zama sai bare. A matsayinsa na namiji kuma yana da gida nasa na kansa bai kamata ace ƴan'uwansa idan suka shigo garin Abuja basu da gurin zama a gidanshi ba.
Karima ƴa a gurin Mummy Saudah, ita kaɗai ce ƴa mace tilo da yake jin zuciyarsa ta nutsu da ita kuma ta yarda da tarbiyar da ta samu. Kuma a yadda yaga shaƙuwa da ƙauna tsakaninta da Zuly yasan baza ta taɓa ƙin iyayenshi da ƴan'uwanshi ba ko da sun fi haka ƙauyanci.
Yini yayi a ranar yana tunanin al'amarin. Wani abun ikon Allah kuma sai yake jin har wani ɓurɓushin soyayyar Karimar ke taso mishi a zuciyarsa. Da wannan dalilin yasa yayi ta addu'a sosai, ko a hanyarsa ta zuwa gidan yana tuƙa mota yana addu'ar idan babu alkhairi a al'amarin kar Allah ya bashi ikon ƙarasawa gidan balle har ya samu sararin furta abinda ke ranshi. Ya tabbatar da alkhairi a lamarin ne jin yadda yake ta ƙara samun nutsuwa da kwanciyar hankali a tunanin Karima da son aurenta cikin gaggawa.
Ko da Mommy ta fito falon, bayan sun gaisa Hajja da Karima shigewa ɗakunansu suka yi bayan sun bayar da uzurin za su je su gabatar da sallar isha'i.
A karo na uku ya sake kallon Mommy ya sunkuyar da kai yana ɗan sosa ƙeya.
Mamaki ne ya kamata, sai kuma ta ɗan saki dariya tana cewa
"Hafiz? Wai ni ɗin na zama sarkuwarka ce? A sanina dai girmamawa ce a tsakaninmu amma babu ƴar kunya ko ɓoye-ɓoye. Yaushe muka fara ƴar haka da kai?"
A kunyace ya saki dariya, kafin yayi ƙarfin halin cewa
"Mommy yau dai zuwa nayi da ƙoƙon bara wajenki, ban san yadda za ki ɗauki al'amarin ba shi yasa nake jin wani iri. Amma tunda kin buƙaci in faɗa zan faɗa."
Ɗan shiru yayi, sai kuma ya cigaba da cewa
"Ki dubi girman Allah ki bani auren Karima. Na miki alkawarin zan rike miki ita da amana da mutunci!"
A bazata, zancensa ya sauka a kunnen Mommy. Shi yasa tayi ɗan shiru tana jinjina girman maganar a zuciyarta. Sai kuma ta koma ta jingina da kujera tana kallonshi a nutse, kafin murmushi ya ɓalle a fuskarta.
"Hafiz, da gaske kake yi ko da wasa?"
"Da gaske nake yi Mummy. Wallahi tallahi da gaske nake yi."
Ya rantse mata don ma ta tabbatar shi fa ba da wasa yake yi ba.
"Madallah! Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Amma ina so ka sani a wannan gaɓar babu abinda zan iya maka, iyaka in ce ka zage dantse ka nemi amincewa a wajenta, idan ta yarda, tabbas babu wanda zai kaini farinciki da jindadin wannan al'amari. Zuriyar Innaye da Baffa ai abin farin ciki da alfahari ne ƙara haɗuwa da su a karo na biyu."
Lallausan murmushi ya saki da jin kalamanta yana jinjina kai sannu a hankali.
******
****** ******
"My dear..."
Ta kira sunanshi da taushin murya
"Na'am!"
Ya amsa da yanayin muryar da ke bayyana gaf yake da fara barci.
Duk da fahimtar hakan da tayi, bai sa ta fasa faɗin maganar da ke bakinta ba. Saboda gobe tun da wuri take so ta kira Mashkura ta wuce da Aadil gurin Ummansu ko za ta huta da masifar tsotson da ya tsiro mata da shi a kwanakinnan.
"Daman ina so in faɗa maka ne, gobe asabar in sha Allah zan yaye Aadil..."
"Yaye dai Bint?"
