Share this page
har ya kwanta yana danna waya. Shigowarta cikin ɗakin ne yasa shi ajiye wayar, ya juya yana kallonta yana mata wani murmushi kasa-kasa. "Zo kiji wani labari mai daɗin gaske." Tayi duru-duru tana kallonshi duk a daburce. Bakinta na rawa ta ce "Uhmmm... dama... bari in wanke bakina" Ya gyaɗa kai "Ok! je ki wanke ki dawo. Ina nan ina jiranki" Ta fada banɗakin a sukwane ta rufe kamar wacce wani abin tsoro ya biy. Shi kuwa me zayyi in ba dariya ba. Yana kallonta ta dinga shige da fice tsakanin bandakin da dakin, babu wani takamaimai abinda take yi kuma sai zirga-zirgar. Da dai yaga abin nata ba na karewa ba ne, sai ya tashi da kanshi yayi caraf da ita tana fitowa daga bayin sai ganin mutum tayi a gabanta ya riƙo ƙugunta da sauri. Ya cakumo wuyan hijabinta da hannu ɗaya lokaci guda ya ƙarasa haɗe ta da jikinshi. Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi ya saki sannan ya fara kokarin zame mata hijabin, suka hau kici-kici, yana ƙoƙarin cire mata ita kuma tana hana shi. Murya can ƙasa ta yadda take jin shi ƙasa-ƙasa ya ce "Don Allah don Annabi kada kiyi min iyaka da abinda Allah Ya halatta min. Nasan kin fini sanin hukuncin hakan, kiyi haƙuri. Nayi tunanin mun gama magana akan kunyar nan? Don gaskiya wahalar da ke kawai zata yi, ni dai babu ruwana. Ba zan taɓa yarda kunyar nan ta dinga shiga hakkina ba!" Yana maganganun a lokaci ɗaya kuma yana cusa hannunsa ɗaya a cikin rigarta. Bayan nasarar cire mata hijabin da yayi har ya fara ɓalle maɓallan gaban rigarta. Zulaikha dai kunya ta gama rufe ta, ji take ina ma kasa za ta tsage ta shige ciki don kunya. Kamal dai ko a jikinsa, a ƙarshe ma cusa kanshi yayi tsakankanin kirjinta yana sakin wani irin numfashi mai nauyi. Duk yadda taso ta hana wata nannauyar ajiyar zuciya da ta taso mata kasawa tayi. Ya saki murmushi a tausashe jin ajiyar zuciyar da ta saki. Lokaci ɗaya kuma ya cigaba da kokarin cakuda mata lissafi a matsayinta na sabon shiga a wannan harkar. Tsananin kamshin da ko'ina na jikinta yake yi da taushin fatarta da wani irin yanayi da ya ziyarceshi irin wanda zai iya rantsewa bai taɓa shiga cikin makamancinshi ba, ya taimaka kwarai wajen fitar da shi daga dan sauran hayyacin da ya rage mishi a jiki. Ya manta yaushe ne karshe da ya jingina jikinshi da wata mace da sunan romanciyya. Labaran da ya fara bata sun fi karfin tunani da jikinta baki daya. Musamman da yayi nasarar danganata da gado. Sai idanunta suka raina fata, ta fara kokarin yakiceshi da ƙarfin tsiya jiki na rawa hawaye na kwarara a idanunta. A rikice yake, gani yake kamar kokarin raba shi da ruhinshi take yi. Da dukkan ƙarfinsa ya kara mannata da jikinshi har yana wasu ƴan ƙananun shessheƙar kuka. Tsakanin su biyun ya rasa jikin wanne yafi na wani kaɗawa. Murya cike da ƙauna da matsananciyar soyayya yake rallashinta da daɗaɗan kalamai "Ki taimake ni Zuly ta, taimakeni don Allah kiyi hakuri.... It has been so long...!" Duk yadda ta daure kamar yadda ya ce ba ƙaramar wahala ta sha ba, a jigace ta cigaba da sauraren labaran da yake bata daki-daki, cikin