Share this page
sai na kira ta ba Innaye. Idan ma akwai abinda take so sai Zulai ta ɗiba mata. Waɗannan kayayyakin da kika haɗa ma sun isa, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara lafiya." Haka zai ɗauki kayan a boot ɗin mota girma-girma har Abuja, amma tun kafin su isa gidanshi zai yi ma Mal Musa umarnin su fara wucewa gidan Mummy Saudah. Can yake damƙa ma Mummy tsarabar da cewa ga tsarabar ƙauye nan, haka Mummy da Hajja za suyi ta godiya suna saka albarka. Tun kafin ya bar gidan, Mummy za ta kira Zulaikha tayi mata umarnin shiga da kayayyakin kicin. "Tsarabar gida ne Yayanku ya kawo mana, ki rarraba komai ki adana inda baza su samu matsala ba kin ji ƴan matana?" "To Mummy." Daƙyar take iya buɗe baki ta gaisar da Hafiz sannan ta kwashi ledojin zuwa kicin, da yake an ce ba'a raba hanta da jini. Da ganin irin kayayyakin da ke cikin ledojin Zulaikha take gane takanas-ta kano wannan saƙon nata ne daga hannun Innaye. Daɗi ne yake cika mata zuciya, sai tayi murmushi kawai ta cigaba da rarraba kayan zuwa inda suka fi dacewa. Abubuwan ciye-ciye kuma tun kafin ta fice daga kicin ɗin za ta ɗiba ta wanke na wankewa ta kai ma Mummy da Hajja falo. A kwanakinta na farko-farko a gidan, idan Hafiz yaje har ya gama zamansa ya tafi bayan gaisuwa ba ta ƙara yarda wata magana ta shiga tsakaninsu. Sai wata rana da Hajja tayi mata tatas ta umarci taje ta raka ɗan'uwanta gurin mota, haka ta fice ta bi bayanshi tana zumɓura baki. "Hmmm! Komai akai da jaki ai sai ya ci kara. Sai yanzu na ƙara yarda da aka ce baƙauye sai ya shekara arba'in a birni kafin ɗabi'a da al'adun mutanen ƙauye ya bar jikinshi..." "Jaka mai faɗa irinna ƴan daba tana can yanzu za'a tadda ta a gida, da tsinin bakinta irinna jaɓa. Ƙauyanci kuwa naga duk za ni ce ta tadda muje mu, wanda yake gorin shi ma har yanzu ɗabi'a da al'adun ƙauyawan bai sake shi ba tunda ko shekara ashirin baiyi a cikin birnin ba." Tana gama faɗin haka ta wuce fuuuu, ta koma cikin gida ta barshi tsaye a gurin, baki da hanci buɗe don tsabar mamakin irin ƙwarin gwuiwar da Zulai ta samu har ta iya mayar mishi da mummunan baƙar magana irin wannan. Bai ma san ta shige ba, sai da ya dawo hayyacinsa yaga ba ta a gurin. A fusace ya ɗaga ƙafa zai bi ta ya ci ubanta sai kuma ya tuna a gidan Mummy take fa, idan yayi wani mummunan action lallai zai zunguro sama da kara, ƙarshenta Zulaikha ta tona mishi asiri, mutuncinsa na shekara da shekaru ya zube ƙasa war-was a idanun Mummy. Mota ya shige a fusace, ya ɗauki wayarsa ya lalubo tsohon lambar Aunty Balira da a yanzu ya zama mallakin Zulaikha ya danna mata kira, yana fara ringing kuwa cikin sa'a ta ɗaga da siririyar sallama a bakinta. "Ke don ubanki ni kike faɗa ma baƙar magana? Ni sa'an ki ne...?" "Wrong number" Ta katse shi da faɗin haka tun kafin ya aje numfashin maganarsa, kafin ya sake cewa komai ƙit! ta katse wayar. Ko da ya sake kira fiye da sau bakwai na'ura na faɗa masa wayar a kashe take. A fusace ya buɗe motar ya fita ya ƙwalawa direbansa kira, wanda yake zaune acan gurin Maigadin gidan