Share this page
da ɓata lokaci ba kuwa ta lalubo lambarta ta danna mata kira. "Wallahi Mummy ba shi da lafiya ne tun jiya. Kin ganshi nan kwance a gida na ɗaura mishi drip, barci yake yi." Bintu ta faɗa ma Mummy bayan gaisuwar da ya shiga tsakaninsu. "Subhanallahi! Me yake damunshi haka? Har da ƙarin ruwa?" Mummy ta tambayeta da damuwa sosai a muryarta. "To ga shi nan dai Mummy, ya kwana biyu yana yawo da ciwon a tsaitsaye jiya zuwa yau ne dai ya kwanta. Kuma ya ƙi yarda mu tafi asibiti, na ɗibi jininshi dai na tura asibiti yanzu ina jiran sakamako ne, amma na san bai wuce typhoid." Bintu ta amsa itama da tata kalar damuwar. "Allah ya sauwaƙe ya bashi lafiya. Yanzu dai ba na Abuja, idan mun dawo da wuri zan leƙo gidan, idan kuma munyi dare gobe sunday zan shigo in sha Allah. Idan ya tashi ki gaishe min da shi." Da haka suka rabu. A can ƙofar gidan Baffah, Abban Imamu ne zaune a cikin ƙatuwar jeep ɗin sa yana waya da abokinsa Isma'il, bakinsa har kunne kamar gonar auduga. Tsananin farin cikin da yake ciki yasa tun ɗazu ya kasa rufe baki, a yadda yake jin zuciya da ƙirjinsa a yanzu, kamar bai shiga cikin ƙunci da matsananciyar damuwa a iya tsawon sati biyunnan da Zulai tayi ba ta amsa wayarsa kuma ba ta chatting da shi sai lokaci bayan lokaci ba. Shi da kanshi tun ranar da ta tafi da ya kira ta a waya ya fahimci tana cikin damuwa, amma duk yadda ya buga ya kaɗa ya raya ta ƙi faɗa masa abinda yake damunta. Idan ya matsa mata da tambaya ma, sai dai ta saka mishi kuka ta katse wayar. Wannan dalilin yasa a daddafe cikin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali yayi sati biyu bai biyo ta ba. In banda ya kasance yaro mai tsananin biyayya lallai da tuni ya ƙetare umarnin Mummy ya bi bayan Zulai a ɓoye duk da bai san hanya ba, matambayi ai ba ya ɓata. Da gaskiyar Mal bahaushe da ya ce abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala bazai hango ba. Yanzu da ya danni zuciyarsa, ya cigaba da haɗiɗiyar ƙunci da damuwa duk da damuwar Zulai na damunsa. Sai ga shi jinkirin ya zame mishi gagarumin alkhairin da bai taɓa zata ba. Daga zuwa neman aure sai ace a ɗaura auren kawai a wuce gurin? "Wai da gaske kake yi Dude?" Isma'il ya sake tambayarsa daga can ɓangaren da murya mai bayyana matsananciyar mamaki. Ƙaƙƙarfan dariya ya kwashe da ita yana ɗan dukan sikiyarin mota kamar ba shi ba. "Kana mamaki ko Dude? Nima har yanzu mamakin nake yi Wlh. Yanzu fa ana idar da sallar azahar ɗinnan za'a ɗaura aurena... Gaskiya... ina cikin alkhairi dumu-dumu... Alhamdulillahi rabbil-Aalamin." "Ma sha Allahu laaƙuwwata illah billah! Na taya ka murna Aboki. Allah ya sanya alkhairi. Yanzu dai bari in kira Auwal mu tsara yadda za mu biyo jirgin yamma zuwa Kaduna, wannan gagarumin abin farin cikin bai kamata ace bamu a kusa da kai ba..." "Kar ku damu, ba sai kun zo ba. Mu ma bayan Asr prayer za mu kamo hanyar komawa gida. Ka san yanzu ɗaura auren kawai za'ayi, bikin sai daga baya. Iyayenta sun nemi in basu sati uku ni kuma gaskiya bazan iya ba, na ma faɗa