Har Baffa ya fice daga ɗakin bata sani ba.
"Kiyi haƙuri Auta..."
"Innaye tun da na taso Yaya ba ya so na ba ya ƙaunata. Idan na kuskura na shiga gidanshi a matsayin matarsa ni na san kashe ni kawai zai yi."
Ta katse Innaye cikin gunjin kuka, bayan ta tabbatar Baffa ya fita.
"Idan ya kashe ki, ko kuma ya bari muguwar matarsa tayi miki wani mummunan abu, duk su biyun hukuma ba ƙyale su za ta yi ba Auta. Ki kwantar da hankalinki, ni kaina wannan auren bai min ba, kuma bazan taɓa yarda da tabbatuwarsa ba."
Jin wannan jimlar maganar ƙarshe ta Innaye, yasa sannu a hankali ta fara rage ƙarfin kukan da take yi, sai sauke ajiyar zuciya. Ita daman ta san Innaye ta fi Baffa son ta nesa ba kusa ba, domin ta ƙara samun nutsuwa a zuciyarta yasa ta ce
"Da gaske Innaye? Za ki sa Yaya ya sake ni?"
"Ƙwarai da gaske. Dole ma ya sake ki, domin shi da kanshi na tabbata ba son wannan al'amarin yake yi ba, Haɗi ne na Baffanku kawai. Amma ya zama dole a yanzu ki kwantar da hankalinki, ki bi Yayan naki ku tafi, ko na sati ɗaya ne. Na fi so in aikata komai a sirrance yadda Baffanku bazai ga laifi na ko naki ba. Ko ke kina so Baffanku yayi fushi da ke ne?"
Da sauri ta girgiza kai, alamar a'a!
"Yauwa! To kin ga da wannan dalilin ya zama dole in bi komai a sannu, cikin hikima da ƙwarewa. Don haka mataki na farko da za mu bi yanzu shi ne ki daina koke-koken nan da kike yi, kar Baffanku ya sake shigowa yaga kina kuka, saboda ba na so ko kaɗan ya ɗarsa a zuciyarsa baza kiyi masa biyayya ba. Na fi so duk wani laifi ya fito ta ɓangaren Hafizu da matarsa, kin gane ko?"
Ɗaga kai tayi, alamar eh!
Miƙewa Innaye tayi ta shiga uwarɗakinta ta bar Zulaikha zaune akan kujera, ta buga tagumi da hannu bibiyu. Zuciyarta a ɗage, a yadda take ji kamar ta janyo sati ɗayannan tayi ta wuce Innaye ta saka Yaya ya sake ta. Tana waɗannan tunane tunanen sai ga sallamar yayyenta su Balira.
Da yake su ma duk sun samu labarin irin halin da Innaye da Zulaikha suke ciki, duk yadda al'amarin auren ya daɗaɗa musu zuciya ko kaɗan basu nuna ba. Jimami da damuwa suka ara mai yawa suka yafa a fuskokinsu.
Bayan gaisuwa da jaje da suka yi ma Innaye nan kusa da Zulaikha suka zauna suna ƙara tausarta da daɗaɗan kalamai. Ko da suka fahimci ƙudurin Innaye na son raba auren kuma har suka fahimci Zulaikha ta hau kan maganganun ta zauna daram! Sai kawai suka cigaba da ɗora ta akan hakan, suna tabbatar mata ai dole ma a raba auren. Amma a zukatansu sam ba sa fatan hakan ya kasance.
Da waɗannan kalaman hilatar har Balira ta samu ta tsefe mata kai. Ita kuma Rakiya ta ɗaura mata ƙunshin gargajiya da ta taho da shi daga gidanta.
"Ku fa duk dama kun daina wahalar da kanku, auren da duka-duka bazai wuce sati ɗaya ba waɗannan gyaran ai ba su da wani amfani."
Ta faɗa tana zumɓura baki, kanta na kwance kan cinyar Aunty Balira ana tace mata kai a hankali. Riƙe a hannunta wayar Balira ce da Hafiz ya bata tana shiga nan ta fita can.
"Duk da haka dai Autan Innaye, ko ba don auren ba za ki bar gari ko na kwana ɗaya ne ai kya gyara jikinki."
