Share this page
Ko da nake ƴar ƙauye kin san dahuwar indomie dai ba za ta gagareni ba." Zulaikha tayi maganar tana ƙara harhaɗe girar sama da ƙasa. Zuciyarta cike da haushin Baba Rabi yadda take ma Bintu wata irin biyayya ta musamman kamar wacce ta girme mata a shekaru. "Anya...?" Baba Rabi ta faɗa cike da taraddadi da tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo. Sai kuma ta ƙara da cewa "Ko da yake, shi kenan. Bari a dafa mata, ɗan bani mintuna goma kacal. Je ki dawo, yanzu zan gama dafa mata." Gefe guda taja ta tsaya tana bin duk inda Baba Rabi tayi da idanu, akan idanunta ta kunna Gas ɗin girki, daman shi kaɗai ne take ga baza ta iya amfani da shi ba a kicin ɗin. Tana biye da ita har ta buɗe store, ta ɗauko duk abinda za ta buƙata sannan ta fito ta kulle. Abu na biyu da taga yadda ake kunnawa ayi amfani da shi blander ne, don haka ta kura idanu sosai taga yadda ake anfani da shi. Tana kallon komai tana k'ara kwasar ilimin yadda ake amfani da kayan girkin 'yan birni, har zuwa lokacin da Baba Rabi ta gama dafa lafiyayyiyar indomie da ta ji kayan had'i. Ta soya kwai guda hudu kamar yadda Auta ta umarce ta, sannan ta kwashe komai a kula Mai kyau sabanin Wanda ake zuba musu abinci ta mika ma Auta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke lokacin da ta karbi abincin. Ta haske Baba da wani lallausan murmushi, a tausashe ta ce "Na gode, Allah ya biya ki da alkhairi." "Amin ya Allah. Ki gaida Innaye, Allah ya kara sauki." Baba Rabi ta amsa bayan ta mayar mata da martanin murmushinta. Ko da ta koma can bangarensu, akan darduma ta tarar da Innaye, hannunta da casbaha tana ja amma tana gyangyad'i. Sallamar da tayi ma bata amsa ba sai da ta ce "Innaye barci kike yi?" Firgigit! Tayi ta farka, ta bude Baki za tayi magana wata k'atuwar hamma ta k'wace mata. "Sannu Innaye. Kiyi haƙuri, na barki kina jira na ko? Ba'a gama dafa abincin gidan bane shi ne nasa aka dafa miki Indomie..." "Waɗannan siraran taliyar Auta? Kin san dai ko a gida ke ce kike ƙwazzabar a siyo miki ita gurin Isa mai shayi ki ci, ko ki karɓo a shagon Isiya ki dafa, ni kam bata ɗaɗarani da ƙasa ba." "Innaye, wannan haɗi na musamman aka yi gurin dafuwarta. Ba irin ta can ƙauyenmu bane, na tabbata za ki ji daɗinta. Kuma kin ga fa har wata faffaɗar ƙwai aka soya miki da za ki dinga yaga kina haɗawa da taliyar a gayance irin na ƴan birni. Bari in zuba miki ki ɗanɗana ki ji." Bata jira umarnin Innaye ba ta zauna dirshan a gabanta, ta ɗauki faranti da cokali ta buɗe kular ta zuba mata mai ɗan dama a faranti, daga yadda take fitar da daddaɗan ƙamshi tun bayan buɗe kular, duk su biyun sai haɗiye miyau suke yi. Da farko ƙwan gaba ɗaya ta ɗora akan abincin Innaye, sai da ta ce mata ta rage, sannan ta yanka biyu da cokali ta bar mata rabi. Daman tun a frige ɗin falon can cikin gidan ta ɗauko musu ruwa da lemon kwali, a kofi ta zuba mata sannan ta tura mata abincin a gabanta. Ta tura abincin gabanta ta miƙa mata cokalin, Bismillah tayi ta fara ci a hankali ita kuma tana janta da hira, labarin samarinta na can ƙauye da Innaye bata taɓa sanin tana da su ba take ba ta, tana faɗa mata yadda suke nacin bibiyarta ita kuma tana karta musu rashin kirki da kashedin kar wanda ya kuskura ya bi ta gida, a cewarta, duk basu yi mata ba. Sai dariya suke yi kamar babu wani abu da yake damunsu. