da kika yi ta haɗawa a zamantakewarmu ne? Kai... Ni kam me za'ayi da mace irinki Bintu? Iyaye da ƴan'uwana na jini kika so raba ni da su fa... Shi yasa a kullum ba na gajiya da godewa Allah da yasa idanuna suka buɗe tun lokaci bai ƙure min ba... Allah na gode maka..."
"Ha...fiz..."
Ta katse shi da rawar murya, jin da tayi zuciyarta na neman bugawa saboda zafin baƙaƙen maganganun da yake yayyaɓa mata. Maganganun da ita da kanta ta san gaskiya yake faɗa, gaskiya mai masifar ɗaci da maƙaƙi a zuciya.
"Na sani, ni da kaina na aikata kura-kurai masu yawa a baya... Kura-kurai masu girma da gyaruwarsu sai a hankali, domin ba a taɓa ɓari a kwashe duka. Me yasa a yanzu da nake neman tuba baza ka bani dama ta biyu ba? Sannan abu ɗaya da nake so ka sani shi ne, sam ban zo Ofishinka don ƙara fama gyambon da tun asali ni ce sanadiyyar samuwarshi ba. Alfarmarka nake nema Hafiz, dama ta biyu kawai nake buƙata a gurinka... Kwanaki uku da suka wuce na je Faƙo na nemi yafiyarsu Innaye, kuma duk sun yafe min ba tare da wani tashin tashina ba. Shekaran jiya na je gidan Zulai, ita ma na roƙe ta gafara, kuma ta tabbatar min ta yafe min har ma munyi musayar lambar waya a tsakaninmu. Me yasa baza ka kwaikwaya daga halin Iyaye da ƴan'uwanka ba...?"
"Saboda ni ɗin ba su bane da kika saba raina ma hankali kina buga su kamar Tamaula. Look Bintu, salo-salo na munafurcinki kin daɗe kina buɗa min shafi bayan shafi, ko wannan neman yafiyar da kika yi na tabbata wani salon munafurcin ne. Bari in sake maimaita miki, idanuna ya daɗe da washewa a kanki Bintu, yanzu kar nake kallonki. Ki tattara kayanki ki koma Faƙo idan har kina mu cigaba da zama... idan ba haka ba kuwa sai in ce Allah raka taki gona..."
"Me kake nufi Hafiz?"
Ta tambaye shi da maɗaukakin tashin hankali a fuskarta.
Sai da yayi taku biyu zuwa gabanta sannan ya ce
"Ina nufin in dai baza ki koma Faƙo ki zauna da su Innaye ba, ni kuma bazan cigaba da riƙe igiyar auren ki ba. Zan sake baki takardarki ki je can ki sami wani mijin da bashi da iyaye ƙauyawa..."
"Anya kana so na kuwa Hafiz?"
Ta jefa mishi tambayar ƙirjinta na bugawa, domin bata san irin amsar da zai fito daga bakinsa ba.
"A da kenan Bintu. A yanzu kuwa ko rantsuwa nayi miki babu kaffara Kareema ta daɗe da mamaye filin da a baya mallakinki ne... Idan akwai wata ƴar kimarki da ta rage a idanuna bai wuce ta kasancewarki uwar Aadil ba, a bayan haka kuwa na rantse da Allah kallonki ma ba ƙaramin baƙin ciki da takaici yake saka ni ba."
Da saurin gaske Bintu ta lalubi kujerar da ke bayanta ta zauna, jin da tayi lokaci ɗaya wani hajijiya mai ƙarfi yana neman kifar da ita a ƙasa.
"Na gode Hafiz. Na gode ƙwarai."
Tayi maganar da muryarta da lokaci ɗaya ya shaƙe, ya shige can ciki kamar wacce aka maƙurewa maƙogwaro.
Dafe kanta da taji yana bugawa da ƙarfi kamar ana sara mata guduma tayi, idanunta a lumshe. A zuciyarta take ta janyo duk irin addu'ar da ya zo mata. Ta daɗe a cikin wannan halin sannan daƙyar ta ɗan dawo cikin nutsuwarta, ta sake buɗe baki daƙyar ta ce
"Allah ya sani ni har yanzu ina son ka Hafiz... Sannan in da ace ina da tabbacin kana so na, zama a Faƙo tare da su Innaye ba komai bane, ko babu komai zan ƙara gogewa da wani sabon ilimi na zamantakewar rayuwar duniya wanda da can ban san shi ba."
