Zulaikha tayi ta haye ruwan cikinta tayi mata wani mugun shaƙa, ko da ta kalli cikin idanun Bintu, matsanancin tsoro da firgici ne suka ƙara lulluɓeta ganin yadda idanunta suka kaɗa suka yi jajur.
"Munafuka, algunguma, matsiyaciya, tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairi ba. Da gaske ne an ɗaura miki aure da Mijina Hafiz ko kuwa wancan tsohuwar banzan ƙarya take min?"
Ta ƙarasa da tambayar tana zazzaro ma Zulaikha idanu kamar wacce ta hau aljanu.
[1/28, 7:23 PM] Fareeda Abdallah: Sai a lokacin Zulaikha ta fahimci dalilin haukar Bintu, idanu ta ɗan runtse jin yadda Bintu take ta ƙara tattare hijabinta da wuyanta tana ƙara shaƙo ta da hannayenta duk biyu. Lokaci ɗaya kuma tana ƙara maimaita mata tambayar cikin tsawa da ɗaga murya
"Za ki amsa min tambayar da nake miki ko sai na illata ki? Da gaske ne ƙiyayyar da matsiyata kuma ƙauyawan iyayenku suke min ya kai matsayin da yasa suka aura ma mijina ke ko ƙarya tsohuwar banzan nan take min?"
Da ɓacin ran yadda Bintu take ta furta kalaman tozarci ga iyayensu saboda mahaukacin kishi da ya rufe mata idanu yasa ta amsa mata tambayar ita ma cikin tsawa da ɗaga murya.
"Eh! Da gaske ne. Shekaran jiya an ɗaura aure na da Yaya Hafiz. Idan kina da abinda za kiyi ko kuma kin isa kiyi wani abu sai kiyi."
Tana gama faɗin haka da ƙarfi tasa hannuwanta biyu ta ɓamɓare hannayen Bintu daga wuyanta, tayi kukan kura ta wancakalar da Bintu daga ruwan cikinta ta miƙe tsaye a zafafe.
"Ke jaka kuma dabbar ina ce da za ki dinga zagin tsofaffin da suka zama silar zuwan mijin da kike taƙama da shi duniya? Ko kina tunanin tsoronki suke ji da za su zuba ido kiyi ta wulaƙanta su a gidan ɗan da suka haifa da cikinsu? Wannan auren ba kowa ne ya janyo shi ba face ke da kanki, baƙin halinki da mugun halinki na dabbobi yasa suka nema ma kansu mafita ta hanyar ɗaura ma ɗansu aure da ni. Domin sun san duk tsiya ni bazan taɓa wulaƙanta su ba, ranar naka sai naka... ko sun fi haka ƙauyanci da jahilcin da kike kira bazan taɓa tozarta su ko in banbanta su da nawa iyayen ba..."
A haukace, Bintu ta sake ƙwallah wani gigitaccen ihu a karo na biyu. Kalaman Zulaikha kamar zuban tafasasshiyar dalma haka suke sauka a kunnuwanta zuwa ƙwaƙwalwarta.
"Ni za ku ciwa amana??? Ni kike faɗa ma irin waɗannan banzayen maganganun? To na rantse da Allah yau ko ni ko ke a gidannan. Zan kashe ki har lahira, in ga uban da ya isa ya tsaya miki duk faɗin tsinannen ƙauyen naku da jahilan iyayen naku da kike taƙama da su."
Bintu tana gama faɗin haka, da mugun gudu ta nufi cikin babban kicin ɗin ta da yake falon. Ɗaya daga cikin sababbin wuƙaƙenta manya masu masifaffen kaifi waɗanda bata taɓa amfani da su ba ta ɗauka, ta sake ficewa da gudun gaske.
Zulaikha da take tsaye hannuwa riƙe da ƙuƙumi tana huci duk ga tsammaninta Bintu taɓarya za ta ɗauko, shi yasa ta tsaya domin ta gwada mata idan hauka da ɗanyen kai take ji ta dame ta ta shanye.