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Innaye ta cinye abincin tas! Bata ankara ta cinye ba sai da Auta ta ce "Innaye in ƙara miki?" Ta kalli farantin, ta kalli Auta idanu buɗe, lokaci ɗaya sai suka sake kwashewa da dariya. "Lallai kam Auta kinyi gaskiya, wannan dahuwar taliyar ba irin jagwalgwalon da kike yi acan ƙauye bane. Ta yi daɗi sosai, na daɗe rabon da in ci abinci mai yawa irin haka, lallai komai na birni ya fita daban da na ƙauye. Ko don ina jin yunwa ne?" "A'a Innaye. Ta bakinki ne, tsarin dahuwar ba irin tamu bace amma duk indomin iri ɗaya ne. Kar ki damu, ai na zuba idanu sosai na koyi yadda ake dafa irinna ƴan gayun. Idan muka koma gida, irinta zan dinga dafa miki..." "Kya dai dinga dafa ma mijinki. Domin muna komawa gida zan tura Baffanku ya tuntuɓi Idi, Hamisu, da sauran duk masu son ki da kika gama ba ni labarinsu yanzu. Anya Auta? Ashe daman kina da masu son ki kika bari muna ta ɗaga hankalinmu akan ko Aljani ne ya aure ki kika rasa mashinshini? Yayyinki na ta safa da marwa gurin Malam Usaini suna karɓo miki dafa'in farin jini da na kore shaiɗanu?" Ƙirjinta ne ya buga daram! Sai a yanzu ta fahimci irin suɓul da bakan da tayi a dalilin son janye hankalin Innaye har ta ci abinci sosai. Ƙwal-ƙwal tayi da idanunta ta sunkuyar da kanta ƙasa, domin ta san duk abinda za ta faɗa a yanzu dai Innaye baza ta taɓa fahimtarta ba. Kamar an buɗe famfo, haka Innaye ta cigaba da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Domin al'amarin rashin auren Zulaikha abu ne da ya daɗe yana ci musu tuwo a ƙwarya, kawai dai don ba su da yadda za suyi ne. "Shekarunki sha bakwai fa. Saboda Allah duk faɗin ƙauyenmu ki faɗa min wace yarinya ce yanzu sa'arki a shekaru da ba'a yi mata aure ba? Ke ko kunya bakya ji? Ganɗan-ɗan da ke ni da nake Gyatumarki ina tafe muna jera kafaɗa a cikin gida? In banda akwai zaman lafiya tsakanina da su Laraba ai da tuni sun fara yada min habaici da baƙaƙen maganganu. Yanzu sa'anninki fa daga masu ƴaƴa uku sai biyu, Hanne ta gidan Mal Bala kuwa ita da yake kwainika take yi ƴaƴanta huɗu. Saboda Allah kin yi ma kanki adalci mu ma kinyi mana adalci kenan?" Saboda yanayin lafiya da yayi mata ƙaranci a ƴan kwanakin, nan take ta fara numfarfarshi sama-sama saboda faɗan da take yi ba ƙaƙƙautawa. Da sauri Zulaikha ta matsa kusa da ita ta riƙe hannayenta, a tausashe ta fara magana idanunta cike da hawaye. "Ayya mana Innaye Allah sarki. Don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga ba wani wadataccen lafiya kike da shi ba. Kar ki manta, ke kike yawan faɗen aure lokaci ne, kamar layin markaɗe ne idan yazo kaina ko ina so ko ba na so sai an niƙa min..." "Au! Da waɗannan maganganu biyun kika dogara yasa kika