Share this page
mita da son maimaita magana ɗaya. makullin motarsa da yake ajiye nan kusa da shi ya ɗauka ya fice daga falon. ***** ***** A cikin kwanaki goma sha biyu da suka biyo baya, Baffa ya sa an gama shirya ma Zulaikha ɗakunanta da ke ɓangaren Kamal da kayayyaki na gani a faɗa cikin rufin asiri. Duk kuwa da yadda Abban Imam ɗin yace baya buƙatar komai, sam-sam Baffa ya ƙi yarda da haka. Kuma wani abin sha'awa da burgewa shi ne kayayyaki kalar ƴan birni aka zuba mata, dai-dai ruwa dai-dai tsaki. Wani kyawun hange da Baffa yayi shi ne, bai tura ƴaƴansa Kaduna suyi siyayya ba don gudun kar a sayi abinda bazai dace da ɗakunan Zulai a Abuja ba. Alfarmar Abba Lurwanu ya nema, ya tura mishi da kuɗi naira na gugan naira har miliyan ɗaya da cewa matar Abba ta shiga kasuwa ta sayi duk abinda ya dace, Duk da Abban yayi-yayi Baffa yabar kuɗinsa shi zai ma Zulai komai na kayan ɗaki matsayinsa shi ma na uba, amma Baffa ya ce yayi haƙuri, ɗawainiyar da yake da ɓangaren Hafizu da su iyayensa ma ya isa haka. Ko da Hafiz ya samu labarin halin da ake ciki hankalinsa a tashe ya kira Baffa. Domin a saninsa tun da ya fara aiki shi ke da alhakin yima ko wacce daga cikin ƙannenshi kayan ɗaki, kuma ko Zulai in banda Allah baiyi aurenta da Mudan ba a wancan lokacin har kuɗin kayan ɗakinta ya biya, fasa auren da aka yi ne yasa shi karɓan kuɗinsa. Ko da ya gama roƙon Baffa cikin ƙanƙan da kai da taushin murya kan a barshi ya ɗauki ragamar shirya mata ɗaki kamar sauran ƴan'uwansa ƙarara Baffa ya faɗa mishi ya fi so yayi ma Zulai komai da guminsa. "Ba kuma don wai na raina ƙoƙarinka bane Hafizu, ko kuma wai don har yanzu ina jin haushin abinda kayi, a'a! Ko ɗaya ba haka bane." Baffa ya ƙara da faɗa mishi haka don kwantar masa da hankali. Ɗan shiru yayi yana jin babu daɗi a zuciyarsa. Sai kuma ya ce "To Baffa don Allah a barni in ɗauki ragamar yi mata gara, tunda dai hidindimun da yawa. Don Allah Baffa." Kamar Baffa zai ce a'a! Sai kuma ya ce ba damuwa. Yana iya yin ɗan daidai misali ba na ƙarya ba. Sai dai abinda Baffa bai sani ba shi ne, kuɗin da ya bayar na kayan ɗakin da za'a siya mata kaso ɗaya ne bisa uku na abinda aka kashe. Abba Lurwanu ne ya cika kuɗin, matansa suka shiga kasuwa aka yi mata siyayyar kaya masu kyau. Bayan an kai kayan gidanta kuma washe gari suka je da manyan ƴaƴansu mata aka ƙarasa shirya mata gidanta. Yayi kyau sosai. Duk da Baffa ya gargaɗi Hafizu kan kayan gara bai ji ba, kuɗi ya kashe sosai duk don dai ya fanshe takaicin kayan ɗakin da bai mata ba. Ana jibi biki, su Aunty Balira suka yi shatar mota aka loda musu cincin, dubulan, alkaki, nakiya, manshanu, da sauran ƙananun tarkace daga Innaye suka tafi da shi gidan Zulai. Tarba ta mutunci da girmamawa suka samu daga Mummy da mutanenta. Zukatansu cike da farin ciki, sun ci, sun sha, sun yi nak da ƙayataccen abinci na girma. Haka suka dinga santin ɓangaren Zulai da kayan da aka zuba mata. Kayan ciye-ciyen da suka je da su daman tun daga Faƙo Innaye ta sa an raba komai kashi huɗu ne. Biyu na Mummy, ɗaya na Zulai, ɗaya na Hajja. Haka su Mummy suka