Ya tambayeta a mamakance. Kafin ta amsa ya yunƙura ya ɗaga kansa daga cinyarta ya zauna suna fuskantar juna.
"Na zaci shekararsa ɗaya ne? Har ya isa yaye?"
"Ya isa mana My dear... Yana tafiyarsa ko ina, kuma yana cin abinci sosai. To me ya rage?"
Tayi maganar bayan ta kwaɓe fuska don ma kar yace zai hana ta.
Jinjina kai yayi, sannan ya ce
"Kin ga mu kuwa iyayenmu ba tafiya ko cin abinci ne ma'aunin yaye yaro ba. Sai yaro ya kai shekara ɗaya da rabi, idan yakai ɗin ma sai yayi haƙora fiƙa, idan baiyi har watanni ashirin yaro yana yi ana bashi nono, daman ko a addinance watanni talatin ne ciki da shayarwa..."
"Watanni talatin dai My dear..?"
Ta katse shi da sauri bakinta na rawa.
"Ƙwarai kuwa! Watanni talatin."
Ya amsa mata, don ƙara tabbatarwa har yana jinjina mata kanshi.
"Bazan iya ba. Allah ya sani bazan taɓa iyawa ba. Ka tausaya min don girman Allah... Kai baka ga yanzu yanda yake neman fin ƙarfina da tsotso ba?"
Ta jefa mishi tambayar idanunta ciccike da ƴan ƙananun ƙwallah.
"Ki kwantar da hankalinki. Ni daman tunda kin yi niyyar yaye shi bazan hana ki ba Bintu. Allah ya raya mana shi."
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke na samun kwanciyar hankali. A hankali ta amsa da
"Amin ya rabb!"
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na ƴan wasu daƙiƙu. Can kuma sai ta ce
"Gobe tun da safe Mashkura za ta zo ta wuce da shi can gida gurin Umma..."
"Wani gidan?"
Ya sake tambayarta a mamakance. Kafin ta amsa ya sake cewa
"Ba wani gida da za ki kai shi fa. Ki haɗa kayanshi idan zan tafi Faƙo gobe zan wuce da shi gurin Innaye..."
"Amma dai wasa kake yi ko?"
Ta tambaye shi da murmushi a fuskarta. Don ita har ga Allah da dukkan gaskiyarta ta ɗauka da wasa yake mata. Bata tabbatar da gaske yake mata ba sai da cikin ƙanƙanin lokaci ya haɗe girar sama da ƙasa yayi murtuk sannan ya ce
"Wasa? Zancen raha muke yi da zan miki wasa ko kuwa na zama abokin wasanki ne? Look Bintu, na gama yanke wannan zancen tun ba yau ba. Tun da kika haifi Aadil daga ke har shi sau ɗaya kuka taɓa taka ƙafa zuwa Faƙo. Idan a matsayinki na matata kin yanke mu'amala da iyaye da ƴan'uwana na zuba miki idanu shi baki isa ki yanke alaƙarsa da su ba. Su ɗin wajib ɗin sa ne. Don haka gobe zan tafi da Aadil gurin Innaye ta yaye shi acan, faƙat!!"
Sau uku tana buɗe bakinta tana rufewa amma ta kasa furta komai saboda tsananin yadda maganganunsa suka yi mata mugun dukan da yasa jikinta mutuwa murus!! Kalaman bakinta suka ƙafe ƙaf! Miyaun bakinta ya bushe ƙamas! Ta rasa abinda za ta ce masa kamar yadda ta rasa abinda ya kamata ta fara aiwatarwa da gaɓɓan jikinta. Abu ɗaya dai da yake ta amsa kuwwa a zuciyarta amma bakinta ya kasa furtawa shi ne ko sama da ƙasa za su haɗe a gobe, babu yadda za'ayi ta bari Hafiz ya ɗauki ɗanta ƙwara ɗaya ƙwallin ƙwal ya tafi mata da shi ƙauyen Faƙo.
Wani ɗan tunani da ya tsirga mata a zuciya yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Sannu a hankali, ta ɗan tsuguna kaɗan, kamar makauniya sai ta fara lalubar bakin gado da hannunta ɗaya sannan ta ɗosana mazaunanta. Idanunta tsaye ƙyam a kanshi kamar wacce ta warke makanta.
