sani hankalinta ƙara tashi yake yi. Haka kawai ta ji ɗakin yana mata wani irin zafi, numfashinta ya fara fita a wahalce. Tsam ta yunƙura ta miƙe tsaye, duk da ranar ita ce da girki, ita ya kamata ta kwana a turaka, ta rasa dalilin da yasa bakinta ya furta ma Malam ɗin
"Allah ya bamu alkhairi. Sai da safe."
Da idanu kawai ya raka ta har ta fice daga ɗakin bai amsa mata ba.
"Uhmmm! Mata kenan"
Ya faɗa a fili, sai kuma ya saki murmushi.
Kawar da tunanin komai daga zuciyarsa yayi ya koma inda ya zube dabino da goro da sweet, ya cigaba da cakuɗawa yana zubawa a leda.
*****
Aka ce rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Washe gari, Kamar yadda Baffa ya faɗa ma Innaye, mintuna goma sha biyar da idar da sallar azahar sai ga ƴan samarin gidan da yara ƙananu sun shigo da sauri suna kwarmaton an ɗaura auren Zulai yanzunnan bayan an idar da sallar azahar.
Ɗaura auren da tunda ƙarfe goma na safe zuwa sha ɗaya tayi, Innaye ta fara tunanin ko dai Baffa da wasa yake mata? Duba da yadda cikin abokan zamanta biyu babu wacce tayi mata maganar auren, sannan cikin ƴaƴan Baffa mata takwas na ta da na kishiyoyinta da suke gidajen aure babu wacce ta je gidan da cewar ta je yinin biki.
Tsakanin Zulaikha da take cikin uwarɗaki ta idar da sallah, da Innaye da take zaune akan dadduma tana lazumi, na rasa wacce ta riga wata isa bakin ƙofar fita.
Kawai ganinsu aka yi duk su biyun tsaye a bakin ƙofa sun riƙen labule.
"Labaran? Me kuka ce?"
Innaye ta tambayi babba daga cikin yaran bakinta na rawa-rawa.
"Wallahi da gaske Innaye. Yanzunnan aka ɗaura auren Zulai da Yaya Hafizu..."
Wani wawan ƙaƙƙarfan mahaukacin ihu da Zulaikha ta yanka a firgice, sannan ta tafi da baya tai wani mugun kifawa a ƙasa shi ne abinda ya katse maganar da Labaran yake yi.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku na lalace... Auta...! Ke Auta... !! Me ya same ki? Zul..."
Luuuuu itama Innaye ta tafi za ta kifa a ƙasa saboda tsananin firgici da tashin hankalin halin da Zulaikha ta shiga, da saurin gaske Labaran da ya isa gurin tun faɗuwar Zulaikha ya riƙo Innaye ta kifa a jikinsa.
Cikin ƙasa da mintuna biyu, har labari ya kai kunnensu Baffa da ke zaune a masallacin ƙofar gida ana ta rabon Sweet da addu'ar Allah ya bada zaman lafiya cewa ga Innaye can da Zulai sun suma.
Duk cincirindon mutanen da suke gurin fuskokinsu cike da alhini saboda jin abinda yake faruwa, Baffa ne ya fara shiga cikin gidan don kiyaye hakkin addini. Sai da ya shiga, can bayan wasu mintuna kuma sai ya aika yara aka shiga da shaƙiƙan ƴan'uwansa da ƴan'uwan Innaye maza.
A lokacin tuni Innaye ta farfaɗo sanadiyyar ruwa da kishiyoyinta sukai ta sheƙa mata. Tana zaune a gefe sanye da zumbulelen hijabi tana sharɓan kuka. Ita kuwa Zulaikha har lokacin bata farfaɗo ba duk uban ruwan da aka watsa mata, sai dai an ɗauke ta daga bakin ƙofa an shimfiɗar da ita akan doguwar kujera.
Shigar ƴan'uwan Baffa da na Innaye cikin gidan yasa abokan zaman Innaye da yaran gidan suka yi saurin ficewa daga cikin ɗakin.
Ya zama saura Baffa ne zaune kusa da inda aka kwantar da Zulaikha yana tofa mata addu'o'i. Shigowarsu Baba Abubakar yasa Baffa ƙara gyara mata rufar hijabin da ke jikinta.
