ɗan narke fuska, a marairaice ya fara roƙonta
"Haba-haba An Zulai ta Innaye da Baffa. Ai na san baza kiyi ma Yayanki haka ba? Ko kin manta ni da ke mun shirya tsakaninmu yanzu ba ta ɓaci?"
"Ban manta ba Yaya."
Ta amsa da dariya.
"To tunda haka ne zo ki wuce gidanki. Na gode da ƙoƙarinki ƙanwata, Allah ya bar zumunci. Za muyi waya da safe, kina iya tuƙi da daddare ko in haɗa ki da direba...?"
"Direban Mummy na waje yana jira na Yaya, sai da safe..."
Tana gama faɗin haka ta rataya jaka, ta gyara zaman mayafi a kafaɗarta. Sai da ta kai bakin ƙofar fita daga falon sannan ta waiga ta ce
"Yaya?"
"Na'am Zulai."
Ya amsa da sauri, bayan ya mayar da hankalinshi kanta.
"Ka ji tsoron Allah don Allah Yaya, ka bi min ƙawa a hankali..."
Ta ƙarasa maganar haɗe da ficewa a guje tana dariya.
"Uhmmm! Zulai ƙuruciya dangin hauka. Allah ya shirya. Kamar ba ƴar lukuta ba sam ba ta jin nauyin jikinta."
Ba tare da kunyar idanun Ibrahim ba ya maye gurbin da Zulai ta tashi kusa da Kareema, kan kujera mazaunin mutum biyu.
Ibrahim na tsokanarshi
"Ko kunyar idona ba ka ji Hafizu?"
Ya jefa mishi harara ba tare da ya amsa ba.
A gefe guda Ibrahim ya zauna, ya fara da sallama sannan ya buɗe taron da addu'a. Nasiha sosai ya yi musu game da zaman aure da zamantakewa, kafin daga baya yayi musu addu'a sosai da fatan Allah Ya ɗaurar da auransu har a gidan Aljanna. Daga ƙarshe ya yi musu sai da safe ya fice daga falon
Daƙyar Hafiz ya iya tashi ya raka shi bakin ƙofar babban falo, daga nan ya coge ya ce mishi
"Na gode Aboki, a gaida Madam da yara"
A Nan ma sai da Ibrahim ya ƙara mishi shakiyanci kafin ya mishi sai da safe ya tafi. Shi kuma ya tsaya ya rufe kofa da tagogin falon.
Ya samu Amarya a yadda ya barta, da alamun ko ƙwaƙƙwaran motsi bata yi ba. A hankali ya ƙarasa ya tsuguna a gabanta yana leka fuskarta ta cikin lullubin jikinta.
A sanyaye ta zuba mishi idanunta da suka yi ciki sosai, alamun kukan da ta daɗe tana sharɓa.
Cikin marairaice fuska, ya ce
"Ƙurratul-ainiy? Kuka kika yi? Sai kace dai wadda aka kawo ki gidan makiyinki ba masoyi ba? Idan ma kina zaton wai ba zan iya kulawa da ke kamar yadda Mommy take yi to ki canza shawara. Domin yadda zan kula da ke ma sai ya ninka nata uku sau uku! In sha Allah!"
Sai ta samu kanta da sakin ƴar dariya, a hankali ta ce
"Sau tara fa kenan?"
"Eh! Ai tara ma kamar ya yi kaɗan. Ko ita ma taran a ninka ta sau tara?"
Sosai ta sake dariya ba tare da ta shirya ba.
Ganin yadda ta sake tana dariya sai hakan ya sanyaya mishi rai.
Ya mike tsaye tare da mika mata hannu, babu musu ta sanya zara-zaran yatsunta a cikin nashi, yatsunta sun sha zanen lalle baki da ja, sun yi kyau sosai. Ya ɗan ɓata daƙiƙu yana kallon yatsun sannan ya janyo ta ta tashi tsaye.
Kai tsaye ya ja ta zuwa dakinshi.
