Share this page
ƙuruciya a kanta. Kayi shiru haka pls, ka ga da gajiya a jikinka har yanzu, kar ka bari abinda bai kai ya kawo ba ya taɓa min zuciyata." Shiru yayi yana mayar da numfashi, da alamun maganganunta ba ƙaramin taɓa shi suka yi ba. Bintu kuwa mayar da hankalinta kan Zulai da har lokacin take kuka tayi da wadataccen murmushi a fuskarta. "Kin ga Zulai yi shiru, share hawayenki. Daga waɗannan maganganun na Yayanki dai ya isa yasa ki hankalta, ki san yanzu fa ba da bane. Idan wancan karon ganin idanun Innaye yasa kin tsula tsiyarki yadda kike so wannan karon baza kiyi ki ci riba ba. Ɗauki jakarki ki tafi can ɓangaren da kuke sauka ki yi wanka ki huta, gurin a share yake a goge, tun bayan tafiyar su Aunty Balira da aka gyara ba na jin yanzu ya sake yin ƙurar da zai sa ki sabon shara." [1/23, 10:25 PM] Fareeda Abdallah: Duk baƙaƙen maganganun da take yaɓa ma Zulaikha a fakaice tana jin ta, kuma tsaf ta fahimci saƙon da take aika mata. Amma a madadin ta miƙe ta aikata umarnin da Bintu tayi mata, sai kawai ta ƙara gyara zama ta cigaba da kukan da take yi. "Au! Faɗan Yayan naki bai ishe ki ba kenan ko? Ki tashi ki tafi masaukinku na ce tun kafin ranshi ya ƙara ɓaci..." Cikin ɓacin rai da muryar kuka Zulaikha ta katse Bintu da cewa "Ni fa bazan zauna acan ɓangaren ni kaɗai ba. Tun a gida ma ai Innaye cewa tayi a matsayina na..." "Wa ya tambaye ki wani matsayi da kike da shi a gidannan? Za ki rufe mana baki a gurin nan ko sai na ɗora hannu a jikinki?" Hafiz ya katse ta da saurin gaske tun kafin ta ƙarasa ɓaram-ɓaramar da take niyyar yi. Sunkuyar da kai ƙasa tayi ta cigaba da jan shessheƙar kuka. Ba ta ma da niyyar tashi ta ɗauki jakarta balle har Bintu ta saka ran za ta aikata abinda ta umarce ta. A mamakance, Bintu take kallon Hafiz, sai kuma ta kalli Zulaikha. Duk ga zatonta cikin tsawa da faɗa zai sake balbale Zulai da umarnin ta tashi ta tafi can ɓangaren da suke sauka. Amma a madadin ta ji ya faɗi abinda take tsammani, sai kunnuwanta suka jiyo mata kalamansa kamar saukar aradu yana ce mata "Sweetheart! Ki ƙyale ta anan. Kin ga ita kaɗai ce, can ɓangaren baƙi yayi mata girma, baza ta iya zama ita kaɗai acan ba. Tunda ga Mashku anan sai su zauna a ɗaki ɗaya..." "Bazai yiwu ba gaskiya My Dear. Mashku ko a gida ba ta yarda ta haɗa ɗaki da su Amina ƙannenta ballantana ta haɗa da wacce bata sani ba. Tunda akwai wadatar ɗakuna anan ɗin, ita ma sai ta ɗauki ɗaki ɗaya tayi amfani da shi. Excuse me pls! Bari in duba girki." Ta miƙe daga jikinshi da sauri ba tare da jiran abinda zai sake cewa ba. Da haka aka bar maganar saukar Zulaikha a can ɗakunan BQ. Shi da kanshi ya tashi, yaje ya buɗe mata ɗaya daga cikin ƙayatattun ɗakunan da suke nan ƙasa, sannan ya koma gurinta fuskarsa a ɗaure ya umarci ta ɗauki jakarta zuwa cikin ɗakin. Tana shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe, kusa da inda take tsaye ya ƙarasa a bazata ya damƙo kunnenta na dama da yake cikin hijabi ya murɗa, a gigice ta buɗe baki za ta ƙwallah ihu da saurin gaske ya toshe