Hango wuƙar da ke ƙyalli a hannun Bintu yasa ta zare ido, bata tsaya raba ɗayan biyu ba ta juya da gudu zuwa ɗakin da aka yi mata masauki, tana shiga ta danno ƙofar Bintu ta isa gurin. Daƙyar ta samu nasarar murza makullin ƙofar daga can ciki ta kulle tana numfarfarshi.
Bintu a haukace ta kai ma ƙofar wani wawan suka da wuƙar hannunta, amma da yake dakakkiyar ƙofa ce mai tsada ɗan karcewa kaɗan jikin ƙofar tayi.
"Ashe ke ƙaramar mara kunya ce? Jaka, kucakar ƙauye dabba, na rantse da Allah yau sai na ga bayanki a gidannan. Zan nuna miki mijina nawa ne ni kaɗai, ko da macen birni ƴar gayu bata isa inyi sharing ɗin shi da ita balle ke da nake miki kallon ƙazantacciya a cikin dabbobi. Na rantse da Allah yau sai na bar ma waɗancan munafukan tsofaffin mummunar tabon da bazai taɓa gogewa a zukatansu ba. Zan kashe ki, in kashe banza a banza, duk faɗin ƙauyenku sai in ga idan da shegen da ya isa yayi shari'a da ni..."
A haukace ta sake kaima ƙofar wani wawan tokari da ƙafafunta, ihu ta ƙwallah saboda azaban zafi da raɗaɗin da ya ratsa ƙafar nata lokaci ɗaya, sai kuma ta zube ƙasa ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka gwanin ban tausayi, hannayenta duk biyu ɗore a kanta. Ga kuma wuƙar da take riƙe da shi tsirara har lokacin bata yar da wuƙar ba.
A haka Hafiz ya shiga cikin falon a sukwane Raudha na biye a bayanshi. Ya matsa zai ƙarasa kusa da ita da saurin gaske ta nuno shi tsinin wuƙar hannunta.
"Munafuki! algungumi!! maci Amana!! Wanda bai san darajar Alƙawari ba!!!"
Ta jefa mishi munanan kalaman cikin matsanancin kuka na tashin hankali.
"Na rantse da Allah idan ka ƙaraso kusa da ni sai na caka maka wuƙar nan sannan in cakawa kaina. Gara duk muyi mutuwar kasko in san babu wata tsinanniya da za ta sake rayuwa da kai a matsayin mijin aurenta."
Ta cigaba da magana cikin kuka.
Hankalinsa a tashe, ya fara mata magana da taushin murya don ya kwantar mata da hankali.
"Bintu, Bintu, kin ga, don girman Allah kiyi haƙuri ki ajiye wuƙar, ki saurare ni..."
"Me zan saurara?"
Ta katse shi cikin tsawa tana wani zaro mishi idanu kamar ba ita ba.
"Ƙarya? Ko kuwa kalamanka na yaudara da daɗin baki da ka saba cika kunnuwana da su? Ayau na tabbatar babu soyayya tsakanina da kai Hafiz, kuma na rantse da Allah sai dai idan Munafukar Allah ta'alan nan baza ta fito daga ɗakinnan ba, sai na kashe ta har lahira, sai dai duk abinda zai faru ya faru."
Bai san muhimmancin tahowa da Raudha da yay ya kai ƙololuwa ba sai da yaga cikin hikima ta ƙarasa kusa da Bintu ta rungumota jikinta, sannan a dabarance ta zare wuƙar da ke riƙe a hannunta tayi hurgi da shi gefe ɗaya.
Cikin kuka da magagin kishi take yi ma Raudha bayanin abinda Hafiz yayi mata.
"Ki ƙyale ni Raudha... Hafiz ya ci amanata... ku kuke faɗa min namiji ba ɗan goyo bane ni kuma ina muku tutiyar nawa ɗan goyo ne har da majanyi... Ashe duk mazan mamugunta ne halayensu ɗaya? Ashe da gaske ne da Hajiya Binta take yawan faɗin Namiji ƙanin ajali? Wai Raudha kamar ni Hafiz zai yaudara? Ni zai ciwa amana ya karya min alƙawari? Ƙauyensu ya tafi aka ɗaura masa aure da tsinanniyar ƙanwarsa amma saboda ya raina ni shi ne yake faɗa min ya taho da ita ne don ta taya ni aikin gida? To na rantse da Allah sai na kash..."