Rakiya ta amsa mata a tausashe.
Ita Ladidi can cikin ɗaki ta shige tana taya Innaye harhaɗa ma Zulaikha kayan sawarta sabbi a jikin jakar ghana most go, da duk wasu abubuwa da ta san Auta za ta iya buƙata a cikin kwanaki bakwan da za tayi a gidan Hafizu.
[1/12, 12:03 AM] Fareeda Abdallah: Duk yadda Aunty Ladidi ta so Innaye ta ƙara yawan kayan cikin jakar ƙiyawa tayi. Daga ƙarshe ma balbaleta da faɗa tayi ta ce idan baza ta taya aikin bakinta alekum ba ta fice ta ba ta guri.
"Tafiyar da kowa ya tabbatar ba ta zama ba ce menene na girin-giɗishin zuba kaya da yawa a jaka?"
"Haka ne kuma Innaye. Allah ya baki haƙuri."
Ta faɗa tana ƙumshe dariya.
Sai da Innaye ta fita waje ɗauro alwalar sallar magriba sannan Ladidi tayi gaggawar ƙara yawan kayayyakin, sosai ta zaune jakar yadda kayan ciki suka yi ƙasa, sannan ta ƙara wasu masu yawa ba tare da ta tsaya shirya su a nutse ba don tsoron kar Innaye ta shigo.
Zuwa bayan Magriba, babu laifi Zulaikha ta fito a amarya sak! An wanke mata kai tas! Bayan an gama ƙunshi kafin ya kama Aunty Rakiya ta yaryaɗa mata ƙananun kitso masu kyau sosai. Kuma da yake tana yalwar gashi mare cika sai tsawo kuma baƙi ƙirin kitson ba ƙaramin kyau yayi ba. Ɗaya daga cikin Sabbin kayanta Balira ta bata ta saka a jiki da sabon hijabi.
Ko kafin ta saka kayan sai da tayi narai-narai kamar za ta fashe da kuka. Tuntuni daman ƙarfin hali kawai take yi, kalaman Innaye ne kawai idan ta tuna yake saka ta jin ɗan ƙarfi-ƙarfi da kwanciyar hankali.
"Saboda me zan saka sabon kaya? Ni bazan sa ba Aunty. Idan na saka sabon kaya ai kamar na ma nuna ma jama'a ina son auren nan ne."
Tayi maganar bakinta a gaba.
"Daɗina da ke Auta akwai ki da wauta. Ca nake tuni kun gama magana da Innaye kan za kiyi basaja baza ki ƙara nuna ɓacin ranki akan auren ba? Ta yadda idan komai ya tafi yadda ta tsara Baffa bazai ga laifinki ko na ta ba?"
"Eh!"
Ta amsa cikin ɓacin rai da waswasi.
"To maza ɗauki kayannan ki sanya. Wannan duk cikin shirin ne. Idan kuma kina so shirin naku ya ɓaci ne kar ki saka kayan."
Aunty Balira na gama faɗin haka ta fice daga ɗakin.
Haka Zulaikha ta ɗauki kayan ta saka ba don ranta na so ba. A maimakon ta sake fita falo cikin ƴan'uwanta, sai kawai tayi kwanciyarta akan gado, daman tana fashin sallah. Zuciyarta cike da saƙe-saƙe, ta kuma rasa dalilin da yasa tun da rana ƙirjinta ke bugawa ƙasa-ƙasa.
Yinin ranar gaba ɗaya Innaye ta ƙarasa shi ne fuskarta a ɗinke tsaf! Duk matan da sukai ta shigowa yi mata Allah ya sanya alkhairi, haka take amsawa babu walwala ko kaɗan, don ma kar mace ta ƙara cewa wani abu bayan Allah sanya alkhairin. Hatta abokan zamanta da sauran yaran gida sun rasa gane kanta, a dole suka kama kansu, suka cigaba da harkokinsu da Baffa da fuskarsa ta ƙarasa yinin cike da fara'a ta musamman. Domin haka kawai yake jin wani nutsuwa da kwanciyar hankali na saukar masa.
