Share this page
Allah yasa bana sha'awar yi ma ƴaƴana auren dole na rantse da tuni na daɗe da bayar da sadakar Zulai.." "Ai yanzu dai duk wani jira da damuwar rashin mashinshini ya ƙare in Allah ya yarda. Kayi haƙuri, shi aure lokaci ne. Babu mamaki yanzu ne lokacinta yazo. Yanzu dai ya kake ganin za a ɓullo ma al'amarin?" Shiru yayi yana jujjuya sunayen samarin da Zulai ta faɗa ma Innaye sun taɓa yi mata maganar suna son ta a zuciyarsa. Ganin duk su ukun babu wanda ba nagartacce ba yasa shi cewa "Yanzu dai ina ga zan aika a tuntuɓe su ne ɗaya bayan ɗaya. Tunda dukkansu sun fito ne daga nagartattun gidaje, kuma a fahimtata da ɗan gajeren sanin da nayi musu yara ne masu kyawawan halaye. Ko ma dai yaya ne, maganar aure ta wuce wasa, duk wanda na samu tsayayyiyar maganar har yanzu yana son ta dole in ƙara faɗaɗa bincike domin gudun yin kitso da ƙwarƙwata." "Haka ne kam! To Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi." Innaye tayi addu'ar fuskarta da bayyanannen farin ciki. Kamar yadda Baffa ya alƙawarta ma Innaye. Tun a daren ranar ya naɗa wakilai ya tura su gurin Khalilu, ɗaya daga cikin samarin da Zulaikha ta ambata ya taɓa furta yana son ta. Amma cikin hukuncin Allah bayan gama sauraren jawabin wakilan kai tsaye ya faɗa musu a yanzu dai kam akwai wacce yake so. Har ma an kai kuɗin na gani ina so gidansu yarinyar. "Tsahare ce ƴar gidan Mal Isiya. Ayi haƙuri, sai dai inyi ma Zulai fatan alkhairi da addu'ar Allah ya haɗa ta da wanda ya fi ni." Haka wakilan Baffa suka bar gurin jikinsu a sanyaye. Su kuwa sauran samarin biyu Yusufa da Sani da farko duk sun amince har lokacin suna son ta. Amma daga baya ba tare da sanin me ya faru ba daga gidajensu aka aikewa Baffa da wakilai ɗauke da saƙon yayi haƙuri. Zancen soyayya ma bazai yiwu ba balle har a kai ga maganar aure a tsakaninsu. Ba kuma tare da sun faɗi wani ƙwaƙƙwaran dalili da zai gamsar da Baffa dalilin fasawar tasu ba. Ranshi a ɓace ya shige cikin gida ya huce haushinshi akan Zulai ta hanyar yi mata wankin babban bargo sannan ya wuce turakarsa ya barta a tsakar gidan tana kuka. Kasancewar zancen duniya da baya ɓuya balle kuma a ƙauye irin Faƙo da ya kasance ƙaramin gari sai ga zancen bibiyar samarin Zulai ya fasu. Shi Mudan tun kafin a aika mishi ya bayyanar da kanshi, a cewarsa ya daɗe yana son ta. Amma ganin yadda ta ƙare tsakaninta da abokinshi Khalilu yasa bai taɓa yunƙurin faɗa mata ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ya samu karɓuwa a cikin gidansu Zulai. Amma gare ta babu yabo babu fallasa, saboda dalilai mabanbanta. Dalili na farko shi ne Mudan yana da mata. Duk da a shekaru Mudan ɗin bai haura shekaru ashirin da biyar a duniya ba yana da mata ɗaya da ƴaƴanshi uku. Auren miji mai mata kuwa abu ne da Zulaikha bata taɓa tsammanin yin shi ba. Dalili na biyu kuwa shi ne matar Mudan mai suna Yahanasu. Tun a wancan lokacin kasancewar Zulai me tsawon ƙafa duk da Yaha ta girme mata da shekaru biyu sun yi zamanin ƴan matanci da juna, tun a wancan lokacin jininsu sam bai haɗu da na Yaha ba. Dukkansu ba su