a tausashe ta fara magana har lokacin bata cire idanunta a cikin nasa ba.
"A irin koyi da tarbiyar da Mummyna ta ba ni, ta nunar mini miji yana da ƙololuwar daraja a gurin matarsa fiye da komai da kowa a rayuwarta. Idan na ce komai kuwa ina nufin komai, cikin komai da kowa ɗin nan kuwa har da iyayenta. Kuma idan ba na manta ba har a addinance ma haka ne, right?"
"Haka ne Beby"
Ya amsa mata yana jin wani shauƙi da girma na ƙara lulluɓe zuciyarsa.
Ko kusa bai fahimci inda maganganunta suka dosa ba, don haka ya ƙara buɗe kunnuwansa na basira yana sauraren inda za ta kai shi. Abu ɗaya dai da zai ƙaras da maganganunta ba na zafi bane shi ne, yadda tun a saɗarar farko na fara maganarta zuciyarsa ya ƙara cika da tumbatsa da alfaharin samun mace ta gari kuma mai tarbiya irin Bintu. Irin matar da hadithi ingantacce ya tabbatar duk namijin da ya same ta an bashi rabin addininsa, sai kuma ya ji tsoron Allah a sauran rabin.Ta sake ɓata wasu daƙiƙu masu ɗan dama tana ƙara tsara irin maganganun da za ta faɗa masa, waɗanda take da tabbacin za suyi kwanciyar girma da muhimmanci a zuciyarsa. Kuma zai ƙara yarda da gasken gaske ita ɗin fa mai son shi da ƙaunarshi, muhimmanci da girman da yake da shi a gurinta yasa sam ba ta iya haɗa al'amarinshi da na kowa.
"Ina jin ki Sweetheart"
Ya sake faɗa a tausashe don dawo da ita daga duniyar tunanin da ya lura tana ƙoƙarin lulawa.
7)
Lumshe manyan idanunta tayi a hankali, can kuma sai ta buɗe sannan ta saki wani nannauyan numfashi.
"A gidanmu, na taso na ga Mummy ba ta haɗa al'amarin Daddy da na kowa. Al'amarin Daddy da duk wani abu da ya shafe sa ako da yaushe kuma ko wani lokaci yana kasancewa na musamman ne a gurinta.
Da irin wannan tarbiyar ta raine mu, wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa duk wani al'amari na ka yana da matuƙar muhimmanci a gurina. Amma na lura kamar dai kai ba na maka gwaninta, ba na burge ka, kamar ma ka raina yadda nake ƙoƙarin sauke nauyin hakkinka da Allah ya ɗora min..."
Tayi ɗan shiru tana mayar da numfashi a raunane. Ya buɗe baki zaiyi magana da sauri ta girgiza mishi kai, ta ƙara da ɗora yatsarta manuniya akan laɓɓansa.
Tayi mar-mar da ƙwayoyin idanunta sai ga wasu siraran hawaye sun ziraro daga cikinsu.
"Don Allah Dear ka faɗa min, ta ina ne nake kuskure maka? Zuciyata baza ta iya jurar ganin yadda nake tattalinka da ƙoƙarin faranta maka kai kuma kana gwasale ƙoƙarina ba. A tunanina, ɓangaren iyaye daban na matarka daban! Duk mu biyun muna da girman haƙƙi a kanka. Me zai sa ka dinga ƙoƙarin nuna musu ni ɗin ba kowan kowa bace a gurinka?"
Ta ƙarasa mishi da tambayar wani raunataccen kuka na ƙwace mata. Kifa kanta tayi a ƙirjinshi, ta cigaba da rera kukan da ya ƙarasa kassara duk wani ɗan sauran karsashi da ƙwarin gwuiwa da suka rage masa.
Ya nemi kalamai a bakinsa ya rasa ɗif! Kamar ɗaukewar ruwan sama. Tsawon wasu daƙiƙu ya kasa ce mata komai, duk kuwa da yadda yake jin zafi sosai a zuciyarsa saboda yadda take rera kuka, kuma ya tabbatar wannan hawayen suna fita a dalilin wani abu na rashin kyautawa ne da shi da kanshi yayi mata.