mata baki bayan ya saki kunnen da sauri. "Kin san Allah? Muddin kika yi gangancin faɗa ma matata an ɗaura mana aure da ke acan gida na rantse sai na ɓatar da ke a cikin garin nan, sai dai duk abinda zai faru ya faru." Cizon da ta gantsara mishi a tafin hannu yasa shi sakin bakinta da sauri ya matsa baya yana yarfe hannu, ga dukkan alamu ya ji zafi sosai. "Cizo na kika yi?" Ya tambayeta fuskarsa a ɗaure. "Eh ɗin" Ta amsa a tsiwace, zuciyarta cike fam da takaicinsa. "Kuma na rantse da Allah idan ka sake min irin wannan cin mutuncin a gaban matarka sai na kira Baffa da Innaye na faɗa musu duk irin wulaƙancin da kake min tunda kazo da ni garinnan." A fusace ya miƙa hannu zai damƙo ta. Da mugun sauri ta zille masa, sannan ta ƙwalla wani gigitaccen ihun da yasa ba shiri ya fice daga ɗakin da saurin gaske jin da yayi karaɗin ihun na barazanar toshe mishi dodon kunne. A guje Bintu ta fito daga ƙaramin kicin ɗinta suka yi kiciɓis da shi a tsakiyar falon. "Lafiya ? Ihun me nake ji? Kar dai ace dukanta kayi?" Bintu ta tambaye shi da damuwa a fuskarta. A zuciyarta kuma addu'a take yi Allah yasa dukan Zulaikha yayi. "Yarinyar ba ta da kunya Sweetheart. Idan ba taɓa lafiyarta nayi ba baza ta shiga taitayinta ba. Bari in je ɗaki, ki kawo min abincina sama." Yana gama faɗin haka ya fara hawa matakalar sauri-sauri. Zuciyarsa cike da damuwa da ƙuncin aura mishi Zulaikha da aka yi. Gaba ɗaya kanshi ya kulle, ya ma rasa ta ina ya kamata ya ɓullo ma al'amarin? Ga shi ya rasa hanyar da zai bi wajen sanar ma da Bintu yanzu matsayin mata Zulaikha take a gurinsa. Domin bai manta irin alƙawurran da suka ɗauka ma junansu kafin aure da kuma bayan aure ba. A alƙawuran da ya ɗauka mata akwai, ita kaɗai ƙwallin ƙwal ta ishe shi rayuwar duniya. Ita kuma kaɗan daga cikin alƙawuran da ta ɗauka mishi shi ne ako wane hali wuya ko daɗi za ta kasance tare da shi, za ta bashi ƙololuwar farin ciki fiye da wanda yake tsammanin samu daga gare ta. Za kuma tayi duk iya mai yiwuwa wajen bashi dukkan tarairaya da soyayyar da zai kawar da hankalinshi daga kan ko wace mace sai ita ƙwallin ƙwal. To ga shi tun ba'a je ko ina ba an fara samun karya alƙawari daga gare shi, shi kam ya zayyi ne? Ina zai sa kansa? Kuma ta wace hanya zai ɓullo ma wannan ƙaddararren aure da su Baffa suka ƙulla masa? ****** ****** Zulaikha mai bala'in son girma sama da ƙasa ta kalle ta, sai kuma ta ɗanyi dariya. Tana jin wani girma na ƙara mamayeta, daga yadda ta ga yanayin jikin Mashkura ɗan daidai kamar na Bintu, duk ga tsammaninta bata wuce shekaru goma sha biyar ko sha shida ba. "Uhmmm! Ta ina kika taɓa ganin anyi ƙawance tsakanin ƴar birni da ƴar ƙauye? Sannan kuma ni ba yarinya bace fa, na girme ki nesa ba kusa ba, shekaruna sha takwas cif..." Sassanyar dariyar da Mashkura ta ƙyalƙyale da shi yasa Zulaikha tayi sakalau da baki tana kallonta. Sai da tayi dariyarta ma'ishi kafin ta ce ma Zulaikha "Shekaru sha takwas ne kike faɗin kin girme ni nesa ba kusa ba? To ni shekaruna ashirin da ɗaya, Wallahi da gaske nake miki. Kawai