ƙi mayar da hankali kan abinda ya kamata kina gani kullum hankalinmu a tashe?" Innaye ta jefa mata tambayar fuskarta na bayyana ɓacin rai. Sai kuma ta ɗan sassauta muryarta yayi rauni ta sake cewa "Auta ko dai so kike in koma kushewata ba tare da na ga ƴaƴanki ba?" "A'a! A'a! Wallahi ba haka bane Innaye. Don Allah kiyi haƙuri." Ta ƙarasa maganar tare da gangarowar hawayen da tun ɗazu take riƙewa a cikin idanunta. "Idan ba haka bane to yaya ne? Sanin kanki ne babban burinmu a yanzu ni da Baffanki da ƴan'uwanki mu hannanta ki a hannun miji na gari wanda muka yarda da nagartar halayensa. Me yasa baza ki sadaukar da farin cikinki don ki cika mana burinmu ba?" "Kiyi haƙuri Innaye." Ta sake faɗa cikin kuka mai tsanani. Duk da matsanancin tausayinta da ya cika zuciyar Innaye bata bari yayi tasiri a fuskarta ba. Haka ta cigaba da tsattsareta da maganganu masu karya zuciya har sai da suka kai gaɓar da Zulaikha ta ɗaukar mata alƙawarin suna komawa gida za ta ba masu sonta damar fitowa neman aurenta. Kuma duk wanda su iyayenta suka tabbatar ya fi nagarta ko da zuciyarta ba ta so za ta amince a ɗaura musu aure. "Allah yayi miki albarka Auta ta. In Allah ya yarda baza ki taɓa yin da na sani ba a auren da za muyi miki. Allah yayi miki albarka." Duk yadda addu'a da saka albarkar suka yi mata daɗi a zuciya ta kasa amsawa a fili sai a zuciya. Sunkuyar da kanta ƙasa sosai ta sake yi wasu sabbin hawayen na sake ɓalle mata, don Allah ya sani, Aure, ta bar gaban Innaye zuwa gidan wani ƙaton gardi haihata-haihata shi ne abu na ƙarshe da bata fatan ya faru a kanta. Kuma ita da kanta idan za'a ɗora mata wuƙa a maƙogwaro baza ta taɓa cewa ga dalilin da yasa take ƙin aure a rayuwarta ba. ****** ****** "Uhmmmm! In faɗa miki gaskiya Bintu? Kin ga duk irin matsananciyar soyayyar da kike ganin tana gudana tsakaninki da Abdul-hafiz? Wallahi baza ki taɓa samun kwanciyar hankalin mijinki da nutsuwarsa guri ɗaya ba matuƙar tsohuwar nan tana raye. Iya zallar gaskiyar magana kenan, babu wani ɓoye-ɓoye ko kwana-kwana. Kar fa ki manta, duk lalacewarta da ƙauyancinta mahaifiyarsa ce. Akwai wannan ƙauna da soyayyar ta musamman da Allah ya saka tsakanin ɗa da mahaifiya, to ke wacece da za ki ce dole ya fifita ki akan mahaifiyarsa? Ai in faɗa miki ƙawata kin riga kin baro shiri tun rani. Yo uwar miji na birni ma ya aka ƙare da ita ballantana ta ƙauye? Waɗanda tun asali sun riga sun ginu da rayuwa akan makirci da matsanancin sa'ido na tsiya ga bin ƙwaƙƙwafi? Ai fa ina sake jaddada miki sai dai kiyi haƙuri, shi yasa ni bana taɓa ganin laifin ƴan matan da suke ture soyayya su ƙi auren saurayi muddin mahaifiyarsa tana raye. Uwar miji???!! Uhmm! Ciwon zuciya da hawan jini ake faɗa miki ƙawata. Ko ni abinda yasa baki san ɗan ƙaramin biki da cikan da muka kwasa da tawa ba kafin Allah ya ɗauki rayuwarta don dai baki yi aure bane a lokacin, ko na faɗa miki irin matsalar da nake ciki ba lallai ki fahimci inda na dosa ba. Da Allah kuma ya dubi zuciyata sai ya raba mu tun kafin tafiyar tayi tsawo, shi