tsawa da hargaginsa bayyi tasiri kan Zulaikha ba, ƙam! Ta riƙe ƙafafun Innaye tana rusa ihun kuka da kurarin ita babu inda za ta je, a barta a gurin Innayenta in dai ba so ake ta mutu ba. Ita ta yarda a kwance aure da Hafiz a ɗaura mata da ko tsoho ne, ko gurgu ko kuturu ta yarda za ta zauna tayi biyayya in dai kusa da Innaye ne.
A fusace Baffa ya fice daga ɗakin zuwa ɗakinsa da nufin ɗauko zabgegiyar bulalarsa da yake ladaftar da yaran gidan ƙananu, lura da abinda yake shirin yi yasa da saurin gaske Yayyinta suka ɓamɓareta daƙyar daga jikin Innaye suka fice da ita zuwa mota tana gunjin kuka.
Ƴan kayayyakinta daman tun da sassafe an riga an zuba a cikin mota, fitowarta kaɗai Hafiz da direba suke jira, ya riga ya gama sallama da kowa. Ranshi yayi mummunar ɓaci da yadda ƴar ƙanƙanuwar yarinya kamar Zulai take ta ɓata mishi lokacin tafiya, sai dai ko kaɗan bai nuna ba. Domin babban burinsa a wannan gaɓar shi ne ya rabu lafiya da iyayensa.
Da farko yana zaune ne a ƙofar gida kan dakali, amma da yaga wasu daga cikin mutanen ƙauyen sun ƙi sarara mishi ya huta, kowa da irin neman taimakon da zai zo gurinshi, shi kuma ga irin ƙuncin da zuciyarsa ke ciki, da yayi iya taimakon da zai iya kuma Zulaikha bata fito ba kawai sai ya shige ɗakin ƙannenshi maza da ke cikin zauren gidan.
Kukan da Zulaikha ke yi lokacin da za'a wuce da ita ta cikin zauren shi ne abinda ya dawo da shi hayyacinsa daga zuzzurfan tunanin da ya afka.
Mamaki mai tsanani ne ya kama shi jin irin kukan da take yi. Sai kuma ya mele baki gefe ɗaya ya miƙe tare da ɗaukar wayoyinsa ya fice daga cikin ɗakin.
[1/20, 11:43 PM] Fareeda Abdallah: Akan idanunsa Aunty Balira ta buɗe tafin hannun Zulaikha ta saka mata wayar Android ɗin da ya bata. Kamar Aunty Baliran ta san kallonta yake yi da mamaki a fuskarsa, sai ta juya tana kallonshi da ƙayataccen murmushi a fuskarta.
"Aro na ba ta ba kyauta ba. Na san a matsayinta na matar ƙanina Hafizu nan da kwanaki kaɗan za ka siya mata ƴar sha-far da ta ninka wannan a tsada, ka ga idan ta mallaki na ta sai ta dawo min da nawa."
"Uhmmm!"
Abinda ya iya ce mata kenan ya mayar da hankalinsa gurin dandazon ƴan'uwansa da suke tsaye jikin motar suna ƙara rarrashin Zulaikha da har lokacin take kuka ƙasa-ƙasa da tausasan kalamai.
Ranshi ne ya ƙara ɓaci, da ma ace yana da ikon yin abinda yake so ba tare da an samu mishkila ba, tabbas da babu abinda zai hana shi lallasa Zulaikha a gurinnan. Sanin ba shi da wannan damar yasa shi yin ƙwafa ƙasa-ƙasa, yayi ta maza gurin rage girman ɓacin ransa.
"Kuyi haƙuri, lokaci na tafiya. Duk yadda ake ciki idan mun isa za muyi waya da ku."
Yayi maganar da sanyin murya.
Ba tare da ɓata lokaci ba duk suka ja baya daga jikin motar, Aunty Rakiya ce ta rufe ƙofar baya na motar inda suka zaunar da Zulaikha bayan ta cusa kanta cikin motar ta raɗa ma Zulaikha magana a kunne.
Fatan alkhairi da addu'ar Allah ya tsare gaba ɗaya suke mishi haɗe da ɗaga mishi hannu, har direba ya tayar da motar suka ɓace ma idanunsu basu koma cikin gida ba.
