Share this page
fara jan shessheƙar kuka kamar yadda ta saba, tana yi tana taushe bakinta don kar Mashku ta ji kukan da take yi. A karo na farko, tun bayan faruwar al'amarin da tsawon dararen da ta kwashe tana raba biyu bisa uku da kuka Mashkura ƙanwarta da suke kwana ɗaki ɗaya tayi mata magana a tausashe. "Aunty Bintu a ganina kukan nan da kike kwashe tsawon lokaci kina yi ko wane dare, ke baki yi barci ba, ni baki barni na yi nutsattsen barci ba bazai taɓa miki magani ba. Why not baza ki ɓata lokacin kukan akan dadduma kina kaima mahaliccin sammai da ƙassai kukanki ba...?" "Mashku... Don Allah ki faɗa min. Aduk cikin wannan al'amarin ina abin saki? Me nayi ma Hafiz da zai sake ni? Me nayi masa?" Ta katse Mashkura da jerin tambayoyin muryarta na fita da matsanancin kuka. Abu ɗaya da Mashkura ta fahimta a maganganun Bintu shi ne har yanzu ita bata yi da na sanin abinda tayi ba. Kamar ma laifin ɗungurungum ta kwashe ta ɗora kan Hafiz ne da danginsa, bayan kuma ita ke da laifi kaso casa'in da biyar bisa ɗari. Kafin ta amsa ɗaya daga cikin tambayoyin Bintu, lalubawa tayi a kusa da filonta ta ɗauko wayarta ta duba lokaci, ƙarfe uku da minti arba'in na dare. Barci ne sosai a idanunta, don haka ta katse dogon maganar da Bintu ke neman jan ta da shi ta hanyar cewa "Uhmmm! Ba ni da amsar ɗaya daga cikin tambayoyinki Aunty Bintu. Ni dai shawara kawai na ba ki, da ki dinga ɓata tsawon lokaci kina rusa kukan da bazai miki magani ba, gara ki dinga ɗaukan lokacin kacokan kina kai ma Allah kukanki. Ko babu komai za ki samu sanyin zuciya da nutsuwa. Allah ya tashe mu lafiya." Daga haka bata sake ce mata komai ba ta juya mata baya. Da yake Bintu ba ta daga cikin irin matannan da ibada ya dame su, duk da wannan shawarar da ƙanwarta ta ba ta bata yi amfani da shi ba. Sharɓen Kukanta ta cigaba da yi, tana haɗa da jan ajiyar zuciya tana saukewa, ta ɗauki tsawon lokaci a haka har zuwa sadda gwanin iya sata da taimakon shaiɗan yayi awon gaba da ita, lokacin ana ta kiraye-kirayen sallah a wasu masallatai. Washe gari, kamar yadda Raudha ta saba zuwa gidan duba jikin Bintu duk bayan kwana biyu, misalin ƙarfe huɗu na yamma tayi ma gidan dirar mikiya. A waɗancan kwanakin, duk zuwan da take yi bata taɓa samun damar yin nutsattsen hira da Bintu ba. Cikin kuka ta faɗa mata Hafiz ya sake ta, sannan kuma zai ƙara aure. Daga haka har ta bar gidan ba ta ƙara samun kan Bintu balle har suyi wata doguwar magana, sai dai ta gama zamanta da maɗaukakin damuwa a fuskarta daga bisani tayi ma Umma sallama ta tafi. A yau, ko da ta isa gidan ta yi mamakin samun Bintu cikin ƴar nutsuwa kaɗan. Ta yi wankanta tsaf, duk da dai babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta. Wayarta ne ma a hannunta tana dannawa, fuskar nan a ɗaure tamau. "Raudha... Ashe don tsabar wulaƙanci tun ranar da muka je Faƙo misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma Hafiz ya turo min saƙon saki ta text message..." "Da gaske kike yi?" Raudha ta jefa mata tambayar da mamaki a murya da fuskarta. Bata iya amsawa ba, sai wayar ta miƙa mata tana nuna mata saƙon. "Uhmmm! Allah ya kyauta... Sai