rawar jiki da fitar hayyaci. Sai dai zuwa lokacin da ya samu nutsuwa, tuni ta gama yin wujiga-wujiga ta fita haiyacinta. Ya haɗeta da jikinshi yana jin kamar ya tsaga kirjinshi ya sanyata a ciki don tsananin so da ƙaunar da yake mata. Sai kuma ya ɗago fuskarta ya fara share mata hawaye da tarin zufan da tayi, duk da sanyin AC da ya wadaci ɗakin. ****** Tunda suka yi sallar asubahi, ya haɗa mata tea mai kauri ta sha, sannan ya bata paracetamol da ibuprofen ta sha saboda zazzabi da ta kwana da shi, suka koma barci. Janta yayi cikin jikinshi ya rungumeta tsam! Duk da tabbacin cewa babu abinda zai mata da ya dinga faɗa mata, bata natsu ba sai da taji yayi barci da gaske. Sannan itama ta saki jikinta sosai ta yi barci. Wajen karfe tara na safe ta farka, ta ji dama sosai akan azaban raɗaɗin da take ji a jikinta da kuma zazzaɓin da yake damunta. A hankali ta fara ƙoƙarin zare kafafunta daga na Kamal da ya haɗe su da nashi ya makalkaleta. Kafin ta gama zame jikin ta daga nashi ta ji ya sake janta ya rike ƙam! Murya cike da barci yake tambayarta "Ina zuwa da wannan farar safiyar?" Agogon da ke jikin gadon ta sake kalla, da shaƙaƙƙiyar murya ta ce "Karfe tara ta gota fa. Ya kamata mu tashi haka nan. Kuma ina son ɗora mana abinda zamu yi karin kumallo da shi ne." A hankali ya girgiza mata kai. "Kar ki damu. Na san daga gidan Mommy za ta bada a kawo mana abinci. Don haka zo mu koma barci ni bai ishe ni ba." Murmushi ta saki tana kallon fuskarsa da har lokacin bai buɗe idanunsa ba. A tausashe ta ce "Ai kuwa sai dai kai ka cigaba da barcin, amma ni dai na gama. Na gaji da kwanciya. Wanka nake son yi." Ta gangara ta zame daga jikinshi ta dira daga kan gadon tana mishi dariyar yadda yaso ya sake damkota ta zulle. Sai a lokacin ya buɗe idanunsa gaba ɗaya yana kallonta da murmushi kaɗan a fuskarsa. "Ke ko? Za mu haɗe ne yarinya" Ta kuwa sake kyalkyalewa da dariya sannan ta faɗa banɗaki. Don ma kada ya biyo ta, sai ta murza makulli ta kulle ƙofar. Aikuwa tana cikin haɗa ruwan wanka ta ji ana kokarin turo kofar, tayi murmushi kawai tana mamakin rashin kunya irinta Abban Imam. Ko da asubahi duk yadda ta kai ga zullewa shi yayi mata wanka tsaf ya gargasa mata jiki, daƙyar ya barta tayi wankan tsarki bayan ta bashi tabbacin za ta iya yi da kanta. Daga can waje ya fara mata magiya yana roƙon ta buɗe mishi kofar, tayi mirsisi kamar ba ta jin shi. Don ta san idan ya shiga ba lallai ya barta ta shirya akan lokaci ba. Kuma yadda ta ji su Anty Balira suna fadin sammako za suyi gurin tafiya gida tasan lallai babu jimawa za su dira a gidan don yi mata sallama. Don haka ta kyale shi. Ya gaji da magiyarsa ya tafi dakinshi yana maimaita mata za ta sani ne idan suka haɗu. Ta sake shiga ruwan zafi sosai ta zauna a ciki kamar yadda Anty Balira tayi ta jaddada mata. Bayan ta gama wankan kuma ta samu man zaitun mai kyau ta shafe yammatancinta da shi. Kwalliya sosai tayi cikin ɗinkin shadda surfani ƴar kasar Mali. Zama a group ɗin Aunty Hibbah yasa ta iya ɗaurin ɗankwali iri-iri, ko da ta kalmasa, ta lanƙwasa, ta