Ya umarceta da ta shiga bayi ta dauro alwala. Daƙyar, ta shiga bayin tayi alwala cikin dar-dar. Ganin yadda duk ta bi ta tsorata da shi a fili yasa yayi kokarin kin kai hannu ya tabata duk da yadda zuciyarshi take azalzalarshi da yayi hakan. Ya jira ta tayi alwalar ta fito, kafin shima ya shiga bayin don ɗauro alwala.
Bayan fitowarsa daga bayin, kai tsaye inda take rakuɓe a gefen gado ya fara kallah. Bai san sa'adda murmushi ya suɓuce masa ba, ganin yadda ta wani takure, kamar ace kyat! Ta zura a guje.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya ƙarasa kusa da ita, ya ɗauki babbar rigarsa da ya ajiye a gefen gadon sadda zai shiga banɗakin.
"Pls ɗan bani mintuna biyu Ƙurratul-ayn, ina zuwa."
Kai kawai ta iya ɗaga masa alamar to. Shi ma bai takura sai ya ji maganarta ba ya fice daga ɗakin. Mintuna uku tsakani ya sake komawa cikin ɗakin, jikinsa sanye da jallabiya mai laushi sosai, kalar ruwan madara.
Hannunsa riƙe da darduma. Kai tsaye, wadataccen ɓangaren da aka ware don yin a cikin ɗakin ya nufa ya shimfiɗa sallayar hannunsa.
"Amarya zo muyi sallah, mu gode ma rabbil-izzati da ya mallaka mana junanmu cikin ƙanƙanin lokaci. Sannan muyi addu'ar dacewa da dawwamammen zaman lafiya, kwanciyar hankali, zuri'a masu albarka."
Da yake idanunsa a cikin nata yake maganar, ya ga saukar lallausan murmushi a fuskarta. Sai kuma ta miƙe tsaye ta warware babban mayafin jikinta, ta rufa shi da kyau. Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki haka ta tafi laƙaƙai-laƙaƙai har zuwa bayansa, inda ya shimfiɗa mata ƙaramar sallayar da ya gani an ninke an ajiye da Alƙur'ani mai girma kan wani ƙaramin stool da yake gurin.
Ya ja su suka yi sallar nafila raka'a biyu masu tsayin surori. Bayan sun idar, ya jima a zaune yana kwararo musu addu'ar samun daidaito da fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma zuriya ɗayyiba, a hankali ita kuma take amsawa da Amin, har zuwa sadda suka shafa Fatiha.
Duk da tabbacin da yake da shi kan ilimin addininta, hakan bai hana shi yi mata tambayoyi kan addininmu ba. Kuma ya samu gamsassun amsoshi kamar yadda yayi hasashe.
Abinda ya gabatar na ƙarshe shi ne matsawa kusa da ita, ya dafa goshinta yayi addu'ar da fiyayyen halitta SAW ya koyar don dacewa da alkhairinta, da kuma neman tsari daga dukkan sharrin da yake tattare da ita.
Bayan sun gama komai, a hankali ya kama hannunta ya miƙar da ita tsaye, sannan ya saka idanunta cikin nasa ya fara kashe ta da lallausan murmushi, lokaci guda kuma yasa hannunsa yana aikin warware naɗin gyalen da yake jikinta.
Ƙugunta ya riƙe da hannayensa biyu yana tafe da baya da baya suna tafe a slow motion cikin rausaya har zuwa tsakiyar ɗakin, inda aka shimfiɗa lallausan kafet, da wani irin salo na soyayya da kulawa ya zaunar da ita kan kafet ɗin. A kunne ya raɗa mata
"Ɗan ba ni minti ɗaya Sarauniyata, yanzu zan dawo."
Bai jira amsawarta ba ya fice daga ɗakin da sauri. Falo ya koma, ya ɗauko ledar da suka shigo da ita shi da Ibrahim.
Kai tsaye kicin ɗin Kareema ya wuce, ya samu babban faranti ya ɗauraye, sannan ya warware ledar jikinshi na rawa, zuciyarsa cike fal da tunanin Kareema, da irin shape ɗin jikinta na coca-cola da ya gani yanzu da ya cire mayafin jikinta.
Yana gama warware ledar, daddaɗan ƙamshi ya cika hancinsa. Gashin naman talo-talo ne aka yi da albasa da tumatiri da yaji haɗi da kayan ƙamshi. Gaba ɗaya ya sake a cikin farantin, sannan ya ɗauki wani farantin ya rufe ya kai ɗakin Kareema da sauri.