"Ubangiji Allah ya kaɗe fitina, ya bada zaman lafiya da Zuriya masu albarka."
Indo, babbar ƴa a ɗakin Umma Laminde tayi addu'ar.
"Ameen ya Allah"
Suka amsa gaba ɗayansu.
***** ******
Da ɓacin rai sosai a muryarsa ya ɗan waiwaya baya ya kalli Zulaikha da har lokacin yake jin shessheƙar kukanta ƙasa-ƙasa ya ce
"Kin san Allah? Idan bakiyi mana shiru ba a tsakiyar dajinnan da babu gida gaba babu gida baya zan saka a sauke ki. Kuma kin san halina sarai, tsaf zan iya aikata fiye da haka."
Maganar na dira a kunnuwanta ɗif! ta tsayar da kukan da take yi kamar ɗaukewar ruwan sama. A tsorace ta ɗan ɗago kanta daga cikin hijabi ta saci kallon gefe da gefen hanya.
Sai taga kamar yadda ya faɗa ne, a cikin daji suke tabbas! Kuma ta san mugu ne na ƙarshe in dai a kanta ne, kaɗan daga cikin aikinsa ne ya yasar da ita a gurin, balle ma a yanzu da yake ganin ta zame mishi ƙarfen ƙafa. Kuma kasancewarsa gogaggen ɗan boko da ya saba da ƙarya ƙirƙirar abinda zai faɗa don wanke kansa a gurin iyayensu bayan ya ɓatar da ita ba abu ne da zai mishi wahala ba.
Tana jin shi ya ja ƙwafa mai ƙarfi, sannan yayi dogon tsaki. Ga dukkan alamu dai bai so tayi shiru ba.
'Mugu! Aniyarka ta bi ka. In Allah ya yarda har mu raba gari muguntarka ko na matarka bazai taɓa tasiri a kaina ba. Allah nake roƙo ya cigaba da bani kariya daga dukkan sharrinku.'
Tayi maganganun a zuciyarta.
Kasancewar ta daɗe tana kuka, kuma daren jiya gaba ɗaya barcinta raba da rabi ne. Don haka bata ɓata lokaci cikin tunani ba nannauyan barci yayi awon gaba da ita.
Kamar a mafarki, ta ji saukar wani zazzafan duka a gefen kafaɗarta. A firgice ta ɗago fuskarta idanu a warwaje ta ce
"Wayyo Allah Innaye..."
Cike da jin haushi ya kai hannu zai make mata baki, Allah ya taimake ta taga tahowar hannunsa, da saurin gaske tayi gaggawar kawar da fuskarta can gefe ɗaya.
"Idiot! Kina barcin ma baki san idan an tashe ki kiyi salati ba sai ihu."
Ya faɗa da ɓacin rai yana harararta.
Ƙasa-ƙasa ta mayar mishi da martanin hararar da yayi mata, duk da bata san cikakken fassarar kalmar 'Idiot' ba ta san zagi ne, domin malamansu na boko suna yawan faɗa ma ɗaliban da basa jin magana. Bakinta a gaba a zuciyarta ta ce
'Ni dai ba Idiot bace.'
A fili kuma cewa tayi cikin guna-guni
"Yaya duka na fa kayi ba tashi na ba... Kuma da zafi sosai. Bayan Innaye ta ce amana maci amana maye..."
"Idan kika sake min maganar Innaye anan sai na ɓata miki rai. Za ki fito ko sai na sa an kulle ki cikin mota?"
Kafin ta fito, sai da ta waiga ta tabbatar ba'a tsakiyar daji suke ba. Mamaki ne ya kamata da taga ashe har sun isa gidanshi a Abuja, bata ce komai ba sai girgiza kai da tayi. A maimakon ta fito ta ɓangaren ƙofar da yake tsaye yana jiran fitowarta, muskutawa tayi zuwa can ɗaya ƙofar ta buɗe da sauri ta fita tun ma kafin ya sake cewa komai.
