Share this page
gabansu, abinda tayin ya taka muhimmiyar rawa gurin rage girman ɓacin ransu. Hatta su Aunty Rakiya da suke ta cika suna batsewa abinda Aunty Sadiyar tayi ya tsaya musu arai. Ga dai maganganun da suke burin sake gargasa ma Bintu da ƙarara ya nuna ta basu haƙuri don babu yadda za tayi ne, amma kwarjinin Aunty Sadiya yasa dole suka haɗiye komai a ransu. Godiya kawai Aunty Balira tayi ma Aunty Sadiya ba tare da ta amsa roƙonta na su yafe ma Bintu sannan kar su faɗa ma Hafiz abinda ya faru ba. Ficewa tayi daga falon ƙannenta suka rufa mata baya. Suna hanyar komawa ɓangaren da aka sauke su babu abinda Aunty Balira take yi sai sharar hawaye. Daman tun farko abinda ta guda kenan, sanin halin Bintu na wulakanci da daukarsu da take yi a banzan-banza yasa sam bata so zuwa sunan ba balle har wasu su ce za su biyo su. Daman ta sani, in dai Bintu ne dole sai ta aikata mummunan abinda zai haska ma sauran dangi yadda ta ɗauke su gaba ɗaya a marasa daraja. Yanzu zuwan na su me ya haifar kenan? Duk da sauran ƴan'uwan basu yi magana ba ta sani dole sun dasa ma zukatansu ayar tambaya. Abincin karin da aka kai musu da safe ragowar ne aka ba yara zuwa ƙarfe ɗaya da rabi na rana. Zuwa ƙarfe biyu da rabi, uku manyan gaba ɗaya idanunsu ya fara raina fata. Da kunnenta taji yadda suke ƙananan maganganu kan yunwa suke ji. Haka ta kwashi kulolin abincin safe da aka kai musu waɗanda ana gama cinye abincin ciki aka wanke ta fita can tsakar gidan tayi shiru cikin tunani da damuwa. Kwatsam sai Allah ya dawo da Mal Musa gidan bayan ya dawo daga kai mutane can gurin taron suna. Da mamaki yake tambayarta su baza su gurin taron sunan bane? "Ai ba ma wannan ba Mal Musa. Yanzu dai ina za ka samo mana abincin sayarwa kuma mai sauƙi da gaggawa? Kasan da yara a cikinmu, sun cinye abincin da aka bamu tas! Yanzu yunwa muke ji kuma matar gidan ba ta nan." Da farko shiru yayi, zuciyarsa cike da tunani. Duk yadda Aunty Balira tayi ma zancen kwaskwarima nan take ya harbo jirgin abinda yake faruwa, domin ya san halin Bintu sarai, ko su ma'aikatan gidan ba wani daɗinta suke ji ba. Da yawansu ma in ba don kirkin Oga Hafiz da girmama na gaba ba da tuni sun ajiye aikin. "Abinci bazaiyi wuyar samuwa ba Aunty Balira. Sai dai kin san nan Abuja ne, komai yana tsada ba kaman can gurarenku ba. Na nawa ne za'a siyo muku abincin?" Ɗan shiru tayi tana sake kallon girman babban kulan da take riƙe da shi. Sai kuma ta ce "Abincin dubu goma zai cika wannan kular ba?" Duk yadda yaso hana kanshi dariya sai da ya ɗan ƙyaƙyata kafin ya amsa da "Ai abinci garau-garau na dubu talatin ma bana jin zai cika kular nan. Abuja ne nan fa Aunty, Sai dai kawai aje a siyo na yadda ya samu kuyi maneji." Kuɗin gudummuwar da suka tara ma Hafiz da bai karɓa jiya ba ya ce ta ajiye mishi zuwa safe gaba ɗaya ta miƙa ma Mal Musa. "Ga lambar wayata, don Allah idan ka siyo ka kawo min a sirrance. Ka kira ni nan zan fito in karɓa." Wannan abinci da aka siyo musu, shi ya rufa musu asirin yunwar da Bintu ta barsu da shi da rana har