Ta ɗanyi shiru tana mayar da numfashi a wahalarce, daƙiƙu sittin ta ɗauka sannan ta cigaba da magana
"A fahimtata da zaman aure yarjejeniya ta amincewar zamantakewa tsakanin mutane biyu, ba nau'i ne na cutarwa ko bautarwa ba. Kuma ko wane aure akwai wasu muhimman turaku da suke riƙe da wannan aure, So, Ƙauna, Yarda, amincewa haɗe da yima juna uzuri su suke taka muhimmiyar rawa gurin jan ragamar ko wane zamantakewar aure zuwa tudun mun tsira. Daga abinda na fahimta a kalamanka na yanzu Hafiz ba ka so na, sannan kuma ka daɗe da yanke min tsammanin zan shiryu, don haka da waɗannan dalilan ina ga babu amfanin cigaba da zaman aure a tsakaninmu..."
Tana zuwa nan a maganganunta ta fara shessheƙar kuka da ƙarfi, amma duk da haka bata tsagaita ba sai da ta kai aya
"Allah ya sani ina daga cikin matan da matsananciyar soyayya ta yi kaɗan ta rufe min idanu inyi zaman kwantai da wulaƙanci a gurin ɗa namiji... Bazan yi zaman cutuwa sannan inyi haƙurin da babu lada in hallaka ba, sannan kai ma in halakar da kai, saboda rashin ƙauna zai sa baza ka iya sauke nauyin haƙƙina da ya rataya a wuyarka ba. Don haka, ina roƙon mu kawo ƙarshen wannan tafiyar Hafiz... Allah ya sada mu da alkhairinsa."
Da saurin gaske ta duƙunƙune gogaggen hijabinta ta cusa a baki saboda kukanta da ya ƙara ƙarfi, sannan ta fice daga Ofis ɗin da sassarfa tana sharɓen hawaye.
In da Allah ya taimaketa shi ne da direba ta je Ofis ɗin, ba don haka ba lallai da sai dai ta ɗauki shatar Taxi ya mayar da ita gida, domin a irin wannan halin da take ciki sam baza ta iya tuƙa mota ba.
"Baba Mamuda gidan Aunty Halima za ka kaini."
Ta faɗi haka ga direba bayan sunyi nisa a kan hanyarsu ta komawa gida.
"To Hajiya Likita. An gama, Allah ya huci zuciyarki ya yaye miki abinda yake damunki."
Direban ya faɗa da murya mai bayyana damuwa da halin da Bintu ke ciki.
******
"Anya Bintu kin yi tunani mai zurfi kuwa? Kina ganin rabuwarki da Hafiz shi ne zai zama maslaha a rayuwarki?"
Aunty Sadiya ta faɗi haka da murya mai bayyana damuwa sosai, bayan ta gama sauraren duk irin bayanin da Bintu tayi mata cikin kuka da tashin hankali.
Ita kanta ta shiga cikin ɗimuwa. Kuma ta sani duk irin abubuwan da suka faru a zamantakewar auren Bintu laifin Bintun ne. Amma bata yi tsammanin bayan sakkowa da Bintu tayi ta gane kuskurenta har tayi aniyar gyarawa Hafiz zai cigaba da riƙe laifukanta a zuciyarsa ba.
"Kiyi haƙuri Aunty... In sha Allah hakan shi ne mafi alkhairi."
Bintu ta amsa da shaƙaƙƙiyar murya, gwanin ban tausayi. Idanunta sun kumbura sun yi tulu-tulu saboda kukan da ta ɗauki tsawon lokaci tana yi.
"Shi kenan Bintu. Za mu cigaba da taya ki addu'a Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi. Amma dai na so ace kin ƙara zurfafa tunani. Mata da yawa Bintu suna rayuwa ne a gidan mazajensu ba tare da wata aba wai ita soyayya ba. Idan za ki tara mata ɗari, ko wacce za ki ji dalili ne mabanbanta ke zaune da ita a gidan mijinta ba don tana jin wani mashahurin daɗi ba..."