karɓi kayan suna murna, zuciyarsu da fuskarsu ɗauke da bayyanannen farin ciki, kamar anyi musu kyautar duniya. Sha tara ta arziki aka haɗa sake haɗa ma su Aunty Balira a matsayin tukeuici suka juya da shi. Washe gari kuma ana gobe tarewa Mummy ta haɗa manyan mata guda shida, danginta biyu, dangin Abban Imamu biyu, ƙawayenta biyu, suka hau jirgi zuwa Kaduna, daga can suka ɗauki mota da haɗaɗɗun akwatunan lefe guda shida zuwa Faƙo, shaƙe da haɗaɗɗun kayayyaki. A ɓangaren su Innaye ma sunyi musu tarba daidai ƙarfinsu, haka aka rabu zukatan ko wane ɓangare da farin ciki, babu raini ko wulaƙanci balle kallon banza daga mutanen Mummy har suka bar Faƙo. Farin cikin wannan kaɗai ya ishi Innaye da sauran dangi. "Wani hanin ga Allah baiwa ne. Ke kam Zulai kin dace da miji da iyayensa, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba." Ire-iren maganganun da ke fita daga bakunan ƴan'uwa da abokan arziki kenan. Tun ana gobe biki, gidan Baffa yake danƙam da mata, sai sauke girke-girke ake yi ana ɗora wasu tukwanen. Washe gari kuwa tun ƙarfe goma na safe manyan motocin ɗaukar amarya da danginta har motoci takwas suka faka a ƙofar gidan Baffa. Kuma basu takura kowa ba, domin umarni ne daga Abban Imam, har zuwa ƙarfe uku na rana kafin aka gama shirya amarya da ƴan rakiyarta suka kama hanyar tafiya Abuja. [4/2, 6:12 AM] Fareeda Abdallah: ****** Cikin ƙanƙanin lokaci nan da nan sai gasu a cikin Abuja, wajen karfe shida da rabi na yamma. Tafiyar da ko kaɗan Amarya da tagawarta basu ga nisan ta ba. Fuskar Amarya wasai, sai ƴan ƙananun ƙwallan da tayi na sake rabuwa da su Innaye a karo na biyu. Amma babu irin kururuwar nan ko ƙuncin zuciya mai bayyana ƙarara auren dole aka mata, tana cikin farin cikin albarkar da su Baffa sukai ta sa mata. A gefe da gefenta kuma ga Yayyunta da za su raka ta har ɗakin mijinta. Bayan sun iso kai tsaye gidan Mummy Sauda aka wuce da ita, kamar yadda aka tsara sai an gama duk bukukuwan a gidan sannan za a wuce da ita gidan mijinta. A wannan sha'anin ne su Aunty Rakiya suka ƙara tabbatar da lallai fa ƴan birni masu kuɗin ma suna suka tara, ba ko wasu masu arziki ne masu wulaƙanta ƴan ƙauye irin Bintu ba. A bikin Zulai, kwanaki biyun da suka yi a Abuja gidan Mummy komai za'ayi ana saka su gaba-gaba matsayinsu na dangin Amarya. Duk wani shagali da aka yi sai da aka kai su gurin kuma a masauki na musamman. A taiƙaice dai, an girmama su iya girmamawa. Wani abin mamaki shi ne har aka gama bikinnan na kwana biyu Bintu ko leƙe bata yi ba, tana can gida ta ɗora ma kanta ciwon ƙarya har da su ƙarin ruwa don kawai kar Hafiz ya ƙullace ta. Shi kaɗai yayi ta zirga-zirgan zuwa gurin ƴan'uwansa. Ko da ya faɗa musu Bintu ba lafiya, fatan samun sauƙi kaɗai suka yi mata suka shashantar da maganar. Wani abu da ya sosa zuciyar Hafiz amma ya danne bai musu ƙorafi ba shi ne, yadda ganin yawan waɗanda suka zo bikin daga can ƙauye yasa shi suɓutar bakin yi musu tayin ya rage wasu suje gidanshi su kwana. "Wa? Mu? Allah suturi buƙwui... Ai gidan Bintu shi ne ramin kura sai ƴaƴanta... Idan ka ganmu lahira kaimu