cokara ɗaurin sai ta fito a amaryar sak! Da angon ya ganta kasa ɗauke idanunshi daga kanta yayi. Banda direba da ya kai musu abinci ya katse shi a lokacin, da lallai sai Ango Kamal ya saka ta sake sabuwar kwalliya, wataƙila ma har da sabon wanka. Haɗaɗɗen dahuwar naman kan rago da yaji kayan ƙamshi kuma yayi romo sosai aka kai musu da wainar farar shinkafa. sai ruwan tea mai kayan ƙamshi a cikin flask da biredi da sultan chips. Zulaikha dai tunda ta zuba naman kai da uban romo shi taci tayi ƙat! Sai da ya tilastata da rarrashi da ban baki sannan ta ci wainar kaɗan. Bayan sun gama duk yadda tai ta hana shi ƙiyawa yayi, shi ya taya ta suka gyara wajen tsaf, ta jona burner ta zuba turaren wuta, nan da nan falon ya ƙara gamewa da ƙamshin turare mai daɗin ƙamshi. Bayan sun ɗauraye farantai da kofunan da suka ɓata jan ta yayi suka zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon suna hira mai daɗi, ga kuma TV a kunne suna suke kallo jefi-jefi. Cikin ɗan kankanin lokacin Zulaikha ta fahimci Kamal mutum mai son haɗa jiki da iyalinshi. Shi dai duk wani abu da zasu yi, to sai ya ji ta a cikin jikinshi. Idan cin abinci ne, hannunshi cikin nata, idan zama ne, sai ya jata cikin jikinshi, idan kwanciya ce, sai ya dangana jikinshi da nata. Tun tana dari-dari tana jin kunya, har ta sadakar ta hakura. Don kuwa bata ga alamun zai daina hakan ba. Su Anty Balira basu je gidan ba sai bayan sallar azahar, nan din ma a tsaitsaye suka musu sallama suka tafi, saboda direbobin da za su mayar da su suna jiransu a waje. Bayan abin arzikin da Mummy ta haɗa su da shi, har da wanda za su kaima Innaye, Baffa, da kishiyoyin Innaye haka Kamal ya musu sha tara ta arziki. Sun bar garin Abuja bakunansu har kunne, babu abinda suke faɗa sai son barka da fatan alkairi. Sun gama tabbatar da cewa Zulaikha dai ta yi dacen abokin zama da surukai na gari. Bayan tafiyarsu duk yadda yaso ya zauna a gidan hakan ya gagara, saboda baƙi da suka cigaba da zuwa ta ɓangaren danginshi, da iyalan gidan Abba Lukman waɗanda suka je ƙwansu da ƙwarƙwatansu don ganin gidan Amarya. A dole ya yi sallama da amarya ba don ranshi ya so ba ya tafi wajen abokanshi dake ta aikin kiranshi a waya tun safe. Yanayin baƙin da suka dinga yi akai-akai yasa bata samu kanta ba sai can bayan La'asar sosai. Gidan ya rage daga ita sai Mashku da Karima, suna ta mata shakiyanci. Su din ma ana yin magriba da direba ya kai abinci, suka mata sallama suka tafi. Sai lokacin ta samu ta zauna ta kira Innaye suka gaisa, taji cewa yan tafiya sun isa tuni. Bakin Innaye har kunne saboda murna da jin farincikin yadda kowa yake yabon halin da suka bar diyartata a ciki. Ita ma Zulaikha da murnarta take ƙara jaddada ma Innaye tana lafiya kuma tana cikin farin ciki. Sun daɗe suna hira, Innaye tana ta jaddada mata tayi haƙuri dai, don zaman aure sai da haƙuri kafin suka yi sallama. Tana katse kiran ta shiga cikin messages ta fara maidawa angon nata amsar sakonnin da ya tura mata, bayan kiranta da ya dinga yi a waya akai-akai duk bayan awa guda sai ya tura mata saƙon yadda