Bayanta yake ɗan bubbugawa sannu a hankali alamun rarrashi.
"Kiyi haƙuri."
Ya iya faɗa daƙyar bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana kokawa da bakinsa kafin ya samu zarafin buɗewa har kalmomi biyun suka fita.
Sun ɗauki tsawon lokaci suna a haka, kafin daga bisani ya ɗauketa can-cak a jikinsa ya nufi banɗaki da ita. Ba yau ne karo na farko da ya fara yi mata wanka ya naɗo ta kamar ƴar jaririya ba, don haka a yanzu ɗin ma bai sha wata wahala ba, haɗin kai ta bashi ɗari bisa ɗari tun tana kukan har ta koma sauke ajiyar zuciya, duk inda yayi da ita haka take bin shi da ido har ya gama komai ya sake ɗaukarta ya mayar da ita gefen gado ya shimfeɗeta. Lallausan bargo ya rufa mata a jikinta ya ɗauki remot ya daidaita mata yanayin sanyin A.c, sannan shi ma ya shige banɗaki da niyyar yin wanka, ko kafin ya fito, har wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita.
Gefen gadon ya zauna, ya tsura mata idanu yana kallonta a tausashe. Kamar dai yau ne ya fara ganinta. Maganganun da ta gama rattaba masa ne yake sake bitarsu yana musu karatun dalla-dallah.
A iya hange da zurfin tunaninsa, bai ga ta inda ya kuskure mata ƙarara a tsawon yininsu na yau da har ta kasa danne ɓacin ranta ba sai akan sabbin kulolin nan da ya kwashi abincin ciki da yake mallakinsa ya kai ma mahaifiyarsa.
Daga shi har ita basu yini a gida ba balle wani abu na saɓanin fahimta ya gifta a tsakaninsu. Ko da sun yini tare ma, samun saɓani ko banbancin ra'ayi ba abu ne da ke yawan faruwa a tsakaninsu ba.
Soyayya da ƙauna mai tafe da yarda tsaftatacciya suka gina a tsakaninsu tun kafin kasancewarsu ma'aurata. Bayan sun dunƙule ta hanyar zamowa abu guda ƙarƙashin inuwar aure kuma, musamman suka zauna suka sake sabunta sabbin tsare-tsare akan waɗancan turaku uku da suke riƙe da igiyar soyayyarsu har ta kai su ga zama ma'aurata.
Da waɗannan dalilan yasa sam ba sa faɗa, saɓanin fahimta kuwa zai iya ƙididdige sau nawa suka same ta a iya zamantakewarsu na shekaru biyu.
Da gaske kamar yadda ta faɗa, ɓangaren mahaifiyarsa daban tata a matsayin matarsa daban. Ya zama dole ya ƙara yin tsayuwar daka wajen ganin ya ba kowa a cikinsu haƙƙinta da Allah ya ɗora mishi.
Zulaikha da yake kallonta da matsayin mai ƙara ma wuta fetur sannu a hankali zai bi da ita ya koya mata hankali cikin ruwan sanyi ba tare da Innaye ta zargi wani ba. Lallausan murmushi ya sakar ma Bintu da take barci, yasa hannu sannu a hankali ya shafi gefen fuskarta, sannan ya miƙe tsam daga gefen gadon.
Idanuwansa ne suka faɗa kan ɗan madaidaicin agogon da ke gefen gadon, ƙarfe shida har da minti biyu na yamma. Gaf ake da kiran sallar magriba, banɗakinsa ya koma ya ɗauro alwala, bayan ya fito kuma sai ya nufi gaban madubi ya fara shafa mai. Cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin jallabiya ya fice daga ɗakin zuwa falo.
Sai da idanunsa suka sauka akan teburin cin abinci sannan ya tuna a yinin yau gaba ɗaya bai ci wani ƙwaƙƙwaran abinci ba. Kuma wani abin mamaki shi ne sam ba ya jin yunwa, bayan ɗan tunani da yayi sai ya alaƙanta hakan da rashin nutsuwar da ya samu bayan dawowarsa gidan.
"Shaiɗaniya Zulai."
