suger, kafin a karya ake yin shi. Shi yasa za mu fita da wuri, don Allah ki bar maganar komawa mu tattali lafiyarki tukunna. Kin ga babu daɗi ace kin taho da ciwo kuma ki koma da ciwon ba tare da an samu sauƙi ba. Ki yi haƙuri don Allah, in Allah ya yarda baza'a sake samun matsala makamanciyar wacce aka samu yau ba."
Shiru Innaye tayi kamar baza ta amsa roƙon ba. Hafiz har ya buɗe baki zai cigaba da magiya daga inda Bintu ta tsaya sai ya ji Innaye ta ce
"Zuwa yaushe za'a gama duk gwaje-gwajen a bani magunguna?"
A tare duk su biyun suka yi magana. Hafiz cewa yayi
"Bazai wuce nan da wata biyu ba in Allah ya yarda."
Ita kuma Bintu cewa tayi
"Nan da kwanaki goma ma an gama komai Innaye."
Ba Innaye da mamaki ke neman sumar da ita a zaune ba, hatta Zulaikha sai da ta juyo da wani irin mamaki sosai a fuskarta tana ƙare musu kallo. Su kansu kallon junansu suke yi, irin kallon nan mai bayyana rashin jin daɗin yadda aka samu banbanci a maganganunsu, kuma a daidai gaɓar da ya kamata su haɗa baki gurin furta abu ɗaya.
Kallon baki kyauta min ba Hafiz ya jefa mata, sai kuma ya duƙar da kai a kunyace yana jin babu daɗi sosai a zuciyarsa.
Ko yana so ko baya so ya san Innaye da maganar Bintu za tayi amfani, tunda dai ita ce Likita. Amma Allah ya sani yana matuƙar son zama da mahaifiyarsa na ɗan lokaci, shi yasa ya faɗi maganar watanni biyu, domin a daidai wannan gaɓar da zaman gidansa ya sanewa Innaye a zuci ya san zancen lafiyarta ne kawai zai sa ta danni zuciyarta ta ƙara daɗewa yadda yake so.
Ita kuwa Bintu ko a jikinta, tana sane ta ce nan da kwanaki goma duk da kafin shigowarsu Hafiz ya nuna mata buƙatarshi na son mahaifiyarsa ta daɗe a gidan.
Amma tun a yanzu cikin sati ɗaya an fara samun irin wannan gagarumin matsalar ta ya za tayi saken da zamansu zai ƙara tsawo a gidan? Gaskiyar magana shi ne duk abinda za'a yi ma tsohuwar a asibiti bazai wuce kwanaki goman ba za'a gama komai. Don ma tun zuwansu bata yi himma akan komai na binciken lafiyar tata ba ai da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba. Da a gaggauce za ta haɗa mata duk magungunan da take buƙata su ƙara gaba, Umma ta gaida Assha. Ba'ayi wata halitta a duniya da za ta zo lokaci ɗaya ta dagula zaman lafiyar da ta ɗauki lokaci tana shimfiɗawa a gidan aurenta ba.
Aka ce abinda babba ya hango, yaro ko ya hau dutsen dala bazai taɓa hangowa ba. Duk su biyun Innaye ta fahimci inda suka sa gaba, hakan ne ma ya saka ta sakin wani ɗan taƙaitaccen murmushi.
"To shi kenan. Allah ya kaimu nan da kwanaki goman. Bayan nan ƙarin kwanaki huɗu za muyi in Allah ya yarda za mu koma inda muka fi wayau."
"Nan da sati biyu kacal Innaye?"
Hafiz ya tambayeta da sanyin murya.
"Eh! Nan da sati biyu idan Allah ya kaimu Hafizu. Zuwa lokacin ka ga satinmu uku kenan. To ina laifi? Ni da ka ɗauko ni da wayan bai fi in kwana huɗu ba ka mayar da ni gida ga shi yanzu zanyi har sati uku? Ai babu laifi ko?"
"Ƙwarai kuwa Innaye. Mun gode Allah ya ƙara lafiya."
Bintu ta faɗa a gaggauce.