aka yi Hafizu. Ai ko sha'ani ake yi a gidanka mun daina zuwa mu kwana Hafizu." Ire-iren maganganun da ƴan'uwansa sukai ta yaɓa mishi kenan. "Uhmmm! Hafizu kenan. Ai kai da kanka ka ture wannan damar da aka miƙa maka na zuwan ƴan'uwa gidanka su sake. Ban san dai ko can gaba ba, amma a yanzu ko sha'ani ake a gidanka sai dai muyi maka fatan alheri ta waya, babu wacce za tayi gigin zuwa balle har ta ƙunshi takaici da baƙincikin da ba shi kenan ba." Cewar Aunty Balira. "Yo wai ko da ka ganmu da yawa aka ce maka muna takure ne anan ɗin? Ai surukan Zulai sai dai muyi musu fatan alkhairi, wadataccen gurin kwanciya suka samar mana da wadataccen abinci, kai baka ga har wani kumari muka ƙara a cikin kwana guda da zuwanmu ba? Mun gode Allah a yanzu ba kai kaɗai bane a binni, ga gidan Zulai nan, na san ko za mu zo muzo gobe jibi mu sake zuwa baza ta taɓa gajiya da mu ba. Ai ranar naka sai naka." Aunty Rakiya ta yaɓa mishi maganganun. Haka ya fice daga gidan zuciya cike da ƙunci amma ba shi da halin tofawa balle har cibi ya zama ƙari. Sai kuma a wannan lokacin ne ya fara tunanin to ko dai Bintu tayi ma ƴan'uwanshi wani wulaƙanci ne lokacin sunan Aadil? Idan ba haka ba waɗannan baƙaƙen maganganun duk na menene? A ganinsa guje ma auren Zulai kaɗai bazai sa su dinga nuna tsangwamar zuwa gidanshi ƙarara haka ba. Su dai ko a jikinsu, bayan fitarsa ma walwala da warwasawarsu suka cigaba da yi. Washe gari da wuri Mummy tasa Hibba ta sake tsantsara ma Amarya rantsattsiyar kwalliya aka ɗauketa da danginta sai gidan mijinta da ke unguwar Aso rock. Ƴan'uwanta sai hangame baki suke yi cikin tsananin ƙauyanci da mamaki suna ƙarewa gidan kallo. Tun daga farkon unguwar za'a gane ba ta ƙananun masu kuɗi bane. Tsarin gidan na musamman ne. Madaidaici ne zaman mace ɗaya da iyalanta da tarkacen da ba za a rasa ba. Ya so ƙwarai ya sake zama acan ɓangarenshi da ke gidan Mummy, kamar yadda suka zauna da marigayiya matarsa. Amma shi kanshi ya rasa dalilin da yasa Mummy ta ce su zauna a sabon gidan nashi da ba'a daɗe da kammala komai ba. Sai dai can ɗin ma yana nan a matsayin nashi, an ƙara gyarawa an zuba sabbin kayayyaki, da yake shi ɗin mai yawan tafiye-tafiye ne sai Mummy ta ce idan zaiyi tafiya Zulai za ta dinga komawa can gidan tana zama kafin ya dawo ƙasar. Tsarin gidan Amarya Zulai idan aka shiga falo babba za a fara tararwa, wanda aka tsara shi da tsadaddun funitures, daga can jikin bango kuma wata ƙatuwar TV stand ce wadda ita ginata ma aka yi kuma aka kafe wata ƙatuwar TV plasma dake barazanar cinye bangon saboda girma. A gefe da gefe kuma ga wasu tsadaddun show glass waɗanda aka ƙawata cikinsu da kayan ado da hasken wuta mai sheƙi. Acan wani ɓangare na falon kicin yake, inda aka ɓata basira wajen zuba duk wani abu da ƴa mace za ta buƙata a cikin madafin gidanta, na gargajiya da na zamani. Abin sha'awar kuma shi ne komai an killaceshi wajen da ya dace. Store ɗin ta shaƙe yake da kayan gara wanda Hafiz ya siya kamar bai san zafin kuɗi ba, nan ma dai babu ce kawai babu a cikin kayan abincin. Daga can wani ɓangare na falon kuma