"Bazan iya ba Aunty."
Bintu ta katse ta da sauri.
"Allah yana gani bazan iya irin wannan zaman ba. Da dai ace in ƙare rayuwata a irin wannan zaman da ƙarara miji ya nuna min kuma ya faɗa min ba ya so na, na rantse da Allah gara in haƙura da auren gaba ɗaya. Ban ce bazan iya haƙuri a cikin rayuwar aure ba, haƙurin da na san ina cutuwa ne gaskiya bazan taɓa iyawa ba..."
"To Aadil fa? Yanzu ko rayuwar ɗaya-ɗayan ɗan da Allah ya baki bai isa yasa ki haƙuri da Ubansa ba Bintu? Malam bahaushe fa cewa ya yi duk bakin da ya furta so a farko, ko daga baya ya zo ya furta ƙi ɓacin rai ne yasa shi faɗin haka. Ki tausaya ma rayuwar yaron ki."
"Uhmmm! Aunty kenan! Ni fa duk wata shaci-faɗi ta Malam bahaushe ba da ni za'ayi ta ba. Ina duba maslahar rayuwata ne, idan da rabon mu sake zama can gaba wata ƙila mu haɗu, amma a yanzu kam na rantse da Allah ko son Hafiz zai kashe ni bazan koma gidansa ba.
Batun Aadil kuma yara da yawa suna rayuwa ba tare da mahaifiyarsu ba, kuma Allah yana raya su cikin aminci. In da ace mutuwa nayi kuma fa?"
"Shi kenan. Tunda har kin rantse. Yanzu sai ki tashi mu tafi can gida gurin Daddy, tunda dai ta inda aka hau ta nan ake sauka."
*******
Ko da suka je ma Daddy bayanin halin da ake ciki, Tambaya ɗaya da yayi ma Bintu shi ne
"Tausayin halin da kika shiga sanadiyyar rabuwarki da Hafiz, da irin mawuyacin halin da kika sake faɗawa ranar da kika ga hoton auren Hafiz yasa na karya gwuiwata na roƙi mahaifinshi ya kira Hafiz ya tilasta mishi mayar da ke ɗakinki. A yanzu da ke da kanki ki ke ganin rabuwar ta fi alkhairi a tsakaninku, ina fatan baza ki sake ɗaga mana hankali da koke-koken baza ki iya rayuwa ba tare da mijinki ba?"
"In sha Allahu hakan baza ta sake faruwa ba Daddy."
Ta amsa idanunta a ƙasa, wasu sabbin hawayen suna tsattsafo mata amma tayi ƙoƙarin haɗiyewa.
"Shi kenan. Allah hakan shi ne mafi alkhairi a tsakaninku."
"Amin thumma Amin."
Umma da Aunty Sadiya suka amsa cikin haɗin baki.
Sallamarsu Daddy yayi suka koma falon Ummansu. Yayi shiru cikin tunani, zuciyarsa cike taf da rashin jin daɗin al'amarin. Can kuma sai ya ɗaga waya ya kira Abba Lurwanu ya kora mishi bayanin duk halin da ake ciki.
Shi ma sosai ya nuna alhini akan lamarin, daga bisani kuma ya ƙarke da addu'ar Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi. Bayan gama waya da Abba Lurwanu kai tsaye lambar Baffa ya lalubo ya danna mishi kira, bayan sun gaisa, a nutse ya faɗa mishi duk abubuwan da ke faruwa.
Da farko sosai Baffa ya ɗaga hankalinshi, saboda a tunaninshi duk laifin na Hafizu ne, sai da Daddy yayi mishi bayani gwari-gwari, da irin hujjojin da Bintu ta bashi sannan yayi sanyi, da rashin jin daɗi da alhini sosai a muryarsa shi ma yayi ta jera addu'ar tabbatuwar abinda ya fi zama mafi alkhairi tsakanin ma'auratan biyu.