Har suka zaz-zauna, Innaye ta kasa ɗaga idanu ta kalli ko mutum ɗaya daga cikinsu, balle kuma har gaisuwa ya shiga tsakaninsu. Kukan da take yi ƙasa-ƙasa kuma bata daina ba.
"Haba Rahina? Saboda Allah menene haka kike yi kamar ƙaramar yarinya? Ni na zaci za ki fi kowa murna da wannan al'amarin saboda tuwon ki ne kuma man ki? Duk wannan kukan da kike yi har da su suma duk na menene?"
Yayan Innaye Mal Kabiru yayi maganar cikin faɗa-faɗa, saboda shi mutum ne mai zafin rai.
Innaye dai ba baka sai kunne, ta kasa ko ɗaga kai ta kalle shi balle yasa ran za ta amsa mishi.
"Assha! Assha! Yaya Rahina don girman Allah kiyi haƙuri. Wannan al'amarin fa duk ba wani abin damuwa bane kamar yadda kika ɗauke shi, tunda dai ke da kanki kin san ba haramun muka aikata ba. To menene abin tashin hankalin?"
Baba Abubakar ya faɗa a tausashe.
Shi ma dai bai samu amsa ba. Nan take kuma kowa a cikinsu ya fara tofa albarkacin bakinsa, suna sake tunatar da Innaye babu fa haramci a cikin auren Hafiz da Zulaikha tunda dai ba iyayensu ɗaya ba.
'Hafiz shi ne ɗan da Innaye ta haifa a cikinta. Zulaikha ƴa ce ɗaya tilo ga ƙanwar Innaye da kuma ƙanin Baffa mai suna Hamisu da suka kasance uwa ɗaya uba ɗaya.
Sun rasu ne sanadiyyar mummunar hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar komawa Faƙo daga Kaduna. Hatsarin da aka rasa rayuka da dama, Zulaikha tana cikin ɗaiɗaikun rayukan da suka tsira a wancan lokacin shekaranta ɗaya da wata biyu a duniya.
Tun daga sannan, riƙon Zulaikha ya koma hannun Innaye da Baffa. Yarinyar da ƙauna da shaƙuwar da ke tsakanin iyayenta da su Innaye yasa suke mata wani irin so na musamman kamar ma fiye da ƴaƴan da suka haifa a cikinsu.
Duk da bata isa yaye ba a lokacin, yaye ta aka yi tunda tana tafiya. Kuma inda Allah ya sauƙaƙa lamarin shi ne tana cin abinci sosai. Sannan tun iyayenta na raye tana yawan yini a gurin Innaye, ta saba da su gaba ɗaya.
Ƴaƴan da Innaye ta haiha huɗu ne a duniya, Balira ita ce Babba, kuma duk cikin ƴaƴan Baffa ma ita aka fara haifa. Sannan Rakiya, sai Ladidi, Abdul Hafiz wanda daga bisani aka yanke sunan ya koma Hafizu shi ne Auta, kuma shi ne ɗa Namiji na farko da aka fara haifa a gidan Baffa.
A lokacin da riƙon Zulaikha ya koma hannun Innaye Hafiz yana da shekaru goma sha ɗaya a duniya. Amma kamar ɗan shekara biyu zuwa uku, haka iyayen suke lelensa suna shagwaɓa shi saboda tsananin ƙaunar da suke masa.
Zuwan Zulaikha gidan shi ya hamɓare gwamnatinshi daga gurin Innaye da Baffa. Kulawa, tattali, shagwaɓa, lelen da ake masa duk suka koma kan Zulaikha. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da wata rana Innaye ta rufe ido tayi mishi matsiyacin duka saboda kawai ya mari Zulaikha. Bayan dawowar Baffa kuma Innaye ta faɗa masa abinda Hafiz ɗin yayi, cikin ɓacin rai ya rama ma Zulaikha marin sannan ya rufe shi da faɗa kamar zai dake shi.
Wannan shi ne mafarin ƙulluwar ƴar tsama tsakaninshi da Zulai. Wacce ita kuma tun da ta fara wayau ta lura ba ya ƙaunarta ta masifar raina shi, a lokacin ita bata san ma ba Innaye bace ta haife ta.
