kwanto mishi.
Yana ji, Zulaikha ta gama bayar da labarin rikicin da ya shiga tsakaninta da Bintu, da har yayi sanadiyyar ɗauke ta daga gidan da yayi zuwa gidan Mummy. A hankali, kuma cikin nutsuwa ta cigaba da bayanin zamanta a gidan Mummy, da irin kyakkyawar kulawar da ta samu a hannun zuri'ar gidan. Wanda shi ya hana rayuwarta tagayyara ko kuma taji ta ƙosa ta dawo gabansu iyayenta.
Abu ɗaya da ta ɓoye musu a labarin shi ne soyayyarta da Kamal (Abban Imam), tafi-tafi har zuwa jiya da ta buƙaci lallai Hafiz ya kawo ta Faƙo ayau, ko kuma ita da kanta ta taho a motar haya.
Tana zuwa nan a labarin da take ba su tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, irinna wacce ta jima tana kuka. Muryarta a shaƙe ta cigaba da cewa
"Rashin zama na a gidan Yaya ba shi ne abinda ya fi damuna ba Baffa. Wannan takardar da kuka ji ina tambayarsa ya tuna ta?"
Ta fito da takardar da har ta fara jiƙewa da gumi saboda cukwuikwuiyeta da tayi a tafin hannunta tana nuna musu, da karkarwar murya ta cigaba da cewa
"Duk da ya rubuta bayanin cikin takardar da yaren nasara ne, ba saƙon komai takardar take ɗauke da shi ba illah na yanke igiya ɗaya daga cikin igiyoyi uku da suka ƙulla aure tsakanina da shi... Sannan ya rubuta takardar ne tun ranar da ya rabo ni daga gidansa, saboda rashin iya karatun turanci yasa ban san me takardar ta ƙunsa ba sai bayan sati biyu da ba ni takardar. A yanzu haka kuma fiye da watanni shidda kenan da faruwar wannan al'amari, kuma duk da yana zuwa gidan Mummy ga shi nan ku tambaye shi na rantse da Allah bai taɓa furta cewa ya mayar da ni ɗakina ba har na gama iddah... A taƙaice dai Baffa, Innaye, Aunty Balira don Allah kuyi haƙuri ku yafe mana irin wasa da hankalinku da muka yi ni da Yaya, amma zance na gaskiya shi ne babu wani aure ko zamantakewar aure tsakanina da shi."
Lallai wannan shi ne asalin karin maganar nan da Malam bahaushe ke cewa Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana.
Izuwa yanzu da Zulaikha ta gama koro musu wannan cukurkuɗaɗɗen labarin da basu taɓa tsammanin faruwarsa a nesa da ƙauyensu bama balle har ya faru a cikin ahalinsu. Ba Hafizu ne kaɗai bakinsa da tunaninsa ya tsaya na wucin gadi ba, Innaye da Aunty Balira ma sun bi sahunsa.
Shi kuwa Baffa tsananin mamaki, takaici, baƙin ciki, haushi ne suka taru suka zame mishi wani dunƙulallen abu a maƙoshi. Sau uku yana ƙoƙarin kalato miyau don ya haɗiye ko zai samu dunƙulallen abun ya sauka a cikinshi amma bakinshi ya bushe ƙayau, kamar mai azumi a lokacin da ake tsananin ƙwallara rana.
Shi da ba mura yake yi ba, ba kuma kuka ya ɗauki lokaci yana yi ba balle ace su suka zama sanadiyyar shaƙewar muryarsa. Ko da ya buɗe baki da niyyar tambayar Hafizu daƙyar maganar ta fito a dusashe ya ce
"Da gaske ne duk abinda ƴar'uwarka ta faɗa? Ka sake ta tun washe garin ranar da kuka bar ƙauyen nan?"
Sai a wannan lokacin da Baffa ya jefa mishi waɗannan kausasan tambayoyin guda biyu, sannan ya ji kamar an kwance duk wani dabaibayi da aka yi ma bakinsa, ƙwaƙwalwarsa, da jikinsa. Cikin sauri ya motsa ƙafafunsa da suka yi masa tsami sosai saboda doguwar tsayuwar da yayi ya zube a ƙasa.