yake son ta da yadda yayi kewarta, tun tana tsayawa mayar mishi da martani har dai ta fahimci abin ba na ƙare bane ta ajiye wayar ta cigaba da hidimar baƙinta. Tana gama mayar masa da martanin zaƙaƙan kalamai ta faɗa wanka. Kafin tafiyar su Karima sai da suka gyara mata gidan ƙal suka kunna turaren wuta, shi yasa bayan tafiyarsu wanka kawai tayi tai sallah ta tsantsara kwalliya ta zauna zaman jiran dawowar angonta. A gefe guda kuma tana cikin matsananciyar fargaba na yadda darensu na yau zai kasance, domin bata manta azabar da ta sha daren jiya ba. Wajajen karfe takwas na dare ya shiga gidan tare da zugar abokanshi. Nan suka zauna suka sha shakiyancinsu, suka ɗora da nasiha da addu'a da fatan zaman lafiya, kafin suka yi ma Amarya kyautar manyan kuɗaɗe da cewar na bakin da basu siya ba sannan suka musu sallama suka tafi. Yana kallon yadda take tafiya tana wani dingishi da kanainayewa wai ita ala dole bata da lafiya. Har wani magana take yi kasa-kasa, motsi kadan sai ta taba gefen wuyanta ta ce "Wash!" Ba tare da gajiyawa ba yake ta jera mata sannu cike da tarairaya, ko abinci a baki ya ciyar da ita yana haɗa mata da rarrashi, a zuciyarshi ko dariya yake mata, don shi kaɗai yasan irin alwashin da ya ciwa dare na biyun nan. Ƙarfe goma na dare, ya samu kiran Oganshi yana tambayarshi wasu documents da shi Kamal ɗin ya haɗa tun sati biyu da suka wuce. Umarni yai mishi cewar ya tura mishi documents ɗin a daren, zai yi wani aiki a kansu. Da ƙwarin gwuiwarshi ya amsa da Ok Sir! Amma wani abin haushi da takaici a gare shi shi ne ko da suka gama wayar, ya duba cikin ɗakinshi da nufin ɗaukar Kwamfutarshi sai bai gani ba. Nan ya gane ya barta a can ɓangarenshi na gidan Mummy. Agogo ya sake kallah a karo na biyu, goma da kusan rabi na dare. Wayarshi ya ɗauka da nufin kiran Karima ya umarci ta ɗauko Kwamfutar a ɗakinshi ta ba direba ya kawo mishi amma sai yaji wayarta a kashe. Ko da ya kira Mummy kuma wayar tai ta ringing bata ɗaga ba, haka ma lambar Hajja. Da damuwa a fuskarsa ya kalli Zulaikha yana faɗa mata ƙila fa dole sai ya tafi can gida a daren nan. "Ayya mana Abban Kamal... Ni kaɗai za ka bari a darennan? Don Allah ka tafi da ni mana..." "Keh! So kike Mummy tayi min faɗa ta ce na fara yawo da ke tun yanzu..." "Don Allah!" Ta fara mishi magiya a shagwaɓe. "Ai baza ta san tare da ni kaje ba. Ni da kawai muna shiga zan wuce ɓangarenmu na can gidan in ɓuya, idan ka gama abinda za kayi sai mu dawo." Shi kanshi ba ya son barinta ita kaɗai, don haka bai ƙara ja da nisa ba yace ta sako hijabinta su tafi. ******* ******* "Laaa'ilaha illallahu muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wa-sallam! Na shiga uku ni Ta rasulu!! Waye anan??" Hajja ta jero salati da maganganun cikin ɗaga murya da firgici, hannunta dafe da ƙirji, idanunta a warwaje alamar tsorata ƙarara. Da yake barcin nata raba da rabi ne, baiyi nisa ba, ga kuma firgici da tsoron da zuciyarta ke ciki. Hajja na fara salatin ta buɗe idanu a firgice tana kallonta. "Hajja... Nnnnni ce fa... ni ce.. Zulaikha ce." Tayi maganar cikin