Ta sani, idan ta ce za ta biyo mishi da sigar tashin hankali babu abinda hakan zai haifar sai ƙara samar da ƙatoton giɓi a zamantakewarsu. Dama yaya lafiyar giwa balle ta yi hauka? Tun watanni biyu baya da suka kai ziyara gidan matsiyaciya Zulai har ta kasa mallakar zuciyarta tayi ta aikata abubuwan da ƙarara suka fallasa ma Hafiz ba ta ƙaunar ƴan'uwansa har yau basu koma kamar tif da taya irin yadda suke a baya ba.
Ba faɗa suke yi ba, suna gudanar da komai lafiya ƙalau, musamman daga gare ta da ya kasance kullum tana ƙirƙirar sabbin abubuwa don ƙara janyo hankalin mijinta gare ta. Amma ita da kanta ta sani Hafiz ya canja mata, irin canjin nan da baza a kira shi ɗari bisa ɗari ba, amma fa lallai canjin ya wawuke hamsin bisa ɗari. Kaso hamsin ɗin ne take ta lallaɓawa tana ta-ka-tsan-tsan don kar a sake samun matsala daga gare ta.
A karo na biyu, ta sake sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tayi narai-narai da idanunta tayi ƙasa da su sosai. Da sanyin murya mai bayyana tsananin ladabi da biyayya ta ce
"Allah ya huci zuciyarka Abban Aadil. Ubangiji Allah ya huci zuciyarka. Wa ce ni in ce zan raba Aadil da kakanninsa? Ni a su wa? kuma ko ni da kake ganin kamar na yanke alaƙata da su wallahi ba haka bane... Kawai dai na ɗan ja baya ne har zuwa sadda za su huce sosai saboda abinda ya faru na lamarin Zulai... Don Allah kayi min kyakkyawar fahimta masoyi..."
Ajiye maganar yayi daidai da silalowar wasu siraran hawaye daga kwarmin idanunta.
Kuma karaf a idon Hafiz. Amma wani abin mamaki shi ne, duk waɗannan tausasan kalaman, da waɗannan hawayen da suka cigaba da sauka a idanunta kamar an buɗe famfo, ko gezau baiyi ba balle har ya ruɗe ya fara ɓare-ɓaren jiki yana rarrashinta kamar yadda yake yi a baya. Sai ma wani siririn tsaki da yaja ƙasa-ƙasa ya nemi bakin gado ya zauna, wayarsa da take ajiye gefe ɗaya ya janyo ya fara latsawa sannu a hankali.
Wani matsanancin tsoro ne ya tumbatsa a zuciyar Bintu. Abu ne da bata taɓa tsammani daga Hafiz ba shakulatun ɓangaro da zubar hawaye a idanunta. Abu kamar aikin asiri? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Daga zubar hawaye na kissa sai na gaske suka koma zuba a idanunta.
Kamar za ta share shi, amma niyyarta na yaye Aadil gobe kuma Ummanta take so ta yaye mata shi domin har sun gama magana da ita Umman tun kwanaki yasa ta ja sanyayan ƙafafunta kusa da shi ta jingina kanta da kafaɗarsa tana cigaba da shessheƙar kuka. Da rawar murya irinta wacce kuka ke neman cin ƙarfinta ta ce
"My dear yaye yaro ɗan shekara ɗaya abu ne da ake buƙatar ya kasance kusa da mahaifiyarsa. Musamman da ya kasance Aadil yaro ne mai masifar ƙulafuci ga ƙwuiya, ka ga kuma ko babu komai ya saba da su Umma, sannan ga Mashku wacce duk tashen ƙwuiyar da yake yi sam ba ya mata. Ba ka ganin idan aka kai shi can Faƙo gurin mutanen da bai san su ba, bai taɓa ganinsu ba, bai saba da su ba, zai iya shiga wani mummunan hali da ba'a fata?"
Bai amsa mata ba, bai kalle ta ba, sannan bai fasa danna wayar da yake yi ba.