yasa kika ganni yanzu hankalina kwance, kamar tsumma a randa. Don haka idan za ki ɗauki mataki tun wuri gara ki ɗauki mataki, musamman a yanzu da wasu ƴan damarmaki suke a hannunki..." "Kamar ya? Me kike nufi Raudha? Don Allah buɗa min bayanin sosai yadda zan gane." Ta katse ta da tambayar a ɗokance, a zuciyarta take jin kamar wata gwaggwaɓar mafita Raudhan za ta faɗa mata wanda zai haura da ita tudun mun tsira a cikin ƙanƙanin lokaci. Ɗan dariya Raudha tayi tana karkaɗa ƙwayoyin idanunta, sai kuma ta gyara zama ta cigaba da cewa "Daɗina da ke Bintu wani lokacin duk wayewarki kanki kullewa yake yi, jiya fa kika gama cika mana bakin mu ƙyale ki, ke kin san yadda za ki bi da komai daki-daki ki warware matsalar da ke gabanki. Yanzu kuma me ya canja miki ra'ayi kike neman mafita a waje na?" "Uhmmm! Baza ki gane bane Raudha. Wallahi da farko duk yadda nake hango girman matsalar kamar bata kai haka ba. Allah ya sani ko ƙaramin kular abincina Sweetheart ban taba tsammanin zai iya dauka ya kai ma tsohuwar nan ba, sai ga shi ya goge min hadda ta hanyar kwasar abincin da na ɗauki fiye da awa biyu ina shirya mishi kuma na zuba a cikin tsadaddun kuloli ya kai ma ƙauyawan can. Allah ya gani wannan abu ya bakanta min rai ba kadan ba. Yanzu dai duk ba wannan ba, warware min maganar da kika yi ta karshe yadda zan gane sosai." Ta ƙarasa maganar fuskarta na bayyana takaici, kamar a lokacin ne take kallon kulolinta a ɗakin Innaye. Dariya sosai Raudha tayi kafin ta matsa da bakinta kusa da kunnen Bintu ta rad'a mata wasu maganganu, lokaci daya Bintu ta waro idanu warwaje had'e da bude baki a mamakance. Da sauri ta janye kunnenta hannunta dafe da haɓa ta ce "Ke Raudha !!! Anya kuwa zan iya? kina ganin wannan mafita ce da za ta samar da hanya mai ɓullewa? Ni dai gaskiya tsoro nake ji" "Oho miki! Sai ki je kiyi ta jin tsoron. Ni dai shawara na baki, ko ki dauka ko ki cigaba da zama a cikin matsaloli ba ma matsala ba. Sai ma nan gaba idan ita da kanta tsohuwar da tsohonsa suka nemi dawowa gidanku da zama gaba ɗaya..." "Haba-haba-haba-dai! Su ma baza su fara ba. Sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa." Bintu ta katse ta da sauri hankalinta a tashe. "Kina ganin bazai yiwu ba? Su ai daman a garin gaɓa-gaɓan su ke. Kuma ma kanki farau zama gida ɗaya da iyayen miji? Kin san dai ɗansu na da wannan ƙaton gidan da duk ƙauyensu babu irinsa, kuma mai ɓangarori da yawa baza su taɓa yarda ya kama musu haya ba. Yanzu dai tashi ki tafi Ofis, daga baya ma karasa maganar..." Ita kaɗai a cikin Ofishinta ta gama tunanin irin maganganun da suka tattauna da Raudha kafin ta ƙaraso asibitin. Da farko, sam bata ji a zuciyarta za ta iya aiwatar da shawarar da Raudha ta bata ba, amma a yanzu da ta ƙara yi ma al'amarin karatun ta nutsu sai ta fahimci lallai fa ya kamata ta ɗauki mataki tun kafin wankin hula ya kaita dare. Kuma a yanzu dai babu wani mataki da take gani a matsayin mafita ta gaggawa face bin hanyar da Raudha ta ɗora ta akai. A hankali, ta mik'a hannu ta dauki