haƙuri kawai." Raudha ta faɗa jikinta a sanyaye, bayan ta gama karanta saƙon. "Ni yanzu kin san menene damuwata?" "A'a! Sai kin faɗa!" Raudha ta amsa mata. "Wace ƴar iskar matsiyaciya tsinanniya annamimiyar yarinyar ce za tayi gangancin aura min miji uban ƴaƴana? Duk tunanina ya ƙuƙe, na rasa gane wace Karimatu ce? Ko dai wata baƙauyiyar ce matsiyatan danginsa da basa ƙaunar Allah da Ma'aiki SAW suka sake haɗa shi da ita..." "Uhmmm! Za kiyi mamaki idan na ce miki Nurse Karima ce, ƴar gidan Hajiya Saudah da kike kira Mummy sama Mummy ƙasa..." "Mmmmm.... me kika ce Raudha? Dddddddda gaske kikkkkkkkeeee yi?" Bintu ta tambayeta da wata fitinanniyar in'ina a muryarta saboda tsananin tashin hankali. "Wallahi da gaske nake yi. Lamarin maza ba sai dai a barsu ba Bintu? Abinda ya kawo ni gidanki kenan ranar sai na tarar da ke cikin tashin hankalin ɗauke Aadil da Hafiz yayi." Gyara zama Raudha tayi, ta kora ma Bintu labarin duk abinda ya faru wancan ranar a asibitinsu gaban idanunta. "Karima dai Raudha? Karima? Yanzu sakayyar da Mummy za tayi min kenan? Ni ce fa na shiga na fita har na sama mata aiki a asibitinmu, ashe sakayyar da za suyi min kenan?" Ta jera ma Raudha tambayoyin cikin rawar murya da tashin hankali. Kafin Raudha ta amsa ta cigaba da cewa "Saboda Allah me Karima take da shi wanda ni bani da shi da har za ta ɗauki hankalin Hafiz..." "Uhmmm! Bintu kenan! Sau nawa ina faɗa miki Namiji ɗan kunama ne ga zaƙi ga harbi kina saka auduga ki toshe kunnenki? Ko da yake yanzu da layi ya biyo ta kanki ai za ki ƙaras a gaba." Raudha ta katse mata sambatun da take yi hankalinta a tashe kamar wacce ƙwaƙwalwarta ya fara taɓuwa. "Bar tuna min Raudha! Don girman Allah ki bar tuna min." Bintu ta katse ta da sauri, da murya mai bayyana matsanancin takaicin da zuciyarta ke ciki. Babbar yatsarta ta sanya ta ɗauke wasu zafafan hawaye da suka sake taruwa a kwarmin idanunta. Da asubahin ranar tasha alwashin in Allah ya yarda za ta danne zuciyarta baza ta sake yi ma wannan mummunan al'amarin kuka ba, amma duk yadda ta so tsayar da fitar hawayen ta kasa, shi yasa take saurin share hawayen tun kafin su gangaro zuwa kumatunta su saka ta azumin kaffara. Nannauyar ajiyar zuciya ta ja ta sauke, a hankali ta cigaba da cewa "Abinda ya wuce mu barshi a matsayin wanda ya wuce Raudha. Ilimi ɗaya da na ƙaru da shi a cikin kwanakinnan shi ne, duk mazajen duniya halayensu ɗaya, kuma a kullum sauyawa suke yi kamar wahainiya. Lallai da gaske ne duk matar da ta ɗauki namiji uba za ta mutu marainiya... Yanzu dai mafita nake nema da gaggawa... Ya zanyi Raudha? Ya zanyi? Wallahi zuciyata zafi da tafarfasa take min kamar za ta babbake... Don Allah ki taimaka min" "Kul! Kul!! Kul Bintu!! Kar ki kuskura ki bari zuciyarki ta buga akan namijin da idan kika mutu yau, ya yi tsananin daɗewa ne yayi wata shida zai manta da shafinki ya buɗo na wata kamar yadda yake shirin faruwa da ke a yanzu." Ta yi shiru tana mayar da numfashi, sannan ta cigaba da magana a hankali, tana yi tana waige-waige, alamun duk abinda za ta faɗa ba ta so kowa ya ji "Akwai mafita... Amma sai kin nutsu sosai kin