zuwa dare. Da daddaren ma gajiya sukai da kukan ƙananun yara ta kira Rakiya da Ladidi suka shiga can cikin gidan gurin Bintu, shi ne fa har aka yi wannan ɓatacciyar. ***** ***** Kamar yadda Aunty Sadiya ta alƙawarta musu, cikin ƙanƙanin lokaci aka wadata su da lafiyayyar dafadukar macakaroni da taji kifin gwangwani. Bayan ruwan gora da aka kai musu har katan huɗu, katan shida aka kai musu na kalolin lemuka mabanbanta. Duk yadda ƙamshin abincin ya gama baɗe falon da suke ciki daga buɗe kular, ko kusa su Aunty Balira basu matsa gurin ba balle har su nuna sha'awar son ci kamar yadda sauran suke nunawa a fili. Gwaggo Asabe, uwargidan Baba Abubakar ita ta jagoranci rabon abincin da ya ishi kowa a wadace, har suka bar saura a kula. Hatta waɗanda suka fara barci duk an tashe su sun wanko baki sun fara cin abinci, duk da a lokacin ƙarfe goma sha ɗaya na dare ta gota da ƴan mintuna. Gwaggo Asabe ita ta ɗauki na su Aunty Balira ta kai musu har inda suke zazzaune sun buga tagumi. Ajiye musu tayi, sannan ta koma ta ɗauko nata abincin ta zauna a gefensu. "Rayuwar duniya haƙuri ake yi ƴaƴan nan, ko baku faɗa ba, da yawanmu a cikin nan mun san abinda yake damunku kuma yake ci muku tuwo a ƙwarya. To amma ya za kuyi? Su fa wasu ƴan binnin haka suke, sai dai mu cigaba da haƙuri da mayar da komai ba komai ba a matsayinmu na waɗanda Allah ya ƙaddara ma rayuwa a ƙauye. Don Allah ku ci abinci, idan kun yi haƙuri, duk gobe za mu koma inda muka fi wayau. Sannan ina mai baku shawara, kar ku kuskura ku bari matar ɗan'uwanku ta shiga tsakanin kyakkyawan zumuncinku, tunda dai shi ba haka yake muku ba." Cokali ta ciko taf da Macaroni da tunda ta fara magana ƙamshinshi yake baɗaɗe mata hanci ta cusa a baki. "Kuma..." Ta cigaba da magana tana shishita da baki saboda zafi da daɗin macaroni da ya haɗe mata guri ɗaya, amma tsabar yadda maganar ke cin ranta ta kasa haƙuri ta gama haɗiye abincin da ke bakinta. "Imu-imu... manya da muka zo sunan nan... munyi shawara a tsakaninmu ko mun koma gida baza mu taɓa bada labarin abinda matar Hafizu tayi mana ba. Domin Hafizu shi ne namu, daga gare shi kuwa bamu fuskanci wulaƙanci ko kaɗan ba. Kun ga don abinda matarsa tayi mana ai sai muyi mishi uzuri. Abinda ya rage muku dai ku kwaɓi bakunan ƙannenku, don idan mu manya munyi shiru ba lallai su suyi shiru da bakunansu ba. Musamman ma da ya kasance gaba ɗayanku ba ƴan ɗaki ɗaya bane." Daga haka bata sake cewa komai ba ta mayar da hankali kan abincinta ta cigaba da saka loma, a hanzarce, kamar mai tsoron wata a cikinsu za ta cinye nata ta ce ta ƙara mata. [1/7, 10:17 PM] Fareeda Abdallah: Wannan zazzafan abinci kuma daddaɗa, da duk loma ɗaya sai an haɗa da kifin gwangwani da aka dafo musu a ƙarshen dare, ga Lemu da ruwan gora a wadace, shi ya goge duk yinin da suka yi suna ɗame-ɗame da yunwa. Kamar dai ba su bane a ɗazu duk basa cikin walwala da karsashi, lokaci ɗaya hira ta game falon, sai shewa suke suna dararraku a tsakaninsu. Su Aunty Balira kuwa duk da maganganun da Gwaggwo Asabe tayi musu