Miƙa tayi haɗe da salati a hankali, a zuciyarta take ayyana ƙarshen tika tiki tik! Ga ta dai a cikin gidan, kuma a matsayin matar mai gidan. Sanin irin wainar da za'a toya kuma a cikin gidan Allah kaɗai ya bar ma kansa sani.
Da saurin gaske ta ɗaga ƙafa ta bi bayansa ganin har ya kusa isa bakin ƙofar shiga ɓangarensu ba tare da ya ƙara ce mata kanzil ba. Har ta kusa cimma inda yake, sai ta tuna da jakar kayanta da yake cikin boot ɗin mota. Ba tare da kunya ko jin nauyin jikinta da ta kasance irin yarannan masu ƙiba ba ta juya da gudu zuwa gurin motar.
"Mal Musa jakar kayana da wayata a cikin mota."
Ta faɗa da ƙarfi kuma cikin karaɗin da yasa hatta Hafiz sai da ya tsaya a inda yake ya waiga yana kallonta.
"Wawuya kawai."
Ya faɗa a fili haɗe da jan tsaki ganin irin gudun da take yi.
"Afuwan ranki ya daɗe. Ai da ma kin shiga daga ciki sai in ɗauko miki jakar kayan naki."
Mal Musa ya faɗa cikin girmamawa, domin tun a ƙauye yasan matsayinta a gurin maigidansa yanzu tudu biyu ne.
Dariya ne ya kamata ganin yadda yayi mata magana, har da wani ɗan durƙusa mata irin bayar da girman nan. Duk yadda ta so fuskewa ta ci magani kasawa tayi, sai da ta ɗanyi dariya kafin ta ce
"Ka ga Mal Musa, ni fa ba wata baƙuwar zafi ba ce. Kar ka wani ɗaura min girman da ko kusa bazan iya ɗauka ba. Buɗe min mota kawai in ɗauki wayata da jakar kayana."
Yana buɗe boot ɗin motar, bata tsaya jiranshi ya ciro jakar kayan ba da sauri ta ciro abarta, ta buɗe gidan baya na motar ta ɗauki wayar da Aunty Balira ta bata sannan ta nufi ɓangaren masu gidan. Idan tayi taku ɗaya, biyu, sai ta waiga ta kalli hanyar ɓangaren BQ inda aka sauke su ita da Innaye.
Haka kawai tsoro ya mamaye zuciyarta
"Allah yasa dai ba a can ɓangaren za su ce in zauna ni kaɗai ba."
Tayi addu'ar a fili, zuciyarta cike da tsoro.
"Taɓ! Ai Wallahi idan Yaya ya ce in koma can ni kaɗai bazan je ba, sai dai yasa a maidani Faƙo, haka kawai ni kaɗai ƙwal kamar mayya za su tura can gurin? Taɓ! Bazai yiwu ba."
Ta sake faɗa a fili tana ɗan murguɗa baki kamar Yayan yana gabanta.
A daidai lokacin ta isa ƙofar shiga ɓangaren masu gidan, bata tsaya wani ƙwanƙwasawa ba kawai ta murɗa hannun ƙofar tare da cusa kanta cikin falon, bakinta ɗauke da siririyar sallama.
Cak! Taja ta tsaya tana ƙare ma tanƙamemen falon kallo, babu kowa a ciki. Matsanancin mamaki ne ya kamata ganin gaba ɗaya falon an canza kayan ciki da ta sani, wasu tsadaddun setin kujerun aka canja da kayayyakin more rayuwa kala daban-daban. Duk da daman can falon mai bala'in kyau ne, amma yanzu sai taga ya ƙara ninka kyau fiye da yadda ta san shi a baya.
Ga kuma wasu tanƙama-tanƙaman hotunan Yayanta da Anty Bintu da jaririnsu da aka kafa a kusurwoyin falon. Saboda tsabar ƙauyanci bata san sa'adda ta saki jakar kayanta a tsakiyar falon ba, ta fara zagayawa a hankali tana ɗan tattaɓa abubuwan kwalliyan da tunda aka haife ta bata taɓa ganin irinsu ba.