Da saurin gaske Raudha tasa hannu ta rufe mata baki. A tausashe ta fara ma Bintu magana, fuskarta na bayyana yanayin ɓacin rai da jimami, alamun itama tana jin ciwon abinda Hafiz ɗin yayi ma Aminiyarta.
"Tabbas! Hafiz bai kyauta ba Bintu. Amma kar ki manta, idan hankali ya ɓata hankali ke nemo shi. Yanzu abinda nake so da ke kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki. Ki sama ma kanki nutsuwa ko ɗan kaɗan ne don mu samu mafita cikin ƙanƙanin lokaci. Tashi mu tafi zuwa ɗakin ki, Hafiz ɗin me? Ina ƙudan yake balle romonsa? Ai shi ma ya san yayi kaɗan, ba irinmu ake yiwa wannan cin amanar a zauna lafiya ba."
Da ire-iren waɗannan kalaman tayi amfani har ta samu nasarar miƙar da Bintu tsaye, tana riƙe da ita a jikinta suka taka a hankali tana sake faɗa kalaman kwantar da hankali har suka haura sama zuwa ɗakinta.
Suna ɓace ma ganinsa, hankalinsa a ɗugunzume ya ƙarasa zuwa ƙofar ɗakin. Ya daɗe da sanin Bintu tana da masifaffen kishi, amma bai taɓa tsammanin kishi zai iya rufe mata idanu har tayi yunƙurin kisan kai ba. Yau in da ace kafin dawowarsa gidan ta samu nasarar caka ma Zulai wuƙar nan fa?
"A'uzu billahi minasshaiɗanirrajim"
Yayi ta'awizi da sauri yana ƙoƙarin kawar da mummunan tunanin daga zuciyarsa.
Wuƙar da Raudha ta cillar zuwa gefe ɗaya ya fara ɗauka ya kai kicin ya ɓoye, ba ma ita wannan wuƙar ba, duk wasu wuƙaƙe manya da ƙananu da suke kicin ɗin kwashe su yayi gaba ɗaya zuwa cikin wata durowa ya kulle, ya zare makullin ya jefa a aljihu.
Ƙofar ɗakin da Bintu take ciki ya koma ya fara ƙwanƙwasawa. Bintu da take ciki hankalinta a tashe, izuwa wannan lokacin ta shiga bayi sau biyar don tsananin firgita da tashin hankali. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zabge gaba ɗaya kamar wacce ta kwana ta yini tana amai da gudawa.
Duk irin maganganun da Bintu take yi tana jin ta. Ta kunna wayarta ya fi sau talatin don kiran can ƙauye ta bada wasiyyar halin da take ciki, amma da yake matsiyaciyar waya ce da ta kawo sai ta ɗauke. A ƙarshe ma wayar sai ta daina kawowa. Tsananin tashin hankali yasa ta zube a ƙofar bayi tana sharɓan hawaye, hannayenta duk biyu dafe da bakinta, don kar sautin kukanta ya fita balle har ta ƙara janyo ma kanta wani tashin hankalin daga Bintu.
Tana cikin wannan halin ne taji an fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da ɗan ƙarfi. Idanu ta zazzaro a tsorace, ta cire hannuwanta daga baki ta ɗora a kai hankalinta a tashe. Ko da ta ji ƙwanƙwasar ya ƙi tsagaitawa sai ta yanke ma kanta shawarar gara ta fara ƙwallah ihu, wataƙila idan aka ji ihunta ya karaɗe gidan wasu daga cikin ma'aikata suyi ƙoƙarin kawo mata ɗauki.
Ta buɗe baki za ta yanka ihu kenan sai ta ji muryar Hafiz a fusace yana cewa
"Zulai don ubanki baza ki zo ki buɗe ƙofa in fitar da ke daga gidannan ba? Na rantse da Allah idan kika yi wasa zan ficewata in ƙyale ki da Bintu, in yaso ba caka miki wuƙa ba, idan taga dama ma ta ƙona ki ƙurmus! Ko babu komai an rage mugun iri a doron ƙasa..."
