Share this page
ƙarin wata shawarar. Why not yanzu kafin mu isa gurin ita wancan ƙanwar tasu mu fara biyawa butique mu sayi belt da za mu ɗumama mata jiki da shi? Don dai ina ga kai kyawawan hannayenmu zuwa jikin wancan local yarinyar zubar da aji ne. Amma idan muka samu belt, cikin ƙanƙanin lokaci za mu farfasa mata jiki da fuska, don da gurin ƙarfen za mu ci ubanta..." "Muguwa Ƙawata." Bintu ta katse ta da faɗin haka, sannan suka kwashe da dariya haɗe da tafawa. Bayan sun sayi belt ɗin a hanya suka cigaba da tattauna yadda za su ci uban Zulai la'ada waje har suka isa gidan Momy Sauda. Saboda tsabar ƙarfin hali irinna Bintu har cikin gidan ta shiga da motarta. Bayan sun fito suka nufi cikin gidan tinƙis-tinƙis, da belt tsirara riƙe a hannayensu. Ko da suka danna madannin da ke isar da na ciki akwai baƙo a waje, bakunansu cike yake da addu'ar Allah yasa Zulai ce za ta buɗe ƙofar. 'Lallai da tun daga nan za su fara tafka mata belt, sai sun ruɗa ta da duka sun farfasa mata jiki. Sannan a wulaƙance Bintu za tayi mata wani shaƙa da sai ta fara jiyo ƙamshin mutuwa, za ta wancakalar da ita a ƙasa ta mutsuke mata ƙazantattun yatsun hannayenta da har suka yi kuskuren riƙe mata ɗa na kwana biyu. Ita da kanta za ta shige ɗakunan gidan ta zaƙulo duk inda ɗanta yake ta tafi da shi.' Wannan duk tunani ne da yake danƙare a zuciyar Bintu. Cikin rashin sa'a Imam ne ya buɗe musu ƙofar Falon, kuma yana buɗewa ta ciki, bai tsaya ba a guje ya koma cikin falon ya cigaba da wasanshi. Haɗa idanu suka yi, sannan suka gyaɗa kai kamar wasu ƙadangaru, Bintu ta ƙara da ƙwafa a hankali sannan suka bi bayan Imam zuwa cikin falon. Kiciɓus aka ce mugun gamo! Kamar haka ne ya same su bayan sun shiga falon suka yi arba da Zulaikha zaune akan kujera, ta pose kamar wacce za a ɗauka hoto, cikin wani ƙayataccen kwalliya da kayan turawa, wandon jeans ne a jikinta ya matse ta sosai. Ta miƙar da ƙafafunta ta ɗora ɗaya kan ɗaya tana ɗan girgizawa sannu a hankali cikin ƙasaita da aji. Daga inda take zaune, suna hango tudun mazaunanta yadda suka wani botso ta cikin wandon jikinta sannan suka ɗan baje akan kujera. Rigar da ta saka irin mai wawakeken wuyan nan ne, ta saman na shanunta da suke farare tas sun bayyana a fili. Babu hula ko ɗan kwali a kanta, sai sumanta da yasha gyara tun daga nesa yake ɗaukar ido ta sake shi ya sauka har kan kafaɗunta. Wata iriyar siririyar dariya take saki sannu-sannu gwanin ban sha'awa. Sai da suka sake ƙure ta da kallo sai suka ga ashe Laptop ne ajiye akan wani ɗan teburi da ke gabanta. Bisaga dukkan alamu Vidio call take yi da mijinta. Duk da ta ji ƙarar buɗe ƙofa alamun an shigo bata tsaya da dariyar da take yi ba, kuma bata ɗaga kai ta kalli su Bintu da suka yi suman tsaye suna kallonta ba. Sai da ta gama dariyar sannan a tausashe da wata iriyar siririyar murya ta ce ma Abban Imam ya bata minti biyar anyi baƙi. Daga can cikin laptop ɗin sumbatar hannayensa yayi ya hura mata, ba tare da kunyar idanun su Bintu ba ta mayar mishi da martani sannan ta katse kiran. Mayar da hankalinta kan su Bintu tayi, kallon