kamar wata sarauniya. Jikinsa na rawa-rawa ya shige gurin ma'ajiyar kayan sawansa, ya buɗe ɓangaren da kayayyakin sakawarta ne sababbi shaƙe da gurin. Kama daga laces, atamfa, shadda, har zuwa kayan barci da Inner wears.
Kayan barci masu kyau sosai ya ɗauka mata ya fice daga gurin ya nufi inda take zaune. Daga irin yadda ta takure kanta ta naɗe hannaye cikin ƙirjinta kamar mai jin sanyi ya kusa saka shi dariya, amma sai ya daure baiyi dariyar ba.
"Babe sanyi kike ji?"
Ya tambayeta a tausashe.
"A'a! Barci kawai nake ji."
Ta amsa a kasalance.
"Sorry. Ga kayan barci na ɗauko miki. Yanzu dai ki shiga bayi kiyi wanka sai ki canja kayan jikinki zuwa na barci ki kwanta."
Har ta buɗe baki za ta ce mishi ta yi wanka tun a gida, sai kuma tayi shiru bayan ta tuna yadda Aunty Balira ke ta jaddada mata banda yi ma miji musu. Kayan barcin hannunsa ta karɓa, ta miƙe tsaye a hankali tana kallonshi ƙasa-ƙasa.
"Ina ne banɗakin?"
Da yatsarsa manuniya ya nuna mata inda banɗakin yake, ita kuma bata ɓata lokaci ba ta nufi hanyar zuwa banɗaki tana tafiya kalalau-kalalau kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki.
Duk yadda yake ta ɗoki da zakwaɗin wannan dare don maimaita wainar da suka soya jiya, tsoro da fargabar da yake gani ƙarara a cikin idanuwanta ya hana shi taɓuka komai.
Ta bakin Hajja ce, matarsa sabuwar shiga ce a komai, lallai ya kamata ya bita sannu a hankali, idan ba haka ba kuwa da sannu zai haifar da gagarumin tsoron gamuwa da shi a zuciyarta.
Bayan ta yi wankan shi ma yayi, rungumeta da yayi tsantsan a ƙirjinsa, bayan haka bai mata komai ba suka yi barci har ladanin masallacin unguwar ya kwaɗa kiran sallar asubah.
********
A kwanakin da suka biyo baya amarci suke zubawa tsantsa abinsu, soyayya zallah ake shimfidawa a gidan, mai tsafta da burgewa, wanda ko kaɗan babu algus a cikinta.
Karima da ta je gidan a cikin satin, kasa rufe bakinta tayi. Cikin ɗan kankanin lokaci har sun kara yin wani fresh su biyun, fata ta kwanta luwai-luwai, saboda hutu da kwanciyar hankali, ga kuma lafiyayyun abinci da ake dafawa daga gidan Mommy ana kai musu.
Ga Zulaikha gwana ce da ta kware wajen tarairaya da kulawa da Kamal, a ɓangaren auratayya ne dai sai a hankali take sabawa. Ta gama karantar mijinta ciki da bai, tasan duk wani abu da ke faranta mishi rai kuma ta kware akan shi.
Karima Tana zaune tana kallonsu akan kujera 2 seater, kankana da abarba suke sha wanda Zulaikha ta yanka musu bayan zuwanta. Yadda Kamal yake wani zuba ma Zuy shagwaba son ranshi kamar wani karamin yaro shi ne abin ke bata mamaki, ita kuwa ta dage tana ta tarairayarshi, sun hade kawuna suna ta kus-kus suna dariya ba tare da kunyar idanunta ba, sai ta kama ma suke sanyata cikin hirarsu.
Ana nan kuma sai ya tashi wai zai shirya yaje ya gaida su Mommy, Zulai kuma ta tashi ta bi bayanshi bayan ta ba Karima uzurin za ta raka shi sama ya shirya.
Karima tana nan zaune shiru-shiru tana jira har aka fi minti ashirin babu duriyarsu. Abin ma ya kasa bata haushi ko dariya, sai kawai ta yayimi jakarta ta fita. A ranta tana fadin idan sun kara ganinta a gidan su mata abinda suka ga dama.