Ita kuma bata gaji ba ta cigaba da magana cikin ƙanƙan da kai da magiya, daga jingina kai a kafaɗunsa sai ta zame zuwa ƙasa ta haɗa hannayenta biyu alamar roƙo ta cigaba da cewa
"Ina roƙonka don Allah ka yi haƙuri My dear, Umma ta yaye a yanzu, nan gaba kaɗan ko shekaru biyu idan ya cika a duniya ni da kaina zan haɗa kayanshi ka kaishi gurin Innaye ya kwana musu biyu..."
Wani mahaukacin kallo da ya watsa mata kamar zai rufe ta da duka yasa ta ajiye numfashin maganarta ba tare da ta shirya ma hakan ba. Ajiye wayarsa yayi, ganin haka yasa taja da baya da sauri, don a tsammaninta zai kai mata hannu ne karo na farko a tarihin rayuwar aurensu.
"Uhmmmm! Bintu kenan! Na rasa abinda ya rufe min idanu tun a baya na kasa gano munana kuma baƙaƙen halayenki!! Yanzu saboda ba ki da kirki ni kike kallo tsakiyar idanuna kina kiran iyaye da ƴan'uwana wasu mutane can??? To bari in faɗa miki, ko Aadil zai mutu saboda ƙwuiya da rashin sabo Innaye ita za ta yaye shi..."
Izuwa wannan lokacin, duk yadda ta kai ga ƙoƙarin danne ɓacin ranta kasawa tayi. Ranta a ɓace ta miƙe tsaye ta tsaya a gabansa suna musayar kallo, da ɓacin rai mai bayyana maɗaukakin tashin hankali ta ce
"Amma gaskiya tsakani da Allah idan kayi min haka baka min adalci ba Hafiz. Saboda Allah ya kake so yaron da ya taso cikin gata, tsafta, tarairaya, shagwaɓa irin Aadil ya gudanar da ƙazantacciyar rayuwa irinta su Innaye...?"
Tahowar tafin hannunsa kawai ta gani a cikin idanunta, a zafafe ta yunƙura za ta ja da baya ankara da hakan da yayi yasa shi saka hannunsa na hagu ya finciko wuyar hijabinta.
Cikin sauri da sadaƙarwa haɗe da faɗuwar gaba tayi gaggawar runtse idanunta tana jira taji saukar mari a kumatunta, sai kuma taji shiru. Sakan ɗaya, biyu, uku, a hankali ta ɗan buɗe idanu ta saci kallonsa sai taga hannunsa maƙale a iska daf da kumatunta. Ko da ta kalli fuskar Hafiz da sauri ta sauke idanunta ƙasa saboda irin fusata da hucin da taga yana yi kamar zai ci babu.
"Kin ci sa'a! Kin ci sa'a Bintu tun da na tashi a rayuwata ban taɓa ganin Baffa ya daki Innaye ko ɗaya daga cikin matansa ba. Don haka ba na fatan ni ɗansa ace na fara dukar matata. Amma idan giyar wake kike sha ki ci gaba da aibata Iyaye, ƴan'uwa, ƙauyen Faƙo a gabana. Na rantse da Allah sai na koya miki hankali ta inda baki taɓa tsammani ba. Kuma ina sake faɗa miki, Wallahi Tallahi Aadil ko mutuwa zaiyi Innaye ce za ta yaye shi ba Ummanki ba."
Wuyan hijabinta da ya shaƙe ya wancakalar da ita, tayi taga-taga za ta faɗi, daƙyar ta iya tsayawa guri ɗaya. Bai sake kallonta ba ya ɗauki wayarsa, wallet ɗinsa da makullin motarsa ya fice daga ɗakin bayan ya ja mata wani dogon tsaki.
Ko bayan fitarsa ta daɗe cikin shiru, bayyanan tashin hankali da maɗaukakin tsoro ƙarara a fuskarta. Duk da wannan taratsin da ya mata ko kaɗan ba ta ji a ranta za ta iya saduda ya ɗauki Aadil ya kaishi gurin Innaye ba. Abu ne da sam-sam bazai taɓa yiwuwa ba ko da za suyi tashin hankalin da ya ninka wannan ya ƙara ninkawa. Don haka ta watsar da zancen ta fara tunanin yadda gobe da sassafe za tayi sammakon ɗauke Aadil daga gidan tun ma kafin ya farka daga barci, za ta gani, ko idan ta kai ma Ummanta Aadil yana da ƙwarin gwuiwar da zai iya zuwa ya ɗauko shi?