Tsulum! Ya ganta a gabansa ba tare da ya ji sadda ta buɗe ƙofar ba. Kallo ɗaya yayi mata ya gane a bala'in firgice kuma a tsorace take, Zulai da ba ta ƙaunar zama ba hijabi sai ga ta tsaye a gabansa ƙiƙam babu hijabi babu ɗankwali. Rigar ma duk ta tattare, har yana hangen wani sashe daga farin fatar cikinta. Ko da ya kalli idanunta duk sun zurma ciki sun canja kala.
Da bala'in haushi da takaicinta da ke cike da zuciyarsa ya galla mata harara.
"Ina hijabinki?"
Da saurin gaske ta koma cikin ɗakin jikinta na rawa ta fito riƙe da hijabin a hannunta, ta ma kasa sanyawa, sai da ya daka mata tsawa da umarnin ta saka hijabin mana, sannan ta saka a baibai tana ta zare idanu tana waige-waige don kar Bintu ta shammaceta ta caka mata wuƙa.
Lura da yayi Zulaikha fa ba ta a cikin nutsuwarta, harara ya sake galla mata sannan yasa hannu ya finciki hannunta ɗaya ya matsar da ita daga ƙofar ɗakin ya shige ciki. Ɗankwalinta da ya gani yashe a ƙasa, wayarta da ke ajiye a ƙofar bayi da takalmanta da suke ajiye a bakin ƙofa ya ɗauka ya cusa mata a cikin jakar kayanta.
Duk abinda yake yi shi ma a gurguje yake yi da tsoron kar Bintu ta fito ta tarar da Zulai a falon. Bai tsaya ba ta umarnin su je ba kawai ya finciki hannunta da sauri tana biye da shi tana harharɗewa har suka fice daga cikin falon.
Bai saki hannunta ba, sai da ya buɗe ƙofar baya na motar ya zaunar da ita a ciki, ya aje jakar kayanta a kusa da ita sannan ya mayar da ƙofar ya rufe.
Mal Musa har ya taso a zatonshi tare za su fita amma sai Hafiz ya dakatar da shi.
"Yanzu zan je in dawo Mal Musa, ba nisa zanyi ba. Idan na dawo sai mu koma Ofis."
Makullin motar ya amsa ya shiga mazaunin direba ya figeta a guje suka bar gidan.
Hankalin Zulaikha bai fara kwanciya ba sai da taga sun bar unguwar gaba ɗaya, sun harba kan babban titi suna ta ɓanana gudu. A fili taja wani nannauyan ajiyar zuciya da yasa Hafiz ɗan kallonta ta cikin madubi.
Harara ya sake gallah mata, ya ƙara da jan wata doguwar tsaki, ya saki wata ƙaƙƙarfan ƙwafa.
Duk abinda yake yi tana jin shi, amma ko kallo bai ishe ta ba. Sai ƙara gyara zamanta tayi akan kujera a fili ta fara godiya ga Allah, addu'a lokaci ɗaya tana haɗawa da sambatu.
"Allah na gode maka da ka kuɓutar da ni. Allah kasa ko mutuwata ce tazo bazan mutu a wulaƙance hannun wacce ba ta so na, ba ta ƙaunata, kuma bata san darajar rayuwata ba. Na yi dambe iri-iri zamanin yarintata, na ga dambe-dambe kala-kala a rayuwata. Amma irin wannan ta'addancin damben da ake amfani da wuƙa mai shegen tsini da kaifi ban taɓa yi ba, kuma ban taɓa gani ba. Sai yau a gurin matar birni da take tutiya da wayewa amma ta bari linzamin kishi ya ja ta zuwa hauka, har take yunƙurin aikata abinda ni ƴar ƙauye bazan taɓa aikatawa ba..."
"Ƙiiiiiii..."
Ya taka wani wawan burki da yasa ta katse surutan da take yi a tsorace. Ta ɗaga kanta a firgice tana kallonsa. Sai taga ashe har ya gangara gefen titi bata sani ba, hankalinta a tashe take kallon yadda ya buɗe ƙofarsa a fusace ya fita daga cikin motar.