suna hirar rayuwa. A wannan ranar, haka ya isa gida ranshi na ƙuna da raɗaɗi, duk yadda Bintu tayi ƙoƙarin shawo kanshi ta kasa, kuma ya ƙi faɗa mata takamaimai abinda ya ɓata masa rai. A ƙarshe sai kawai yayi mata ƙaryar kanshi ke ciwo, da rawar jiki ta ɗauko mishi paracetamol yasha, sannan ta lallaɓashi ya kwanta, ta daidaita mishi yanayin sanyin A.C ta bashi guri da cewar yayi barci. "Idan ka huta, in sha Allah ciwon kan zai tafi. Allah ya baka lafiya Sweetheart." "Ameen." Ya amsa daƙyar yana cije laɓɓa, kamar da gaske ciwon kan yake yi. Nan kuwa tsabar ɓacin ran kalaman Zulaikha ne da suke ta amsa kuwwa a ƙwaƙwalwarshi kamar bitar karatu. Wannan shi ake cewa baki idan ya san abinda zai faɗa, bai san amsar da za'a mayar mishi ba. Tun daga wannan ranar, bai ƙara gangancin taƙalarta da mummunar magana ba. Sai dai ya ƙara kamewa daga gare ta, idan ya je gidan, ta gaishe shi a gaban mutane yana iyakar ƙoƙarinsa wajen amsawa da sakin fuska. Amma idan zai tafi ta bi bayanshi da niyyar yi mishi rakiya ko kallonta ba ya yi, balle har ta saka ran zai amsa Allah ya tsare hanyar da take mishi. ***** ***** Da gaske ne da ake cewa babu wani al'amari da ya gagari bawa ya koya, sai dai idan tun asali shi wannan bawan bai saka a ranshi yana so ya koya ba. Zulaikha da ta saka ma ranta kuma ta ƙwallafa zuciyarta tana so lallai ta koyi turanci, sai ga shi a cikin watanni biyu an shiga na uku sosai bakinta ya faɗa da turanci. Bayan ƙoƙarin koyarwa kuma a sauƙaƙe da makarantar online ɗin da Karima tayi mata register suke da shi. Mummy, Karima, Imam sun taimaka mata ƙwarai gurin faɗawar bakinta a iya magana da turanci, domin gaba ɗaya suka daina yi mata magana da Hausa, sai turanci. Tun tana fahimta kaɗan-kaɗan, suna fassara mata manyan kalmomin da suke amfani da su a jimlolin maganganunsu. Wata kalmar kuma idan ta gani ko a kafar sadarwa a google take searching ta ga ma'anarta da Hausa. Daga nan fa ta kafa ma kalmar ƙahon zuƙa kenan har sai ta haddace a ƙwaƙwalwarta. Yanzu dai a gidan idan aka ji tana hira da hausa tana ƙyalƙyala dariya da Hajja ne kaɗai. Sauran mazauna gidan idan tana so suyi dogon hira dole sai da turanci, tun tana kwaɓo jagwalgwalo suna dariya, a haka har bakinta ya goge da iya turancin. Da gaske ne fa da aka ce da babu makoyi gwani ma da ya ji kunya. Zulaikha dai ta dage da koya, kuma Alhamdulillahi ta ɗauko hanyar zama gwana. Ta inda rayuwarta yake burge mazauna gidan shi ne, ba ma turanci kaɗai ba, abubuwa da yawa waɗanda bata iya ba a baya, yanzu ka'in da na'in ta dage da koyonsu. Rayuwarta ya ɗauko hanyar canjawa gaba ɗaya, ta fara zama wata ƴar gayu kuma ƙasaitacciyar mace ta musamman. Komai na ta ya canja, hatta yanayin yadda take magana yanzu a ƙasaice kuma cike da yanga da nutsuwa take yi. Saboda kuskure ƙalilan za tayi Karima ko Mummy su gyara mata, ita kuma da hanzari take karɓar gyaran tayi godiya. Yawan zuwan Hibbah gidan akai-akai. Da kuma yadda take ɗaukarta a mafiyawancin lokuta tana raka ta guraren sana'arta, ko babu Karima a gidan Mummy bata cika hana