[1/10, 10:29 PM] Fareeda Abdallah: Wata rana, a lokacin Zulaikha bata fi shekaru shida ba a duniya, cikin suɓul da baka Hafiz ya goranta ma Zulaikha Baffa da Innaye ba iyayenta bane.
"Duk son da suke gwada miki da iskancin da kike yi suna goya miki baya na banza ne. Watan-wata rana za ki gane kuranki yarinya, tunda dai iyayenki ba sa raye."
Karaf! Maganganunnan a kunnen Baffa, ran Baffa ta yi mummunar ɓacin da bai taɓa yi ba. Bayan mugun dukan da ya lakaɗa ma Hafizu kamar ba shi ya haifeshi ba, sai da ya tara iyalanshi kaf! Yara da manya ya kafa musu dokar cewa duk wanda ya sake goranta ma Zulai ba su ne iyayenta ba bai yafe mishi ba.
Wannan shi ne mafarin da yasa zancen ba Innaye da Baffa bane iyayen Zulaikha ya ɓace ɓat a gidan. Ta cigaba da zuba sangarta da shagwaɓarta yadda take so, Innaye tana kiranta Auta. Kuma saboda ƙaƙƙarfan dangantaka da ke tsakanin su Innaye da Iyayen Zulaikha babu wanda zai ganta ya ce ba Innaye bace ta haife ta.
Hafizu kuma wannan laifin da yayi shi ne dalilin da yasa Baffa ya ɗauke shi can-cak daga ƙauyen Faƙo, ya kai shi wani ƙauye mai suna Kasuwar magani gurin wani abokinshi, da niyyar yayi karatun Allo. Ashe rabon yayi zurfi a karatun boko ne.
Kasancewar ƙauyen Kasuwar magani ta fi ƙauyen Faƙo wayewa nesa ba kusa ba. Akwai makarantun boko har zuwa sakandire, saɓanin Faƙo da makarantar boko iya firamare ne, a hakan ma ba ko wasu iyaye ke saka ƴaƴansu ba. A kasuwar magani kuwa ga makarantun islamiya da makarantun hadda masu kyau babu laifi. Ko da Mal Bello ya tambayi Hafizu yana sha'awar karatun boko ya ce eh! Har ma ya ƙara da faɗa mishi ya gama firamare acan Faƙo, Sai kawai ya saka shi a Sakandire da makarantar Islamiya da hadda, ba tare da sanin Mal Aminu ba. Wannan shi ne mafarin samun ingantaccen karatun Hafizu.
Kasancewarsa yaro mai tsananin ƙoƙari ako wane fanni, ga nacin karatu, yana aji biyu na ƙaramar sakandire malamai suka saka shi za na ƙaramar jarabawa ta zuwa babbar sakandire. Yana aji biyar na babbar sakandire Principal ya saka sunanshi cikin ɗalibai masu zana jarabawar WAEC da NECO saboda ƙoƙarinsa.
A wancan lokacin, karatu a ƙauyuka kusan kyauta ake yi, saboda iyaye basu gama yarda da bokon ba balle har su saki jiki suyi tururuwar kai ƴaƴansu.
Bayan sakamako ya fita ne sunanshi ya fito cikin waɗanda suke da maki mai yawa, anan ma dai principal ɗin shi yayi cuku-cuku ya jefa sunan Hafizu cikin ɗaliban da gwamnati ta ɗauki nauyin karatunsu zuwa jami'ar Ahmadu Bello da ke zariya.
Acan ne kuma Allah ya haɗa shi da Ibrahim ɗan gidan Alh Lurwanu, taraiya ce irinta ɗan gidan talaka futuk mai bala'in ƙoƙari da ɗan gidan mai kuɗi mare ƙoƙari amma akwai nacin karatu. Aka samu arashi kuma shi Ibrahim ba shi da girman kai ko kaɗan, a taƙaice ma shi ne ya maƙale ma Hafiz ɗin saboda ilimin da yake kwasa daga gare shi.
A can ƙauyen Faƙo kuwa, tafiya ta tafi, an samu cigaba kaɗan amma ba sosai ba. Sanin kowa ne ire-iren waɗannan ƙananun ƙauyuka da suke cikin lunguna sosai ba kasafai cigaban gwamnati ya cika samunsu ba, sai ɗan abinda Allah ya tsaga da rabonsu kawai.