sakan goma tayi musu sannan ta buɗe baki a hankali ta ce "Au! Ashe ma ku ne." Ta faɗa tana ɗan yamutsa fuska da salon wulaƙanci da tozarci. Bintu da takaici da baƙin cikin irin canjin da ta sake gani na sosai a jikin Zulai yake neman kaita kushewa bata san sadda ta buɗe baki cikin ɗaga murya ta lailayo wata bamagujiyar ashar ta maka mata ba. Da ɗan sauri Zulaikha ta saka yatsarta manuniya ta toshe kunnenta ɗaya, sannan da yanayin muryar da ta goge da furta kalaman turanci cikin ƙasaita ta ce “Keep it low, you are so loud” Bintu da bata taɓa tsammanin bayan wayewar da Zulai tayi har turanci ta iya ba taga-taga tayi za ta kifa saboda tsananin yadda maganar ya dake ta. Da saurin gaske Raudha ta yar da belt ɗin hannunta ta riƙo Bintu kafin ta kai ƙasa. Fincikewa Bintu tayi, hankalinta tashe da irin tozarcin da Zulai tayi mata ta yi zaman ƴan bori a ƙasa, sannan ta ɗora hannu biyu akai ta saka kuka wi-wi kamar ƙaramar yarinya. Hankalin Raudha a tashe ta ce "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye haka kike yi Bintu? Kuka a gaban wannan yarinyar ai sai ki ja ma kanki raini da tozarci..." "Raini? tozarci? wulaƙanci na nawa kuma Raudha? Baki ji irin kalaman da ta furta min bane?" Tayi maganar cikin kuka wasu sababbin hawaye na sake ɓalle mata. "Ki ce mata ta bani ɗana. Kuma Allah ya isa tsakanina da ita da duk danginsu. Kuma na rantse da Allah basu ci bulus ba duk sai na saka ƴan sanda sun ci kutumar ubansu..." Zulaikha tana hakimce akan kujera, babu abinda take yi sai ƙyalƙyala dariya amma a hankali. Gogewar da tayi yasa hatta dariya idan za tayi yanzu a ƙasaice take yi. Kukan da Bintu take rusawa ba ƙaramin faranta mata rai yayi ba. Jin irin maganganun da take furtawa yasa ta ɗaga waya ta kira Hafiz yana ɗauka ta saka a hands free. Su Bintu basu san ta kira shi ba sai jin muryar Hafiz suka yi ya karaɗe kunnuwansu yana ce ma Zulai "Hello Sis! How far?" "Normal Luvly Bro." Ta faɗa da salon ƙara cusa ma Bintu haushi, kafin yayi magana ta sake cewa "Yaya kai ne ka turo Bintu ta zane ni da belt sannan ta ɗauki Aadil...?" "Zana kuma Zulaikha?" Ya katse ta cikin tashin hankali. "Eh! Ga su nan rirriƙe da belt ita da wannan figaggiyar ƙawar tata wai za su min duka." Ta ƙarasa maganar a shagwaɓe. "Ke kuma sai ki tsaya su zane ki? Ke ce fa Zulai shago ta Innaye. Ko rayuwar birni yasa kin zama saiwar-sala ne?" Yayi mata kirarin da Baffa yake mata tana ƙarama, saboda tsabar ƙarfinta, duk yarinyar da ta kuskura suka haɗa ƙashi da Zulai duk girmanta sai ta kai ta ƙasa. Shi ne Baffa ke kiranta Shago ta Innaye. "Ni ɗin ce dai. Har gobe ruwa na maganin dauɗa Yaya." Ta amsa tana dariya. "Yauwa Ƙanwata. Kina ji na? Bintu da ƙawarta mahaukata ne a cikin riguna. Cikin su biyun duk wacce tayi gigin taɓa ki nayi miki izini ki ɗaga ta sama ki nuna ma Allah sannan ki damfarata da ƙasa... Allah yasa ma su kakkarya ƙasusuwan baya... kin ga ko babu komai an rage miyagun iri da basu san darajar mutane ba. Kuma a hukumance ba ki da laifi, biyo ki suka yi har muhallinki, kuma ƙwararren lauya za mu ɗauka ya kare