Yana ajiyewa a gabanta bai ɓata lokaci ba ya koma cikin kicin ɗin. Fridge ya buɗe, ya ɗauko kwalin lemun five alive, ya haɗa da kofuna guda biyu, ya sake ɗaukar faranti guda ɗaya, cokula masu yatsu guda biyu, da ƴar ƙaramar wuƙa da cokula na cin abinci guda biyu ya koma cikin ɗakin.
"Yau zan ƙara tabbatar miki ke Sarauniya ce a zuciyata Ƙurratul-ayni. Da kaina zan ciyar da ke har sai kin ce kin ƙoshi."
Yayi maganar a tausashe, da ƴar ƙaramar dariya a muryarsa.
Dirshan ya zauna a gabanta bayan ya tattare jallabiyarsa. Farantin naman ya janyo, ya fara yankawa sannu a hankali cikin ƙwarewa yana zubawa a empty plate da yake ajiye a gurin.
Lokaci ɗaya kuma a tausashe, bakinsa na raira mata waƙar Ke ce Aljannata, na Auta waziri.
Duk da tana jin yunwa sosai, saboda rabonta da ƙwaƙƙwaran abinci tun karin da tayi a Faƙo, sai ɗazu da Zulaikha ta takurata ta sha ruwan tea mai kauri. A yanzu, ta kasa sakin jikinta sosai ta ci naman yadda ya kamata saboda kunya da fargaba, idan ta tuno irin shaƙiyancin da Zulai tayi mata kan wannan dare, sai ta ji tsoro ya sake cika cikinta.
Ya dube ta kasa-kasa yana ɗan murmushi
"Bari in ajiye miki sauran da safe sai ki ɗumama ki ci kayanki. Kin san dai dole ne sai amarya ta ci naman amarci ko? Amma tunda naga kunya ta hana ki ci, ba zan takura ki ba. Sai dai assignment ɗina na farko yanzu shi ne inyi ƙoƙarin cire miki wannan kunyar da take neman hana mu walawa yadda ya kamata. Don tsakani da Allah ni ba zan bari in cutu ba."
Bata amsa ba, sai ɗan murmushi da tayi kanta a sunkuye. Sannu a hankali ya cigaba da yagar naman yana korawa da lemu.
Shi ma kaɗan ya ci, don daman a ƙoshe yake. Maƙasudin siyo naman ita ce, kuma ta kasa ci sosai. Yana gamawa ya ɗauke komai ya kai kicin.
Yana dawowa ya fice zuwa ɗaya ɗakin bayan ya faɗa mata tayi shirin barci, yana dawowa.
Tunanin ya daren zai kasance a gare ta ne ya lulluɓe zuciyarta, bata ankara ba kawai sai sallamarsa ta ji a bakin ƙofa, ko kafin ta amsa har ya shigo ciki, ya maida kofar ya rufe, tare da kashe wutar dakin.
Ganin duhu ya mamaye ɗakin lokaci ɗaya yasa ta yi zumbur ta tashi tsaye tana laluben hanyar banɗaki. Bata san sadda ya tako zuwa gare ta ba, sai ji tayi caraf ya riƙota, lokaci ɗaya ya rungumota zuwa jikinsa.
"Haba Sanyin idaniyata, ni ne fa hasken Zuciyarki. Ko kin daina so na ne?"
Kanta yana jikinsa ta girgiza mishi kai a hankali.
"To tunda haka ne ki daina ƙoƙarin guduna. Ni fa ba dodo bane. Ba kuma zan taɓa cutar da ke ina sane ba. Na san profession ɗin ki da ilimin da kike da shi sun sanar dake duk wani abu na rayuwar aure. To menene kuma na wani shure-shure bayan ba ya hana mutuwa? Sannan kuma idan baki sani ba ina so yanzu ki sani, babban burina shi ne nan da wata tara ki bani takwarar Innaye ko abokin zuwa Masallaci."
Cusa kanta ta ƙara yi a ƙirjinsa a kunyace tana yar dariya.