saurare ni da kunnen basira..." Jikinta a sanyaye ta tari numfashin Raudha da cewa "Allah yasa dai mafitar ba na bin hanyar da Hajiya Rabi ta faɗa min rannan bane." Sai da Raudha tayi dariya sannan ta amsa da "Wannan old version kenan ai. Ita ma don tsohuwar yayi ce shi yasa har yanzu take ganin idan ba ta hanyar malamai da bokaye da ƴan tsibbu ba babu hanyar da za ta bi wajen ladabtar da ƊA NAMIJI har yayi laushin da zai rusuna mata..." Fitowar Mashkura daga banɗaki, wacce shaf Bintu ta manta da shigarta daf da Raudha za ta shigo cikin ɗakin, shi ya katse Raudha daga maganganun da take yi masu ɗauke da zallar cika baki. A tsorace suka kalli Mashkura, itama ta ɗaga idanu tayi musu wani kallo mai bayyana ƙasƙanci ƙarara. Sannan ta ɗauki hijabin sallarta ta zura a jikinta ta fice daga ɗakin. Da damuwa sosai a fuskar Raudha ta ce "Na shiga uku ! Amma dai Bintu baki kyauta min ba. Me yasa tun ɗazu baki faɗa min Mashkura tana bayi ba kika barni ina ta zuba zance? Allah dai yasa bata ji maganganun da nake yi ba..." "In Allah ya yarda ma bata ji ba. Wallahi sam na manta ta shiga wanka sadda kika shigo, kuma kin santa da bala'in daɗewa gurin wanka kamar wacce za ta canja halitta. Yanzu dai ina ga ki tashi kawai ki tafi, ma ƙarasa zancen da muka fara yi a waya..." Numfashin maganarta ne ya ɗauke ɗif lokacin da Ummansu ta shiga cikin ɗakin da wata iriyar murtukakkiyar fuska, kamar bata taɓa dariya ba. A ɗarare duk su biyun suka kallete da yanayin rashin gaskiya. Da saurin gaske Raudha ta yayimi jakarta da mayafi ta miƙe tsaye. "Bintu bari in wuce, sai na sake leƙowa..." "Ki leƙo ina Raudha?" Ummansu ta tambayeta cikin tsawa. "Munafuka algunguma, dama ke ce kike hure mata kunne har kika hana ta zama gidan mijinta bayan ke kina naki gidan?" Cikin rawar murya da in-ina Raudha ta fara yunƙurin kare kanta. "Babbbbbbaaaa haka bane Wallahi Umma..." "Idan ba haka bane to yaya ne? Saurareni ki ji da kyau!! Daga yau, na raba ki da Bintu tunda dai ke ba ƙawar arziki bace. Idan kuma kika bari na sake samun labarin kin zo gurinta, ko kuma ita taje gurinki har a ganku tare, ko kuma ki kirata a waya ko ita ta kira ki na rantse da Allah da Aliyu zan haɗa ki. Kuma kin san halinshi sarai, don ya bi ki har gidan mijinki ya hukunta ki ba abinda ya dame shi bane. Ɓace min da gani munafuka kawai." Sum-sum Raudha ta fice daga ɗakin kanta a ƙasa, hankalinta a ɗugunzume, ko ƙwaƙƙwaran kallo ta kasa ɗaga idanu tayi ma Bintu balle mahaifiyarta. Har ta fita daga ɗakin, Bintu ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa yi, tsumu tayi a zaune inda take kamar kazar da aka tsamo a cikin ruwan zafi. Hankalinta a tashe ainun, miyaun bakinta ya ƙafe ƙaf! Ta rasa wasu irin kalamai ne ya kamata tayi amfani dasu gurin ba Ummansu haƙuri. "Ke kuma na dawo gare ki! Sakarya! Wawuya!! Shashasha!!! Wacce duk irin shekarun da tayi a duniya bata san inda yake mata ciwo ba." Mahaifiyarta ta katse mata tunani da faɗin waɗannan maganganun cikin matsanancin fushi da ɓacin rai. Kafin ta buɗe baki tayi magana Umma ta cigaba da cewa "Ba ni da lokacin ɓatawa wajen baki shawara Bintu, saboda