A nan kan gadon, ta cigaba da Azkhar har zuwa sadda wani daddaɗan barci ya kwasheta.
Sallamar da Hafiz yake ta dokawa a ƙofar ɗakin shi ya farkar da ita a firgice daga wani mummunan mafarki da take yi a daidai lokacin. Karaf idanunta suka faɗa kan agogo, ƙarfe bakwai da minti arba'in da biyu na safe.
Izuwa lokacin, Hafiz ya gaji da sallamar da yake ta yi yana ƙarawa ya shiga cikin ɗakin don ganin lafiya suke kuwa?
Idanunsa cikin nata ya zabga mata harara.
"Don tsabar iskanci kina ji ina ta doka sallama kin ƙi amsawa?"
"Yi haƙuri. Barci nake yi, sallamarka ce ta tashe ni. Ina kwana?"
Ta jera mishi maganganun cikin sanyin murya, kamar dai ba Zulai ba da yasan ta bala'in raina shi.
Irin yadda ta amsa mishi har sai da yasa shi ƙara kallonta sau ɗaya. Sai yaga ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannayenta. Taɓe baki yayi, ya ƙarasa cikin ɗakin har kusa da gadon idanunsa akan Innaye da har lokacin take barci.
"Wani irin barci Innaye take yi haka? Ina fatan dai lafiyarta ƙalau?"
Ya tambayeta ba tare da ya amsa gaisuwarta ba. Babban dalilin da yasa shi yin tambayar kuwa shi ne barci bayan sallar asubahi ba ɗabi'ar Innaye bace, ko lokacin azumi ita ba ta komawa irin barcin nan na bayan sallar asubah.
Zama take tai ta tasbihi da istigfari har gari yayi haske sosai tayi sallar walha. Ko za ta kwanta sai bayan ta idar da sallar walha, tara da rabi zuwa karfe goma na safe.
"Ba ta da lafiya. Kwana tayi da zazzaɓi mai zafi a jikinta kamar baza ta wayi gari ba..."
"Bakinki ya sari ɗanyen kashi. Sakarya kawai wacce bata iya magana ba. Kawai don ta kwana da zazzaɓi a jikinta sai ki ce kaman baza ta wayi gari ba?"
Nan ya cigaba da zazzaga mata faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kawai don ta ce Innaye kamar baza ta wayi gari ba.
Ita dai Zulaikha shiru tayi mishi, a madadin ta ce wani abu ma sai ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tayi idanuwanta na tsiyayar da hawaye. A zuciyarta take ƙara tunanin irin rijiya da bayan da Innaye ta tsallake jiya, duk da tana yarinya kuma ba'a taɓa yin mutuwa a gabanta ba ta san bata yi kuskuren cewa irin zazzaɓin da Innaye tayi jiya kamar baza ta wayi gari ba.
Amma tunda ba a gabanshi aka yi ba dole tayi mishi uzuri, ta san babu ma amfanin yi mishi ƙarin bayani don bazai fahimce ta ba. Tana jin shi har ya gama zazzaga masifar da yake yi ya fice daga ɗakin a gaggauce yana jan tsaki.
Zuciyarsa cike da ɓacin ran kalmar da Zulaikha ta faɗa. Shi yasa sam ba ya shiri da yarinyar, bata iya magana ba. Wasu lokutan haka take sakin maganganu kamar ta ci kashi.
Bai daɗe da fita ba ya dawo cikin ɗakin, Bintu na biye da shi cikin shirinta na fita aiki, sai ɓata fuska take yi kamar anyi mata dole.
Amma ko da Hafiz ya juya yana nuna mata Innaye da yi mata ƙarin bayanin kwana da tayi da zazzaɓi, sai tayi saurin daidaita fuskarta zuwa yanayin jimami da tausayawa.
Duk abinda take yi, ƙasa-ƙasa Zulaikha ke kallonta zuciyarta cike da mamakinta. Tana sane ko gaishe ta bata yi ba, don har lokacin ɓacin ran cin mutunci da tozarcin da tayi mata jiya bai bar zuciyarta ba.
