An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf
*RANAR NAKA...*
©️ _Fareeda Abdallah_
1)
Duk da yadda ƙofar ta kasance ta bature mai masifar tsada, irin mai taushinnan sosai da ko an buɗe ba ta ƙara, daga yadda ta murɗa hannun ƙofar da ƙarfi, ta danno a haukace kuma a fusace, sai da ƙofar tayi wata siririyar ƙara mai kama da fitar iska. Hakan yasa mazauna ɗakin waiwayowa da sauri suna kallonta da wani yanayi mai kama da maɗaukakin mamaki a fuskokinsu.
Ganin irin kallon da suke mata yasa ta ƙara harhaɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk! Kamar an sheƙawa ƙullun kunu tafasassasshen ruwa. Kallon huɗu saura kwata ta watsa musu gaba ɗaya, sannan ta ba iska ajiyarsu ta hanyar jan tsaki ƙasa-ƙasa. Ta taka kai tsaye ba tare da tsoro ko fargaba ba zuwa gurin mamallakiyar ɗakin da take zaune kan kujerar gaban madubi, da kakkausar murya ta ce
"Abincin Innaye da aka manta da wanzuwarta a cikin gidannan na zo karɓa..."
"Ke dabbar ina ce ƴar ƙauyen-ƙayau da bata san abinda ya kamata ba? How dare you da za ki shigo min ɗaki kai tsaye da wani ƙazamin jikinki ba tare da neman izini ba ina tare da abokan aiki na?"
Ta katse yarinyar da maganganun cikin fushi. Da miƙewarta tsaye a fusace, da ɗaga hannu ta kai ma yarinyar wani mahaukacin mari baza'a ce ga wanda ya riga wani ba.
Cikin zafin nama da ƙwarewa a zamiya yarinyar tayi saurin duƙawa ƙasa marin ya bi iska. A haukace ta miƙe tsaye tana haki, domin an shammaceta, a zuciyarta take ayyana lallai da marinnan ya sauka a kumatunta ta rantse da girman Allah babu abinda zai hana ta ɗaukar wannan figaggiyar matar mai shegen girman kan tsiya da wulaƙanta ɗan Adam ta nuna ma Allah sannan ta maka ta da ƙasa. Sai dai duk abinda zai faru ya faru.
"Kan Uba... Ni kika mara?"
Ta faɗa cikin ɗaga murya.
"Me nai miki da za ki mare ni?"
Ta sake jefa mata tambayar tun kafin ta bata amsar tambayar farko. A ranta take kitsa lallai ya kamata ta nuna ma matar nan halin dabbobi da jahilan ƴan ƙauye da take yawan zaginta da su.
Bazai yiwu duk zagi da tozarcin da tayi mata a cikin kwanaki bakwai na zamansu a gidan ya tafi a banza ba, lallai ya kamata ta nuna mata shiru-shiru fa ba tsoro bane, gudun magana ne.
Kafin matar ta amsa, ko kuma ɗaya daga cikin mazauna ɗakin ta ce wani abu ta ɗaga hannu biyu da sauri ta ɗora akai, ta fasa wani gigitaccen ihu da muryarta mai bala'in ƙara, cikin ƙanƙanin lokaci muryar yayi amsa kuwwa a ko wane lungu da saƙo na cikin gidan.
Tsakanin Innaye da take zaune kan dadduma a ɗakin da aka sauke ta acan BQ tana gyangyaɗi, da Hafiz da dawowarsu kenan mai gadi ya buɗe musu ƙofar get direba yana ƙoƙarin daidaita fakin ɗin motar a tsakar gidan. Baza a ce ga wabda ya riga wani isa cikin ɗakin Bintu da ihun Zulaikha ke fitowa ba.
Tana ganin Innaye da Hafiz sun shigo ba tare da jin nauyin jikinta ba kasancewarta yarinya mai garin jiki da wani irin gudu tayi gurin Innayen ta ruƙun-ƙumeta tana ƙara ƙarfin kukanta.
Taga-taga sukai za su faɗi, domin jikin Innaye irin na fulani ne ga kuma rashin ƙarfi saboda tsufa da rashin lafiyar da take fama da shi cikin kwanaki biyun, a dabarance Zulaikha ta riƙe Innayen tare da rage nauyin da ta sakar mata.