Sun samu cigaba ta fannin makaranta, an gina musu sakandire, amma fa irinta je ka na yi ka. Domin ko malaman da aka zuba musu ma ba kasafai suke zuwa aikinsu ba saboda nisan ƙauyen.
An kai musu Network ɗin Glo a ƙauyen. Sannan an gina musu ƙaton asibiti amma fa babu wasu likitoci da ma'aikatan jinya sai ɗai-ɗai.
Zulaikha Aminu Faƙo, tana ɗaya daga cikin yaran da suka nace ma iyayensu bayan gama karatun firamare aka jefa musu a makarantar sakandire da ke ƙauyen. Tafi-tafi za tayi karatun baza tayi ba har Allah yasa ta kai aji biyar na babbar sakandire sai kuma ta watsar da karatun. Saboda a lokacin duk ajinsu babu ƴa mace mai shekarunta, ƴan matan ƙauyen da sun fara aji ɗaya, biyu, na ƙaramar sakandire suke watsar da karatun ayi musu aure.
Ita kuwa da ta kai aji biyar na makarantar sakandire har wani kallo take yiwa kanta matsayin babbar yarinya. Duk da abinda ta tsira da shi a karatun bokon kawai hausa ne ta iya karantawa gar-gar, turanci kam ƙananun kalmomi kawai ta sani sai kuma ƴan abinda baza'a rasa ba na yaƙi da jahilci.
A bakin mutanen gari Zulaikha ta san ba su Innaye bane iyayenta, a lokacin ta kai shekaru goma sha biyar a duniya. A wannan ranar tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai fita, daga ƙarshe zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe ta. Kuma sam ta kasa faɗa ma Innaye dalilin kuka da zazzaɓin da take yi, a ganinta idan ta nuna musu ta san ba su ne iyayenta ba duk da irin wannan ƙoƙarin da suke yi a kanta bata yi musu halacci ba.
Daƙyar ta iya yakice maganar a ranta ta kwantar da hankalinta, ta cigaba da yima iyayenta addu'a a ɓoye, ganin yadda Innaye da Baffa ke ta jelar kai ta asibiti ana yi mata allurai da bata magunguna kala daban-daban. Ƴan'uwanta da suke gidan aure na ta zirga-zirgar zuwa gaishe ta.
A lokacin ana gaf da yin bikin Hafizu. Ya gama karatu tuni, mahaifin abokinshi Ibrahim shi ya sama mishi babban aiki a Abuja saboda tsananin kyawun sakamakon karatunsa. Kuma cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya tarfawa garinsa nono ya tara dukiya mai yawa, a hakanma don yana taimaka ma iyaye da ƴan'uwansa da mutanen ƙwauyensu. Hatta iyalin marigayi Mal Bello da ya zama sanadiyyar cigaba da karatunsa yana taimaka musu matuƙa gaya.'
Daɗaɗɗen buri ne a zuciyar Baffa tun da yaga yadda Hafizu ke samun manyan kuɗaɗe, da kuma yadda yaga hankalin Hafiz ɗin sam ba shi akan zama a ƙauyen ko misƙala zarratin, yaso Hafizun ya duba a cikin ƴaƴan ƴan'uwa ko na mutanen gari ya zaɓi mata a cikinsu.
Ta yadda duk cigaban da zai taka a duniya shi da matarsa dai tushensu ɗaya. Kuma matarsa baza ta taɓa gudun ƴan'uwansa ko kuma ta wulaƙantasu ba tunda dai garinsu ɗaya kuma ita ma ƴan'uwanta ne. Amma kafin ya kai ga furta wannan ƙuduri nashi ga Innaye ko Hafizu kawai sai ga zancen zuwa neman auren Bintu Hafiz ya zo musu da shi.
"Mahaifinta abokin Abba Lurwanu ne na kurkusa. Ya san komai a kan yarinyar da iyayenta, tare muka yi karatu da ita a Zaria. Amma saboda ita karatun Likita take yi shi yasa har muka gama ita bata gama ba. Amma yanzu ta gama har ta fara aiki, shi yasa iyayenta suka ce ta fitar da mijin aure. Za ka iya kiran Abba Lurwanu yayi maka cikakken ƙarin bayani Baffa."