Gaf da za ta fita sai ga Zuly ta biyo bayanta a sukwane, ta hau sunne kai tana bata hakuri cikin dadin murya, da kyar ta samu ta lallasheta suka koma cikin gida. Shi kuma ya musu sallama ya tafi.
Sai lokacin suka samu lokacin zama su yi hira sosai. Kwarai Karima ta yabawa yanayin da ta gansu a ciki, har cikin ranta tayi murna da fatan Allah Ya dorar da su akan wannan rayuwa da soyayya har abada. Itama kuma tana yiwa kanta fata da dacewa da samun rayuwar aure irin wannan.
Sai can bayan isha'i sannan ta bar gidan lokacin da Kamal din ya koma.
Sai da Zulaikha ta cinye sati uku cif ana kai musu abinci daga gidan su Mommy kafin ta fara cancada musu kalolin girke-girken da ta kware akai na gargajiya da na bature.
Rigima kuma sai ta koma akan a dawo mata da Imamu gidan. Shi kuwa gogan tsoron akai shi can yake, kulawar da ake bashi tayi kasa, a raba musu ita biyu. Shi ne yake ta mata kauce-kauce da bada excuses iri-iri.
Ita kuwa da ta ga haka sai ta dangana shi ga Mommy, ita ta dage tsakaninta da Allah a bar mata Imamu, shi kuma yace ai Imamu ya riga ya zama dan gidan Mommy. Ta hakura kawai ta lalubi junior Imamu. Sai gata tana kuka riri har abin ya so basu dariya. Har cikin ranta tana kaunar zama da yaron.
Ga zaman kadaici da take tunanin shiga ciki idan Baban Imam din ya koma bakin aikinshi ka'in da na'in.
Daga karshe dai Mommy ta kashe rigimar ta hanyar raba musu gardama, tace Imam zai dinga zuwa yana yi musu weekend duk karshen sati, sannan a ranakun karatu watarana zai dinga zuwa da yamma yana kai dare daga can makaranta. Duk da ba haka taso ba, a haka dai aka tashi.
Suna komawa gida ya hau kalallameta da dadin baki da ban hakuri don ya kula dai hukuncin da Mommy ta yanke ba haka taso ba. Daga karshe dai ya samu ya shawo kanta da kyar. Don kuwa shi yasan yar kayanshi, ya kuma san ta yadda yake shawo kan abinshi.
******
Watansu biyu da aure, rayuwarsu na tafiya cikin tsari da ban sha'awa. Rayuwace suke shimfidawa mai kyau da tsafta wacce babu boye-boye da cutarwa a cikinta.
Kamal yana girmama matarshi da ɗaukaka duk wani sha'ani nata, haka itama tana kaffa-kaffa da al'amuranshi, kuma tana iyaka kokarinta wajen ganin ta kyautata mishi yadda yakamata.
A cikin satin ne kuma kwatsam ba zato ba tsammani Bintu da Hafizu suka kai musu ziyara. Bayan sun buga rikici mai yawa har Hafiz yayi mata rantsuwar idan bata shirya sun tafi gidan tilon ƙanwarsa ƙwallin ƙwal da take aure a garin Abuja ba za ta haɗu da mummunan ɓacin rai daga gare shi.
Haka ta shirya ranta a ɓace, bakinta a gaba, ta ja tsaki ƙasa-ƙasa ya fi sau hamsin kafin su isa gidan. Tun daga bakin gate ta fara buɗe idanu tana kalle-kalle. Lokaci ɗaya zuciyarta ta ƙara jagulewa, komai ya ƙara kwance mata.
Tun sadda aka yi bikin, taji labarin irin gidan da aka kai Zulai a bakin Mashku, amma ko da wasa bata yi tsammanin irin wannan tsararre kuma haɗaɗɗen gidan aka kai Zulai ƴar ƙauyen ƙayau ba. Da gaskiyar bahaushe da yace gani ya kori ji.
Ashe haka gidan yake da masifar kyau tun daga bakin gate sai kace a kasar turawa? Aka ce ido wa ka raina? Ya ce wanda ya saba gani kullum! Duk ƙayatuwar gidansu da irin kwalliyar da ke ciki sai taji ta raina kyawunshi saboda gani yau da gobe.