A tausashe Bintu ta kalli Hafiz tana mishi ƙarin bayani bayan ta ɗan tattaɓa jikin Innaye sama-sama. A lokacin ita ma Innaye ta farka, ta buɗe idanunta a jigace tana rarraba idanu a tsakaninsu.
"Sweetheart, ka kwantar da hankalinka. Daman dole za'a sami irin waɗannan ƙananun matsalolin. Magunguna da alluran da na kawo mata masu kyau ne sosai, don haka a karon farko dole ta fuskanci irin waɗannan matsalolin, tunda a iya tsawon rayuwarta bata taɓa amfani da magunguna masu kyau da ƙarfin waɗannan ba. Cikin ƙanƙanin lokaci za ta daina fuskantar zazzaɓin, magungunan kuma za su fatattaki duk wani typhoid da maleria da yake jikinta."
Da damuwa sosai a fuskarsa ya ce
"Yanzu babu wani taimako da za'a iya mata ta daina fuskantar zazzaɓin? Ki dubi fa yadda idanunta suka yi zuru-zuru zazzaɓin dare ɗaya kawai."
"I'm sorry to say gaskiya babu. Haka nan za muyi haƙuri ta cigaba da shan magungunan. Ka san kuma jiki-jiki, kowa da yadda magani da allura ke aiki a jikinshi. Ita wannan alamun shi ya bani tabbacin magani da alluran sun karɓe ta, kuma fa ba lallai yau tayi zazzaɓin ba. Ka kwantar da hankalinka pls."
Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Innaye, a tausashe ta fara gaishe ta da jiki.
"Sannu Innaye. Allah ya ƙara sauƙi. Yanzu dai Zulai ki kamata zuwa bayi a wanke mata baki tayi break fast, sai inyi mata allura kafin in fita. In sha Allah za ta samu sauki sosai."
Ta ƙarasa maganar idanunta na kan Zulaikha da har lokacin ta ƙi yarda ta ɗaga fuska su kalli juna cikin ido.
Ko kafin Zulaikha tayi yunƙurin ɗaga Innaye da ko magana bata iyawa har Hafiz ya tarairayota zuwa jikinsa a tausashe ya zaunar da ita.
"Sannu Innaye. Allah ya baki lafiya."
Innaye dai ba baka sai kunne, ta kasa amsawa, sai raba idanu take yi tsakanin shi da Zulaikha da suke ta jera mata sannu kamar za su ari baki.
Taɓe baki Bintu tayi ta fice daga ɗakin bayan ta ba Hafiz uzurin bari taje ta ƙarasa shiryawa kafin Innaye ta gama.
"Zanyi wanka... Sai inyi sallah."
Innaye tayi maganar a hankali sosai yadda har basu ji abinda ta ce ba sai da Hafiz ya kara kunnensa daidai bakinta.
Zaunar da ita yayi a gefen gadon ya jingina mata filo, da rawar jiki ya shige banɗaki ya sirka mata ruwan wanka. Har cikin banɗakin ya kai ta ya umarci Zulai ta taimaka mata tayi wanka da alwala kafin ya fice daga banɗakin.
Can ɓangarensu ya koma a gaggauce. Ɗakinsa ya shige ya sauya kayan jikinsa saboda yamutsewar da yayi a dalilin hidimta ma Innaye, bai ɓata lokaci ba ya fice daga cikin ɗakin ya wuce kicin. Tsaye yayi yana ɗan tunanin abinda ya kamata yayi, sai kuma ya buɗe kayan karin kumallon da Bintu ta shirya mishi a cikin basket zai wuce da shi Ofis ya ɗauko ɗaya daga cikin kulolin da ya siyo ma Innaye ya sake musu gaba ɗaya. Jikinsa sai rawa yake yi, bai ce ma Bintu da take tsaye tana kallonsa komai ba ya fice daga kicin ɗin.
Duk abinda yake yi tana tsaye tana kallonshi ranta a ɓace, ta kasa ce mishi komai saboda ƙuncin zuciya. Bayan fitarsa a fili take ƙara Allah wadarai da zuwan Innaye gidanta. Domin a zuwansu ne ta ga abubuwa mabanbanta da bata taɓa tsammanin za ta gansu daga ɓangaren Hafiz ɗin ba.