Tana kallonshi, har ya gangara gurin wani mai kanti da yake can gefen hanya. Baza ta iya cewa ga takamaimai abinda ya aikata a gurin ba, tunda hangen bayansa kaɗai take yi daga cikin mota. Yana hanyar dawowa dai ta hango shi yana saka wani abu a cikin aljihun rigarsa.
: Duk da bata taɓa yin doguwar tafiya a motar haya ba, amma ta gama sakankancewa tashar mota zai kai ta ya saka ta a motar zuwa Faƙo. Bata ankara duk doguwar tafiyar da suke yi ba tasha suka nufa ba sai da taga ya faka motarsa a ƙofar wani gida madaidaici amma kuma mai kyau tun daga waje.
"Fito muje."
Ya umarceta bayan ya fita waje, fuskarsa a ɗaure tamau. Babu walwala ko misƙala zarrah.
A tsorace ta kalle shi, ta sake kallon ƙofar gidan da suke tsaye a gabansa. A marairaice ta ce
"Yaya ina ne nan ɗin ka kawo ni? Dan girman Allah kayi haƙuri ka saka ni a motar zuwa gida. Wallahi gaba ɗaya a firgice nake da Habujan nan, ka taimaka ka mayar da ni gurin Innaye inda na fi wayau."
Sai ga hawaye sun zubo mata shar... Da rawar murya ta cigaba da cewa
"Ni Wallahi daman auren nan yadda kake jin tsanarsa a ranka na ma fi ka jin tsananin tsanarsa a zuciyata. Ka kwantar da hankalinka, idan ka mayar da ni gida salin-alin na yi alƙawarin zan bi duk hanyar da ya kamata gurin wanke ka a gaban Baffa da Innaye. Bazan taɓa bari su ga laifinka ba, Wallahi da gaske nake yi..."
"Za ki koma gida, amma ba yanzu ba. Don haka gara ma ki rufe min tsattsamar bakinki tun kafin in canza shawarar da na yanke. Fito muje."
Ya sake ba ta umarnin da tsawa a muryarsa.
Tana hawaye, ta fito daga cikin motar ta tsaya ɗan nesa da shi. Shi ya buɗe motar ya fito mata da jakar kayanta, ya zage zip ɗin ya fito mata da takalminta ya bata umarnin ta sa a ƙafafunta. Bayan ta saka ya sake umartarta da ta gyara hijabinta da yake a baibai, har ta gama gyara hijabin hawayen idanunta basu daina sauka a guje kamar an buɗe famfo ba.
Hannu yasa a aljihunsa ya zaro kuɗi masu ɗan dama za su kai dubu ashirin ƴan ɗari biyar-biyar ya damƙa mata a hannunta.
"Ki riƙe wannan, ko za ki buƙaci wani abun ba ni a kusa. Nan ɗin gida ne na mutanen kirki da karamci ba na so ki ishe su da bani-bani. Kina ji na?"
A raunane ta ɗaga mishi kai alamar ta ji.
Hannunsa ya sake cusawa a aljihu ya zaro wata farar takarda da take a nannaɗe, ɗan shiru yayi yana kallon takardar. Sai kuma ya sake naɗe takardar sosai ya miƙa mata
"Ki ɓoye wannan a cikin kayanki, idan kin samu nutsuwa kin dawo cikin hankalinki sai ki karanta..."
"Takardar mece ce Yaya?"
Ta tambaye shi tana ɗan jujjuya takardar a hannunta.
"Muhimman bayanai ne waɗanda ba ni da lokacin da zan iya ɓatawa wajen karanto miki su da bakina. Allah yasa dai su Baffa basu yi asarar kuɗin tara ba, domin da turanci na rubuta. Wuce muje."
Jikinta a sanyaye ta bi bayansa, ranta a ɓace da baƙar maganar da ya gwaɓa mata da ya ce anyi asarar kuɗin tara. Ta sani tabbas asarar kuɗin taran aka yi, domin baza ta iya karanta dogon rubutu da turanci ba. Sai a wannan lokacin Mashkura da alƙawarin da tayi mata na koya mata karatun turanci ya faɗo mata a zuciya.
'Ba komai. In da rai, da rabo.'