takardar da ke ajiye akan teburin gabanta, sakamakon gwajin da aka yi ma Innaye ne don ganin ko tana da ciwon suger ko babu. Ba tare da ta buɗe ta ga me sakamakon ya ƙunsa ba ta keta shi gida biyu, hakan be ishe ta ba, sai da ta ƙara yayyaga shi gutsi-gutsi sannan ta watsa a cikin abin zuba sharar da ke cikin ofishin. Tattara yan karikitanta tayi ta zuba a cikin jaka, ta ɗauki wayarta da ke ajiye a gefe ta gyara zaman mayafinta sannan ta fice daga cikin Ofishin. Bata ɓata lokaci ba tayi sallama da sauran abokan aikinta bayan ta hannanta komai ga likitan da ta karɓe ta ta shige motarta ta bar asibitin. Kafin ta ƙarasa gida, sai da ta biya wani babban shagon sayar da magani ta sayi magunguna da alluran da za ta ɗora Innaye akai a matsayin na ciwukan jikinta sannan ta wuce gida. A gefe guda, tana jin wani nutsuwa na musamman yana ratsa zuciya da gaɓɓan jikinta. ******* Duk matsananciyar fara'ar da ke fuskarta lokaci ɗaya ɗaukewa tayi ɗif! Sakamakon ganin wasu setin kuloli har guda uku da ya nuna mata da cewar a cikinsu za a cigaba da zuba ma su Innaye abinci. Saɓanin waɗanda ta ware guda biyu masu matsanancin arha da sauƙin kuɗi, ta kuma tabbatar ma Rabi duk halin da ake ciki in dai ba ita ta canja ba kar a taɓa canja su wajen zuba ma Innaye da Autarta abinci. "My Dear? Lafiya kuwa? Me ya canja yanayinki lokaci ɗaya haka?" Ya tambayeta cikin kulawa da tarairaya, lokaci ɗaya shi ma yanayin fuskarsa ta ɗan canja saboda damuwar da ta shiga duk da bai san ko ta mece ce ba. Duk yadda ta so wayancewa kasawa tayi, sai kawai ta ɓuge da cewa "Uhmmm!" Sai kuma ta sake wulƙita idanunta kan kuloli biyun da ya siyo a matsayin nata kulolin, canjin wancan da ya kai ma Innaye abinci irinsa sak sai banbancin kala da kuma wani sabo mai zane daban da ya siyo mata don faranta zuciyarta. A hankali ta miƙa hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin kwalin kulolin wanda ya kasance irin nata, reciept na kuɗin kular da ke manne a jikin kwalin ta duba, dubu ɗari da hamsin ya siya, ita kuwa da yake Oder ne da kuɗin kawowa da komai a dubu da ashirin ya iso mata har gida. Ajiyewa tayi ta ɗauki ɗaya kwalin kular, ita kuma dubu tamanin da biyar take. Ba kunya ba ta sake duba kulolin da suke matsayin na su Innaye sai taga ɗaya dubu arba'in, ɗaya dubu talatin da biyar, ɗaya dubu arba'in da takwas. Duk da kuɗaɗen da aka siyo kuloli ukun basu taru sunyi kuɗin nata guda biyu ba, ta rasa dalilin da yasa ranta yayi mummunan ɓaci da ganin kulolin a matsayin na su Innaye. 'Bintu ki nutsu fa... Idan kina son komai ya tafi miki dai-dai sai kin saka siyasa a ciki.' Wani sashe na zuciyarta ya ankarar da ita. Wannan tunanin da tayi yasa da sauri tayi ƙoƙarin kawar da damuwar fuskarta ta maye gurbinsa da murmushi. "Uhmmm!" Ta sake cewa a karo na biyu. "Allah dai ya ƙara mana imani da lafiya Sweethert. Wallahi yau na ga abubuwa kala-kala masu ɗaga hankali a asibiti, ni da nake ta damuwar ciwon Innaye sai naga ashe tana cikin nagartattun tsoffi masu lafiya da ƙwarin jiki sosai a