Kai tsaye falon gidan aka yi musu masauki, ta zauna akan kujera tana yatsine-yatsine na rainin ajawali. Ita da kanta ta sani ko hasidin Iza hasadin idan ya gani sai ya yaba, amma don tsananin tsanar da take ma Zulai yasa taƙi ba zuciyarta damar bayyana irin kyawun da gidan yayi mata akan fuskarta.
Falon a gyare yake ƙal, ga wani daddaɗan ƙamshi kuma tattausa na turaren wuta da yake fitarwa. Kasancewar ranar Assabar ce, Kamal yana gida, bayan zaman mintuna biyar da suka yi suna jiran masu gidan suka fito shi da ita a lokaci guda.
Daga ganin yadda Zulai ta ƙara yin ɓul-ɓul, farar fatarta da ya dusashe saboda zaman ƙauye ya goge ya tsatso kamar a taɓa ta jini ya ɓullo, daga kallon fatar za a fahimci jikinta sumul-sumul yake sai shekin hutu da jindadi yake fitarwa.
Daga cikin matsakaicin hijabin da ke jikinta suke hangen kananun kayan da take sanye da shi. Shi kuwa gogan nata gaba-daya ya kasa dauke idanunshi a kanta sa'ilin da take zirga-zirgar ɗauko musu ɗan abin taɓawa da jiƙa maƙoshi.
Ta tare su da fara'arta, sosai fuskarta ya bayyana jin daɗin ganinsu. Har kasa tasa gwiwoyinta ta gaishe da Hafiz. Shi kanshi Hafiz ɗin bakinshi ya ki rufuwa ganin irin kyau da tayi da girma da nutsuwar da ya bayyana a tattare da ita. Babu wannan yarinta da gigin da ya saba gani a jikin Zulan Innaye.
Bintu kuwa baƙin ciki kamar zai kashe ta, ita kaɗai take ƙara kumbura tana hanƙoro kamar za ta fashe. Jindadi da farincikin da ta gani a tattare da Zulai ya bala'in ƙona mata rai. Wani rashin wayau da ta yi kuma shi ne kasa boye hakan da tayi.
Hassada da bakinciki da kishi suka bayyana a fuskarta ƙarara. Ita duk a tunaninta wai me wannan banzar Zulai ɗin take da shi ne da zata kasance a cikin irin wannan daular? Yarinyar da ko karatun sakandare bata fita da sakamako mai kyau ba? Yarinyar da tayi rayuwar kauyen kayau? Wacce ta rayu a cikin duhun jahilci da rashin wayewa? Amma ace yau ita ce a cikin babban birnin tarayya, a cikin unguwar da sai wane da wance suke zama a cikinta?
Shi daman Kamal irin matasan nan ne masu kwarjini da nutsuwar da in ba sabo kukayi sosai a tsakaninku ba basa iya sakin fuska da jiki suyi hira. Ita kuwa Zulai ko da taga take-taken Bintun sai tayi banza da ita, ta share ta, ta mayar da hankali kan ɗan'uwanta suna hirar yaushe gamo. Aadeel da ke hannun Bintu ma da taga tana ta wani kara rirrike shi da kankameshi don kar ma ta amshe shi sai tayi kamar ma bata ganshi ba.
Tana zaune kusa da mijinta tana sunne kai cikin kunya sa'adda Hafiz ya fara tsokanarta kan irin ƙiban da ta ƙara, a nutse Kamal ɗin ke tare mata suna dariya su ukun, kamar sun ma manta da Bintu a cikin falon.
Izuwa sa'adda suka yi mintuna talatin a cikin gidan, Bintu ta kai maƙura wajen takura, so take yi su tafi, amma ko kallonta Hafiz baya yi balle tayi mishi alamar su tafi.
Daga ƙarshe dai da taga hirar tasu ta ƙi ƙarewa sai ta fara saka hannu tana tsikarinsa. Ta yi na ɗaya, ta yi na biyu bai kalleta ko ya tanka ta ba, tana tsikarinsa na ukun kuwa ya daka mata wani gigitaccen tsawa ranshi a ɓace.
