masu wahala, da taji sauƙaƙan sharuɗɗa ne yasa ta amsa har da murmushinta.
A maimakon ya miƙe ya fice, sai yayi tagumi ya ƙura mata idanu.
"Menene kuma?"
Ta tambayeshi tana ɗan tura baki gaba.
"Ina son ki ne..."
"Ni ma haka. Abban Imam don Allah ka tafi..."
Da saurin gaske ya fice daga ɗakin tun kafin ta gama maganar da take yi, fuskarsa cike fal da murmushi.
******
Duk da zancen tafiyar Zulaikha ya zo ma Mummy, Karima, Hajja a ƙurarren lokaci, bayan ƙorafi da nuna mata ɓacin ran rashin sanar da su batun tafiyar akan lokaci, ita kuma ta ɗauki laifin ɗungurugum ta ɗora akan Hafiz cewa shi ne bai sanar da ita za su tafi tare ba sai a ranar. Haka suka haɗa mata tsaraba mai yawa da za ta tafi ma da iyaye da ƴan'uwanta.
Karima dai hankalinta sam ya ƙi kwanciya da tafiyar Zulaikha. Gani take kamar idan Zulan ta tafi baza ta dawo ba kamar yadda ta ce. Minti ɗaya biyu sai ta kalle ta ta ce
"Zuly ina fatan dai ba tafiyar gaba ɗaya za kiyi ba? Don Allah kar kiyi mana haka, bamu shirya rabuwa da ke a yanzu ba."
"Ki kwantar da hankalinki Aunty Karima. Zan dawo in sha Allah, ai kin ga ko kayayyakin sawa ta ma ba duka na ɗiba ba. Zan dawo, don Allah ki daina damuwa."
Tun da yammacin ranar, bayan Abban Imam ya gama ramakon barcin da ke kanshi, ya fitineta a waya da tambayar me take so a matsayin tsaraba? Ita kuma tana ta sake maimaita mishi ba ta son komai.
Duk da haka dai be yarda ba, ana idar da sallar magriba ya ɗauki Karima da Imam suka shiga kasuwa siya mata tsaraba. Tunda yayi-yayi da ita tazo su je ta ce baza ta je ba.
Ba tare da jin zafin kuɗin da zai kashe ba haka Karima ta zage ta zaɓo mata turamen zannuwa masu kyau da tsada, ta ɗauki shaddoji kala uku da turaruka, sannan ta ɗibi ƙananun abubuwa wanda Zulaikha za ta raba ma sauran mutanen gidansu. Domin labarin ahalinsu Zulaikha ba wanda bata faɗa mata ba, sai dai kawai ace bata san su a idanu ba.
A ƙarshe bayan sun gama siyayya gaba suka ƙara zuwa wajen sayar da wayoyi. Wayar samsung ya siya mata mai kyau da tsada ya biya kuɗin komai suka fice daga gurin.
Ita dai Karima sai murmushin farin ciki take saki lokaci bayan lokaci, domin tun kwanaki ta fara fahimtar take-taken Yayan nata akan Zuly, amma da yake duk su biyun suna ta nuƙu-nuƙu, sai ta kawo idanu ta zuba musu. A yau kam ta tabbatar da gaskiyar komai, duk da Yayan nata mutumin kirki ne mai hannun kyauta, wannan uban siyayyar ba kowa za'a iya yima ba sai wacce zuciya ke tsananin So da ƙauna.
Daga Zulaikha har mutanen gidan babu wanda ya faɗa ma Imam washe gari za ta tafi, saboda gudun irin rikicin da zaiyi. Kawai sun bari ne idan ya dawo makaranta washe gari sai yaga ba ta nan.
Tsoro ne sosai ya kama Zulaikha da ganin irin tsarabar da Abban Imam ya kawo mata, a gabansu Mummy. Jikinta na rawa ta miƙe tsaye, idanunta a warwaje ta ce
"Mummy... Don Allah ku rufa min asiri. Na rantse da Allah idan na tafi da kayayyakinnan gida daga Innaye har Baffa sai sun kusa karairaya ni. Don Allah ku bar su, waɗanda kuka haɗa min ke da su Hajja ma na rantse da Allah sunyi yawa, kawai dai zan tafi da su ne in faɗa a gaban Yaya cewa ke kika bani, idan basu yarda ba sai in kira a waya kiyi musu ƙarin bayani..."