Baza ta ce ga iya adadin mintunan da ta ɓata tana kallon ƙauyancin ba, kafin daga bisani ta tsaya gurin wani ƙaton hoton Jariri Aadil da yayi kyau sosai kuma ya fito fes a cikin hoton kamar ɗan turawa. A hankali ta miƙa hannunta ta taɓa fuskarsa a cikin hoton, ita kaɗai sai sakin murmushi take yi tana shafa fuskarsa kamar a gaske shi take shafawa.
Allah ya sani tana son yara, musamman yara masu kyawu tun suna jarirai, shiyasa ko a maƙwafta in dai aka haifi yaro ko yarinya kyakkyawa ta dinga jelar ɗauko yaron yana yini a gurinta kenan.
"Keh! Wace ce ke?"
Saukar gigitaccen tsawa da tambayar Bintu a kunnuwanta yasa ta ɗauke hannunta a jikin hoton da sauri tare da waigawa baya a tsorace. Da yake ta ba hanyar saukowa daga matattakalar baya ne, shi yasa tun daga saman benen bayanta kawai Bintu take hange ba tare da sanin ko wacece ba sai yanzu da ta juyo suka yi ido biyu.
Da maɗaukakin mamaki sosai a fuskar Bintu take kallonta, domin ko da suɓutar baki Hafiz bai faɗa mata tare da Zulaikha yake ba. Farin cikin ganin kyakkyawar zinariyar matarsa da ɗansa mafi soyuwa a zuciyarsa ya mantar da shi duk irin ɗunbin damuwar da ya kwana ya yini da shi.
Tunda suka haura sama wanka kawai yayi suka yi musayar sumbata da rungumemeniya tsakaninsa da matarsa ya ɗauki ɗansa yana ta mishi wasa kamar wani babba. Saukowar nan da Bintu tayi ma ta sauko ne da nufin ta ɗauko mishi abubuwan motsa baki kafin ta ƙarasa mishi abinci ashe rabon tayi tozali da ɓacin rai ne.
Yo ɓacin rai mana, idan ba ɓacin rai da takaici ba me zai kawo Zulai gidanta a irin wannan lokacin bayan ko sati gayyar na'ayyen danginsa basu yi da komawa can ƙauye daga taron sunan da suka zo ba.
"Ke ce?"
Ta tambayi Zulai da murya mai bayyana fushi ƙarara tana harhaɗe girar sama da ƙasa.
"Me ya kawo ki gidana?"
Ta sake tambayarta a tsawace ba tare da ta jira amsar tambayar farko ba.
Ƙasa-ƙasa Zulaikha ta galla mata harara, zuciyarta cike da tunanin irin cin kashin da Bintun tayi musu wancan karon zuwansu gidan ita da Innaye. Tana kuma ayyana lallai wannan karon baza ta taɓa ɗaukar wulaƙanci daga Bintu ko Yayanta ba sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Sai da ta kawar da fuskarta gefe ɗaya, da taƙama-taƙama a muryarta ta amsa ma Bintu da cewa
"Gidan Yayana dai. Kuma tare da shi muke tafe, abinda baki gane ba shi za ki je ki tambaya ba ni ba."
[1/21, 8:22 PM] Fareeda Abdallah: Har ta buɗe baki za ta yi magana, sai kuma ta katse maganar ta hanyar jan ƙaƙƙarfan tsaki. Da sassarfa ta juya ta fara haura matakalar benen bibiyu ranta yana ƙara ɓaci, har ta isa ɗakin Hafiz. Tsabar yadda ganin Zulaikha ya tunzurata ta ma kasa tsayawa ta rage girman ɓacin ran da ke bayyane ƙarara a fuskarta, ko kuma tayi ƙoƙarin saisaita yanayin kalaman bakinta.
"Hafiz? Zulai na gani a falo? Me ya kawo ta gidana?"
Ta tambayeshi cikin ɗaga murya ba tare da damuwa da barcin da taga ya fara yi ba, Aadil na kife a ƙirjinshi shi ma yana barci.
Kamar a mafarki, haka muryarta ya sauka a kunnuwanshi da wani irin tsawa-tsawa. A hankali ya buɗe idanunsa da suka fara canja launi saboda gajiya da kuma barcin da ya fara ɗaukarsa.
