima ɗin saida ta sake yimasa faɗa sosai tare da nasiha sannan ta nuna masa komai ya wuce ta haƙura, suna zaune suna fira da ita Jabir ya shigo gidan yazo kawo mata ganye data bugawa Momy ta ce asiyo mata, wani irin ƙololo ne ya tasowa Abba yayi saurin ɗauke kansa gefe don kar Hajiya ta fahimta, shi kuwa Jabir yana tunkarowa falon daya hango Abba sai yayi saurin juyawa, kallon Abba Hajiya tayi haɗe da cewa,
"Duba Don ALLAH, yanzu kai haka adda daɗi ace ɗanka ka zame masa abokin gaba, ka koma tamkar maƙiyinsa saboda hali irin naka?" Shi dai Abba baice komai ba sannan kuma bai juyo ba sai faman tafarfasa zuciyar sa keyi, yana jin muryar Jabir yana faɗin,
"Ke ƴar tsohuwa mai kuka turo a karɓar maki saƙonki na wuce"
"Haba kai kuwa mijin yarinya shigo mana"
"Wa? ALLAH ya tsari gatari da shuka, kedai aiko karɓar maki don nikam yau banga wajen zama agidan ki ba"
Miƙewa tayi tsam ba tare da yaji tahowarta ba har ta ƙara so ta kamo kunnensa tana faɗin,
"Ni kake faɗawa hakan don gidan ku" ta matse kunnen tare da jawosa ta shigo cikin falon dashi, "Awwshh.." ya faɗa yana dariya tare daci gaba da cewa,
"Sakeni grandma ma kada kiyiwa Momy illa ga ɗan zaki ɗin nan nata da take ganin ya girma ta kusa fara cin moriyar sa"
"Waye ɗan zakin?, Saina makeka anan" ta faɗa tare da ɗaga ɗayan hannunta kamar zata dake sa, dariya yasa ya haɗe hannayensa waje ɗaya yana faɗin,
"Tuba nake uwar ɗakina, wannan irin fushi haka ai saiki kumbura
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 40