ma Mummy gaskiya bikin kar ya wuce nan da sati biyu. So kaga duk wasu shirye-shirye muna da isassun lokacin da za muyi a Abuja, duk da dai ni bidi'o'innan ba burgeni suke yi ba. Bari in je inyi alwala kar in rasa jam'i, za mu yi magana bayan ɗaura auren." "To Aboki, once again Allah yasa albarka yasa mahaɗin arzikinka ce." "Amin ya Allah Dude. Na gode." ***** ***** [2/15, 9:35 PM] Fareeda Abdallah: Zulaikha da tun ɗazu taja Karima da Imam suka tafi gidan Aunty Balira sam ba su da labarin halin da ake ciki. Suna zaune suna hira da dararraku sun tasa lafiyayyiyar gurasar da Aunty Balira ta gasa musu a gaba suna ci, kawai sai jin sallamar abokan zaman Innaye tayi wai sun zo tafiya da ita in ji Baffah. A tsorace, duk suke kallon su Umma Laraba, ita ta ma kasa cewa komai don tsoro da faɗuwar gaba. Sai Aunty Balira ce tayi ƙarfin halin tambaya bakinta na rawa "Umma lafiya kuwa? Me Autar Innayen tayi kuma?" "A'a lafiya ƙalau Balira. Bata yi laifin komai ba, abin alkhairi ne ya faru da ita. Auranta aka ɗaura yanzu da ɗan'uwan wannan yarinyar da take zaune kusa da ke. Duk da tarewar ba yanzu ba sai nan da sati biyu, kinga matsayinta na matar aure ai bai kamata ace an barta tana yawace-yawace ba, shi yasa Baffanku ya ce muzo mu tafi da ita." Tsananin murna da farin ciki yasa Karima bata san sa'adda ta ture kwanon man ƙuli da yake gabanta ba ta miƙe tsaye ta fara kwaso shoki tana watsa ma Zulaikha. Lokaci ɗaya tana haɗa da waƙar gwanja ta Ahayye sama cibiyar nisa, tsakaninki da yaro sai kallo. Aunty Balira babu abinda bakinta ke furtawa sai kalaman godiya ga Allah, da jinjina girman hikima irinta Ubangijin sammai da ƙassai, da ya ƙaddara faruwar komai cikin ƙanƙanin lokacin da basu taɓa tsammani ba. Zulaikha kuwa, da farko daskarewa tayi a zaune, bakinta a ɗan buɗe, ta ƙura ma Umma Laraba idanu don ji take kamar dai kunnuwanta basu ji abinda aka faɗa daidai ba. Sai da karaɗin Karima ya isheta sannan tayi firgigit, sai kuma matsananciyar kunya, da wani irin matsanancin daɗi da farin ciki suka lulluɓe sassan jikinta. Cusa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana murmushi ƙasa-ƙasa. Ita kaɗai take jin ta kamar wacce take yawo a kan gajimare. "Ashe haka ake ji a jiki da zuciya idan aka auri wadda ake so?" Ta tambayi kanta da kanta. Da gaske tana son Abban Imam, irin matsanancin son nan da ita kanta baza ta ce ga iyakarsa ba, domin a wasu lokutan soyayyarta har zillo da tsungulin zuciyarta take yi. Kawai dai a matsayinta na mace, wacce aka fi sani da kunya da kawaici, da iya danne abu a zuciya yasa take matuƙar ƙoƙari wajen yi ma soyayyar tasa waigi a zuciyarta. Amma in da ba don haka ba... Wata-kila da tuni ta ƙwace da sambatun sunansa da labarin irin son da take masa duk bayan minti ɗaya biyu... A ƙarshe dai gurasar da basu samu ƙarasa ci ba kenan. Ita ma Aunty Balira miƙewa tayi ta bi bayansu bakinta har kunne bayan ta haɗa sauran gurasar a cikin ƙaton kwanon samira, ta yayyanka kabeji ta tafi da shi da nufin kai ma mahaifiyar Karima da