Can kuma sai idanunta ya faɗa kan agogo bayan ta ji ƙarar ficewar motarsa daga gidan, ƙarfe tara da minti goma sha bakwai na dare.
"Ina my dear yake haramar zuwa a darennan?"
Ta tambayi kanta a fili.
Lokaci ɗaya kuma sai tunanin yadda yake yawan yawace-yawace a cikin kwanakin ya faɗo mata a rai. Ƙirjinta ne yayi kwance-kwance ya buga daram!
"Na shiga uku ni Bintu? Kar dai ace yawon zuwa club My dear ya tsira abinda ba halinsa ba?"
Ta sake tambayar kanta hankalinta a tashe. Domin tunanin yi mata kishiya a soyayya balle har ya fara neman aure abu ne da ko a mugun mafarki bata taɓa hasashen zai iya faruwa ba.
******
A hankali yake tuƙa motar, jefi-jefi idanunsa na sauka akan fuskar wayar yana kallon lambar Karima da yayi saving sunanta da Ƙurratul-ayni. Kamar bazai kira ba, sai kuma ya danna mata kira, domin a yadda zuciyarsa ke tafarfasa ita ce kawai zaiyi tozali da kyakkyawar fuskarta ya nemi ɓacin ran da ke danƙare a zuciyarsa ya rasa.
Har ya cire ran za ta ɗauka sai kuma ta ɗaga a lokacin da kiran ke daf da tsinkewa. Bayan sallama, shiru tayi daga can ɓangaren tana jan fasali irinna macen da ake bibiya ana neman soyayyarta. Domin har yanzu ba wai ta sake mishi bane, jan zarenta take yi yadda take so shi kuma yana bibiye da ita sawu da ƙafa, abinda ke ƙara fasa mata kai kenan tana ci gaba da murza kambunta yadda take so.
"Ƙurratul Ayn..."
Ya kira ta a tausashe.
"Na'am.... Nurul-ƙalb"
Ta amsa shi da wani irin salo da ko a fili ko a waya bata taɓa gwada mishi irinsa ba.
Wani zirrrr da ya ji tun daga tsakiyar kansa zuwa babbar yatsarsa yasa shi saurin gangarawa gefen titi tun kafin ya buga ma motar gabansa. Ƙara ƙanƙame wayar yayi a kunnensa kamar me tsoron kar a ƙwace masa. Ya sake yin ƙasa ƙasa da muryarsa yana jin yadda zuciyarsa ke bugu sauri-sauri da matsanancin soyayyar Kariman. Allah ya sani yana son Karima, irin soyayyar nan mai saiɓi da shiga cikin zuciya sannu sannu kafin malallakiyar zuciyar ya ankara ta yi masa mugun kamu.
Idan za a ritsa shi da wuƙa shi da kanshi bazai ce ga abinda ke ƙara jansa a afka ma soyayyarta ka'in da na'in ba. Lallai sai yanzu ya ƙara yarda so tsuntsu ne, yana tashi haihata-haihata daga wannan bishiyar ya koma wancan. Bazai ce ya daina son Bintu ba, amma fa shi baya jin ta a ransa kamar yadda yake jin Karima.
Da gaske yanzu idan za a bashi Alƙur'ani zai rantse da Allah Karima yake so! Karima yake ƙauna!! Da Karima yake burin yin rayuwar aure na har abada!!!
"Ina so in ganki Ƙurratul-ayn! Yanzu...!"
Ya sake faɗa da murya ƙasa-ƙasa.
Shiru tayi na ƴan wasu daƙiƙu! Ta buɗe baki za tayi magana sai yayi saurin katse ta da cewa
"Kar ki ce min a'a dare yayi don Allah sanyin idaniyata. Ina cikin matsananciyar damuwa, tabbas idan banyi tozali da kyakkyawar fuskarki ba zanyi kwanan baƙin ciki ne a wannan dare."