"Me kika ce Sweetheart?"
Ya tambayeta a nutse, a ƙoƙarinsa na ƙaryata zuciyarsa da take ta raya mishi kamar fa ɓacin rai yake gani a fuskar Bintu kuma tsawa tayi mishi yayin magana don kawai ta ga Zulai ƙanwarsa a cikin gidan. Wai a hakan ma don bata san matsayin Zulai a gare shi ya ƙara sama daga ƙanwa zuwa mata ba.
"Zulai na gani a falo. Na tambayeta me ya kawo ta tace min in tambaye ka. Shi ne nake neman sanin abinda ya kawo ta da ƙaton jakar kaya bayan ko sati ɗaya ba'ayi da su Aunty Balira suka koma ba..."
"Don su Aunty Balira sun zo suna sun koma wata a cikin dangina ba ta da ikon zuwa bayansu?"
Ya katse ta da tambayar tun kafin ta aje numfashin maganarta, mamaki mai girma bayyane akan fuskarsa.
Suuu tayi a tsaye guri ɗaya, sai da yayi mata wannan tambayar ne yasa ta jin kamar fa ta kwafsa a yanayin yadda ta zo mishi da ƙorafin. Narai-narai tayi da idanunta kamar za ta saka kuka, muryarta a raunane ta amsa da
"A'a ba haka bane. Kawai dai na yi mamaki ne."
Har ta yi shiru sai ta ƙara da
"Kuma dai My dear sanin kanka ne Zulai ba ta wani ƙaunata, ba shiri muke yi ba. Saboda Allah sai ka rasa wacce za ka ɗauko ta kwana biyu a gidannan sai ita? Ka sani sarai ni raini ne ba na so... Amma idan maganganuna sun ɓata rai Allah ya baka haƙuri."
Shar... hawaye suka sauko daga idanunta, a sanyaye ta juya za ta fice daga ɗakin.
Bata san sa'adda ya kwantar da Aadil akan gado ba sai ji kawai tayi ya riƙo hannunta na dama. Ko kafin tayi wani yunƙuri har ya kwantar da ita a ƙirjinsa, a tausashe, ya fara shafa bayanta alaman rarrashi.
Ita kuwa hawaye ne suka ɓalle mata kamar an buɗe famfo, sai tsiyayar da su take yi a ƙirjinsa zuciyarta na ƙara zafi. A yadda take ji, kamar ta buɗe baki tayi ta kwarma ihu ko za ta samu sauƙin damuwarta amma babu hali.
Allah ya sani, ta tsani mu'amala ta kusa ko ta nesa ya dinga haɗa ta da dangi da iyayen Hafiz. Wai me yasa baza su sakar mata mara tayi walwalarta bane tunda dai shi da ya kasance dolen-dole a gare su yana zuwa can ƙauyen? Da gangar tun bayan komawar Innaye ƙauyen ta ƙi zuwa, duk sa'adda ta ji ya fara zancen zai je duba iyayensa za ta fake da laulayin ciki, ko kuma ta ce cikinta baiyi ƙwari ba a matsayinta na likita baza ta iya jure doguwar tafiya a cikin mota ba don gudun abinda zai je yazo wanda ba'a fata.
Shi kuma da yake Allah ya jarabce shi da masifaffen son cikin haka yai ta mata uzuri bai taɓa matsa mata ba har Allah ya sauke ta lafiya. Kullum idan yaje, da irin uzurin da zai ƙirƙira ya faɗa ma iyayen a matsayin abinda ya hana Bintu zuwa duba Innaye. Su kuwa da yake dattawan arziki ne ko a fuska basu taɓa nuna mishi ɓacin ran rashin zuwan nata ba, tunda dai shi da yake nasu yana zuwa akai-akai, to Alhamdulillahi.
"Beb kukan kuma na menene?"
Ya tambayeta da mamaki bayan ya ɗago fuskarta yaga hawaye kaca-kaca har ta jiƙa mishi gaban lallausar rigar shan iskar da take jikinsa.