******
"Yaya? Wai kuna duba lokaci kuwa? Yanzu fa ƙarfe goma sha ɗaya saura kwata na dare, daga yini ɗaya har yanzu baku dawo min da ɗana ba. Gaskiya in dai haka ne yinin bazan sake baku aron shi ba."
Zulai tayi maganar tana kumbura baki, kamar Hafiz ɗin yana gabanta.
Dariyar Kareema da Hafiz da take jiyowa ƙasa-ƙasa ta cikin wayar yasa ta sakin baki galala.
"Kinga Zuly, gara ma ki kwanta kiyi barcinki. Aadil ya dawo gida kenan. Tun ɗazu ma ya yi barci, haba!! Yaye fin wata ɗaya ai kinyi na Allah da Annabi. Ke ma ki huta ki ji da lafiyarki."
Kareema tayi maganar daga can ɓangaren har lokacin da dariya a muryarta.
"Kar ku min haka Aunty Kareema, kina sane dai na faɗa ma su Innaye gobe da Aadil zan je Faƙo..."
"Jibi idan Allah ya kaimu mu ma muna tafe. Don haka ki kwanta kiyi barci, gobe kafin ku wuce ki barma Mummy duk kayanshi zan aiko a karɓa."
Hafiz bai jira ƙorafin da za ta sake yi ba ya katse wayarsa.
Tsananin haushi yasa bata duba tazarar lokaci da ke tsakanin inda take da ƙasar da Abban Imam ya je ba ta lalubo lambarsa ta danna mishi kira. Kiran farko da na biyu bai ɗauka ba, sai a kira na uku ya ɗauka, da magagin barci a muryarsa ya ce
"Beb...!"
Kukan da ta sakar mishi yasa shi wartsakewa ba shiri. Hankalinshi a tashe ya fara tambayarta lafiya? Me yake faruwa?
"Ba Yaya bane da Aunty Karima..."
Ta amsa mishi a shagwaɓe.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na samun nutsuwa sannan ya sassauta murya ya ce
"Su basu san da a taɓa min ke gara aje a rungumi transformer bane? Amma dai faɗa min, me suka yi miki don in san irin matakin da zan ɗauka a kansu."
Tana ƙananun kuka ta bashi labarin duk abinda ya faru.
Ɗan murmushi ya saki, amma ko da wasa bai bari murmushi ya bayyana a muryarshi ba ya fara rarrashinta yana kakabin rashin kyautawar da suka yi mata.
"Amma ba komai, sun yi ma kansu. Kiyi zuciya kin ji ki ƙyale musu ɗan su. Abinda ma nan da sati uku zan dawo mu duƙa da noma mu ma mu samo namu ɗan. Kila ma a karon farko ƴan'uku za ki haifa min, ai na san Matata jaruma ce ko?"
Dariya ta fara ƙyalƙyalawa sannan ta katse wayar bayan ta ce
"Ni dai sai da safe. I love you wujiga-wujiga Hubbyna."
******** *******
*_BAYAN SHEKARU BIYU_*
"Ina ga kamar duk mun gama siyayyar da ya kamata muyi ko Ƙurratul-ayn?"
Hafiz ya tambayi Kareema cikin kulawa, kyakkyawar babynsu ƴar watanni Shida mai sunan Innaye ana kiranta da Najma saɓe a kafaɗarsa. Ita kuma Kareema tana riƙe da hannun Aadil wanda ya girma sosai ya ƙara wayau, idan ma sani mutum yayi ba, sai ayi tsammanin ya shekara biyar a duniya. Ya yi kyau sosai cikin kayan turawa da aka saka masa, kallo ɗaya za ayi mishi a fahimci yaro ɗan gatan iyayensa gaba da baya.
"Eh kamar dai mun gama Nurul-ƙalb! Mu je mu biya Bill ɗin kawai, idan da wani abu da muka manta ma ai gobe rana ce. Mu je kawai, tun ɗazu Zuly take kira na wai mai lallen ta kusa gama mata."
"Ok!"
Ya amsa a taƙaice, sannan suka nufi gurin biyan kuɗi.
Kusan duk inda suka gitta sai sun zama abin kallo a idanun jama'a saboda tsananin haɗuwar da suka yi. Da ganinsu an ga masoya da suke bala'in son juna, ga ƴaƴayensu guda biyu gwanin ban sha'awa.