rawar murya. Duk da muryarta da Hajja ta shaida, bata gasgata da gaske ita ce ba sai da ta kunna ƙwan lantarki mai haske ta ganta ra'ayil aini. Domin ƙara share tantamar ita ce ko ba ita ba sai da Hajjan ta sake cewa "Zulai? Da gaske ke ce nake gani anan ko gizo idona ke min?" Tayi mata tambayar zuciyarta cike da mamakin abinda zai kawo Zulai da take Amarya ɗanya shakaf cikin gidan kuma cikin falonta a irin wannan lokacin da dare ya fara tsalawa, Zulai dai da jiya ne aka kai ta gidan Kamal matsayin matarsa. "Ni ce Hajja." Zulaikha ta amsa a marairaice. Idanunta ciccike da ƙwallah. "Ikon Allah!" Hajja ta faɗa hannunta ɗaya riƙe da haɓa. Kafin Zulaikha ta ce wani abu ta sake jefa mata tambayar "To me ya kawo ki gidannan? Kuma har kika shigo falo na a irin wannan lokacin na talatainin dare? Ca nake jiya ne yayyinki suka kai ki ɗakin miji?" Mar-mar tayi da ƙwayoyin idanunta, wasu ƴan ƙananun ƙwallah suka gangaro, da rawar murya ta ce "Hajja don Allah ki barni in kwana anan. Wallahi ni tsoron can nake ji. Mun zo ne fa tare da Abban Imam zai ɗauki kwamfurarshi da ya manta, shi ne ni kuma na gudo gurinki." Cikin ƙasa da mintuna biyu Hajja ta gano abinda ke faruwa. A zuciyarta ƙara gamsuwa da irin tarbiyar da su Innaye suka ba Zulai tayi, lallai ita ɗin rainon ƙauye ce, da aka hore ta da kunya da rashin rawar kai ba irin wasu ƴan matan na yanzu ba. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta taka sannu a hankali ta ƙarasa inda Zulaikha ke kwance bisa kujera mazaunin mutum uku ta zauna kusa da ita. A tausashe ta fara mata magana da sigar rarrashi. "Haba Zulai, a ina kika taɓa ji an ɗaura ma yarinya aure a darenta na biyu ta gudo ta bar angonta shi kaɗai ? Kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki. Ko wace mace da haka take sabawa kin ji ko?" A raunane kuma a tsorace ta ɗaga kai, alamar ta ji. "Kuma ma Abban Imam ɗin ki ne fa, ko kin manta halayensa ne na haƙuri da kawar da kai? Kin manta irin matsananciyar soyayyar da yake miki ne? Na tabbata a irin kyawawan halayen Kamalu da na sani bazai taɓa yin wani abu don ya cutar da ke ba. Ko so kike tun a daren nan ki fara dasa mishi tunanin wata ƴa mace a zuciyarsa?" Da sauri ta girgiza kai, tana jin yadda ƙirjinta ya buga daram saboda kishi daga jin saɗarar maganar Hajja ta ƙarshe. "To in dai bakya so hakan ta kasance ya zame miki dole ki jure, ki daure, ki kwantar da hankalinki ki faranta ma mijinki rai a wannan dare da sauran dararen da za su biyo baya. Yanzu ina shi Kamalun?" "Yana can" Ta amsa daƙyar! Kamar wacce aka shaƙewa maƙogwaro. "Tashi maza muje in raka ki gurin mijinki. Kuma kar ki kuskura ko da wasa ki ba Karimatu ko wata labarin abinda ya faru. Kin ji?" A karo na uku kai ta sake ɗagawa. Sannan ta miƙe tsaye jikinta a sanyaye ta bi bayan Hajja suka fice daga ɗakin. Wani abin mamaki shi ne suna fita daga ɓangaren Mummy suka hangi Kamal tsaye a ƙofar ɓangarensu yana ta safa da marwa, bisa ga dukkan alamu ba shi cikin nutsuwarsa. "Kin ga irin damuwar da kika jefa mijinki a ciki ko? Ki tabbatar kin bashi haƙuri