kin daɗe da goge min hadda, kin yi abinda ban taɓa tsammanin ko rabi-rabinshi za ki aikata ba. Abinda ya faru yasa na daɗe da yanke tsammani a kanki Bintu. Magana ɗaya zuwa biyu zan faɗa miki a yanzu, idan kin so ki bi, idan baki so ba za ki iya aikata duk abinda ya kwanta miki a rai. Ni kuma za ki ga abinda zan aikata a matsayina ta wacce tayi naƙudarki zuwa duniya. A matsayina na mahaifiyarki, daga yanzu har zuwa nan gaba ko da wasa kika yi yunƙurin aikata wani abu, ko sakawa a aikata wani abu da zai cutar da Amaryar Hafiz, ko shi kanshi Hafiz ɗin, ko auren da yake yunƙurin yi ban yafe miki ba.!" A haukace Bintu ta ɗago kai, jikinta babu inda ba ya rawa, daƙyar ta iya buɗe baki ta ce "Umma..." Da saurin gaske Umma ta ɗaga mata hannu alamar dakatarwa. "Magana ta biyu shi ne idan kika sake zuwa gurin Raudha, ko kiranta a waya, ko ita ta kira ki a waya kika ɗauka har kika yi amfani da ɗaya daga cikin munanan shawarwarin da take baku ban yafe miki ba. Na ga kamar dusa ne a ƙwaƙwalwarki, dole sai ana yi ana taka miki burki ƙarfi da yaji. Sakarya kawai." Da gama faɗin haka bata tsaya saurararta ba ta fice daga ɗakin, bayan ta ja wani dogon tsaki kamar bakinta zai taɓa ƙasa. Ta fita ta bar Bintu cikin wani mawuyacin hali na tashin hankali. Zuciya da ƙwaƙwalwarta a tsaye cak! Ta ma rasa wani irin tunani ya kamata tayi? ******* Labarin sakin da Hafiz yayi ma Bintu, abu ne da ya zama a sirrance ta ɓangaren Hafiz ɗin. Ko da wasa baiyi gigin faɗa ma wani daga ɓangarensa ba, hatta Zulai da a yanzu suke very close da ita. Bayan sati biyar da faruwar al'amarin ne Mahaifin Bintu ne ya kira Alhaji Lurwanu yake mishi ƙorafi kan yadda bai kira shi a waya ya jajanta mishi kan abinda ya faru ba. Mamaki mai girma ne ya kama Alhaji Lurwanu, da takaici sosai a muryarsa yake nuna damuwar yadda Hafiz ɗin ya iya sakin Bintu ba tare da ya kai mishi ƙorafinta ba. "Uhmmm! Shi fa Hafizu ba shi da laifi Alh Lurwanu. Gaba ɗaya laifin na Bintu, kuma ko ni ne a matakin da yake kai iya hukuncin da zan iya ɗauka kenan zuciyata tayi sanyi-sanyi." Ba tare da ɓata lokaci ba ya kora ma Alh Lurwanu bayanin duk abinda ya faru. "Ikon Allah! Amma kuwa in dai haka ne Bintu bata kyauta ba. Sai dai kuma shi Hafizu kamar ya yi gaggawa gurin sakinta. A sanina akwai hanyoyi da dama na ladabtar da mace, saki shi ne mataki na ƙarshe-ƙarshe bayan duk an bi waɗancan hanyoyin an kasa cimma matsaya. Amma Alh Aminu (Baffa) ya sani kuwa?" "To gaskiya ba na jin shi ma ya sani, don dai bai kira ni ba. Ko kai ɗinma dalilin da yasa na kira ka ganin yadda Bintun ta kasa haƙura ta rungumi ƙaddara ne. To ya zanyi? Hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar Lurwanu. Duk da dai ita ce ba ta da gaskiya, kuma har yau na kasa nuna mata a fili ina tausaya mata. A can ƙarƙashin zuciyata ina jin zafin yadda ta lalace, ta ƙare, ta shiga cikin halin ƙaƙa-ni-kayi. Ko gurin aiki fa ba ta iya zuwa, a yanzu idan ka ga Bintu na rantse ba lallai ka gane ta ba. Don Allah idan da hali kayi wani abu akan lamarin..." "Yin wani abu ya zama dole Alh! Amma ina roƙonka alfarma ɗaya. Alfarmar kuwa ita ce don Allah yanzu muyi ma Hafiz uzuri, ka ga jibi idan Allah ya kaimu za'a ɗaura aurenshi... Muyi haƙuri, zuwa sati na sama idan mai duka ya kaimu da kaina zanyi takakkiya zuwa Ofis ɗin shi in ji ya za mu ɓullo ma al'amarin. Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah komai zai zo ya wuce..." "Ba damuwa Alh! Na gode." ****** Ta ɗauki tsawon mintuna goma sha biyu hawaye masu zafi na sauka daga kwarmin idanuwanta. Duk da hawayen da ke jerangiyar sauka daga idanunta, kallon fili da na idanun zuciyarta bai ɗauke daga kyakkyawan hoton free wedding pic na Hafiz da Amaryarsa Kareema ba. Zuciyarta ƙuna, raɗaɗi, zafi, azaba take yi mata, kamar za ta faso ƙirjinta ta fito don tsananin baƙin ciki da takaici. "Yanzu shi kenan? Tana ji tana gani za ta sadaukar da mijin da ta gama shan wahalar ɗawainiyarsa ga wata banza can da bata san darajarsa ba?" Ƙarin baƙin cikinta shi ne, Hafiz ɗin ne da kanshi ya saka kyawawan hotunan a status ɗin shi na whatsapp. "Yanzu shi kenan har Hafiz ya manta da babinta a rayuwarsa?" Yatsa ta saka, ta ƙara zumin ɗin hoton fuskarsa tana ƙara kallon wani masifaffen kyau da yayi. Dama can Hafiz mai kyau ne, kyawunsa na ɗaya daga cikin abinda yasa take mutuwar son Hafiz. Domin idan ba faɗa aka yi ba, irin kyawun Hafiz da gayunsa ko rantsuwa aka yi babu kaffara za a ce bai haɗa jini na kusa ko na nesa da mutanen ƙauye ba. *Assalamu alaikum* Ina yininku? Akwai set ɗaya na maganin mata wanda wani malami ya haɗa bisa amana. Amma don girman Allah ƴar'uwa ki ji tsoron Allah idan kin san ba kya fama da matsala tsakaninki da mijinki kar ki siya. Saboda maganin ya taɓo wani ɓangare na mallaka, wata ƴar'uwa ce da mijinta ke neman mata aka haɗa ma maganin. To kuma cikin hukuncin Allah sai auren ya mutu kafin isowar maganin, kun ji dalilin da yasa na tallata maganin. Kuɗin maganin 10k ne. Idan baki shirya ba don Allah kar ki taɓo ni ta pc. Maganin rashin haihuwa. Cutar sanyi na infection ko wani iri. Maganin cancer ko wane iri. Maganin wankin nono ga masu jego. Maganin sanyi na masu jego. Da sauran cututtuka in sha Allah muna da ingantattun magunguna na gargajiya akan farashi mai sauƙi🙏🏽 07039080978, 09077591726 "Yanzu haka za ta zauna ta naɗe hannu a ƙirji ta zura ido tana ji tana gani wata mace can da ba ita ba ta mallaki Hafiz bayan ita ta gama shan wahala da shi?" Ta sake tambayar kanta a fili. Lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki rawa kamar ana kaɗa mata ganga. Umarnin zuciyarta jikinta ya bi, ba don ranta yana so ba ta talubo lambar Hafiz ta danna mishi kira. Cikin ƙanƙanin lokaci wayar ta fara ringing daga can ɓangaren, ƙarar da yake bugawa kamar da sautin bugun zuciyarta. Daga can ɓangaren Hafiz, barci yake yi hankalinsa kwance. Sun shafe fiye da mintuna talatin suna hira da Kareema a waya tana ta zuba mishi shagwaɓa da ƙananun koke-koke. wacce rashin ganinta da baya yi kwanaki biyar kenan wai an ɓoye ta ana mata gyaran jiki, ko ya je sai dai ya gama hira da Zulai da Hajja yasa shi rage zuwa gidan, sai dai bini-bini kaɗan zai kira ta, ko kuma ita ta kira shi tayi ta ƙara rikita shi da zafafan kalamai na