da haƙuri kamar zawayi. Yahanasu akwai bala'in son girma ita kuma Zulai akwai ta da raini, musamman ga babban da ta zubar da girmanta. To ita kuma Yaha akwai shiga abinda babu ruwanta. Ga masifa da bala'i kamar ruwan shan ta, duk yawan taron jama'a ba ta kunyar ta kwaɓe mayafi su dambatu da wacce ta shiga hanyarta. Allah dai ya kiyaye duk wannan rashin jituwar tasu har Yaha tayi aure Zulai bata taɓa ba ta damar da za su ba hammata iska ba. Saboda ita kura ce, ga tsoro ga ban tsoro, akwai dai baki kamar me amma da an zo batun dambe yanzu za'a neme ta a rasa. Sam ta tsani abinda zai sa ta haɗa jiki da wata in dai ba an shammaceta ba. Dalili na uku shi ne shi kanshi Mudan ɗin a halayenshi mutum ne mai tsananin iko da rashin haƙuri. Da shi da matarsa kamar an duba halayyarsu ne aka haɗa su aure. Amma kuma wani ikon Allah suna zaman lafiya sosai, domin Yaha ta iya bi da halayenshi. Wadannan dalilai uku suka hadu suka sa duk da zancen Mudan ya shiga gidansu Auta bata dauke shi wani kayan gabas ba. Haka take ta jan shi da dadi babu dadi har zuwa sadda aka tsayar da ranar aure a tsakaninsu. A lokacin ne ta dan nutsar da hankalinta guri daya ta fara daukarshi da daraja. A lokacin kuma sai Yahanasu ta taso ta gaba da sakonnin tanadin da tayi mata na masifa da bala'i kala daban-daban matuk'ar tayi kuskuren auren mijinta. Ashe tun fara neman auren yana yi a b'oye ne bai fad'a mata ba kuma ƴan'uwa da mutanen gari ba'a sami wanda ya tsegunta mata halin da ake ciki ba har sai da aka tsayar da rana sannan ta san halin da ake ciki. Wannan tashin hankali da matsanancin kishin da Yaha ta ɗora ma ranta shi ya taso mata da naƙuda gadan-gadan, lokacin haihuwarta baiyi ba. Ga mummunar ɗabi'ar mutanen ƙauye ta rashin wayewa da zuwa asibiti musamman idan naƙuda ta taso. Wannan dalilin yasa ta sha baƙar wahala, kamar baza tayi ba a hannun Ungozoma na gargajiya kafin aka kwashe ta zuwa asibiti. Kuma cikin hukuncin Allah duk da asibitin babu wasu ƙwararrun likitoci ko malaman jinya ana zuwa bata cika awa uku ba ta haifi ɗanta namiji. Wannan haihuwa ya zo ma Mudan da iyayensa da ita kanta Yaha da wani gagarumin farin ciki da basu taɓa tsammani ba. Na ɗaya saboda duk ƴaƴansa uku da Yaha ta haifa mata ne. Na biyu kuma a ranar ne ya kai amfanin gonarsa kasuwa suka yi gagarumin tsadar da basu taɓa yi ba. Kuma a ranar ne ya samu nasarar siyan mota golf wacce ya daɗe yana buri Allah bai nufa ba sai a wannan rana. Waɗannan dalilai suka tattaru suka sa yake ɗaukar haihuwar nan da wani irin girma da ƙima kamar ba'a taɓa mishi haihuwa ba. Shukuranu shi ne sunan da yake kiran yaron tun kafin ranar raɗin suna ta zo, saboda a ganinsa duk waɗannan alkhairan sun zo ne dalilin haihuwarsa. Tun a washe garin ranar da akayi haihuwar ya fara yi ma Zulaikha nacin taje tayi ma Yahanasu barka, wacce aka sallamota daga asibiti bayan ta kwana ta yini. Amma haka tayi ta mishi yawo da hankali har dai ranar ta biyar da aka yi haihuwar inda ta fito ƙeƙe-ƙeƙe ta faɗa mishi baza ta je ba. Shi kuma yasha alwashi sannan ya rantse da girman