Duk inda Yayye da ƙannen Hafizu suke nemansa don suyi masa Allah ya sanya alkhairi sama ko ƙasa sun neme shi sun rasa a cikin gidan da waje. Ga kuma motarsa a ƙofar gida, ga direbansa a ƙofar gida, amma ba shi ba labarinsa. Tun da aka kira sallar la'asar ya lallaɓa yana jiri ya fice daga ɗakin Baffa, har zuwa bayan sallar isha'i babu wanda ya ƙara saka shi a ido.
"Ku ƙyale shi, duk inda ya shiga ma zai fito ne. Shi ai ba baƙo bane, ciki da wajen ƙauyen nan babu inda bai sani ba. Duk inda ya shiga bazai ɓata ba."
Kalaman da Baffa yayi musu kenan lokacin da ya ga damuwa da jajen Hafizu da suke yi ya fara yawa.
Mata masu aure haka nan suka bar gidan bayan isha'i ba tare da sun ganshi ba. Amma duk sun ƙuduri aniyar washe gari da sassafe za su dawo su gaisa da Hafizun, suyi masa Allah ya sanya alkhairi sannan su bashi amanar ƴar'uwarsu.
Hafiz bai bayyana ba sai a masallaci wajen sallar asubah, ana idar da sallah kuma yayi wuf zai fice da sauri ƴan'uwansa da jama'ar gari da suke son taya shi murna suka lulluɓeshi. Haka nan ya tsaya ba don ranshi ya so ba, fuskarshi da ƴar dariyar da ana kallo an san na yaƙe ne.
Bayan ya ƙwaci kansa daƙyar daga cikin mutane suna hanyar zuwa gida ƙaninsa ke tambayarsa.
"Yaya ina ka shiga ne? Jiya sama da ƙasa mun neme ka mun rasa, sai direba da motarka kawai a waje. Mun tambayi direba ya ce shi kanshi bai san inda kake ba."
"Uhmmm! Ina nan!"
Abinda ya iya cewa kenan a taƙaice.
Ko da suka shiga gidan, ɗaya bayan ɗaya ya bi ɗakin kishiyoyin Innaye ya gaishe su. Duk ɗakin da ya shiga, sai da ya ɓata lokaci saboda nasihar da suke masa, abu ɗaya da suka fi jaddada masa duk su biyun shi ne lallai yayi ƙoƙarin riƙe amanar Zulaikha. Tunda dai sunyi -sunyi da Baffa ya bari ko mutane uku su raka ta ɗakinta ya ƙi.
"Ka ji tsoron Allah Hafizu. Ka riƙe ƴar'uwarka amana don girman Allah. Ka ga marainiya ce, Fiyayyen halitta SAW ya ce ni da mai taimakon maraya kafaɗa da kafaɗa za mu shiga aljannah. Ka ga kai riba biyu ma za ka ci, ga ta matarka ce, sannan kuma marainiya ce. Don Allah ka ji tsoron Allah, ka riƙe ta amana. Kar ka ga don ba idanun iyaye da ƴan'uwa ka ce za ka zalunce ta."
"In sha Allah! Zan kiyaye"
Ya faɗa daƙyar! Kamar me ciwon baki.
Ko da ya isa ƙofar ɗakin Baffa, ya daɗe a tsaye cikin shiru, kamar kar ya shiga ciki yake ji. Amma ya sani ko bai shiga yanzu ba dole ya shiga ɗan anjima kaɗan, ya gaida Baffa sannan kuma yayi mishi sallama. Domin da safen yake so su juya zuwa Abuja.
Huci mai zafi ya fesar a bakinshi, idanunshi sun kaɗa sunyi jaa, ga wani fitinannen ciwon kai da yake damunsa. Domin Jiya kwana yayi a takure cikin mota, Ƙwaƙwalwarsa a cushe, ya ma rasa wani irin tunani ya kamata yayi. Bai samu wani wadataccen barci ba.
Fargaba da tsoro ne cike taf da zuciyarsa, a yanzu da zai sake fuskantar Baffa, bai san kuma wasu zafafan maganganu zai zo mishi da su ba. Haka kawai, ya tsinci bakinsa da yin addu'o'i yana tsaye a ƙofar ɗakin, sai da ya shafa addu'ar, kafin yayi ƙarfin yin siririyar sallama, ya shiga ɗakin bayan an amsa mishi daga ciki, a bayyane yake jikinsa a sanyaye.