fitar ba, saboda ta yarda da nutsuwar Hibba da kamun kanta. Wannan yawan fitar, tana haɗuwa da wayayyun ƴanmata iri-daban-daban, shi ma ya ƙara taimakawa ƙwarai da gaske gurin gogewarta. Abun daɗin shi ne har yanzu bata yarda ta zubar da kyawawan halayenta na koyi da addininmu ba. Duk wani abu da za tayi addini shi ne gaba, kafin aikata komai. ***** ****** "Daddy pls kar ka yanke wayar, ga Aunty Zulai ta shigo ku gaisa." Imam bai jira amincewar uban ba ya ruga a guje ya kamo hannun Zulaikha da shigowarta cikin falon kenan da waya maƙale a kunnenta, tana magana tana sakin wani lallausan murmushi. Ita da Mashkura ce a wayar, wacce da farko kamar zumuncin nasu zai yanke bayan barin Zulaikha gidan, saboda tsoron abinda zai je ya zo kasancewarta ƙanwar Bintu. Shi yasa Zulaikha ta so yanke duk wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ita. Amma saboda naci irinna Mashku, duk yadda Zulaikha take ƙin ɗaga wayarta ita kuma ba ta taɓa gajiya da kira ko nuna ɓacin ranta ba har dai ta gaji ta sakar mata. Suna gaisawa da zumunci ta waya sosai da sosai, tunda har yanzu da take cikin wata na uku a Abuja ta ƙi yarda Mashkura ta san gidan da take zaune. "Oyoyo Aunty Zulai." Imam ya faɗa cikin karaɗin murna sannan ya rungumeta kamar sun daɗe basu haɗu ba. Riƙe shi tayi ita ma tana dariya fuskarta na nuna jin daɗin ganinshi ƙarara. Da harshen turanci take tambayarsa yaushe ya dawo gidan? Ina tsarabar makaranta da ya kawo mata? "Tsarabarki na nan ta musamman Aunty Zulai. Ga Daddyna can ya kira Vidio call a wayar Granny, zo muje ku gaisa. Pls yau ma kar ki ce a'a! Pls... pls... pls Aunty Zulai... ba don shi ba don ni kaɗai." Ya ƙarasa mata magiyar a marairaice, lokaci guda kuma yana ɗan jan hannunta zuwa inda wayar take ajiye akan kujera. Kamaluddeen, babban ɗan Mummy Saudah kuma baban Imam, wanda ziyarar aiki na tsawon watanni shida ya kai shi ƙasar Gambia. Watanninshi biyu acan ƙasar Zulaikha ta zo gidan, har izuwa yanzu da yake wata na biyar acan ƙasar ko sau ɗaya bai taɓa gaisawa da Zulaikha a waya ba. Sai dai yana ganin hotunanta jefi-jefi a status ɗin ƙanwarsa Karima. Sannan labarin Aunty Zulai a bakin Imam ɗan shi sai dai idan bai kira a waya an haɗa shi da yaron ba. Tun yana kore hirarta daga bakin ɗan har ya haƙura, domin matuƙar yana so hirar shi da yaron yayi tsawo to kashi biyu cikin uku na hirar labarin Aunty Zulai da irin yadda take kula da yaron ne. Idan ya zauna shi kaɗai har mamaki yake yi, na yadda a cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa mai girma ya shiga tsakanin Imam da Aunty Zulai amma bai shiga tsakanin yaron da Safina da ta kasance ƙanwa a gurin marigayiya Aisha mahaifiyar Imam ba. Yau dai haka kawai, shi da kanshi ya ji a ransa lallai ya kamata ya ga Aunty Zulan nan ya gaisa da ita. Sannan yayi mata godiyar irin kulawar da take ba yaronsa, ko a ɓangaren Haddar karatun Alƙur'ani mai girma na yaron da a baya yake tafiyar wahainiya, amma a yanzu ba ƙaramin nisa yayi ba, abin mamaki har ya kusa haɗa izufi goma cif a kansa. Ko da uban ya