Allah idan bata je ma Yaha barka ba bazai aure ta ba. Zai gwada mata ya fi ta ɗanyen kai. ****** Tun da ya fito yayi tozali da Baffa, nan take yanayin fuskarsa ya canza daga farin cikin da ya fito da shi zuwa ba yabo ba fallasa. "Au! Baffa kai ne da safen nan?" Ya faɗa yana ɗan ciccijewa. Duk da ganin yadda ya canja fuska farat ɗaya daga ganinshi bai hana Baffa faɗaɗa tasa fuskar da murmushi ba. "Assalamu alaikum!" Yayi mishi cikakkiyar sallama haɗe da miƙa ma Mudan ɗin hannu. A kunyace ya ɗan kawar da fuska yana sosa ƙeya. Sai kuma ya ɗan duƙa ƙasa a ladabce ya fara gayar da Baffa, ba tare da ya mayar mishi da hannu kamar yadda Baffa ya buƙata ba. Bayan musayar gaisuwa a tsakaninsu da tambayar lafiyar masu jego ɗan shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Can kuma sai Baffa ne ya karya shirun da cewa "Jiya na dawo da daddare nake jin wasu zantuka na shirme daga bakin Zulai. Amma kasancewar kai ne namiji mafi girma a kanta ban ɗauki maganganunta da muhimmanci ba. Sai ma faɗa da nayi mata na miƙa mata laifin gaba ɗaya duk da bansan cikakken bayanin abinda ya faru ba. Domin a ƙa'ida shari'a ba ta yiwuwa da jin ɓangare ɗaya. Wannan dalilin yasa nayi sammakon zuwa jin abinda ya faru sannan in baka haƙuri. Don Allah kayi haƙuri, ka san Zulai yarinya ce har yanzu akwai ƙuruciya a kanta..." "Shekarunta goma sha takwas ne kake kira mata yarinta Baffa?" Ya katse shi da faɗin haka yana ƙara ɗaure fuska. Shi dai Baffa bai sake cewa komai ba. Tun da ya katse shi sai kawai ya sakar mishi ragamar maganar ya tsaya yana saurarenshi. Lura da hakan da Mudan yayi yasa shi naɗe hannaye a ƙirji idanunsa na kallon gefe ya cigaba da sakin duk irin maganganun da suka zo bakinshi. "In dai za mu faɗa ma kanmu gaskiya babu wani ƙuruciya a jikin Zulai. Yarinyar da duk sa'anninta sun tara ƴaƴa huɗu biyar ita ake kira ma ƙuruciya? Tsabar raini ne kawai da iskanci, kuma daman tun farko an faɗa min. Ta riga ta riƙa ta gandare a gidansu ko na aure ta baza ta taɓa jin magana ta ba. Sannan kuma tana ji da kanta don Yayanta na da kuɗi tana zuwa Habuja ita gani take ta fi ƙarfin mazajen ƙauyen nan. Kuma tana ganin duk ƴan matan ƙauyennan ita kaɗai ce ta samu nasarar gama sakandare tana taƙama da boko shi yasa take jin ita ɗin ta kai wata shegiya. Bayan abinda ya faru jiya ni gaskiya na riga na yanke ma kaina shawara, tunda dai ita fitsararriya ce, ni da zan aure ta ma tun yanzu ban isa in bata umarni ta aikata cikin daɗin rai ba to ina ga mun yi aure? Kana ganin ni da hankalina zan yarda in auri macen da take min gani-gani ne? Ita fa a yadda na lura gani take kamar alfarma tayi min idan ta aure ni. Don haka gaskiya sai dai kuyi haƙuri Baffa..." "A'a! A'a Mudansiru!! Don Allah don Annabi kayi haƙuri. Kar ka ce ka fasa aurenta don Allah. Na ɗauki alƙawari zan yi mata faɗa sosai, idan ta kama da duka ma Wallahi zan haɗa mata. In Allah ya yarda baza ta sake ƙin bin umarninka ba, kayi haƙuri don Allah." Baffa ya faɗi maganganun cikin tashin hankali, idanunsa sun kaɗa lokaci ɗaya sunyi jaa saboda tsananin