ki a kotu da cewar garin kare kanki ne tsautsayi ya afka musu..." Dariyar da yayi ma Zulaikha yawa yasa ta katse kiran tana cigaba da ƙyalƙyala dariya. Tsawon wasu daƙiƙu ta ɗauka sannan ta tsaida dariyar ɗif kamar ɗaukewar ruwan sama. Da ɗaurarriyar fuska take kallon Bintu da jiniyar kukanta ya tsaya sai tsiyayar hawaye. "Kin dai ji ko? Ko a gurin mijinki farashinki ya riga ya daɗe da faɗuwa ƙasa war-was! Sakarya kawai!!!" Daga Bintu har ƴar kanzagi Raudha an rasa wanda zai tanka ma Zulai da miyagun kalaman da take yaɓa ma Bintu. Har sai da ita da kanta Zulaikha ta gama jan aji ta cigaba da gargasa mata maganganu masu ɗaci. "Tabbas! Ɗanki Aadil yana hannuna. Don haka ki daina wahalar da kanki kina yawo daga wannan gida zuwa wancan gida kina nemanshi. Yana gurina, kuma idan sama da ƙasa za su haɗe na rantse da Allah bazan taɓa baki shi ba, matuƙar ba Yaya da kanshi bane yazo ya karɓe shi kamar yadda ya kawo min shi. Ku tashi ku ɓace min da gani kafin inyi rehazal ɗin irin dukan da na sha yima su Ladiyo a dandali akan ku." Ta ƙarasa maganar haɗe da miƙewa tsaye. A ƙauyen Faƙo, Raudha ce take jan Bintu ita kuma tana turjewa. Ayau kuma Bintu ce ta miƙe tsaye ta riƙe hannun Raudha ta ja ta a fusace suka fice daga falon, ba tare da sun ɗauki belt ɗin da suka kashe dubu goma sha biyar gurin siyansu ba. Suna fita daga cikin falon, Zulaikha ta ƙyalƙyale da dariya har tana tafa hannuwa. Al'amarin ya yi mata daɗi ba kaɗan ba, zuciyarta cike da godiya ga Allah da ya kasance babu kowa a gidan daga ita sai Imam. Mummy da Karima tun safe suka yi sammakon tafiya gurin aiki. Ita kuma Hajja ƙarfe tara da rabi ta shirya ta tafi rabon dabino da sweet na auren Karima da Hafiz da aka tsayar nan da sati huɗu masu zuwa. Tun jiya da daddare Aunty Rakiya ta kira ta a waya ta bata labarin duk irin ba ta kashin da suka yi da Bintu. Kuma ta jaddada mata lallai ta zama cikin shiri, domin bisa ga dukkan alamu baza ta rusina ba sai ta gano inda ɗanta yake kuma ta karɓe shi. "Kar ki kuskura ki ɗaga mata ƙafa Zulai. Dukan da naso inyi mata anan ban samu dama ba don Allah ki cika min wannan burin." Cewar Aunty Rakiya, muryarta cike da takaicin yadda har yau bata samu damar ɗunɗuma ma Bintu jiki ba. "Kar ki damu Aunty. Ai ita Bintu ta san karonmu da ita babu daɗi. Za ta kwashi kashinta a hannu." Ta amsa tana dariya. Tun daga lokacin take ta addu'ar Allah yasa idan Bintu ta tashi zuwa su Mummy basa nan, sai kuwa ga shi addu'arta ta karɓu. Tana wannan dariyar ta ɗauki wayarta da Laptop ta wuce cikin ɗaki inda Aadil ke kwance yana barci cikin kwanciyar hankali. Yaron da a kwana ɗaya da tayi da shi ta fahimci sam ba shi da damuwa, idan anji kukanshi yunwa yake ji. Da an bashi abinci zai cigaba da wasa da Imam, wanda zazzaɓin dare da yayi ya hana shi tafiya makaranta a ranar. ******* Tun da ta figi motar suka fice a guje daga gidan Mummy Sauda, tsakanin ita da Raudha an rasa wanda zai fara kore zaman ƙuda da yake tsakaninsu. Sai dai daga yanayin yadda Bintu take sauke zazzafan huci akai-akai, take murza sitiyarin da uban ƙarfi