Kakarta Hajja. Ko da ta isa gidan Baffa, irin yadda ta ga Mummy da Hajja na tarairayar Zulaikha da ina za'a saka ina aka aje da ita cikin matuƙar ƙauna da tarairaya yasa ta ƙara ji a ranta lallai fa yanzu ne Autar Innaye ta daje da miji ɗaya tamkar da dubu. Irin wannan ƙauna da tarairaya haka? Gaba ɗaya sun babbake komai sun hana kowa kusantar Zulaikha. Hajja da ta kasance haifaffiyar ƙauye ita ta dinga lissafa irin kayayyakin da take buƙata a kawo mata, wanda za ta fara yi ma Zulaikha amfani da su wajen gyaran jiki. Cikin ƙanƙanin lokaci aka haɗa mata komai, sai ga Hajja a gaban murhu tayi bake-bake kamar ƴar gida, Balira, Indo, Rakiya, Ladidi da sauran manyan ƴaƴan Baffa suna kusa da ita tana basu umarnin daka wannan, miƙo wancan, ɗauraye wannan, kuma ta riƙe sunayensu ram a bakinta, kamar dai daman can ta san su. Cikin awanni biyu da suka biyo baya, Hajja ta haɗa lafiyayyen ruwan lalle da yaji magunguna da turaruka irin nasu na mutanen da tayi ma Zulaikha wanka da shi. Ana wankan tana zazzaga ma Zulai masifa saboda yadda take ta noƙewa cikin kunya. "Kin san Allah Zulai zan ci ƙaniyarki. Kalle ni dakyau! Jikata na ɗauke ki ba matar jika ba. Yadda zan bugi ƙirji in shirya Kareema ranar aurenta haka zan shirya ki Zulai. Don haka duk wannan nuƙu-nuƙun da kike yi gara ma ki bari, bai sha min kai ba in saka tsumagiya a cikin banɗakinnan in zane ki ciki da bai idan kika ce za ki min taurin kai. Atoh! Ni ba ruwana. Haka nake free falo, kin sanni sarai." Ko bayan gama wankan, haka ta tasa ta gaba da hayaƙi kala daban-daban. Daga ƙarshe aka yi mata wankan turare, a cikin sabbin kayayyakin da suka tafi mata da shi aka zaɓi doguwar riga ɗaya aka ba ta ta saka. Bayan dogon naci da roƙo da Abban Imam yai tayi ma Mummy, a ƙarshe ya bi ta hannun Anty Balira da sabo na surukuta ya shiga tsakaninsu cikin ƙanƙanin lokaci ya samu damar ganawa da ita a falon Baffa. Tunda ta shiga cikin ɗakin, ta kasa ɗaga idanu ta kalle shi, wata matsananciyar kunyarsa ce ta lulluɓeta. Ko gaisuwa daƙyar ta iya buɗe baki ta gaishe shi, ƙirjinta banda bugawa babu abinda yake yi, har yanzu, ganin komai take yi kamar ba da gaske ba. Shi kuwa babu kunya yayi zaman dirshan a gabanta kan dadduma yana leƙen fuskarta. Bakinsa har kunne, da farko ya kasa cewa komai bayan gaisuwarta da ya iya amsawa. "Beb kin ga ikon Allah ko?" Ya tambayeta bayan ya ga kiran Mummy na shigowa cikin wayarsa, yasan ba kiran komai bane face na tunasar da shi ƙurewar da lokaci ya fara yi, ƙarfe huɗu na yamma har ta gota. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Daga yau, har zuwa ƙarshen rayuwata, bazan taɓa gajiya da cigaba da godewa Ubangiji da ya nufe ni da samun aurenki a sauƙaƙe ba Zulaikha. Wallahi ina son ki, irin matsananciyar soyayyar da ni kaina ban san iyakarta ba. Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba." "Ameen." Ta amsa daƙyar, a ciki-ciki. "Baffa yace bikin sai nan da sati biyu, amma ni dai ina jin gaskiya bazan iya bari har sai nan da sati biyu ba... zan je in roƙe shi ya bari mu tafi da ke yau kawai..." "A'a don Allah kayi haƙuri." Tayi maganar a shagwaɓe, tare da buɗe fuskarta da sauri tana kallonshi da dara-daran idanunta. Da sanyin murya ya ce "To bayan ma tunda kika taho ja min aji kike tayi don kin ga ba na kusa da ke, na san yanzu ma idan nayi gangancin tafiya na barki haka za ki cigaba da ja na a ƙasa tunda ba wani so na kike yi ba..." "Ayya Ayya mana Abban Imam." Ta sake faɗa a shagwaɓe. Kafin yayi magana ta sake cewa "Allah kuwa ba haka bane. Kawai dai tunda nazo ba na cikin nutsuwa ne saboda abubuwan da suka faru. Kayi haƙuri, bazan sake ba, ka ji?" Ƙuriii yayi mata da idanu yana kallonta, yadda hatta muryarta yake fita da wani irin sanyi da ƙamshin da yake ɗan bugun fuskarsa. Wani daddaɗan shaukin ƙauna na ƙara ratsa duk sassan jikinsa. Tun da ya fara ganinta, ya rasa dalilin da yasa, komai tayi burge shi take yi, kuma kyau na musamman take ƙarawa a idanunsa ko wane lokaci. Domin kawai ya ƙara ganin shagwaɓa da taɓarar da take masa yasa ya maƙale kafaɗa kamar ƙaramin yaro ya cigaba da tsokanarta. "Na ƙi ɗin! Ba wani nan. Na san wayau kawai za ki min. Ni dai gara kawai mu tafi yau gaba ɗaya." "Allah ba wayau zan maka ba. Don Allah ka bar maganar tafiyarmu yau." Tayi ƙwalƙwal da idanunta kafin ta ci gaba da cewa "Ka ga fa yanzu an ce an ɗaura mana aure, idan na ƙi bin umarninka ai sai mala'ikun rahama suyi ta tsine min. Haka ne ko? To don Allah ka yi haƙuri, ka ji Abban Imamuna?" Tayi masa far da idanunta, ƙasa-ƙasa ta cigaba da cewa "Kuma maimakon sati biyu ma ina laifin wata biyu? Kamar gobe ne za kaga sati biyun ta zo ta wuce, a cikin sati biyu bazai isa inyi shirye-shiryen komai ba..." "Lallai ma Yarinyar nan. Baki isa ba Wallahi." Ya katse ta da sauri yana ɗan buɗa mata idanu. "Sati biyun ma Wallahi don Baffa ya yanke ne, amma Wlh da bazan bari ba ki ƙara sati biyu ba tunda kin zama matata. Ni fa ba na son komai, na faɗa ma Baffa tun ɗazu amma ya ƙi cewa komai. Ke nake so, don haka ke ɗin kawai nake buƙata. Alfarmar da aka yi min ma wajen mallaka min wannan zuƙeƙiyar yarinyar ba tare da na wahala ba ya ishe ni abin alfahari..." "Yaya? Wai Mummy ta ce anan za mu kwana ne? Ƙarfe biyar na yamma ta wuce fa" Ya tsinkayi muryar Karima daga can bakin ƙofa tana faɗin haka. Da sauri Zulaikha ta miƙe tsaye tana zazzare idanu tana kallon ƙofa, a tsorace take sosai kar Karima ta shigo taga irin zaman da Abban Imam yayi a gabanta. "Je ki ce mata ga ni nan zuwa." Ya amsa yana ɗan ɓata fuska, kamar Kariman tana gabansa. Hannu yasa ya janyo Zulaikha da ta nufi hanyar fita daga ɗakin da sauri, da yake janyowar na bazata ne, taga-taga kamar za ta faɗi yayi saurin tareta ta faɗa jikinsa. Ko kafin tayi wani yunƙuri na ƙwacewa, yayi mata wata kyakkyawar runguma, kansa ya ɗan kwantar a saman ƙirjinta yana sauke ajiyar zuciya sauri-sauri. Lokaci ɗaya jikinta ya mutu murus, bata yi wani yunƙurin ƙwacewa ba don riƙo yayi mata ba na wasa ba. Runtse idanu tayi da ƙarfi, tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa sauri-sauri, a tsorace take gaba ɗaya. "Ina son ki. Don Allah ba don ni ba ki kula min da kanki sosai. Kuma ko da yaushe ki zama kusa da wayarki. Kin ji?" Sosai bakinta yayi mata wani irin nauyi, sai da ƙyar ta iya ɗaga masa kai, alamar ta ji. Wasu daƙiƙun ya sake ɓatawa yana riƙe da ita a jikinsa kafin ya sake ta a hankali, hannunta na dama ya kamo, ya laluba aljihun wandonsa ya ɗebo kuɗaɗen ciki gaba ɗaya ya damƙa mata. "Ko da za ki buƙaci wani abu don Allah kar ki tambayi su Baffa. Ki faɗa min a waya, zan saka a kawo miki duk abinda kike buƙata." "Tam!" Ta faɗa a hankali. "Don Allah ka bar kuɗinka, babu abinda zan nema. Allah ya mayar da ku gida lafiya." "Amin Maman Imam." Ya amsa da sanyin jiki, bai karɓi kuɗin ba kamar yadda ta nema, sannan kuma bai saki hannunta ba. Allah ya sani shi fa gaba ɗaya ji yake kamar kar ya tafi ya barta a garin, gara kawai ya tafi da matarsa, ko kuma ya zauna har zuwa sadda za a bashi matarsa. Kamar ta san tunanin da yake yi, sai ta kalli hannayensu da ke maƙale da juna. Kafin ta mayar da kallon kan fuskarsa, a kunyace ta sakar masa murmushi. "Kayi haƙuri, sati biyu ne fa kacal. Kuma na maka alƙawarin in sha Allah duk sadda ka kira za ka same ni a waya. Ka kwantar da hankalinka, ka je, Su Mummy na jiranka." Ya kasa cewa komai don tsananin sanyin da jikinsa yayi, hankalinsa a tashe. Hannunta da yake cikin nasa ya ɗaga yakai bakinsa, ya sumbata a hankali sannan ya fice daga cikin ɗakin da sassarfa. Ko da ya fita, ta kasa bin bayansa don tsananin kunyar su Mummy da mutanen gida, yau dai hatta Karima da Yayyenta kunyar haɗa idanu da su take yi. Don haka ta cigaba da zamanta a ɗakin Baffa, zuciyarta cike taf da tunanin mijinta. Lokaci bayan lokaci ita kaɗai sai ta saki lallausan murmushi, tana shafa bayan hannunta inda ya sumbata da tausasan laɓɓansa. "Allah na gode maka." Ta faɗa a fili, zuciyarta cike da matsanancin farin cikin da baki bazai iya furta adadinshi ba. [2/17, 10:59 PM] Fareeda Abdallah: Kamar yadda Mummy ta alƙawarta ma zuciyarta, sai da ta sake roƙar ma Hafiz gafara a gurin Innaye da Baffa. Ta ƙara tunasar da su komai fa na duniya yana faruwa ne bisa doron ƙaddarar da aka shirya faruwarsa tun kafin muzo duniya. "Kuma idan kun duba, a yanzu komai da ya faru za mu iya cewa mafificin alkhairin da muke ta roƙa ne ako wane lokaci Allah ya tabbatar da faruwarsa a sauƙaƙe." "Haka ne Hajiya. Daman mun yafe mishi, Allah ya yafe mana gaba ɗaya." Baffa ya faɗa da yanayin da ke nuna tun daga ƙarƙashin zuciyarsa yayi maganar. Ita kuma Innaye cewa tayi "Daman babbar damuwa da ɓacin ran na yadda ya mayar min da ƴa ƙaramar bazawara ce, amma yanzu tunda Allah ya canja mata da wanda ya fi shi alkhairi komai ya wuce. Allah ya shirya mana zuri'a." "Amin ya rabbi." Kamar haɗin baki, shi ma Alhaji Lurwanu gaf da za su bar ƙauyen ya nemi ganawa da Baffa da Innaye a keɓance ya sake roƙar ma Hafiz gafara. "Babu komai Alhaji. Wallahi har ga Allah mun yafe masa. Allah ya yafe mana gaba ɗaya." Baffa da Innaye suka haɗa