Sako sunan Abba Lurwanu matsayin abokin mahaifin Bintu ya katse ma Baffa duk wani hanzari. Domin Abba Lurwanu ya taka gaggarumin rawa a rayuwar Hafizu ta yadda bazai taɓa iya watsa mishi ƙasa a ido ba in dai shi ɗan halak ne.
Haka nan ya watsar da burinshi. Kafin ma shi Baffa ya kira Abba Lurwanu shi Abban ne ya kira shi, cikin girmamawa da mutuntawa yayi masa bayanin duk halin da ake ciki game da yarinyar da Hafiz yake so.
A ƙarshe ya ƙara da cewa
"To amma ya ka gani Baffa? Domin na faɗa ma Hafiz duk matakin da ka yanke shi ne ƙarshe, ni da shi duk umarninka ne abun bi a gare mu."
Wannan wuƙa da nama da Abba ya miƙa ma Baffa yasa a kunyace ya nuna amincewa. Sannan ya ƙara da sallama ma Abba komai na hidimar bikin Hafizu, kama daga walittaka da komai da ake buƙatar uba mahaifi ya bar ma Abba. Godiya sosai Abba yayi da matuƙar farin ciki a muryarsa kafin suka yi sallama da Baffa.
Tun da aka yi bikin Bintu, ire-iren abubuwan da suke biyo baya na daga irin ɗabi'un da take nunawa idan ta je ƙauyen duk Baffa yana gani. Amma saboda dattako sai yake kawar da kai, kuma daga ɓangaren Innaye bata taɓa masa ƙorafi ba.
Irin ƙorafin da Yayyen Hafizun suke yi ma idan suka je gidan acan Abuja duk yana ji. Rakiya a cikin ƴaƴansa ta kasance ba ta da rufi, ko a waya ya kira ta cikin hikima ya tambayeta halin da gidan ɗan nasa ke ciki ba ta ɓoye masa komai.
Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da Innaye ta je jinya gidan Hafizu, abubuwan da suka biyo baya sun ɗaga masa hankali ba kaɗan ba. Amma saboda kar ya raba zumuncin da ke tsakanin ƴaƴanshi yasa yayi saurin kashe maganar, tunda ya lura ƙarara har yanzu Hafiz bai fara ganin laifin Bintu ba. Matsananciyar soyayyar da yake mata yasa a kullum alkhairanta kawai yake kallo.
Zuwan da suka yi barka gidan, yasa jikinsa ya ƙara yin sanyi. Duk irin naɗe tabarmar kunyar da Bintu tayi yana sane, ai wawa ba mahaukaci bane. Da wannan dalilin yasa da gangar ya tura mata da yara zuwa suna duk don dai ya ƙara gwada hankalin Bintun.
Bayan dawowarsu suna da irin labarin da ya samu daga bakin Rakiya da sauran ƴaƴansa yasa shi yanke tsammani akan Bintu. Ƙarara ya gane manufarta na ƙoƙarin janye Hafiz daga gare su iyayensa da ƴan'uwansa, idan kuma hakan bai samu mata ba, babban burinta shi ne duk wani dangin Hafiz ya daina zuwa inda suke acan Habuja. Wannan kuma abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba, da wannan dalilin yasa shi yin amfani da karin maganar nan ta malam bahaushe da yake cewa
"Ranar na ka sai na ka."
Duk cikin ƴaƴan dangi ya duba kaf bai ga wacce zai aura ma Hafizu ta samu dama-dama idan ba Zulaikha ba.
Duk da kwanciyar da al'amarin yayi a zuciyarsa, baiyi gaggawar aikatawa ba sai da ya ɗauki kwanaki yana Istikhara. Kuma cikin hukuncin Allah lamarin sai ƙara kwanciya yake yi a zuciyarsa.
Ko da ya tunkari ƴan'uwansa da maganar haɗa auren, yayi matuƙar mamaki da yaga sun goya mishi baya. Ta ɓangaren dangin Innaye kuwa su ma addu'ar fatan alkhairi kawai suke yi.
Ya riga ya sani, idan da inda zai samu tasgaro daga Innaye ne, shi yasa ko da suɓul da baka baiyi gangancin sanar da ita wanda zai aura ma Zulaikha ba. Ita kuwa Zulai duk haukar da za tayi za ta gama, aure ne an ɗaura kuma in Allah ya yarda mutu ka raba.