Cikin kuka da yanayin shagwaɓa da taɓara ta fara cewa
"Innaye mari na fa tayi, wai don kawai a ladabce na ce mata Aunty Bintu ina abincin Innaye? Mai aikin da take kai mata kila yau ta manta ne bata kai mata ba, ga shi har yamma ta yi. Shi ne fa kawai ta ɗaga hannu ta gaura min mari... Wayyo Allah kumatuna, zafi, zafi, zafi kumatuna Innaye ki duba min ko ya saɓule..."
Tana zuwa nan a maganganun da take yi cikin kuka ta sake yanka ihun da yasa da sauri Hafiz ya saka yatsarshi manuniya ya toshe kunnuwansa, saboda jin wani zazzaƙar ƙara da ya karaɗe cikin kunnuwanshi mai barazanar fasa dodon kunne.
Ita kuwa Innaye da ta yarda da maganganun da Zulaikha ta faɗa ɗari bisa ɗari, wani kallon kin kyauta ta aika ma Bintu a fakaice, sannan ta ƙara janyo Zulaikha jikinta tana duba ɓangaren kumatunta na hagu da hannunta ke dafe da gurin tana risgar kuka. A lokaci guda kuma tana rarrashinta da tausasan kalamai
"Yi haƙuri Auta, ƙyale ta kin ji ko? Ta yi ma kanta. Yau in sha Allah za mu tattara ina-mu ina-mu mu koma inda muka fito."
Tana gama faɗin haka bata jira wani ƙarin bayani ba ta ja hannun Zulaikha suka fice daga ɗakin zuwa masaukinsu.
2)
Hankali tashe, a firgice Hafiz ya bi bayansu bayan ya aika ma da Bintu da abokan aikinta wani kakkausan kallo da ko a wasa bai taɓa shiga tsakaninsu da shi ba.
Gudu-gudu yake taka matakalar benen yana kiran sunan da suke faɗa mata cikin magiya da ban haƙuri.
"Innaye, Innaye, don Allah kiyi haƙuri... Ki saurareni don girman Allah..."
Duk yadda yake bin bayanta yana magiya da maganganun ban haƙuri bata saurare shi ba sai da suka isa masaukinsu a can Bq.
Babban waje ne, kuma masauki ne mai kyau, ɗauke da gado da saitin kujeru masu kyau na matsakaitan kuɗi. Sai dai fa Bq ɗin can bayan gida ne da yayi banbaraƙwai ace an sauki Uwar miji a gurin. Idan da sanin darajar ɗan'adam ko ƙanwar miji bata cancanta a sauketa a gurin ba ballantana uwa. Domin tun tale-tale an tsara gurin ne a matsayin masaukin ƴan aikin gidan.
Baya ga haka kuma, a can cikin muhallin da masu gidan ke zaune, akwai ɗakunan baƙi har guda uku, ko wane ɗaki da bayi a ciki, ɗauke da setin gado masu tsada. Sai dai duk bayan sati guda mai aiki ke buɗewa ta gyara a sake mayar da ƙofofin ɗakunan a kuk-kulle. Saboda masu gidan basa amfani da su, sai dai idan matar gidan tayi baƙi daga ɓangarenta masu matuƙar muhimmanci sosai take buɗe musu suyi masauki a ciki.
"Ina saurarenka! Ya aka yi Hafizu?"
Innaye ta tambaye shi da murmushi a fuskarta, murmushin da duk mai hange da lura idan ya kalle ta kai tsaye zai fahimci murmushin yaƙe ne, irin murmushinnan da ko kusa bai kai zuci ba.
Amma da yake Hafiz a firgice yake, sam bai lura da kalar murmushin da take yi ba. Ajiyar zuciya kaɗan ya sauke don ganin murmushin yasa shi ji a ransa lallai fa Innaye bata ɗauki abinda ya faru da zafi ba.
Daman tun tale-tale ita ɗin mai haƙuri ce, kuma har yanzu ita ɗin uwa ce mai matuƙar haƙuri da kawar da kai akan duk muradun ƴaƴanta, matuƙar bai saɓawa doron addininmu na musulunci ba.
A marairaice ya duƙa a gabanta ya cigaba da magiya
"Innaye, don girman Allah da darajar fiyayyen halitta SAW kiyi haƙuri da abinda ya faru."
Yayi maganar cikin ƙanƙan da kai da taushin murya, fuskarsa a takwarkwashe kamar zai saka mata kuka.