tsattsakuran abincin kawai suka yi, duk dadinsa da d'andanon da yake fitarwa kamar mad'aci haka suke jin sa a bakunansu, ba don komai ba kuwa sai don yadda zukatansu babu dad'i. Ko da suka gama ba tare da sun tankawa kowa ba suka bar gurin zuwa makwancinsu. Sai da tasa haƙarƙarinta akan katifa, ta ciro wayarta a cikin ƴar pose, sannan taga kiran da aka rasa na Hafizu har guda biyar. Ta rasa dalilin da yasa haka kawai ta ji baza ta iya magana da shi a daren ba, a taƙaice ma tausayinsa ne ya cika mata zuciya. Wannan fa shi ne misalin karin maganar nan ta bahaushe da yake cewa "Ga doki har doki amma ƙafar na sakaina." Hafizu yaron arziki, ɗan albarka mai son zumunci da ƙaunar iyaye da ƴan'uwansa. Amma sam baiyi sa'ar matar aure ba. Mace ta gari kuwa ga duk namijin da ya same ta an bashi rabin addininsa ne in ji fiyayyen Halitta SAW, sai ya ji tsoron Allah a sauran rabin. 'Ko yaushe rayuwar iyalin Hafizu za ta saisaitu?' Ta tambayi kanta da kanta. Domin Bintu dai in dai ba wani iko na Allah ba bata ga alamar canji a gurinta ba, yadda ta san halayenta tana amarya, a yanzu ma babu wani canji sai ma abinda ya karu. Ga kuma masifaffen so da suka san Hafizu yana yi mata, balle su saka ran kila acan gaba ya dauki kwakkwaran matakin gyara, ko kuma yayi hobbasa ya kara aure ko zai dace da wacce za ta kaunace shi don Allah kuma ta kaunaci 'yanuwansa a yadda suke. "Uhmmm! Allah kai ka san karatun kurma." Ta fada a fili da murya kasa-kasa. Sai kuma tunanin Innaye ya fado mata arai. 'Baiwar Allah' Ta fada a zuciya. Ita ta san ko Innaye bata fada ba sanin mugayen halayen Bintu ne yasa tunda suka iso akai-akai take kiranta don jin ba wata damuwa ko? Ita dai bata ce mata komai ba don gudun kar ta daga mata hankali. Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke. Ta danna maɓallin kashe wayar ta kashe gaba ɗaya don ma kar ya sake kiranta, gobe idan ya dawo sa hadu. Sannan a yadda ta yanke shawara, ita dai da bakinta baza ta yi ma kannenta da suke uba daya magana a kan kar su bada labarin abinda matar Hafizu tayi musu ba. Shi da ya gayyaci azo mishi suna, har yana daukar shatar motoci, bayan ya san halin matarsa sarai ba kaunar 'yanuwanshi take yi ba. Shi ya kira ma kansa tonon asiri a cikin dangi. Lumshe idanunta tayi ta fara karanto addu'ar kwanciya barci. 'Yan'uwanta ma da suke kwance kowa da irin tunanin da take yi a zuciyarta, daga karshe ko sai da safe basu iya yima juna kamar yadda suka saba ba. Barci ya dauke su a mabanbantan lokuta. ****** Washe gari duk yadda yaso su dawo Abuja da safe basu samu isowa ba sai misalin sha biyu ds kwata na rana. Daga filin jirgi kuma kai tsaye Ma'aikatarsu aka wuce da su, hankalinsa duk ba'a kwance ba, saboda har lokacin bai samu yayi magana da Aunty Balira ba. Sauran yan'uwansa kuma da yake ta kira akai-akai yana tambayar lafiyarsu duk sun tabbatar mishi lafiya kalau suke. Ko da ya bukaci a bashi Aunty Balira a waya ya kasa samunta sai suke ta bashi uzurirrika mabanbanta, wadanda sam basu kwanta mishi arai ba. Ya rasa dalilin da