Sai da ta ja shessheƙa kafin ta iya danne zuciyarta ta amsa da
"Damuwar yadda na ɓata maka rai daga dawowarka ne My Dear... Kayi haƙuri don Allah ka ji?"
Ta bashi haƙurin a shagwaɓe. Kafin ya amsa ta ƙara da cewa
"Kuma zuciyata cike take da tsoron irin zaman da za muyi da Zulai, Allah yasa bata zo da nufin sauke min kwando-kwando na rashin kunyarta ba, domin ko yanzu daga tambayarta a mutunce baka ga wata uwar harara da ta aiko min ba..."
"Zan ja mata kunne sosai, ko kusa bata isa ta ce za ta maimaita iskancin da tayi mana lokacin zuwansu da Innaye ba. A gabanki zan gargaɗeta."
Ya faɗa a tausashe, zuciyarsa na ta canki-cankar ya faɗa mata matsayin Zulai a gare shi yanzu ko kuma ya bari sai can gaba?
Duk da dai maganar da Innaye tayi mishi na bata yarda ya ɓoye ma Bintu matsayin Zulaikha a gare shi ba yana ta bugun can ƙasan zuciyarsa.
"Shi kenan My dear. Ina mata barka da zuwa. Bari in je in kawo maka abin motsa baki."
Ta faɗa da sanyin murya bayan ta goge hawayen fuskarta tsaf! Har ta kama hannun ƙofar za ta buɗe ta fita maganarsa yasa ta tsayawa cak!
"Baffa ne yace in taho da ita zuwa nan da ki gama wanka, ko wasu ƙananun ayyukan ne sai ta taya ki da su, ko kuma rainon Aadil, don ita ɗin gwana ce gurin rainon ƙananun yara."
Da shi da yayi ƙaryar don samun maslahar kai da kai, da ita da take saurarensa hankalinta a ɗugunzume, a tare ƙirajensu ya buga daram!
Lumshe idanu tayi tana jan Lahaula walaƙuwwata illah billah a zuciyarta. Ko da ta buɗe ido, bata yarda ta kalli fuskarsa ba balle yaga yadda wasu sabbin hawaye suka sake cicciko idanunta.
Da shaƙaƙƙiyar murya ta ce
"Allah sarki Baffa... Ai kuwa na gode sosai... Amma da an barta tunda ga Mashkura (Ƙanwarta) har yanzu bata koma gida ba. Amma tunda an zo da ita ma bai ɓaci ba. My dear bari in je in dawo, na bar Zulai a falo ko ruwa ban bata ba."
Bata jira amsawarsa ba ta wuce da sauri don ma kar ya sake tsayar da ita.
Sai da ta tsaya a tsakiyar bene na sharɓi hawaye na cikakkun mintuna uku kafin ta iya ƙarasawa cikin falon fuskarta a ɗaure tamau. Turus! Ta ja ta tsaya ganin Zulaikha zaune akan kujera ta yi ɗaiɗai, hannunta riƙe da babbar kwalin madarar hollandia tana ɗaɗɗaka, ko kofi bata samu zarafin ɗaukowa a kicin ba, haka take gwaɓa bakinta a jikin kwalin tana sha babu abinda ya dame ta.
"Wani shegen ne yasa ki buɗe min frig ki ɗauki abu ba tare da umarnina ba?"
Ta tambayi Zulaikha ranta a ɓace. Duk da zamanta akan kujera ya ɓata ma Bintu rai ba kaɗan ba, amma ganinta tana shan madara hankalinta kwance kamar a ɗakin uwarta ya danne ɓacin ran zamanta akan kujerar.
Kafin Zulaikha ta amsa mata, sai da ta lumshe idanu ta ƙara zuƙar madarar sosai da irin salon cusa haushin nan sannan ta kalle ta tana murmushi.
"Yaya ne fa ya siyo, saboda Allah Aunty Bintu a gidannan da irin matsayin da nake da shi har sai na nemi izininki kafin in ɗauki wani abu da nake da tabbacin ɗan'uwana ne ya siyo?"