bayan tafiyata. Kar ki sake aikata irin wannan shirmen ko ba yanzu ba, domin mazajenku na yanzu ba irin namu na da bane. Tun yana lallaɓa ki yana bin ki a hankali kina botsarewa sannu a hankali zaiyi watsi da lamarinki ya fara nema ma kansa mafita..." Maganganun Hajja sun ɗauke ne bayan Abban Imam ya ƙaraso gurinsu da sauri. Sai da ya isa, sai kuma kunya ta kama shi, ja yayi ya tsaya yana ɗan sosa ƙeya cikin kunya. "Hajja Afuwan! Ta taso ki ko?" Duk yadda Hajjan taso cijewa sai da dariya ta ƙwace mata ganin yadda yake ta sussunne kai, kamar ba Kamal ɗan bokon nan da bai cika jin kunyarta ba. "Kai dai ɗauki matarka ku tafi. Na yi mai wuyar tunda na dawo maka da ita. Amma dai kar ka manta, matarka ba irin ƴanmatannan bane masu buɗaɗɗen idanu da suka san me ke cikin rayuwar aure tun kafin su shiga cikinta. Bayan haka kuma girman jikin ne kawai, amma yarinya ce ƙarama. Ka bi ta sannu a hankali, kayi haƙuri da duk shirmen da za tayi maka. Allah ya bada zaman lafiya." Bata jira amsawar ɗaya daga cikinsu ba ta juya za ta shige cikin falon Mummy. "Amma dai ina fatan ba a cikin talatainin darennan za ku koma can gidanku ba?" Ta tambayi Kamal tana daf da shigewa cikin falon. "A'a Hajjah. Dare ya riga yayi. Gobe dai da asubah in sha Allah za mu tafi don kar Mummy tayi faɗa." Kamal ya amsa a nutse. "Ba laifi. Allah ya tashe mu lafiya." "Amin." Kamal ya amsa da ɗan ƙarfi yadda za ta ji shi. Bayan shigewar Hajja, tsayuwar daƙiƙu sittin suka ƙara a gurin, shi yana kallonta da karantar yanayinta, ita kuma tana kallon ƙasa, gaba ɗaya jikinta a tsarmame, kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi aka tsamo. "Kayi haƙuri Abban Imam" Ta karya shirun da faɗin haka, muryarta na ɗan rawa, a kunyace. Bai ce komai ba. A madadin yayi magana ma sai hannunsa ya miƙa a hankali ya kamo hannunta. A fili take jin yadda yake sauke ajiyar zuciya sauri-sauri, ya daɗe a haka, kafin ya ɗaga hannunsa da ke riƙe da nata ya ɗora a ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa. "Allah ya sani ina tsananin son ki Zulaikha. Ina son kasancewa tare da ke a wannan dare. Amma idan kin fi son kwana a gurin Hajja zan ɗaga miki ƙafa... Har zuwa sadda ke da kanki za ki ji a ranki kina son kasancewa tare da ni. Kin amince? In mayar da ke gurin Hajja?" "A'a!" Ta amsa da sauri. Kafin yayi magana ta sake cewa. "Kayi haƙuri." Cikin sanyin murya. A hankali kuma ta ɗaga kanta ta saci kallonsa, karaf! Idanunta suka faɗa cikin nashi. Ya sakar mata lallausan murmushi. "Kin amince da ni? Mu tafi ɓangarenki mu kwana da asuba mu koma can gidanmu?" Ya tambayeta a tausashe. "Eh! Na amince." Ta amsa a hankali, a zuciyarta take ta ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ma kanta gwuiwa tana yaƙar tsoron da ke danƙare da ranta. Ɗan shiru yayi, sai kuma ya sake cewa "Baza ki sake guduwa gurin Hajja ki barni daga shiga cikin ɗaki ba ko?" Kunya ne ya kamata. Hannunta ɗaya da bai riƙe ba ta ɗaga ta rufe fuskarta tana dariya ƙasa-ƙasa, a zuciyarta take tuna abinda ya faru har ta gudu ɗakin Hajja. 