wannan zamani da muke ciki. Allah ya ƙara mata lafiya da nisan kwana." "Amin ya Allah." Ya amsa da sauri yana sauke ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali. "Kuloli sunyi kyau gaba ɗaya Sweethert. Allah ya ƙara buɗi da arziki mai albarka." "Ameen." Ya sake amsawa cikin jin daɗi da farin cikin da ya gaza ɓoyuwa a zuciyarsa. Ledar magani da alluran Innaye da ke ajiye kusa da ita ta janyo ta fara nuna masa tana mishi ƙarin bayani a rarrabe. 'Daman arashi akayi, bata yi tsammanin dawowarsu zai zo lokaci ɗaya ba sai ga shi tana shiga da motarta cikin gidan shi ma direba ya shiga da tasa. Lokacin da misalin ƙarfe biyu da minti arba'in da biyar na rana. A yadda ta saba idan tana aikin safe kuma ta tsara tun tana hanya, idan ta isa gidan ko a gurguje ne za ta samar mishi da lafiyayyen abincin da zai ci idan ya dawo. Tunda ƙa'idar lokacin dawowarsa a kullum huɗu da rabi ne zuwa biyar na yamma. Sai dai idan da wata ƙwaƙƙwaran dalili yakan ɗauki askis a gurin aiki kamar dai yau ɗin da ya dawo ba lokacin da ya saba ba, duk da bata san dalilin dawowar tasa a yau ba. Bayan ta yi masa sannu da zuwa tun a tsakar gidan, jakar hannunsa ta Ofis da wayoyinsa biyu ta karɓa ta wuce masa da su ciki, duk da farko so tayi su jera amma ya ce ta shiga ciki yana tafe. Da kanshi ya dinga shiga da kwalayen kulolin yana ajiyewa a gabanta bayan direba ya gama aje masa su a ƙofar falon har ya gama shiga da su gaba ɗaya. Tun ma kafin yayi mata bayanin kulolin, har fuskarta ya cika da matsananciyar fara'a tana jin ƙarin matsananciyar ƙauna da soyayyarsa a zuciyarta. A tunaninta, gaba ɗaya kuloli biyar ɗin ya siyo ne don wanke zuciyarta daga laifin da yayi mata na jiya. Tun kafin ya ce komai, ta bashi kyakkyawan runguma da sumbata biyu a kuncinsa dama da hagu, ta kuma ƙara da godiya da addu'ar Allah ya ƙara buɗi. Ranta bai fara ɓaci ba sai da ya ware biyu a matsayin nata uku kuma na mahaifiyarsa. Domin a idanunta, da saƙar wani ɓangare na zuciyarta, sai take ga kamar ba asalin kuɗaɗen kulolin da ya kira na Innaye aka rubuta a jikinsu ba. Kamar dai sun nin-ninka haka, kamar dai an rubuta kuɗi kaɗan ne domin a ninke ta a baibai. Idan ba haka ba taya za'a ce kuloli masu sauƙi haka yanayin zane da ƙayatuwansu har sun fi na ta masu tsada kyau a idanun mai kallo?' Ƙoƙarin kawar da tunanin komai tayi a zuciyarta ta tsayar da hankalinta guri ɗaya ta cigaba da yi mishi bayanin magunguna da alluran. "Alhamdulillahi! Duk sakamakon gwaje-gwajen nata sun fito yau. Irin ciwukan da mukai hasashen samu a jikinta ma ba'a samu ba. Ba ta da ciwon suger kuma babu hawan jini, ba ta ulcer, hanta ma da ake tsammanin za'a samu a jikinta duk babu. Ka ga amfanin yin gwaje-gwaje sosai kafin a fara shan magunguna ko?" Ta ƙarasa maganar idanunta cikin nashi tana sakar mishi murmushi. "Ƙwarai kuwa Dr. Bintu." Ya amsa bayan ya mayar mata da martanin murmushinta. Hararan wasa da soyayya ta jefe shi da shi kafin ta cigaba da cewa. "Izuwa yanzu abu biyu zuwa uku dai muka tabbatar suna damun Innaye. Ɗan