Tun bayan zuwansu kwanaki biyu kawai ta ɗauka tana yi musu abinci a mutunce kuma sau uku a rana. A rana na uku ta sakar ma mai aikinta Rabi ragamar komai na su, aka koma basu dafaffen abinci sau ɗaya a rana.
Ita da kanta ta ɗebi kayan tea da flask da kofuna ta kai musu can ɓangaren da suke. Sannan ta zauna cikin gwari-gwari tayi musu bayanin da ta ɗauki tsawon daƙiƙu tana tsarawa a zuciyarta.
'Innaye ga waɗannan kayayyakin. Kayan tea ne wadatacce da za ku dinga amfani da su gurin karyawa a iya tsawon kwanakin da za kuyi a gidannan, idan sun ƙare kar kuji komai a faɗa min. Sannan a ɓangaren abincin rana da yamma, na faɗa ma Baba Rabi ta dinga dafa komai a wadace tana zubo muku isasshe a kula wanda zai ishe ku cin rana da dare.
Kuyi haƙuri, kun san yanayin aikina ba na zama bane, a mafiyawancin lokuta ni da My dear abincin dare ko na safe kawai muke iya ci tare cikin nutsuwa saboda yanayin aikinmu na da banbancin lokuta.
Ko a cikin kwanaki biyunnan da kuka ga na samu lokacin kula da ku sosai hutu ne na samu a gurin aiki. Yanzu kuma hutun ya ƙare, ina fatan za ku fahimce ni kuma kuyi min uzuri.'
A lokacin, daga yadda Innaye tai ta saka mata albarka tana ƙara ƙarfafa mata gwuiwa akan aikinta na ceton rayukan al'umma ya tabbatar mata Innaye ta gamsu da maganganunta ɗari bisa ɗari.
Shi kuma Hafiz kasancewarsa irin mazajennan masu sakarwa matayensu ragamar komai bai taɓa tuhumar ko me za ta ko ta aikata ba. Ko da yaga an daina kai ma su Innaye abin karyawa sai dai sunƙin biredi kawai bai taɓa tambayarta dalili ba.
Ko yanzu ba ta tsammanin zai nuna mata wani ɓacin rai, amma irin wannan ɓare-ɓaren jikin da yake yi akan tsohuwar shi ne abinda yake ƙona mata zuciya. A ganinta ba komai zai ƙara janyo mata a gurinsu ba sai ƙasƙanci da rashin godiya akan duk abinda za ta musu nan gaba.
'Saboda Allah in banda salon zubar da mutunci da niyyar janyo mata tozarci kayan karin kumallon da ta hana idanunta komawa barci ta shirya musu ita da shi shi ne zai juye nashi gaba ɗaya ya kai musu?' Dogon tsaki taja ɓacin ranta na ƙara hauhawa.
Ta daɗe a gurin tana saƙe-saƙe kafin ta wuce ta cigaba da shiryawa, duk bayan mintuna take jan tsaki ƙasa-ƙasa idan ta tuno abinda ya faru. Haka nan ba don ranta na so ba ta sake raba nata abincin gida biyu ta zuba mishi rabi a kulolinsa.
Ko da Hafiz ya koma cikin ɗakin, a kan dadduma ya tarar da Innaye tana sallah a zaune. Ita kuma Zulaikha tana tsaye jikin gado tana gyara shimfiɗar gadon.
Kusa da Innaye ya zauna, ya buɗe kulolin abincin ya fara zuba mata. Lafiyayyen alalen dankalin turawa ne da miyan ganye, a gefe guda kuma ga kunun gyaɗa da aka dama shi da madara, yayi fari kar gwanin ban kyawun kallo a idanu. Sai ƙamshi yake fitarwa.
Ɗauri biyu ya zuba alalen dankalin a faranti, ya sa cokali ya buɗa cikinsa yadda zaiyi saurin shan iska. Kunun gyaɗar ma ɗan madaidaici ya zuba a kofi ya saka cokali yana jujjuyawa don kunun yasha iska da sauri.
Ya duƙufa kan abinda yake yi har bai san Innaye ta idar da sallar ba sai da ya jiyo muryarta ƙasa-ƙasa ta kira sunanshi.
"Hafizu?"
"Na'am Innaye. Kin idar? Sannu ya jikin naki?"