Har ta miƙe za ta fice daga ɗakin ba tare da jiran komai ba karaf! Idanunta suka faɗa kan sababbin kulolin abincin Mijinta da ke ajiye gefe guda. Da mamaki sosai ta ƙara ware idanu tana kallon kulolin, eh tabbas su ne. Kulolin da duka-duka basu wuce sati uku da tayi Odarsu suka iso akan naira na gugan naira har dubu ɗari da ashirin ba.
Shi kan shi Hafiz da ya kasance miji mafi soyuwa a zuciyarta, wannan shi ne karo na biyu da ta zuba mishi abinci a cikin kulolin. Amma saboda tsabar rashin adalci da rashin sanin darajar abu mai tsananin tsada ya rasa inda zai kawo mata haɗaɗɗun kulolinta sai gurin tsohuwar baƙauyiyar Mamarsa da jahila fitsararriyar mara kunyar ƙanwarsa? Lokaci ɗaya idanunta suka cicciko da hawaye. A jere ta haɗiyi wasu kauraran miyau har daki biyu masu barazanar yaga mata maƙogwaro don tsabar baƙin ciki da takaici.
A haukace ta nufi gurin kulolin za ta ɗauka ta wuce da su sai jin muryar Zulaikha tayi a ladabce kamar ba ita ce ke yi mata magana a tsaitsaye ba tana cewa
"Aunty Bintu bamu ci abincin ba fa. Daman Yaya ne ya kawo ma Innaye to kuma zan zuba mata kenan kuka shigo. Kije kawai, idan mun gama zan kai miki kulolin kicin."
Duk yadda ta so daure ɓacin ran da ya cunkushe zuciyarta kasawa tayi. A fusace ta waiga ta aika ma da Zulaikha wani kakkausan kallo tana zazzaro idanu kamar za ta haɗiɗiyeta. Karaf! Akan idanun Innaye da Hafiz da tun da Zulaikha ta fara magana hankalinsu ya koma kan abinda yake faruwa. Ta buɗe baki za tayi magana a bazata wani ƙaƙƙarfan kuka ya taho mata, ba shiri ta fice daga ɗakin da sassarfa hannayenta biyu dafe da bakinta don kar ta fashe da kuka a gaban waɗanda take ma kallon maƙiya.
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu bayan ficewarta. Duk sun fahimci dalilin fusatarta tunda dai su ba yara bane. Amma tsakaninsu an rasa wanda zai fara cewa uffan! sai can bayan mintuna uku Innaye tayi ƙarfin halin cewa.
"Da ganin kulolinnan sababbi ne, kuma za suyi tsada sosai. Ko kusa basu yi kama da irin kular da aka saba zubo mana abinci a ciki ba. Me yasa ka ɗauko mata sababbin kuloli ka kawo mana abinci a ciki Hafizu?"
"Innaye... waɗannan kulolin fa da sunan nawa ta saye su. Saboda Allah menene aibu don na ɗauko kular abincina na kawo ma mahaifiyata?"
Ya ƙarasa da tambayar ƙarara fuskarsa na bayyana rashin jin daɗin canjin fuskar da matarsa ta nuna kan abinda bai taka kara ya karya ba.
"Uhmmmm!"
Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Muryarta na fita sannu a hankali ta cigaba da cewa
"Hafizu kenan. Baza ka gane abinda nake ƙoƙarin nusar da kai ba. Amma don Allah ina roƙonka daga yau, kar ka sake irin wannan. Tunda dai ana zubo mana abincin, duk ranar da ba'a kawo akan lokaci ba in sha Allah zan tura Auta ta ɗauko, tunda dai ta san kicin ɗin. Ta shi kaje can ɓangarenka ka huta. Kayi ƙoƙarin daidaitawa da matarka, kar ka kuskura wannan abin da ya faru ya janyo saɓani a tsakaninku."
"In sha Allah zan kiyaye Innaye."
Ya amsa shi ma tasa muryar na fita a sanyaye.
Har ya kama hanyar ficewa daga ɗakin ya waiga yana kallon Zulaikha, akayi arashi karaf suka haɗa idanu. A fakaice ya watsa mata harara.