"Kin san Allah baki isa ba. Kin karɓi tsarabar kowa sai nawa da nake shirin aurenki za ki ce baza ki karɓa ba?"
Abban Imam ya faɗa ransa a ɓace, ba tare da kunyar idanun Hajja da Karima da suke gurin ba, kuma sam basu taɓa sanin da zancen soyayyar ba sai yanzu da bakinsa ya suɓuce ya faɗa.
"Ayyyuririririiiiiiii"
Hajja ta kama hanci ta rangaɗa ƙaƙƙarfan guɗa. Fuskarta na bayyana matsanancin farin ciki da jin wannan daddaɗan labari.
Mummy da Karima kuwa me za suyi ba dariya ba. Ita kuwa Zulaikha ina ma ƙasa zai tsage ta shige don kunya? Daƙyar ta iya juyawa da sassarfa ta gudu zuwa ɗakinta.
Sai a lokacin, shi kanshi ya tuna da ɓaram-ɓaramar da yayi. Amma da yake shi namiji ne sai kawai ya fuske ya daka ma Karima tsawa da tambayar wa take ma dariya?
"A'ah Yaya! Yanzu fa lallaɓani ya kamata kayi gaskiya... Domin a ɓangaren Zuly ka san dai ina da ƙarfin sakawa da hanawa, don haka gara ka bi ni a sannu kar in ɓata maka budget."
Waige-waigen neman abinda zai jefe ta da shi yasa ta miƙe da saurin gaske ta wuce zuwa ɗakin Zuly tana ƙyalƙyala dariya. Ko da ta shiga, haka ta tasa Zulaikha da tsiya da tsokana har sai da taga za tayi mata kuka sannan ta rabu da ita.
A gefenta ta zauna, ta cigaba da bata shawarwari, a fakaice kuma tana ƙara yi ma ɗan'uwanta kamfen. Domin al'amarin ba ƙaramin daɗaɗa mata zuciya yayi ba.
[2/9, 10:20 PM] Fareeda Abdallah: Saboda yadda Abban Imam ya kafa ya tsare a dole aka yi raba dai-dai tsakanin tsarabarsa da ta su Mummy. Aka rage yawan na su, aka zuba wasu daga cikin nashi. Sauran kuma aka haɗa a cikin babban jaka aka ajiye a ɗakin Mummy da cewa bayan sati ɗaya da tafiyarta ahalin gidan gaba ɗaya za su kai mata ziyara can ƙauye, a lokacin sai a tafi da sauran kayan a matsayin tsarabar da suka yi mata.
Wayar da ya siya mata kuwa ba don ranta na so ba tana ji tana gani Aunty Karima ta kwashe komai nata da ke cikin tsohuwar wayar, ta mayar mata a sabuwar wayar, tana kwashe kayayyakin tana mata mitar yadda komai aka ce ta tafi da shi sai ta ce a'a, ita tana tsoron Baffa da Innaye.
"Wannan wayar dai ko kin je gida da ita na tabbata basu san kuɗinta ba balle ayi miki faɗa. Kina zuwa ki mayar ma da Aunty Balira tsohuwar tata, tunda daman aro ta baki. Ki ce musu Mummy ce ta siya miki wannan, na tabbata baza suyi miki wani faɗa ko ƙorafi ba."
Yarda da Aminci mai yawa ne ke tsakanin Zulaikha da Karima. Ta yadda a tarihin Zulaikha ɗai ɗai ne abinda Karima bata sani ba, daga cikin abubuwan da har yau Zulaikha ta kasa buɗe baki ta ba Karima labari aurenta da Hafiz yana ciki.
Auren da tunaninsa kaɗai ke tsittsinka mata zuciya. Amma dai tana addu'a, kuma tana fata da yaƙinin wannan tafiya gidan da za tayi ya kawo ƙarshen komai, kuma ƙarshen komai ɗin ya taho a sauƙaƙe.
******
Tafiya Faƙo a wannan satin sam-sam ba ya cikin lissafinsa, saboda satin da ya wuce ya je. A yadda ya tsara, sai sati na sama zai tafi.