"Wai ke miye matsalarki ne?"
A tsorace kuma a kunyace ta saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa, ta kasa ce mishi komai saboda kunyar wannan tsawar mai cike da tozarci da yayi mata a gaban Zulai da take gani babban maƙiyiyarta.
Ƙasa-ƙasa yaja tsaki, sai da ƙyar ya iya mayar da hankalinshi kan Kamal suka cigaba da tattaunawa kan halin da ƙasarmu ta tsinci kanta a ciki. Zuciyarsa cike da tunanin murɗaɗɗen hali irin na Bintu.
'Tun a mota ya faɗa mata zai barta a gidan Zulai ita da Aadil su ƙarasa yini, idan aka yi sallar magriba sai ya koma ya ɗauko ta. A cikin mota bata ce masa za ta zauna ko baza ta zauna ba, shi kuma ganin ta yi shiru sai ya ɗauka ta amince ne. Tunda suka shiga gidan, ganin take-takenta yasa shi tunanin baza ta zauna ba. Shi da kanshi a zuciyarsa ya rushe shawarar da ya yanke na barinta a gidan, amma yadda take ciccin magani tana ɓata rai abu ne da bai taɓa tsammani daga gare ta ba. Sai a yau ya ƙara tabbatarwa da gaske ne Bintu ba ta ƙaunar ƴan'uwansa, abinda Innaye da ƴan'uwansa suka daɗe suna yi mishi hannunka mai sanda yayi kamar ba ya gani.'
Ana kiran sallar Azahar, Hafiz da Kamal suka tashi don su je suyi alwala. Zumbur! Itama Bintu ta miƙe a tsammaninta tafiya za suyi, don hankalinta ba shi akan hirar da suke yi bata san sun miƙe da nufin yin sallah bane, ita dama ko gyalenta bata cire ba balle ayi tunanin ta ji daɗin zama.
A mamakance Hafiz ya juya yana kallonta
"Wai ina kike shirin zuwa Bintu? Ki zauna muje muyi sallah mana!"
Ganin da ɗan sassauci a fuskarsa ba kamar ɗazu ba yasa ta yi kwaba-kwaba da fuska, a hankali ta ce
"Wallahi ba na jin daɗi ne My dear, don Allah muje ka sauke ni a gida sai kayi sallar a can. Aadeel ma na ji jikinshi kamar da zazzaɓi."
Tsananin haushi da takaici yasa Hafiz kasa magana, ƙarin baƙin cikinsa ga Kamal da Zulai duk suna tsaye suna jinsu, ya sani tun ɗazu sun fahimci hassada da ƙyashi ke ɗawainiya da Bintu, a yanzu kuwa daga yadda tayi magana ko ƙaramin yaro zai fahimci karya ce kawai take shirgawa ba kunya ba tsoron Allah.
Ya sani idan basu tafi ba, Bintu baza ta taɓa nutsuwa tayi yadda yake so a gidan Zulai ba, ta dinga kunyata shi kenan tana zubar mishi da mutunci. Karo na biyu da ya sake ƙarewa Bintu kallo, zuciyarsa cike da tunanin irin maganganun su Anty Balira a kan Bintu, da irin abubuwan da take nunawa akan idanunshi tun shigarsu gidan Zulai ayau. Ayar tambayar da ya daɗe da ɗiga mata a take ta koma alamar motsin rai!!
Ya kasa daina mamaki, ashe da gasken-gaske Bintu ba ƙaunar ƴan uwanshi take yi ba? Da gaske ne abinda ake mishi shaguɓe a kanta? A wannan karon lallai idanunshi sun washe.
"Uhmmm!"
Yayi ƙwafa a fili. Ya ƙara tamke fuska idanunshi a kanta da salon bayar da umarni ya ce
"Bintu ki zauna inje inyi sallah in dawo."
Har yayi shiru sai kuma ya ƙara da cewa
"Na zaci idan da ƙauna da soyayya gidan Zulai kamar gidan Mashku yake a gurinki?"
Ya jefa mata tambayar yana ƙara tsattsareta idanu.