"Kina ji na? Daga yau ki tabbatar kin kiyaye duk abinda zai kai ki can ɓangaren, idan kika sake shige ma Matata na rantse da Allah ba abinda zai hana ni goya mata baya ta zane ki ciki da bai."
Ko kusa bai yi kuskuren saka idanunsa a cikin na Innaye ba don ya san bazai sha da sauƙi ba. Fuuu ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama.
Kwaɓa-kwaɓa tayi da fuska tana kallon Innaye ta ce
"Innaye kina jin shi ko...?"
"Ƙyale shi Auta. Duk ranar da matarsa ta sake dukanki ba tare da kin mata komai ba ko ban gama karɓan maganin ba a wannan ranar za mu bar gidannan. Rabu da su, in Allah ya yarda munyi zuwan farko kuma na ƙarshe."
Ta ƙarasa maganar a raunane. Irin raunin nan da ke fita tun daga ƙarƙashin zuciya.
'Ba tun yau ba Ƴan'uwan Hafiz suka sha zuwa mata da ƙananun maganganu kan yadda ƙarara Bintu take nunawa a fili tana ƙyamarsu. Su da suka zo gidan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, zuwan farko ne kawai suka koma da daɗin rai. Na biyu da na uku duk labaran da suka koma mata da shi ba mai daɗi bane.
Kuma babban abin haushi da takaici shi ne duk irin abubuwan da take nunawa da wanda take yi a aikace Hafiz bai taɓa nuna ɓacin rai ko damuwarsa akan hakan ba.
Ita kuma da yake Dattijuwa ce ta gaske da aka shaide ta da tsananin haƙuri bata taɓa mayar da hankalinta ko ta saka ma ranta damuwa kan irin maganganun da suke yi ba. Zulaikha ita ce mai biye musu, tai ta ƙara ingiza su tana tuna musu irin abubuwan da Bintu ke nunawa wanda ƙarara duk mai hankali zai fahimci ƙyamarsu take yi.
"Ni fa shi yasa tun ranar farko da Yaya ya kawo ta sam! bata kwanta min arai ba..."
Da Zulaikha ta fara irin waɗannan maganganun a tsawace Innaye ke korarta daga ɗakin.
Su kuma Yayyin nan take za ta kwaɓe su ta nuna musu ɓacin ranta. Kamar dai abubuwan basu taɓa damunta ba. Duk abinda ke faruwa idan Bintu taje can kawar da kai take yi tayi kamar bata gani ba kuma bata damu ba, sai dai ma tayi ta bin Bintun da murmushi a matsayinta na matar shalelenta Hafizu.
Kamar misalin rashin shan ruwan ɗakinta da Bintu ke yi. Kuma duk tsaftar dadduma ko sabuntar tabarma idan tasa aka shimfiɗa mata da umarnin ta zauna ba ta taɓa zama sai ta ɗauko wani sabon dadduma daga mota ta shimfiɗa sannan za ta zauna tana yamutsa baki a fakaice, domin sam ba ta hawa kan kujerunta da suka fara kwana biyu.
Duk da ginin gidansu da ɗakunan gidan yana daga cikin gini mafiya kyawawan gini na bulo da bulo a ƙauyen, saboda Hafiz ya sa an gyara gidan sosai. Kuma ya gyara mata ɗakunanta ya zuba mata sabbin kayan ɗaki irin dai na tsofaffi masu gata. Bintu ta dinga kalle-kalle kenan tana ɓata fuska, alamun dai komai bai mata yadda take so ba.
Ruwan sha, abinci, kayan ciye-ciye dangin ƙwalam da maƙulashe da Bintu za ta buƙata na ƴan awannin da za tayi a ƙauyensu duk da abinta take tafiya a cikin mota.
Wani tozarci da wulaƙanci da tayi musu da yasa ta ƙara ficewa a zuciyarsu wanda har yau sun kasa mantawa shi ne haihuwar Aunty Balira tayi. Da rawar jiki Hafiz ya ɗauki Bintu suka je har gidan Yayar tasa barka. Aunty Balirar ita ce babbar ƴa a ɗakin Innaye. Shekarunta ashirin da aure Allah bai ba ta haihuwa ba sai a wannan lokacin. Shi yasa duk wani makusancinsu yake ɗokin haihuwar, saboda abu ne da aka daɗe ana nema har an fidda rai sai ga rabon ya samu.