Mamaki ne ya rufe shi ganin fuskar Baffa yalwace da murmushi, abinda bai sani ba shi ne, tun tsayuwarsa a bakin ƙofar da duk abinda yake yi Baffa yana kallonshi ta cikin labule.
"Zauna mana Hafizu"
Baffa ya bashi umarni.
Da saurin gaske kuma a tsorace yakai gwuiyawunsa zuwa ƙasa ya zauna. Idanunshi har lokacin na kan Baffa, duk a tsammaninsa ko laifi yayi. Amma fara'ar da ke fuskar Baffa ita ke saka shi cikin wasi-wasi.
"Fushi kake da ni ko Hafizu?"
"A'a Baffa"
Ya amsa da sauri.
"Wallahi ko kaɗan ba na fushi da kai. Wane ni inyi fushi da kai Baffa? Kawai dai al'amarin ne yazo min a bazatan da ban taɓa tsammani ba. Ka yafe min irin yanayin da na nuna a jiya..."
"Babu komai Hafizu. Allah yayi muku albarka."
"Ameen Baffa"
"Ka yi haƙuri. Ka rungumi ƙaddarar da ta afka maka. Ni kaɗai nasan dalilan da suka sa na yanke shawarar haɗa aurenka da Zulai, ba tare da ita kanta Rahina ta san zan haɗa auren ba. Idan ka riƙe Zulai da kyau, lallai nan gaba kaɗan in Allah ya yarda za ta zame maka matar rufin asiri. Amanarta na damƙa maka ! Amanar Zulai na baka Hafizu!! Ina umartarka da ka riƙe Zulai da Amana Hafizu!!! Lallai idan ka ci amanarta za ka gamu da mummunar ɓacin rai daga gare ni.
A yanzu Zulai matarka ce, kamar yadda Bintu take matsayin matarka. Idan ka fifita Bintu a kan Zulai ka zalunce ta, kuma ni ma ka zalunce ni, Allah bazai taɓa barinka ba Hafizu.
Lallai ina mai tunasar da kai ka kiyaye haƙƙoƙin iyalanka biyu da Allah ya ɗora a wuyanka. Kar ka kuskura son zuciyarka ko tasirin ƙiyayyar da kake yima Zulai tun tana ƙanƙanuwa, ko kuma zugar shaiɗaniyar mace yasa idanunka su rufe ka kasa yi ma Zulai adalci. Ko kuma ka kasa sauke nauyin haƙƙinta da Allah ya ɗora a kanka, idan hakan ta faru, tabbas za ka tashi a ranar lahira da shanyayyen ɓarin jiki.
Yaushe ne tafiyar taku?"
"Da safen nan ne Baffa."
Ya amsa a hankali, gaba ɗaya hankalinsa a ɗugunzume, saboda nasihar da Baffa yayi mishi sun ƙarasa kashe mishi jiki gaba ɗaya.
"Tashi kaje ka gaida Rahina. Allah ya kai ku lafiya ya kiyaye hanya."
"Ameen Baffah"
Haka ya miƙe ƙafafunsa a sake kamar wanda ya wuni yana zawayi ya fice daga ɗakin.
Ko da yayi sallama a ƙofar ɗakin Innaye ya shiga ciki, bayan amsa sallamar da gaisuwarsa da ta amsa a taƙaice babu wata magana da ta sake shiga tsakaninsu. Kamar surukan juna na gaske, haka suka kasance.
Shi kanshi yana ƙasa yana ɗan matsa yatsun hannayensa kaɗan-kaɗan yana jiran jin abinda za ta ce masa. Ita kuma fuskarta na kallon gefe, fuskarta babu walwala ko kaɗan, casbahan hannunta take cigaba da ja sauri-sauri.
"Innaye?"
Ya katse shirun da ke tsakaninsu ta hanyar kiran sunanta a raunane.
A fakaice ta kalle shi, bata amsa ba ta sake kawar da kanta gefe ɗaya.
Ajiyar zuciya yaja ya sauke kafin ya cigaba da cewa
"Da safen nan za mu tafi. Kiyi haƙuri, a saka mana albarka..."