ɗakunan baƙi ne guda biyu da bayi a cikin ko wane ɗaki. Can gefe guda kuma matakala ce da za'a haura sama inda ƙaramin falo da ɗakunan mazauna gidan suke. Dakin Zulai daban, shi ma ya sha jerenshi, na Abban Imam yana kallon nata, duk da a rufe yake amma shima a gyare yake tsaf. Idan ka matsa gaba kaɗan kuma zaka tarar da ɗakunan yara na maza daban na mata daban. Gida kam ya haɗu iya haɗuwa, sai dai fatan Allah Ya ba mazauna cikinshi zaman lafiya da zuriya masu albarka. Bayan tawagar amarya sun gam kallon gida sun huta, suka yi watanda da soyayiyar shinkafa da ta ji soyayyen nama da ganyayyaki, ga soyayyar agada da coleslaw, suka kuma ɗora da kalolin lemuka mabanbanta. Sai da aka yi la'asar sannan Mummy ta kira Aunty Balira ta sanar da ita su yi ma Amarya sallama, za a mayar da su gidanta su kwana, washe gari kuma da sassafe za'a mayar da su Faƙo. Da jin wannan maganar nan da nan sai idanun Zulaikha suka fara kawo ruwa, tsakaninta da Allah ita duk tunaninta anan ƴan'uwanta za su kwana. Ta kalli Karima cikin marairaicewar fuska ta ce "Ayya mana Aunty Karima don Allah ki sa baki su zauna anan mana su kwana? Kin ga fa har yanzu bamu gama sallama da su Aunty Balira ba." Karimah ta kama baki tana dariya ƙasa-ƙasa tace "Lallai ma yarinyar nan, daman wa ya faɗa miki ana gama sallama da dangi? Ai auren kenan. Ko so kike Yaya ya ci ƙaniyata da yammacinnan? To wallahi ba dani ba aikata wannan ɗanyen aiki. Ke baki lura da yadda tun ɗazu mijinki yake ta auno min kira yana tambayar baƙi sun tafi? Kina tunanin idan ya zo ya samu gidannan da mutane zai saurara min ne? Bayan haka kuma dai umarnin Mummy ne a dole za kiyi haƙuri." Shigar Aunty Balira cikin ɗakin yasa dole suka bar maganar, Karima ta fice daga cikin ɗakin tana yima Zuly dariya ganin yadda ta kwaɓe fuska ta cigaba da matsar ƙwallah. Kusa da ita Aunty Balira ta zauna, itama da fara'a sosai a fuskarta ta fara raira ma Amarya waƙar ke kika ce kina so, da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba. Duk yadda Zulai ta kai ga ɓata fuska bata san sa'adda ta fara ƙyalƙyala dariya ba. Ganin ta saki fuskar yasa Aunty Balira amfani da wannan damar ta ƙara yi mata nasiha mai Nasiha mai shiga jiki. Daga bisani ta ɓuge da bata sirruka da kissosin kama miji a tafin hannu irin nasu na mutanen ƙauye, amma fa kamu wanda zai ƙara kwantar da mace a cikin zuciyar mijinta, babu boka balle Malam. Zulai har mamakinta ta dinga ji. Anty Balira ta kalleta da dariya ta cigaba da cewa "Haba yarinya! Don kina ganinmu a ƙauye kuma sai aka ce miki kan duk dusa ne? Mun fa san yadda zamu bi da mazajenmu, dai-dai gwargwado ba na tunanin ko wata ƴar birnin za ta iya kamoni ta wannan fannin. Ke dai ki riƙe abinda na faɗa miki za kiga aiki da cikawa." Ana haka su Aunty Rakiya da Ladidi suka shigo, a gurguje suka yi nasu nasihar sannan sauran waɗanda suka rakota duk suka shigo suka mata sallama. Har bakin ƙofa ta raka su sannan ta rungume Yayunta cike da kewa tana kuka su kuma suna aikin lallashi. A haka dai har suka lallabata ta koma cikin gida ita da Karima su kuma suka shige