Ya faɗa a fili. Sai kuma yayi ƙwafa mai ƙarfi ya ƙara da cewa
"Zanyi maganinki. Ke baki isa ki zo ki hargitsa min zaman lafiya da kwanciyar hankalin da na ɗauki tsawon shekaru ina ginawa tsakanina da iyalina ba."
Kaɗa kai yayi yana cije laɓɓa ya fice daga gidan zuwa masallacin cikin layinsu da yaji an fara kiran sallar magriba.
***** *****
"Innaye sai kin dawo. Allah ya ƙara lafiya yasa mu ji alkhairi."
A karo na huɗu Zulaikha ta sake faɗin haka fuskarta a marairaice. Kamar za ta saka kuka.
"Amin Auta. To shi kuma ɓata fuskar ta mece ce? Ca nake kina ji Fatima ta ce da an gama gwajin za ta saka a dawo da ni gida?"
Innaye tayi maganar da sigar rarrashi hannunta riƙe da na Zulaikha.
"Innaye..."
"Ke dallah ki rufe mana baki anan gurin sakarya kawai. Sallama da addu'ar sun isa haka, ko an faɗa miki ke kaɗai ce kika damu da lafiyarta?"
Hafiz ya katse maganar da tayi niyyar yi cikin wani irin gigitaccen tsawa da yasa babu shiri ta saki hannun Innaye, a ɗimauce ta juya zuwa ɓangaren da aka sauke su da saurin gaske kamar za ta kifa a ƙasa.
Da kallo Innaye ta bi ta, sai kuma ta dawo da idanunta kan Hafiz ƙarara take nuna mishi rashin jin daɗin tsawar da yayi ma Zulaikha. Ta kasa daurewa, sai da ta ce
"Haba Hafizu. Saboda Allah menene aibun bankwana da kyakkyawar addu'ar..."
"Kiyi haƙuri Innaye. Kin ga fa tun ɗazu Bintu take jiran fitowarki. Kamata yayi ace yau ƙarfe bakwai na safe tana asibiti amma saboda ke kinga yanzu bakwai da rabi, kuma duk ba kowa ne ya janyo ɓata lokacin ba sai Zulai. Yi haƙuri ki hau mota ku tafi, na san in Allah ya yarda zuwa ƙarfe goma an gama komai za ta saka a dawo da ke gida."
Bata ce komai ba sai idanunta da ta ɗauke daga kan fuskarsa. Ta ɗan kalli Bintu da tun fara maganar Hafiz take haske shi da murmushi, ta ɗan girgiza kai ta yunƙura da nufin kai hannunta ta buɗe ƙofar baya na motar don ta shiga ta zauna.
Da saurin gaske Hafiz ya riga ta kai hannu ya buɗe mata ƙofar. Sai da ya tabbatar ta gama daidaita zamanta sannan ya sake yi mata a dawo lafiya ya maida ƙofar ya rufe.
Gurin matarshi da take zaune a mazaunin direba ya ƙarasa da murmushi a fuskarsa yake sake bata haƙurin ƙara ɓata mata lokacin da aka yi.
Har wannan lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba. A tausashe ta amsa mishi da cewa
"Kar ka damu My Dear. Komai zan iya yi don kai kaɗai. Bayan haka ma Innaye ta wuce komai a gurinmu, zan iya jure fiye da haka saboda ita."
Ƙaunarta da ganin girmanta ne ya ƙara cika mishi zuciya, bai iya mayar mata da zaƙaƙan kalamai ba saboda Innaye da ya san tana saurarensu illah cewa da yayi a taƙaice
"Na gode"
Sai ya ja da baya ya ɗaga hannu yana mata bye-bye ita kuma ta tayar da motar yana tsaye yana kallonsu har ta fice daga gidan bayan mai gadi ya wangale mata get.
Daga nan tsakar gidan, kai tsaye ɓangaren da aka sauki Innaye ya wuce. Babban burinsa ya ɗan sassaɓa ma Zulaikha kamanni kafin Innaye ta dawo gidan.
Wani rashin sa'a da yayi shi ne yana murɗa hannun ƙofar sai ya ji an rufe ta ciki.