baki gurin amsawa. Kafin tafiyarsu sai da Hajja ta damƙa komai na gyaran jikin Zulaikha a hannun Umma Laraba da Aunty Balira. "Amana! Ga amana nan na damƙa muku. Kuma kun san dai amana maci amana maye ɗan'wuta ne inji yara. Ban yarda ko dai dai da rana ɗaya a tsallake yi mata gyaran nan ba, duk abinda ya ƙare kafin kwanaki sha huɗunnan ke Balira ki ranta kuɗi a siyo. Duk abinda aka kashe idan kun zo zan biya ki, ƙwandalarki baza tayi ciwon kai ba ƴar nan. Alƙawari na ɗauka." Maganganun da tayi ta jaddada musu kenan har suka fice daga cikin gidan zuwa gurin motocinsu. Duk sun riga sun sani kunya ce ta hana Zulaikha fitowa suyi sallama, shi yasa babu wacce ta matsa da son ganinta tsakanin Mummy da Hajja. Ita kuwa Karima a ɓoye ta shige ɗakin Baffa tayi ma Zulaikha tsiya son ranta kafin ta fito daga ɗakin tana ƙyalƙyala dariya. Basu bar Ƙauyen Faƙo ba sai ƙarfe shidda saura kwata na yamma. Sun rabu ne ko wane ɓangare zukatansu cike da matsanancin farin ciki. Su Mummy basu wani tayar da hankulansu kan yamman da suka yi ba, saboda sun sani komawarsu Abuja bazai yiwu a ranar ba, in dai ba so suke suyi tafiyar dare ba, wanda sam Hajja baza ta bari ba. Sun tsara za su kwana a Kaduna, washe gari suyi sammakon wucewa Abuja. Shi kuwa Alhaji Lurwanu da yake yana da harkokin da zai gabatar a Kaduna, ba ma a washe garin zai koma Abuja ba. Labarin da Hafiz ya samu na aurar da Zulaikha ga Ya Kamal ɗan gidan Mummy ba ƙaramin farin ciki ya jefa zuciyarshi a ciki ba. Ko kaɗan ranshi bai ɓaci, domin shi daman babu soyayyar Zulaikha irinta aure ko kaɗan a zuciyarsa. Ba ma kamar da ya samu labarin yafe masa da iyayensa suka yi daga bakin Abba Lurwanu da Mummy. Bayan uban faɗan da yasha, ƙiris ya rage ya karɓi tukwuicin mari daga gurin Abban, saboda ɓacin ran yadda irin wannan muhimmin al'amarin zai faru amma ya ɓoye masa. Shi dai haƙuri yayi ta basu cikin ƙanƙan da kai, har zuwa sadda suka tabbatar mishi da su Baffa sun yafe masa, komai ya wuce, da fatan zai kiyaye gaba. Samun waɗannan daɗaɗan labarai guda biyu da bai taɓa tsammanin jin su a irin wannan lokacin ba yasa ɗan sauran zazzaɓin da ya rage a jikinsa ƙarasa fecewa. Sai ga shi ya miƙe garas, da ƙwarin jiki yayi ma su Mummy rakiya zuwa gurin motocinsu yana ta zabga musu godiya kamar zai ari baki. Da yake a lokacin da suka je gidan Bintu tana asibiti, shi yasa duk bata san abinda ke faruwa ba sai da ta koma gida ya labarta mata. Ƙarara ɓacin rai, hassada, ƙyashi, baƙin ciki suka bayyana a fuskarta jin irin cigaba da ɗaukakar da Allah yayi ma Zulai a lokacin da bata taɓa tsammani ba. Ta san Mummy Saudah tun da daɗewa, Ogar Hafiz ce a gurin aiki, babbar macece hakima da ta tara ɗumbin abin duniya, don ma dai ba ta da girman kai ko kaɗan. Ta kuma san Kamal, babban ɗan Mummy da ya auri Zulai, haɗaɗɗen gaye ne da ya tara dukiya mai yawa sanadiyyar aikinsa, kuma an mutu an bar musu gadon dukiya mai yawa. A taƙaice saboda irin alfarmomin da suke ci ta sanadiyyar Mummyn ita da Hafiz yasa sadda Karima ta gama Karatunta