motoci suka tafi. Duk yadda su Aunty Balira suka gyara gidan saboda ɓata shi da abinci da ƴan'uwansu suka yi. Suna tafiya Mummy ta tura masu aiki suka sake ƙalƙale gidan, aka kunna turaren wuta a lungu da saƙo na gidan. Hibbah da isarta gidan kenan ta sa Zuly ta sake yin wanka, sannan ta suka taimaka mata ta shirya cikin tsadaddiyar lafaya mare nauyi, tayi mata sassauƙar kwalliya. Daga cewa za su zagaya cikin gidan su ga yanayin kwalliyar fulawoyin tsakar gidan sai jin tashin motar Hibba tayi. Ko kafin Zulai ta sauka ƙasa ta leƙa har mai gadi ya buɗe musu get sun fita. Haka ta tsaya a tsakiyar falon ƙasa jikinta a sanyaye. Ko da ta ɗaga wayarta ta kira Aunty Karima, wayar har ta ƙaraci ringing ɗin ta bata ɗaga ba daga can ɓangaren. Sai bayan kiran ya tsinke ta turo mata da gajeren saƙo cewa tayi haƙuri ta bi Hibbah sun wuce gida, amma gobe da safe tana nan tafe. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai bayan ta gama karanta saƙon. Duk da fargaba da tsoron da ke danƙare da zuciyarta bai hana ta ƙare ma falon da yake matsayin mallakinta kallo ba. Duk da falon bai kamo na gidan Hafiz tarkace da kayan ƙawa ba, amma fa daga kallon farko ta san ya kere na Hafiz aji da kashe naira kamar ba'a san zafinsu ba. Ta lallaɓa cikin sanyin jiki ta koma ɗakinta, ta lalubi bakin gado ta zauna tana ta aikin sauke ajiyar zuciya jefi-jefi, zuciyarta cike fal da tunanin yadda ranar zai kasance tsakaninta da Angonta. Babu jimawa kuma taji dirin mota a waje, kafin ta ji an shigo cikin falon gidan. Kafin ta ankare ta yi wani abu, an turo ƙofar ɗakinta an shigo, bakinshi ɗauke da siririyar sallama cikin nutsuwa da tausasa murya. Kamar wacce aka kullewa baki, ta kasa amsa sallamarsa. Sai ɗaga kai da tayi a hankali tana kallonsa, bugun zuciyarta yana ƙaruwa sannu a hankali kamar ana luguden daka. Farar shadda ce a jikinshi kar da ita, ta sha ɗinkin hannu irin na gidan sarauta da zare kalar brown mai cizawa, hular kanshi sai ya sanya brown wadda ta hau da takalmin kafarshi sau ciki. Wani kwantaccen murmushi mai matukar daukar hankali ne akan fuskarshi, da ba don yadda cikinta yake cunkushewa da fargaba ba, a gefe guda ga wata irin matsananciyar kunya da ta rufe ta, da baki za ta buɗe tayi ta yabon kyawun da yayi a idanunta. Don kuwa yayi kyau sosai da sosai, ya fito a Ango ɗanye sharaf! Ya ƙarasa shiga cikin ɗakin tare da maida ƙofar ya rufe. Rufewar da yayi daidai da ƙara saurin bugun zuciyarta. Tsoronta ya sake ninkuwa. Shi kuwa ko a jikinshi, duk da ya kula da yadda take ta wani mutsu-mutsutu akan gadon kamar mai jin fitsari. A hankali da wani irin taku na ƙasaita ya ƙarasa jikin gefen gadon, inda aka ajiye ɗan ƙaramin teburi, ledar dake hannunshi ya ajiye akai. Sai kuma ya hau kici-kicin cire babbar rigarshi yana kallonta murmushin fuskarshi yana ƙara faɗaɗa. "Manya-manya maganin ƙananan ƙwari. Hajiya Zulaikha amarya a gidan bawan Allah Kamaluddeen! Iye!! Irin wannan kyawu Ummu Imam anya ba zaki sa ɗan Mommy ya ƙarasa haukacewa a kanki ba?" Kalamanshi suka bata kunya matuƙa, har ta kai ga sanya hannu tana kare