"Ke! Ke!! Ke Zulai?"
Ya kira ta da sunan da shi yake faɗa mata cikin tsawa. Kafin ta amsa ya cigaba da magana cikin hargagi
"Me kike yi a cikin ɗakin har da rufe ƙofa? Zo ki buɗe min ƙofar nan yanzun nan tun kafin in shigo ciki in same ki."
Ƙirjinta ne ya buga daram! Tana jin shi, amma ta sake yin luf akan gadon ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa yi.
'Tun jiya ta san a masifar ƙufule yake da ita, sanin halinsa na mugunta musamman a kanta yasa sam bata so tafiyar Innaye asibiti ita a barta a gida ba.
Daga yadda ya daka mata gigitaccen tsawan da yasa ta baro Innaye a gurin mota ba tare da ta jira ta ga tafiyarsu ba. Ta ƙara yarda ma kanta lallai akwai wani mugunta da Yayan yake kitsawa a zuciyarsa game da ita, shi yasa ko da ta koma ɗaki ta shige ciki har ta zauna tana matsar ƙwalla sai kuma ta tashi da sauri taje ta rufe ƙofar ta murza ɗan makulli.
Shi da kanshi ya nuna musu yadda ake kulle ƙofar ranar da suka je gidan, ya kuma ƙara musu da bayanin idan suka kulle ƙofar suka bar mabuɗin a jiki to ko daga waje wani ya je da irin makullin zai buɗe ƙofar bazai taɓa buɗuwa ba.
A sadda yake musu wannan bayanin, bata ɗauki abin da wani muhimmanci ba, kawai dai ta saurare shi ne ba don ta wani ba bayanan nashi muhimmanci ba. A ganinta, cikin wannan ƙaton gidan, kuma a unguwar masu kuɗi da tun a ƙofar shigowa layin sojpji ne masu gadi wani abin cutarwa ne zaiyi gigin kawo musu farmaki? Ai kura ma ta san gidan mai babbar sanda. Ko ƙananun ɓarayi ƴan kuci ku bamu irin waɗanda ta sani a ƙauyensu da waɗanda take ji a labarai sun san irin gidajen da suke shiga suyi sata ba irin na Yayanta ba.
8)
Shi yasa daga ita har Innaye basu taɓa kulle ƙofar da makulli ba, ko wani dare da sun tura ƙofar a haka suke barin t...'
Da saurin gaske ta dawo cikin hayyacinta lokacin da ta sake jin muryarsa yana mata magana cikin faɗa da ɗaga murya.
"Zulai? Baza ki zo ki buɗe min ƙofar ba ko? Na san kina ji na. Na rantse da girman Allah idan kika bari na ɗauko safayar makulli na buɗe ƙofar Wallahi na lahira sai ya fi ki jin daɗi. Gara ma tun wuri ki buɗe in kora miki kashaidi da jan kunnen da zanyi miki a wuce gurin tun kafin in buɗe ƙofar da kaina."
A karo na biyu ƙirjinta ya sake bugawa daram! Ta zazzaro idanu a tsorace hannayenta biyu dafe da ƙirjinta. Tsoron ta Allah tsoronta ya buɗe ƙofar da kansa yayi mata mugun bugun da tunda uwarta ta haife ta ba'a taɓa yi mata shi ba. A raunane ta yunƙura da nufin tashi taje ta buɗe mishi ƙofar sai kuma ta sake tunawa da yadda yai ta jaddada musu idan suka kulle ƙofar suka bar makulli a jiki babu wanda zai iya buɗewa daga waje.
Ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke. Ta sake komawa tayi laƙwas akan gadon tana jin kwanciyar hankali kaɗan akan fargabar da ya lulluɓe ta.
Daga can waje shi kuwa bai fasa buga ƙofar yana zazzaga mata masifa da shan alwashin irin dukan da zai mata idan ta bari shi da kanshi ya buɗe ƙofar.
"Ai kuma sai kayi."
Ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda ta tabbatar bazai taɓa ji ba.
"Ta Allah ba taka ba, idan ka buɗe kar ka barni da rai."
Ta sake faɗa a hankali tana murguɗa baki kamar yana kallonta.