Ya amsa yana kallonta a tausashe.
"Jiki Alhamdulillahi Hafizu."
Ta sake amsawa da sanyin murya sosai. Sai kuma ta mayar da idanunta kan Zulaikha da itama ta tsaya da gyaran gadon da take yi tana kallonta cikin kulawa da tausayawa.
"Sannu da ƙoƙari Auta. Jiya ban bari kinyi barci ba. Allah yayi miki albarka."
"Amin Innaye. Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana."
"Amin ya rabb!"
Hafiz yayi gaggawar amsawa tun kafin Innaye ta amsa. Ta buɗe baki za tayi magana ya riga ta da cewa
"Innaye kiyi shiru haka nan. Kin ga jikinki babu ƙarfi, ki karya sai ki sha magani, Bintu za tayi miki allura kafin ta fita aiki."
"To"
Ta amsa a sanyaye. A zuciyarta take ji kamar ta ce mishi a dakata da magani da alluran, amma da ta tuno irin bayanin da ta ji Bintu tana yi mishi ɗazu sadda ta farka barci sai bata furta abinda yake zuciyarta ba.
A baki yai ta bata abincin yana ba ta kunun tana kurɓa a hankali har sai da ta kawar da kanta alamun ta ƙoshi.
"Ki daure ki ƙara ko kaɗan Innaye, kin san wasu magungunan rashin isasshen abinci a ciki yana sa su wahalar da mutum."
"Na ƙoshi Hafizu. In dai ba so kake in amayar da wanda ya shiga cikina ba."
Ta faɗa tana ƙoƙarin yin murmushi amma ya gagara saboda tsananin yadda ta jigata da ciwon dare ɗaya kacal.
Kafin yayi magana Bintu tayi sallama ta shiga cikin ɗakin, idanunta kan agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta take cewa
"My dear lokaci ya tafi sosai fa, sai kira na ake yi a Ofis. Ta gama break fast ɗin?"
"Eh! Ta gama."
Ya amsa shi ma yana sauke idanunsa kan agogon bangon da ke cikin ɗakin. Ƙarfe takwas da mintuna talatin da uku.
Bintu idanunta ta mayar kan Innaye da fuskarta yayi zuru-zuru, idanunta suka zuz-zurma ciki sosai, ciwon dare ɗaya kawai gaba ɗaya ya sa kamanninta ya canja, tsufanta ya bayyana ƙarara. Haushi da tsanar Innaye da yayi kaka-gida a zuciyarta ya hana ɗan guntun tausayin da ya taso mata yin tasiri.
"Innaye ina kwana? Ya ƙarfin jiki?"
"Lafiya ƙalau. Da sauƙi Alhamdulillah"
Ta amsa da yanayin maganar da take yi ƙasa-ƙasa tun da ta idar da sallah.
"Allah ya ƙara sauƙi."
Tayi addu'ar a gaggauce. Muryar Hafiz kawai ta ji ya amsa mata. Cikin rashin damuwa ta ɗauki ledar magungunan Innaye da ke ajiye a gefe guda ta fito da su ta fara harhaɗa ruwan alluran, duk abinda take yi cikin sauri ne tana yi tana kallon agogo.
Babu wani tausasawa Innaye ta juya baya ita kuwa ta zurkuɗa mata alluran biyu ba tare da tantance inda ya kamata tayi mata ba. Ta ɓalli magungunan kamar jiya shi kuma ya miƙa ma Innaye, ya tsiyayi ruwan gora a kofi ya miƙa mata ta haɗiyi maganin.
"Zulai sakko ki ga magungunan da za ki ba Innaye da rana."
Bintu ta faɗa idanunta kan Zulaikha da take zaune a gefen gado tun bayan shigarta cikin ɗakin.
Da farko ƙin motsawa tayi, sai da Hafiz ya daka mata wani gigitaccen tsawa kafin ta taso da sauri ta tsuguna gaban Bintu tana zumɓura baki.
"Ki shiga taitayinki da ni na rantse da Allah. Idan ba haka ba kafin in fita Ofis na rantse sai na koya miki hankali..."
Hannun da Innaye ta ɗaga masa alamar dakatarwa yasa shi katse maganar ba tare da ya kai ƙarshen maganar ba.