fuskarta, a ɓoye take sakin wani lallausar murmushi tsigar jikinta na tashi. A gefenta ya ajiye rigar, ya zauna a kusa da ita har jikinshi yana gogar nata, kamshin turaren da jikkunansu ya cakuɗe ya haɗe waje ɗaya, ya bayar da wani irin daɗi mai matuƙar sanyaya zuciya. Ba ma kamar daddaɗan ƙamshin da Zulai din take yi na haɗaɗɗiyar humra ta amare da Anty Hibba tayi mata amfani da shi. Cikin ƙanƙanin lokaci Kamal ya ji kamshin yana neman ya sanyashi fita a hayyacinshi. Ƙoƙarin zamewa Zulaikha take yi saboda kusancin da suka yi da juna yayi yawa. Fahimtar abinda take ƙoƙarin yi yasa shi yin caraf ya kamo ruwan cikinta, sannu a hankali da wani irin salo ya ja ta cikin jikinshi yana sauke numfashi sannu a hankali. Lokaci ɗaya Zulaikha ta hau kifkifta idanu kamar wacce tayi ma sarki ƙarya. Jin baƙon lamari a tattare da ita yasa ta faɗawa cikin matukar kidime, tsoro da fargaba ya sake lulluɓeta. Lura da halin da ta shiga yasa shi kama hannuwanta ya rike ƙam a cikin nashi, cikin taushin murya mai nuna kulawa da son amintar da ita yake mata magana, ƙamshin Listerine yana fita daga bakinshi yana bugun fuskarta, lokaci ɗaya yana aikawa sassan jikinta wasu irin saƙonni da suka sanya taji jikinta ya fara rawa sannu a hankali. "A'a fa! Kar muyi haka dake ba Babyna. Kina sane da alƙawarin da muka yiwa juna ko? Ko in tuna miki? Da bakinki kika yi ta jaddada min za mu gudanar da rayuwar gidanmu babu kunya, babu tsoro, kuma shakka sai girmamawa da so da kaunar juna. Ya aka yi kuma tun a yanzu zaki sage min gwiwa Ammata?" Tayi shiru ta kasa magana. Ya kai hannu ya daga fuskarta yadda zata kalleshi da kyau, amma ta kasa haɗa idanu da shi sam. A maimakon ta kalleshi ma sai ta lumshe idanunta. "Uhmmm! Ko dai don ban sayi bakin amaryar tawa bane take sha min ƙamshi? Kiyi hakuri to! zakwaɗi da zumuɗin zuwa inyi tozali da kyakkyawar fuskarki ni kaɗai ƙwal ya sanyani hana masu sayen bakin zuwa, don nasan lokaci za su ɓata min. Amma a min uzuri, in Sha Allah gobe za a sayi bakinnan da abu mafi daraja! Kin ji?" Ɗan murmushi tayi kawai, har lokacin idanunta na lumshe. Sai ta hau girgiza mishi kai alamun ba haka bane fa. "To menene?" Ya jefa mata tambayar bayan ya fahimci manufarta. Kafin ta amsa ya sake cewa "Ko rowar daddaɗan muryar ake min ni marayan Allah?" Yadda yayi maganar yana lanƙwasa kai gefe guda sai ya bata dariya. Ta sake yin murmushi tana kara girgiza mishi kai a nutse. "Talk to me pls Baby! Tun dazu babu abinda nake ta son gani da ji kamar ke da kuma muryarki. Me yasa zaki hanani jin muryarki a yanzu?" Ya ƙarasa maganar a marairaice kamar zai saka ihu. Ganin yadda ya matsa yasa dole ta buɗe baki kamar mai tsoron magana, don taga alamun bashi da niyar barinta ta sarara matuƙar bata buɗe baki ya ji muryarta ba. "Yi haƙuri Abban Imamuna. Ina yini?" Yayi murmushi sosai har hakoranshi suka bayyana "Yauwa! Good girl. To ko ke fa amaryata? To ya amarcin? Ya hanya? Ya kuma kika baro su Innaye?" A hankali da dabaru ya fara janta da hirarraki, tun tana amsawa a ɗarare har ta saki jiki da shi. Daga ƙarshe ya miƙar da ita, suka