Cikin ƙanƙanin lokaci Hafiz ya biya duk bill ɗin yaran shagon suka kwasa musu manyan ledojin kayan zuwa gurin motarsa.
'Zulaikha ce ta haihu, tun farkon auren da tayi ɓari sau ɗaya bayan watanni biyar da aurensu, a lokacin ita kanta bata san da cikin ba. Allah bai sake ba ta wani rabon ba sai da ta shafe watanni takwas, a hakan ma sai da Innaye tasa aka karɓo mata maganin sanyi da na haihuwa a wani ƙauye can nesa da su. (Masu buƙatar ingantaccen maganin sanyi da na haihuwa ko na cancer su tuntuɓeni ta wannan lambar 07039080978)
A watan da ta sha maganin cikin hukuncin Allah ta samu ciki, haka ta raini cikin a wahalce cikin kulawa da tarairaya daga mijinta Abban Imam, Sarkuwarta Mummy, kakarsu Hajja, Kareema da Hafiz, Innaye, Baffa, yayyenta har Allah yasa ta haihu lafiya. Ta haifi ɗanta namiji ƙato da shi.
Tun da aka yi haihuwar Hafiz ba ya nan, yana can Lagos ma'aikatarsu ta tura shi sai jiya ya dawo, sayayyan kayan barka ne suka zo yi shi da Kareema.'
Suna daf da ficewa daga gurin Bintu ta sawo kai cikin Store ɗin. Kallon-kallo aka tsaya yi na wasu daƙiƙu tsakanin Hafiz da Bintu, saboda shekara ɗaya kenan cif ba ta Nigeria.
'Bayan riƙo da kalmar nan ta Mal bahaushe da ya ce idan so cuta ne, haƙuri magani ne. Ta sha wahala ba kaɗan ba duk a ƙoƙarinta na yakice Hafiz daga zuciyarta. Haka ta dinga murgina rayuwar da daɗi babu daɗi cikin godiya ga hukuncin Ubangiji ta cigaba da aikinta, amma da taimakon MD ɗinsu ta samu canjin gurin aiki, saboda ba ta son tana ganin Kareema balle har ta dinga jin ɗacin rabuwa da Hafiz.
Sai da aka yi watanni huɗu cif da rabuwarsu wata rana kwatsam ta koma gida daga gurin aiki ta tarar Hafiz ya kai Aadil hutu gidansu. A wannan ranar ta yi kuka a ɓoye kamar babu gobe, zuciyarta cike da tunanin baya da abubuwan da suka faru a cikinta.
Sai daga bisani ta wartsake ta rungume ɗanta tsam tana shaƙar daddaɗan ƙamshin da ke fita a jikinsa. Daga bisani ta fara ina aka saka ina aka aje da shi zuciyarta cike da jin daɗi, ko kaɗan bata ga alamun wani wahala a jikin ɗanta ba. Sati biyu cif yayi a gidan sannan Hafiz ya aika direba da saƙon jibi zai aika a ɗauko shi. Zuwa jibin kuwa biyu bisa uku na tattalin arzikinta haka ta ƙarar da shi akan sayi banza sayi wofi na siyayyar yaron, boot ɗin motar Hafiz cike taf da kayayyakin tsarabar yaron aka mayar da shi gida.
Tun daga sannan, duk sadda yaron suka samu dogon hutu yana aike mata da shi har zuwa sadda suka shafe shekara guda cif a cikin wannan rayuwar mai rangwamen daɗi ga Bintu, mai cike da daɗin daɗi ga Hafiz, saboda bayan kulawa, tarairaya, nutsuwa, kwanciyar hankali, soyayya, ƙauna da yake samu daga Kareema ya samu ɗaukaka sosai ako wane fanni na rayuwarsa.