kamar shi ya kar zomon, take ƙara taka giyar motar tana ƙara gudu kamar wacce za ta kai wasiƙa, za a fahimci matsanancin ɓacin ran da yake danƙare sunƙi-sunƙi a zuciyarta. Da farko ta yi tunanin ita da kanta za ta ladabtar da Zulai, amma a yanzu ta yanke shawarar gara ta haɗa ta da su Aunty Balira hukumar ƴan sanda su koya musu hankali. Gudun da take zurawa yanzu ba ko ina ta nufa ba sai ofishin kwamishinan ƴan sanda. Kiran da Babbar Yayarsu Aunty Sadiya tayi mata, shi ya katse duk wani hanzari da take tafe da shi. Kamar baza ta ɗauka ba, sai kuma ta ɗaga bayan ta yi tunanin haka kawai Aunty Sadiya ba ta kiran mutum a waya sai da ƙwaƙƙwaran dalili. "Helloo Aunty..." "Bintu kina ina ne?" Ta katse ta da tambayar da muryar da ke bayyana rashin wasa. Har Bintu ta buɗe baki za ta faɗa mata gaskiya, sai kuma tayi tunanin gara kawai tayi mata ƙarya. Domin za ta iya dakatar da ita daga ƙudurinta. "Ga ni a hanya zan koma gidana..." "Gidanki ko gidan Hafiz?" Ta sake jefa mata tambayar a tsawace. Kafin Bintu ta amsa ta cigaba da cewa "Anya Bintu ko dai kin fara shaye-shaye ne bamu sani ba? To duk inda kika nufa ina umartarki da gaggawa ki juyo kizo ki sameni a gidan Daddy... Tunda hauka da rashin hankali da rashin kunyar ɗan fari yasa ki iya rufe ido ki zazzagi uwar mijinki da yayyensa sai ki dawo gida ki cigaba da zama a ɗakin Mashku... Ga takardarki Hafiz ya kawo min ni kuma na kawo ma waɗanda suka haife ki..." Ƙit! Wayar ta katse, daga can ɓangaren Aunty Sadiya. Bintu da ta kasance cikakkiyar bahaushiya gaba da baya, kalaman Aunty Sadiya duk da da hausa tayi su sai suka sauka a kunnenta kamar da wani irin yare ne da bata taɓa sani ba. Sam! bata fahimci me maganganun suke nufi ba, infact bata ma fahimci inda suka nufa ba. Da wani yanayi mai wuyar fassaruwa ta kalli Raudha, kasancewar a handsfree ta saka wayar bayan ta ɗaga "Ko kin fahimci inda maganganun Aunty Sadiya suka nufa?" Tsaf! Raudha ta fahimta. Amma tsoron aji mutuwar sarki a bakinta ga shi suna tsakiyar babban titi yasa tayi saurin gyara yanayin tashin hankalin da maganganun Aunty Sadiya suka jefa ta tace "Nima dai ba wani fahimta nayi ba. Amma na san bai wuce ace Hafiz ya kai ƙararki gidanta ita kuma taje ta faɗa ma su Mummy. Don haka ina ga ki bar batun zuwa gurin kwamishina yanzu, kije ki ji kiran da take miki." "To shi kenan. Bari in fara sauke ki a gida..." "Ai ba ma sai kin kaini gida ba Bintu. Sauke ni anan in samu taxi ya ƙarasa da ni. Gara kiyi gaggawar zuwa kiji dalilin kiran, idanma wasu ƙarerayin Hafiz ya shirya miki kiyi gaggawar warwarewa da bayanin gaskiyar abinda ya faru. Idan basu yarda ba kina iya kira na in bada shaida." "Na gode Raudha. Allah yabar ƙauna da zumunci. Shi yasa a kullum ba na gajiya da godiya ga Allah da ya bani ke matsayin babbar ƙawa." "Kar ki damu Bintu. Kin cancanci fiye da haka a gurina." Da haka suka rabu, zuciyar Bintu cike da karsashi da ƙwarin gwuiwa, ita kuwa Raudha zuciyarta cike da fargaba, da addu'ar Allah yasa Hafiz ba sakin Bintu yayi ba. Tunda da kunnenta ta ji maganar takarda, to wace takarda ce kuwa za ayi maganarta idan ba ta saki ba? Bintu tana shiga layin gidansu da mota, ta hangi motar Hafiz na fitowa daga cikin layin. Lokaci ɗaya zuciyarta ta ƙara ƙuntata da ɓacin rai. 