Ya sani, laifi ne ya riga da ya aikata shi. Yunƙurin yin ƙarya don kariyar kai ko kuma musanta abinda ta faɗa duk ba shi zai hana tonuwar asirinsa komai daren daɗewa ba. Don haka yaga gara kawai ya faɗi gaskiya, tare da yi musu gagarumin sadaukarwar da a wancan lokacin da aka ɗaura aurensa da Zulai a karo na farko ya kasa yi musu.
"Da gaske ne Baffa. Na sani ni mai laifi ne sosai, domin na yi wasa da hankalinku. Amma don Allah kuyi haƙuri ku yafe mana kamar yadda Zulai ta roƙa mana. Sannan tunda yanzu lokacin da nake da damar mayar da ita ya wuce, na rantse da Allah yanzu a shirye nake in karɓi aurenta da hannu bibiyu don in faranta muku rai..."
Saukar wasu tagwayen maruka a kuncinsa dama da hagu shi yasa shi rufe baki ba tare da ya shiryawa hakan ba. Duuummm! Shi ne ƙarar sautin da yake ji a kunnuwansa na tsawon wasu daƙiƙu. A idanunsa kuwa babu abinda yake kallo sai gilmawar wasu ƙananun taurari masu tsananin haske da sheƙi.
Da saurin gaske ya rufe idanunsa don tsoron kar hasken taurarin su illata mishi ƙwayoyin idanu. Da farko, ya zaci ya kurmance saboda ƙarar duuummm ɗin da yake ji a kunnuwansa ya daɗe bai daina ji ba. Sama-sama kuma sai ya fara jiyo muryar Innaye tana mishi magana kamar daga can nesa kafin maganar ya matso kusa da kunnensa sosai.
A tsorace, ya buɗe idanunsa yayi arba da Innaye da Baffa suna tsaye a gabansa suna huci. Da ganin irin tsayuwar da suka yi ba shi buƙatar a faɗa mishi daga hannun su wa tagwayen marukan da ya amsa suka fito.
[2/11, 10:54 PM] Fareeda Abdallah: "Hafizu su wa ka mayar sa'anninka?"
Innaye ta sake jefa mishi tambayar da matsanancin ɓacin rai a muryarta.
"Mu za ka wulaƙanta Hafizu? Mu? Mu za ka wulaƙanta?"
Izuwa wannan lokacin, muryarta rawa yake sosai, zafafan hawaye na sauka daga idanunta. Cikin fushi da gushewar hankali ta sake buɗe baki ta ce
"Hafizu Allah..."
Da wani mahaukacin tsawa Baffa ya katse ta
"Keh Rahina kin yi hauka ne? Ɗan naki za kiyi ma baki saboda abinda bai taka kara ya karya ba?"
Ba Baffa kaɗai ba ya shiga firgici da jin kalaman da Innaye ke ƙoƙarin furta ma Hafiz ba. Aunty Balira da Zulai ma sai da suka miƙe tsaye, hannayensu biyu ɗore akai hankulansu a tashe.
Kamar ƙaramar yarinya, haka ta fashe da kuka zuciyarta na ƙuna da raɗaɗi
"Ya zanyi Malam? Shin akwai inda na ragi Hafizu a tarbiyya ne da zai min wannan mummunar sakayyar? Ya zanyi?"
Hannayenta biyu ya riƙe ya ja ta ya zaunar akan kujera. A tausashe ya fara mata magana
"Kiyi haƙuri. Hannunka ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. Ki yafe masa, ita kuma Zulai mu cigaba da yi mata addu'ar dacewa da wanda ya fi shi alkhairi."
Hannayenta ya saki ya koma gurin Hafizu da kallo ɗaya za a mishi a fahimci ba ya cikin hankalinsa.
"Ka je, je ka Hafizu. Babu komai ai, wani zamani ne Allah ya kawo mu da kuyanga take haifar uwargijiyarta. Je ka, mun sallama, mun kuma yafe maka. Allah ya haɗa fuskokinmu da alkhairi."