Amma maganganun Zulaikha da suka tsaya mishi a zuciya yasa ya katse komai da ya tsara gudanarwa a asabar ɗin ya shirya tafiya Faƙo.
Da damuwa sosai a fuskar Bintu take mishi ƙorafin tafiyar, saboda sun riga sun gama tsara ziyarar muhimman guraren shaƙatawa za suyi a wannan weekend ɗin.
"Kiyi haƙuri Sweetheart. Wallahi tafiyar ce tazo min bazata. Amma duk yadda ake ciki zanyi ƙoƙarin dawowa da wuri, idan lokaci bai ƙure ba sai mu fita, idan kuma lokaci ya ƙure sai mu bari lahadi."
Da haka suka rabu, ba don ranta ya so ba tayi mishi rakiya har bakin ƙofa, sannan ta karɓi Aadil daga hannunshi, ya sumbaceta a kunci kafin ya fice daga falon tana mishi addu'ar Allah ya kiyaye hanya.
Da yake shirin tafiyar a fusace yayi ta, ana idar da sallar asubah babu daɗewa suka fita shi da direba, ƙarfe shida rabi na safe yana ƙofar gidan Mummy. A lokacin Zulaikha ko wanka bata yi ba.
A taƙaice ma tana kicin tana yi ma Imam gashin Meat pie da yace zai tafi da shi makarantar Tahfeez. Wayarta kuma na ɗaki, shi yasa yayi ta kira bata san yana yi ba.
A ƙarshe sai Mummy ya kira, ya faɗa mata ga shi a ƙofar gida. Don Allah ta faɗa ma Zulai ta fito su wuce, idan ya dawo da yamma zai shigo.
Da ɓacin rai a muryar Mummy ta fara mishi faɗan ƙin faɗa mata tafiyarsu da yayi.
"Hafiz? Wani irin tafiya ne ka shirya haka tun da wuri baka sanar da ni za ka tafi da Zulaikha ba? Sai jiya take sanar da ni a ƙurarren lokaci wai ka ce tare za ku tafi gida. Akwai wani abu da ya faru acan gidan ne? Ko kuwa sun shirya komawarta can gida ne gaba ɗaya?"
Da farko shiru yayi, ya rasa amsar da zai bata, domin dai asalin wannan tafiya ba shi ya tsara ba, kuma shi kanshi bai san takamaimai abinda zai kai Zulai Faƙo ba. Amma saboda kar ya kware mata baya a gurin Mummy ita ma ta kware masa nasa bayan a gurin Innaye yasa shi cewa
"A'a Mummy, ba abinda ya faru. Kiyi haƙuri, za ta dawo in sha Allah. Innaye ce hankalinta ya ƙi kwanciya ganin tunda Zulai ta taho bata taɓa zuwa can ba sai dai su gaisa ta waya, shi yasa zan tafi da ita don hankalinta ya kwanta. Amma ba na jin za ta wuce sati ɗaya ko biyu, idan na je sati na sama zan dawo miki da ita. Kiyi haƙuri don Allah."
"Shi kenan. Allah ya tsare ya dawo da ku lafiya."
"Amin Mummy. A faɗa mata ta fito da sauri don Allah."
Duk yadda yake sauri sai da Zulaikha ta sake ɓata mintuna arba'in kafin ta fito cikin rakiyar mutanen gidan, Abban Imam da Imam ne kawai basu biyo ta ba.
Manyan sabbin jakunkuna biyu da yaga Karima na jaye da su har zuwa gurin boot ɗin motarsa ne yasa shi buɗe baki da mamaki a fuskarsa.
"Waɗannan kayayyakin fa?"
Ya tambaye ta.
"Na Zuly ne."
Ta amsa mishi a taƙaice.
A zuciyarsa ya ce
'Uhmm! Su Zuly manya.' Sai kuma a fakaice ya juya ya kalli Zulai da aka kira da Zuly, a bazata, ƙirjinsa yayi wani wawan bugawa, ganin wasu canje-canje ƙarara da yake gani tattare da Zulai.
Kamar dai ba ita ba. Ta zama wata babbar yarinya mai aji da kwarjini, doguwar rigar abaya da yake jikinta ya zauna mata cas! Kamar wata Hadiza gabon sadda take da ƙiba kafin tayi sleeming. Ta yi kwalliyarta sama-sama, wanda ya ƙara bayyana cika, ƙasaitarta, da wayewarta.