Daƙiƙu talatin ta ɓata tana kallonshi, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta. Daga bisani ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. A hankali ta ce
"Babu komai Hafizu. Ya wuce."
Ta faɗa a taƙaice. Sannan ta kawar da idanunta daga kan shi ta maida kan Zulaikha.
Wacce izuwa wannan lokacin ta daina kukan da take yi, tana kwance ne akan gado ta duƙunƙune ƙafafu da hannaye cikin hijabin jikinta, ja juya fuskarta can ta basu baya, ita kaɗai take sakarwa kanta ƙayataccen murmushi, idan ta tuna diramar da ya faru yanzu-yanzu.
Abin kamar a shirin film, ko kuma a iri labaran nan na littafi.
Ta sake sakarwa kanta murmushi tana maganar zuci
'Ko babu komai dai a yanzu an fara goge raini tsakaninta da matar can. Ta gwada mata kaɗan daga cikin halin dabbobi da jahilan ƴan ƙauye da take kiranta da su. Idan da ragowar hankali a jikinta gobe baza ta sake gwaɓa mata maganar banza makamantan waɗannan ba...'
"Auta?"
Innaye ta katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta a tausashe.
Da saurin gaske ta ɓata yanayin fuskarta kafin ta juyo a hankali da shagwaɓaɓɓiyar murya ta ce
"Na'am Innaye."
Cikin kulawa Innaye ta sake ce mata
"Ya kumatun na ki? Ya daina zafi?"
Ƙif-ƙifta idanu tayi, nan take suka cicciko da ƙwallah, sannan ta amsa da
"Ya dai ɗan ragu, ba kamar ɗazu ba, amma fa har yanzu yana min zafin."
Duk maganar da take yi, ko kusa bata yarda ta saka idanunta cikin na Hafiz ba, duk da kuwa yadda shi ɗin yake ta ƙoƙarin su haɗa idanun, amma fau-fau ta ƙi yarda hakan ya faru.
Da rarrashi Innaye ta sake cewa
"To kiyi haƙuri. Zan shafa miki man zafi a gurin, zai daina gaba ɗaya in sha Allahu. Yanzu dai miƙe ki kwaso mana shanyar kayanmu da suke igiya, yau in sha Allahu komai dare gida muka kwana."
Irin yadda lokaci ɗaya ta ƙayata fuskarta da murmushi, sannan ta diro daga kan gadon da sauri ba tare da kasala ko jin nauyin jikinta ba, shi ya ƙara bayyana ma Hafiz lallai abinda yarinyar take jira kenan. Ya bi ta da wani mugun kallo, a yadda yake jin matsanancin tsanarta a ransa ji yake kamar ya janyo ta yayi ta bugu har sai ya tabbatar ta yi mugun jigata.
Na daga cikin dalilan da suka sa a kullum yake ƙara tsanar ƙanwar tasa, tun da suka zo gidan cikin taƙaitattun kwanakin da suka yi gani yake ita ce Ummul-aba'isin da aka kasa samun gwaggwaɓar shaƙuwa tsakanin matarsa da yake matuƙar so, da mahaifiyarsa da yake tsananin ƙauna...
"Kayi haƙuri Hafizu."
Innaye ta katse mishi tunani da faɗin haka. Kafin ya ce wani abu ta cigaba da cewa
"Yau in Allah ya yarda zan ɗauke ta mu koma inda muka fi wayau. Na san a zuciyarka ji kake kamar ka kamata ka yanka saboda an taɓo zinariyar matarka ko?"
Innaye ta jefa mishi tambayar da muryar da ke bayyana ɓacin rai ƙarara, saboda akan idanunta ya bi Zulaikha da mugun kallon da babu abinda yake bayyanawa sai matsananciyar tsana da ƙiyayya
"Ba haka bane Innaye."
Yayi maganar a sanyaye. Kafin ta amsa ya sake cewa
"Da gaske ba haka bane. Ni dai roƙo na a gare ki don girman Allah kiyi haƙuri ki daina batun tafiyarki gida yau..."
"Yau za mu tafi Hafizu."
Ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa.
"Ba ki haƙura ba kenan Innaye? Don darajar Allah kiyi haƙuri ki yafe min, kuma ki yafe ma Bintu. Ni na tabbata ko rantsuwa nayi babu kaffara da gan-gar baza ta hana ki abinci a gidannan ba. Bari in je in kawo miki abincin..."