Yana gama faɗin haka ya koma kusa da Innaye ya zauna, tafukan hannayensa biyu yasa ya rufe fuskarsa. Kamar yana kuka, amma a zahiri ba kukan yake yi ba, nauyayan ajiyar zuciya yake ta sassaukewa akai-akai. Ba ya ko son ganin fuskar Hafizu, shi kanshi in banda ƙarfin zuciya da mazantaka babu abinda zai hana shi furta mummunan kalami ga Hafizu kamar yadda Innaye tayi niyya.
Hankalinshi a tashe, maɗaukakin tashin hankali irin wanda tunda ya zo duniya bai taɓa shiga kwatan-kwacinsa ba. Da rarrafe, ya fara muskutawa da nufin ƙarasa gurinsu Baffa a fusace Aunty Balira ta dakatar da shi.
Hannunsa ta kamo, ta miƙar da shi tsaye a fusace, yana waigen su Baffa yana cijewa a haka ta ja shi har sai da ta fice da shi daga cikin ɗakin. Bata ƙyale shi ba sai da ta kai shi har gurin motarsa.
Direba da tun ɗazu yake jiran fitowarsa yana ganinsu ya buɗe ƙofar, tura shi ciki Aunty Balira tayi sannan ta cusa kanta cikin motar suna kallon juna
"Kayi haƙuri. Mu kam su kaɗai muke da, ba mu da makwafinsu a wannan duniyar. Gara kai, ko da sun mace kana da Tauraruwa Bintu da gudan jininka Aadilu. Kaje kawai, domin cigaba da ganinka kaɗai ya isa yasa zuciyar Innaye da Baffa bugawa. Mun sallama ka ga Bintu Hafizu."
Fuuuuu ta wuce zuwa cikin gidan ba tare da ta saurari ko zai ce mata wani abu kamar yadda taga bakinshi na motsi ba.
A ɓangarensa har ya yunƙura zai bi bayanta, sai kuma ya tuna wasu daga cikin maganganunta gaskiya ta faɗa. A yadda ya ɓata ma Baffa da Innaye rai lallai ya kamata ya basu iskar da za su huce ko na kwana ɗaya ne.
"Mu je."
Ya faɗi haka ga direba daƙyar! Sannan ya janyo ƙofar motar ya rufe, ya lumshe idanunsa ya jingina da jikin kujera, yana jin yadda kanshi ke wani irin matsanancin sarawa kamar zai faɗo.
****** ******
Kwanaki bakwai da suka biyo baya wasu irin zafafan kwanaki ne suka kasance ga Baffa da Innaye da Aunty Balira. Duk da labarin mutuwar auren ya bazu ga sauran dangi, amma waɗannan mutane uku su ne waɗanda al'amarin yafi yi wa mugun dukan da in banda Allah ya kiyaye tabbas da sun samu matsala a lafiyarsu.
Innaye da Baffa jininsu ne yayi mummunan hawa, gara ma Innaye daman an san tana da hawan jini, shi kuwa Baffa da ba'a taɓa sanin yana da shi ba sai yanzu Allah ne ya tsare shi amma da ya kamu da cutar mutuwar ɓarin jiki.
Kasancewar yanzu an samu gagarumin cigaba a asibitin ƙauyen, duk ranar litini da talata da laraba, akwai babban likita da yake zuwa daga kaduna ya duba marasa lafiya. Kuma an zuba ma'aikatan jinya ƙwararru a asibitin, cikin hukuncin Allah da taimakon wannab likitan na kyawawan magunguna da ya rubuta musu, da kuma nasiha da tunatarwa kan muhimmancin yarda da ƙaddara daga bakin babban malaminsu Zulaikha Baffa da Innaye har ma da Aunty Balira suka cigaba da rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Kaso sittin da biyar na damuwarsu ya ƙaura, musamman ganin yadda Zulai ita da kanta take iya ƙoƙarinta wajen rarrasarsu da kalaman kwantar da hankali.
A cikin waɗannan kwanaki bakwai, zuwan Hafizu sau uku ƙauyen, amma sam ko kusa ya kasa samun yadda yake so. Lallai wannan shi ne BAYAN TIYA AKWAI WATA CACA. Sa'adda ya yanke ma kanshi shawarar rabuwa da Zulaikha salin-alin don samun kwanciyar hankalinsa da na iyalinsa ko kusa bai hango ma kansa faruwar wannan ƙalubalen ba.