A ɗan firgice, ya mayar da hankalinsa kan Hajja ta take masa tsiyar irin wannan sammako da ya bugo musu kamar wanda zai bar ƙasar?
Har suka bar ƙofar gidan, da dariyar yaƙe yayi ta bin su Mummy. Zuciyarsa cike da ɗumbin mamakin gagarumin canjin da ya gani tare da Zulai, wanda bai taɓa mayar da hankali ya lura ba sai a yau da suka kama hanyar zuwa Faƙo shi da ita bayan watanni shida da wasu ƴan kwanaki da tayi rabonta da ƙauyen.
Duk da yadda baƙaƙen maganganu ke cike da bakinshi kafin su haɗu, ya kuma yi niyyar yi mata wankin babban bargo tas! Domin ta san har gobe fa ruwa na maganin dauɗa. A yanzu da suka haɗu, kuma suna tare a cikin mota ɗaya sai ya zama kamar wanda aka ɗaure masa baki, ya kasa ce mata komai. Lokaci bayan lokaci dai yana ɗago fuskarsa ya kalleta ta cikin madubi.
Ita kuwa bata ma san yana yi ba, kanta yana ƙasa, tana danna sabuwa kuma tsadaddiyar wayarta, fuskarta cike fal da wani lallausan murmushi.
Mamaki da tsoro mai girma ne ya kama shi ganin wayar da ke riƙe a hannunta,
'Na shiga uku! Kar dai a ce Zulai ta fara bin maza?'
Wani sashe na zuciyarsa ya jefa masa tambayar, sai kuma yayi saurin kore maganar ta hanyar yin ta'awizi.
Kamar bazai tambayeta game da wayar ba, sai kuma ya tuna idan bai tambayeta ba tabbas ya ci amanarsu Baffa. Fuskarsa a ɗaure, ya daka mata tsawa ya ce
"Keh! Wannan wayar fa? Ta waye kike amfani da ita kamar ta ki?"
A taƙaice, ta ɗan ɗago kai ta kalle shi da gefen idanunta.
"Tawa ce, Mummy ta siya min jiya."
Ta amsa mishi a taƙaice, sannan ta sake mayar da hankali kan chatting ɗin da take yi da Abban Imam.
Har zai bar maganar a yadda ta faɗa, amma sai zuciyarsa ta kasa nutsuwa guri ɗaya. Wayarsa ya ɗauka ya kira Mummy, bai ji kunya ba yake tambayarta wai ita ta siya ma Zulai waya?
"Eh! Ni ce. Akwai wata matsala ce tattare da hakan?"
Ta tambaye shi.
A daburce ya amsa da
"A'a! Babu komai Mummy. Daman kawai na yi mamaki ne, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki."
******
Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi a ƙofar gidan Baffa tayi musu. Tun kafin direba ya gama daidaita fakin ɗin motar a ƙofar gidan, Zulaikha da ganinta a ƙauyen nasu ya taso mata da matsananciyar kewar Innaye da ƴan'uwanta ta buɗe motar da sauri ta fice da sassarfa ta nufi cikin gidan.
Hafiz yana ƙwalla mata kira amma ko saurarenshi bata yi ba, kafin ƙiftawa da bismillah har ta ɓace ma ganinshi.
"Assalamu alaikum! Mutanen gidannan barkanku da safiya... Oyoyo Innaye na..."
Tayi maganganun da karaɗinta da mutanen gidan suka daɗe suna kewa.
Kai tsaye ɗakin Innaye ta nufa a guje saboda rashin ganinta a tsakar gida, sauran mutanen gidan suka rufa mata baya bakunansu har kunne don murnar ganinta.
"Maraba lale marhaban da Amarya Zulai... Lale lale, barkanku da zuwa... Sannunku sannunku, kun sha hanya. Sannunku da zuwa.
Ire-iren kalaman da ke fita daga bakin mutanen gidan kenan yara da manya, cikin ƙanƙanin lokaci aka cika ɗakin Innaye taf da jama'a.