Da saurin gaske ta taɓe baki, ta ƙara da wani zazzare idanu kamar wacce ta ji yayi wani babban saɓo a maganarsa.
"Gidan Mashku dai?"
Ta tambayeshi da mamaki sosai a muryarta. Kafin ya amsa ta ƙara da cewa da cewa
"Mashkura ƙanwata fa? A'ah wallahi! Wannan misalin sam bai ko kusa hawa ba. Kada ma ka ƙara jona min wannan ka-re-ren! In banda ma ƙaddara me haɗo gabas da yamma me zai haɗa kifi da kaska?"
Tsananin mamaki da takaicin maganganunta yasa shi kasa ce mata komai, sai baki da ya ai hangame yana kallonta, Kafafunshi suka daskare guri ɗaya kamar an zare mishi laka.
Ita kuwa Zulai, dariya maganganun Bintu suka bata, a ƙasaice, ta saki wata siririyar dariya kafin ta kalli Kamal, da taushin murya sosai ta ce
"Abban Imam kar ka makara sallah fa, lokacin yana ƙoƙarin wucewa"
Ta sake mayar da idanunta kan Hafiz da murmushi a fuskarta ta ce
"Yaya mun gode da ziyara, ku gaida gida. In Allah Ya yarda idan na fara fita ni zan zo in muku yini."
Daga shi har ita sun san ta fada ne kawai, ba zuwan za tayi ba. Ita kuwa a ranta tuni ta gama kudurtawa nan da shekara biyar masu zuwa idan muna raye ba lallai su ga keyarta a cikin gidansu ba.
Ya kasa amsa ma Zulaikha, sai ɗan murmushi da ya sakar mata. Ya ɗaga hannunshu daƙyar ya cusa a aljihu, ya ƙirgo dubu ashirin ya aje mata a gefen hannun kujera. Bai saurari godiyar da take masa ba yaja kafa jiki a sanyaye ya fice daga falon, Bintu ta bi shi a baya tana saɓe da Aadil a kafaɗa, ko arzikin sallama su Zulai basu samu daga bakinta ba.
Sai da suka isa gurin mota sannan Hafiz ya lura da Kamal na biye da su a baya, sallama yayi mishi a mutunce kafin ya wuce masallaci. Kunya duk ta cika Hafiz, saboda irin rashin kirkin da matarsa ta zuba a gidan ƙanwarsa kuma a gaban mijinta. Shi kuwa Kamal da yake wayayyen mutum ne, ko a fuska bai nuna ma Hafiz rashin jin daɗin abinda ya faru ba ba.
Hafiz ya tayar da mota kenan sai ga wata motor tana ƙoƙarin shigowa, a dole ya dakata har sai da wancan motar ta shigo, ta samu gurin perking kafin ya fara ƙoƙarin fita da motarsa.
Kamar an ce ya kalli wancan motar da ta shigo, karaf! Idanunsa suka faɗa cikin na Karima da take zaune a mazaunin direba, da waya maƙale a kunnenta tana magana tana sakin murmushi akai-akai. A gefenta Imam ne gishingiɗe akan kujera yana barci.
Akan idanunshi Zulai ta fito daga cikin gidan da saurinta da bayyananniyar murna a fuskarta ta ƙarasa gurin motar Karima, buɗe ƙofar mai zaman banza tayi, ta rungumo yaron cikin tsananin kauna da kulawa ta ɗauko shi cak ta fito da shi daga cikin motar, a lokacin ita ma Karima ta fito, suka wani kashe hannu da Karima alamar da ke nuna amincin da ke tsakaninsu.
Bai san cewa ya saki baki da hanci yana kallonsu ba sai da Bintu ta taɓa shi tana tambayar lafiya? mai yake kallo?
"Karima ce fa ƴar gidan Mummy Saudah, baka santa bane ko akwai wani abu ne a tsakaninku?"
Ta ƙarasa tambayar ƙarshen da salon da ke bayyana zargi ƙarara a muryarta.
Bai ce mata komi ba, ya cigaba da jan motar a sanyaye suka fice daga gidan.