Ko da suka isa, sai suka tarar yaron yayi kashi, an cire mishi nafkin ana wanke mishi kashin a cikin baho nan tsakar ɗakin. Da saurin gaske Bintu ta sake gyara zaman face mask ɗin da ke hancinta. Ta sake tamke fuska tamau, ta kawar da kai tana shan ƙamshi. Daga irin zaman da tayi ɗofane a bakin kujera kamar wacce ke kan ƙaya za'a gane a takure take ƙwarai. Shi kanshi zaman, kafin tayi sai da Hafiz ya bata umarnin ta zauna mana, fuskarsa babu walwala ko misƙala zarrah. Shi yasa ta zauna tana jin babu daɗi a ranta, a zuciyarta take ta addu'ar Allah yasa kar ta kwashi kuɗin cizo ko ƴan matan kaduna a jikin kujerar.
Da rawar jiki Ladidi wacce Hafiz yake bi ta gama wanke ma jariri kashi, aka naɗe ɗuwawunshi da sabon fallen zani aka miƙa ma Bintu. Da farko kamar ba za ta karɓe shi ba, ko tunanin me tayi? Oho!
Sai ta buɗe jakarta ta zaro safar hannu ta saka sannan ta karɓi jaririn a wulaƙance. Irin wasa-reren riƙonnan da ko jikinta bata yarda jinjirin ya taɓa ba.
Kamar za ta yar da shi, daga ƙarshe dai cikin sauri Hafiz ya karɓi ɗan yana mata tsiyar a matsayinta na babbar likita bata iya ɗaukar jariri ba, zai ga wanda zai dinga ɗaukar mata nata idan ta haifa.
"Dear! Ka san jaririn da zan haifa zai kasance dabanne da duk wasu jarirai da ka taɓa gani a rayuwarka. Ko shugaban ƙasar Sa'udiyya ne ba zaiyi ƙyamar taɓa ɗana ba saboda tsananin kyawu da tsaftar jikinsa da na muhallin da muke ciki."
Amsar da ta bashi kenan a gaban kowa ba tare da damuwar maganar za ta ma ƴan'uwansa daɗi ko akasin haka ba.
Kamar bai ji abinda ta ce ba, haka Hafiz ya nuna, sai ma ya ƙara mayar da hankali kan addu'o'in da yake karantawa ƙasa-ƙasa yana tofa ma jaririn.
Aunty Rakiya da ta kasance mara haƙuri daga cikin ƴan'uwansa, har ta buɗe baki za ta ba Bintu amsa da sauri Aunty Balira ta mintsine ta. A dole tayi shiru ba don ranta yana so ba sai don bin umarnin na gaba.
Ko da suka tashi tafiya, dubu ashirin ɗin da ta ajiye da cewa a siya ma jariri pampers babu wanda ya ce uffan! Balle tasa ran samun godiya kamar yadda suka saba yi mata sadda take amarya jikinsu na ɓare-ɓare idan tayi musu alkhairi, kamar ba yayyen mijinta ba.
Ko da suka ba Innaye labarin, bata nuna ɓacin ranta ba sai haƙuri da ta basu da kalamai na kwantar da hankali. A ƙarshe ta ɓuge da nunar musu da illar miƙa ma Bintu jaririn ba tare da sun sake yi mishi nafkin ba.
"Ku kalli irin suturun da take sakawa a jikinta mana? So kuke yaron yayi mata fitsari a jiki? Idan yayi mata fitsari duk cikin kayan sakawarku kuna da kwatan-kwacin wanda za ku bata ta saka a jikinta?
Haka dai ta kore maganar ba tare da ta nuna musu ta ji babu daɗi kan abinda ya faru ba.
Ko da suka ce mata sun yanke zuwa gidan ɗan'uwan nasu idan ba da wani ƙwaƙƙwaran dalili na dolen-dole ba bata takura su da cewar su cigaba da zuwa ba.