Ita dai Zulaikha har lokacin tana maƙale da Innaye tana bin masu iyaye da ƴan'uwanta da dariya, ta hana Innaye tashi gaba ɗaya, don gani take kamar mafarki take yi, Innaye tana tashi daga kusa da ita za ta farka daga nannauyan barcin da take yi.
Mama Laminde da Mama Laraba su ne sukai ta ɗawainiyar kawo ma Zulaikha da Hafizu da ya shigo daga baya ruwa da sauran kayayyakin motsa baki. Tunda a lokacin ba'a gama abincin rana ba.
Ko kafin su fice daga ɗakin har labarin zuwa da Zulai da Hafizu yayi ya iske Baffa da ke can bakin kasuwa. Ai kuwa sai ga shi bagazan-bagazan yana saɓa babbar riga, bakinshi har kunne. Da gaske yayi kewar ƴar marainiyar ɗiyar tashi, matsayinsa na namiji ne kawai ba ya magana kamar yadda Innaye take yi.
Kuma sanin da yayi a yanzu Hafizu ya fi shi ƙarfin iko da Zulai shi yasa bai taɓa mishi ƙorafin me yasa baya zuwa da Zulai ba? Yau da shi Hafiz ɗin da kanshi ya yanke shawarar tahowa da ita, ba ƙaramin faranta mishi rai hakan yayi ba.
Ba ma kamar yadda yaga Zulai ta ƙara kyau da cika na musamman, alamun da ke nuna lallai fa ba ta cikin matsala ko kaɗan. Idan ya kalle ta yayi murmushi, sai ya kalli Hafiz yayi murmushi. Alamun da ke nuna zuciyarsa cike take da matsanancin farin ciki.
Minti ɗaya biyu kuma sai ya kalli Hafiz ya ce
"Hafizu na gode. Lallai ka cika ɗan halak! Allah yayi maka albarka."
"Amin Baffa."
Ya amsa addu'ar da farin ciki sosai a fuskarsa, domin ya manta rabon da yaga irin wannan farin cikin a fuskar mahaifinsa.
Ita kanta Innaye bakinta ya ƙi rufuwa, kamar gonar auduga haka take ta yaƙe haƙora tana shafa kumatun Zulaikha da ta ji sun ƙara laushi sosai.
"Zulai? Auta ke ce kika koma haka? Tubarakallah ma sha Allah! Lallai Hafizu baka watsar da amanar da na baka ba. Me kuke ba Autar tawa ne tayi irin wannan cikar ɗakin Hafizu?"
Ya rasa amsar da zai ba Innaye, sai kawai yayi murmushi yana ɗan sosa ƙeya.
Ita kuwa Zulaikha da ake ta caftar a kanta ganin irin matsanancin farin cikin da tsofaffin suke ciki yasa jikinta yin sanyi. Ƙuduri na daban ke a cikin zuciyarta, a yanzu kam ta shiga tsaka mai wuya, anya idan ta zama sanadiyyar yanke wannan farin cikin a cikin taƙaitaccen lokaci ta yi ma tsofaffin da suke matsayin mahaifa a gare ta adalci kenan? Ko kuwa haƙuri za tayi ta cigaba da zama a sagale, cikin wata iriyar rayuwa ita ba mai ƴanci ba ita ba mare ƴanci ba har zuwa lokacin da bata san iyakarsa ba?
Tana wannan saƙe-saƙen da canki-cankar, har aka kira sallar azahar. Baffa da Hafiz suka fita zuwa masallaci, ita da Innaye suka yi alwala suka yi sallah a cikin ɗaki. Ta daɗe sosai tana addu'o'i kala-kala bayan ta idar da sallah, har Innaye ta tashi ta fice ta shigo ma da Zulaikha abinci bata tashi daga kan dadduma ba.
[2/10, 10:39 PM] Fareeda Abdallah: "Auta addu'o'in sun isa haka. Ki katse haka nan ki tashi ki ci abinci."
Innaye ta faɗa da murmushi cike fal da fuskarta, domin kallon Zulaikha da yadda ta koma kaɗai ba ƙaramin farin ciki yake saka ta ba.
"Innaye sannu da aiki. Ni fa bana ma jin yunwa, ki zauna mu ci tare don Allah. Na yi kewar hakan Wallahi."
Ta ƙarasa maganar a shagwaɓe.