tashin hankali da damuwa. Duk da maganganun Mudan ɗin sun ƙona masa zuciya, musamman in da ya kira Zulai da shegiya. Amma zai iya shanye fiye da haka akan dai ace ya fasa auren Zulai, a cikin waɗannan ƙidayayyun kwanakin da suka rage ya aurar da ita. Da wannan dalilin yasa bai tsaya tunkarar iyayen Mudan ba tunda dai shi ne mai aure, kuma shi Mudan ɗin ba yaro bane tunda har ya tara iyali. Sannan bai tsaya turo ɗaya daga cikin ƴan'uwansa gurin Mudan ɗin ba ya zo da kansa, zuwa da kai ai ya fi saƙo. Kuma yadda zai ƙasƙantar da kai yaba Mudan haƙuri ya san ba lallai ne ƴan'uwansa su iya yin haka ba. Ɗan shiru Mudan yayi yana ciccijewa yana hura hanci, irin a dole shi fa an takura shi ɗinnan. Kamar bazai tanka ba, amma kuma wani tunani da yayi yasa shi cewa. "Baffa... Ni fa gaskiya na gama magana. Amma tunda ka ce za ka mata faɗa zan je inyi shawara, duk yadda ake ciki zuwa yamma ko gobe za ka ji ni. Na barka lafiya, a gaida iyali." Yana gama faɗin haka da saurin gaske ya wuce ya ba Baffa guri, don ma kar ya sake tare shi da wasu kalaman magiya da ban haƙurin da yake ji babu abinda za su canja matuƙar Zulai bata sauke girman kanta ta je ma Yahanasu barkan haihuwa yau ko gobe ba. Haka Baffa ya bar ƙofar gidan Mudan jikinsa a sanyaye, jan ƙafafunsa yake tayi hankalinsa tashe har Allah yasa ya isa gida lafiya. Saboda tsananin damuwa duk yadda Innaye ke ta bin shi da kallon tuhuma ya kasa sanar da ita yadda suka yi, ya bari ne tukunna sai ya ji tsayayiyar magana daga bakin shi Mudan ɗin. Ita kuma Innaye saboda tsananin ladabi da biyayya irinna matan da ta kasa titsiye shi da tambayar yadda suka yi, sai kawai ta kawo ido ta zuba masa tana cigaba da addu'ar tabbatuwar auren kamar yadda aka saka shi. [1/1, 12:01 AM] Fareeda Abdallah: Tun safe har yamma babu wata ƙwaƙƙwaran saƙo da Baffa ya samu daga Mudan ko wakilansa. Tsananin tashin hankali da damuwa yasa ya kasa faɗa ma ƴan'uwansa halin da ake ciki. Idan ya kalli Zulaikha da ita ma tun bayan abinda ya faru jiya sam ba ta cikin walwala sai yaji kamar zai saka kuka. Ya sani ko Zulai ta ƙi Allah a wannan gaɓar da bikinta yazo daf baza ta taɓa so ace an fasa bikin ba. Kwanakin baya da kunnensa ya ji hirar Zulan da Yayarta Balira, tana faɗa mata ita kanta tana so ace yau ga shi tayi aure, amma tunda mijin bai zo ba ya za tayi da ranta? 'Wallahi Aunty Balira ko da kuke ganin kamar ba na damuwa ina damuwa fa, amma ya na iya da abinda ya gagari tuwo in ji kishiyar ƙonanniya? Mudan da kuke ganin kamar ina wulaƙanta shi don kar ya aure ni ina da dalilai da dama da nake ganin bamu dace da juna ba ni da shi. Amma ya zanyi? Tunda babu wanda ya fito neman aure na bayan shi? Haka nan zan aure shi. Ina ta addu'ar idan aurensa alkhairi a gare ni Allah ya tabbatar da shi.' A Lokacin da ya tsinkayi waɗannan maganganun, a zauren gidan ne tayi ma Yaya Balira rakiya za ta koma gidanta, shi kuma ya sako kai zai shiga gidan da yaji maganar da suke yi sai ya tsaya ya saurara. Da la'asariyya liƙis yana zaune a cikin turakarsa ya ƙwalla ma Bilya ɗaya daga cikin ƙananun