Shi dai kam Allah ya sani ko na daƙiƙa ɗaya bai taɓa jin soyayyar Zulai a zuciyarsa ba. Kuma tun da aka ɗaura aurensa da ita ya shafe kwanaki biyu ne cif cikin zazzafan tunanin ta yadda zai iya fara gudanar da rayuwar aure tare da Zulai.
Bai hango ma kanshi zai iya ko da kwatantawa ba. A ganinsa, zaman aure da Zulai zaluntarta kawai zaiyi ƙarara, ba ya son ta, Bintu ita ce zaɓin zuciyarsa. Ta yaya zai iya kwatanta adalci a tsakaninsu? Ya gama haƙƙaƙe ma kansa zama da Zulai tamkar jefa kansa a halaka ne.
Sake tunawa da babu ɗa'a ga abokin halitta wajen saɓa ma mahalicci yasa shi rubuta ma Zulai takardar saki bakinshi ƙanin ƙafarshi. Kuma ko a yanzu, baiyi da na sanin sakin Zulai ba, domin har yanzu shi ba ya jin sonta a zuciyarsa.
Amma kuma irin gagarumin farin cikin da ya gani a fuskar iyayensa, lokacin da suka je Faƙo shi da Zulai, yasa shi ji a ransa lallai zai iya yarda a sake ɗaura mishi aure da ita su zauna a wani gida daban ba tare da sanin Bintu ba ko don ɗorewar faffaɗan farin cikin da ya gani a fuskar iyayensa.
Ko da Zulai bata tona asirin abinda ke faruwa ba, shi da kanshi zai bayyana abinda ke faruwa idan lokacin da ya tsara yayi, cikin hikima da iya magana ta yadda al'amuran baza su taɓarɓare haka ba.
Shi yanzu ta ina zai ɓullo ma wannan al'amari? Sai da yayi kwanaki huɗu a Kaduna kafin ya koma Abuja saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki, ya san ko ya koma Abuja Bintu, ɗansa, da gurin aikinsa da sauran abokan arziki baza su taɓa samun nutsuwarsa ba. A cikin kwanaki huɗun da yayi a Kaduna zuwanshi Faƙo sau biyu, ya koma Abuja a daddafe cike da damuwa yayi kwana uku sannan ya sake tafiya Faƙo, nan ma dai babu wani cigaba.
Gaba ɗaya iyayen sun ƙi sauraransa, duk yadda yake tunanin girman al'amarin ya wuce haka. Ko da yayi tunanin bi ta hannun Ƙannen Baffa su Baba Abubakar su ma gaba ɗaya sun ƙi masa hannu. Haka ma ƴan'uwan Innaye sun ƙi sauraransa.
A zuwansa na huɗu ne ya tara Aminan Baffa da waɗanda yasan Baffa yana jin maganarsu har da ƙwallarsa ya roƙi don Allah su shige mishi gaba wajen sasanta shi da iyayenshi.
Sun yi mishi faɗa sosai kamar za su ari baki. Shi dai kanshi yana ƙasa, sai haƙuri yake cigaba da bayarwa yana sharar ƙwallah, tunda matar na tuba ba ta rasa mijin aure.
A ƙarshe Mal Liman ya kira Baffa a waya ya roƙe shi alfarman ga su nan zuwa gidan, yana so zaiyi magana da su shi da Innaye. Baffa zai musa Mal Liman ya haɗa shi da Baba Lurwanu a wayar, a dole ya amince da ziyarar tasu.
Ko da ya gansu tafe da Hafizu baiyi wani mamaki ba, gaba ɗayansu suna zaune ne a falon Innaye saboda ya fi girma. Hankalin Hafiz bai ƙara tashi ba sai da yaga yadda Baffa da Innaye suka ƙara ramewa sosai a cikin kwanakin, kuma wani abu da ya lura shi ne sam ba sa ko ƙaunar kallonsa, a ɗazu, matso ƙwallar dole yai tayi a gaban su Mal Liman, a yanzu kuwa kukan na gaske yake yi.