na aikin jinya ta shiga ta fita har sai da ta samar ma Karima gurbin aiki a asibitinsu. Yanzu shi kenan Zulai ta samu ɗaukaka? Ta faso gari kenan za ta goge duk wani ƙauyanci da jakanci haɗe da dabbanci su bar jikinta? "Taɓɗijan! Shi kam a ina ya haɗu da ita ne haka har aka haihu a ragaya?" Ta tambayi Hafiz ɗin fuskarta babu walwala ko kaɗan. A taƙaice, ya bata labarin irin zaman da Zulaikha tayi a gidan Mummy na tsawon watanni. A fili ta taɓe baki "Amma kuwa dai ya ji kunya, ya kuma yi faɗuwar baƙar tasa. Ace duk wayewa da gayu haɗe da aji irin tasa ya rasa yarinyar da zai aura sai ƴar ƙauyen ƙayau kuma jahila daƙiƙiya irin Zulai. Gaskiya ya ci baya..." "Me kike nufi kenan Bintu?" Hafiz ya tambayeta da ɓacin ran da ya bayyana a fuskarsa tun da ta fara maganganun da ke nuna baƙin cikinta ƙarara. "Me nake nufi kuwa Dear? Kawai dai abinda ke raina na faɗa, kai ma kuma kasan ai gaskiya ne." Fuuu ta miƙe tsaye ta ɗauki jakarta za ta wuce sama. Da saurin gaske ya janyo ta ya dawo da ita baya sannan ya danƙwafar da ita akan kujera. "Kar ki manta, abinda yayi Zulan da kike kira baƙauyiya, jahila kuma daƙiƙiya shi yayi ni Hafiz da kike aure. Domin ita ɗin Ƙanwata ce, jininmu ɗaya, ƙauyenmu ɗaya, ashe ke ma baya kika ci da kike aure na?" "A'a da banbanci fa My dear... banbanci mai nisan gaske ma. Kai ai ka daɗe da shigowa birni, ka waye, kuma ka yi zuzzurfan ilimin boko. Idan ma ba ka faɗa ba babu wanda zai kalleka yace kana da jiɓi da wasu ƙauyawa can... Amma dai duk inda ka nufa ni ba haka nake nufi ba, idan ka ji haushi Allah ya baka haƙuri." A karo na biyu ta sake ɗaukar jakarta da nufin wucewa sama, ba tare da ta yarda ko fuskarsa ta kalla ba. Domin Allah ya sani labarin irin cigaban da ya sami Zulaikha ba ƙaramin baƙanta mata rai yayi ba. Ta zaci zai sake dakatar da ita a karo na biyu, sai taji bai janyo ta ba har ta fara haurawa matattakala. Shi kuwa Hafiz tsananin mamaki da girgizar da kalamanta suka jefa shi a ciki ne yasa ya kasa sake ce mata komai, har ta ɓace ma ganinsa. Duk da farin sanin da yayi ma halayen Bintu na son harkar wayewa da birnanci da nuna ilimi, abu ne da bai taɓa tsammani ba ta iya tsayawa a gabansa ƙeƙe da ƙeƙe ta faɗi munanan kalamai irin haka akan ɗaya daga cikin ƴan ƙauyensu ma ba Zulai da ta kasance jininsa ba. Ya daɗe zaune a gurin maganganunta suna wujijjiga shi, zuciya da mugun saƙe-saƙe sai ga shi cikin ƙanƙanin lokaci ta fara shigo mishi da wasu irin tunanika mabanbanta da juna. Duk yadda yaso yayi watsi da tunanikan da yake yi, ya kasa, a dole suka samu matsuguni a zuciyarsa suka yi darshe-darshe, ya cigaba da ɓata lokaci a gurin yana sake raba ɗaya biyu a kalaman Bintu. Daga ƙarshe dai, tattara tunanin komai yayi ya aje gefe ɗaya. Ya miƙe tsaye, har ya nufi hanyar da zai sada shi da ɗakunan barcinsu sai kuma ya canja shawara, yana ji a ransa in dai ya haura sama suka yi ido biyu da Bintu tabbas zai cigaba da tuhumarta kan kalaman da ta faɗa masa ne. Shi kuma a halayensa ba mutum bane mai yawan

Chapter 26 of 40