don kin ganni da ɗan ƙaramin jiki ke kina da ƙiba shi ne kike min kallon ƙaramar yarinya? Sannan in banda ke da abin ki, da ni da nake birni da ke da kike ƙauye ai duk Allah ne ya halicce mu. Babu wacce ta fi wani a gurin Allah sai wacce ta fi tsoronsa. Sannan kuma ƙawance ba'a shekaru bane, shekaru lambobi ne kawai. Ni dai don Allah ki karɓi tayin ƙawance na, kin ga, yanzu ma dai bani lambar wayarki." Duk yadda Zulaikha ke zillewa a dole ta saki jiki da Mashku har suka yi musayar lambobin waya. Da yake Mashku irin yarannan ne da in suna son ka suna so ne da dukkan zuciyarsu, tana da miskilanci amma idan ta so hira sosai take sakin jikinta tayi har da ƙyaƙyata dariya. Balle kuma ta haɗu da Zulaikha ga barkwanci ga wauta, cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu. Yadda suka bararraje a tsakiyar gadon suna hira da dariya, kamar sun daɗe da sanin juna. Har Mashkura ta fice zuwa kicin ta haɗo musu tea mai kauri a kofuna biyu, suna sha suna hira. A daren, Mashkura ta tura ma Zulaikha fina-finai masu yawa a cikin wayarta. Sannan ta ƙara da wayar mata da kai kan yadda ake amfani da wayar Android, ta kuma koya mata games ɗin da ta tura mata masu daɗi da za su taimaka gurin ɗebe mata kewa da zaman kaɗaita. Tunda ita Mashkura ba zaman gidan sosai ta cika yi ba, kullum da safe takwas zuwa tara na safe take ficewa zuwa makaranta. Ba tare da kunya ko wani kwana-kwana ba Zulaikha ta faɗa ma Mashkura ita fa ba ta jin turanci. "Kin san karatunmu na ƙauye, ba ɗaya ne da naku na birni ba. Sai dai na iya karatun hausa fiye da yadda kike tsammani, turancin ne dai ƴan ƙananun kalmomi kawai nake iya ji in fahimci abinda ake nufi." "Kar ki damu. Don wannan ai ba wata matsala bace. Sannu a hankali zan tsara mana jadawalin da za mu dinga bi ina koyar da ke abubuwa masu yawa, idan kika mayar da hankali kuma kika nace cikin wata uku bakinki zai goge da turanci kamar ƙanwar mangwafak! Kin san shi karatu naci yake so, sannan kuma hausa ya fi turanci wahalar koyo, tunda kika iya karatun hausa, turanci bazai wahalar da ke ba in Allah ya yarda." Maganganun Mashkura ba ƙaramin daɗaɗa ma Zulaikha rai suka yi ba. Sai godiya take zuba mata kamar ma har ta iya turancin. Allah ya sani a yanzu ba ƙaramin son ta koyi turanci take yi ba. Ta iya a baki, idan an faɗa ta san me aka ce, kuma ta iya mayar da martani da yaren turanci, sannan idan ta gani a rubuce ta karanta ta kuma fahimci me ake nufi. Idan ta iya waɗannan, ɗaya daga cikin manyan burikanta sun cika. A da can baya bata taɓa damuwa da koyon turancin ba, bata ma ɗauke shi a wani kayan gabas ba. Sai bayan shigowar Bintu cikin ahalinsu ne ta gane lallai fa ta tafka kuskure rashin mayar da hankalinta a karatun boko. Ba ma kamar yadda minti ɗaya biyu Bintu take goranta mata da munanan kalmomi kamar jahila, daƙiƙiya, baƙauyiya, wawuya, a ganinta, rashin iya turancin shi ke sa Bintu goranta mata da waɗannan munanan kalmomin. Mashkura bata bar ɗakin ba sai misalin ƙarfe ɗaya da minti arba'in na dare. Sun rabu duk su