tambayeshi ya akai haddarshi take sauri yanzu? Kai tsaye yaron ya faɗa mishi Aunty Zulai ce take ƙara mishi, kuma tayi ta maimaita mishi cikin nutsuwa da lalama har sai ya haddace. Duk diramar da yake gudana tsakaninta da Imam na yadda yake ƙoƙarin janyo ta zuwa gurin wayar ita kuma tana tirjewa, tana ba shi wasu ƙananun uzurirrika marasa muhimmanci yana jin su. Amma ba ya hangen fuskarta sosai sai gefen kafaɗunta. Shi kaɗai ta cikin wayar, babu abinda yake yi sai murmushi. "Haba Aunty Zulan Imamu. Kiyi haƙuri mana don Allah, yau dai ɗaya ki gaisa da Baban Imamu shi ma yaga wacece Auntyn Imam." Mummy da take zaune acan kan dining ta saka baki don kawo ƙarshen taƙaddamar da ke tsakanin Imam da Zulaikha. "To Mummy." Zulaikha ta amsa a kunyace, don bata san Mummy na zaune a falon ba. A kunyacen dai ta bi bayan Imam da har lokacin ya ƙi sakin hannunta har suka ƙarasa kusa da wayar. Daƙyar ta iya ɗaga kai ta saci kallon fuskarsa, wani kwarjini da haiba sosai da yayi mata a idanunta yasa babu shiri ta zube a ƙasa ta fara gaishe shi a daburce. "Ina yini...? Au! Ina kwana...? Lah! Yi haƙuri... Good evening." Ta ƙarasa maganar a tsorace da tunanin kila ma ba ya jin hausa. Da wani irin tattausan murya mai tafe da zallar kwarjini da mazantaka ya fara magana, har lokacin murmushin da yake yi bai bar kan fuskarsa ba. "Aunty Zulan Imam! Barka da yamma. Ai ni ya kamata in gaishe ki, saboda ƙoƙarin da kike yi wajen jure surutun Imam. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi." "Amin. Nima na gode." Ta amsa a kunyace sannan ta tashi da ɗan gudu-gudu har tana harɗewa ta wuce ɗakinta. Mummy da Kamal suka bi ta da kallo fuskokinsu cike da murmushi. Shi kuwa Imam me zaiyi in ba ƙyalƙyala dariya ba. Tun daga wannan ranar, bata sake yarda gaisuwa ta waya ko ta Vid call ya shiga tsakaninta da Baban Imam ba. Don a yadda take ji a zuciyarta kamar ma tsoronshi take ji, shi yasa sawunta a likkafa da ta ga an fara gaisawa da shi za ta zame ta gudu zuwa ɗakinta. ***** ****** [2/3, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: "Sweetheart?" Ya kira ta a tausashe. Siririyar hamma ta sake, cikin saiɓi da mutuwar jiki ta sake gyara kwanciyar kanta a ƙirjinshi. "Na'am...My Dear." Ta amsa aɗan shagwaɓe. Lallausan gashin kanta ya cigaba da shafawa, yana mata waiwayi sannu a hankali. Kamar bazai yi magana ba, can kuma sai ya ce "Jibi idan Allah ya kaimu, ki shirya da wuri. Tare za mu tafi Faƙo..." Da saurin gaske ta ɗago kanta tana kallonshi cikin ido, sai kuma tayi laƙwas! Ganin shi ma kallonta yake yi, yana karantar yanayinta. Saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa tayi a hankali, sai kuma ta mayar da kanta ƙirjinsa ta kwantar, duk a ƙoƙarinta na danne maɗaukakin tashin hankalin da yake taso mata. "Aadil just 4 month yake da a duniya. Ba ka tsoron muyi doguwar tafiya da shi ya kwashi iskar hanya? Ka san mura a jikin jarirai fa, yanzunnan sai ta zame musu Nemonia..." "Babu abinda zai faru in sha Allah! Za mu tafi tare da shi, kuma mu dawo lafiya. Ki tuna fa yaushe rabonki