Ta ayyana hakan a zuciyarta, sannan ta fara ƙoƙarin tsayar da hawayen da take yi ganin har sun isa ƙofar gidan ya fara ƙwanƙwasawa.
"Waye?"
Muryar namiji dattijo ya tambaya daga cikin gidan.
"Baba ni ne. Hafiz ne."
Ya amsa da girmamawa.
Cikin sauri aka buɗe ƙofar daga ciki. Daga yadda dattijon yake gaisar da Hafiz da girmamawa sosai har yana ɗan duƙawa ƙasa yasa ta fahimci Mai gadin gidan ne.
"Ina kwana."
Ta gaisar da tsohon a mutunce da shaƙaƙƙiyar murya bayan sun gama gaisawa da Hafiz. A daraje ya amsa mata, sannan ta bi bayan Hafiz da taga ya nufi cikin gidan kai tsaye.
Daga yadda yake kutsawa lungu da saƙo na gidan har suka isa ɗan madaidaicin falon matar gidan yasa ta gane Yayanta ba baƙo bane a cikin gidan. Ita dai tana biye da shi a baya, da alamun gajiya ƙarara a fuskarta.
Ko da ya zauna akan kujera ita a ƙasa ta zauna, ta nannaɗe ƙafafunta a cikin hijabi, hankalinta a tashe. Ta rasa dalilin da yasa sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan baƙon muhallin da ya kawo ta, don dai kawai ba ta da yadda za tayi ne.
Sallamar da matar gidan tayi ta shigo cikin falon yasa ta ɗaga kai a hankali ta saci kallonta. Kyakkyawar dattijuwa, wacce gayu, gyara, cin abinci masu gina jiki suka taka muhimmiyar rawa gurin ɓoye shekarunta. A haka idan aka bar Zulaikha za ta iya rantsewa da Allah Aunty Balira ta girmi matar, amma kuma a zahirin gaskiya ba haka bane.
Tana waɗannan tunane-tunanen har matar ta zauna, suka gaisa da Hafiz. Sai da Hafizu ya katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta sannan ta iya gaisar da matar.
"Lafiya ƙalau. Ya kike?"
Matar ta amsa mata a mutunce, sannan ta ƙara da tambayarta lafiyarta, da fara'a sosai a fuskarta take kallon Zulaikha, kamar dama can daɗe da saninta.
"Lafiya ƙalau nake."
Ta amsa cikin sanyin murya, tana jin ɗan nutsuwa kaɗan a zuciyarta da ganin fara'ar da ke fuskar matar. Bata yi kama da mugaye ba sam!
"Kar dai ka ce min kaima yau baka je Ofis ba?"
Matar da Hafiz ke kira Mummy ta tambaye shi bayan ta mayar da hankalinta kan shi.
Ɗan sosa ƙeya yayi, kafin ya amsa da
"A'a! Na je Mummy. Wani ɗan rikici ne ya mayar da ni gida. Don Allah alfarma nazo nema idan bazan takura miki b..."
"Dalla rufe min baki. Ashe ɗa yana neman alfarma a gurin wacce take kamar mahaifiyarsa? Me kake buƙata Hafiz? Feel free and ask me anything, in sha Allah bazai gagara ba."
Duk da ya san babu abinda zai nema gurin Hajiya Balkisu ta gagara yi mishi, ƙara tabbatar mishi da hakan da tayi a yanzu ba ƙaramin daɗi da nutsuwa ya ƙara samu a zuciyarsa ba.
"Na gode Mummy."
A nutse ya cigaba da yi mata bayanin abinda ya kawo shi gidanta a daidai wannan lokacin
"Wannan yarinyar da kike gani, ƙanwata ce, Sunanta Zulaikha. Jiya da na tafi gida nazo da ita, aurenta nan da sati uku ne sai aka samu matsala daga can ɓangaren mijin ya ce ya fasa.