Kwatsam! Sunan Bintu ya fito a cikin wasu gungun likitoci guda talatin da gwamnati ta ɗauki nauyinsu don zuwa yin couse na shekara guda a ƙasar India. Wannan dama da Bintu ta samu shi ya zama sanadiyyar manta baya a gare ta, ta cicciɓa rayuwarta zuwa tudun mun tsira ta fuskanci gaba, a yanzu haka bayan kammala couse ɗin ta dawo ne da mijinta a hannu. Likita ne ɗan'uwanta Dr. Hashim, ya taɓa aure sau ɗaya amma matarsa ta rasu, masifar ƙaunar Bintu yake yi yayinda a ɓangarenta za'a ce babu yabo babu fallasa.
Tun kafin su dawo Nigeria, iyayen Hashim sun miƙa komai na kayan aure gidansu Bintu, yanzu haka bikin saura sati biyar da kwanaki biyu.
Lokaci ɗaya Hafiz da Bintu suka yi saurin wayancewa daga kallon da suke ma juna, saboda idanuwan Kareema da take tsaye kamar mutum-mutumi tana kallonsu, da wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskarta.
"A'a! Mummyn Aadil ku nake gani haka? Ya kuke? Ya bayan rabuwa kuma?"
Bintu tayi saurin jero maganganun ga Kareema, fuskarta cike taf da dariyar yaƙe. A zuciyarta kuwa yaƙi take da shaiɗanin da ke neman ɗarso mata wani banzan tunani akan Hafiz daga ganinsa sau ɗaya bayan shekaru biyu da suka shafe basu ƙara haɗuwa ba.
"Aunty Bintu ashe kin dawo? Shi ne babu ko labari ai da mun zo miki sannu da zuwa ni da Yaro na."
Kareema ta faɗa tana dariya. Kafin Bintu ta ce komai Kareema ta sake cewa ga Aadil cikin harshen turanci.
"Aadil ka ga Ummee ta dawo? Je ka gaishe ta kayi mata oyoyo."
Da gudu Aadil ya tafi ya rungume ƙafafun Bintu yana murnar ganinta. Cike da ƙauna ita ma Bintu ta tsuguna daidai tsawon yaron tana biye ma surutunsa. Aadil ɗin ne ma yake faɗa mata ai Auntynshi Zulai ta haifi baby boy ƙatoto.
Tsakanin Hafiz da Bintu an rasa wanda zai fara cewa da kowa komai har sai da Kareema ta karɓi makullin motar da ke riƙe a hannunsa bayan ta bashi uzurin za ta buɗe boot a zuba kayayyakin da suka siya.
"Dr. Bintu! Hope kin dawo lafiya."
Hafiz ya karya gwuiwa matsayinsa na namiji ya tambayeta da muryarsa mai cike da kwarjini.
Ba ƙaramin namijin ƙoƙari tayi ba gurin danne tsohon mikin da ke taso mata a zuciyarta ta amsa mishi a mutunce. Sannan ta gaishe shi, ta ƙara da tambayarsa bayan rabuwa.
"Lafiya ƙalau. Congratulation."
Ya amsa gaisuwar a taƙaice, ya ƙara da yi mata murna.
Amsawa tayi cikin sanyin murya, sannan ta miƙa hannu ta karɓi Najma da ke riƙe a hannunsa tana yi mata wasa lokaci guda kuma tana tambayar sunanta.
Karima da take zaune a cikin mota tana kallon duk abinda yake faruwa, shiru tayi ƙirjinta na bugawa, zuciyarta na suya saboda kishi. Shaiɗan da iya ƙayata abu kuma sai take ga kamar har wani murmushi na musamman Hafiz da Bintu suke sakar ma juna. Ta samu sauƙin damuwarta ne sanadiyyar addu'o'i da tayi ta ja cikin zuciyarta.
Kamar Hafiz ya san halin da Kareema ke ciki sai cewa ya yi
"Bari mu wuce, Ƙurratul Ayni na jiranmu a cikin mota. Duk da de waccan weekend ɗin a gida gurinsu Umma Aadil ya yi gobe da safe direba zai kawo miki shi ku gaisa, zuwa yamma sai a dawo da shi. Saboda jibi sunan Zulai, za su tafi da wuri."
"Na gode ƙwarai Daddyn Najma. In sha Allah nima zan leƙa gidan sunan don mu gaisa da su Aunty Balira. Allah ya raya."
"Amin."