"Au! Dariya na baki? Ko ya yi kusa ne?"
Kafin ta bashi amsa sai ta ji ya fara zuge zip ɗin rigarta. Sai kuma ya duƙar da kansa saitin wuyanta ya fara manna mata sumba, irin sassanyar sumbar nan da ke saka tashin tsigar jiki lokaci ɗaya.
Can kuma sai ya ɗago fuskarta ya haɗe leɓenta da na shi, ya cigaba da sumbatarta a hankali yana ɗan kallonta ta cikin hasken da ke shiga ta windojin ɗakin, idanunsu ya hade waje ɗaya, zallar soyayya da kauna haɗe da shauƙi da suke yiwa juna manne akan fuskokinsu ɓaro-ɓaro.
Ya ƙara rirriketa a jikinshi yana jin kamar ya tsaga kirjinshi ya sanyata a ciki ko ya samu ya huta da abinda yake ji a game da ita.
"I love you baby girl, so much. Bakina da kalmomina har sun fara gazawa wajen bayyana miki hakan. Kin shigo cikin rayuwata kin haskata a lokacin da na gama cire rai da samun wani haske. Ina ƙaunarki sosai, fiye da tunaninki."
Gaba-daya sai tsoron da take ji ya bar jikinta, ta daga ido ta kalleshi, zuciyarta na gaya mata wannan shi ne mutumin da ta amincewa ta mallakawa zuciya da ruhinta, wanda take yiwa so irin wanda bata taba yiwa kowa irinshi ba.
Bata san wa yayi motsi na gaba ba, ita ce ko shi? Kawai dai tasan cewa ta sake tsintar bakinta ne dumu-dumu cikin nashi, yana kwance duk wasu notikan kanta da suke kara maidata putty a hannunshi, ta kasa yin kataɓus.
Haka ya cigaba da lulluɓeta da soyayyarshi mai sanyaya rai, har bata san lokacin da ya kai ta kan gado ba, ya zare mata duk wata sutura ta jikinta. Ya hilaceta ta biye mishi suka keta hazon kauna, sai can da azaba tayi azaba ta fara shirin kwatar kwanta. Lokacin shi ai tuni ya gama yin nisa a duniyar da ta kaishi, baya jin kira balle ayi maganar dakatawa. Sai gashi tana bashi hakuri da kukan ya mata rai, shi ma yana bata hakurin.
Wannan dare dai bai saurara mata ba sai da ya maidata mace cikakkiya, sannan ya sarara mata, ya rungumeta cikin kirjinshi yana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa a lokaci guda. Kalamai yake amayar mata na godiya da zallar kauna, wadanda ita a karan kanta tasan cewa ba a cikin hayyacinshi yake fadarsu ba. Da yana sane kam da ya rage wani abun.
Dare ya tsala sosai lokacin da ya samu ya rabata da jikinshi da kyar, tana ta kuka da shessheka na azaba da zallan shagwaba. Shi da kanshi ya hada mata ruwan wanka bayan ya tsarkake jikinshi. Ya taimaka mata itama tayi wankan, yana bayin haka tayi a gabanshi duk da yadda taso ya fita.
Da ta gama kuma ya naɗe ta da showel dauketa cak kamar jaririya, bai dire ta ba sai da ya je kan kujerar gaban mirror, ya jona hand dryer ya mika mata don ta busar da kanta, shi kuma ya tafi dauko mata kayan barci da zata sanya.
Bayan gama ɗaɗɗaga kalolin rigunan barcin a ƙarshe ya zaɓa mata wata doguwar riga tsayinta iya gwuiwa, kalar ruwan hoda. Rigar ta yi kyau sosai a idanunsa. Ganin duk motsin da zata yi sai tace 'wash!' yasa shi sake ɗaukarta cak zuwa kan gadon da ya gyara da kansa..
Gabadaya ta bi ta gama rikitashi da salon kissarta, sai nan-nan yake yi da ita. A ƙarshe dai a ƙirjinsa yayi mata makwanci bayan ya kunna musu ƙwan lantarki mai duhu na barci, ko da ya duba fuskar wayarsa a lokacin, ƙarfe uku da kwata na tsakiyar dare.