da Faƙo? Tun bayan haihuwar Aunty Balira, to ga Babyn nata nan har yayi 2years. Duk irin jinyar da Innaye baki samu kin je gaisheta ba saboda laulayin ciki. An haifi Aadil har yau Innaye bata taɓa ɗaukar gudan jinina ba balle ta saka mishi albarka. Jibi tare za mu tafi tabbas, ku shirya da wuri." "To shi kenan! Allah ya kaimu." Ta amsa da sanyin jiki, duk zuciyarta a ƙuntace. Amma ba ta da yadda za tayi ta nuna mishi, saboda ko kaɗan ba ta ƙaunar abinda zai sake janyo wani saɓani ko misƙala zarratin a tsakaninsu. Shiru suka yi duk su biyun, kowa da irin mabanbantan tunanin da yake yi a zuciyarsa. A haka barci ya kwashe su. Washe gari da yamma, bayan sun dawo guraren aikinsu, suna zaune a falo suna hira. Tana zaune a gefensa, Aadil na riƙe a hannunsa yana mishi wasa, yaron kuma sai dariya yake yi, da alamun ya fara gane fuskar Babansa. A tausashe ya kalleta ya ce "Gobe idan muka je gida, duk irin magana ko tambayar da za'a yi miki game da Zulai ki amsa musu da to kawai, ki kuma tabbatar musu muna zaune lafiya ƙalau. Kin gane?" "Eh!" Ta amsa, ba don ta gane ɗin ba. "Good. Duk da tun bayan faruwar al'amarin har yau bamu zauna ni da ke na warware miki yadda al'amuran suka faru ba, domin a ganina sam hakan ba shi da wani amfani, tunda dai matsalar na riga na maganceta. Amma na san a wancan lokacin Raudha ta yi miki bayani kamar yadda nayi mata, ko ba haka ba?" "Haka ne." Ta amsa, a zuciyarta take sake tunano cikakken bayanin da Raudha tayi mata wancan lokacin, wanda har yayi sanadiyyar zubda makaman kishinta, hankalinta ya kwanta luf kamar tsumma a randa. "Madallah! To ko bayan da na magance matsalar har yanzu su Innaye basu san takamaimai halin da ake ciki ba. Akwai lokacin da na tsara zan musu cikakken bayanin komai, yadda ransu bazai ɓaci da ni ko ke ba, amma ba yanzu ba. Don haka gobe idan mun je ki kama bakinki, kar ki kuskura ki bada wata kafar da zai sa su gane akwai matsala tsakaninmu da Zulai. Kin gane ko?" "Eh" Ta amsa a sanyaye. Shiru yayi yana cigaba da yi ma ɗanshi wasa. Can bayan wasu daƙiƙu ta matsa kusa da shi ta rungume shi ta gefen kafaɗarsa. "Na gode My dear... Na gode. Ina roƙon Allah yabar ƙauna da tabbatacciyar soyayya a tsakaninmu. Da ace a wancan lokacin baka ɗauki matakin da ya dace ba, na tabbata da yanzu na daɗe a kushewata..." "Shshshshhhhhhh! Kar ki sake faɗan irin wannan maganar." Ya katse ta da sauri, jin tana zancen mutuwa. "Na daina Daddyn Aadil. Allah ya huci zuciyarka." Bai amsa ba, sai lallausan murmushi da ya sakar mata, kafin ya mayar da hankali kan Aadil yana cigaba da yi mishi wasa. ***** Washe gari da sassafe suka kama hanyar tafiya Faƙo kamar yadda suka tsara. Saboda a ranar yake so suje su dawo. Bayan motarshi shaƙe yake dam da tsaraba, saboda a wannan karon ba tsarabarsa bace kaɗai, har da zannuwan da Bintu ta lodo da sunan za tayi tsaraba wa su Innaye. Wani irin shirin jibga-jibgan kayan sanyi da Bintu tayi ma Aadil shi kaɗai ya isa abin dariya. Amma a zahirin gaskiya kayan ta saka mishi ba don iskar hanya bane, ta saka mishi ne