yasa, haka kawai zuciyarsa ta ki nutsuwa guri daya. A bangaren Bintu ma suna ta waya cikin kulawa da kaunar juna kamar yadda suka saba, ko da ya tambayeta lafiyar yan'uwan nashi da yadda suka kwana sake tabbatar mishi tayi suna cikin koshin lafiya. "Na je da Baby Aadil mun gaisa da su da safe. Ya dade ma a goye bayan Aunty Balira." Ta yanko karya ta gilla mishi duk don ta sake kankaro ma kanta girma a gurinshi, sannan ta cigaba da cewa "Kuma tun da sassafe Aunty Sadiya ta jagoranci aikin wadataccen abin karyawa aka kai musu. Yanzu haka kiris ya rage a gama abincin rana da soya naman suna a mika musu, tunda sun ce baza su sake kwana ba yau za su koma gida. Dazu da Raudha za ta shigo ma take ce min ta ga direbobin da suka kawo su sun iso." Da matukar murna da jin dad'i a muryarsa yake mata godiya da saka albarka. "Shi yasa a kullum nake kara son ki Bintuna, Allah ya barmu tare. Sai na dawo. A shafa min kan Babana." Da haka suka yi sallama bayan ta mayar mishi da martanin zakakan kalaman soyayya. Dakyar ya yakice ayyukan komai ya isa gidan misalin karfe biyu saura kwata na rana. Kuma kamar yadda Bintu ta sanar da shi, ya tarar da abinci waja-waja a gurin yan'uwansa, alamun suna cikin alkhairi dumu-damu. Sun ci, sun koshi, sunyi hani'an, ga kasusuwan naman kaji nan a cikin farantan abincin da suka gama ci, babbar alamar da ke nuna ba'a basu abinci lami ba. Ya tarar duk sun gama shiryawa, jakunkunan kayansu da wadanda suka kullo a leda duk suna ajiye a falo. Da alamun dai shi kadai suke jiran dawowarsa. Musayar murmushi ne ya gudana tsakaninsa da Aunty Balira bayan 'yan'uwan sub gama jerangiya wajen yi mishi sannu da zuwa. Shi kuma ya bi Innoni da Gwaggwagganninsu daya bayan daya ya gaishe su. Ficewa yayi, Aunty Balira ta rufa mishi baya suka kebe can gefe guda. "Ya hanya? Fatan an dace da abinda aka je nema?" "Alhamdulillahi Aunty. Me ya samu wayarki? Ina ta kira ba ta shiga, kuma na kira su Aunty Ladidi su had'a mu a waya suna ta bani wasu kalar amso shi..." "Wayata batir ke da matsala." Ta katse shi tun kafin ya gama korafin. "Sai mun koma gida in Allah ya yarda zanyi kokari in canja batirin." "A'a ba sai kun koma gida ba. Idan na shiga ciki akwai wata karamar waya Torching screen zan dauko miki sai ki saka layinki ki ci gaba da amfani da ita." "Menene Tochan scrub?" Ta tambaye shi da yanayin kauyanci. Kafin ya amsa sai ta sake cewa "Ohoo! ko kana nufin waya 'yar sha-fa? Idan ban manta ba kamar ita naji Zulai na cewa tochan scrub." Sai kuma tayi dariya ta cigaba da cewa "Ina ni ina waya 'yar sha-fa Hafizu? Barni dai da mai maballai na. Na fi gane amfani da ita a saukake. Waya 'yar sha-fa a k'auye hannun mata sai irin su Zulai da suka yi boko, idan kuma za ka bani in tafi mata da shi to?" "Ko ke ma za ki iya amfani da ita Aunty Balira. Kun ki karbar canjin da zamani yazo da shi shi yasa har yanzu kuke a guri daya. Ni ke nayi niyyar ba wayar ba Zulai ba. A sannu za ki saba amfani da ita." "To shi kenan. Na gode Allah ya kara arziki." Da murmushi a fuskarsa ya