Lumshe idanunsa yayi da zummar barci, zuciyarsa cike da matsanancin farin ciki da ƙaunar Kareema. Hannunsa na hagu dafe da tsakiyar bayanta, na dama kuma yana kanta yana aukin shafa lallausan gashin kanta da yake ta ƙamshi.
A hankali yake jin saukar numfashinta a saitin wuyarsa, alamun ta fara barci.
********
Da saurin gaske ya riƙo wayar da take ƙoƙarin suɓucewa daga hannunsa saboda tsananin mamakin da ya ji na maganganun da ke fita daga bakin Innaye.
Domin share ma kansa tantama, don tunanin ko kunnensa ne bai ji daidai ba ya saka shi cewa
"Innaye wai kika ce me?"
"Na ce ƙaniyarka Hafizu"
Ta faɗa daga can ɓangaren, muryarta na ɗan bayyana ɓacin rai, saboda karo na uku kenan yana sake tambayarta tana maimaita mishi magana ɗaya.
Ɗan dariya ya yi, idanunsa cikin na Ibrahim da yake tuƙa motar za su je gaisuwar surukai gidan Mummy.
"Allah ya baki haƙuri Innaye. Ɗazu ina cikin mota ne, kuma kin san iskar hanya na saka network yin rawa ba'a ji sosai. Don Allah kika ce Bintu mene?"
"Na ce maka ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na safiyar yau a ƙauyen nan ya yi ma Bintu. Da fari, duk mun zaci wani cin mutuncin ta zo yi mana, shi yasa bata samu wani tarba daga gare mu ba. Amma a yanzu tunaninmu ya canja Hafizu... Ina fatan dai ba tilastawa ko barazana kayi ma Bintu kan lallai dole ta zo ta bamu haƙuri cikin ƙanƙan da kai ba?"
"A'a! Wallahi ba ruwana Innaye. Ni ban san ma za ta zo ba."
Ya amsa da mamaki sosai a fuska da muryarsa.
"Madallah! To Bintu dai ta zo, ta bamu haƙuri sosai, har da kukanta Hafizu. Ta bi duk ɗakunan su Laraba da na Baffanku ta zauna dirshan a ƙasa ta nemi gafararsu. Wani abu da bata taɓa yi ba shi ne shan ruwan ɗakina, yau, ruwan randata Bintu ta sha Hafizu, na san ba ta shan komai ko cin wani abu na ƙauyen nan, shi yasa ko tayi banyi mata ba. Amma da ta ji ƙishi da kanta ta ƙarasa gurin randar ta buɗe ta ɗebo ruwa da kofina ba tare da wani ƙyanƙyami ba ta kafa kai ta shanye Hafizu. Kuma ka san wani abun ban al'ajabi?"
Innaye ta jefa mishi tambayar da muryar da ke bayyana jin daɗinta ƙarara kan irin yadda Bintu ta girmamata a yau.
"A'a ban sani ba. Sai kin faɗa Innaye!"
Ya amsa yana mamakin irin sauƙin halin Innaye da sam ba ta da riƙo, ka shekara dubu kana ɓata mata rana ɗaya idan ka tuba a gurinta an wuce gurin har abada. Lallai a gaida Innaye, a ɓangarenshi kam ko kaɗan bai ɗauki al'amarin a wani abu da Bintu take yi har zuciyarta ba. Ya daɗe da sanin ita ƙwararriya ce a pretending, don haka duk wani salo-salo na makircinta baza ta taɓa layance mishi ba.
Tunaninshi ya katse lokacin da Innaye ta cigaba da cewa
"Uhmmm! Da yake ban san za ta ci abincina ba, cikin ɗaki na barta na fita waje nayi aikin haɗa dambun zogale da Baffanku ya ce yana sha'awa. Wallahi ina gama haɗawa tun kafin inyi mata tayi ta ce
"Innaye a sammin dambun zan ci. Da mamaki na zuba mata, haka ta cire hijabin jikinta tana cin dambun nan tana shan ruwan randa, bata daina ci ba sai da ta cinye tas!