biyun zukatansu cike da farin cikin hirar da ta gudana a tsakaninsu. Har Zulaikha ta kwanta, ta ɗaga hannu za ta fara karanto addu'ar barci kenan sai ga Mashkura ta sake shiga cikin ɗakin bakinta ɗauke da siririyar sallama. "Kiyi haƙuri da ni Ƙawata. Yau dai na hana ki barci." Ta faɗa tana murmushi. Kayayyaki masu ɗan dama da suke riƙe a hannunta ne ta zube su a gefen gadon, ta fara ɗaɗɗaga su ɗaya bayan ɗaya. Kayan barci ne masu kyau da laushi sosai a ido har kala uku, riga da wando biyu, sai kuma riga ƴar ciki da ta samanta guda ɗaya. Sai kuma Abaya sababbi masu kyau sosai kala uku. "Ban san ko nayi miki karambani ba. Allah yasa dai kina saka kwance, duk da dai kamar sabbi suke a gurina. Domin bayan sau ɗai-ɗai ban ƙara saka su ba. Na kawo miki ne ko kina so, na ga manya ne, za suyi daidai da jikinki." Tsananin murna da farin ciki, yasa Zulaikha ta kasa cewa komai. Lokaci ɗaya tayi ƙwal-ƙwal da idanunta, can kuma sai ga hawaye shar... sun zubo daga kwarmin idanuwanta. Lallai sai a yanzu ta ƙara yarda da maganar Mashku da ta ce ba halinsu ɗaya da Bintu ba. Ashe haka Allah ke ikonsa dare ɗaya ya haɗa ƙauna a zukatan bayinsa? "Na gode Mashku. Na gode, Allah yabar ƙauna da zumunci." Kalaman da take ta maimaitawa kenan cikin kuka da dariya, sai ɗaɗɗaga kayan take yi tana jinjina kyawunsu a idanunta. Ko Mashku bata faɗa ba, daga yanayin kyawun kayan sun isa su bayyana maka masu tsada ne sosai. In dai ba ta manta ba za ta iya rantsewa da Allah ba'a taɓa yi mata kyautar kaya irin haka kuma daga bare wacce basu haɗa komai da ita ba. "Don Allah ki daina hawayen nan da kike yi. Miye don na baki ɗan waƴannan kayan? Ba komai bane fa, kuma don ma yanayin jikinmu ba ɗaya bane ai Wallahi da sai na haɗa miki akwati guda. Ni kin ga ma tafiyata tunda baza ki daina kuka ba. Allah ya tashe mu lafiya." Da sauri ta fice daga ɗakin taja mata ƙofa, fuskarta yalwace da farin ciki. Ko bayan fitar Mashku, ta daɗe bata yi barci ba. Bayan ta gama matsar ƙwallar da take yi murza key tayi a ƙofar ɗakin ta kulle. Ta canja ƙwan lantarki zuwa mai haske ta fara gwada kayan ɗaya bayan ɗaya. Wani ikon Allah kamar da man can kayan domin ita aka siya. Sunyi mata dai-dai, kuma sunyi mata a wadace, basu yi kaɗan ba sannan basu yi mata yawa yadda take saka manyan riguna ba. Ba ma kamar Abayoyin nan, sai ta fito shar a ciki kamar wata balarabiya, kasancewar tana da hasken fata. Saboda murnar ganin yadda tayi kyau sai juyi take yi a gaban madubi tana ƙyalƙyala dariya ita kaɗai a cikin ɗaki. Gaba ɗaya ta manta da damuwar Bintu, Hafiz da wani ƙaddararren aurensa da aka ɗaura mata. "Ashe daman haka nake da kyau?" Ta tambayi kanta a fili tana dariya. "Gaskiya daga yanzu zan zo nima in koyi gayu ko gurin Mashkura. Kuma bazan sake yarda Innar Hadiza (Telarta acan Faƙo) tayi min burguza-burguzan ɗinkunan nan da take min ba. Ƴan cas-cas za ta dinga min irinna ƴan gayu, musamman ma dai yanzu da zan koyi turanci. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya tana shafa ƴan yiri-yirin kitson da suke kanta. Ko da ta cire kayan naɗe su tayi tsaf ta shirya su can ƙasan jakar kayanta, sannan ta mayar da sauran kayan ta rufe zip ɗin jakar. Kafin ta kwanta, ƙarfe uku saura minti goma sha biyar. Da yake tana cikin farin ciki ga bashin barcin da yake kanta bata daɗe ba nannauyan barci yayi awon gaba da ita. Sabo da yin sallar asubah akan lokacinta shi ya tasar da ita, daƙyar ta iya miƙewa bayan ta yi salati da addu'o'i tana tangaɗi ta faɗa banɗaki. Alwala da ruwa mai ɗumi da tayi shi ya taimaka mata gurin dawowa hayyacinta. Ko da ta koma cikin ɗakin, kafin ta kwanta sai da ta murza makullin ƙofar ɗakin ta buɗe, sannan ta saka babban hijabi ta tayar da sallah. Bayan ta idar tana cikin yin azkhar kamar yadda ta saba nannauyan barci ya sake yin awon gaba da ita nan kan daddumar da tayi sallah. ***** ***** Ƙirjinta ne ya buga daram!! Ganin kiran Innaye na shigowa cikin wayarta, abinda bai taɓa faruwa ba tun bayan musayar lambar waya tsakaninta da Innaye matsayinta na Uwar mijinta. Matsanancin tsoro ne ya lulluɓeta, ƙirjinta ya cigaba da bugawa akai-akai. Kamar baza ta ɗaga kiran ba, domin duk a tsammaninta Zulaikha ce ta kira Innaye ta kai mata ƙararta. Har kiran farko ya tsinke na biyu ya sake shigowa tana canki-cankar ta ɗaga ko kar ta ɗaga kiran? Tunanin idan bata ɗauka ba Innaye za ta iya kiran Hafizu ta kora mishi kashaidi zuwa gare ta yasa tayi shahadar ƙuda ta ɗaga kiran, a zuciyarta take tunanin yaushe rabonta da magana da Innaye ko da ta waya ne balle har suyi ido biyu? "Barka da safiya Innaye, ina kwana? Da fatan duk kun tashi lafiya?" Tayi saurin miƙa gaisuwa bayan ta yi sallama da ƴar karkarwa a muryarta kamar tana gaban Innaye. "Lafiya ƙalau Fatima. Ya wanka?" Innaye ta tambayeta a nutse. Bayan ta amsa da lafiya lau daga can ɓangaren Innaye sake gyara zama tayi akan daddumar da ta idar da sallar walha. Cikin nutsuwa ta sake jefa ma Bintu tambayar da shi ne ƙwaƙƙwaran dalilin da yasa ita da kanta ta ɗaga waya ta kira Bintu ba saƙo ba. "Am nace ba? Ina fatan dai Hafizu ya faɗa miki matsayin da Zulai take da shi yanzu a gurinsa?" "Eh ya faɗa min. Ya ce za ta taya ni ƴan aikace-aikace har zuwa sadda zan gama wanka." Bintu ta amsa kai tsaye, ba tare da tunanin komai a tambayar da Innaye tayi mata ba. "Uhmmm!" Innaye ta faɗa daga can ɓangarenta, fuskarta bayyane da ɗan mamaki kaɗan, domin daman ta yi tunanin hakan zai iya faruwa. Ta daɗe da fahimtar idan al'amari ya biyo ta ɓangaren Bintu kamar dai Hafiz tsoronta yake ji. Shi yasa ta kira da kanta don ta faɗa ma Bintu yanzu Zulai matsayin matar Hafiz take, kuma tayi mata ƙwaƙƙaran jan kunne kan kar ta kuskura ta ce za tayi gigin ci mata amanar Zulai, idan hakan ya faru da ita da Hafizu za su gamu da mummunar ɓacin ran da basu taɓa tsammani ba. "Shi Hafizun ne yace miki an kai Zulai ne don ta taya ki aiki?" Kafin ta amsa da zafi-zafi a muryar Innaye ta cigaba da cewa "Ƙarya yake yi, bai faɗa miki gaskiya ba. Yanzu Zulai matsayin matarsa take ta sunnah kamar yadda kike matarsa. Shekaran jiya Baffansu ya ɗaura musu aure... Domin ita Zulaikha ba ni na haife ta ba, ɗiyar ƙanwata ce..." Ɗif! Wayar ta ɗauke daga can ɓangaren Bintu bayan wani ƙaƙƙarfan ihu da ta yanka da yayi barazanar kashe ma Innaye dodon kunne. "Subhanallahi! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Fatima lafiya kuwa? Me yake faruwa?" Innaye ta tambaya hankalinta a tashe bayan ta kawar da wayar daga kunnenta saboda amsa kuwwar da ihun yayi mata a kunne, daga bisani kuma ta mayar da wayar bayan taratsin ihun ya ragu a kunnuwanta. Shi ne har take jera ma Bintu waɗannan tambayoyin, duk a tsammaninta, wani abun ne can na daban ya ɗaga hankalin Bintu ba maganar da taji daga bakinta ba. Jin shirun yayi yawa babu amsa daga can ɓangaren yasa ta ciro wayar ta duba, sai a lokacin ta fahimci kiran ya tsinke. Hankalinta a tashe ta sake danna kiran lambar Bintu, nan take na'ura ta sanar da ita wayar a kashe take. Amma da yake ba jin abinda ake cewa take yi ba sai da ta kira kamar sau biyar ana maimaita mata amsa ɗaya sannan ta haƙura da kiran lambar. Da damuwa a fuskarta ta ajiye wayar ta cigaba da lazumin da take yi. 'Idan kuma ya kasance matsanancin kishi ne yasa Bintu ƙwallah ihun da kika ji ta waya fa?' Kwatsam! Wani sashe na zuciyar Innaye ta jefa mata wannan tambayar. "Autata." Ta faɗa a fili hankalinta a tashe. "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un! Auta tana cikin gidan kuma tun ɗazu da Hafizu ya kira ni mu gaisa ko da na nemi ya bani Auta ya faɗa min tun safe yana Ofishin shi." Ta sake faɗa a fili, tashin hankalinta na ƙara hauhawa. Sai a lokacin ta tuna ai Balira ta faɗa mata ta ba Auta wayarta ƴar sha-fa ta tafi da shi Habuja. Kenan idan ta kira lambar Baliran za ta ji a wane hali Autarta take ciki... Ba tare da wani ɓata lokaci ba ta rarumo wayarta ta fara bin lambobi tana neman lambar wayar Balira, wanda aka yi mata saving da alamar ƙwallo a jikin lambar. Saboda tsananin ruɗewa daƙyar ta iya gano lambar, jikinta na ɗan karkarwa ta danna ma lambar kira. Sai dai kuma cikin hukuncin Allah kira tayi har sau bakwai bai shiga ba. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel. Ya Allah ka tsare min Zulai aduk inda yake." Tayi addu'ar a fili hankalinta a tashe. Zuciyarta cike da fargaba da tsoron irin kishin matan birni da take jin labari a radio. Matan birni da idan kishinsu ya motsa don su yanke ma namiji mazakuta ba komai bane a gurinsu, tsoronta Allah tsoronta kishi yasa Bintu ƙona mata Auta da tafasasshen ruwan zafi. Domin a irin labaran kishin matan birni da take ji a shirin In da Ranka... wannan ba komai bane. Da saurin gaske ta lalubo lambar Hafizu mai alamar mota ta danna mishi kira. Yana ɗauka, bata tsaya jan wani dogon zance ba ta fara kora mishi ƙwaƙƙwaran kashaidi "Hafizu, kabar duk abinda kake yi yanzunnan ka tafi gidanka ka duba min halin da Auta take ciki. Domin na kira Bintu na faɗa mata Zulai matarka ce, na ji ta ƙwallah ihu, to ina rantse maka da Allah idan mahaukacin kishi yasa Bintu illata min Auta bazan taɓa yafe muku ba har