Ita kam ta rasa dalilin wannan ƙiyayya da Yayanta yake mata. Kamar ba ciki ɗaya suka fito ba? Ta ja tsaki ƙasa-ƙasa.
"Duk abinka dai baka isa ka canja ni a matsayin ƙanwarka ba."
Ta sake faɗa idanunta na kawo ruwa tana ƙoƙarin mayar da su ba. Da taji bugun ƙofar ya ƙi tsagaitawa yatsunta manuniya guda biyu tasa ta toshe kunnuwanta da ƙarfi, har ya gama hargaginsa ya wuce a gurin bata sake jin ɗuriyarsa ba.
******
"Innaye minti biyu don Allah, zan shiga gidan Raudha in karɓi wasu sakamakon gwaje-gwajen marasa lafiya a hannunta. Yanzu zan fito, ki jira ni a cikin mota."
Ko kafin Innaye ta amsa har ta buɗe ƙofar motar ta fice, da makullin hannunta tayi amfani wajen kulle motar ta waje sannan ta shige cikin gidan da ta kira na Raihana.
Fiye da mintuna arba'in ta ɓata a cikin gidan bata fito ba. Tun Innaye tana zaman daɗi har ta koma yin na wahala, kasancewar gilashin ɓangaren da take zaune kaɗai a buɗe, kuma shi ma ɗan kaɗan ne a buɗe, shi yasa shige da ficen iska yayi ƙaranci a cikin motar.
Innaye ta haɗa zufa tayi kashirɓin. Kayan cikinta sai hautsinawa suke yi kamar za tayi amai duk da babu abinda ta karya da shi. Ta muskuta ya fi sau ashirin, tun tana iya fifita da gefen hijabin jikinta har tayi laƙwas ta zuba ma sarautar Allah idanu tana jira taga ta inda Bintu za ta ɓillo.
Can bayan wasu mintuna goma sha biyar sai ga Bintu ta fito daga cikin gidan ita da wata matashiya da baza ta wuce sa'arta ba suna magana suna dariya. A ƙofar falon gidan suka sake tsayawa, akan idanun Innaye suke maganar da ba ta jin me suke cewa saboda tazarar da ke tsakaninsu suna nuna motar da take ciki da yatsa manuniya suna cigaba da ƙyalƙyala dariya.
Don tsananin baƙin ciki da takaici, Innaye bata san sa'adda ta sunkuyar da kai wani zazzafan hawaye ya silalo daga cikin idanunta ba. Da saurin gaske tasa babbar yatsa ta ɗauke hawayen tun kafin Bintu da take ƙarasowa gurin motar fuskarta a ɗaure tana daddana waya ta ga kukanta.
Kamar ba ita ne ta gama ƙyalƙyala dariya da Aminiyarta ba. Ta buɗe baki a cushe ta ce
"Innaye yi haƙuri fa. Na ɗan daɗe ko?"
Innaye kasa cewa komai tayi, don a yadda take jin ɓacin rai a zuciyarta, lallai tana buɗe baki da nufin yin magana tabbas mummunar magana za ta faɗa. Shi yasa tayi shiru don koyi da faɗin Fiyayyen halitta SAW.
Bintu ma bata ƙara cewa komai ba ta tayar da motar ta ɗaga ma ƙawarta da ke tsaye can nesa hannu ta figi motar a guje suka fice daga gidan.
Kasancewar gudu take da motar ba kaɗan ba cikin ƙanƙanin lokaci ta isa asibitin da take aiki.
Izuwa wannan lokacin, Innaye da take zaune a bayan mota ta kai matuƙa wajen galabaita, abu goma da ashirin ne ya haɗe mata, ga yunwa, kasancewarta mutumiyar ƙauye wacce tayi sabo da karin kumallo da sassafe matuƙar ba azumi take yi ba, ga gajiyar zaman da tayi a cikin mota ga zafi da ya fara taka muhimmiyar rawa gurin fara galabaitar da ita. Ga irin gudun da Bintu tai ta zugawa da motar kamar wacce za ta kai wasiƙa.