soyayya. Yana cikin nutsuwa ƙwarai, irin nutsuwar nan da shi da kanshi idan aka titsiye shi bazai iya tuna lokacin da yake cikin makamanciyar wannan nutsuwar ba. Bintu, da duk wani abu da ya shafeta ya tattara shi ya ajiye gefe ɗaya. Daman a gyaran gidan da yayi duk wasu abubuwa nata da suke cikin ɗakinsa ya tattara ya mayar mata da su ɗakinta. Idan ya kwanta, barcinsa yake kwasa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ko mafarki zaiyi na Karima yake yi, saboda ita ce a cikin zuciyarsa. Gaf da kiran zai tsinke, ya jiyo vibration ɗin wayar kamar a mafarki. Daƙyar ya iya miƙa hannunsa ya lalubo wayar, ba tare da ya duba mai kiran ba kawai ya ɗauka ya kara a kunne. Hafiz yana ɗaya daga cikin mutanen da suke da ɗabi'ar idan suka farka daga barci mai nauyi suna ɗaukar wasu sakanni kafin suyi magana. Don haka ko da ya ɗauki wayar, shiru yayi yana ɗan mayar da numfashi a hankali. Shessheƙar kuka da ya fara jiyowa yana tashi ƙasa-ƙasa ta cikin wayar yasa shi ƙarasa wartsakewa. Ya ɗan buɗe idanu kaɗan, sai kuma ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli fuskarta. Ganin Bintu ce akan layi yasa fuskarsa faɗaɗa da yanayin mamaki, mamaki na sosai, ba kaɗan ba fa. Abu ne da anan kurkursa bai taɓa tsammanin ganinsa akan wayarsa ba. Da wannan dalilin yasa dole yayi mamaki. Har ya ɗaga wayar zai katse, sai kuma wata zuciyar ta bashi shawarar ya ɗauka. Bai san me ke tafe da ita ba, kuma duk da sun rabu, ko don darajar ɗa da yake tsakaninsu ai an rabu ba'a rabu bane. Da wannan dalilin yasa shi mayar da wayar a kunnensa, haɗe da yin ɗan gyaran murya ƙasa-ƙasa. Gyaran muryar da ya tabbatar ma da Bintu yana saurarenta. "Hafiz... Yanzu shi kenan Hafiz?" Tayi maganar cikin rawar murya. Bata jira ya amsa ba ta cigaba da cewa "Saboda Allah ka yi min adalci kenan? Bayan duk rashin adalcin da kayi min ka rasa sakayyar da za kayi min sai na auren Kareema? Haba Hafeez! Kareema fa? Ƴar gidan Mummy Saudah, wannan local ɗin yarinyar... Bayan tozarcin auren kuma ka rasa sakayyar da za kayi min sai ta saki... Ina duk alƙawurran da kai min Hafeez?" Ta ƙarasa maganar haɗe da fashewa da wani ƙaƙƙarfan kuka da yake tahowa tun daga ƙarƙashin zuciyarta. A ɓangaren Hafeez kuwa da sauri ya cire wayar a kunnensa, saboda yadda sautin kukan ya dira a kunnensa da ƙarfi... Kamar tana barazanar fasa masa dodon kunne. Wani abin mamaki shi ne duk irin yadda ta jero maganganun da salon a tausaya mata, take kuma rusa kuka kamar ƙaramar yarinya, irin kukan da ya daɗe a fili ko a waya bai ji Bintu ta yi irinsa ba. Ko kaɗan maganganunta basu taɓa mishi zuciya ba, sai ma wani ɗan ƙaramin murmushi da ya suɓuce a fuskarsa, ya daɗe yana sakin lallausan murmushi kamar tana kallonsa, yana jin saukar kukanta a kunnensa kamar busar sarewa. "Bintu..." Ya kira sunanta a hankali, bayan ya ji ba ta da niyyar tsagaitawa a kukan da take yi. "Ki saurara da kukan nan muyi magana, idan ba haka ba Wallahi zan kashe wayata." Yayi maganar cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara. Ta sani tsaf zai aikata abinda ya faɗa, musamman a yanzu da ƙarfi da yaji maƙiyanta suka ci galabar