ƴaƴansa kira. "Salamu alekum. Ga ni Baffa." Yaron ya faɗa a ladabce, bayan ya durƙusa har ƙasa a gaban Baffa. "Yi maza ɗakin Innaye ka kira min Zulai." "To Baffa." A guje yaron ya fice daga ɗakin yana haɗawa da ƴan tsalle-tsalle. Ba'ayi cikakken mintuna uku ba sai ga sallamar Zulaikha a ƙofar ɗakin. Sai da ya amsa, yayi mata umarnin shiga sannan ta shiga cikin ɗakin. Tana sanye da wani zumbulelen hijabi kamar mai takaba. Idanun nan sunyi kozai-kozai sun kumbura alamun ta sha kuka, a bakin kofa ta tsuguna. "Ga ni Baffa." Ta fad'a da dasasshiyar murya. "Zulaikha?" Ya kira sunanta a tausashe. "Na'am Baffa" Shiru yayi yana sake kare mata kallo na wasu dakiku kafin ya cigaba da cewa. "Da safe na je har gida na sami Mudansiru. Irin maganganun da na ji daga bakinsa a kanki sam ban ji dad'insu ba. Amma na yi mishi uzuri, saboda ban san girman laifin da kika yi mishi ba har idanunshi suka rufe ya farfaɗa min waɗannan maganganun." Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba "A taƙaice dai, ya faɗa min cewa kin raina shi. Sam bakya bin umarninshi a matsayinshi na wanda yake niyyar aurenki. Da wannan dalilin yasa na kira ki yanzu don in tambaye ki gaskiyar abinda ya faru. Kuma ina roƙonki don Allah ba don ni ba ki ji tsoron Allah ki faɗa min gaskiyar abinda ya haɗa ku." A cikin ɗabi'un Zulaikha da kusan duk ƴan gidansu suka shaide ta akai shi ne ƙarya ba ya daga cikin halayenta. Za ta fito ta faɗi gaskiya ko da ita ce da laifi. Don haka a yanzu ma bata yi ƙasa a gwuiwa ba wajen sanar ma da Baffa gaskiyar abinda ya faru. Bayan ta gama sanar da shi kuma ta ƙara da faɗa masa babban dalilin da yasa ta ƙi zuwa barkan matarsa kamar yadda ya nema. "Baffa, matarsa Yahanasu tun zamanin ƴanmatacinmu da su ta tsane ni. Ban samu sauƙinta ba sai da tayi aure. Amma jin zancen mijinta yana neman aure na babu irin baƙaƙen maganganu da munanan zagin da ba ta aiko min. Kwanaki can har aiko min tayi muddin na kuskura na auri mijinta ta rantse da girman Allah a daren ranar za'a fitar da gawata a gidanta. Innaye shaida ce, duk irin maganganun da take min aike Innaye ta sani. Ban taɓa faɗa maka bane don kar ku ga kamar ba na son auren ne. Duk na faɗa ma Mudan amma ya ƙi fahimtata. Tsorona Allah tsorona in je mata barka tayi min lahani, ko kuma ta ƙulla min sharrin da zan shiga bakin duniya. Wannan shi ne dalilin da yasa kai tsaye na ce mishi bazan je ba." Tsawon mintuna biyu Baffa ya kasa magana, babu abinda yake sai jujjuya maganganun Zulaikha a zuciyarshi. A karo na biyu ya sake sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan yayi mata umarnin komawa cikin gida. Bayan sallar isha'i ya shiga ɓangaren Innaye da nufin yi mata sai da safe, tunda ranar ba girkinta bane. Daga yadda idanuwanta suka zurma ciki lokaci yasa matsanancin tausayinta ya ƙara lulluɓe shi, bai shiga cikin falonta da niyyar zama ba, amma lura da halin da take ciki yasa shi zama kan kujera nesa da ita kaɗan yana yi mata nasiha kan muhimmancin yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau a matsayinta na cikakkiyar