"Idan ka bari Bintu ta zalunci Auta ban yafe maka ba Hafizu."
Innaye ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa, da muryar faɗa-faɗa.
"Sannan kuma ban yafe maka ba idan ka ɓoye ma Bintu matsayin Auta a gare ka yanzu. Duk da dai wannan al'amarin ba wai ya kwanta min arai bane, har izuwa yanzu tunanin yiwuwarsa ko rashin yiwuwarsa nake yi, amma a iya ɗan zaman da Auta za tayi da ku kafin mu samu hanya mai ɓullewa, idan kai ko Bintu wani ya cuta mata don zalunci ban yafe masa ba. Ɓace min da gani"
Har ya miƙe zai fita yana rangaji ta sake kiran sunanshi a tsawace.
A hankali ya juya yana kallonta, idanunsa sun ƙara kaɗewa sunyi jajur!
Babu tausayinsa ko kaɗan a fuskarta ta sake cewa
"Kuma ban yarda idan kuka isa can Habuja ka ajiye min Auta a wannan ƙaton ginin na bayan gida inda kuka saba saba yasar da mu ƙauyawa ba. Ita ma ka ajiye ta cikin aljannar duniyar da kuke kai da matarka, tunda dai a yanzu itama matarka ce. Allah ya bamu alkhairi."
Ko da ya buɗe baki zai amsa addu'ar, inda kasan an saka zare da allura an ɗinke masa baki. Ga wani nauyi na musamman da bakin yayi mishi, a dole ya amsa addu'ar a zuciya ya kama hanyar ficewa daga ɗakin.
"A'ah! Ango Ango! Na Bintu da Zulai ba da kanka a sare kaje gida ka cewa Innaye ya faɗi."
Aunty Rakiya da ta sanyo kai cikin ɗakin tayi maganganun da salon tsokana tana kallon cikin idanunshi.
Ita kuwa Aunty Balira cewa tayi
"Idanunka kenan Hafizu? Jiya ƙad da bus muka neme ka a cikin gidannan muka rasa. Ko duk murnar auren gatan da Baffa yayi maka ne?"
Ya rasa dalilin da yasa, yana kallon cikin idanun Aunty Balira wasu hawaye masu ɗumi suka cicciko idanunshi. Kawai sai ya ƙara sauri ya fice daga ɗakin don kar hawayen su zuba a gabansu.
Bai san Aunty Balira tana biye da shi ba, sai da ya shiga cikin soron gidan yaji muryarta ɗan nesa da shi kaɗan tana kiran sunanshi.
A yadda zuciyarsa ke wani irin zafi da tuƙuƙi, gani yake idan ya buɗe baki da nufin yin magana tabbas babu abinda zai hana shi fashewa da ƙaƙƙarfan kuka. Don haka kawai ya zaɓi yin shiru yana kallonta, har ta ƙarasa kusa da shi ta riƙo hannunsa na dama a cikin nata.
A tausashe, da yanayin kalami mai nuna rarrashi da damuwa da halin da yake ciki ta ce
"Kayi haƙuri Ƙanina."
Ɗan shiru ne ya ratsa tsakaninsu, kuma har lokacin ya kasa buɗe baki yayi magana, sai ajiyar zuciya kawai yake saukewa akai-akai.
Ita ne ta cigaba da cewa a tausashe.
"Na sani ba'a kyauta maka ba Hafizu. Kayi haƙuri ka ji? A cikin biyayyar iyaye duk tsananinsa in dai ba saɓon Allah bane in sha Allah alkhairi ne yake biyo baya. Saboda yardar Allah tana tare da yardar iyaye. Fushin Allah shi ma yana tare da fushin iyaye. Kar ka kuskura ka biye ma son zuciyarka ko kuma wata ƙiyayya ka saɓa ma iyayenka ka ji ko?"
"Na gode Aunty. Zan kiyaye in sha Allahu"
Taƙaitacciyar nasiha ta sake mishi har Aunty Ladidi ta shigo ta tarar da su a tsaye a zauren. Ita ma ta ɗan tofa albarkacin bakinta cikin sigar rarrashi da tausasa kalami.
Godiyar ya sake musu, da alƙawarin zai yi aiki da duk shawarwarin da suka bashi. Kafin ya fice zuwa waje, su kuma suka koma cikin gida.