Kala uku a cikin magungunan ta ware ta nuna ma Zulaikha da cewar su za ta ba Innaye tasha da rana.
"Ki kiyaye fa, kar ki kuskura shirme da wawancinki yasa ki dawo min da treatment baya. Domin yadda ta fara shan magani da allurannan kuskure kaɗan za a samu na jinkirin shan maganin aiki ya dawo baya, ba fata nake yi ba amma irin ciwukan da za su taso mata sai sun fi waɗanda tayi fama da su a baya."
Ta yi maganganun cikin faɗa-faɗa tana aika ma Zulaikha mummunan kallo.
Bata amsa ba, a madadin tayi magana ma ɗaga idanunta tayi a fili itama ta galla ma Bintu wata matsiyaciyar harara kafin ta miƙe ta koma gurin zamanta gefen gado.
Baki buɗe Bintu ta bi ta da kallo, fuskarta cike fal da mamaki. Ta buɗe baki za tayi magana da sauri Hafiz da yake ankare da komai ya ɗan taɓe ta, suna haɗa idanu ya girgiza mata kai sannan ya nuna mata Innaye da ƙwayoyin idanunsa.
Ƙasa-ƙasa tayi ƙwafa kafin ta miƙe tsaye, fatan ƙara samun sauƙi tayi ma Innaye sannan ta kama hanyar ficewa daga ɗakin.
"My Dear ni kam na wuce. Sai munyi waya."
Bata jira amsawarshi ba ta fice daga ɗakin.
Aka ce albarkacin kaza ƙadangare ke shan ruwan kasko. Albarkacin Innaye, yasa duk yadda Zulaikha ta ɓata ma Hafiz rai bai ce mata komai ba har ya gama tarairayar Innaye ya fice daga ɗakin bayan yayi musu sallama zai wuce Ofis.
Da harara Zulaikha ta raka shi har ya ɓace ma ganinta.
Innaye dai jingina tayi da jikin bango ta lumshe idanunta. A yanzu babu zazzaɓi a jikinta, amma fa ba ta jin ƙarfi ko misƙala zarratin, sakayau take jin ta kamar an kwashe duk wani ƙwarin jiki da Allah ya huwace mata. Tana a haka har barci ya fara ɗaukarta.
"Innaye ko za ki dawo kan gado ki kwanta sai in gyara tsakar ɗakin?."
Maganar da Zulaikha tayi shi ya farkar da ita daga barcin da ya fara ɗaukarta.
Bata ce komai ba, sai yunƙurin miƙewa da ta fara yi, da sauri Zulaikha tazo ta kamata ta miƙar da ita, tana tallabe da ita har sai da ta kwantar da ita akan gadon ta rufa mata bargo a rabin jikinta.
Kafin ta gyara ɗakin sai da ta zauna ta take cikinta tayi nak! Tana cin alalen dankalin turawan tana korawa da daddaɗan kunun gyaɗar a zuciyarta take zabga Allah ya isa ga Bintu da a dabarance ta daina basu dafaffen abinci lokacin karyawa sai dai su sha shayi.
Ita kam da yake rainon ƙauye ne abu mai suger da safe bai cika damunta ba. Ko a gida idan akwai ɗumamen tuwo ko sauran abincin da aka dafa da daddare sam ba ta kallon kokon da ake damawa a rarraba ma yaran gida a cikin kofuna ƙananu. Ɗumamen Tuwo take sakawa ta zambaɗa yaji ta cika cikinta tayi nak, sai ta kai ƙarfe ɗayan rana da ƙoshinta ko da an samu jinkirin gama abinci sanadiyyar ɗanyen itace ko gawayi.
Bayan ta gama karyawa tattare kuloli da farantai da kofuna tayi gefe ɗaya ta gyara tsakar ɗakin ƙal, har mopping ɗin kan tiles ɗin tayi ya fita fes! Sannan ta maida hijabin jikinta ta bi lafiyar gado ta kwanta gefen Innaye domin ta rama barcin da bata samu yin isasshe jiya ba.