musulma. "Shi ma ya fasa auren Auta ta ko?" Ta katse shi da tambayar da raunin murya. "Eh toh! Bazan ce eh ba bazan ce A'a ba. Domin har zuwa yanzu ban samu wata gamsasshiyar amsa daga gare shi ba kamar yadda ya ce zai min aike. Kawai dai mu cigaba da addu'a." "Uhmmm! Allah ya jisshe mu alkhairi." Abinda ta iya cewa kenan ta sunkuyar da kanta ƙasa. Har Baffa ya fice daga falon bata iya sake ce mishi komai ba. A wannan dare, idan Baffa ya ce ya yi cikakken barci na awa ɗaya yayi ƙarya. Duk yadda yake ganin kamar abin bazai dame shi ba inaa... Mama Laminde da take da girki tun tana mishi nasiha da tausasan kalamai har dai ta gaji ta zuba ma sarautar Allah idanu. A ƙarshe ma juya baya tayi ta kwanta ta ƙyale shi yana ta tufka da warwara. Babban damuwarsa ɗaya ne, idan Mudan ya ce ya fasa auren Zulai a waɗannan kwanakin wa za'a samu kuma yayi ƙundubalan fitowa ya ce zai aure ta? Ya sani duk maganganun da Zulai ta faɗa masa akan Yaha gaskiya ne, domin Rahina tana faɗa masa, amma duk su biyun basu ɗauki hargagin Yahan da muhimmanci bane domin a ganinsu surutu ne kawai irinna mace me mahaukacin kishi. Sannan shi da kanshi sai yau ya ƙara yarda da halin Mudan da ake ta faɗa mishi na rashin haƙuri da rashin iya magana. Amma duk waɗannan abubuwan bai ɗauke su da muhimmanci ba, babban burinsu shi da Rahina shi ne su aurar da Zulai. Domin anyi ittifaki a yanzu dai duk faɗin ƙauyen Faƙo babu yarinya budurwa da take da shekarun Zulai. Sa'anninta duk suna ɗakin mazajensu da ƴaƴayensu. Tun da daɗewa da ace shi mutum ne mai yarda da camfi da tuni ya daɗe da fantsama gurin masu magunguna yana nema ma Zulai taimako. Domin da yawan mutane na ganin Aljani ne ya aure ta. Wasu kuma na ganin nauyin jini take da shi, dole sai an nemi taimako sannan za ta sami mashin-shini. Maganar ta saka ma kanta girman kai don ta yi boko ko kuma don Hafizu yana da gida a Habuja ne yasa take ɗaga ma samarin ƙauyen kai bai taɓa ji ba sai yau a bakin Mudan. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a karo na barkatai. Ya ɗauki ƴar ƙaramar wayarsa mai tocila da take ajiye kusa da shi ya danna ta kawo haske ya duba lokaci, ƙarfe uku da minti ashirin da bakwai na tsakiyar dare. Hasken tocilar wayar ya kunna, sannan ya miƙe tsaye ya buɗe ƙofa hannunsa riƙe da buta ya fita can tsakar gidan ya ɗauro alwala. Ya sani duk wani tunani da saƙe-saƙe baza su samar mishi da mafita ba. Don haka ya ƙarasa daren yana miƙa kukanshi ga mai kowa mai komai mahaliccin sammai da ƙassai da abinda ke cikinta. Washe gari ko da ya tashi zuciyarsa babu damuwa kamar na jiya. Da asubah bayan idar da sallah ya tare ƴan'uwansa shaƙiƙai guda uku da suke uba ɗaya ya faɗa musu duk halin da ake ciki, sun nuna alhini sosai. Sannan suka daɗe suna tausarsa da daɗaɗan kalamai. A ƙarshe suka ɓuge da addu'ar Allah ya kaɗe fitina yasa su ji alkhairi. Ko da ya shiga gida, ya leƙa matansa gaba ɗaya yadda suka tashi turakarsa ya shiga ya kwanta. Yana tasbihi da hailala daga kwance nannauyan barci yayi awon gaba da shi. Ƙarfe goma da rabi na safe Innaye