[1/18, 10:59 PM] Fareeda Abdallah: Duk yadda Zulaikha ta so ta cigaba da nuna dauriya kasawa tayi, lokacin da taga gadan-gadan da gaske tafiya Abuja za a sake yi da ita. A Abuja ma ba ko ina za'a kaita ba sai gidan Bintu, Bintu da ta tabbatar duk cikin ƴan'uwansu ta fi tsanarta. Kuma za ta je gidan ne yanzu ba'a matsayin ƙanwar miji ba, a'a! Matsayin matar maigidan za ta je.
Ita ba jahila bace, daidai gwargwado tana da sani sosai a ɓangaren Islamiya. Domin wani jajirtaccen malami suka samu daga ƙungiyar malamai masu shiga ƙwauyuka yin da'awa. Tun da aka ajiye musu shi a ƙauyen yana koyar da ƴan mata da safe, da rana matan aure, da yamma samari, da daddare maza magidanta fiye da shekaru biyar bai taɓa barin ƙauyen da sunan tafiya gaba ɗaya ba. Sai dai ya je can birni gurin iyalinsa kwana ɗaya, biyu sai ya sake komawa ƙauyen.
Da yawan ƴanmatan da yake koyar da su karatun shashatau suke yiwa islamiyar, tana daga cikin ɗaiɗaikun yaran da suka nace ma karatun, domin a yanzu haka tana da haddar izu ashirin cif a kanta. Kuma ta samu karatun littattafai da dama.
Domin lokuta da yawa ita ke ƙara ma su Innaye karatun Alƙur'ani mai girma a gida da sauran littattafai, hatta wasu hukunce-hukuncen addini ita suke fara tambaya, idan ta sani ta amsa musu, idan bata sani ba sai ta tambaya musu Ya Sayyadi a makaranta.
A yanzu, ta sani tunda aka ɗaura aurenta da Hafiz haƙƙoƙinta sun hau kansa, kamar yadda nasa suka hau kanta. Kuskure kaɗan za tayi mala'iku su fara tsine mata. Bata son auren ko baya son auren wannan bai isa uzuri ba a gurin Allah SWT. Idan tana son kanta da arziki ya zama dole tayi taka tsantsan wajen kiyaye haƙƙoƙinsa da suke kanta, har zuwa lokacin da Allah zai ƙaddara rabuwar auren. In dai ba kuma tana so ta jefa kanta a halaka bane.
Kafin ta birkice musu da kuka na tashin hankali, a ɓoye Aunty Rakiya ta ja ta zuwa ɗakin Umma Laraba, tayi mata karatun dallah-dallah na yadda za ta zauna da Bintu, har ma da shi kanshi Hafiz ɗin ba tare da ta wahala ba.
Bakinta a gaba ta ce
"Aunty Rakiya auren nan fa Innaye ta tabbatar min bazai wuce sati ɗaya ba, don zaman sati ɗaya da zanyi acan ni me ma zai sa in shiga harkarsu har su wulaƙanta ni..."
"Amma ke kam anyi sakaryar yarinya Auta. Wai halin Bintun ne kika manta ko kuwa tsoronta kike ji? Kina sane da cewa in dai daga ƙauyen nan mutum ya je gidan Hafizu ko na yini ɗaya ne muguwar yarinyar nan sai ta san yadda tayi ta ƙuntata masa.
Hatta su Baffa basu tsira da wulaƙancinta ba. Balle kuma ke da tun a farkon-fari a bayyane take nuna ma kowa ba ta son ki ba ta ƙaunarki. Kuma kin sani sarai ba wani shiri kuke yi da Hafizu ba, balle ganin idanunsa yasa ta jin shakkar yi miki wani muguntar.
Yarinya idan ma za ki zage damtse ki shiga gidan da shirinki gara ki zage, idan ba haka ba kuwa..."
Ta saki ƙaƙƙarfan ƙwafa kafin ta cigaba da cewa
"Ba sati ɗaya ba, Ko zaman auren kwanaki biyu za kiyi a gidan irin gashin aya a tafin hannun da Bintu za tayi miki na rantse da Allah sai kin gane shayi ruwa ne. Don haka gara ma ki farka daga magagin da kike yi, ki shiga da shirinki da taƙamarki, ki nuna mata Zulan nan fa da ta sani a baya mare tsoro da ɗaukar iskanci har yanzu dai ke ce ba'a canja ki ba."