amsa addu'ar da tayi mishi cikin jin dad'i. Har yayi mata sallama kan cewa zai shiga cikin gidan sai ya fito ya sallame su ta ce to. Ya fara tafiya sai ta kira sunanshi "Hafizu?" "Na'am Aunty. In zo ne?" Ya fada a ladabce. Girmanta yake gani ba kadan ba, domin idan babu Innaye a guri tudu biyu Balira ke ci a gurinsa, Uwa kuma babbar Yaya. "Kayi hakuri. Kudin gudummuwar da muka kawo maka na ara, idan mun koma gida zan sayar da tunkiya sai in ba Innaye ta ajiye maka kudin..." "Na bar miki halak-malak Aunty." Ya katse ta da murmushi a fuskarsa. Martanin murmushinsa ta mayar masa tayi godiya, tana tsaye a gurin tana kallonsa har ya bace ma ganinta. Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke kafin ta koma cikin dakunan da aka yi musu masauki. ****** "Wai me yasa a hotunan taron suna da kika tura min jiya ko daya ban ga hoton su Aunty Balira ba?" Kasancewar tambayar tazo mata a bazata ne, kiris ya rage ta fad'ar da Aadil da yake rike a hannunta tana kokarin saka mishi nono a baki. Da saurin gaske ta rik'o shi, idanunta a kasa ta ce a daburce. "Iye! Na'am! Me ka ce Sweetheart?" Da yake hankalinshi na kan turaren da yake fesawa a jikinsa, sam bai ga yanayin rud'anin da ta shiga ba. A nutse ya sake maimaita mata tambayar da yayi mata. "Uhmmm!" Ta fara jan ajiyar zuciya ta sauke, a zuciyarta take ƙara tsara abinda za ta fada mishi ya gamsu. "Ka san halin su Aunty Balira fa, wai ganin a cikinsu da dattijai da ƙananun yara yasa ta ce kawai ba sai sun je can ba, za suyi taronsu a gida. Da wannan dalilin yasa aka bar musu komai a wadace muka tafi. Ga kyaututtukansu can ma a ɗaki na, ɗazunnan su Aunty Sadiya suka gama packaging." "Ok!" Ya amsa a takaice. Suna hira yana bata labarin yadda tafiyarshi ta kasance har ta gama ba Aadil nono, suka jera suna hira kasa-kasa har suka fice daga d'akin. Tana biye da shi har gurinsu Aunty Balira, duk da yadda kirjinta ke bugawa haka ta daure ta fuske, ko kadan bata nuna wani alamun firgicin gamuwa da su ko tsoron kar su bi ta da wani mummunan kallo ba. Cikin hukuncin Allah kuma sai suka bi ta a yadda ta zo musu, kadaran-kadahan suka amsa gaisuwar da take ta bin su da shi a ladabce. Kannenta ne suka yi sallama a kofar falon suka fara shigowa hannayensu rike da jakunkunan da aka zuzzuba ma su Aunty Balira kyaututtukan suna.. Kyaututtuka ne aka hada musu na girma, domin cikin ko wane jaka akwai turmin zani mai kyau ba roba ba, turaren wata a cikin kwalba madaidaiciya, Sunkin sabulun wanka, sai katon kalandar hoton jariri Aadil. Haka ta bi su daya bayan daya ta mika ma kowa a ladabce. Bayan ta ba su Aunty Balira nasu haka sake basu jakunkuna biyar a kaima Innaye, Biyar a kaima Baffa, ta bayar da uku-uku a kai ma kishiyoyin Innaye. Abu dai tubarakallah, kamar ba Bintun nan da take gwada musu wulakanci akan abinci ba, kamar kuma ba ita ce jiya ta rufe idanu ta ci musu mutunci ba. Su Aunty Balira bin ta kawai suke da idanu, zukatansu cike da matsanancin mamakinta, wato yanzu da yake a gaban d'anuwansu ne, dubi yadda take yi kamar za ta kwanta musu. 