Hankalinshi ba ƙaramin sake tashi yayi ba ganin duk irin nasiha da kyawawan kalaman da aka yi ta faɗa ma su Baffa sun ƙi cewa komai. Har dattijan suka gama duk maganganu da nasihar da za suyi, suna ƙoƙarin rufe taron da addu'a. Baffa bai ce komai ba, balle Innaye da tun ɗazu fuskarta ke lulluɓe cikin hijabi.
"Baffa, Innaye, don girman Allah ku yafe min. Na san na aikata kuskure mai girma a gare ku, bazan sake ba in Allah ya yarda. Kuma a shirye nake a sake ɗaura min aure da Zulai in riƙe ta..."
Da sauri Baffa ya katse shi da cewa
"Hafizu, a madadin Rahina zan ari bakinta in ci mata albasa. Mun yafe maka. Amma daga yanzu, zancen aure tsakaninka da Zulai ya haramta har abada, kar in sake jin ta daga bakinka. Ina fatan ka fahimce ni?"
"Na fahimta Baffa."
Ya amsa jikinsa a sanyaye.
Godiya Baffa yayi ma dattijan da Aminansa sannan Mal Liman ya rufe taron da addu'a. Bayan shafa fatiha suka fice daga ɗakin Hafiz ya bi su a baya yana ƙara yi musu godiya. Ko da ya koma cikin gidan, ya zaci ko ɗan kaɗan ne zai ga canji a fuskar Baffa da Innaye, sai yaga ba wani canji.
Bayan kashaidi mai girma da Baffa ya kora mishi cikin ɓacin rai akan kar ya kuskura ya sake tattaro mishi mutane kan matsalar da shi kaɗai ya jaza ma kanshi ficewa yayi daga falon Innaye yana jan ƙaramin tsaki.
Ita kuwa Innaye ko kallo bai isheta ba, miƙewa tayi daga falon ta fice tsakar gida, don ma kar ta shiga ɗaki ya ce zai bi ta da wani magiyarsa na banza da wofi. Ba komai yake ƙara ɓata mata rai da lamarin ba face idan ta tuna yadda Hafiz ɗin yayi wasa da hankalinta, tsawon watanni tana harhaɗa mishi tsaraba da abubuwa da yawa kan cewa ya kai ma Zulaikha ashe sam ba sa tare da juna.
Don tsabar ya raina ta har yana zuwa da matarsa tana ƙara jaddada mata lallai suna zaune lafiya da Zulai. In dai ɗan da ta haifa a cikinta zai iya yi mata irin wannan rainin wayau wanene ma a duniya bazai raina ta ba? Babu!
Tabbas ta yafe ma Hafizu kamar yadda Baffa ya nema, amma ba ta ji a ranta ko can gaba za ta iya sakewa da Hafizu ta yarda da shi kamar yadda suke a baya. Abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba.
Haka Hafiz ya ƙaraci zamansa a ɗakin ya fito yayi musu sallama ita da sauran matan gidan duk zuciyarsa a jagule. Fatan Allah ya kiyaye hanya suka yi masa ba wani walwala da ƙauna irin ta da a muryoyinsu ya fice yana jan ƙafafu.
Ko da yaja motarsa kamar zai kai ma Aunty Balira ziyara, amma sai ya tuna yadda suka rabu baram-baram a wancan zuwan nasa, da kukanta har tana mishi Allah ya isa kan ɗaukar haƙƙinta da yai tayi yana ce mata lafiya ƙalau suke zaune da Zulai.
Anty Ladidi da Anty Rakiya kuwa tun da suka haɗu a gidan Baffa ya gaishe su babu wacce ta amsa mishi ko kusa baiyi gigin zuwa gidajensu ba, ya san idan ya je duk munin abinda suka yi mishi shi ya siya da kuɗinsa.
Haka yabar garin Faƙo zuciyarsa cike da saƙe-saƙen sabbin hanyoyin da ya kamata ya bi don daidaitawa da iyaye da ƴan'uwansa.
"To Alhaji ina ga me zai hana tunda duk an fahimci juna a ɗaura auren kawai a wuce gurin?"
Da fara'a sosai a fuskar Abba Lurwanu, Kamal, Alhaji Musa suka ɗaga fuskokinsu suna kallon Baffah.
"Da gaske kake yi Malam Aminu?"
Abba Lurwanu ya jefa ma Baffa tambayar don kore tantama.