"Da ma ka barshi Hafizu. Idan mun isa gida za mu samu abinda za mu ci."
Ta sake katse shi da fuska mare walwala tana ninke ƴan kayayyakinsu da suke ajiye a gefen gadon.
Bai sake cewa komai ba ya miƙe a hanzarce ya fice daga ɗakin. Ƙiris ya rage su gwabza karo da Zulaikha da ta dawo hannunta ɗauke da kayayyaki, ko kallonta baiyi ba ya wuce da sauri kamar zai tashi sama.
Babbar yatsarta na hagu tasa a kunnenta, da wani irin salo na shaƙiyanci ta karkaɗa harshe da ƙarfi tana mishi gwalo.
Karaf a idanunsa da ya juyo kamar an umarce shi da juyowa. Cije gefen baki yayi, ya ƙanƙance idanu kamar zaiyi magana amma tuni ta faɗa cikin ɗakin a gaggauce ta barshi tsaye a gurin kamar mutum-mutumi.
Tunawa da abinda ke gabanshi yasa shi yin ƙwafa, ya karkaɗa kai sannan ya wuce da sassarfa zuwa cikin gidan. Yana shiga yaga Bintu ta fito daga ɗakinta ita da abokan aikinta su huɗu, da alamun rakiya za tayi musu.
Da kalle shi da tattausan kallo mai bayyana matsananciyar soyayyarta a gare shi. A fuskarta babu alamun damuwa ko misƙala zarratin, sai ma lallausan murmushin da take aika mishi.
"Hi Dear... barka da dawowa."
Ta faɗa da sanyin murya tana kallonshi fararen idanunta kar-kar masu ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen namiji.
Duk yadda yaso ɓoye damuwar da ke zuciyarsa ya amsa mata kamar babu komai kasawa yayi. Daƙyar ya iya tausasa harshensa ya ce
"Ki same ni a sama yanzunnan Bint, ina son magana da ke."
Yana gama faɗin haka ya wuce ciki ba tare da ya saurari Aminiyar Bintu mai suna Raudha da take ƙoƙarin janshi da wasa kamar yadda suka saba a tsakaninsu ba.
"Bint, ko dai in tsaya inyi ma Hafiz bayanin gaskiyar abinda ya faru ne? Kin ga fa kamar ya yarda da abinda wancan bulkut ɗin ƙanwar tashi ta faɗa..."
"Haba... Haba Raudha."
Ta katse ƙawar tata da sauri tun kafin ta aje numfashi.
"Kar ki wani damu kanki. Ke kanki kin san ba wancan jahilar ƙanwar tasa ba, ko ita baƙauyiyar tsohuwar bata isa ta shiga tsakiyar ginin kyakkyawan tubalin zaman takewa da yarda da juna da muka ɗauki tsawon shekaru biyar muna ginawa tsakanina da My Dear ba. Da kaina zan yiwa tufkar hanci... Ba sai na sake bari sun zo min gida sannan za ta zo min da wani munafurcinsu na ƴan ƙauye ba? Ni kam daman kin san ba wani zuwa can ƙauyen nasu nake yi ba, ko wani abu na dolen-dole ya faru da ya kamata in je ba na wuce awa biyu zuwa uku acan. Zan yi wa tufkar hanci very soon. Kar ku damu kanku."
Ta amsa cikin fariya da ɗagawa.
"To ke dai kiyi a hankali Bintu. Irin waɗannan ƙauyawan da kike gani kaska ne mashaya jini. Basu cika gane akwai babbar tazara tsakanin talaka da mai arziki ba sai an taka musu birki, an nuna musu iyakarsu da gasken-gaske. Amma... Ki iya takunki. Ko ɗan kaɗan ne kin san yana ƙaunar tsohuwarsa da ƴan'uwansa."
Ɗaya daga cikin ƙawayen nata mai suna Aliya ta sake faɗin haka tana ƙara jinjina girman al'amarin da ya faru akan idanunsu.
"Hmmm! Kar ku damu fa, kamar dai baku san hali na ba? Zan ɗauki matakin da ya dace, kun sani ba na barin matsala komai ƙanƙantarta ba tare da na kawar da ita ba."