'Kenan zancen Raudha ya tabbata?' "Uhmmm! Namiji kenan! Ƙudan zuma ga zaƙi ga harbi. Na rantse da Allah ko me za kayi Hafiz kai da su Umma baku isa ku hana ni ƙwatar ƴancina ba a matsayina na uwa." Tayi maganar a fili cikin masifa, ko da suka zo gitta juna daƙyar ta iya dannar zuciyarta bata buɗe gilashi ta watsa mishi daƙuwa ba. Ta ja motarta a guje ta wuce shi ma ya cigaba da tafiya, ko ɗan horn ɗinnan babu wanda ya latsawa juna, kamar dai ba su ne masoyannan da suke bala'in ƙaunar junansu ba. Ko da ta isa gida, da farko ta shiga ne da wani irin fitinannen izza da jiji da kai. Sai da taga ba a cikin falon mahaifiyarta bane Aunty Sadiya da sauran yayyenta maza uku suke zaune. Suna cikin falon mahaifinta ne, kuma ƙarin ɗaga hankali a gareta shi ne idanun magahaifiyarsu da Aunty Sadiya ya yi jajur, alamu ƙarara da ke nuna sun ci kuka sun gode Allah. Tun daga nan jikinta ya fara sanyi. A ɗarare ta nemi kan kafet ta tsuguna, bayan ta yi sallama babu wanda ya amsa mata a cikinsu. "Daddy..." Wani gigitaccen tsawa da mahaifinta ya daka mata yasa bata san sadda ta zame daga tsuguno tayi zaman ƴan bori a ƙasa ba. Lokaci ɗaya idanunta suka kawo ruwa, lallai wannan shi ne a dake ka a hana ka kuka. Bata daddara ba da tsawan da yayi mata ba, don ta sha alwashin baza ta taɓa bari shirunta ya ja Hafiz ya ci galaba a kanta ba, cikin rawar murya da saurin baki ta sake cewa "Daddy don girman Allah ka bari inyi muku bayanin gaskiya..." "Ba ma buƙatar wani bayani na gaskiya daga bakinki Bintu." Ya sake katse ta a karo na biyu, da yanayin magana mai bayyana ɓacin rai a fili. Kafin ta amsa ko ƙoƙarin kare kanta ya cigaba da cewa "Mun ji gaskiyar zance daga bakin yayyen mijinki biyu da aka kira a waya aka saka su a handsfree. Sannan Mun ji rekodin ɗin muryarki jiya da kika je tsakiyar ɗakin sarkuwarki a can ƙauyensu kika yi mata cin mutunci na ƙarshe ita da ƴaƴanta. Sannan mun ji bayanin yadda kika je gidan ƙanwar mijinki yau za kiyi mata duka. Daga nan ɓangarenki kuma Yayarku ga ta nan ta kora mana bayanin duk irin rashin mutuncin da taga kin yi ma dangin mijinki lokacin haihuwar ɗanki. Wannan shi ya ƙara tabbatar mana da gaskiyar maganganun mijinki da ƴan'uwansa. Don haka ki riƙe bayanin gaskiyarki, wata ƙila za tayi miki amfani a gaba. A ƙarshe dai ungo wannan." Ya ƙarƙare maganar haɗe da ɗaukar wata farar nannaɗaɗɗiyar fallen takardar da tun shigarta cikin falon bata lura da ita ajiye kusa da shi ba, sai yanzu da ya ɗauka ya miƙa mata. Da farko ƙin karɓa tayi, sai da Yayanta Faruƙ da yafi sauran zafi ya ƙunduma mata ashariya haɗe da yunƙurawa zai mare ta sannan ta karɓi takardar a tsorace. Lokaci ɗaya Jikinta ya ɗauki rawa, kamar wacce aka watsawa ruwan sanyi lokacin hunturu. Duk da bata buɗe takardar ta ga ko ta mece ce ba haka kawai jikinta ke bata babu alkhairi ko kaɗan tattare da wannan takarda. Yayanta Abubakar ne ya fara