fara takawa sannu a hankali gwanin ban sha'awa har zuwa ƙaton bayin dake manne a dakin. Alwala suka ɗauro, ya ja su suka yi sallar nafila raka'a biyu. Bayan yayi sallama ya dafa kanta yayi addu'a sosai da sosai, yayi mata tambayoyi kan addininta tana amsa mishi da gwargwadon sanin da take da shi. Ya sha mamaki ƙwarai jin irin sanin da take da shi a addinance duba da inda ta rayu. A fili ya dinga shi mata albarka yana godewa Allah da ya mallaka mishi ita matsayin matarsa. Shi da kanshi ya zare mata hijabin jikinta sannan ya ce "Kiyi shirin kwanciya Beb, ina zuwa." Ledar da ya shiga da ita cikin ɗakin ya ɗauka ya fice da ita. Zaman minti biyu ta ƙara a gurin bayan fitarsa, babu abinda ƙirjinta ke yi face dakan lugude. Amma tunawa da karin maganar da take cewa duk wayon amarya sai an sha manta yasa ta miƙe a hankali ta nufi wardrobe din ta ta buɗe. Kafin tafiyar Karimah duk ta nuna mata yanayin yadda tsarin shirin kayayyakinta suke, shi yasa bata sha wahalar gano ɓangaren kayan barci ba. Dai-dai gwargwado tana da iliminta na addini, na fannin rayuwa ma da zamantakewa tana da su gwargwado. Ta san tana son mijinta kamar yadda shi ma yake sonta, don haka tayi ɗamarar kula da shi da sauke duk wani nauyi na shi da ke kanta in dai ba tana son ta wayi gari taga wata mai zafin naman ta yi wuff da shi bane. A hankali take ɗaɗɗaga tarin kayan barcin da aka zube mata tana dubawa har Allah Ya hadata da wata doguwar riga mai gajeren hannu ruwan madara. Ta dauka ta sanya, ta ƙara feshe jikinta da turare. Da ta tsaya gaban mirror taga yadda rigar tayi mata kyau ta kuma kamata, sai taji ba zata iya tsayawa gabanshi a haka ba musamman a daren yau. Don haka ta ɗauki madaidaiciyar hijabi ta dora akai wadda ta tsaya mata a ruwan ciki. Tana cikin saka hijabin sai gashi ya shiga dakin saye da pyjamas na barci masu budadden kirji. Hannunshi rike da babban tray. Tayi duru-duru tana kokarin hana idanunta kallonshi, kafin kuma ta yunkura da nufin karbar farantin hannun nashi, yayi gaggawar dakatar da ita. Ya ajiye farantin a tsakiyar daki, ya zauna yana linke kafafunshi tare da kama hannunta ya kara zaunar da ita kusa dashi kugu da kugu. "Yau ke amarya kike fil! Oya, zo in ciyar da ke in kuma shayar da ke madara." Haka nan tana noƙewa da sussunne kai, ya dinga yankar wani lafiyayyen gashin nama yana bata a baki, gefe guda kuma ga tatacciyar madarar yoghurt mai masifar daɗi yana bata. Sai da ya tabbatar ta koshi sannan shi ma ya ci yayi nak! Ko da ya tashi da niyar dauke kayan wannan karon hana shi tayi, ta daukesu ta kai kicin. Sauran naman ta nade a foil paper ta sanya a cikin firjin, kayan da suka ɓata kuma ta daurayesu ta jingine a jikin rag. Ta tunkari hanyar dakinta zuciyarta na bugu, jiki na mazari. Da ta je jikin kofar ta jima tana kokonton budewa, har sai da ta jiyo muryarshi daga cikin dakin yana cewa "Wai dodo ne a cikin dakin da ba zaki shigo ba Umman Imam? Ko dai so kike in bar miki ɗakinki in koma nawa?" Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki ta buɗe ɗakin ta shiga. Sai ta gan shi

Chapter 27 of 40