Shi kuwa mai gayya mai aiki Hafizu duk da bai sanar da shi halin da ake ciki ba a wannan karon ya sha alwashin nuna mishi lallai fa da kai da kaya duk mallakar wuya ne.'
Nannauyar ajiyar zuciya Baffa yaja ya sauke, ya cigaba da kallo da sauraren ƴan'uwansa da na Innaye da suke ta mata maganganu na kwantar da hankali, suna ƙara nuna mata idan fa tayi haƙuri, kuma ta kwantar da hankalinta, lallai aure tsakanin Zulai da Hafizu alkhairi ne. Amma har lokacin ta tafasa sauke bata ce musu ba, sannan bata daina sharar hawaye ba.
"Assalamu alaikum"
Sallamar da Hafiz yayi da nutsattsiyar murya yasa duk mazauna ɗakin suka mayar da hankalinsu da idanuwansu kan ƙofar, kafin suka amsa sallamarsa.
[1/11, 6:51 AM] Fareeda Abdallah: Hafiz na shiga cikin falon, Innaye tayi gaggawar miƙewa tana tangaɗi ta shige cikin uwar ɗakinta. Wasu sabbin hawaye suna sake ɓalle mata, zuciyarta cike taf da tausayin Autarta.
Allah ya sani, wannan lamari ko kusa bata yi murna da shi ba. Da ace Baffa yayi shawara da ita tun farko, Wallahi baza ta taɓa goya masa ba. Kuma ko a yanzu da tana da ikon tilasta Hafizu ba tare da zuciyar Baffa ta yi baƙi ba a take za ta sa ya saki Zulaikha.
A ganinta, zaman Zulaikha a yanzu babu aure har zuwa sadda wani mijin zai bayyana ya fi gaggawar aura mata Hafiz da aka yi. A ture ma batun Hafiz da ko kusa ba ya ƙaunar Zulaikha tun tana ƴar ƙarama. Bintu? Bintu fa? Bintun nan da ta kasance azzaluma kuma makirar da take ƙoƙarin bin duk hanyar da ta san za ta raba Hafiz da iyaye da ƴan'uwansa? Ita fa Malam ya ɗauki Zulai haihuwar ƙauye rainon ƙauye girman ƙauye ya miƙa ma Bintu ita a matsayin kishiya.
Tun daga zuwanta jinya gidan Hafizu, da irin abubuwan da suka biyo baya, ta yanke tsammanin Bintu za ta ƙaunace su. Shi yasa ko da ta samu labarin abinda ya faru ga masu zuwa suna ta bakin Balira bata yi wani mamaki ba. Ta san in dai Bintu ce za ta aikata fiye da haka.
Ita yanzu ta wace hanya za ta bi ta dakatar da wannan mummunan al'amari???
A falo kuwa, daga kallon fuskar Hafiz za'a fahimci irin mamakin da zuciyarsa ta shiga na ganin taron dangi haka a falon mahaifiyarsa. Amma sai bakinsa bai furta ba, ya durƙusa a ladabce, ya bi su da gaisuwa ɗaya bayan ɗaya har zuwa kan Baffansa.
"Hafizu an samu ƙarasowa? Barka da sauka. Ya hanya?"
Baffa yayi maganganun idanunsa cikin na Hafiz.
Saukar da idanunsa ƙasa yayi daga kan Zulaikha da yake kallo zuciyarsa cike taf da mamakin barcin banza da wofi haka da take yi ƙatuwarta da ita a cikin Babanninsu. Lallai da a kusa da ita ya zauna, babu abinda zai hana shi fakaitar idanun mazauna falon ya manna mata wani zazzafan tsungule da zaiyi sanadiyyar tashinta a firgice.
"Eh! Na ƙaraso Baffa. Ayi haƙuri da jinkirin amsa kiran da nayi, hakan ya faru ne bisa dalilin manyan baƙi da muke da su a gurin aiki. Sai da muka sallame su sannan na kamo hanyar tahowa..."
"Ai babu komai. Tunda dai ka iso lafiya Alhamdulillahi. Leƙa nan Chemis ɗin Habu idan yana nan yazo ya duba min Zulai, sumewa tayi. Tun ɗazu ake yayyafa mata ruwa har yanzu bata farfaɗo ba..."