******
Darare uku masu kama da darare dubu saboda masifar tsawonsu a gurin Zulaikha Innaye ta kwashe tana fama da balaƴaƴƴen zazzaɓi mai zafin gaske kamar baza ta wayi gari ba.
Wani ikon Allah kuma da asubahi tayi sai zazzaɓin ya sauka. Haka za ta yini cikin rashin ƙarfin jiki da kasala, ba ciwon jiki kaɗai ba, hatta tafin ƙafafun Innaye jin su take kamar an kwashe ƙasusuwan da suke taimaka mata gurin yin tafiya an bar zallar tsoka kaɗai. Dai dai da zuwa banɗaki sai Zulaikha ta riƙe ta sannan take iyawa, sallah kuwa tun ranar farko da ta fara yi a zaune har yau bata ƙara samun ƙwarin gwuiwar yi a tsaye ba.
Innaye ta rame ta zabge ta tsuke kamar ba ita ba. Tsufa da galabaita sun bayyana ƙarara a jikinta. Ba Innaye da take fama da ciwon cikin dare ba, hatta Zulaikha da take jinya duk ƙibar nan ta fara zazzagewa.
Ita kanta kallo ɗaya za'a yi mata a fahimci rashin nutsuwa da rashin kuzari a tattare da ita.
Shi kuwa Hafiz duk yadda ciwon Innaye yake ɗaga mishi hankali har lokacin bai ji a jikinsa ya kamata Bintu ta canja ma Innaye magunguna da allurai ba. Maganar da ta faɗa mishi tun ranar farko ita ya riƙe daram a zuciyarsa
'Jikin Innaye bai taɓa karɓar magunguna masu kyau da ƙarfin waɗannan ba shi yasa a yanzu dole za ta galabaita na kwana biyu. A bayan waɗannan cututtukan lafiya wadatacciya ce za ta biyo baya fiye ma da wanda suke nema.'
Da waɗannan kalaman yake ta dannar zuciyarsa da irin damuwa da tashin hankalin da yake ciki.
Abu ɗaya dai da ya iya yi shi ne kullum bayan ya dawo sallar asubahi zai umarci Bintu ta haɗa ma Innaye lafiyayyen abin kari, idan ta gama ya kwasa ya fice musu da shi.
A rana ta uku har yayi ma Innaye sallama zai tafi Ofis bayan Bintu tayi mata allurai ta bata magunguna ta fice gurin nata aikin Innaye ta riƙo gefen rigarsa.
"Innaye? Sannu. Akwai abinda kike so inyi miki kafin in tafi Ofis ne?"
Ya tambayeta a tausashe bayan ya dawo ya zauna a kusa da ita.
"Hafizu, gida nake so ka mayar da ni yau. Ko da mutuwa za ta ɗauke ni na fi so ta ɗauke ni a cikin iyalaina."
Tayi maganar daƙyar, shi kanshi bai ji abinda ta ce ba sai da ya kai kunnensa daidai bakinta.
Hankalinsa ne ya ƙara ɗugunzuma fiye da wanda yake ciki. A yadda ya ɗauko Innaye da ƙarfi-ƙarfinta ko kusa bazai so ya mayar da ita can ƙauyensu yadda ta fara kwararraɓewa haka ba.
Saboda ba ya son ɗaga ma ƴan'uwa da mahaifinshi hankali ne yasa shi tun fara zazzaɓin daren Innaye kullum sai ya gargaɗi Zulaikha kar ta kuskura idan ɗaya daga cikin Yayye, mahaifinsu, ƴan'uwa suka kira Innaye don jin yanayin jikinta tayi suɓul da bakan sanar da su irin ciwon da ya taso ma Innaye gadan-gadan.
Daga bisani ma karɓe wayar Innaye da ke hannun Zulaikha yayi ya kashe. Ya zama sai lambarshi kaɗai ake kira aji ya jikinta, shi kuwa duk wanda ya kira shi ya san abinda yake faɗa musu. Ko sun nemi yin magana da ita kai tsaye yake kawo wani ƙaƙƙarfan uzuri ya basu.
Hankalinsa a tashe ya gyara zama zai fara kalallame Innaye da daɗin bakin tayi haƙuri ga mamakinsa da tsoro kawai sai ta fashe mishi da kuka. Wani abu da bai raɓa faruwa tsakaninshi da ita ba.