Gaba ɗaya kayan cikinta sun takura sun dunƙule guri ɗaya, miyau bakinta sai tsinkewa yake yi, alamun ko wane lokaci amai yana iya kawo mata ziyarar ba-zata duk da babu komai a cikinta. Ita kaɗai take sakin nishi sama-sama.
Bintu tana jin ta sarai, kuma tana kallonta ta madubin da ke gaban motar. Amma ta tafasa sauke bata ce mata don tsananin haushin tsohuwar da jikanyarta da take ji tun bayan abinda ya faru jiya. In banda hanya mai haɗin zumuntar dole ta ina za ta haɗu da wannan baƙauyiyar balle har wani dangata ya ƙullu a tsakaninsu?
Shi yasa a mafiyawancin lokuta take ƙara godiya ga Allah da ya kasance Hafiz ɗin ta bai ɗauko kamannin tsohuwar ba. Da marigayi mahaifinsa yake kama, mahaifin nasa kuwa ya kasance kyakkyawan bafulatani ne amma mazaunin ƙauye.
Ta ɗauki tsawon mintuna biyu tana ƙara gyara kwalliyar fuskarta da kayan kwalliyar da ta ciro a cikin jakarta, bayan ta gama ta ciro wani farin gilashi ta ƙwama a idanunta sannan ta buɗe ƙofar ta fita.
Har ɓangaren da Innaye ke zaune ta zagaya ta buɗe mata ƙofa sannan ta ce
"Fito muje Innaye."
Sau uku tana yunƙurin fitowa sai kuma ta koma ta zauna laƙwas! A galabaice, Bintu na kallonta amma sai ta kawar da fuska kamar ba ta ga abinda ke faruwa ba. Sai a karo na huɗu Innaye tayi ƙarfin halin fitowa daƙyar ta tsaya bisa ƙafafunta da taimakon motar da ta jingina da ita.
"Innaye daurewa fa za kiyi, saboda Allah kina gani dai asibiti muka shigo, kuma bamu taho da Zulai ba balle ta dinga ɗawainiyar riƙe ki zuwa ɗakin gwaje-gwaje. Ni kam muna shiga ciki Ofis ɗina zan wuce don marasa lafiya na can na zaman jira na, ƙoƙari ɗaya da zan iya miki dai shi ne zan haɗa ki da ma'aikaciyar jinya ɗaya ta raka ki ɗakin gwaji. Ina fatan dai baki ci komai ba tun bayan tashin ki da asubah?"
"Eh"
Ta amsa daƙyar! tana jin yadda ɓacin ranta ke ƙara hauhawa. Gefe ta kawar da fuskarta ta tofar da miyau mai yawa kwaɓal, sannan ta sake mayar da fuskarta tana kallon Bintu da take aiko mata da kallon ƙyama a fili.
"Haba Innaye! Wani irin ƙazanta ne kike mana haka saboda Allah? Ki kiyaye pls! Nan fa asibitin birni ne ba irin na can ƙauye da kika saba gani a wulaƙance ba."
Bintu tayi maganar da muryar faɗa-faɗa kamar tana yi da ƙanwarta. Sai kuma ta ja tsaki ƙasa-ƙasa ta cigaba da cewa
"Ki jira ni anan, zan turo a shiga da ke ciki."
9)
Daman tunda za ta fito daga cikin motar ta gama tattaro duk ƴan kayayyakinta, Don haka kulle motar tayi da makulli ta nufi cikin asibitin ko waige ba ta yi, zuciyarta a ɗugunzume da ganin wannan ƙazantar da Innaye ta tofar a gabanta, ji take kamar za tayi amai. Har ta ƙarasa cikin asibitin tsaki take ja akai-akai fuskarta a ɗaure.
A karo na biyu, wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanun Innaye, da sauri tasa hannu ta share tana ɗan waige-waige. Ganin babu mai kallonta yasa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana ƙara sakin nauyinta a jikin motar.
Zuciyarta cike da mamakin yadda halayen mutane ke saurin sauyawa a mabanbantan lokuta.