Ka ga abinda nake faɗa maka ko Hafizu? Shi ɗan Adam, ba'a taɓa yanke masa tsammani da shiryuwa zuwa hanya madaidaiciya... Na san a yanzu haka tunani kake kila wani ƙaryar ne yasa Bintu zuwa da wannan salon ko?"
Da mamakin yadda ta san tunanin da yake yi ya ce
"Ƙwarai kuwa Innaye. Kamar kin shiga zuciyata."
Ta yi dariya, sannan ta cigaba da cewa
"Hafizu kenan. To bari ka ji, da ace ana yanke ma bawa tsammani daga rahamar Ubangiji da ba'a ba bayi damar yin istigfari ba. Me yasa aka ce duk laifin da bawa ya aikata matuƙar ya tuba Allah zai yafe masa? Mu ma fa ƴaƴan Adam ne, muna kura-kurai da dama, kuma Allah yana yafe mana. Idan kuwa haka ne to me yasa mu a junanmu idan muka yi laifi baza mu yawaita yafiya ga kawunanmu ba? Daɗin gushi akan haka Kar dai ace ka manta da Hadithi na huɗu da ke cikin arba'una? Ko wane bawa kafin mutuwarsa sai littafi ya tabbata a kansa shaƙiyyun au sa'idun. Ina yi ma Bintu kyakkyawan zaton ta samu tuba ne tun kafin ajali ya riske ta."
Ta ƙarasa maganar tana jinjinawa. Kafin ya ce komai ta cigaba da jaddada masa maganar da take yi
"Tabbas! Na hango tuba da shiriya na gaske a idanu da halayen Fatima a yau ɗinnan. Sai dai dalilin tuba da shiryuwar cikin ƙanƙanin lokaci ne dai Allah kaɗai ya bar ma kansa sani.
Ni yanzu babban dalilin da yasa na kira ka shi ne, ko da ta zo bata tarar da su Rakiya ba. Rashida ta haihu a can Ƙauyen Wusar, sun tafi tun sassafe, ayi suna yau, gobe idan sun soya hakika su dawo gida. Na yi na yi Bintu ta komo Habuja yau ta ce baza ta bar ƙauyen nan ba ko da kwana za tayi sai su Rakiya sun dawo ta roƙe su gafarar irin abubuwan da ta aikata musu tun daga farkon aurenku har zuwa yanzu..."
"Innaye ita Bintun ce da kanta ta ce za ta kwana a Faƙo?"
Ya sake tambaya da maɗaukakin mamaki.
"Ƙwarai kuwa. Baffanku ma ya ce ta tafi, idan sun dawo shi da kanshi zai isar musu da roƙon gafararta ta ce ya yi haƙuri. Duk abinda ta ɓata ita da kanta take so ta gyara, ashe wai ko zuwa ta bamu haƙurinnan iyayenta da Yayarta sun so su biyo ta tace su bari ta taho ita kaɗai. Hafizu ko dai za ka kira ta a waya ka ce ta tafi kawai ba sai ta kwana ba...?"
"A'a Innaye!"
Ya katse ta da sauri.
"Ku ƙyale ta kawai.. Tunda dai ita da kanta ta ce za ta kwana ba wani ne ya takura mata ba ai shi kenan. Kar a matsa mata da cewa ta tafi kuma taga kamar baku yafe mata irin munanan laifukan da ta daɗe tana aikata muku bane..."
"Kuma fa haka ne."
Ta amsa da alamun gamsuwa da maganarsa.
"Yauwa to kin gani. Ku ƙyaleta kawai, ita tace ta ji ta gani ai. Duk yadda ta yiwu dai zan kira ki anjima. Yanzu muna hanya ne za mu je gaishe da iyayen Kareema."
"To Hafizu, Allah ya kaimu jimawar. Ina fata dai Kareematun tana nan lafiya?"
"Lafiyarta ƙalau Innaye."
Ya amsa fuskarsa cike fal da murmushin jin daɗi don an tambayi lafiyar abar ƙaunarsa.
"Madallah! Ka gaishe ta, yarinyar arziki. Tun da aka yi bikin nan yau kwanaki bakwai kullum da safe da yamma sai ta kira ni ta gaishe ni. Don Allah Hafizu ka riƙe matayenka da amana ka ji ko?"