'Makira, in Allah ya yarda alkadarinki ya kusa karyewa.' Aunty Rakiya tayi addu'ar a zuciyarta tana harararta kasa-kasa. Kyaututtukan basu tsaya anan ba, Aunty Sadiya da kanta ta shiga falon ta bi su da kullin naman suna da yaji, kowa kullinsa daban. Sannan ta bayar da na Innaye da Baffa, da kishiyoyin Innaye. Hafiz yana tsaye a gefe yana kallon duk abinda ke faruwa, da yake bai san dawan garin ba. Har ga Allah zuciyarsa cike take taf da farin ciki ganin yadda aka karrama yan'uwansa. Musamman idan ya kalli yadda dattijan cikinsu ke ta zuba murmushi suna kalaman godiya da saka albarka. Su kuma yaran matan suna ta dararraku suna kara yi ma Bintu addu'ar Allah ya raya Aadil ya kara daukaka, ya kuma kare ta daga sharrin makiya da mahassada. 'Yanuwansa uku ne kawai basu yi magana ba, amma labarin da fuskarsu ke bayyanawa karara shi ne suna cikin farin ciki da wannan karamci da aka yi musu. 'Lallai Bintu ta fidda ni kunya. Alhamdulillah' Kalaman da yake ta maimaitawa kenan a zuciyarsa dad'i yana k'ara lullube shi. Bayan duk wadannan kyaututtukan, haka ya sake bin duk yawansu da naira dubu biyar-biyar. Ya sake ba su Baban Yasi wadataccen kudin da za su sake cika tankunansu taf har da raran canji, sannan suka kama hanyar tafiya. Kusan kowa aka kalla a cikinsu baki har kunne, saboda matsanancin jin dadin alkhairan da suka samo a gidan Hafizu. A lokacin karfe uku da rabi na yamma, amma da yake komai dare suna saka ran gida za su kwana in Allah ya yarda. Shi yasa basa fargaban dare da zai iya musu a hanya, fatansu dai Allah ya tsare ya mayar da su gida lafiya. ******* [1/8, 11:02 PM] Fareeda Abdallah: "Yauwa! Gara da Allah ya shigo da ke yanzu. Na riga na gama yanke shawara gobe idan Allah ya kaimu, bayan sallar azahar za a daura auren Zulaikha da duk wanda Allah ya kaddari shi ne mijinta in sha Allahu." Tsananin yadda maganar ya duke ta yasa bata san sa'adda ta saki kwanon shan ruwan da ke rike a hannunta ba. Wani jiri ne ya debe ta nan take tayi taga-taga za ta fad'i, da saurin gaske tayi gaggawar dukewa zuwa kasa ta dafe kujerar da ke kusa da bakin kofa. "Subhanallahi! Rahina? Lafiya kuwa? Ba ki da lafiya ne?" Baffa ya jero mata tambayoyin da sauri hankalinsa a tashe. A gaggauce ya mike tsaye, ya tsallake huhun goro da dabino da suke ajiye a gabansa ya karasa kusa da ita yana jera mata sannu. Shi ya kama ta ta mike ta zauna da kyau akan kujerar da ke kusa da ita. Sai sannu yake jera mata ganin yadda take ta hada zufa kamar mare lafiya, ta kasa magana, sai numfarfashi take yi tana kure shi da wani irin kallo da ya rasa gane inda ta dosa. "Sannu! Daman ba ki da lafiya ne?" Ya sake tambayarta. Dakyar ta iya girgiza mishi kai, alamar a'a lafiyarta kalau. Sau uku tana yunkurin yin magana kafin dakyar ta iya kwato kalmomin "Wa za ka aura mata Malam?" "Ko wani bawa dai ba ya wuce kaddararsa Rahina. Sa'annan matar mutum kabarinsa. Don Allah ki kwantar da hankalinki, wani ba ya taba auren matar wani. Kuma kin san da son zuciya dai bazan taba yima 