magana shi ma da nashi salon ɓacin ran. "Kin bani kunya Bintu. Na rantse da Allah ban taɓa tsammanin irin wannan munanan halayen daga gareki ba. Haba!! Sai kace wacce bata yi ilimin boko da Arabi ba? Ta ina kika taɓa ji mata ta fi uwa da ƴan'uwa? To bari in sake tuna miki, ana canja mata, amma ba a taɓa canja uwa da ƴan'uwa. Don haka kin ga yanzu ga sakamakon ƙoƙarin raba miji da danginsa nan kin karɓa, zai canja ki, amma bazai taɓa canja ƴan'uwansa ba. Dubi nan" Wayarsa ya buɗe ya lalubo hoton Invitation card ɗin Auren Hafiz da Karima ya matsa har kusa da inda take zaune tana rawar ɗari ya aje mata a cinyarta. Duk yadda ta so ta runtse idanu don kar ta karanta hoton I.V ɗin kasawa tayi, raɗau idanunta suka sauka akan hoton, cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa baƙaƙen ta karanta sunayen da ke manne a jikin hoton. Wata wawuyar bugawa zuciyarta ya yi, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara jan numfarfashi daƙyar, kuma sama-sama kamar mai cutar athma. Hannunta shi ya jagoranci umarnin zuciyarta gurin warware fallen takardar da ke damƙe a hannunta don ganin me ta ƙunsa. _".... Hafiz Aminu Faƙo na saki matata Fatima Bintu saki ɗaya..."_ Kalaman da suka manne a cikin idanun zuciyarta kenan, kuma kalaman da suka ƙara assasa hauhawar bugawar zuciyarta fiye da misali. A haukace, cikin ɗimuwa, gigita, ficewar hayyaci Bintu ta miƙe tsaye a zabure. Tayi taku ɗaya, biyu, uku, sai kuma ta zauna daɓas! Ta ɗaga idanu a gwalale ta kalli Ummansu da Aunty Sadiya. Sai kuma kamar tsikarin basir ta ƙwalla wani gigitaccen ihu! Sai kuma ta ɗauke Ɗif! Kamar an saka seletef an ɗaure mata baki. Da saurin gaske ta sake miƙewa tsaye, ta tattare siket ɗin jikinta za ta yanka da gudu Yayanta Aliyu da yake mata kallon wacce gigita yasa ta haukace yayi gaugawar damƙo kafaɗunta, da ƙarfin gaske ya girgiza kafaɗunta haɗe da ƙwalla kiran sunanta da ƙarfi. "Yaya... Hafiz... Ya sake ni... Na mutu..." Daga faɗin haka sai ta tafi luuuu ta kife a kafaɗunsa a sume. ******** Tabbas da gaske ne... A yayinda saki ya shiga tsakanin ma'aurata biyu wanda ya kasance bai da gaskiya shi zai fi jigatuwa. Irin haka ne ya kasance a ɓangaren Bintu. Shi kuwa Hafiz kwanakin da suka biyo baya harkokinsa yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Shirin aurensa yake yi a nutse, rashin Bintu a gidanma sai ya bashi damar cin karensa babu babbaka. Soyayya mai lasisi kuma irin ta bugawa a jarida suke sha shi da Karima, a gefe guda kuma Zulaikha tana ƙara ƙarfafa masa gwuiwa akan duk wasu shirye-shirye nasa. Sai a yanzu ne ya fahimci ma'anar karin maganar da Aunty Balira take yawan faɗa masa na *RANAR NAKA SAI NAKA...