'Duk da shedar da suka yi ma Bintu na sanin kirkinta ragagge ne. A karon farko na zuwa da ita asibiti washe garin ranar da suka zo garin, ko kaɗan bata fuskanci irin wannan tozarci da wulaƙancin daga Bintu ba. Ko don a wancan ranar tare suke da Hafiz shi yasa Bintu tayi musu tarbar arziki tayi ta ina aka saka ina aka aje da su?
Da ta san a wannan karon lamarin zai sauya, tabbas da ta tilastawa Hafiz su taho tare kamar wancan lokacin, ko kuma ta matsa mishi lallai Auta tayo mata rakiya. Ga shi garin sauri da gudun ɓatawa Bintu lokaci yasa ta manta da wayarta a gefen gado.
Da a gaban Hafiz ne ta tabbata Bintu baza tayi mata haka ba. Ko a gaban Auta ne ta tabbata wulaƙancin da Bintun za tayi bazai kai haka ba, don sam! bakin Auta ba ya mutuwa duk kuwa da yadda take yawan tsawatar mata. Ba ta taɓa yin shiru musamman kan abinda ya shafi mahaifiyarta ko ƴan'uwanta.
Da ace kuma ta taho da wayarta, wata ƙila da ko ɗaya daga cikin ƴaƴanta mata da suke can ƙauye ta kira za su ɗebe mata kewa da wannan dunƙulallen ɓacin ran da ya tsaya mata a wuya shi bai sauka ciki ba kuma bata amayar da shi ba...'
"Assalamu alaikum! Wai ke ce Innaye?"
A bazata ta ji saukar wata zazzaƙar murya a kunnuwanta. Kafin ta amsa sallamar, sai da ta ɗago idanunta ta kalli matashiyar yarinyar da take tsaye a gabanta sanye da kayan ma'aikatan jinya, lokaci guda kuma tana aika mata da wani sassauƙan kallo mai tafe da rangwame.
Sallamar ta fara amsawa, kafin ta ƙara da cewa
"Eh ni ce."
"Yauwa! Ina kwana? Daman Dr. Bintu ce ta aiko ni in shiga da ke ciki."
"To! Na gode."
Ta amsa a raunane. Har ta yunƙura za ta ɗaga ƙafarta da niyyar fara tafiya sai tayi taga-taga kamar za ta faɗi ƙasa.
"Subhanallahi! Sannu Innaye. Kiyi a hankali fa kar ki faɗi."
Yarinyar ta jera maganganun cikin sauri a lokaci guda kuma tasa hannayenta duk biyu ba tare da wani ƙyama ba ta tare Innaye daga faɗuwa ƙasa.
"Sannu!"
Ta sake faɗa a karo na biyu.
"Idan baza ki iya tafiya ba sai in ɗauko kujerar asibiti ki zauna in tura ki zuwa ciki."
Ta sake faɗa a tausashe. Ƙarara fuskarta ke nuna yanayin tausayi da jin ƙai da ake buƙatar gani a fuskar duk wani ko wata ma'aikaciyar lafiya.
"Zan iya! Na gode Yarinya."
Innaye tayi maganar a hankali. Har za tayi shiru sai kuma ta ga kar ta cuci kanta, da alamun wannan yarinyar da bata sani ba tana da kirkin da yayi ma Bintu ƙaranci. Sai ta ƙara da cewa
"Kawai dai na ɗan galabaita ne da zaman mota ga kuma tsayuwar da daɗe ina yi anan. Idan baza ki damu ba, don Allah ko hannuna ne ki ɗan riƙa mu ƙarasa ciki in samu gurin zama..."
"Laaa... don wannan babu komai Wallahi. Mu je."
Matashiyar ta katse Innaye da taƙaitaccen fara'a a fuskarta.
Haɗuwar jini ne na farat ɗaya ya faru tsakanin Innaye da matashiyar ma'aikaciyar jinyar nan. Tallafin da Innaye ta samu a lokacin da bata taɓa tsammani ba yasa tayi wani irin sakin jiki da Matashiyar kamar dama can sun daɗe da sanin junansu.
Ita kuwa yarinyar kasancewarta mai surutu da saurin sabo, ga kuma ƙauna ta farat ɗaya da taji tana yi ma Innaye yasa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 40