'yarki auren da bai kamata ba. Ki kwantar da hankalinki don Allah." Ya fad'i maganganun a tausashe, idanunsa na kanta yana ƙara karantar yanayinta. Ta daɗe cikin shiru, babu abinda take ja a zuciyarta sai 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirnee fi musibati, wa aklifnee khairan minha.' Baffa dai yana ta aikin kallonta, bai ƙara matsa mata da maganganu ba. Har sai da ita kanta ta samu nutsuwa hankalinta ya dawo jikinta, sannan ta tambaye shi "Me tayi Malam?" Kafin ya amsa ta cigaba da cewa "Duk da ban san laifin me tayi maka ba don Allah kayi hakuri. Na san a baya ka ce ranar aurenta da aka sanya da Mudan bazai canja daga yadda ka saka shi ba, amma har yanzu ai da sauran kwanaki goma sha biyu. Me tayi? Ko kuma me ya canja wancan ƙudirin naka?" Allah ya sani, ba na so a aurar min da Auta haka kwatsam ba tare da wata ƙwaƙƙwaran sanarwa ba." Ta jero maganganun da bayyanannen tashin hankali a fuskarta. "Idan ka duba har yanzu Zulaikha ba ta cikin walwala. Fasa aurenta da Mudan ya ƙara jefa rayuwarta cikin zulumi ne da fargaba. Maganar da ta ji ana yi kuma na ranar auren bai canja ba za'a ɗaura da ko waye ya ƙara jefa ta cikin tunani da tsoron wane irin miji za'a aura mata. Ba ta walwala. Ba ta dariya. Magana idan ba ya zama dole ba sai mu kwana mu yini bata yi min ba. Dai-dai da abinci da ya zama dole sai na zauna kusa da ita na matsa mata sannan take ɗan tsakura ta tashi. Kai baka ga yadda duk ta rame ta lalace ba? Allah ya sani ni da za ka ji ta tawa ma, ko nan da kwanaki sha biyun don Allah ka daga mata ƙafa. Kai ne fa ke ƙara tunasar da ni aure lokaci ne Malam. Ina ji a jikina mijin Auta na musamman ne in Allah ya yarda. Ko ba jima ko ba daɗe yana nan tafe, lokacin bayyanarsa a duniyarta ne kawai baiyi ba. In Allah ya yarda mijin da za ta aura zai kasance abin alfahari ne a gare ta da gare mu iyaye da ƴan'uwanta da sauran jama'ar ƙauyen nan baki ɗaya..." "Kiyi haƙuri Rahina. Na riga na gama yanke shawara, tabbas in Allah ya yarda gobe iwar haka Zulai tana ɗakin mijinta. Kiyi haƙuri, ki kuma yi fatan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi, ya kuma sa shi wanda za ta aura abokin arzikinta ne." Shiru tayi, tana kallonshi yana kallonta. Banda bugawa fafafat! Babu abinda ƙirjinta yake yi, ta san halin Malam sarai. Tunda ya ce za'ayi tabbas za'ayi ne, babu abinda zai hana auren nan sai dai wani ikon Allah. A raunane ta sake tambayarsa. "Wa za ka aura mata?" "Mijinta" Ya amsa kai tsaye. "Na sani mijinta za ta aura Malam. Sunan shi da ahalinsa za ka faɗa min don Allah..." "Wai duk wannan tambaye-tambayen na menene Rahina? Ke kin san dai idan ban fi ki son Zulai a cikin ƴaƴa ba sai dai muzo kan-kan-kan! Na ce miki ki kwantar da hankalinki. Banyi gaggawa a al'amarin Zulai ba, sati guda na kwashe ina Istikhara akan auren nan kuma babu abinda nake gani sai alkhairi. Ki nutsu, ki kwantar da hankalinki don Allah." Ajiyar zuciya mai nauyi taja ta sauke, duk da yadda yake mata magana a tausashe don ta samu nutsuwa, Allah ya

Chapter 13 of 40