To kin san lamarin ƙauye da ƙananun maganganu, wannan dalilin ne yasa Baffana ya ce in taho da ita nan ko za ta samu nutsuwa. To kasancewar tun asali babu shiri tsakaninsu da Bintu, kwananta ɗaya kawai har sun fara samun saɓani, rikicin ne yasa har sai da na tsallake ayyukan Ofis na koma gida... Kawai don dai a samu maslaha, shi yasa na ɗaukota na kawo ta nan ta ɗan kwana miki biyu.
Baza ki samu matsala da ita ba in sha Allahu, duk wasu aikace-aikace za ta taya ki. Da farko na yi tunanin in kai ta gidan Abba Lurwanu sai kuma naga kamar an gudu ne ba'a tsira ba, daga cikin gidan baza'a rasa wanda zai kira Baffa ya faɗa mishi halin da ake ciki ba."
Zulaikha dai kanta a ƙasa, zuciyarta cike da baƙin ciki da takaicin yadda saboda tsananin ƙiyayyar da Yaya yake mata ba ya iya jingina mata matsayin matarsa. Daɗin abin ba shi kaɗai yae ƙin auren ba, ita kanta ta tsani auren, kila ma fiye da yadda ya tsana. A yadda take ji gara ta ƙare rayuwarta babu aure da dai ace ta tabbata matsayin matarsa ba ya son ta ba ya ƙaunarta. Saurin kawar da tunanin tayi, lokacin da ta ji Mummy na cewa
"Allah sarki. Babu komai in sha Allah Hafiz, ka san lamarinmu na mata sai haƙuri. Kuma na ji daɗi sosai da baka bari ka samu saɓani da matarka akan ƙanwarka ba, tunda dai ko wacce tana da ɓangaren muhimmancinta da haƙƙinta da yake wuyanka. Ka barta anan ɗin, kuma ba kwana biyu ba, iya tsawon satittika ko watannin da su Baffa suke so tayi ka barta tayi anan ɗin. Ba mu da damuwar hakan in sha Allah."
Da murmushi a fuskarta ta mayar da kallonta kan Zulaikha ta ce
"Zulaikha? Za ki zauna nan tare da ni ko?"
"Eh Mummy."
Ta amsa a hankali.
"Yauwa! Kin ga nima ba ni kaɗai bace a gidan, akwai mahaifiyata Hajja, da Yayanku Fadil, da ƙanwarsa Kareema, sai yaron Fadil mai suna Imam. Ko da na tafi Ofis i'm very sure zaman kaɗaita bazai dame ki ba. Kin ji ko? Ki saki jikinki kamar kina gidanku. Kuma ina fatan daga ɓangarenki baza ki kira su Baffa ki faɗa musu Yayanki ya canja miki muhalli ba?"
"Eh! In sha Allah bazan faɗa musu ba."
"Yauwa! Madallah! Hafiz za ka iya tafiya."
Godiya mai yawa ya sake yi ma Mummy har sai da ta nuna mishi ɓacin ranta kafin ya daina godiyar, sallama yayi mata. Ko kallon Zulaikha baiyi ba ya fice daga gidan.
Mummy da kanta ta shiga kicin ta kawo ma Zulaikha lafiyayyiyar sakwara miyar agushi, wacce ta ji naman rago zuƙu-zuƙu a cikin miyar. Sannan ta kawo mata ruwa da lemu ta ajiye mata a gabanta.
"Baby ki ci abinci, idan kin gama ga kicin can ki shiga da farantan ciki. Ga kuma ɗaki can na tsakiya daga ɓangaren dama, ki shiga ciki ki ajiye jakar kayanki, akwai banɗaki a ciki sai kiyi alwala, daga yau nan ne ɗakinki, kin ji ko?"
"To Mummy, na gode! Allah ya saka da alkhairi. Ubangiji ya ƙara girma."
"Ameen. To ni bari in shiga ciki inyi sallah."
"To Mummy! A fito lafiya."
Idanunta na kan matar da a zuciyarta take jin nutsuwa da ita har ta ɓace ma ganinta. Kafin ta ci abincin, sai da ta shiga ɗakin da aka nuna mata a matsayin nata ta ajiye jakar kayanta, ta shiga banɗaki ta wanko hannuwanta duk biyu ta fito zuwa falo ta zauna a gaban abincin.
"Uhmmm! In ba gayu irinna ƴan birni ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 40