Wannan kuka da Innaye take yi haiƙan ba ji ba gani sam ta ƙi tsayawa ta saurare shi shi ne abinda ya ƙara ɗaga hankalinsa zuwa ƙololuwa. Afujajan ya miƙe tsaye ya fice daga cikin ɗakin, can jikin famfon da ke tsakar gurin ya hangi Zulaikha zaune ta tasa kayan wankinsu a gaba tana zaune dirshan a ƙasa tana matsar ƙwallah.
Kaman zararre, ya ƙarasa gurinta da sauri.
"Kukan me kike yi?"
Ya tambayeta cikin tsawa.
A tsorace ta ɗaga idanu ta kalle shi. Maimakon ta amsa tambayar da yayi mata kuma kamar haɗin baki itama sai ta fashe mishi da ƙaƙƙarfan kuka.
"Gida kike son tafiya?"
Ya sake jefa mata tambayar hankalinsa a tashe.
Da saurin gaske ta dinga gyaɗa mishi kai alamar eh kamar ƙaramar yarinya, ta kasa buɗe baki ta amsa mishi saboda kuka.
"Ki haɗa kayayyakinku bari inje in dawo mu tafi yanzu."
Ya sake faɗa hankalinsa a dagule.
Yana kallonta ta kwashi kayan wankin nasu da ko jiƙawa bata yi ba ta wuce cikin ɗakin da sassarfa jikinta na rawa.
Jikinsa a sanyaye yaja ƙafafunsa da yake ji kamar baza su iya ɗaukarsa ba ya wuce zuwa ɓangarensu.
A yadda ya tsara da farko, ƙarasa shiryawa zaiyi yaje gurin aiki ya ɗan rage wasu ayyukan kafin yazo su tafi. Amma da zaran ya tuna irin kukan da ya bar Innaye tana yi, sai hankalinsa ya ƙara ɗugunzuma.
Ya rasa abinda ke mishi dad'i, a kasalance ya k'arasa shiryawa ya fice daga falon ya nufi can tsakar gidan ya sanar da direba ya canja motar da za su fita da ita. Ba Ofis za su ba can ƙauye za su je.
"Ƙauye a yanzu Oga? Allah yasa dai lafiya?"
Direba ya jefa mishi tambayar fuskarshi na bayyana damuwa.
"Lafiya ƙalau. Innaye ce ta matsa lallai a mayar da ita gida yau."
Ya amsa mishi yana cigaba da tafiya zuwa ɓangaren Innaye, wayarsa na hannunsa yana daddanawa don kiran Bintu ya sanar da ita abinda yake faruwa.
Kamar ta miƙe ta taka rawa take ji don tsananin farin cikin da ya sauka a zuciyarta lokaci ɗaya daga jin bayanin da yake mata. Amma da yake ta ƙware a nuna yanayin da ba haka bane a zuciyarta sai ta kwantar da muryarta sosai, cikin yanayin damuwa da jimami ta ce mishi
"Sweetheart ƙauye kuma? To ya bayanin sauran alluranta da suka rage na kwana biyu? Kuma ka san halin mutanen naka dai da rashin kulawa, idan suka tafi da magungunan nan ba lallai su kiyaye ba ta akan lokaci ba. Kar ciwon ya dawo baya fa..."
"To ya zanyi mata Bintu?"
Ya katse ta da kalar tasa damuwar da yake ji kamar ya ɗora hannu aka yaita rusa ihu.
"Duk irin kalaman da ya kamata in yi amfani da su gurin yi mata bayani sam ta ma ƙi saurarata. Ni babban damuwata ma Wallahi ba ragowar allurai da magungunan bane, ki tuna yadda na ɗauko Innaye daga gida.
Ko da dai ba ta da lafiya amma ke kin san yanayin jin jikinta ko kaɗan bai kai yanzu ba. Ki duba yadda ta rame ta lalace, raunin tsufa ya bayyana ƙarara a jikinta. Ko tafiya ba ta iya yi ita kaɗai fa sai an riƙe ta, saboda Allah idan na mayar da ita a irin wannan halin da take ciki me mutanen gida za su ce a kaina?"
Irin yadda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 40