Ɗan muskutawa Baffa yayi, kafin ya kalli ƴan'uwansa uku da Yayyen Innaye biyu da Malam Liman da su ma fuskokinsu ke bayyana farin ciki da nutsuwa da jin kalaman bakinsa. Sai kuma ya sake mayar da hankalinsa kan su Abba Lurwanu.
"Ƙwarai kuwa. Da gaske nake yi. Tunda dai duk na faɗa maka muhimman abinda ya kamata ku sani dangane da Zulai, kuma kuka ce duk waɗannan ba matsala bane. Wanda ke da alhakin aurenta ya rantse min da girman Allah shi ko a matsayin bazawara take yana son ta a haka, kuma zai riƙe min ita tsakani da Allah. To me za'a jira?
Kuma don yin kitso da ƙwarƙwata a gabanku na kira yarinya na tambaye ta ta amince da auren Kamalu? Ta nuna kunya da murmushi wanda a gurinmu babbar alama ce ta amincewa.
Muhimmin abu kuma da fiyayyen halitta SAW ya umarcemu da yi kafin mu bada auren ƴaƴanmu shi ne bincike, kai da na yarda da kai ɗari bisa ɗari ka tabbatar min da nagarta da ingancin halayen wannan yaro. To me za'a jira bayan haka kuma? Ai ina ga kawai a ɗaura auren kafin ku tafi, ko zuwa nan da sati biyu ko uku sai ta tare a ɗakinta in sha Allah.
Saboda mu kanmu abun ya zo mana bagatatan ne, bamu shirya komai na aurenta ba..."
"Alhamdulillah! Ma sha Allah! Baffah na gode, na gode, Allah ya saka da alkhairi. Ubangiji ya ƙara lafiya da nisan kwana. Ni Wallahi auren Zulai ma da za'a bani a sauƙaƙe haka ya fiye min komai, ita ɗin kawai nake buƙata. Ba sai kun wahalar da kanku wajen siya mata komai ba."
Abban Imamu yayi maganganun da matsananciyar farin cikin da ya gaza ɓoyuwa a fuskarsa.
Ganin komai yake yi tamkar a mafarki. Sai ga shi cikin lokaci ƙanƙani Alhaji Musa ƙanin mahaifinsa ya zaro bandir na dubu ɗari daga Aljihunsa, Abba Lurwanu ya ƙara wata dubu ɗarin akai suka zama dubu ɗari biyu. Nan take aka miƙa ma Baba Abubakar a matsayin sadakin Zulaikha. Suka tashi daga zaman da cewa idan aka idar da sallar azahar sai a ɗaura auren, tunda a lokacin ƙarfe goma sha biyu da rabi ne na rana.
Ko da labarin halin da ake ciki ya iske Mummy Saudah da Hajja a cikin gida ɗakin Innaye zubewa kawai sukai goshinsu a ƙasa suna godiya ga Allah. Bayan sun miƙe tsaye kuma Hajja ta karkace kai ta riƙe hanci ta fara rangaɗa wata ƙaƙƙarfan guda kamar yarinyar mace.
Daga bisani kuma ta fara rera waƙa irin tasu ta mutanen da tana ƴan raye-raye. Innaye dai tun tana kawaici tana ɗan murmushi har ta sake ta fara dariya sosai. Cikin ƙanƙanin lokaci, ɗakin Innaye ya cika da abokan zamanta da yaran gida, matan maƙwafta suna yi mata Allah ya sanya alkhairi.
Mummy Saudah kuwa uwar ɗakin Innaye ta shige ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara latso lambar ƴan'uwa da abokan arzikinta tana faɗa musu za'a ɗaura auren Baban Imam yanzu da bayan sallar azahar.
"Haba Hajiya Saudah? Wani irin aure ne haka na bazata babu ko gayyata? Ko sadaka aka bashi?"
Kaɗan kenan daga cikin ire-iren tambayoyin da mutanenta suke mata suna mamakin al'amarin.
"Tsaleliyar yarinya ce ɗaya tamkar da miliyan. Ba sadakarta aka bashi ba, shi da kanshi ya gano ta ya nace yana so, da yake dai iyayenta dattijan ƙwarai ne shi yasa daga zuwa tambaya suka ce za'a ɗaura aure nan da sati biyu sai ayi biki."