Haka Aunty Rakiya ta ɓata lokaci sosai tana ƙara kitsa mata yadda za ta dinga ƙwatar kanta a hannun Bintu da Hafiz. Kuma inda Allah ya taimake su shi ne Mama Laraba ita ke aikin abin kari, har Aunty Rakiya ta gama yi ma Zulaikha bayanin da za ta mata babu wacce ta shiga cikin ɗakin ballantana a kwaɓa mata.
Basu fito ba, sai da Aunty Rakiya ta ji muryar Ladidi tana jajen ina suka shiga.
"Ki ji tsoron Allah Rakiya, me kike kitsa mata? Na fa san halinki ba ki da haƙuri kamar zawo."
Aunty Ladidi ta faɗa tana ɗan hararar Rakiya cikin wasa.
"Ba ruwana. Nasihar zaman aure kawai nayi mata irin wanda ake yiwa ko wacce amarya."
Ta amsa tana dariya.
"Ai kuma sai kiyi, dama ba'a san asalin balbela ba sai ta ce daga madina take. Kin ji Auta zo muje kiyi wanka, lokaci ya ƙure, tun ɗazu Hafizu ke aiken idan kin gama shiryawa za ku wuce ga shi ko wanka baki yi ba."
Tun daga jin kalmar za su wuce ɗinnan jikinta ya ƙara wani irin sanyi ƙalau. Nan take ta fara matsar ƙwallah, har Aunty Balira tayi mata wankan Amare da ruwan turare da lalle kuka take yi ƙasa-ƙasa.
Da yake fuskar Aunty Baliran a ɗaure yake tamau, shi yasa ko kaɗan bata samu damar kawo mata wargi ba har aka gama wankan, da su hayaƙin tsuguno da na jiki, da wasu mabanbantan turaruka da tayi ta mutsuka mata a sassan jiki, a dole nata kallo da shatatar hawaye har aka gama shiryata cikin wata doguwar riga ƴar saudiyya mai kyau, kuma sabuwa fil, wacce bata san daga ina Aunty Baliran ta samo ta ba. Ta saka mata sabon hijabi mai girma da ya sauka mata har ƙasa saboda ba wani tsawon azo a gani take da shi ba.
Sannan Aunty Balira da Ladidi da take ta yaba irin kyawun da tayi suka kama ta a lulluɓe jikinta babu inda ba ya rawa suka kai ta gurin Innaye da tun ɗazu take zaune a falonta ta zuba tagumi, idanunta sun kaɗa sunyi jaa, kallo ɗaya za ayi mata a hangi gagarumin damuwa a tare da ita.
Sai da aka zaunar da ita gaban Innaye da cewar tayi mata nasiha sannan Zulaikha ta samu damar sakin ƙaƙƙarfan kukan da tuntuni take dannewa. Lokaci ɗaya ita ma Innaye ta saki na ta kukan a raunane, da alamun tun ɗazu kukan ke son ƙwace mata tana matsewa. Abin dariya abin tausayi, Zulaikha kuka Innaye kuka, haka ƴaƴan suka tasa su gaba suna kallo kamar suyi dariya ga kuma tausayin da ya lulluɓe zukatansu, saboda a bayyane yake ga kowa irin matsananciyar shaƙuwa da ƙaunar da ke tsakanin Innaye da Autar ta. Basu taɓa tsammanin aure zai nesanta su nisa mai nisa irin haka ba.
Ganin irin kukan da Innaye ke sharɓa yasa lokaci ɗaya Zulaikha ta sake birkice musu da kuka kamar wacce aka ce mata idan ta tafi ta tafi kenan har abada.
Tun ƴaƴan suna rarrashi su kaɗai, har sai da su Umma Laraba da Mama Laminde da sauran ƴaƴan gidan mata da suka je gidan suka shiga ɗakin su ma suka fara aikin rarrashi.
Suna cikin wannan halin, Baffa ya shiga ɗakin da sallama a tsawace, amma a wannan karon duk
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 40