"Daman in banda da abinku, jelar tafiya daga nan Faƙo, zuwa Kaduna, a sake hawa mota zuwa Abuja ai ba nan kusa bane. Ku ɗaga ƙafan ya fi, tunda dai Allah ya sa shi Hafizun yana ƙoƙarin zuwa akai-akai ai babu laifi. Idan kuma wata buƙata ce ta gaggawa kuke da ita sai ku tuntuɓe shi a wayar zamaninnan da ta samar ma talaka sauƙi. Da katin naira ɗari za ku isar da saƙon da idan zuwa za kuyi sai kun kashe kuɗin mota fiye da dubu biyar."
Da waɗannan zantukan ta sake ƙarfafa musu gwuiwar janye ma zuwa gidan Hafizu akai-akai.
Da gaskiyar Bahaushe da yace gani ya kori ji. Kwanaki uku na farkon zuwanta gidan a cikinsu kawai za ta ƙaras da marari da ɗokin ganinta a wajen matar gidan. A bayan waɗannan kwanaki uku, duk abubuwan da suka biyo baya haƙuri kawai take yi tana kawar da kai.
Zulaikha da ta kasance mara haƙuri kamar fitar zawayi kuma tun dama can ba'a shan inuwa ɗaya da matar Hafizun ita take ta cika tana batsewa kan abubuwan da suke gani na rashin kyautawa. Har zuwa yau da tayi gaban kanta ba tare da saninta ba ganin har ƙarfe huɗu na yamma ba'a kawo musu abinci ba tun bayan karin safe, ta shiga har can cikin gidan har wannan abun ya faru.'
"Auta?"
Ta kira sunan Zulaikha bayan ta katse tunanin da take yi ta mayar da hankalinta kanta.
"Na'am Innaye."
Ta amsa tana cigaba da zuba farfesun naman kaza kan soyayyar shinkafar da ta zuba cike dam da faranti.
"Kin ga matar gidannan? Ki fita daga harkar ta. Duk abinda take yi kanta take ma. Roƙo na gare ki don Allah don Annabi ki lallaɓa ki kawar da kai kamar yadda Yayyenki suka yi a kanta har mu koma can inda muka fi wayau ba tare da mun janyo ma kanmu abin magana ba. Ko so kike a fara ya-maɗiɗi da mu a jakar magori ana cewa Uwar miji da ƙanwar miji sun zo daga ƙauye sun zama sanadiyyar mutuwar aure?"
"To ayi mana Innaye. Wa yake tsoron a mutu? Saboda Allah irin abubuwan da matar gidannan take yi mana ita tana kyautawa kenan? Ki duba fa yadda take ɗaukarmu a wulaƙance. Shi Yaya haka yake ma Iyayenta da ƴan'uwanta? Innaye ko kin san har yau ban kai matsayin da matar nan za ta dinga kiran sunana kai tsaye ba sai dai ta ce min Ke jahila, ko ke baƙauyiya, ko ke dabba? Saboda Allah Innaye don Allah yasa an haife ta a cikin babban birni Abuja ni an haife ni a ƙauyen-ƙayau Faƙo sai ta dinga tozarta ni tana wulaƙanta ni? Na rantse da Allah idan su Aunty Rakiya sunyi haƙuri da ita ni kam bazanyi ba, daga yanzu bazan sake ɗaga mata ƙafa ba. Tunda dai ita ba ta da mutunci. Sai dai duk abinda zai faru ya faru."
Ta ƙarasa maganar idanunta ciccike da hawaye na gaske ba na taɓara ba kamar yadda take yi a mafiyawancin lokuta. Gefen hijabin jikinta ta kama ta fara sharar ƙwallah, da alamun tozartata da Bintu take yawan yi ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya.
Ita kuwa Innaye shiru tayi, ta rasa ta cewa. Zuciyarta cunkushe da matsanancin damuwa, domin sai a yanzu da ta ƙara karantar halayen Bintu duk wasu maganganu da ƴaƴanta suka sha faɗa na ƙorafi a baya ke dawo mata daki-daki a cikin zuciyarta. Kamar dai a lokacin abubuwan suke faruwa.