cusa mishi tsanarta a zuciya. Don haka a sannu-sannu ta fara rage kukan har ta daina gaba ɗaya. Nannauyar ajiyar zuciya ya ja ya sauke a hankali, sannan ya cigaba da magana da wata irin murya mai bayyana rashin damuwa ko misƙala zarratin da halin da take ciki. "Kin ga barci nake yi fa... kiran wayarki ne ya tashe ni. Don Allah idan ba ki da abin cewa mai muhimmanci ki ƙyale ni in huta Bintu." Daƙyar ta iya riƙe wayar saboda tsananin kaɗuwar da tayi sakamakon jin irin kalaman da ke fita a bakinsa. Har ga Allah ta yi tsammanin kalaman rarrashi da ban hakuri ne za ta ji suna fita daga bakinsa. Wannan wane irin mummunan al'amari ne haka ya dabaibaye kyakkyawar zamantakewarsu? Gaskiya duk wanda yayi wani ƙulli don wulaƙanta tubalin zamantakewarsu baza ta taɓa yafe mishi ba... "Kina ji na?" Hafeez ya sake faɗa. "Ina tunanin sauƙaƙa miki nayi ta hanyar yi miki abinda kike so Bintu. Bazai taɓa yiwuwa mu cigaba da tafiya a haka ba, ke ma kin sani. Iyaye da ƴan'uwana sun fiye min kowa da komai a wannan duniya. Ke kuma babu wanda kika tsana sama da su, don haka na sama miki sauƙi ta hanyar yanke alaƙarki da mutanen da kika fi tsana a rayuwarki. Don Allah Bintu ki manta da ni, kamar yadda nima na daɗe da mantawa da ke. Na kama hanyar nemo wacce rayuwarta za tayi daidai da rayuwata ta baƙauye da rayuwar ƴan'uwana ƙauyawa. Don haka ina miki fatan alkhairi, da addu'ar dacewa da miji muradin rayuwarki, wanda ba shi da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ƙauyawa. Idan da abinda ya rage tsakanina da ke a yanzu, bai wuce ɗa ɗaya da Allah ya bamu ba. Albishir ɗaya da zanyi miki shi ne ni bazan raba ki da ɗanki ba, lokaci bayan lokaci zan dinga kawo shi gurinki kina ganin lafiyarshi. Amma fa ki sani, rayuwar ƙauyennan da kika tsana tabbas sai Aadil ya ratso ta wannan hanyar kamar yadda ni mahaifinsa na ratsa har nazo kan wannan matakin da nake ciki. Sannan ina sake gargaɗinki ki daina kira na a waya idan ba da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba. Kayanki na gidannan tuni an tattara miki su an kulle a ɗakinki, da wasu daga cikin ɗakunan BQ, duk sadda kika shirya ko ta text message ki sanar da ni za ki turo ƴan'uwanki su kwashe miki kaya. Amaryata tana da matsanancin kishi, ko kaɗan bazan bari ki zama sanadiyyar da baƙin ciki zai ratso ta tsakiyar farin cikin matata abin son zuciyata ba..." Ƙit! Bintu ta katse wayar daga ɓangarenta, saboda yadda kalamansa suke babbakata kamar ana zuba mata tafasasshen ruwan dalma, tun daga tsakiyar kanta har zuwa diga-diginta. Wasu irin zafafan numfarfashi take ja, kamar mai cutar numfashi. Da farko a zaune take a tsakiyar gado, ba tare da sanin yadda aka yi ba sai gata a tsakiyar ɗakin tana safa da marwa. Ashe wani tashin hankalin ya fi gaban ayi mishi kuka? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Gaba ɗaya kukan ɗaukewa yayi daga idanunta, sau uku tana ɗaga hannu ta ɗora akai da nufin ta ƙwalla wani matsiyacin ihu, sai kuma ta ji muryarta ya ƙi fitowa sam! kamar wacce aka shaƙewa maƙogwaro. Daga yadda take jan numfashi da ƙyar, tana haɗawa da shishitu da baki,

Chapter 35 of 40