"Subhanallahi! Suma kuma Baffa?"
Yayi tambayar da ɗan damuwa a fuskarsa.
"Me yake damunta haka? Wani mummunan abu ne ya faru da ita har ya jefa ta cikin halin suma?"
Ya ƙara jera ma Baffa tambayoyin tun kafin ya samu amsar tambayar farko.
Sai kuma ya miƙe zumbur! Ya fice daga falon, tunawa da yayi duk minti ɗaya da zai ƙara a falon fa hankalinta na ƙara nisa ne. Gara ya taho da Habun idan aka samu nasarar farfaɗo da ita sai ya samu amsar tambayoyinsa a nutse.
Jim kaɗan bayan minti goma suka shiga cikin gidan shi da Habubakar. A lokacin, duk Babanni da Kawunnansa da suke cikin falon sun watse. Baffa ne shi kaɗai, zaune kan kujerar da ke kusa da wanda Zulaikha ke kwance da casbaha a hannunsa yana ja.
****** ******
"Aure kuma Baffa?"
Yayi tambayar hankalinsa a tashe. A zaune yake a ƙasa. Amma tsananin tashin hankalin yadda zancen auren ya duke shi bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba. Da rawar murya ya sake cewa
"Kuma Auren ma a rasa wacce za'a aura min sai Zulai? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!"
Taga-taga yayi kamar zai faɗi da saurin gaske ya zauna akan kujerar kusa da wacce Baffa ke zaune a kanta.
Amma tsabar tashin hankali bai ma san abinda ya aikata ba. Hannayensa biyu na rawa ya ɗaga ya kamo hannayen Baffa ya riƙe a cikin nasa
"A'a Baffa! Don girman Allah kayi haƙuri... idan ma wasa kake min ka daina. Na rantse da Allah zuciyata gaf take da bugawa. Taɓa ka ji yadda bugunta ya ƙara matsanancin sauri saboda tashin hankalin da wannan wasan ya jefa ni a ciki."
Da saurin gaske, yaja hannun Baffa ya cusa a cikin rigarsa ya taɓa dai-dai saitin zuciyarsa.
"Ka ji ko Baffa? Don Allah ka daina min irin wannan wasan. Irin wasan nan ne fa ko a musulunce ma ba shi da kyau..."
"Ba da wasa nake yi maka ba Hafizu. Lallai da gaske yau na ɗaura aure tsakanin kai da Zulaikha. Idan kuma ban isa bane, sai ka ɗauki duk matakin da kake so."
Tsam! Baffa ya miƙe tsaye, ya karɓe hannayensa daga na Hafizu. Sannan ya fice daga cikin ɗakin.
A kunnensa ya ji Hafizu yana jan
"Laahaula walaa ƙuwwata illah billahil-aleeyul-azeem"
******
Tun da aka samu nasarar farfaɗowarta, ta kifa fuskarta a cinyar Innaye da take riƙe da ita, babu abinda take yi sai rusa kuka kamar za ta haɗiyi zuciya ta mace.
Ita ma Innaye kukan take yi, tsakanin ita da Zulaikha an rasa wanda zai fara cewa komai.
Baffa ne ya ɗaga labulen falon da siririyar sallama a bakinsa, fuskar nan tasa a murtuke tamau, babu sauƙi ko kaɗan. Tun da Innaye ta ɗaga kai ta kalle shi sau ɗaya bata sake marmarin kallonsa ba.
"Idan kun gama kukan, ki haɗa mata duk kayayyakinta, domin gobe idan Allah ya kaimu za ta bi mijinta. In yaso daga baya idan ta kwantar da hankalinta ƴan'uwanta sa bi ta da sauran kayayyakin da aka tanadar mata..."
A fiegice Zulaikha ta miƙe zaune tana kallon Baffa. Ta buɗe baki za ta yanka ihu ya daka mata wani gigitaccen tsawan da yasa ba shiri ta haɗiye kukanta.
"Idan na sake jin ihunki a gidannan, na rantse da Allah sai na baki mamakin da baki taɓa tsammani ba."
Da mazarin jiki kuma a tsorace ta ruƙunƙume Innaye tare da cusa fuskarta a jikinta tana sauke ajiyar zuciya sauri-sauri.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 40