"Me yake damunka Nurul ƙalb? Wa ya taɓa min kai ?"
Ta tambaye shi da murya mai bayyana damuwa da damuwarsa.
"Ke kaɗai nake son gani kawai... I'm very sure hankalina zai kwanta idan na ganki. Pls ƙurratul-ayn"
Ya sake faɗa cikin magiya, ba tare da ya amsa ɗaya daga cikin tambayoyinta ba.
"Shi kenan! Allah ya kawo ka lafiya. Amma yanzu ina asibiti..."
"Ga ni nan zuwa."
Bai jira ta sake cewa komai ba ya katse wayar. Tayar da motar yayi ya harba kan titi a guje yana jin yadda zuciyarsa ke tsallen baɗaken murnar za tayi tozali da muradinta.
A can ɓangaren Karima, narai-narai tayi da idanu tana kallon Hibba haɗe da cewa
"Na shiga uku Hibbah! Mijin Aunty Bintu ne fa...!"
"And so what?"
Hibba ta katse ta haɗe da gallah mata harara.
"Wani lokacin ke dai banza ce Wallahi Karima. Na rantse da Allah da tuntuni na san da wannan labarin da tuni kun daɗe da wuce wannan matakin. Sai me don mijin Bintu ne? Haramun ne? Uban me kuka haɗa da Bintun da har kike shakkar auren mijinta?"
Taja dogon tsaki ta sake gallah ma Karima harara a karo na biyu sannan ta cigaba da cewa
"Dama ace Bintun wata mutuniyar arziki ce shi ne har za ki ɗan ji wani ɗar don mijinta na son ki. Na zaci ke kika bani labarin irin yadda Bintun take wulaƙanta iyaye da danginsa don sun kasance ƙauyawa? Kuma baya ga haka ma ko asibitin nan nazo gurinki ai ina ganin yadda take wulaƙanta ku Nurses tana daka muku tsawa don kawai taƙamar ita likita ce. Don haka ki aje wata Bintu a gefe ɗaya ki rungumi masoyinki da gasken-gaske.
In dai har za ki ji shawarata, ki bashi dukkan goyon baya ɗari bisa ɗari. Tunda kika ga Mummy ita da kanta ta zaunar da ke tana faɗa miki kyawawan halayen Hafiz ɗin, alamun da ke nuna ta yi na'am da al'amarin ɗari bisa ɗari kawai dai ba ta son yi miki tilas ne.
Yanzu dai duk ba ma wannan ba, tashi ki shiga bayi ki wanke fuskarki kizo in miki kwalliya sama-sama don kar ya ganki garau-garau duk kin jigata da aiki..."
"Don Allah ki bari Hibbah, ni ba wani kwalliya da zanyi..."
Ai ko kafin ta rufe baki har Hibba ta finciki hannunta taja ta da ƙarfi suka fara tafiya zuwa banɗaki.
"Wallahi baki isa ba. An faɗa miki namiji irin Hafiz da sanyin jiki ake samun hankalinsu? Ko don kina ganin Allah ya kashe ya baki? To in faɗa miki ko kina da kyau sai kin ƙara da wanka kamar yadda ba'a bori da sanyin jiki."
A ƙasa da mintuna goma sha biyu Hibba ta yi ma Karima sassauƙar kwalliyar da ya ƙara fito da ita fes! Ta tsiyayi humrah ta shafa mata. Don saboda tsabar sabo da gayu da gwalli duk inda Hibba za ta saka ƙafa a cikin jakarta akwai komai da za ta buƙata na kwalliya. Ko don ya kasance sa'na'arta ne oho!!!
Kamar yanzu dai, ƙanwar Hibban aka kwantar a asibitinsu Karima, mahaifiyarta ita ta yini da mare lafiyar ita kuma Hibba za ta kwana da ita. Duk da sanin jinya za ta je asibiti hakan bai hana ta zuwa da kayan kwalliya da ɗaya daga cikin kalolin humrar da mahaifiyarsu take sayarwa ba. Ashe rabon tayi ma Karima amfani da kayan kwalliyar ne.