Ta sake amsawa cikin yanayin yarda da kai tana sakin murmushi.
Dariya suka yi gaba ɗayansu, sannan suka fice daga falon zuwa tsakar gidan in da motocinsu suke. Anan ma sai da suka sake ɓata lokaci mai yawa suna jaddada ma Bintu lallai fa tasan yadda za tayi da gaggawa ta ɗauke hankalin Hafiz daga kan danginsa da iyayensa da suka kasance ƙauyawa.
3)
Duk da ce mata da yayi yana jiranta za suyi magana, bata je inda yake ba sai da ta sake ɓata fiye da mintuna goma a gurin ƙawayenta suna ƙara tattaunawa duk akan matsalar su Innaye.
Ko da ta haura saman benen ɗakinsa ta fara shiga, a zatonta yana ciki, sai taga baya nan. Tana fitowa daga ɗakinsa shi kuma ya gaji da jiranta a nata ɗakin ya fito zuwa ɗakinsa a gaggauce, a rashin sani sukai gware da kawunansu.
"Auuuuchhhh! My dear za ka fasa min kai... Zafi..."
Ta faɗi maganar a marairaice da shagwaɓa tana liliya goshinta inda sukai karo.
"Yi haƙuri."
Ya faɗa a taƙaice. Har lokacin fuskarsa babu walwala ko kaɗan. Tsintsiyar hannunta ya damƙa ya ja ta suka kama hanyar sauka daga saman benen
"Mu je ki ba Innaye haƙuri. Abinda ya faru yayi matuƙar tunzurata ta yadda har ta sha alwashin barin gidannan a yau. Kuma ai kin ga hakan bai dace ba ko?"
Ya jefa mata tambayar yana kallon cikin idanunta, fuskarsa damalmale da damuwa.
Matuƙar dauriya tayi gurin danne ɓacin ranta, har ta iya sakin taƙaitaccen murmushi.
"Eh! Gaskiya kam bai kamata ta tafi yanzu ba. Ka san akwai wasu gwaje-gwaje guda biyu da aka yi mata wanda har yanzu sakamakonsu bai fito ba. Gobe dai in sha Allah nake sa ran fitowarsu sai in ga wasu magunguna ne zan ɗora ta akai."
"To kin gani. Kuma saboda Allah ni da na ɗauko ta da nufin aƙallah ta samu ko wata uku tare da mu don jikinta ya ƙara warwarewa sosai? Kawai yanzu cikin sati ɗaya ta fara zancen tafiya? Wai ma taya akai har hakan ta faru? Ina Rabi ta tafi da har aka kai irin wannan lokacin ba'a kai ma Innaye abincin rana ba har wannan tsautsayin ya faru?"
A daidai lokacin suka isa ƙofar ɗakin da aka sauki Innaye. Don haka Bintu bata ba shi amsa ba, ba ƙaramin godiya tayi ga Allah ba da yasa suka isa ƙofar ɗakin a daidai wannan lokacin. Da tabbas babu abinda zai hana ta fashewa da kuka idan ta buɗe baki da nufin ba shi amsoshin tambayoyinsa.
A zuciyarta take ta tufka da warwarar maganganunsa
'Wata uku? Saboda Allah a ina yake nufin wannan tsohuwar za ta zauna har na tsawon watanni uku? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Sai a yanzu take da na sanin amince masa tun farko da ya ce mata zai ɗauko mahaifiyarsa a duba lafiyarta. Da kawai tubure masa tayi da cewar ba sai ya ɗauko ta ba, a matsayinta na likita gara ta bishi can ƙauyen ta duba ta, in yaso daga baya ta tattara duk magungunan da ciwon tsohuwar ke buƙata ta bashi ya kai mata.
Abu ɗaya tayi tunani da yasa ta amince da ɗauko tsohuwar, shekarunsu biyu ne da aure. Kuma a cikin shekaru biyun ko sau ɗaya tsohuwar bata taɓa taka ƙafafunta zuwa gidan ba, hana rantsuwa dai ƴan'uwansa mata da suka kasance masu bala'in naci da takura sun je har sau uku. Su ɗin ma karon farko ne kawai ta tarbe su da fara'a, karo na biyu da na uku kuwa tarba ne tayi musu irinna lallai idan suna da hankali za su janye jikinsu daga na ta da na mijinta, irin tarbar nan ta kora da hali ya fi kora da sanda. Kuma haƙarta ya cimma ruwa domin idan ba ta manta ba, watanni bakwai kenan babu wacce ta sake tako ƙafarta zuwa cikin gidan.