Amsar da take basu kenan, da matsananciyar murna a muryarta.
Ko a wannan lokacin, sai da ta sake gwada kiran lambobin Hafiz amma gaba ɗaya basu shiga ba. Mamaki ne ya kamata, don ya saɓa daga cikin ɗabi'unsa haka kawai ya kashe waya tun daren jiya har wayewar garin yau ga shi ana neman a sake yini bata same shi ba.
Ko da yake ta wani ɓangaren rashin samunsa a wayar ma ya zame musu alkhairi. Domin rashin samun nasa don ya kwatanta musu hanyar da za su bi don su zo Faƙo su kawo ma Zulai ziyara bayan sati biyu da tafiyarta yasa ta nemi Alhaji Lurwanu a waya, tunda ta san irin zumuncin da ke tsakanin Alhajin da iyayen Hafiz ɗin.
Ita kuma Alhaji Lurwanu ya kasance Amini ne ga marigayi mijinta Babansu Kamal. Da yake ita ɗin ba mace ba ce mai ɓoye-ɓoye, kai tsaye ta faɗa ma Alhaji Lurwanu halin da ake ciki, da kuma a taƙaice abinda zai kai su ƙauyen shi ne gaisuwa da roƙon iri.
"Ai kuwa Hajiya Saudatu ina ga faɗuwa ce tazo daidai da zama. Dama akwai abinda zai kai ni Kaduna gobe, to kuma ina tunanin ƙarasawa har can ƙauyen in kai ma shi Malam Aminu ziyarar bazata, shi yasa ma ban faɗa mishi ba. Don haka ina ga goben kawai sai mu tafi gaba ɗaya. Amma kuma ba kya ganin ya dace mu tafi da Alhaji Musa? Ko don acan ɗin su ƙara sanin lallai fa da gaske Kamal yake ƙaunar yarinyar."
Abba Lurwanu ya ƙara mata da wannan shawarar.
Hangen nasarar da za'a ƙara cimmawa idan aka tafi da Alhaji Musan yasa bata ɓata lokaci ba wajen saka Kamal ya kira shi ya faɗa mishi halin da ake ciki. Daga bisani itama ta ƙara kiranshi a waya ta sanar da shi halin da ake ciki, ta kuma roƙi alfarmarsa na idan goben ba shi da muhimmin uzuri ya shirya su tafi tare.
Da yake tsakaninta da dangin mijin nata akwai kyakkyawar fahimta. Duk da yana da uzurin haka ya katse komai nashi ya shirya aka yi tafiyar da shi.
Ko da suka iso, irin kyakkyawar tarbar da suka samu daga su Baffa duk da ba'a san da zuwansu yasa ta ƙara ji a ranta lallai Kamalu yayi sa'ar mata da surukai. Ita ma bata mishi zaɓen tumun dare ba.
Duk da mamakin da tayi na jin labarin an taɓa ɗaura aure tsakanin Hafiz da Zulai abin bai ɓata ranta ba. Musamman da taji cewa duk zaman da Zulai tayi a gidanta a lokacin babu auren, ko kaɗan bata ƙullaci Hafiz ba balle Zulai.
Abinda ta ɗauka ma rabon ɗanta Kamal ne ya rantse shi yasa da Hafiz yake neman inda zai aje Zulai na ɗan lokaci gidanta ne kawai ya faɗo mishi arai. Yo menene a ciki don Hafiz ya saki Zulai ɗanta Kamal ya aura? Ai daman haka rayuwa take. Sai wani ya aje wani zai ɗauka, kuma sai wani ya rasa wani zai samu.
Ko yanzu da take sake kiranshi a waya ba komai take son yi mishi ba face godiya, sannan kuma ta bashi labarin duk irin halin da ake ciki. Kuma tayi mishi alƙawarin in Allah ya yarda kafin su bar ƙauyen ita da Abba Lurwanu za suyi iya ƙoƙarinsu wajen daidaita shi da iyayensa da suka lura ba ƙaramin fushi sukai da shi ba.
Sai a wannan lokacin, tunanin kiran Bintu don tambayar halin da Hafiz yake ciki ya faɗo mata arai. Ba tare
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 40