Daƙyar ta iya yakice tunanin da take yi ta fara rarrashin Zulaikha da hawaye suka kasa tsayawa a idanunta, tana sharce wasu suna sake gangarowa.
Duk ƙamshi da kyawun abincin a idanun Zulaikha ta kasa yi mishi mugun ci kamar yadda ta ƙudurtawa zuciyarta da farko. Daga ita har Innaye tsakuran abincin suka yi. Da gangar ta ƙi mayar da kulolin ko bayan sun gama cin abincin.
"Ko na mayar ma ba ci za suyi ba. Wata ƙila zubarwa za tayi saboda ƴan ƙauye sun ɗiba sun rage. Da tayi wannan almubazzarancin kuwa gara mu ajiye da daddare mu ci, abinda ya rage da safe mu ƙarasa cinyewa sai in mayar mata da kulolin da take ta sauke zafafan numfarfashi kamar za ta haɗiyi zuciya a kansu."
"Ko da safen ma ai sai dai ke ki ci. Kin manta ta ce gobe za ta kaini asibiti da safe kafin in ci komai ayi min gwaji?"
Innaye ta faɗa hankalinta na kan Zulaikha da take sakacen haƙorinta da tsinken-tsinyiya.
"Allah ya kaimu goben. Sai kiyi ƙoƙari ki cika cikinki dam anjima da daddare, tunda goben bamu san iya wane lokaci za ki ɗauka kafin ki karya ba. Ai wallahi gara dai a gama komai na asibitin nan a baki magunguna mu koma gida. Da birnin da komai na cikinsa Wallahi sun gundure ni, ƙauyen nan dai da take yiwa kallon banza da ƙyama ni shi ne abin alfaharina. A guri na ya fi Abuja sau miliyan ɗari."
6)
Shi ba yaro bane. Ya san ya kamata ya tuhumi Bintu akan abubuwa da dama da take yi ma ƴan'uwansa da mahaifiyarsa. Abubuwan da tun tana yi a fakaice ba ya lura, a yanzu gaba-gaɗi take aikatawa ba tare da shakkar idanunshi ba. Kawai yana yi mata uzuri ne saboda dalilai mabanbanta da shi kaɗai ya barwa zuciyarsa.
Marin da tayi ma Zulaikha ba abinda ya shafe shi bane, saboda ya san halinta kamar yunwar cikinsa. Ba Bintu da take matsayin matarsa ba, ko shi Zulai ta daɗe tana shiga mishi hanci da ƙudundune, aduk sa'adda yayi yunƙurin fyatota sai Innaye ta taka mishi burki. Da wannan dalilin yasa ba ƙaramin farin ciki yayi ba da Bintu ta tsinkawa Zulaikha mari, a ganinsa, hakan zai rage kaifin rainin yarinyar a gare shi da matarsa.
Amma duk da haka, ya san ya kamata yayi ma Bintu ƙwaƙƙwaran tuhuma akan sakaci da abincin mahaifiyarsa. Ya kamata ya tuhume ta akan yadda ya faɗa mata yana so mahaifiyarsa tayi watanni a gidan, amma taƙi yi ma Innaye dabarar cewa binciken lafiyarta zai ɗauki lokaci mai tsawo. Ya kamata ya tuhume ta akan yadda ta nuna ɓacin ranta don kawai ya ɗauki kulolin abincinsa da abincin ciki ya kaiwa mahaifiyarsa... Tuhume-tuhumen suna da yawa, amma a yanzu dai, waɗannan su ne abubuwan da suka faru akan gaɓa. Saboda shi ɗin ba mutum ne da ya cika riƙe abubuwan da za su janyo mishi jin babu daɗi a zuciyarsa ba.
Ko da ya shiga cikin falonsu, zuciyarsa cike take da niyyar zai yima Bintu waɗancan tuhume-tuhumen. Amma yana yin tozali da ita zaune akan kujera tana sharar ƙwallah. Sai yaji duk abinda ya ƙullo a ransa ya bi rariya da gudu ya wuce, babu abinda ke gaban idanunsa da zuciyarsa sai Bintu da damuwar da ya saka ta kuka. Wani abu da bai taɓa gani ba tun da suka zama mallakin juna tsawon shekaru biyu.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Sweetheart? Subhanallahi! Me ya faru? Wa ya rasu?"