duk a ƙoƙarinta na kiyaye yaron daga kwasar cututtuka saboda ɗaukar da take tunanin zai sha a hannun mutanen gidansu Hafiz. Da yake gudu sukai ba na wasa ba, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi ta yi musu ne a ƙofar gidansu Hafiz na ƙauyen Faƙo. Wani sauƙi da Hafiz yake ganin sun samu shi ne taron sunan Balki, ƴar ɗakin Umma laraba da ake yi anan gidan Baffan. Haihuwar fari ce, kuma ta zo mata da gardama. Shi yasa tun daga can asibiti kai tsaye gidan iyayenta aka dawo da ita domin ta samu ingantaccen kulawa. Yau ta kama suna, don haka sun tarar da gidan Baffan ne damƙam da ƴan'uwa da abokan arziki, wanda hakan ko kusa baiyi ma Bintu daɗi ba, domin ta san jagwalgwalon da Aadil zai sha a hannun mata ƴan ƙauye sai ya ninka wanda tayi tsammanin zai sha da farko. Motar na fakawa, kafin ma tayi yunƙurin saka yaron a ɗan abin ɗaukarsa mai kama da kwandon ɗaukar jarirai ta kulle shi har Hafiz ya ɗauki yaron daga cinyarta. Ya buɗe mota ya fice waje sannan ya saɓa ɗan a kafaɗarsa "Fito muje. Kin ga na manta yau ake sunan Balkin Umma Laraba. Kin ga shi kenan ma mun samu sauƙi, ba sai munyi ta jelar zuwa gidajen ƴan'uwa a gaisa ba. Na san duk za mu tarar da su a nan gida." "Haka ne." Ta amsa daƙyar! Tana jin yadda bakinta ke wani irin ɗaci kamar ta tauna flagyl. Tun kafin su shiga cikin gidan, har labarin isowarsu ya riga isa cikin gidan. Ko kafin Bintu ta fito daga cikin mota har wasu daga cikin ƴan'uwansu sun lulluɓe jikin motar suna yi musu barka da zuwa. "Yauwa... Sannunku. Labaran, Inusa, ina su Kadiri? Ku zo a buɗe muku boot ku kwashi kaya ku shiga da su cikin gida." Ya faɗa da fara'a sosai a fuskarsa, idanunsa na kan ƙannensa maza da yayi ma umarnin kwasar kaya. "Hafizu? Ina Zulai? Baku taho da ita ba?" Indo ta tambaye shi bayan ta ga Bintu ce kaɗai ta fito daga cikin motar, kuma ta rufe ƙofar ba tare da ta ga fitowar Zulai ba. Kafin ya amsa ma Indo ƙanwarsa Halima ta miƙa hannu da nufin karɓan Aadil, nan take kuwa ya sakar mata shi ba tare da wani damuwa ba. "Oyoyo Babanmu! Tubarkallah ma sha Allah! Kai ne haka kayi kukkuɓeɓe barakallah? Hajiya Bintu sannunku da zuwa." Bata jira amsawar Bintu ta take ta ƙoƙarin haɗiye wani gululun takaici da ya tsaya mata a wuya ba ta wuce da yaron cikin gida. "Zulai tana gida Indo, ban zo da ita ba. Ai ita da zuwa gida sai ta yi wata shidda cif a ɗakin aurenta. Idan ba na manta ba haka Baffa ya saka doka ga duk ƴaƴansa mata da suka yi aure, kin ga bai kamata a karya dokar daga kanta ba." Kafin ma Indo ta amsa nan take sauran ƴan'uwa da suke gurin suka fara yi mishi surutun wannan ai wayau ne. Tunda ita Zulai ɗan gida ta aura ai ko bayan sati biyu ne da yin aure za ta iya zuwa gida. Shi dai bai sake cewa komai ba sai dariya da yake ta bin su da shi, har suka shiga cikin gidan. Bintu na biye da su a baya ranta na ƙara ɓaci, ganin yadda da yawansu suka nuna kamar basu santa ba, babu irin wannan ɓare-ɓaren da rawar jikin da suka saba yi mata acan baya idan tazo garin. Yanzu ta ɗan'uwansu da ƴar'uwarsu kawai suke yi, ga ɗan