Karaf! Maganganun suka sauka a kunnen Hafiz da yake saukowa daga bene. Ranshi a ɓace, ya daka ma Zulaikha wani gigitaccen tsawan da yasa ta yarda kwalin madarar ba shiri, a tsorace ta ɗaga idanu tana kallonsa ƙirjinta na bugawa akai akai har ya ƙarasa saukowa daga benen.
Kai tsaye gurinta ya nufo kamar zai rufe ta da duka ya tsaya a kanta yana huci
"Sa'arki ce ita da za ki dinga faɗa mata maganar banza? Yi maza ki ba ta haƙuri kafin in tattaka ki anan gurin"
A tsorace, ta ɗaga idanu ta sake kallonsa. Ganin yadda yake zazzare mata idanu kamar zai haɗiye ta yasa da saurin gaske ta kawar da idanunta ta mayar kan Bintu da take tsaye a bayansa hannayenta harɗe a ƙirji, da alamun al'amarin ba ƙaramin daɗi yayi mata ba. Domin idan ba idanun Zulaikha ke mata gizo ba sai taga kamar murmushi Bintu take yi.
A tsorace da salon kare kai ta fara magana bakinta na rawa
"Yaya ita ce fa..."
"Na tambaye ki ƙarin bayani?"
Ya katse ta cikin tsawa.
"Za kiyi abinda na umarce ki ko sai na tattaka ki a tsakiyar falon nan?"
Lokaci ɗaya itama ranta ya ɓaci, a ganinta wannan ai rashin adalci ne ƙarara. Taya zai yanke hukunci kai tsaye ba tare da jin dalilin da yasa ta mayar ma da Bintu baƙar magana ba? Har ta tsuke baki alamun baza ta ba Bintu haƙurin ba, sai dai duk abinda zayyi yayi, idan yaso ya kashe ta.
Sai kuma wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita matsayin Yayan yanzu a gurinta. Ƙin aikata abinda ya umarceta matuƙar ba saɓon Allah bane kamar ta gayyato ma kanta tsinuwar mala'ikun rahama ne.
"Kiyi haƙuri."
Ta faɗa cikin fushi bakinta a zumɓure.
Guri ya nema ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon ya fara zazzaga mata faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Da alamun haushin abinda ya faru da shi a ƙauye yake son saukewa a kanta bayan ba ita ta kar zomon ba.
"Bazai yiwu ba. Bazan taɓa yarda da irin wannan rainin da iskancin da kika saba yi mana ba. Idan ma za ki saka ma kanki nutsuwa da karatun ta nutsu gara ki saka, tun wuri gara ki sauke duk wani rawar kai da wani gigi da yake damunki, idan ba haka ba na rantse da Allah ba ƙaramin wahala za ki sha da ni a gidannan ba.
Ko ban faɗa ba ke kanki kin sani, ta ko wane ɓangare na rayuwa matata gaba take da ke. Ta sha gabanki fiye da yadda kike tsammani, in dai kika ce raini da tsaurin idanu za ki nuna mata, lallai kuwa zan kawar da duk wata sanayya da dangantaka in koya miki hankali fiye da yadda kike tsammani..."
Bai san Zulaikha kuka take yi ba, sai da ya ji shessheƙarta ya cika falon. Duk da haka bai sassauta faɗan da yake yi ba, sai ma ƙara caccaɓa mata baƙaƙen maganganu yake yi kamar bai san daga inda ta fito ba, duk da sunan ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunnen ta kiyaye irin zaman da za tayi a gidansa da kuma iyalinsa.
Bintu da matsanancin farin ciki ya gama ƙume ta, kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha take ji. Sai da ya daɗe yana cin zarafin Zulaikha ita kuma tana ta rusa kuka kafin a yangace ta ƙarasa inda yake zaune, akan cinyarsa ta zauna, ta ɓalle maɓallai biyu na gaban rigarsa ta fara shafa ƙirjinsa ba tare da kunyar idanun Zulaikha ba.
"Ayya mana My dear... don ɗan wannan abin da ya faru ne kake ɓata ranka haka? Ka san fa halin Zulai ciki da waje, ni kawai ina mata uzuri ne saboda har yanzu yarinya ce, da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 40