"To Innaye. Na gode. In sha Allah zan ƙara kiyayewa."
"Madallah"
Ta amsa sannan ta aje wayar.
A ɓangaren Hafizu inda suka gama magana da Innaye nan ya watsar da zancen Bintu, ko Ibrahim bai ba labarin abinda yake faruwa ba, shi ma Ibrahim ɗin bai tambaye shi abinda yake faruwa ba.
******
Mintuna biyar Innaye ta ƙara a ɗakin Umma Laraba suna ƙara jajanta irin canjin da suka gani a gurin Bintu, sannan ta fice daga ɗakin zuwa na ta.
Da siririyar sallama ta shiga cikin ɗakin, tausayin Bintu ne ya kamata, ganin yadda take kishingiɗe akan daddumar Innaye da tayi sallah tana barci, kuma da alamun barcinta ya fara nisa, domin numfashi take saukewa cikin kwanciyar hankali.
Ƙara tabbatar da gaskiyar canjin da ta gani a tattare da Bintu tayi. Wannan ya wuce a ce duk tana yi ne don kissa ko makirci. Kamar dai ba Bintun nan mace ƴar gayu mai cike da ƙwalisa da gwalli ba. Bintun nan da ko akan kujerar ɗakinta ba ta iya zama sai ta shimfiɗa sabon daddumar da ko wane lokaci ba sa rabo da shi a mota. Yau ita ce kwance akan daddumar Innaye, ƙafafunta na taɓa dandaryar tile, lallai da gaske ne ba'a yanke ma bawa ƙauna daga rahamar Ubangiji.
Innaye ta sake ƙura ma Bintu idanu, sai a lokacin ta lura ba ƙaramin rama tayi ba, fuskarta ya ƙara tsawo, sai karan hancinta ya fito sosai. Nannauyar ajiyar zuciya Innaye ta sauke, sannan ta shige uwar ɗakinta da tafiyar sanɗa don kar ta tashi Bintu. Zuciyar Innaye cike da saƙe-saƙen ko auren da Hafizu yayi ne yasa Bintu yin laushi? Allahu aa'lamu. (Da yake ko da Baffa ya koma gida ranar ɗaurin aure bai faɗa ma Innaye Hafizu ya saki Bintu amma ya saka shi ya mayar da ita ba.)
Kusan ko wane ƙauye suna da ɗabi'ar shimfiɗa tabarmi a tsakar gida daf da sallar magriba, idan aka idar da sallah a fita tsakar gida yara da manya a zazzauna akan tabarmi. Wacce take da girki ta zuzzuba abinci, ana cin abinci ana hira. Wannan al'adar har yanzu ana yinta a ƙauyaku, musamman lokacin zafi.
Su Innaye suna zaune a tsakar gida, Umma laraba ce tayi tuwon dare, tuwon dawa miyar busasshiyar kuɓewa. Da an doshi gurin abincin babu abinda ke tashi sai ƙamshin daudawa.
Su Innaye suna zaune akan tabarma suna cin abinci a kwano ɗaya su uku, yara na zaune a gefe ɗaya. Ita kuma Bintu tana cikin ɗaki Innaye ta dafa mata ruwan zafi ta kai mata kayan tea, duk da ta ce a ƙoshe take ba ta jin yunwa, domin da rana dambu ta ci da yawa, har lokacin cikinta dam yake.
Ga mamakinsu kwatsam sai ga Bintu ta fito tsakar gidan, da murmushi a fusjarta ta zauna a gefen tabarmar da ta gani Innaye ta shimfiɗa a ƙofar ɗakinta.
"Sannunku da hutawa Innaye. Tun ina cikin ɗaki ƙamshin daudawa ke bugun hancina. Ko za a ɗan saka min tuwon kaɗan in ci..."
"Kin gani fa Hajiya Bintu."
Inna Ladiyo ta ɗaga kwanon tuwon da suke ci ta nuno ma Bintu da sauri, kafin Bintu ta amsa ta cigaba da cewa
"Tuwon dawa ne fa, kin gansa baƙiƙirin babu ko kyawun gani a ido sai laushi a baka. Wannan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 40