Ya jera mata tambayoyin hankalinsa a tashe ainun. Da sassarfa ya ƙarasa kusa da ita, sannan yasa hannuwa biyu ya tattagota zuwa jikinsa gaba ɗaya ya ruƙunƙume yana sake jera mata tambayar me yake faruwa? Waye ya rasu? Domin duk a tsammaninsa rasuwa kaɗai rasuwar ma na makusanci sosai shi zai sa Bintu zama tana risgar kuka.
Sai dai wani abu da ya sake ɗaga mai hankali zuwa ƙololuwar tashi duk irin maganganu da tambayoyin da yake mata bata amsa shi ba. Hallau kuma bata tsayar da kukan ba. A yadda yake ji, kamar ya ɗora hannu biyu aka ya fara rusa ihu. Kawai sai ya fara tattaɓa jikinta da tunanin ko ba ta da lafiya ne?
Yanayin jikin na ta daidai ne, babu zafi ko kaɗan. Don haka ya kawar da tunanin ko rashin lafiya ke damunta. Can-cak ya ɗauke ta kamar jaririya ya nufi cikin ɗakinsa, ba tare da ya san taka-maimai abinda zaiyi mata ya tsayar da kukan da take yi kuma ya kore mata damuwar zuciyarta ba.
Kamar ɗanyen ƙwai sabon sakawa, haka ya ajiye ta sannu a hankali akan faffaɗan gadonsa ƙirar italiya da ya mamayi fiye da rabin ɗakin. Maɓallan rigar jikinsa ya fara cirewa sauri-sauri har ya zare rigar daga jikinsa. Kan gadon ya koma, jikinsa babu inda ba ya rawa ya sake tarairayota zuwa jikinsa, baiyi wata-wata ba ya haɗe bakinsu waje guda, hannayensa biyu tallabe da fuskarta, ya saka idanunsa cikin nata yana aika mata da wasu zafafan saƙonni waɗanda ita kaɗai za ta iya fassarawa.
Tun tana mutsu-mutsun ƙwacewa har ta bada kai bori ya hau. Tun hawayen suna sauka da gudu, har suka koma sauka sannu a hankali, daga bisani ma suka tsaya da zuba, sai ajiyar zuciya take saukewa akai-akai. Bai saki fuskarta ba sai da ya tabbatar jikinta ya mutu murus, sannan ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa yalwataccen gashin kanta da yake fitar da daddaɗan ƙamshi.
"Wa ya taɓa min zuciyata?"
"Kai ne!"
Ta amsa mishi ba zato ba tsammani da wata siririyar murya mai ɗaukar hankali.
"Ni kuma? Me nayi?"
Ya sake jefa mata tambayoyin yana ɗan ware idanunsa kaɗan, alamun amsar na ta ya bashi mamaki ƙwarai da gaske.
A karo na barkatai ta sake jan nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Shiru tayi kamar baza ta amsa shi ba, a zuciyarta take ta jujjuya maganganun da za ta karanta mishi ba tare da ya zarge ta da ƙyamar mahaifiyarsa ba.
"Ina jin ki Sweetheart! Faɗa min laifin me nayi miki da har yasa kika zauna tsawon lokaci haka kina sharɓan kuka. Abinda bai taɓa faruwa ba a tarihin zamantakewar aurenmu. Abu ɗaya dai da nake so ki dinga tunawa ako da yaushe shi ne, Hafiz, mutum ne mai tsananin ƙaunar matarsa Bintu. Da gangar bazai taɓa yin abinda zai taɓa zuciyarta ba. Kina sane da haka ko?"
A hankali ta ɗaga mishi kai alamar ta sani. Cire kanta tayi daga ƙirjinsa, ta ɗaga fuskarta tana kallon tasa. Sannu a hankali ta saka idanunta da suka canja launi saboda kuka a cikin nasa idanun. Ta riƙo hannayensa biyu a cikin na ta, sannan ta buɗe tsukakken bakinta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 40