Ya amsa sannan ya karɓe ƴaƴanshi ya nufi mota, ita kuma ta tsaya tana kallon bayanshi, zuciyarta na ƙuna da tafarfasa. Dama ta sani, za'a daɗe bata daina da na sanin kura-kuran da ta aikata har suka janyo rabuwarta da Hafiz ba.
Da ƙyar ta iya haɗiye ƙwallar da ya taho mata kafin ta juya da sauri ta shige cikin Mall ɗin.
********
Bubbuga ƙafa ta fara yi a shagwaɓe sannan ta ce
"Ni dai gaskiya Aunty Ruwan wankannan ya yi zafi da yawa. Don girman Allah ki surka. Wallahi ni kaɗai na san azabar da nake sha idan kika ɗebo tafasasshen ruwan zafin nan a tawul kika danna min a baya."
Daƙuwa Aunty Balira tayi mata, ta ƙara da cewa
"Ƙaniyarki Zulai, Wankan jego idan ba'a yi da tafasasshen ruwa ba da me kike so ayi? Ba kya so jikinki ya yi ƙarfi ki samu lafiya a gaggauce da juriya fiye da da ne?"
Shiru tayi, sai kuma ta amsa a hankali
"Ina so mana Aunty. Amma azabar ruwan zafin ne ba sauƙi..."
"Kin san Allah Aunty ki daina biye ma Zuly. Ki gargashe ta da kyau yadda ya kamata, idan ruwan ma ya fara sanyi ki ƙwalla min kira in ƙaro tafasasshe. Gaba ɗaya Yaya Kamal ya sangartata kamar ba mace ba."
Kareema da take zaune a cikin ɗakin ana yi mata lalle ta tsoma bakinta a cikin zancen da suke yi, tana maganar tana dariya.
Da fuskar tausayi Zulaikha ta ce
"Ba komai! Ba komai Aunty Kareema. Na gode. Na san zama na da ke. Kuma wannan maganar da kika faɗa kamar a kunnen Abban Imam..."
Da sauri Kareema ta ce
"Aaaa ni kar ki ƙulla min jakar tsaba in tafi kaji su tsattsaga.. Ba ruwana. A kanki Abban Imam idanunshi rufewa yake yi..."
"Kamar yadda na Yaya Hafiz suke rufewa a kanki ba."
A tare duk su biyun suka yi dariya.
Haka suka ci gaba da hira da raha a tsakaninsu har ruwan ya ɗan sha iska kaɗan sannan aka yi wankan.
Tana fitowa daga bayin ta ji shigowar motar Abban Imam cikin gidan, da saurin gaske ta cire tawul ɗin da yake kanta, ta ɗauki babban hijabinta ta saka ta kama hanyar fita daga ɗakin da sauri, bata saurari Kareema da ke ƙwalla kiran sunanta ba.
Cikin mita da mamakin rashin ta idon Zulaikha a fuskar Aunty Balira ta ce
"Uhmmm! Ai in dai Zulai ce za kiyi ki gama, ba ta haɗa lokacin mijinta da komai duk da jego take yi. Ni da nake gidannan ai ina shan kallo. Shi yasa sati biyu kacal zanyi in tattara komatsaina in koma inda na fito. Ga Hajja nan, da taimakon Mummy sai su ɗora daga inda na tsaya."
"Ki ƙyale su kin ji Aunty, idan kika yi sati biyun anan, kawai mu wuce gidanmu ki ƙarashe sauran kwanakin a can..."
"Taɓɗijan! Ashe kuwa da na yi gudun gara na faɗa zago. Bazan iya da rashin kunyar Hafizu ba, ke dai da kunya a idanunki, Hafizu kuwa kunya ta bi can! Shi ya bi nan."
A kunyace Kareema ta sunkuyar da kanta ƙasa tana dariya. Ita ma Aunty Balira dariya ta yi.
Can kuma sai ta fara jajen mutanen Faƙo masu zuwa suna, har yanzu basu iso ba saboda basu fito gida da wuri ba.
Su Aunty Rakiya sun iso ne daf da kiran sallar magriba. Nan take gidan ya ƙara kaurewa da hayaniya. Dom ma dai tunda cikin ya tsufa suka koma ɓangarensu na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 40