'Sai da suka gama shan madarar holandiya mai sanyi sosai da ya ɗauko a cikin frig. Bayan ya gama kwashe kofunan da suka ɓata yakai kicin. Ya dawo ya ce mata bari yaje ɗakinsa ya ɗauko abu sai su tafi, har yana bata tukwuicin sumbata saboda duk yadda yayi da ita su shiga cikin ɗakinshi ko nata ta ƙiya. Yana shiga ɗaki, ita kuma ta gudu cikin gidan ta shige ɗakin Hajja...' Maganarsa ne ya katse mata tunanin da take yi. "Kin san fa ɗazu ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba bayan fitowata cikin falo ban ganki ba." Hannunta yaja suka fara takawa a hankali zuwa ɓangarensu, lokaci ɗaya kuma yana cigaba da yi mata bayanin irin damuwar da ya shiga bayan nemanta da yayi ya rasa a cikin falon. "Bayan duba ki da nayi tayi lungu da saƙo har ƙarƙashin gado da cikin durowa da cabinet na kicin ban ganki ba. Afujajan na fito ina duba ki a harabar gida, binciken inda kika shige bayan dube-dube lungu da saƙon fulawoyi ni ne har gurin mai gadi ina tambayarshi ko ya ga fitar ki? Da mamaki sosai a fuskar Baba maigadi ya tabbatar min babu wacce ta fita a darennan. Na yi yunƙurin zuwa ɓangaren Mummy ya fi sau hamsin amma sai in kasa, tunda bata san mun zo gidan ba. Kuma bayan haka Kin san miye tunani da fargabata?" Girgiza kai tayi. Kafin ya cigaba da cewa "Idan na shiga duba ki me zan ce musu? Kin fita ba da sanina ba? ko kuma wani abu nayi miki kika gudu don ceton kanki? Kin dai san halin Mummy da tambayar ƙwaƙwaf. Da waɗannan dalilan yasa nayi fakare a ƙofar ɓangarenmu kamar maraya, daga bisani kuma na fara safa da marwa tsakanin ɓangarenmu da na Mummy, zuciyata cike da addu'ar duk inda kika shige Allahu yayi gaggawar bayyana min ke. Sai kuma ga shi da yake Allah maji roƙon bawa ne, ya tausashi zuciyar Hajja ta fito min da ke a lokacin da ban taɓa tsammani ba." A daidai lokacin suka isa ƙofar ɓangarensu, da hannu ɗaya ya tura ƙofar, kasancewar har lokacin hannunsa na dama na sarƙafe da hannunta na hagu. "Kar dai ki manta, ki yi Bismillah! Don kore shaiɗanin da ya fara zuga ki ki gudu ki bar mijinki." Ya faɗa idanunsa na cikin nata. A tare duk su biyun suka yi murmushi. Suka ɗaga ƙafafuwansu na dama lokaci ɗaya za su shigar, kamar haɗin baki kuma a fili suka ambaci Bismillahirrahmanir raheem. A karo na biyu lallausan murmushi suka sake haske junansu da shi kafin suka shigar da ƙafafuwansu na hagu. Har lokacin yana riƙe da hannunta ya mayar da ƙofar ya rufe, ya murza ɗan makulli, yaja hannunta suka nufi cikin ɗakinsa. "Kiyi haƙuri. Ɗazu na tsorata sosai, kar in barki a falo ko in shigar da ke ɗakinki ki sake tafiya ki barni..." "Bazan sake ba. Kayi haƙuri." Ta katse shi a marairaice tun kafin ya aje numfashin maganarsa. "Na yi! Amma duk da haka bazan kai ki ɗakinki ba. Ɗaki na za mu je, domin can ɗin ma kamar naki ne, akwai komai da za ki buƙata a ciki. Na san kina jin barci ko?" "Eh! Ina ji." Ta amsa a hankali. Zuciyarta cike fal da fargabar da take ta ƙoƙarin dannewa kar ya bayyana a fili. Ko da suka shiga cikin ɗakin a gefen faffaɗan gadonsa ya zaunar da ita, cikin lallaɓawa da tarairaya

Chapter 28 of 40