typhoid ne kaɗan, sai maleria, sai kuma rashin hutu da bata cika samu ba. Duba da yanayin shekarunta, a yanzu ta kai matakin da ba ko wane irin aiki da ta saba yi ada can za ta cigaba da yi ba. Lallai tana buƙatar ta dinga hutawa sosai. Ka ga waɗannan su ne magunguna da alluran da zan ɗora ta akai, in sha Allahu cikin ƙanƙanin lokaci duk wani ciwo da yake damunta za mu neme shi mu rasa." "Ma sha Allah! Allah yasa haka My Dear, don dai Allah ya sani waɗannan ƙananun ciwo ce ciwo cen da suke addabar Innaye cikin satittikannan suna matuƙar ɗaga min hankali." "Kar ka damu. Za ta warke da wuri in Allah ya yarda." Ta amsa a fili. A zuciyarta kuwa cewa tayi 'In sha Allahu ta kusa macewa gaba ɗaya ma kai ka huta nima in huta.' Ruwan gora me madaidaicin sanyi da tun kafin shigowarsa ta ɗauko a cikin frig ta tsiyaya a kofi ta kafa mishi a baki cike da soyayya, kallon ƙwayar idanun junansu suke yi cike da shauƙi a zukatansu, don haka bai ma san lokacin da ya shanye ruwan ba sai da ya ji ta janye kofin daga bakinshi. Hannunshi ta kama kamar ƙaramin yaro suna tafe zuwa dakinshi tana ba shi labarin wasu dattijai biyu mata da aka kawo asubitinsu, shekarunsu bai kai na Innaye ba amma irin ciwukan da suke jikinsu sam ita ba ta d'auke da su. "Ka ga wannan ke k'ara nuna mana ba wani gata ko rayuwa a cikin birni ke hana bawa ya kamu da cututtuka ba. Abin ikon Allah ne kawai da jarabawarsa, sai mu k'ara gode ma Allah da ya kawo mana na ta jarabawar da sauk'i. Allah ya k'ara mata lafiya." Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na k'ara samun kwanciyar hankali da maganganunta. Kafin ya amsa da "Amin ya Allah My dear. Haka ne kam, na ji dadin maganganunki. Ina tsananin son ki matata..." "Ni ma ina son ka Mijina." Ta katse shi da amsar tun kafin ya aje numfashin maganarsa, fuskarta cike da murmushi. Kamar ko da yaushe in dai ya dawo tana gidan, ita ta taya shi ya rage kayan jikinsa sannan ta shige bandaki ta hada mishi ruwan wanka. A zuciyarta take dariyar yadda ta iya kirkirar zancen an kawo tsofaffin da suka fi Innaye jin jiki don kawai ta kwantar da hankalinsa. 'Yo miye a ciki? A fakaice dai ta isar mishi da sakon ba rayuwa a birni ko kauye ke sa mutum ya kamu da cututtuka ba. Duk da dai ita da kanta takan kiyaye tu'ammali da kayan kauyen da kuma 'yan kauyen don gudun kamuwa da cutuka. In jifa ya wuce kanta ya fada kan ko ma waye, gara su can sun saba rayuwa a haka.' Ko da ta gama haɗa mishi ruwan wanka, kafin ta fice a ɗakin sai da ta fitar mishi da ƙananun kayan shan iska da zai saka idan ya fito daga wanka, ta fesa turare, ta ajiye a gefen gadon sannan ta fita zuwa kicin a gaggauce domin samar musu abinda za su ci. Baba Rabi ta gama rabon abinci kenan ta shiga cikin kicin ɗin, kamar ko wane lokaci in dai ta shiga a irin wannan lokacin, bubbuɗe kular abincin kowa tayi taga yadda aka zuba masa. Idanunta ƙur akan miyar su Innaye da aka zuba tsokokin nama masu yawa saɓanin yadda aka saba sakawa. "Rabi?" Ta kira sunanta bayan ta janye

Chapter 5 of 40