Share this page
can gidan Mummy, a can ta haihu. Don haka ba su da matsalar gurin saukar baƙi. ****** Washe garin suna, yaro ya ci suna Abdulfatah. Taron sunan da ya haɗa gagga-gaggan ƴan gayu abokan aikin Abban Imamu da na Mummy. Suna ne aka yi na ƴan gayu, an dafa kalolin abinci sun yi kala goma. Sannan duk wani abu da za'a ci, a sha, ba daga gidan aka dafa shi ba. Tun da wuri waɗanda aka ba kwangilar dafa abincin suka taho da yaran da za su raba abincin. Duk yawan mutanen da suka taru a gidannan sunan sun ci, sun sha, sun ture, saboda komai a wadace ake zubowa. Mutanen Faƙo kuwa sai da suka yi ta cizon yatsa saboda yadda suke ganin kiɓi-kiɓi na abinci an ci kaɗan an barshi, ga guri nesa, balle su ce za suyi guzuri su tafi da shi gida. Misalin ƙarfe uku na rana Bintu da Aunty Sadiya, Mashkura, da Ummansu suka isa gidan sunan. Nan take kallo ya koma sama, saboda yadda Bintu ta haɗu ta haɗe, ta fito a Dr. Bintu sak! Dama in dai gurin gwalli, kwalliya, ƙwalisa ne in dai aka haɗu da Bintu to a shafa lafiya, ita ɗin ƙarshe ce. Abinku da ƴan ƙauye da basa rabo da tsegumi, nan take suka fara hum-hum-hum ana ai tsohuwar matar Hafizu ce. Sai dai tambarin rashin kirki da aka yi mata a baya yasa bata yi wani kwarjini ba a idanunsu, duk da yadda ta dinga bin su tana gaisar da su cikin girma da mutuntawa. Turamen zannuwa uku masu tsadan gaske da rigunan Baby guda huɗu Bintu ta kaima Zulaikha. Sannan ta kawo wani babban akwati shaƙe da kayan arziki ta damƙa a hannun Aunty Balira cewa ta kai ma Innaye. Duk waɗanda za a ba da sunayensu manne a jikin kayayyakin. Rakiya da Ladidi iyayen riƙo da rashin mantuwa. Ko kaɗan bata wani burge su ba. Sai dai duk yadda suke ta cin magani suna share Bintu a dole suka saki fuskarsu, saboda yadda take ta musu shisshigi tana jan su da hira da dariyarta, kamar ma bata san suna ɗaure mata fuska ba. Bintu shigewa cikinsu tayi sosai, kamar ita ɗin ƴar'uwar Zulai ce ta jini. A Canjin kaya kala na bakwai da Zuly tayi ita Bintun ce tayi mata sassauƙar kwalliya ba Hibba ba. "Bari in ɗan tsara miki fuska mana ƙanwata. Ni ma fa na iya kwalliyar nan, amma abubuwa da yawa a yanzu sun sha min kai ba ma na ko samun lokacin yin kwalliya sosai." Bintu ta faɗa lokacin da taga Hibba ta shigo da akwatin kayan makeup ɗinta za tayi kwalliya ma Mai jego. Maganar da tayi yasa Hibba bar mata fagen kwalliyar, kuma cikin hukuncin Allah sai Zuly tayi kyau sosai, kamar duk sauran lokutan da aka mata kwalliyan. Tun da Bintu ta shiga gidan sunan, Kareema ta zama a ɗarare, sai take jinta kamar ma a muzance. Saboda irin kyawu da ajin da ya bayyana ƙarara tattare da Bintu, duk da ita ma tana da nata kyawun dai-dai ita, amma ita da kanta ta sani wutsiyar raƙumi ta riga ta yi nesa da ƙasa. Haɗin ma ai ba na haɗi bane, baba ma da babansa. Bata san Zuly tana lura da halin da take ciki ba sai da ta damƙi hannunta taja suka shige ɗakin Abban Imam. Lokaci ɗaya Zulai ta ɗaure fuska, kamar ita ce Yayar Kareema. Da ɓacin rai a muryarta ta ce "Mene ne kike ta wani ɗari-ɗari kin kasa sakin jiki tun da Bintu ta shigo cikin taron nan? Miye matsalarki da ita?" Jikin Kareema a sanyaye ta ɗaga idanu ta kalli Zulai, sai ga hawaye shar, zuciyarta cike da wani irin raɗaɗin kishi, a gefe guda kuma ga wani tsoro na daban da ta rasa gane ta inda yake ɓuɓɓugowa. Bakinta na rawa ta ce "Zuly... Tsoro nake ji Wallahi. Ki ga yadda Aunty Bintu ta ƙara komawa wata mace mai aji ta musamman fa... Dama ya ya lafiyar giwa bare ta yi hauka? Na shiga uku! Shi yasa auren mijin wata bai ba. Idan Nurul-ƙalb ya ce zai mayar da ita ban san inda..." Make bakinta da Zulai tayi yasa ta yi shiru tana hawaye. "Wani lokacin dai ke banza ce Aunty Karima. Ni Wallahi kin ma ba ni haushi. Yanzu ke har akwai wata mace mai ɗaura ɗankwali da kike fargabar za ta iya ƙwace mijinki a hannunki? Ba'a aure ita aka aure ta? Kar ki sake faɗa min zancen banza wai wani mijin wata. Bayan haka ma, ke kina ganin a irin matsanancin Son da yaya yake miki har akwai wata ƴa mace da za ta sha gabanki a zuciyarsa? Bintun da dai ita ce a yanzu, babu wani abu na musamman da ta canja. Sannan kuma Miji naki ne, a hannunki yake, ki daina ma wani banzan tunanin wai Yaya zai mayar da Bintu ɗakinta, da zai mayar da ita da tuni an wuce gurin. Ki saki zuciyarki kiyi walwala a cikin mutane..." Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da aka fara yi ta waje yasa Zulai ta katse maganar da take yi. Da muryarta ƙasa-ƙasa ta cigaba da cewa. "Saura kuma ki fito in ga kin cigaba da tsangwamar kan ki, ki shiga bayin Abban Imam ki wanke fuska. Zan turo Hibba ta sake miki kwalliya." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin ba tare da ta saurari cewar Kareema ba. Wasu ƙawayen Mummy ne suka shiga gurin mai jego duba ta da baby, ashe shi ne kiran da aka yi mata. Da ladabi sosai Zulaikha da gaishe su, suka ƙara yi mata barka suka bata kayan barka, sannan suka fice daga ɗakin. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba Kareema ta dawo cikin ƙawayensu da su Mashkura suka cigaba da warwasawa. Bintu na can cikinsu Aunty Balira suna hira, tun da tazo ko idanun Aadil bata gani ba, yana can tare da Imam da sauran yara suna wasa. Kareema ta zo fita daga falon Zuly zuwa cikin gida karaf maganar Aunty Balira ya sauka a kunnenta, maganar da yasa ta rage saurin tafiyar da take yi, don kawai ta ji amsar da zai fito daga bakin wacce aka jefa ma tambayar. "Bintu? Na ce wai ya maganar aure ne? Kar dai ki ce na yi miki shisshigi, amma tsakani da Allah zaman hutun dai isa haka. Aure shi ne daraja da cikar mutuntakar ko wace ƴa mace, in dai Allah ya kawo miki miji, ki daure kiyi aurenki. Idan kuma kun daidaita da Hafiz ne..." "Babu maganar daidaitawa Aunty Balira. Zama ya ƙare tsakanina da Daddyn Aadil. Domin a yanzu haka saura wata ɗaya ne da ƴan kwanaki a ɗaura min aure." A hankali Kareema ta sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa, sai kuma ta ƙara sauri har ta fice daga falon. Wani kwanciyar hankali na musamman na sauka a duk sassan jikinta. "Too ma sha Allah! Allah ya sanya alkhairi, yasa ayi da mu." Rakiya da Ladidi suka faɗi haka da fara'a a fuskarsu. Dama can su ba sa wani ƙaunar dawowar Bintu cikinsu, duk da dai ta shiryu, taje can ta ƙarata da shiryuwarta. Ita kuwa Aunty Balira a sanyaye tayi fatan alkhairi. Allah ya sani duk da Kareema bata rage su da komai ba, ta so ace Hafiz ya yi haƙuri sun daidaita da Bintu. Ko don Aadil, amma inaa... Sam-sam Hafiz ya tsani ma a dinga tayar mishi da maganar wata tsohuwar matarshi wai ita Bintu. Sai gaf da Magriba Bintu da Tawagarta suka bar gidan sunan. Sun rabu suna raha a tsakaninsu. Daɗai wani abu na muni ko rashin fahimta bai taɓa shiga tsakaninsu ba. Anyi taron suna lafiya, an tashi lafiya. Mai jego da Jaririnta sun tashi da rikitiɓar arziki mai yawan gaske. Sai fatan ayi wanka lafiya a gama lafiya Zulaikha ta Abban Imam. *_Alhamdulillah. Komai yayi farko zai yi ƙarshe. Anan na kawo ƙarshen labarin RANAR NAKA SAI NAKA DAƊIN ZAMA SAI BARE. Kuskuren da ke ciki ina roƙon Allah ya yafe min. Alkhairan da ke ciki Allah yasa mu amfana gaba ɗaya ya haɗa mu a cikin ladan. Ina godiya gare ku ƴan'uwana masu karatun wannan littafi tun daga farko har ƙarshe. Sunayenku da yawa, bazan iya ambatanku ɗaya bayan ɗaya ba🥰🥰🥰 Na gode, na gode. Allah ya bar ƙauna da zumunci. Sai mun haɗu a Cigaban labarin ƘASAITACCIYAR MACE... In sha Allah😍😍😍 Fareeda Abdallah ce, domin magana da ni kai tsaye a tuntuɓeni ta wannan lambar 07039080978_* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 40 of 40