A cikin mota haka ta cigaba da mita kamar cin ƙwan makauniya, duk dai akan kallon da ya ƙure Karima da shi kamar bai taɓa ganinta ba. Shi kuwa ta tafasa sauke bai ce mata ba sai da suka ƙarasa gida, sannan ya fara sauke mata kwandon bala'i da tashin hankali irin wanda bai taɓa mata ba, duk dai akan irin wulaƙanci da tozarcin da tayi masa a gidan Zulai. Da irin yadda take wulaƙanta danginsa a ɓoye amma a gaban idanunsa sai ta dinga nuna mishi tana ƙaunarsu.
Itama da yake a wuya take haka ta biye mishi yana faɗa tana faɗa, kamar za su ba hammata iska. Daga karshe ma da abin ya kai ta maƙura haka ta nannaɗo wani murgujejen zagi ta laulayawa ƙauyensu da kafatanin mutanen da ke rayuwa a ƙauyen.
Ɗif! Ya ɗauke wuta na wasu ƴan daƙiƙu, kafin ya farfaɗo ya nuna kanshi da yatsarsa manuniya, fuskarsa ɗauke da matsanancin mamakinta ya ce
"Bintu! Ni kike kallon tsakiyar idanuna ki zagi ƙauyen da na fito da duk mutanen cikinta? Har da ni da iyaye da dangina fa kenan? Kika cewa iyayena da dangina kucakan ƙauye? Masu datti dangin ƙazanta da dauɗa? Ashe dangina ba danginki bane?"
Dogon tsaki ta ja babu alamun nadama ko kaɗan a fuska da kalamanta ta amsa da
"Allah suturi buƙwui in ji kishiyar mai mageɗuwa. Can ga su gada wallahi, wannan tarkacen ba da ni ba. Kaje dai can ka ji da danginka kai da suka zame maka dolen dole ba ni ba. Kuma zancen gaskiya ka ma nisantani da su da tarkacen da ya kwasosu, don tuni na daɗe da fahimtar yadda ba sa ƙaunata ko kaɗan. Daga yau kar in ƙara ganin ƙafar wani ya tako min gida. Tunda nayi kawaicin da kawar da kan ka ƙi gani, gwara in fito ɓaro-ɓaro in fada maka kawai tunda ka ƙi fahimta! Itama wannan mai gwala-gwalan idanun da jiki kamar na yan dambe, ka fada mata hawainiyarta ta kiyayi ramata, kada ta kuskura ta zo min gida wallahi!"
Ta juya fuu ta wuce ɗakinta tana maganganu
"Auren banza da na wofi! Daga gani wannan auren babu inda zai je, don kuwa ba sa'an aurenta ta aura ba. Wannan jikin da ta saki wai ita ta ganta a cikin daula ta jindaɗi tana ganin ta tsinci dami akala, to tasan cewa ba mai ɗorewa bane...!"
Ta shige ɗaki ta tura ƙofar bam! Bugun da ya ji shi kamar akan fuskarsa.
Ya kama baki hannunsa ɗaya dafe da kai ya haɗiye wani kakkauran miyau. Zancen mamaki ma ba a magana, don kuwa yau dai Bintu ta shayar da shi ruwan mamaki kala-kala. Ya gama fahimtarta sarai, bakin ciki da hassada ne danƙare a cikin ranta ba wani abu ba. Waɗannan abubuwa biyu kuma su suka ja mata gora gurin fallasa wacece ainahin Bintun da bai taɓa sani ba.
Da kyar ya iya ɗaga kafa ya bar gidan. Ya shiga masallaci yayi sallah. Ya jima a masallacin yana lazumi, gaba daya ranshi kamar an cire mishi komai ya ma kasa tunanin komai.
Daga karshe ya tashi ya shiga motarshi yayi ta zagaye a cikin garin Abuja ba tare da takamaiman wajen zuwa ba.
Bai koma gidan ba sai can gab da magriba. Wani tunanine yake ta yawo a kanshi tun da ya idar da sallar la'asar, abin ya kasa fita a cikin ranshi duk kuwa da yadda yaso ya yakice tunanin.