Gare ta hakan ta fi nono fari, ba ta da niyyar raba su da ɗan'uwansu, amma tana so lallai su tsaya iya limit ɗin su. Su gane tsakanin shi da Allah ya tsamo shi daga rayuwar ƙauyen ƙayau zuwa cikin birni, yayi zuzzurfan karatun boko, Allah yayi mishi gyaɗar dogo ta hanyar samun babban aikin gwamnati da gaggawa, ya tara maƙudan kuɗaɗe cikin ƙanƙanin lokaci, ya tamfatsa babban gida sannan ya auro ta ƴar manyan mutane bayan shekaru biyar da suka kwashe suna buga zazzafar soyayya akwai tazara mai ƙololuwar yawa a tsakaninsu. Baya ga duk waɗancan ni'imomin da suke ciki ita ɗin babbar likita ce da take aiki a babban asibitin Abuja. Taya a matsayinta na wayayyiyar mace ƴar boko ma'aikaciyar lafiya da ta san illar yawan cuɗeɗiya tsakanin ɗan birni da na ƙauye za ta yarda waɗannan gidadawan mutanen da suke a matsayin dangi da iyayen mijinta su dinga mata jela a gida?
Shi dai da yake nasu kuma suka zama dolenshi tana ɗaga mishi ƙafa lokaci bayan lokaci yaje gurinsu, amma fa ko kwana idan ya wuce ɗaya ba ta taɓa yarda yayi. Kuma yana dawowa tun kafin ya taɓa komai na amfanin gidan take haɗa mishi ruwan wanka da sinadarai masu kashe ƙwayoyin cuta ta sille shi da kanta. Ba ta samun nutsuwar zuciyarta har ta iya rungumarshi sai bayan ta shafe shi da turarukan jiki na maza masu mabanbantan ƙamshi...'
"Heyyyyy! Tunanin me kike yi haka?"
Hafiz ya katse mata zuzzurfan tunanin da ta afka ciki ta hanyar girgiza kafaɗunta da ɗan ƙarfi.
Firgigit! Ta dawo daga duniyar tunanin da take yi.
"Na'am! Iye? My Dear magana kake yi?"
Ta jefa mishi tambayar a daburce.
Bakinshi ya matsar kusa da kunnenta sannu a hankali ya raɗa mata maganganu masu daɗi da taushi da za tayi amfani da su gurin ba Innaye haƙuri. Sai da ta gyaɗa mishi kai alamun ta ji, kuma ta fahimta sannan ya kama hannun ƙofar ɗakin ya murɗa, suka shiga ciki a tare bakunansu ɗauke da sallama.
Kallo ɗaya Zulaikha tayi musu tayi saurin wawurar hijabinta da ke ajiye gefe ɗaya ta zura a jikinta. Tsabar sauri ma a baibai ta saka, bata damu da hakan ba ta juya musu baya tana kallon bango, ciki-ciki ta fara ƙunƙuni ƙasa-ƙasa bakinta a gaba yadda babu mai jin abinda take cewa sai ita kaɗai.
Daga Bintu har Hafiz babu wanda ya kalli Zulaikha ballantana su damu da abinda take yi. Kai tsaye gaban Innaye da take zaune a gefen gado suka ƙarasa, ba tare da wani ƙyama ko tsantseni ba Hafiz ya zube a gabanta gwuyawunshi a ƙasa. Ita kuwa Bintu ƙasa-ƙasa ta ƙarewa kan tile ɗin kallo, duk da a share yake tas kuma a goge har yana ɗaukar idanu ta kasa zama ko kuma tasa gwuiwa a ƙasa kamar yadda mijinta yayi.
Sai da ta runtse idanu, ta cije leɓe, kafin ta iya tsaro maganganun kamar yadda ya faɗa mata.
"Maganar komawarki gida ma don Allah kiyi haƙuri, ki ƙara mana lokaci kaɗan kafin ki koma. Kin ga har yanzu ban gama tattara sakamakon gwaje-gwajen da aka yi miki a asibiti ba. Kuma ko gobe ma idan zan tafi tare za mu fita, akwai wani gwaji da za'a sake miki na ciwon
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 40