Karima aikin yamma tayi, tun tuni ya kamata ta tafi, amma ganin Hibba ya saka ta zama tana rage mata dare, bayan ta kira Mummy ta faɗa mata ba sai an turo mata direba ba, direban gidansu Hibba zai dawo da ita gida.
Hira ne yayi hira har Allah ya matsi bakinta take ba Hibbah labarin irin naci da matsanancin son da Hafiz ke mata. Bayan ta gama zage ta tas kan irin wasa da dama ɗaya da Allah ya jefo mata sannan ta ɓuge da bata shawarwarin yadda za ta sauke duk wani izzah da aji ta ƙara ruƙo wuyan Hafiz ɗin ƙam! Ta yadda bazai taɓa gigin barinta ba. Suna cikin wannan tattaunawar ne Hafiz ya kira ta a waya, shi ne fa har ta fara gwada masa kulawa da soyayya wanda da can ba ta wani nuna masa saboda tsoron abinda zai je yazo idan zancen soyayyarsu ya koma kunnen Bintu.
Isowar Hafiz harabar asibitin ya yi daidai da isar Dr. Raudha aminiyar Bintu na ƙud-ƙud cikin asibitin. Ita a ranar aikin dare take da shi. Mamaki ne ya kamata don ta san Bintu aikin safe tayi, tunanin ko wani abu yazo karɓa ma Bintu a cikin asibitin yasa tayi watsi da mamakin ta cigaba da latsa waya tana ƙoƙarin danna kiran lambar Mamanta har Hafiz ya shige cikin asibitin akan idanunta.
Tsayawar da tayi amsa waya a cikin mota yasa tayi kyakkyawan ganin da yasa wayarta ya suɓuce daga hannunta ya faɗa kan cinyarta. Bata ko bi ta kan wayar ba ta cigaba da kallon Hafiz da Karima da suka jero suna takun da ke bayyana ƙarara masoya ne su biyun. Kamar ita ce Bintu, saboda wani baƙin ciki da kishi da ya rufe mata idanu, a haukace ta yunƙura za ta buɗe motar ta fita sai kuma tayi gaggawar saka ma kanta linzami.
Wayarta ta rarumo da sauri, bata bi ta kan muryar mahaifiyarta da take ji yana fita a cikin wayar ba ta katse kiran a gaggauce, hannunta har rawa yake yi gurin lalubo lambar Bintu ta danna mata kira, amma wani abin baƙin ciki da takaici shi ne wayar Bintun a kashe take.
Cikin ƙasa da sakan hamsin sau huɗu tana gwada kiran Bintu na'ura na faɗa mata wayar a kashe take. Baki da hanci buɗe zuciyarta tumbatse da maɗaukakin mamaki ta cigaba da bin su Hafiz da kallo har suka shige cikin motarsa shi da Karima. Tsoro ne sosai ya ƙara kamata ganin yadda Hafiz ya buɗe ma Karima ƙofar da za ta shiga yana kashe ta da lallausan murmushi. Idan ma ba idanunta ne ke mata gizo ba, sai taga kamar har wani ɗan duƙawa Hafiz ɗin yayi ma Karima alamun girmamawa.
Ita kuwa Karima sai wani rausaya take yi tana rangwaɗa haɗe da fari da idanu. Ko rantsuwa tayi babu kaffara akan idan ba matsananciyar soyayya ba ce a tsakaninsu babu yadda za ayi ta gansu a cikin wannan yanayin.
"Taɓɗijan! Namiji! Namiji!! Mugu ɗan masara ana goyonka kana gemu... Don ubanki Bintu ki buɗe waya in baki labarin kaɗan daga cikin sakayyar da Hafiz zai miki kan irin alwashin da kika daɗe kina sha akan shi ya fita daban a cikin maza."
Ta yi maganganun cikin masifa kamar za ta ci babu, a lokaci guda kuma tana cigaba da gwada kiran lambar Bintu. Wanda har lokacin na'ura ke sake tabbatar mata wayar a kashe take.
Ita kaɗai a cikin motar take masifa tana zage-zage kamar za
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 40