Zai iya cewa wannan tunanin ma shi ya mantar da shi ɓacin ran da Bintu ta ƙunsa mishi. Don bai tuna da saɓanin da suka yi ba sai da ya shiga falon gidan. Ya same ta ta ci kwalliya, shima Aadeel ta shirya shi tsaf.
Da yake ita ɗin ƙwararriya ce a iya kissa da kisisina sai ta tare shi da matsananciyar farin ciki, soyayya, ƙauna, da tarairaya, kafin ya ce komai ta rushe da kuka tasa gwuiwa a ƙasa tana bashi haƙuri.
Hankalinta bai kwanta ba sai da taga ya saki fuskarshi, ya kuma tabbatar mata da komai ya wuce. Sannan cikin rawar jiki ta gabatar mishi da kalolin girke-girke irin waɗanda ta tabbatar yana so.
Shi ya ma manta rabonshi da ƙwaƙƙwaran abinci tun karin safe, sai lemo da snacks da ya ci kaɗan a gidan Zulai.
Duk yawon da yayi a cikin gari ruwa kawai ya dinga ɗaɗɗakawa cikinshi, ba ya jin yunwa, balle ya tsaya ko gidan abinci ne ya shiga ya cika ciki.
Duk ƙamshi da haɗuwar da abincin yayi ranar dai kasa ko kallonshi yayi balle yayi tunanin ci. Haka ta bishi har cikin dakinshi tana ta kwarkwasa. So tayi ta hillaceshi kamar yadda ta saba don maganar ta ƙarasa wucewa, amma ya ki damar hakan.
Haka tana ji tana gani ya sake yin wanka ya sanya wani yadi mai kyau ya fita. Ta bishi da kallo jiki a sanyaye. Ranta ya gama bata cewa lallai yau ta tsokanowa kanta faɗan da yafi karfinta.
*****
Da misalin karfe takwas da yan mintuna na dare Hafiz yayi sallama a kofar falon gidan Mommy Saudah, sai da ya jira aka amsa daga ciki, aka yi mishi izinin shiga kafin ya danna kai cikin falon.
Karima da Hajja kaɗai ya samu a zaune a falon suna kallo TV. Ya samu kujera ya zauna bayan ya gaishe da Hajja ta amsa a mutunce.
Da sanyin murya Karima ta gaishe shi, bayan ya amsa ta miƙe a nutse ta nufi kicin don kawo mishi ruwa da abin taɓawa. A fakaice yabi bayanta da kallo, a zuciyarsa yake jin ƙarin nutsuwa ta musamman.
Gorar ruwan faro da madarar hollandia ta fara ajiye mishi, sannan ta koma cikin kicin ta kawo mishi Meat pie shaƙe da faranti, da alamun ba'a daɗe da gama soyawa ba, don sai ƙamshi yake yi.
"Yaya Bismillah! Ya su Aunty Bintu da Aadil?"
Ta tambaye shi.
Bayan ya amsa mata da lafiyarsu ƙalau ta sanar da shi Mommy tana amsa waya ne, idan ta gama za ta fito.
Don haka ya zauna anan yana sauraren hirar da suke yi da Hajja, lokaci bayan lokaci yana ɗan tsoma musu baki idan Hajja ta sako shi cikin hirar. A kaikaice yake ƙare ma Karima kallo, wani iko na Ubangiji kuma sai yaji tunanin da yake ta taunawa a cikin ranshi yana ƙara kwanta mishi sosai da sosai.
A da kam, ya riga ya gama ƙudurtawa ranshi cewa shi fa Mijin mace ɗaya ne. Sam! ba shi da wani ƙudiri na karin aure. Amma a yanzu, sai yake jin cewa zai iya, kuma zai yi. Ba wai kuma don kawai munanan halayen Bintu da suka bayyana ƙarara a idanunshi ba, ba kuma wai don ba ta kaunar danginshi da iyayenshi ba, sai don kawai samun damar cin moriyar karin maganar nan ta bahaushe da ya ce gida biyu maganin gobara.
Duk da dai rashin kaunarta ga danginshi shi ya fara ɗarsa masa tunanin lallai ya kamata ya nemi mafita. Aka ce ranar naka sai naka, daɗin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 40