Suna zaune gaban farantin abincin, suna ci suna hira Hafizu da Baffa suka sake shiga cikin ɗakin.
"Kin ji Hafizu wai wucewa zaiyi yanzu, nayi-nayi ya tsaya su ci abinci ya ce a'a!"
"Ba dai tare da Auta zai koma ba ko?"
Innaye ta tambaya da sauri, idanunta a warwaje.
Yanayin yadda tayi tambayar yasa Hafiz da Baffa murmusawa.
"A'a Innaye. Ita kam tana nan, idan na dawo nan da sati biyu zan tafi da ita."
Hafizu ya amsa, har lokacin murmushin bai bar kan fuskarsa ba.
Nannauyar ajiyar zuciya Innaye ta sauke, kafin ta fara jera mishi addu'ar Allah ya tsare ya mayar da su gida lafiya.
"Amin Innaye. Na gode. Sai munyi magana ta waya."
"Yaya? Minti biyu don Allah"
Zulaikha ta kira shi da sanyin murya, a lokacin har sun juya za su fita shi da Baffa.
A tare suka sake juyowa suna kallonta.
"Ya aka yi?"
Ya tambayeta da ɗan murmushi a fuskarsa, ganin idanun iyayen na kanshi.
"Ko za ki bi ni mu koma ne?"
Ya sake tambayarta, tsabar iya duniya irin nashi har yana wani ɗan kashe mata ido ɗaya.
Martanin murmushinsa ta mayar masa, ƙirjinta na bugawa sauri-sauri, amma ko kusa bata bari tsoro ya bayyana akan fuskarta ba. Nannaɗaɗɗiyar takardar da tun ɗazu take ta yuƙwu-yuƙwu da shi a cikin hijabi ta fito da shi ta nuna masa
"Ka tuna wannan takardar?"
Kallon takardar da ke hannunta yayi, ya kalleta, duk da bai gane ko takardar mecece take nuna masa ba ya rasa dalilin da yasa ƙirjinsa bugawa daram!
"Ban tuna ba. Takardar mecece?"
Ya tambayeta, sannan ya taka da sassarfa da nufin ƙarasawa kusa da ita don karɓar takardar ya karanta abinda ke cikinta.
Yana miƙa hannunsa da nufin karɓa, ita kuma ta janye nata ta mayar cikin hijabi.
"Takardar da ka bani ranar da ka kaini gidan Mummy ne, har ka gwaɓa min maganar cewa in dai su Baffa ba asarar kuɗin tara suka yi ba idan na nutsu in zauna in karanta abinda takardar ta ƙunsa. A wancan lokacin, Wallahi tallahi ko cikakkun sati biyu ba'a yi ba na karanta muhimmin saƙon da ka rubuta min a cikin takardar."
Tana zuwa nan a maganganunta ta sauke nannauyan ajiyar zuciya, ga mamakin iyayen biyu sai ga hawaye sun silalo daga kwarmin idanuwanta.
Shi kuwa Hafiz ƙamewa yayi a tsaye kamar mutum-mutumi, jijiyoyin sadar da saƙonni daga zuciya zuwa ƙwaƙwalwarsa suka tsaya da kai saƙonni na wasu daƙiƙu.
Da rawar murya Zulaikha ta cigaba da magana
"Yaya... Zaman ƙaryan nan da yaudarar iyaye baza ta ɓulle da mu ba. Na gaji da tunanin inda ƙarshen tafiyar za ta ajiye ni, domin ta ko ina aka ɓullo ni ce zan kwana a ciki. Don Allah, don darajar fiyayyen Halitta SAW, ina roƙonka kaji tsoron Allah, ka warware ma iyayenmu halin da muke ciki..."
"Mmmmmme yake faruwa?"
Baffa ya katse ta da tambayar da sauri, bakinsa na rawa. Kafin ta amsa ya ƙara tambayarta
"Me kike ƙoƙarin cewa Zulai? Hafizu me kuke ɓoye mana?"
Ya ƙarasa maganar yana rarraba idanu tsakanin Zulai da Hafizu.
Ita kuwa Innaye, tuni ta fara jan duk wata addu'a da ta zo cikin zuciyarta, domin ta gama haƙiƙancewa duk abinda za su ji a yanzu, ba mai daɗi bane a gare su.