laɓuɓun ɗanta kuma an ɗauke shi an shige da shi cikin ƙauyawa, salon ya shaƙi numfashi mai cike da cututtuka irin wanda bai saba shaƙa ba. Ƙasa-ƙasa taja tsaki, tana ƙara haɗe fuskarta, a haka har suka shiga gidan suna gaisawa da mata ba ta da wani walwala har suka ƙarasa ɗakin Innaye. Bayan mitar da ƴan'uwa suka yi ta mishi na rashin zuwa da Zulaikha, har a fuskar Innaye sai da ya fahimci rashin jin daɗinta da bata ga Zulai a tare da su ba. "Auta ita kaɗai kuka baro min a gida kenan Fatima?" "Ba ita kaɗai bace Innaye. Akwai ƙanwata Mashkura. Kuma Daddyn Aadil shi ya ce baza ta biyo mu ba sai ta cike wata shida, saboda kar Baffa yayi faɗan zuwanta gida." Bintu ta faɗi maganganun a ɗarare, kanta a ƙasa, tana jin yadda kaifafan idanun Innaye masu cike da kwarjini suke yawo a sassan jikinta. Aunty Rakiya da Aunty Ladidi kuwa ƙarara suka ce mishi ai dama bai zo da Bintu ba. "Saboda Allah Hafizu kana sane da yadda duk muke ɗokin ganin Zulai, amma kawai sai ka wani zo da Bintu ita kaɗai?" Cewar Aunty Ladidi tana kyaɓe baki. Aunty Rakiya ce ta karɓe zancen da cewa "Ita ma Bintun da tayi zamanta. Yaushe rabonta da garin? Ni Wallahi na zaci ma ta yanke da zuwa kenan. Zulai da take ƴar nan dai na san baza ta taɓa ƙin zuwa ba ko da za su zo kullum! Amfanin auren na gida..." "Ke dallah rufe mana baki. Bana son shirme, kuje ku kawo musu kunun zaƙi mai sanyi kafin a ƙarasa abinci." Aunty Balira ta katse su fuskarta a ɗaure. Sum-sum suka fice suna guna-guni, Hafiz ya bisu da kallo ƙasa-ƙasa, zuciyarsa duk ba daɗi da yadda aka karɓi Bintu. Bayan kuma a ganinshi rashin zuwanta laifinshi ne, tunda da ya matsa mata tazo, tabbas za ta zo ko da zuciyarta ba ya so. Balle ma ya san Bintu baza ta taɓa ƙin asalinshi ba. Bintu da take ta rarraba idanun ta ina za'a miƙo mata ɗanta fiye da awa ɗaya sai ga shi an kawo shi yana ta tsala ihu. Hankalinta a tashe, ko ta manta a inda take ne? Ta miƙe zumbur tana zare idanu, da saurin gaske ta miƙa hannu ta karɓe shi tana ɗan dudduba jikinshi "Me aka mishi ne haka yake kuka? Sam bai taɓa irin wannan kukan ba tunda na haife shi..." "Wannan ɗan yalolon jinjirin me kuwa za'a mishi a gidan Kakanninshi?" Aunty Balira ta katse ta da sauri, daman tana cike da ita ganin yadda tun ɗazu ita kaɗai take ta wani ciccin magani kamar wacce aka tilastawa zuwa. Da Hafizu kaɗai suke hira da Innaye. Jin irin tambayar da Aunty Balira ta gwaɓa mata yasa ta dawo hayyacinta, lokaci ɗaya tayi laƙwas, ta koma gurin zamanta tana jijjiga yaron. "Bai wuce zafi ne ya dame shi ba saboda uban kayan sanyin da kika jibga mishi bayan ba wani sanyi ake yi ba. Ki rage mishi kaya, ki bashi ruwa da nono zaiyi shiru." Hafizu dai kanshi na ƙasa, a kunyace da irin rashin karar da Bintu ta nuna a gaban Innaye. Duk da bai wani ga laifinta ba, ko shi hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba da jin irin ihun da ɗan ke callarawa tun kafin su iso ɗakin. Baiken Bintu ɗaya da ya gani shi ne rashin nuna kara a gaban Innaye da Aunty Balira. Wannan ziyara dai ba Bintu kaɗai

Chapter 21 of 40