*, In banda Zulai ta kasance nasa ta ina ƙaramar yarinya kamar Zulai da ko haihuwa bata yi ba za ta karɓi yayen Aadil? Sai ga Hafiz duk yadda yake yawan faɗi a baya cewa Zulai ba ta da hankali yanzu ba shi da abokiyar shawarar da ya wuce Zulai. Tsarin yadda za'a fasalta gidansa a canja masa tsari, da yadda za'a fitar da gurin saukar baƙi ƴan'uwansa duk da ita yayi shawara. Haka ɓangaren haɗa kayan akwati, ba tare da jin zafin kuɗi ba haka ya dinga antaya mata manyan kuɗaɗe tana shiga kasuwa ita da Hibba da Karima suna haɗo kayan akwati. Ba tare da ƙyashi ba kuwa Zulai ta dinga zaɓo komai mai bala'in tsada, cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa mishi akwatuna guda goma sha biyu cif! Sai daga baya ne ma da Mummy ta ga kayan tayi faɗa kamar za ta ari baki. Ta rage kaya masu yawa har akwati biyu ta damƙa ma Zulaikha da cewar lallai ta aika ma Innaye da su Aunty Balira su samu na cin buki. Ko da Hafiz yaje gidan, Zulaikha ta faɗa mishi yadda aka yi kuma ta nuna mishi kayan ba ƙaramin kimar Mummy ne ya ƙaru a idanu da zuciyarsa ba. A ransa yake ji lallai yanzu ne fa zaiyi aure. Idan ya kalli Aadil kuwa farin ciki da nishaɗinsa ƙara ninkuwa yake yi. Duk yadda Bintu take ji tana gatanta yaron sai dai kawai ace ita ta haife shi, amma ko rantsuwa yayi babu kaffara an fi gatanta shi a gidan Mummy fiye da gurinta. Kuma wani abun burgewa shi ne yaron sam yanzu ba ya ƙwuiya, ga wani wayau da ƙiba, kyau na musamman da yaron ya ƙara. Ba shi gurin Mummy, ba shi gurin Karima, ba shi gurin Hajja, balle kuma Zulaikha da take riritasu shi da Imam kamar su kaɗai ne ƴaƴaye a duniya. ******** Tsawon sati biyu kenan da faruwar al'amarin amma Bintu ta kasa komawa dai-dai. Tun iyayenta suna hantarar ta, suna share al'amarinta, suna watsi da damuwarta, har sun zo sun fara tausaya mata. Amma a ɓoye, saboda dukkansu sun san irin matsanancin soyayyar da take ma Hafiz. Duk wanda yasan Bintu a baya, idan ya ganta yanzu abu na farko da za'a fara tambaya shi ne "Ta yi rashin lafiya ne?" Ƙara auren Hafiz, da sakin da yayi mata na bagatatan, wasu abubuwa ne da ko ana yaƙin duniya na uku a zamantakewar aurensu bata taɓa tsammanin za su gitta a tsakaninsu ba. Ta daɗe da gama sakankancewa Hafiz na ta ne ita kaɗai. Don ita kaɗai aka halicce shi kamar yadda aka halittota don shi kaɗai. Duk da tun kafin faruwar wannan al'amarin zamantakewar na su ya ɗan fara tangal-tangal sanadiyyar sakaci da kasa danne zuciyarta ita bata taɓa tsammanin zai iya kallon wata ƴa mace da idanun so balle har ya nemi sama mata sarari a filin zuciyarshi ba. Saki kuwa... Idan ta tuno wannan kalmar wasu sababbin hawaye ne ke sake ɓalle mata kamar an buɗe famfo. 'Ita Bintu Hafiz ya saka? Ita? Ita Bintu fa?' Zuciyarta na cika da tantamar anya kuwa Hafiz ne da kanshi ya iya sakinta? Ko dai wani mai baƙin ciki da aurensu ne ya shiga rigar Hafiz ya tafka wannan ƙatoton kuskuren? Sai ta yi kamar baza ta yarda da sakin ba kuma sai ta tuna ai ranar da abin ya faru ta ga ficewar Hafiz daga layinsu. Kuma wanda ya bata takardar sakin wani mai mutum ne mai muhimmanci a rayuwarta da bazai taɓa yi mata ƙarya don ya kassara ta ba. A cikin waɗannan kwanakin ƙunci da raɗaɗin, ta yi Allah ya isa ga Innaye da ƴaƴanta mata ya fi baki dubu!! Domin ita a ganinta duk su ne ummul-aba'isin faruwar waɗannan munanan al'amura a gareta. A karo na barkatai, ta yi juyi akan gadon, zuciyarta cike da ƙunci da matsanancin damuwa. Sannu a hankali ta

Chapter 34 of 40