Kafin Hafizu ko Zulai ta buɗe baki tayi magana, sai ga sallamar Aunty Balira a bakin ƙofar ɗakin, tun kafin a amsa mata ta yaye labulen ɗakin ta shigo fuskarta cike fal da fara'a take cewa
"Wai ina Amaryar Hafizun take ne? Duk na ƙosa in ƙarasa aikin alalen da na tsira da ranar nan in zo inga irin ƙiba da kyawun da yara suka kururuta min cewa kin yi."
Ganin yanayin da su Baffa suke ciki kuma sai tayi suuu a tsaye, lokaci ɗaya fara'ar fuskarta ta ɗauke ɗif
"Baffa me yake faruw..."
"Ne mi guri ki zauna."
Baffa ya katse ta tun kafin ta ƙarasa tambayar da take niyyar yi mishi.
Jikinta a sanyaye ta zauna a ƙasa kusa da Zulai da take ta aikin tsiyayar hawaye kamar an buɗe famfo.
Umarnin zama Baffa yayi ma Hafizu, sannan shi ma da sanyin jiki ya lalubi hannun kujera ya zauna, saboda wani jiri da ya ji yana barazanar kayar da shi, tun ma kafin yasan takamaimai abinda yake faruwa tsakanin Zulai da Hafizu.
Idanunsa ya mayar kan Zulai, domin a ganinsa ta fi ɗan dama-dama cikin yanayin da za ta iya musu gamsasshen bayani na abinda yake faruwa.
"Zulaikha?"
Ya kira cikakken sunanta a tausashe.
"Na'am! Baffa"
Ta amsa bakinta na karkarwa.
"Na sani tun kina ƙanƙanuwar yarinya ƙirƙirar ƙarya ki faɗa don cikar wani buri ko son zuciyarki ba ya daga cikin halayenki. Kuma ina da kyakkyawar zaton har na aurar da ke baki canja daga wannan halin da na sanki ba. A bar ki dai da rashin haƙuri ga wanda ya shiga gonarki, da kuma ɗan taurin kai ga wanda kika raina ajawalinsa. Amma na tabbata ko wanda kike ƙi ne baza ki ƙirƙiri ƙarya ki jingina mishi don kawai ki cimma wani muradi na zuciyarki ba. Ina roƙonki kiji tsoron Allah, ki faɗa mana gaskiyar abinda yake faruwa tsakaninki da ɗan'uwanki kuma miji a gare ki..."
"Baffa... Tun da muka bar ƙauyen nan, kwana ɗaya kacal nayi a gidan Yaya Hafiz... Duk sauran watannin nan na yi su ne a gidan Hajiya Saudah wacce yake kira da Mummy, ita ɗin Shugabansa ce a can gurin aikinsa..."
"Ban... gane ba..."
Innaye ta katse ta bakinta na rawa, zuciyarta na bugawa sauri-sauri don jin wani sabon labari da ko kusa hankalinta ya gaza ɗauka.
"Rahina, kiyi shiru don Allah. Mu saurara tayi mana cikakken bayani yadda za mu fahimci abinda ke faruwa."
Baffa ya faɗa ma Innaye da sanyin murya.
Hafizu dai har lokacin yana tsaye ƙi ƙam! Kamar wanda aka sassaƙa shi. Duk da Baffa ya yi mishi umarnin zama, sam ya kasa motsa ƙafafunsa balle har ya ja su zuwa gurin kujera, ko kuma ya zauna a ƙasa kamar yadda sauran suke zaune. Baffa ne kawai a sama kan hannun kujera.
Ya riga da ya sani ko ba jima ko ba daɗe fallasuwar abinda ke tsakaninshi da Zulai dole ne, amma bai taɓa tsammani ko hasashe ko tunanin faruwarsa a irin wannan tsukun lokacin ba. Wani abin mamaki shi ne duk maganganun da ake yi yana ji tsaf, amma kamar wanda aka saka mishi dabaibayi a baki, sam ya kasa buɗe baki ya ce uffan! Balle har yayi yunƙurin kare kansa, ko kuma yayi ƙarin bayani yadda baza'a ga laifinsa ba. A taƙaice ma, kansa ya kulle tamau, ya rasa ta ina ya kamata ya kamo bakin zaren kurar da Zulai take neman ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 40