duniya ta naɗe..." Ɗif! Cajin wayarta ta ɗauke ba tare da ta gama kora ma Hafizu kashaidi ba. Duk yadda take ta kunna wayar a ƙoƙarinta na sake kiransa, wayar da ta kawo sai ta ɗauke. A zuciye tayi cilli da wayar akan gado ta miƙe tsaye tana safa da marwa, bakinta ɗauke da duk wata addu'a da ta zo zuciyarta. A ɓangaren Hafiz ma ko da ya gwada kiran lambar Innaye ya ji swich off! Ya kira lambar Bintu ita ma a kashe, ya kira lambar Aunty Balira da yake hannun Zulai ita ma ya ji a kashe. Hankalinsa a tashe ya tsallake tarin ayyukan da ke gabansa ya fito daga cikin Ofishinsa ya nufi gida. ***** ***** Ba ita ta farka ba sai ƙarfe tara da minti biyu na safiya, ganin yadda garin ya waye sosai yasa ta yin mamakin irin barcin da tayi akan dadduma. Da sauri ta faɗa banɗaki ta yi wanka ko jikinta ya ƙara warwarewa daga gajiyan da yake tare da ita. Bayan ta fito ne ta lura da wata baƙuwar fallen takarda da aka nannaɗe ajiye a gaban madubi. A hankali ta ƙarasa ta ɗauka. "Mashkura" Shi ne sunan da ta gani rubuce da manyan baƙi a farkon saƙon. Ɗan murmushi ne ya suɓuce mata kafin ta fara karanta taƙaitaccen rubutacciyar saƙon da ya kasance da hausa ne. _"Ƙawata, Na shigo mu gaisa sai na ga kina barci. Sanin jiya baki wani samu isasshen barci ba shi yasa na kasa samun ƙwarin gwuiwar tashinki. Ki huta lafiya Ƙawata, ni na wuce makaranta. Idan na dawo in sha Allah yau za mu fara ɗaukar darussanmu kamar yadda muka tsara. Bye._" A hankali ta nannaɗe takardar har lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba. "Allah sarki Mashku. Ubangiji Allah ya dawo min da ke lafiya. Na gode ƙwarai da karamcinki a gare ni." Tayi maganganun a fili. Gefen gado ta ƙarasa ta ɗauki wayarta, sai a lokacin taga wayar a kashe. Ko da ta kunna sai taga ashe cajin wayar ce ta ƙare, kuma Aunty Balira bata ba ta cajar wayar ba. Ɗan ɓata fuska tayi alamun bata ji daɗin haka, wayar da wasiƙar da Mashkura tayi mata ta cusa a aljihun jakar kayanta sannan ta ciro manshafawarta ta zauna a gaban madubi ta fara shafawa. Zuciyarta cike da tunanin Innaye. Ta so ƙwarai ta kira Innaye yau da safennan su daɗe suna hira. Abinda yasa ta kasa kiran Innaye jiya shi ne ba ta so ta ƙara ɗaga mata hankali, shi yasa duk yadda take son jin muryarta ta danni zuciyarta har zuwa safiyar yau. Sai kuma ga shi wayar nasara ta yi mata tsiya. Ta gama shiryawa kenan a fisge ta ji kamar an yanka ihu daga can waje. Tsam! Ta tsaida hankalinta guri ɗaya ta ƙara saurarawa, sai kuma bata sake jin ihun ba. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke, ta ɗauki hijabinta ta zura ta kama hanyar ficewa daga ɗakin a niyyarta na zuwa kicin don sama ma kanta abinda za ta karya da shi. Hankalinta yayi nisa sosai a tunanin da take yi, kuma baza ta ce ga takamaimai abinda take tunani ba. Sam bata lura da tahowar Bintu a haukace ba sai ji tayi anyi mata wani wawan angiza da yasa lokaci ɗaya tayi taga-taga ta zube a ƙasa. A tsorace ta ɗaga idanu tana kallon Bintu da tayi amfani da wannan damar na faɗin da

Chapter 17 of 40