ta shiga ɗakinsa ta tashe shi. Idanunta sun kaɗa sunyi jaa, daƙiƙu talatin ya ɓata yana kallonta kafin a hankali ya ce "Me yake faruwa Rahina?" "Mudan ne ya aiko a bashi kayan auren Zulai da ya kawo. Wai ya fasa aurent..." "Ubangiji Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Allah ya haɗa ta da wanda ya fi shi alkhairi nesa ba kusa ba." Ya katse ta da faɗin haka tun kafin ta ƙarasa faɗa masa abinda ke faruwa. A fuskarsa babu wata shahararriyar damuwa. Daɓas! Ta zube a gefen katifar da yake kwance ta fara matsar ƙwallah, domin Allah ya sani ba haka ta so ba. Da tausasan kalamai yayi ta rarrashinta har ya samu tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. Daga can bakin ƙofa sai ga sallamar Mama Laminde da Baba Laraba. Shi ya amsa sallamar, Innaye kam ta kasa magana. Fuskokinsu a dame suka shiga cikin ɗakin suna ƙara jajanta ma Baffa wannan abin baƙin cikin da ya same su. "Babu komai ai. Wani baya taɓa auren matar wani. In Allah ya yarda ko da shi ko ba da shi ba ranar ɗaurin auren Zulai bazai canja daga yadda aka tsayar da shi ba. Ku kwashe kayansu ku kai musu." Da yake duk kayan da Mudan ya kai gidan hatta ihsani da yake mata na saurayi da budurwa ba amfani da su take yi ba, Innaye take damƙa ma ita kuma sai ta kai ɗakin Baffa ta adana. Don haka cikin ƙanƙanin lokaci aka gama fitar ma da matan da ya aiko kayayyakinshi gaba ɗaya, hatta sadakinshi sai da Baffa ya ba Mama Laminde ta kai musu. Kasancewar kayan ɗaki da na kicin da komai Hafizu ne ya ɗauki nauyin yin su, shi yasa ko sisi ba'a taɓa a cikin kuɗin na gani ina so, kuɗin gaisuwa da kuɗin sadaki da ya biya ba. Kamar wutar daji, zuwa ƙarfe biyu labarin fasa auren Zulai da Mudan yayi har ya zaga ƙauyen Faƙo. Ƴaƴan Innaye da sauran ƴan'uwansu da suke uba ɗaya haka suka cika gidan suna jajanta ma junansu wannan abin baƙin ciki. Amma ko da iyayensu mata suka sanar da su abinda Baffa ya ce za'a ɗaura auren ko ba da Mudan ba sai kuma suka yi tsuru-tsuru. Tsoronsu Allah tsoronsu a aura ma Zulai tsoho ko kuma nakasasshe wanda baiyi mata ba ta ƙi yi masa biyayya saboda rashin haƙurinta. A sako ta kuma da ƙananun shekaru ta zama ƙaramar bazawara a gari a cigaba da mata tofin Allah ya tsine. "Innaye? Amma kina ga aurar da Zulai ga wanda bata sani ba hanya ce mai ɓullewa? Kar fa fushi yasa mu aikata aikin da za muzo muna da na sani..." "Yayansu ke dai kiyi addu'a. Babu abinda zai faru sai alheri in Allah ya yarda." Innaye ta katse Yaya Balira da take maganar fuskarta cike da damuwa. Kafin Balira ta sake cewa komai wayar Innaye da ke cikin hular kanta ya hau tsuwwa. Wayar ta ciro, ko da ta duba sai taga alamar mota, alamar da Zulai ta saka mata a lambar Hafizu. Bata ɓata lokaci ba ta ɗauka don daman ta kira shi a ɗazu domin ta faɗa mishi halin da ake ciki bai ɗauka ba. "Assalamu alaikum! Hafizu..." "Innaye barka da yamma. Ki taya ni murna Innaye, Bintu ta haifi ɗa namiji yanzunnan, ni ma na zama Baba Innaye." Da karaɗin farin ciki da zumuɗi sosai a muryarsa yake jero maganganun. Kamar yana gaban Innaye,

Chapter 10 of 40